Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

abin da ya kamata a bar ta ta haihu, ni kuma zan zo na dauke gudan jinina na kai garinmu."

"Me kake so ka ce?"

"Eh ina so nace maki ni Sadik Wizzy ina son abina. A bar min ciki ta haihu na karɓi abina."

Mami ta yi shiru tana nazari. Idan har Ummita ta haihu ya karɓi abin da ta haifa watarana asiri zai tonu, ita kuma ta rantse ta gwammace gwara abin da za ta haifa din ya mutu da dai wannn gurguwar shawarar ta Wizzy.

"Ya ne wai kika yi shiru Hajiya? Ba ki ji nace maki ina son abina ba? Toh ina son abina, duk wanda kuma ya yi yunkurin aika shi lahira nima zan sanya shi dogon bacci. Ina fatan kin fahimta? Idan na karɓe abina ba sai ta je ko uwar ina za ta je ba mu raba gari?"

Zufa sosai ya rufe Mami, gaba daya kanta ta ƙulle ta kuma rasa mafita. Dole haka ta amsa da toh suka yi sallama.

***

*LITTAFIN NAN NA KUƊI NE. SIYA AKAN NAIRA ₦400 KI KARANTA BA TARE DA SHIGA HAKKI BA.*


*5407827015*
*FCMB*
*Farida Abdullahi*

09034973645



Ganin lamuran bana ƙare ba ne, ya sanya a dole suka rungumi ƙaddarar cikin Ummita. Babu yanda suka iya don a gaban idanunsu an yi dukkan wani kokari don a zubar amma hakan bai yiwu ba. Hankalin su Abba da ma kansu su Humaira ya ɗan kwanta ganin yadda Ummitan ta samu nutsuwa don sosai take kokarin ɓoye nata damuwar saboda samarwa ƴan uwannata nutsuwa musamman Mubarak wanda kullum kokarinsa ya kyautata mata. Shi ne siyo banza siyo wofi, kunna mata fina-finai a wayarsa da ma bidiyon sanya nishadi da dariya, tun ba ta dariyar har ta zo ta ɗan soma murmushi. Ranar da abin ya ishi Mami sai da ta tunkari Abba a siyasance tana ba shi shawarar ya dace Mubarak ya dinga fita kasuwa kafin lokacin da zai tafi bautar ƙasa. Abban ya nuna hakan daidai ne sai dai ya kara da fadin.
  "Amma na so ace ya hakura da kasuwarnan ya cigaba da daukewa yar uwarsa hankali ta hanyar hirar da yake taya ta. Naji dadi kwarai da na ga murmushin fuskarta jiya, na kuma sani hakan yana da alaƙa da shi. A duniya yanzu bani da burin da ya wuce na ganin farin cikin yarinyarnan. Ina kuma cike da fargabar yanda yan uwan Mahaifiyarta za su karɓi batun cikinta."

Wannan magana ta Abba ko a fuska ba ta yiwa Mami ba. Ta fakaici idanunsa ta watsa mishi harara sai kuma da ta ga ya kalleta ta gyara fuskar sosai kai ka ce gaba daya damuwar duniyarnan ita aka ɗorawa.

"Ni kaina hakan yana yimin dari bisa dari, sai dai kuma hakan fa ba mai ɗorewa ba ne tunda wataran din dole ne ya wuce bautar ƙasa. A yi hakan dai yanzu, na maka alkawarin in sha Allahu zan tsaya tsayin daka wajen ganin ba ta faɗa cikin ƙuncin baya ba. Ga yar uwarta Humaira ma kullum tana nan tare da ita."

Sai da ta ambaci Humaira sannan Abba ya ce.

"Af, kinga zan manta, mun yi magana da iyayen Fadeel, mun kuma yanke nan da watanni shida zuwa sadda shi Fadeel din ya kammala gini za a tsaida zancen aurensu."

Wani irin jiri ya nemi kwasar Mami daga zaune, ta hadiyi miyau sannan cikin yaƙe ta ce.

"Wannan abin farin ciki ne sosai Abban yara, amma kuma ba ka ganin kamar zai zama mun zalunci yarinyarnan? Har wannan lokacin fa Humaira ba ta kula shi, ba ta kaunarsa."

