Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

asirinmu ne. Duniya sai ta san halin da muke ciki. Ka kwantar da hankali tunda ana siyar da Pt-strip na awon ciki, gobe da safe mu bayar a siyo a auna fitsarinta don mu ga halin da take ciki. Mu yi fatan alheri da fatan kar zatonmu ya tabbata.

Ajiyar zuciya mai karfi Abba ya saki.

"Innalillahi...Ya Ilahi! Wannan ranar dame zan kirata ni Isuhu? Inama tun farkon fari ban hana Hajiya Maijidda riƙon Ummita ba tun tana ƙarama, da watakila ba zan ga wannan ranar ba."

Wani irin zuciya ya tasowa Mami, ta ji tamkar ta haɗiyi zuciya ta mutu. Ranta ya yi mugun ɓaci, wato duk hakuri da dauriyar shanye damuwa da bakin cikin RIƘON BARE da ta yi, da wannan sakayyar Abban zai bi ta? Ta so ta furzar da abinda ke ranta sai kuma ta daure kamar koyaushe ta shanye rabi da kwatan ɓacin ranta ta ce.

"Wane irin rashin tawakkali ne haka Abban yara? Ka isa ka hana Allah ikonsa ne akan al'amarin Ummita? Ummita ko bangon duniya ta je idan hakan ya ƙadartu a kanta sai ya afku. Ban da haka ma, kenan kana kaicon rayuwar da ta yi a hannuna? Kana kaico da irin abin da ya fada mata? Ko a tunaninka a sanadina ne aka sace su har kaddarar fyaɗe ya faɗa kan Ummita?"

Ta karasa zancen da wani irin kausasshen murya, ganin ya kalleta da sauri da alama zancen bai mishi dadi ba kuma bai san fassarar da za ta ba shi kenan ba ya sanya ta fashewa da kuka mai tsuma zuciya.

"Dama na sani Yusuf, watarana sai ka ga gazawata akan yarannan duk kuwa da..."

"Haba Maryama, don Allah don Annabi s.a.w ki yi hakuri. Wallahi zafin bacin rai da damuwa da tashin hankali ne ya sanya ni wannan maganganun marasa kyawun ji. Ko daidai da kiftawar ido ban taɓa kawowa za ki cutar da wani a cikin yaran da kika haifa a cikinki ba ma balle a kai ga Ummita. Yarinyar da kika daukaka ta kika kuma riƙe ta hannu bibbiyu tamkar ke kika haife ta a cikinki. Wane irin butulu ne ni da zan yi maki haka? Ki yafemin domin Allah. Na tuba kiyi min uzurin halin rudani da tashin hankalin da na tsinci kaina ciki."

Mami ta mike ta ja guntun tsaki ya yi saurin tarar gabanta.

"Haba Maryama, da wanne kike so na ji ne? Da tashin hankalin nan na Ummita ko kuwa da ɓacin ranki? Faɗamin, me kike so nayi ki huce?"

Jin haka sai kuma ta yi shiru tana goge fuska.

"Kar ka ƙara irin wadannan kalaman naka na rashin tawakkali."

Ya yi murmushin karfin hali ya rungumeta.

"Idan har wannan ne ba zan kara ba. Na ma yi istigfari tun sadda kika ankarar da ni kurena. Mu ji da damuwa daya yanzu."

Ta gyada kai, bandaki ta shiga ta ɗora alwala ta sanya hijabi ta hau saman darduma. Sosai yake jin so da kaunarta a zuciyarsa. Shima sai ya fasa neman wuri ya kwanta kamar yanda ya so duk kuwa da irin sakensa a ibada lokuta da dama. Kusan wannan shi ne kadan daga inda ya kuskuro, rashin tsayawa kai da fata wurin ibada sosai sai idan ya fada matsala babba.

***
Washegari tashin hankalin da suka riski kansu ciki sai ya mantar da su wani batun zuwa kai Humaira asibiti.
Gidan ya zama tamkar gidan makoki. Suna zaune jigum suna jira Mami da Ummita su fita daga bandaki don sanin matsayar Ummita, akwai cikin ko babu. Abba ya kasa fita kasuwa si safa da marwa yake a falon balle kuma Raihana wacce tun jin abinda ke faruwa ta kasa motsawa ballantana ta wuce makaranta. Sai Humaira da ta dau carbi tana jin tamkar an yi mata mutuwa. Mubarak kuwa wanda shi ya fita ya siyo abin awon cikin, sai ya jingina jikin bangon falon ya yi shiru cikin bugun zuciya.

