Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

cikin nutsuwarta.

A bangaren Ummita da Ibb, hira suke ɗam taɓawa kaɗan, shi kuwa Gogan da Humaira ba ka jin komai daga bakinsu, babu kamar Fadeel da yake jin waƙar ta zo daidai da yanayin da yake ciki. So yake ya tambayi ya take? Ya lamuran rayuwa? Ba ta hakura ba har yanzu? Ba ta amince ya turo iyayensa ba? Sai yaushe? Amma ina! Babu ko kalma ɗaya da yake jin zai iya furtawa, ba ya fatan rabin shekarar da ya kusan cinyewa ya tashi a banza balle ya ga shekarar ida  da rai da lafiya, wannan ya sa yake takatsantsan ya kuma jure bai ƙara kallonta ba tunda ko ya kalli side mirror ba ya ganin komai face danshin ruwan dake kwarara sai ko hasken fitilun motocin dake saman titi.

Har suka iso gidan ba ka jin uffan daga Fadeel, shi kansa Ibb sanin halin mutumin ya sanya bai takale shi da hira ba ko sau ɗaya. Ya dai san yau Humaira ta fama mishi inda yake mai ƙaiƙaiyi.

"Ko mu karasa da ku har cikin farfajiyar?"

Wannan kalmar ya sa Fadeel cire gilashin idonsa, ya dubi gidan su Humaira, wato har an iso kenan.

"Aa, mungode sosai. Bari mu karasa ciki."

Cewar Ummita. Humaira kuwa har ta kama ƙofar ta bude, amma ina, iska mai karfi da ruwan da ya fesomata ya sa dole ta koma ta rufe. Fadeel ganin haka ya juya bayan, sai a sannan ya kara kallonta ido cikin ido, da sauri ya dauke idanunsa ya dan kai hannu baya ya dauko lemar dake ajiye a wurin. Fitowa ya yi ya buɗe lemar, babba ce don ta fi ta Ummita girma, Ummita kam tuni ta fita itama ta bude nata lemar da ba zai ishe su ba su biyu koda a dazun ne. Kofar Humaira ya bude gami da miƙamata lemar. A sanyaye take dubansa.

"Karɓa mana Humaira." Ibb ya furta, ta kalleshi.

"Mungode sosai, Allah ya kiyaye hanya." Daga nan ta fita, sai ya kasance su biyun a ƙasan lemar. Kan Fadeel a ƙasa ba ya son kallonta gudun ɓarowa kansa aiki, ta sa hannu ta karɓa sannan ta dan ja baya kaɗan.

"Idan na shiga zan aiko a kawo."

Murmushi ya yi mai kyau har a sannan bai kalleta ba ya amsa da toh. Daga haka ya fice ya koma cikin motar ya rufe. Ita ma ta nufi kofar da gudu-gudu.

"Muje."

Ba musu Ibb ya yi reverse ya juya kan motar suka bar layin. Ƴar dariya ya yi.

"Fadeel kana son Humaira."

Fadeel bai iya kallonsa ba ballantana ya samu amsa. Ya kara cewa.

"And you know what? Kun dace sosai."

Nan ma bai kalleshi ba sai dai ya yi murmushi. Ganin ba ya son magana ne ya sa Ibb rabuwa da shi.