Abba ya dan daure fuska.

"Bar ja'irar yarinya marar wayo. Ai ba ita ta haife mu ba. Ni na gaji da wadannan mugayen dabi'unnata na korar samari da wulakantasu. An kawomin ƙararta ya fi a ƙirga, a yan watannin nan da fitowarsu dalilin da yasa ban tayar da maganar manemanta ba saboda halin da yar uwarta ke ciki ne, amma ko sati ba a yi ba akwai wanda ya same ni bayan na fito daga masallaci cewa ɗansa ya gani kuma yana so. Hakuri dai na bayar. Ni ba zan biye mata ba. Aure ne dai sai ta yi, idan ba ta son shi Fadeel din ta zo ta kawo wani."

Tsaki Mami ta ja a ƙasan ranta, kamar ta shaƙo wuyan Abba haka ta ji. Kamar yanda ta saba kuma sai ta shanye bacin ran, fuskarta a ɗan daure ta ce.

"Aa fa Abban yara, nikam ba wanda zan yarda ya yiwa ɗiyata dole. A dai bi abin a sannu. Yanzu dai ya muka kwana batun kai ta wurin mai magani."

Girgiza kai Abban ya yi, wato dai Mami ba ta taɓa ganin laifin ƴaƴanta.

"Duk sadda ku ka shirya zuwa Mamin Humaira, ni mene nawa a ciki zan mata dole ta je ne?"

Ya fadi cikin gatse da kuma zolaya hakan sai ya ba Mamin dariyar da bai kai ciki ba, ta ɗan dara ɗin tana mai farr da idanunta.

"Naji din, ko ma me za ka ce hakan ne kawai. Yau dai muna da baƙi, yaran Abba zasu kawo mishi ziyara. Zuwa gobe sai muje."

Abba murmushin shima ya yi, ya gane Tasleem da Futuha take nufi.

"Toh Allah ya kawo su lafiya."

Ta amsa da amin.

Humaira ce ta yi girkin gidan a ranar, ta dawo da aikinta tuƙuru na shiga kicin ganin hakan yana ɗebemata dukkan damuwa sai dai kuma har gobe masu neman ta karɓi odar su ta kasa, ko Mami ba ta sanarwa ana neman odar abinci ba saboda a ganinta ba ta da nutsuwar da za ta yi abin da ya dace.

Bayan ta kammala komai ta zuba a kuloli, ta bar Ladidi da gyaran kicin din ta koma nasu dakin. Kamar dama jira yake, sai ga waya ta shigo. Koda ta duba Fadeel ne, wani irin ɓacin rai ta ji ya danne wani sashi da ke kokarin sanyayamata rai, ta kasa fahimtar yanayin da take ji akan Fadeel tamkar dai guda biyu ne. Farin ciki da bakin cikin da ya danne wannan farin cikin. Babu walwala ta amsa da sallama. Shima ya amsa sallamarta.

"Ina fatan ban takuraki ba? Fatan kuna lafiya?"

Ta tsuke baki, tsiwa take son ace ta yi amma sai ta ji tamkar wani ɓangare na zuciyarta na kwaɓarta. Ta kai duba ga Ummita da ke kwance idanunta a kan Humairar. Sai ta ji dagaske ta kasa tsiwar a gabanta don haka murya ciki-ciki ta amsa.

"Lafiya muke. Fatan kaima haka?"

Daga ma muryarsa za ka fahimci ya ji dadin yanda ta amsa ba kwanaki da take balbale shi da faɗa da bakaken maganganu ba, shi kuwa bai ma san zafi biyu ne suka hade mata a baya ba, ga na halin da cikin jikin Ummita ya jefata, ga kuma na wani ciwon kai da bacin rai da muryarsa ke haifar mata marar dalili.

"Lafiya kalau nake. Ina neman ɗan wata alfarma wajenki Boddo."

Sarai ta san me yake nufi da wannan sabon sunan da ya raɗa mata, wato kyakkyawa. Sai ta zaɓi ta basar ta hanyar fadin.

"Ina jinka."

"Zan iya shigowa mu gaisa?"