A wannan yanayin Mami ta fito a gigice kuma a guje, gaba daya suka yi kanta har suna rige-rige.

"Meke faruwa?" Faɗin Abba yana jin kamar ya kife tsabar jiri.

Mami ta fashe da kuka.

"Mun shiga uku! Shikenan Abban yara asirinmu zai tonu. Ciki ne da Ummita."

Abba ya ja baya da sauri ya zauna saman kujera mafi kusa da inda yake, yayinda Humaira ta yi mutuwar tsaye. Ita kuwa Raihana kwasa ta yi a guje zuwa bandakin don ganin halin da Ummitan ke ciki. Aikuwa ta iske ta a kife tamkar babu numfashi. Ta kuwa ƙwalla ihun kiran sunan Abba. Kusan da rige-rige suka shiga banɗakin. Mubarak ne ya yi ta maza ya cicciɓe ta bayan ya tabbatar da bugun zuciyarta ya fiddo ta falon ya shimfiɗe saman kujera sai dai duk wani kokari na watsa ruwa da ma sauransu anyi amma babu alamun Ummita ta san ana yi. Ana shirin fita asibiti Mami ta dakatar ta ce gwara a kira makwafciyarsu wata likita gudun fashewar zancen a duniya. Abba ya yi na'am, Mubarak ne ya fita da rawar jiki har gidan Dakta Inteesar an ci saa kuwa ta fito cikin shirin tafiya asibiti. Ganin Mubarak aboki ga babban ɗan ta Najeeb ya sanya ta dakatawa. Roƙon da ya hau yi mata ya sa ba ta iya yi mishi musu ba sai ta shiga motarta suka kama hanyar gidan don akwai ƴar tazara kaɗan ita daga bayansu take. Cikin ikon Allah ta ba Ummita taimakon gaggawa ta farfado sai kuma ta dube su.

"Ya dace a yi mata gwaji sosai din tabbatar da abin da ke damunta."

Ta furta hakan ta yi shiru don jin me za su ce, a matsayinta na likita ta gama tabbatarwa Ummita na da juna biyu. Shiru ta yi musu don ta fi son ji daga bakinsu sun amince da gwajin. Tana sane da labarin abinda ya afku ga Ummita. Su kansu mutanen gida ba su da masaniyar cewa duk yadda suka so da ɓoye labarin fyaɗen Ummitan sai da ya fita ba. A duniyar yanzun ai mutum ake kiwo ba dabba ba, kana abu kana ganin tamkar duniya ba ta sani ba amma zirr ake kallonka.

Abba ya yi yaƙe.

"Babu damuwa Dakta, zamu kai ta asibiti."

Ta lura ba su son zancen ya fasu, ita kanta ta tausaya musu babu kamar Ummita wacce tunda ta farfado uffan ba ta ce ba, kukan ma ta ƙi yinsa sai sauke ajiyar zuciya akai-akai. Haka Dakta Inteesar ta yi musu sallama bayan ta rubuta magungunan da ya dace wanda take da tabbacin zai taimaki Ummita bisa yanayinta na mai juna biyu. Mubarak wanda ke tsaye ya ƙurawa Ummita idanu yana jin abu mai nauyi na taso mishi wanda ya fi kama da tsabar tausayinta da kuma kauna ta ƴan uwantaka.  Kamar dai yanda yake tunani. Shi ne ya karɓi takardar magungunan ya fice.

***
Kwance yake idanunsa a lumshe, babu komai a ransa sai Humaira. Yana ji a jikinsa an soma zuwa gaɓar da yake da tsananin buƙatar kasancewarsu tare a inuwar aure. Shi din fa ba dutse ba ne, namiji ne kuma lafiyye da yake buƙatar aure. Soyayya mai ƙarfin da yake yiwa Humaira shi ne silar da ya danne wannan buƙatuwar ya ɗora shi kacokam a kanta yana jiran lokacin da mafarkinsa zai tabbata. Sai dai kuma yaushe ne?