***
A can kuwa Humaira na shiga ta bada lemar a miƙa musu, ɗan aike ya dawo ya ce babu kowa a wajen, ta karɓa a sanyaye ta shige ɗakinsu da shi. Madadin ta karasa ciki sai ta ajiyeshi a ɗan gefen don ya sha iska. Suka sauya kayan jikinsu saboda jiƙewar da suka ɗan yi. Ummita ta ɗauro alwala sannan itama ta ɗauro, koda ta idar da sallah kwanciya ta yi saman dardumar don kanta har lokacin sarawa yake yi kamar jijiyoyin kan nata za su tsinke. Tuna Fadeel kaɗai yana haifar mata da rawar jiki da ciwon kai, daga haka kuma sai ta ji kamar ana mata ihu a kunne. Kafin ka ce wannan sai ga Humaira ta soma kuka sosai. Ummita da ke kwashe jiƙaƙƙun kayansu ta juya da sauri ta juyo. Allah ya taimaka su kaɗai ne a ɗakin ta roƙi yanmatan akan su fita ta gyara don sun yi kaca-kaca da shi. Tuni ta fahimci matsalar jinnunta ne, ta sha mamaki ma da bai tashi a mota ta yiwa su Fadeel rashin mutunci ba.
Da sauri ta fice zuwa kicin, can baya ta zagaya inda ake dora babban tukunya a icce saboda yawan da aka yi. Garwashi ta zuba cikin kasko ta dauka da sauri gudu-gudu ta nufi dakinsu. Mami dake kokarin shiga kicin don ganin kwandunan kayan miyan da Abba ya ce an kawo na girki ta tsaya cak hankalinta ya yi kan Ummita wacce ke tafiya kamar wani abu ya faru. Da sauri ta bi bayanta.

Ita kuwa Ummita, tun cikin babbar sallah da ta je Bichi ta karɓowa Humaira hayaƙi a wurin ɗan uwan mahaifiyarta hakan yasa Humaira na fara kuka ta yi niyyar turara mata. Abin mamaki har ta isa yanayin kukan Humairar bai sauya ba. Ta ciro maganin ta barbaɗa cikin kaskon ta ajiyeshi kusa da Humaira. Nan da nan kanta ya soma juyawa. Daidai lokacin Mami ta faɗo ɗakin. Abin da ta gani ne ya sanya ta kallon Ummita,

"Lafiya? Meke faruwa da Humairar? Wannan wane irin hayaki ne kuma?"

Ummita ta sha jinin jikinta don gaba daya ba ta sanar da Mami ta karɓowa Humaira hayaƙi ba.

"Ba komai Mami, kukan nan ta soma wanda take yi idan aljanunta suka tashi shi ne.."

Mami ta daka mata tsawa.

"Shi ne me?! Shi ne kike yi mata hayaƙi ba tare da kin sanar da ni ba? Haba Ummita, yanzu idan Abbanta ya ji wa zai yiwa faɗa? Maza ɗauke hayaƙin nan."

Ummita ta dauka ta fitar zuwa bandaki ta kashe, ta sani ta yi kuskure amma kuma cikin ikon Allah Humaira ta yi shiru sai gumi take haɗawa da alama kuma bacci ya ɗauketa.

Ummita ta kai duba ga Mami, zuwa lokacin tana zaune gefen gado.

"Ki yi hakuri Mami."

Girgiza kai Mami ta yi.

"Ba laifi kika aikata ba Ummita, na sani kulawa ce da yar uwarki, amma ko mene ne ya dace na sani saboda nima ina nawa kokarin a kanta don har na yiwa Abbanku maganar wani mai bada magani zan kai ta wurinsa bayan biki ya ga mece ce matsalarta."

Gyaɗa kai Ummita ta yi tana murmushin farin ciki. Ba ta da fatan da ya wuce ta ga Humaira ta samu lafiya ta amince da auren mai kaunarta irin Fadeel.

"Toh Mami. Allah ya sa a dace."

Mamin da murmushi ta amsa da amin. Har ta mike ta kai ƙofa ta juyo.

"Ɗaukomin maganin da kike turara mata, idan ya so sai na yi mishi bayani."

Ba musu Ummita ta ɗauko ta ba ta, murmushi ta yi ta juya ta fita a dakin.

***
BIKI BUDURI....




®️Rufaida Umar.

*LITTAFIN NAN NA KUƊI NE. SIYA AKAN NAIRA ₦400 KI KARANTA BA TARE DA SHIGA HAKKI BA.*


*5407827015*
*FCMB*
*Farida Abdullahi*

09034973645



Da taimakon Allah ta kammala aikin odar da aka bata. Kamar yanda ta saba, wannan karon ma waya ta yi akan a zo a karɓa. Aka ba ta lokacin zuwa karfe sha biyun rana. Bayan sun yi sallama ta sauke ajiyar zuciya tana mai jin wani irin nishaɗi. Hamdala ta yi kamar koyaushe kafin ta fiddo manyan ledojin mai tambarin Deelsha's Delicacies ta sanya.