Ta ɗan yi jim, ba komai take tunawa ba sai zuwansa na karshe a watannin baya da har Mami ta ji babu dadi. Yanzu idan ta ce ya zo kuma fa? Ta ji wani abu na tafasa zuciyarta, bakin cikk na saukar mata da ba ta san na mene ne ba. Wani bangare na jan ta da kokarin ta furta ya zo din, amma wani bangaren na kwaɓarta da nuna ta tsane shi, ta tsani ganinsa to me zai zo ya yi mata?

"Toh."

Ta ji lebbanta kawai sun ba da wannan amsar. Shi kansa sai a ya ji wani shock don bai zaci wannan amsar zai ji ba. Ya yi makamancin tambayar ya fi a ƙirga amma kullum amsar aa, karshe ma ta kashe wayar da hujjar ya dame ta.  Ya yarda addu'a tabbas na tasiri akan Humaira, don duk sadda ya dage iya dagewa a kan lamarinsu sai ya ga sauyi tattare da ita, ya kuma soma yarda da hasashen Hannatu kanwarsa da kafin ta koma Yola da ta ji irin yanda Humairar ke yi da komai ta ce ba yin kanta ba ne a nema mata magani.

"Nagode Boddo, sai na shigo."

Yana fadin haka ya katse kiran, itama Humaira ba ta ce komai ba ta sauke wayar daga kunnenta. Ta dubi Ummita da ke kallonta cikin murmushin da ba ta san dalili ba.

"Mene ne?"

Ta tambaya. Ummita ta girgiza kai.

"Ba komai, ina dai ganin wani abin mamaki ne a saman fuskarki. Idan ban yi karya ba kina mutuwar son Fadeel amma na rasa meke danne wannan son."

Humaira ta dan harareta da wasa.

"Ni ba sonsa nake ba. Mu bar zancen don Allah kafin raina ya ɓaci."

Murmushin dai Ummita ta ƙara yi, ba ta ce komai ba ta lumshe idanu tana ci gaba da jan carbin dake hannunta. Ita kadai ta san tunanin da take yi, Humaira ta dube ta. Tausayinta sosai ta ji, Sahabi har ya gaji da zuwa hira don ba fita take ba, hakanan ta daina daukar wayarsa. Kullum zancenta guda daya ne, ba za ta yaudari Sahabi ba, ta fi kaunar ya san ita din ta haramta aurensu koda kuwa bayan ta sauke nauyin cikin dake jikinta ne. Ba za ta aure shi ba sam. Ba ma za ta yi auren a duniya ba kamar yanda ta ke faɗamusu a yanzu.

Shigowar Raihana ɗakin ne  da sallama ya sa Ummita bude idanun, itama Humaira ta kauda dubanta daga gareta zuwa ga Raihanar. Wannan ne ya katse tunanin dukkansu.

"Mami ta ce ku fito ku gaisa su Tasleem sun zo."

"To." Shi ne amsar da Humaira ta bayar ba don tana kaunar ganinsu ba domin ta gama sanyawa a ranta su din ba masoyansu ba ne. Ba kuma zasu kaunace su ba har gaban abada. Sai da Raihana ta kara maimaitawa sannan Humaira ta mike, Ummita daman tuni ta yi gaba. Cikinta bai da girma bai fito ba.

Tasleem wacce daga makaranta ta shigo gidan sanye take cikin uniform dinta ga tirtsetsan cikinta dan watanni takwas sai faman taunar aya take yi suna hirar makarantar da Mami, watanni shida kawai ya rage ta kammala karatun gaba daya. Ba ta yi ko mintuna uku ba sai ga Hajiya Futuha ta shigo tana ta faman shan ƙamshi. Tasleem ta harareta ta gefen idanu ta kauda kai tana ɗan huci, fatar Futuha ta kara kyau kamar ka taɓa jini ya fito, kamshin turarenta kuwa ya buɗaɗe falon gaba daya. Ƙasim na rike da jakarta yana take mata baya, babban burinsa shi dai ta ba shi na kashewa.

Yassar ya dube ta.

"Ka ga manya matar Alhaji naku daban da nasu. Irin wannan ƙamshi haka? Gaskiya zan zo a sammin turaren."