Wannan damuwar ce ta hana shi fita ko'ina, hatta da mai gyara mishi dakuna bai san yana nan ba, shi dai Nura yana falo yana aiki kafin ya shiga ɗakin. Hatta shi bai dan cewa Fadeel na gidan ba sakamakon motarsa da ba ta nan tun daren jiya. Ɓaci ta yi a hanya ya bar ta can  makanikinsa ya je ya ɗauka.

Daidai lokacin Murja ta faɗo ɗakin da ƙunshin kayan gugan Fadeel din a hannunta wanda ta karɓa a hannun Sadi mai gugansu, dama  ta jima a yar barandar da zau sada ta da ɗakin Fadeel tana tunanin dabarar da za ta yi wa Lawal ta shiga. Sai ko ga Sadi ya zo wucewa nan da nan ta karɓa ta ce za ta karasa da shi.

Suka gaisa da Lawal a falo, ta nuna zai karɓa ya shigar da su ta ce masa ya bar shi za ta karasa ladanta. Bai ce komai ba, dama a farko gargadin da Fadeel din ya yi mishi ne ya sanya shi dakatar da ita, ya hana kowa ya shigo masa sashinsa idan ba ya nan matukar dai ba Fu'ad ko Alhaji da Ibb bane. Amma ganin kayan wankin ne kawai za ta ajiye ta fito ya sanya shi ba ta wuri shi kuma ya ci gaba da kakkaɓe kakkaben kujeru da kayan kallo.

A lokacin da ta shiga dakin, Fadeel ya zagaya bandaki, yana dab da fitowa ya ji motsin mutum a dakinnasa, bai kawo kowa ba sai Lawal. Ya san ba shi da masaniyar yana gida bai fita ba. Don haka ya fito daga shi sai singilet da dogon wandon sport.

Daidai lokacin da ta ajiye kayan a gefe ta yi wurgi da filo ta ɗaga katifar gaba ɗaya da zummar sanya layar. Kasancewar idanunta ya rufe ko kadan ba ta ga wayoyin Fadeel din dake gefe ba a ajiye. Tana zuci-zucin ta yi ta ƙare kafin shigowar Lawal ya isketa.

Fadeel ya bude kofar ya fito, hakan ba  karamin razanata ya yi ba ta saki layun dake a hannunta suka zube a ƙasan darduma. Mamaki mai tsanani ya kama shi har ya bude baki ya kasa magana. Ya karasa sosai ya kara kallo, tabbas layu ne. Nan da nan ya tamke fuska tamkar bai taɓa wani abu wai shi dariya ba.

"Zamanki a gidannan ya ƙare. Wallahi kin ji na rantse maki ko yau Anti Amarya ce ta haifeki dole ki bar gidannan. Ni Fadeel na fi ƙarfinki, na kuma fi karfin duk wani da zai sanyaki aikata mugun abu don ki ci galaba a kaina."

Jin haka sai kawai ta hau tsuma da borin kunya.

"Ni..nifa ba.."

"Shut up!"

Tsawar da ya yi ya sanya Lawal faɗowa ɗakin. Nan da nan hankalinsa ya tashi, shima idanunsa suka sauka kan layar dake ajiye a tsakar dakin. Fadeel ya hau shi da faɗan don me ya bari ta shigo masa daki alhalin ya gargaɗeshi.

"Ka yi hakuri Yallaɓai, wallahi na yi nayi da ita ta bani kayan gugar na kawo ta nunan ita za ta kai. Shi ne.."

"Shi ne me?!"

Fadeel a zafafe ya tari numfashinsa jikinsa har ɓari yake yi ga tsikar jikinsa da ya tashi gaba daya. Abin da ya faru shekarun baya kawai ya fadomasa a rai, sadda ya kama  Mamar Fu'ad tsamo tsamo a ɗakin Mahaifiyarsa tana barbaɗa magani. Daga ranar ya tsane ta, rashin wayo da wauta kuma ya sanya bai yi tunanin sharewa ba. Tun daga kuma sadda mahaifiyarsa ta taka wannan magani ba ta ƙara zaman lafiya ba da Alhajinsu, har dai a karshe Alhaji ya yi mata sakin wulakanci. Shi kuma ya sha baƙar wahala a hannun Mamar Fu'ad. Ya ji ya ƙara tsanar Murja ninkin ba ninkin. Kuma yanda ya rantse ba zai yi kaffara ba sai Murja ta bar masa gida ubansa idan ko Alhaji ya ƙi to fa shi zai bar gidan gaba ɗaya.