***
  Murja ta kammala shiri tsaf sai rawar jiki take yi ta je ta ga Humaira me snacks. Kausar na zaune a falo tana taya Khadija da Hanifa (Ɗiyar Saddika yaya ga Anti Amarya) hura  balan-balan su na tarawa. Murjar ta fito. Kallo ba ta ishe ta ba, ta gefen ido Murja ta watsamata harara. Daidai lokacin da Anti Amarya ta shigo bayan ta dawo daga farfajiyar gidan inda mai decoration ke ƙawatawa don anan za a gudanar da birthday din Abdulmaleek na cika shekaru uku a duniya.

  "Ni na shirya zan wuce."

"Toh tsaya na baki cikon kuɗinta. Don Allah ki yi sauri kina karɓa ki wuce ki karɓo Cake din."

Ta amsa da toh. Anti Amarya na shiga ciki sai ga Fadeel ya shigo falon riƙe da Abdul yana mishi wasa. Nan da nan Murja ta ji ranta ya yi wani irin sanyi. Ta kuramasa idanu tamkar ta lashe shi musamman ganin yanda shigar jan t-shirt da baƙin jeans ya haskaka shi abinka da fari. Ta sauke ajiyar zuciya tana ji inama kawai ta tsinci kanta a faffaɗan ƙirjinsa. Sai da ta ji suna gaisawa da Kausar sannan ta dawo hayyacinta. Ajiyar zuciya ta sauke, ta ƙarasa ta zauna ita mai shirin fita. Murya cike da yanga ta ce.

"Yaya Fadeel barka da rana."

Kallo ɗaya ya yi mata ya kauda kai, shi a yanzu sam ba ta burgeshi tun sadda Alhaji ya faɗamasa saƙonta.

"Yauwa."

Daga haka ya maida hankalinsa ga Kausar suna hirar aikin Fu'ad da babu hutu. Ita kuwa Kausar hakan ba karamin dadi ya yi mata ba, ta gama lura da irin matowar da Murja ta yi a kan Fadeel, ta kuma sani zai wahala ta same shi tunda sam ba ta gabansa. Murja ta shaƙa, saukowar Anti Amarya daga saman bene ya sa ta mikewa. Fadeel ya gaisa da ita. Ta miƙawa Murja kudin tana fadin.

"Ina daɗa roƙonki, na san halinki kar ki je ki zauna don Allah Murja. Kina karɓar snacks din ki biya ki dauko cake."

Ta amsa da toh, ji take inama direban gidan ba ya nan sai ta ce Fadeel ya kai ta. Amma tun dazun yana waje ita yake jira. Fadeel kuwa yana jinsu amma bai sa baki ba. Ba ya son ya zaƙe akan lamarin Humairar har su shinshino wani abu babu ma kamar Murjar da bai gama yarda da ita ba.

***
Ta tsaya daga ƙofar gate din gidan tana ƙarewa gidan kallo, yamutse fuska ta yi. Eh ba laifi su na da rufin asiri amma ko daga waje bai kama ƙafar gidan su Fadeel ba. Ta karasa ta yiwa Maigadi sallama ta kuma faɗi abin da ya kawo ta, iznin shiga ya yi mata kai tsaye don dama yana da masaniyar sana'ar Humairar.

A sadda ta karasa ciki Humaira na zaune tare da su Raihana a falo bayan gama yi mata kwatance a waya, ta sani ba za a ɗau lokaci ba za ta karaso tunda a sanda suka yi wayar tana kusa da su.
Sallamarta ya sa gaba daya suka dube ta. Ba laifi tana da nata tsarin daidai gwargwadod. Abaya doguwa ce a jikinta sai mayafinsa, sai ko wani ƙaton gilashi da ta rufe kwayoyin idanunta da shi. Tunda ta shigo falon ya karaɗe da ƙamshin turarenta mai ƙarfi irin wanda ya zama haramun mace ta fesa ta fita da shi. Suka tarbe ta da hannu bibbiyu aka gaisa. Humaira har da kawomata ruwa da ragowar snacks din ta ci. Kasancewarta wayayyiya ta sake da su aka ɗan taɓa hira har Mami ta fito suka gaisa da ita. Murja ta yaba kwarai da tarbar da aka yi mata, ta kuma ji a jikinta Fadeel ba zai so Humaira ba, ba ita ce wacce yake so ɗin ba don dai wannan din ba wata babba ba ce ba za ta wuce shekaru goma sha biyar ba.