Ta karaso ta zauna jikin Mami tana dariya.

"Har ka bani kunya ɗan uwa. Idan dai turare ne, ko direba zan aiko ya kawomaka na siyo su kala-kala a Dubai."

Aka sa dariya Dawud na fadin.

"Inyeee! Ka ga Hajjaju mutan Dubai."

Mami dake murmushin jin alfahari ta ce.

"Ya ishe ku hakanan toh."

Tasleem dai ba ta tanka ba sai dariyar yaƙe kamar bakinta zai rabe biyu amma ƙasan ranta ji take tamkar ta kurma ihu.

Shigowar Ummita da su Humaira ya sanya hirar ta tsagaita, suka gaishe su, Futuha ta amsawa Humaira faram-faram don tsakani da Allah so take ta wuce da ita gidanta ko don girki. Tana da mai aiki amma ko kusa ba ta iya abincin da Alhaji Yakubu ke so ba kullum sai ya yi mita wannan dalilin ne ya sanya take son tafiya da Humaira gidan koda na kwanaki ne ta nunawa yar aikinta yanda take sarrafa tukunya.

"Humaira sannu, bayin Allah har kun dawo hayyacinku wallahi."

Fadin Futuha, sai kuma Raihana ta sanyo wani zancen gudun kar a tada abin da zai sosa musu inda ke ƙaiƙayi. Yassar da sun riga sun samu labarin komai kuma har a zuci ba su yi farin cikin ƙaddarar cikin Ummita ba sai ya sanyo hirar abinci yana kiran a kawo a ci ya kwaso yunwa daga kasuwa. Tasleem kuwa ƙuri ta yi da idanunta akan Ummita ba ta ko ƙiftawa musamman ma da Ummitan ta mike tsaye ta sauya wurin zama. Da ta kammala tabbatar da zarginta sai ta ga ta nan a tsaye ta miƙe har ayar da take ci na zubewa a saman kafet.

"Kut! Me nake shirin gani Mami?"

Ta yi furucin har a sannan idanunta na kan Ummitan. Gaba daya suka dube ta, Ummita kuwa ganin idanun Tasleem a kanta ya sanya ta ɗago me take son fadi, wato dai itama ta gane tana da ciki don haka sai ta mike da sauri-sauri ta shige daki saboda kukan da ya tahomata na tsantsar damuwa.

"Me aka yi kike mana ihu? Ita kuma wannan me aka yi mata ta miƙe?"

Futuha ta jero tambayoyinta lokaci guda.  Tasleem ta cafe zancen tana kara hura hancinta da ya buɗe saboda ciki.

"Ciki na gani jikin yarinyar nan."

A razane Futuha ta buɗe idanunta ta dubi Humaira da kuma Raihana sannan ta maido hankali ga Tasleem.

"Wa kenan?"

"Ummita mana. Mun shiga uku, shikenan yarinyarnan za ta ɓata sunan gidanmu, image din gidanmu zai lalace a idanun duniya. Meyasa ba a zubar da cikin ba Mami?"

Humaira wani tururi zuciyarta ke yi na ɓacin rai, wato ita Tasleem ba ta ko tausayawa halin da Ummitan ke ciki ba balle tayata jimami. Kamar ta tofa sa kuma albarkacin Mamin dake zaune a wurin ta ja baki ta kuma zuba idanu ga Mamin don ganin me za ta ce. Mami kuwa ta gefen idanu ta ga irin duban da Humaira ke mata don haka nan da nan ta daure fuska.

"Idan ita ba ta ɓata mana suna ba, ke gashinan ai kina ihun da makwafta za su ji su fahimci halin da muke ciki! Wannan wane irin rashin tunani kike aikata mana? Kina haukar tonawa yar uwarki asiri?"

Jin haka sai Tasleem ta koma ta zauna, ta ja guntun tsaki ba ta ce uffan ba. Ita wannan duk bai dameta ba kamar yanda kawayenta da dangin miji da ma abokan hulda da ake kunya za su samu labarin cikin Ummita ya zamar musu abin habaici da zagi. Futuha kuwa, babu abin da take hangowa sai irin yanda labarin zai karaɗe social media alhalin ta gama karaɗe ko'ina da nuna hotunan su Ummita tana shaidawa duniya su din kannenta ne. Yanzu idan zancen nan ya fita ai ta shiga uku.