Murja cike da kunyar kamen da aka yi mata ga uwa uba Lawal dake tsaye ya ƙi fita yana kallon ikon Allah, ta durkusa ta kwashi layun ta fice tana dakawa Lawal wata uwar harara kamar idanunta zasu zazzago.

Fadeel ya dafe kai yana mai runtse idanu zuciyarsa na tafarfasa tamkar an kunna ruwan heater. 

"Ka yi hakuri in sha Allahu zan kara kiyayewa."

Gyada masa kai kawai ya yi gami da yi mishi alama da hannu akan ya fita, Lawal ya juya ya fice mamakin wannan hali na Murja da bai taɓa zato ba. Lallai mutum ba abin yarda bane.

Shi kuwa Fadeel sai da ya samu nutsuwa sannan ya fada wanka, ba shi da niyyar fita daga gidan amman daga faruwar al'amarin ya ji gaba daya gidan ya fita a kansa. Kai tsaye wurin Ibb ya tafi, dama tun jiyan yake faman kiransa akan zancen bikinsa da ya taso yana ƙin zuwa yana ba shi uzurirrika saboda damuwar Humaira da batun auren Ibb ke taso masa da shi.

Murja kuwa tana zuwa ta shiga haɗa kayanta, ta gwammace ta bar gidan da ace Fadeel ya fasa zancen nan har Alhaji ya tsane ta ya kuma ƙi jinin haɗa zuri'ar ɗansa da ita. Anti Amarya kadai ta fadawa, nan da nan hankalinta ya yi mugun tashi, ta hau ta da faɗa tamkar ta ari baki. Babban baƙin cikinta ma ba ta yi shawara da ita ba ta yi raɗin kanta.

"Ba ki da wayo ko kaɗan Murja! Wa ya fadamaki samun Fadeel a hannu abu ne mai sauki? Ke kinsan irin karfin ibadar wannan yaron? Toh wallahi ko wani Malamin ba zai nuna masa tashin dare da nafilfilu ba ko an fadamaki baƙin tabon sallar dake goshinsa da goge dutse a goshin ta same shi? Kai Murja! Toh kuwa  ya zama dole ki bar gidannan! Ni zan samu shi Fadeel din nasan siyasar da zan mishi don kar magana ta je kunnen Babansa."

Murja ta kara jin wani malolon abu ya tsaya a ƙahon zuciyarta. Dama ta sani Anti Amarya ba za ta taɓa goyamata baya ba. Ta kuma soma  yarda da yayarsu Rabi da ta ce Anti Amaryar kanta kawai ta sani, ba wani so take yi ta tallafe ta ba shiyasa ta ce  ta sauya dabi'u ta nuna ita wata salihar ce. Ban da haka ai ta san wannan ba abu ne mai sauki ba da kuma zai yiwu kawai a yi duka ɗaya lokaci daya a wuce wajen.

Ta shareta ta cigaba da hada akwatin kayanta. Kafin wani lokaci ta kammala ta fice abinta, Anti Amarya ba ta kara cewa uffan ba, ba karamin ɓata ranta ta yi ba, ita yanzu babban tashin hankalinta yanda za ta rufe maganar kar ta je kunnuwan Alhaji. Ta tsinewa Murja ya fi a ƙirga. Wannan ya sa ko kallonta ba ta yi ba da ta fice. Allah ya taƙaita Hannatu ba ta gidan ta je wurin dangin Alhajinsu.