"Kina da page a instagram ne?"

Humaira ta gyaɗa kai da murmushinta har wushiryarta na bayyana.

"Eh akwai."

"Mene sunan?"

Nan fa daya, ta sani furtawar ne aiki ba ta iya ba sosai. Raihana ta karɓe zancen ta fadi. Murja har sai da ta ɗan kalli Humaira sannan ta kalli Raihanar da murmushi.

"Ok zan yi following dinki. Na ji dadin ganinki na kuma ji dadin ɗandanon snacks dinki duk da daman na san ɗandanon. Akwai ɗan uwana Yaya Fadeel yana kawomana sosai. Ta wajensa muka sanki."

Murjar ta fadi tana mai ƙurawa Humairar idanu don ta ga yanayinta, so take dai ta samu tabbacin babu komai tsakaninsu. Raihana kuwa ɗan jim ta yi a ranta tana tunanin wane Fadeel din? Kodai Fadeel wanda ta sani ne, tabbas ya faɗamata yana odar snacks din Humaira ta hannun wata Antinsa. Ko shi din wannan ke nufi? Idan kuma hakane ita wace ce a wajensa? Ta maida dubanta ga Humaira don ta ga yanayinta, sai ta lura ko kadan ba ta sauya daga murmushin da take yi ba, sai dai jin sunan kamar jikinta ya dan yi sanyi.

"Allah Sarki, na kuwa gode sosai." Abin da ta ce kenan, wannan ya sa Murja kuma sakin jikinta sosai. Lallai wannan ba ita ce Humairar da Fadeel ke mutuwar so ba, wannan da alama ba ta ma san da zamansa ba. Dama ya ce ba shi ke yin odar da kansa ba. Yanzu kam ta yarda. Murja ba ita ta bar gidan ba tsabar shagala da ta yi suna ta kwasar hira da su musamman Raihana wacce ta fi su sanin mutane, kusan ma akwai ƙawayen Raihana na makaranta wadanda duk Murjar ta san su hakan yasa hira ta musu dadi sai da Anti Amarya ta kira wayarta tana faɗan jimawarta ba shiri ta mike, su Humaira kuwa har mota suka raka ta da ledojin. Murja ta karɓi lambar Raihana da zummar a dinga gaisawa duk da ta girme musu don za ta yi sa'ar Tasleem.

***
Sadda ta isa gidan har yara sun fara zuwa ƴan party. Ta karasa Anti Amarya na mata faɗan dalilin jimawarta. Hakuri ta ba ta, ganin Fadeel a wurin wanda ke cin abinci a nutse saman dinning ta ce.

"Wallahi hira muka sha da su Humaira, mutanen gidan akwai kirki kar ki so kiga kamar kada a rabu."

Fadeel ya ji maganar har ransa, ya kuma ji dadi sosai. Bai dai ko ɗago ya kalle ta ba. Yana ji dai tana ta ba Anti Amarya labari ita dai ledojin ta hau buɗewa tana kallon snacks din. Koda ta dandana sun mata dadi kwarai. Nan aka shiga sanya wa a takeaway ana rufewa, Kausar na nan ana aikin da ita.

An gudanar da party cikin armashi, yaran Daddy da Mommy ne suka cika gidan don Anti Amarya sam ba ta barin mara shi ya raɓe ta. Yawanci duk abokan makarantar Abdul din ne sai ko makwaftansu. Hatta a yaran yan uwanta ba kowa ta gayyata ba.