Yassar ne ya basu labarin duk fadi tashin da aka yi don ganin an zubar amma abu ya faskara. Tasleem ta ja tsaki karo na biyu.

"Ba dai abi hanyar da ta dace ba. Ni wallahi da tun farko an faɗamin da kaina zan zo na yi mata alluran da na tabbatar sai cikin ya zube. Amma yanzun ma ai ba ta ɓaci ba, me zai hana a markaɗe shi?"

"Wai Sis Tasleem meyasa ba ki da imani ko ƙanƙani? Kina magana babu ruwanki idan an yi ko Ummita ta mutu ta rayu."

Tasleem ta harzuƙa da zancen Raihana.

"Da wannan abin kunyar ba gwara ace ma mutuwar ta yi ba! Ai gwara mu lulluɓe ta cikin sutura a kai ta kabarinta da dai ta haifa mana shege."

"Sai dai ke ki mutu! Ai dama wanda bai sonka ba zai taɓa sonka ba. Na kuma gama gasƙatawa ke din azzaluma ce da ba kya kaunar naki. Ciki kuma ƙaddarar Ummita ce da bai wuce faɗawa kan kowa ba koda kuwa matar auren ce. Nawa aka yi? Yanda ba kya kaunarmu har abada ba zamu taɓa kaunarki ba, yanzun ma albarkacin masu albarkar kika ci da ban ɗaga yatsuna na watsa a saman fuskarki ba."

Humaira ce ke wannan zantukan cikin tsananin rufewar idanu jikinta har tsuma yake yi. Tasleem ta yi laƙwas, ina za ta mance shaƙar da ta yiwa Anti Jannat, me ya yi mata zafi da za ta yarda ta yi katoɓarar da itama za a shaƙe ta ga tsohon ciki. Falon gaba daya aka rasa mai tankawa Humaira, su Yassar wadanda sun soma hankali sun ragewa zuƙatansu ƙiyayyar Humairar ba wanda ya goyi bayan zantukan Tasleem din.
Mami kuwa kamar yanda ta saba danne bakin cikinta da soyayyar yarannata a lokuta barkatai don siye zuƙatan yaran wannan karon ma haka ta yi.

"Koda wasa kar na ƙara jin makamanciyar wannan magana daga bakinki. Kina kiran mutuwa ga yar uwar da ke ganin girmanki. Ban san me yarannan suka tare maki ba. Kina dai kan gaɓar haihuwa ki ji tsoron Allah."

Mami na kai wa nan ta mike tana ɓata rai ta kama hannun Humaira suka yi daki wurin Ummita. Itama Raihana ta mara musu baya.

Tasleem ta ja tsaki.

"Ni ban ga amfanin abin da Mami take yi ba. Duk lalacewar naka, naka ne. Ta guji ranar da wadannan mutanen za su yi mata butulci."

"Uwar biyu kenan, sai kin zauna da su sosai za ki fahimci ba su da kowace matsala. Ni kaina a farko rashin ba Humaira dama ya sanya ni tsanarta amma yanzu da na dan zauna na saki jiki da su na fahimci kirkinta. Wallahi sosai na tausaya musu sadda suka yi nesa da mu, na kuma gane ina kaunarsu a jinina, ba zan iya fasalta yanda labarin cikin nan ya jefa ni ba. Duk da ban kai Yaya Mubarak shiga damuwa ba."

Fitowar wannan zancen daga bakin Dawud ya ba Futuha da Tasleem mamaki, dama akwai ranar da Dawud zai fadi mai kyau akan su Humaira? Yassar wanda shima bai jin ƙinsu ko kuma kaunarsu a zuciyarsa, dariya ya yi.

"Kai babban yaya ai ya faɗa, rannan Anna ke fesamin wai son Ummitan yake yi. Tana ta masifa da tsinewa zancen ta ce ko bayan ranta ba da yawunta ba."