***
Gidan su Humaira tamkar gidan makoki, babu walwala a fuskar kowanne, Abba kasuwar ma kasa fita ya yi. Mami kuwa ta ƙulle a ɗaka ba wanda ya san me take yi. Ummita kuwa tana kwance shiru kawai har baccin dole ya dauketa sanadin magunguna da ta sha kuma a daren jiya ko kadan fargaba da damuwa sun hana ta runtsa.
Karatun alkur'ani Humaira ta kunna a waya ya karaɗe ɗakin don su samu nutsuwar zuciya. Tana sauraro tana bi a hankali ta hanyar motsa lebɓanta duk cikinsu sun kasa yiwa Ummita kwakkwarar magana don ba su san ta inda za su fara ba. Raihana kuwa kanta ta cusa karkashin pillow tana kuka a hankali tana kuma bin karatun. Ji take yi inama komai dake faruwa a mafarki ne. Amma ina, wannan zahiri ne, shi ne kuma gaskiya mai mugun ɗacin da ke addabarsu.

Hatta da Mubarak ya shiga wani irin hali, komai yake yi Ummita ce a ransa, bisa umarnin Abban ya bi su Yassar shago amma yana zaune cikin mugun ɓacin rai. Ya rasa dalilin da ya sa ta tsaya mishi a ƙahon zuci watakila kuma tsananin tausayi ne da duba da irin kirkin Ummitan yarinya mai kirki da sanin ya kamata. Bai taɓa ganinta ba face da murmushi saman fuskarta, tana da hakuri sosai da sanyi. Dabi'unta abin so ne ga kowane namiji.

***
Mami a hargitse take ta faman danna kiran layin wayar amma abu ɗaya kwamfutar ke nanata mata, a kashe wayar take. Koda ta gaji ta yi wurgi da ita tana mai jan tsaki. Goshi ta dafe cikin tsananin ruɗu. Can kuma ta ji wayarta ta ɗauki ƙara. Ta yi azamar karasawa saman gadon ta ɗauka. Lambar dai da take ta kiciniyar kira ita ce aka kirata da ita. Ta ɗaga cikin sauri.

"Kai Bala! Ina ka shiga ne?"

"Kiyi hakuri Hajiya, chaji na bayar sadda kika kira ba'a ɗaga ba sai mai chajin kawai ya kasheta gudun a yi ta kira. Ina fatan lafiya?"

Ta girgiza kai idanu a runtse tamkar yana ganinta.

"Ba lafiya ba Bala, aiki ya ɓaci! Duk inda mutanen nan suke ina buƙatar ganinsu. Wannan karon ni da su zamu tattauna. Sun min ba daidai ba, na fadamusu dama idan har sakamako bai yi kyau ba to sai sun maidomin hatta rabin kudin da na ba su. Ba za su ci komai daga dukiyata ba tunda har kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba."

"Hajiya ban fahimci me kike son cewa ba? Ke ce fa kika ba su umarnin barin wajen koda kuwa kudaden ba su shiga hannunsu ba? Ta ya ya kuma za ki ɗora musu laifi kacokam?"

"Bala sun yiwa yarinya fyaɗe, yarinyar da ban so hakan ta kasance da ita ba. Da ace waccan mayyar aka yiwa ba zai dameni ba. Yanzu dai mugun abun da suka yi ya bayar da mummunan sakamako, ciki ya shiga."

Bala ya doka salati mai karfi. Can kuma cikin rage murya ya ce.

"Ciki kuma Hajiya? Toh me ake jira da ba za'a zubar ba?"

Mami ta sauke huci.

"Zubarwa ai wajibi ne. Dole na zubarmata da shi ko don gudun tonuwar asirina. Amma yanzu ni ka nemo min su mutanen ko kuma ka aikon lambar shi Babban nasu sai muyi magana."

"An gama Hajiya, zan kira na sanar da shi sai na hadaku a waya don dama ina shirin ce maki ba ya garin ya dan yi bulaguro zuwa Kaduna."

"Shikenan, sai ka turo."

Tana kaiwa nan ta katse wayar tana ji kamar ta zabga ihu, babu abin da idan ta tuna take takaici kamar rashin cin nasarar mallakar dukiyar Abba da ta kwallafa a rai. Ga kuma shirin tonuwar asirinta da ke son afkuwa, matukar cikin Ummita bai fita ba lallai babu shakka watarana abin ɓoye zai fito fili.