***
Ɓangaren Amare kuwa, Amarya Futuha an ci amarcin sati daya cif ko ƙofar gida ba ta leƙa ba. Hotunansu ita da mijinta kala-kala babu wanda ba ta ɗorawa a Instagram, shi kansa Angon hakan na mishi dadi kwarai bai taɓa hanata ba. Tunda ta zo ba ta taɓa sanya Uwargida a idanunta ba, karshe ma sai Ango Yakubu ke sanar da ita ta yi tafiya Saudia ita da yaranta. Futuha tun da ta ji haka duk sai ta matsa mishi akan ita ma ya dace su tafi hutun honeymoon Dubai. Hakan ya yi mishi dari bisa dari, a lokacin ji yake ko nawa ne zai iya kashewa Futuha saboda dadin angoncin da yake kwasa. Ba ɓata lokaci aka soma shirin yi mata passport da sauran abubuwan da ya kamata ma tafiya. Sai bayan kammaluwar komai sannan washegari ta yi nufin zuwa gidansu ziyara da kuma sallama.

A ɓangaren Tasleem ma, babu laifi Hamza na iyakar kokarin faranta mata, sun ci soyayyarsu yanda ya kamata, ba ta dora koda ruwan zafi daga gidan iyayensa ake kawomusu abincin safe zuwa dare. Sai da ta yi sati cif sannan suka kara shiga ta gaida Mahaifiyarsa da abokan zamanta su uku. Gidan dai babban gida ne mai tarin yara da jikoki. A ranar har gidajen facalolinta sai da ta shiga, wasu sun kata tarbar kirki yayinda wasu kallon tara saura suka dinga yi mata. Haka tattara ta dawo gida.

A ranar da suka yi waya da Futuha take ba ta labarin tafiyarsu Dubai hankalinta ya yi mugun tashi, ji tayi inama ita ce ta samu wannan damar. Ciki-ciki ta yi mata murna, dama tana jin haushin hotunan da take karo da su a media na Futuhar da mijinta yanda kowa ke santin kyawun da suka yi. Futuha ta ce ta shirya za su zo har gida su yi mata sallama. Ba ta ma iya amsawa da toh ba ta katse kiran gami da jan tsaki. Ya yi daidai da shigowar Hamza falon, hannunsa rike da ledoji ya yi mata siyayyar kayan sanyi da kaza. Har ya karaso kusa da ita ba ta san ya yi ba tsabar ta lula duniyar tunani. Sai da ya ajiye ne ya dan zunguri kafaɗarta kadan. Ta dubeshi, murmushi tattausa ya sakar mata, itama ta bishi da na yaƙe. Rungumo kafaɗarta ya yi.

"Tunanin me kike yi ne haka? Har na shigo da favourites dinki amma ba ki lura ba?"

Ta kai duba ga ledojin dake ajiye, har gumin sanyi ɗaya yake, sai ta ji ta kasa farin ciki da abin da ya ajiye din duk da cewa a baya har so take ya kawo su ta dinga tsalle kenan tana rungumeshi. A yanzun kuwa ko ɗigon annashuwa ba ta yi ba. Sai jikinsa ya yi sanyi, ya kamo yatsun hannunta.

"Wai me ya sauyamin ke haka? Ko bayan fita na kin yi baƙi ne?"

Dama kiris take jira ai sai ta tunzura ta yakice hannunta.

"Me kake nufi?! Na yi baƙi sun zugani ko sun ɓatan rai? Yan gidanmu kake nufin sun zo ko ƙawayena?! Au zargina kake yi akan wani zai iya zuga ni akanka? Ai ba sai an zuga ni b, ni mai zuga kaina ce!"

Gaba daya ya razana, ya yi jim yana kallonta, a iya saninsa babu inda maganarsa ta kai nan. Me ya kawo batun zuga kuma ana zaune kalau? A ina ya ce hakan?

"My Noor, me ya kawo zancen zuga? Ban gane inda kalamanki suka dosa ba?"

Sai a sannan ta ɗan dawo hayyacinta. Ta ja guntun tsaki ta zauna. Nan da nan kuma Hamza ya ɗan sauya fuska.