"Wallahi ba za ta saɓu ba. Tab! Me Yaya Mubarak zai yi da sauran ƴan ta'adda?"

Futuha ta yi furucin a zafafe. Tasleem kuwa ta ma kasa cewa komai ji take kamar abin da ke cikinta zai fito idan ta ƙara magana saboda tsabar takaici da ya yi mata lulluɓi a ƙirji.

"To sai me? Ni wallahi don ya riga ni furtawa ne amma na ƙudurta ni zan aure ta matukar wancan Sahabi ya guje ta."

Cewar Dawud. Kiran sallar azahar ne ya tashi mazan, Tasleem ta dubi Futuha.

"Me kike tunani akan maganar cikin nan?"

Futuha ta yamutse fuska.

"To me zamu iya yi tunda an binne zancen ba a sanar da mu ba sai da ya fito?"

Tasleem ta yi ƙwafa. Ta ciro wayarta ta kira Jannat ta fesamata abin da ke afkuwa. Jannat ta feshe da muguwar dariya.

"Dakyau! Ki ce abu ya yi dadi? Toh ai wannan maganar ba abin a ɓoye ba ne. Ke ban da abinki tunda har ya afku ai zai fito. Kawai mu juya zancen mu yaɗa cewar dama karuwancinsu suka tafi, itama Humaira an keta mata haddi. Idan har duniya ta yarda ta amince kinga ai shikenan? Ban da Abbanku da DPO akwai wani da ya san an gan su kafin a kama su sun gudu?"

"Aa." Tasleem ta furta da sauri.

"Toh kinga idan ma an bada wannan hujjar zamu ce a kawo shaida, wacce kuma babu ita ba za a same ta ba."

Shiru dai Tasleem ta yi, Futuha ta zubawa Tasleem idanu, so take ta kammala wayar don ta labarta mata abin da Antin ta ce.

"Anti toh dan jira zan kiraki."

Daga nan suka ajiye waya, ta labartawa Futuha yanda suka yi. Tun ma kan akai aya Futuha ta hau girgiza kai.

"A'a, a'a, Tasleem kar ku yi haka. Nidai Futuha babu hannuna ciki. Ba fa sunansu kadai za a ɓata ba kenan har da na gidanmu. Nikam ba za'a yi haka da ni ba gaskiya, count me out!"

Tasleem ta harareta kawai sai ta yi shiru ba ta ce uffan ba. Futuha ta zubamata idanu, ta san halin muguntar Tasleem, shirunta na nufin abubuwa da dama.

"Ina fatan dai ba kina son cemin za ki haɗa kai da Anti Jannat ku aikata wannan babban kuskuren ba?"

"Sai aka ce maki bani da hankali ko? Mtsw."

Ta ja mata tsaki ta mike ta nufi dakin Anna amma ta gama ƙudurtawa a ranta babu fashi. Idan har ƙimar ita kanta ƴar tiktok Futuha zai taɓu a zage ta a idanun duniya toh wannan daidai ne. Gwara ma su yi hakan kawai.

***
Mami ta taushi Ummita dakyar ta samu ta yi shiru, ta yi musu ƴar nasiha sannan ta fito. Kai tsaye dakinta na nufa ta dauki waya ta kira Hajiya Lubna. Komai dake afkuwa ta zayyane mata. Ta kara da faɗin.

"Yarannan sun tada hankali lallai sai dai a zubar da cikin Ummita, kinsan dai yadda muka yi da Sadik Wizzy. Ina tsoron su kwatanta wani mugun abun."

"Haba Maryam, sai ka ce ba ke kika haife su ba. Ba za ki yi musu jan ido ba? Wai ni Maryam duk ba wannan ba, ina aka kwana batun kai Humaira wajen Babandi?"

Mami ta sauke ajiyar zuciya gami da ƙara gyara zaman wayar.