"No please, zan dauki komai amma ban da raini, ina maki warning na farko da karshe, bana son tsaki. Kar ki kuma."

Ba ta ce komai ba face turo bakin da ta yi, sai ya ji ma gaba daya ta ɓata masa rai kawai ya mike ya yi daki. Ta bishi da harara, ita ta sani ko wannan motar tasa zai siyar ba zai ishe su su je Dubai har su kashe kudade irin wanda Futuha zasu kashe ba. Ta san muddn Futuha ta yi wannan tafiyar to fa kanta zai fasu, za ta ƙara jin wani girman kai har ma ta dinga yi mata fi'ili iri-iri. Don haka hankalinta ya tashi, ga babu yadda ta iya, nata mijin ba ta tunanin ma ya taɓa taka farfajiyar Airport balle ya shiga jirgi. Ta ja tsaki karo na biyu. Madadin ta kwashe ledojin da ya kawo ta adana komai koda ba lokacin za ta sha ba, kawai sai itama ta bar su anan ta shige nata dakin ba ta ko bi ta kansa ba don har sannan zuciyarta zafi take yi, hassada mugun ciwo ne.

***
Tun karfe goma Humaira ta je kasuwa yin cefane bisa umarnin Mami wacce ke ta shirin tarbar Futuha da za ta zo. Tana dawowa kicin kawai ta shiga ta soma shirin girki, tuwon semovita miyar kuɓewa danya wanda ya ji nama da busassan kifi, shi Futuhar ta ce tana muradi sai ko lemun kwakwa. Wuraren karfe ɗaya ta kammala komainta jera a saman tire ta kai falon ta ajiye. Daga nan ta koma dakinsu. Ita ko kusa ba ta wani zumuɗin ganin Futuhar kamar yanda su Ummita ke yi. Tun dawowarsu daga makaranta jin ance tana hanyar zuwa suke faman rawar ƙafa. Ai kuwa ko awa ɗaya cikakka ba su yi da dawowa ba sai ga mota direba ya kawo ta har farfajiyar gidan. Da gudu Raihana ta fice tarbar yar uwarta, itama Ummita ta mara mata baya a nutse take tafiya. Humaira sai ta ja guntun tsaki ta cigaba da danna wayarta tana ganin sabbin likes da comment da sabon hotunan da ta dora na girke-girke suke samu. Ta shagala sosai sai ji ta yi an warce wayar, ta juya da sauri. Raihana ce. Dariya ta yi mata.

"Ki taso inji Mami ku gaisa da Futuha. Ashe Dubai za su wuce da mijinta sati na sama."

Ta ɗan yi murmushi, ba ta fiye son kushe su a gaban Raihana ba don haka ta taya murna a fili.

"Kai amma na mata murna, Allah ya kai su lafiya. Muje toh. Bani wayata kuma."

Raihana ta mika mata suka yi dariya. A falon ta iske Futuha zaune, masha Allah ta ƙara ƙiba da kyau, kumatunnan har wani kyalli suke yi. Wani arnen leshi ne a jikinta fari da ruwan toka ya sha aikin stones sai faman baza ƙamshi take yi, hira sosai take yi da Mami. Ƙassim ma na zaune banda Yassar da Dawud wadanda sula tafi Camp a can garin Jigawa. Humaira ta karaso ta gaida ta, ta amsa mata tana yamutse fuska kaɗan daga nan ta maida hankali ga uwarta su na cigaba da hira. Humaira wacce dama ta san a rina kawai sai ta mike ta saci jiki ta koma daki, Ummita ta mara mata baya.

"Ke kuwa daga gaisuwar sai ki taho?"

Harara ta dan watsa mata.

"Idan na zauna me zan mata? Goyata zan yi? Ai dai kinga yanayin amsar gaisuwar da ta yimin ko? Toh ni kuwa marar zuciyar ina ce da zan tsaya?"

Ajiyar zuciya Ummita ta yi.

"Allah ya kyauta, kinsan Allah na yi zaton aure zai sauya su, amma naga har yanzu da sauransu."

Taɓe baki Humaira ta yi ta ce.