"An kashe wannan zancen, gobe zan kai ta. Na fi so a yi a ƙare, na gaji ba zan iya ci gaba da wannan pretending din ba. Idan an hana ta auruwa a tura ta bariki kawai mana ba shikenan ba? Na tsani wannan Fadeel mai baƙin nacin tsiya, Babandi ya tabbatarmin muddin dai bai fice a rayuwarta ba to lallai shi zai rusa komai. Mun kasa jefa mata ƙiyayyarta a zuciyarsa kamar yanda ita muka jefamata, ba na nasa kaɗai ba har na dukkanin wani namijin da zai furta mata kalmar so. Kamar kuma yadda muka yi wa FATIMA har ya zamo silar rabuwarta da Yusuf. A ƙarshe kuma muka zama ajalinta ta hanyar yi mata turen aljani ya kashe ta."

Wannan zancen ne ya yi dirar mikiya a kunnuwan Futuha wacce ta nufo Mami don sanar da ita yanda suka yi da Tasleem, ta tsaya cak a ƙofar ɗakin cikin wani irin kakkarwar jiki da zufa.

Juyowar da  Mami za ta yi ta ga mutum tsaye cak a bakin ƙofa, ba ƙarama razana ta yi ba wannan ya sanya ta ajiye wayar cikin rawar murya ta ce.

"Ke kuma me ya kawoki nan?"

Futuha ta karasa shigowa dakin sosai har lokacin bakinta a hangame saboda tsananin mamakin da ya gama baibayeta.

"Mami, duk ke kika aikata waɗannan abubuwan?"

Cikin sauri Mamin ta ƙarasa ta rufe ƙofar ɗakin, ita dai Futuha bin ta take yi da kallo har lokacin kamar a ranar ta soma ganinta a duniya. Cikin kausasshiyar murya ta amsa.

"Eh ni ce, na aikata kuma ina kan aikatawar, ina kuma gargadinki da babbar murya! Bar ganin kin fito daga tsatsona na rantse maki matukar kika yi gangancin tonan asiri koda a wurin yan uwanki ne sai na manta da ni na haifeki, zan iya daukar kowane irin mataki muddin dai buƙatana za ta biya."

Futuha ta jinjina kai ta kasa ma cewa uffan don gani ta yi tamkar wata Mamin ce daban a gabanta. Sai kuma ta daure ta hadiye fargabanta ta ce.

"Mami, kenan duk wannan kauna da muke gani kamar kin fi yiwa su Humaira a kanmu duk ba gaske ba ne? Har fa kidnapping din da aka yi naji kin ce ke ce."

Ta juya tana wani mugun murmushi ta karasa ga madubi tana kallon kanta.

"Wawaye, ina ku ka taɓa gani ko ji uwar da ta so ɗan wani sama da nata? Babu ita kaf faɗin duniyarnan. Idan ma akwai toh ni Maryam ba na cikinsu."

Sai ta ƙara sakin murmushi mai haɗe da ƴar dariya.

"Tun auren Yusuf da Fatima, nake ƙunshe da baƙin ciki a zuciyata, kakkarfan shaidar da aka yimin a garinmu da ma makwaftan da muka zauna da su a garin nan kafin rasuwar mahaifina na cewa ina da baƙin kishi kuma har akan kishin ne na taɓa marin (wani ɗan uwana da mahaifina ya so na aura) a bainar jama'a, na zazzagi uwa da ubansa kawai don ya ambatamin sunan tsohuwar budurwarsa kuma yar uwata da aurensu bai yiwu ba yana mai yabonta a kan idanuna. Tun daga wannan ranar ne na fasa aurensa. Ba shi kadai ba, na rabu da mutane da dama saboda kishi, saboda tsanar da na yiwa kishiya, mahaifina ya taɓa neman aure na wanki ƙafa har gidan da ya je nema na ɓata sunansa kuma aka fasa auren. Baƙin shaidar da na samu sanadiyyar zazzafar kishi ya sanya da Yusuf ya shigo rayuwata matsayin saurayin da bai taɓa aure ba, ya shiga zuciyata sosai. Na sa a raina

5 Comments On DUKAN RUWA
avatar
daiy drop

2 years ago

Reply

hhh

avatar
daiy drop

2 years ago

Reply

sss

avatar
daiy drop

2 years ago

Reply

sss

avatar
daiy drop

2 years ago

Reply

sss

avatar
north

2 years ago

Reply

hhhhh

Please Login or Register in order to submit comment