"Toh yaushe ma aka yi daren? Ke ta dai samu duniya ne kawai shiyasa abinta ya ƙara gaba. Nifa kinsan ba abin da ke ban mamaki face irin yadda matarnan ba ta yiwa kanta faɗan ta nutsu ba take faman ɗora hotunanta a media. Shi ma mijinnata soloɓiyo da ya biyemata."

Ummita ta kama baki har da ɗan waigawa ta ga ko babu wani a kusa da ya ji kalamin Humaira.

"Kinga ki rufamana asiri. Mutum ba shi ya ga zai iya ba? Kar ki manta har da shi din Ogan nata ake wannan taɓargazar kinga kuwa abu nasu maganin a kwaɓe su. Wayewar yanzu ce ta shirme ta zo da haka."


Dariya Humaira ta yi.

"Kenan kema haka za ki yi da Sahabinki ko?"

Duka ta kai mata a cinya.

"Allah ya sauwaƙe, mu aurenmu ko party ba zamu yi ba, walima kawai a cikin gida ta isa. Albarkar auren muke nema. Hum, nifa yanzu duk ya dameni akan zai turo a sanya rana kafin nan da shekara idan mun kammala nayi Candy a yi auren. Wallahi kwanakin nan duk akan hakan muke ta rikici. Na rasa yanda zan ɓullo masa."

Humaira ta mike zaune sosai. A duniya ta tsani ta ga Ummita cikin damuwa ko na sakan, don haka ta ce.

"To me kike jira? Me zai hana ki ba shi wannan damar? Kina sonsa yana sonki fa. Kuma sa rana ba shi ne auren ba, don Allah ki yi shawara da Mami tunda kinga ta san da zamansa, na tabbata za ta goyi da bayan ya turo."

Ummita ta zubamata idanu ta yi shiru cike da damuwa, ga mamakin Humaira kuma sai kawai ta ga hawaye sun soma zuba daga kwayar idanunta.

"Lafiya? A maganata akwai wacce ta maki zafi? Kiyi hakuri don Allah kinji?"

Girgiza kai Ummita ta yi,

"Ko ɗaya Humaira, ke ce dalilin da yasa na kasa ba Sahabi damar turo iyayensa. Wallahi bana jin dadin mafarkaina a kanki kwanakin nan. Humaira na damu da rashin bada ƙofa ga kowane saurayi ya nemi aurenki da kike yi. Ba na so na yi aure na bar ki a wannan halin. Gaba daya na damu."

Shiru Humaira ta yi, toh ita da kamar abin yana damunta kamar kuma ba ta damu ba. Ta ma kasa fahimtar komai sai kawai ta dubi Ummita a sanyaye.

"Kin manta ke ce me nusar da ni idan na ɓata? Ke ce me ƙarfafamin gwuiwa akan imani da Allah a irin wadannan lokutan? Toh ki sani, har ga Allah ba na jin son kowane namijin ba balle na ji son auren a raina. Hakan ba yana nufin wata matsalar ba, ki kaddara lokaci ne, duk sadda na ji son wani a raina, watakila..."

Sai kuma ta ma rasa me za ta ce, kawai sai ta sunkuyar da kai ta riƙe hannun Ummita cikin nata. Karon farko da ta ji tana hawaye, hawaye mai dalili ba wanda ta saba yi a irin gaɓar nan babu dalilin ba. Ummita sai ta ji tausayinta ya lulluɓe ta, Humaira ai itama da zuciya a kirjinta. Dole akwai abin da ke damunta amma ba ta faɗa, ba ta magana sai dai ta yi shiru idan sun taso da zance ta maida su wasu cali cali.

"Ki tayani addu'a Ummita, ina
DOWNLOAD
DOWNLOAD

5 Comments On DUKAN RUWA
avatar
daiy drop

1 year ago

Reply

hhh

avatar
daiy drop

1 year ago

Reply

sss

avatar
daiy drop

1 year ago

Reply

sss

avatar
daiy drop

1 year ago

Reply

sss

avatar
north

1 year ago

Reply

hhhhh

Please Login or Register in order to submit comment