***
Mami ta tabbatarwa Abba lalali sai dai a zubar da cikin Ummita gudun zubewar mutuncinsu a idanun duniya. Tun Abba ya na nuna bai amince ba har dai ta ci nasara a kansa ya yarda.

Ranar da zasu je a daren Mami ta shiga wurin Anna don amsa kiranta. Anna ta dube ta a yamutse.

"Sai wani rawar ƙafa kike yi a cire cikin yarinyar nan, idan an cire wa kike tunanin zai aure ta? Shi Sahabin ko kuwa dai shi mijin naki ya ba babban ɗansa aurenta? Ba kya wannan hangen?"

Mami ta ji kirjinta ya buga da ƙarfi. Wannan zance na Anna ko kusa bai mata dadi ba amma sai ta zaɓi ta ɓoye saboda dalilin da ita kadai ta bar wa kanta sani.

"Idan har asirinmu zai rufu mene ne ciki Anna?"

Daƙuwa Anna ta wurga mata.

"Ungo nan nace! Ni dai da ace a asibiti nayi naƙudarki zan iya rantsewa sauyamin ke aka yi ba ke ce jinina ba. Yanzu ke koda wasa idan mijinki ya ce zai hada auren wannan gantalalliyar da ɗansa abin yarda ne a wurinki? Babban ɗanki wanda bai taɓa kusantar zina ba a duniya shi ne za ki yarda a hada shi da ita?"

Kafin Mami ta kai ga cewa komai Anna ta ji an bata amsa.

"Anna, kar ki kara danganta yan uwana da zina, kowa shaida ne ba zina suka aikata ba, kaddara ce da za ta iya faɗawa kan kowa. Sannan idan auren ne ma sai me? Ni ina sonta kuma na rantsemaki a yau Sahabi ya janye da batun aurensa da Ummita to fa ki rubuta ki ajiye ba ta da miji sai ni nan Mubarak!"

Ba Anna kadai ba, hatta da Mami wanda ganin inuwar mutum a farko yasa ta ɓoye abinda ke ranta sai da maganar ta yi mata wani irin duka a kirji. Ta dago tana kallon Mubarak din, sanin da ta yi mishi ba ya taɓa sauya magana. Mutum ne mai magana daya wannan ya yi matukar ɗaga mata hankali har ta kasa siyasar data saba na danne abin a zuciyarta. Fuskarta ta nuna tsantsar ɓacin rai na gaske, idanunta har wani kaɗawa suka yi tsabar bala'i.

"Mubarak! Kar ka kuskura na kara jin makamancin wannan maganar daga bakinka. Wacce kake faɗawa ka dinga tunawa ita ta haifar maku ni. Ka kiyayi harshenka!"

Mubarak ya yi shiru kawai yana jin zafin maganganun Anna har lokacin suna tarfafasa zuciyarsa. Anna kuwa ta hau zagin Mami tana fadin ta yi mata shiru ai da sa hannunta a rainin da yaran suka yi mata. Shi dai ya dubi Mamin ya isar da sakon Abba akan ta fito su wuce asibiti sannan ya kaɗa kai ya bar musu dakin. Mami ta mike ba ta ko biyewa maganganun Anna ba ta bar dakin. Wannan kalma ta so da Mubarak ya furta yana yiwa Ummita ya tsayamata a ƙahon zuci, abu ne da har abada ba za ta bari ya afku ba muddin rai.

***
A kokarin zubar da cikin Ummita aka kusa jaza mata matsala, zubar jini sosai ta shiga yi dakyar aka samu ya tsaya. Sai dai cikin hukuncin Allah mai kaddarawa cikin yana nan daram bai fita ba. Haka aka shafe watanni hr biyu ana fama da abu daya amma cikin bai ko girgiza ba wannan dalili ya sanya Abba cewa a hakura kawai amma gudun masu shiga da fita na gidan Ummitan ta rage fitowa falon idan ya so duk abinda take so a kai mata daki.
Ga biki ya matso amma sun kara neman alfarma an ɗaga bisa hujjar kayan dakin da ba a kammala haɗawa ba na Ummitan. Wannan abu mai yiwa iyayen Sahabi da shi kansa dadi ba, ga raɗe-raɗin da aka kawowa uwar Sahabi wai Ummita na da juna biyu, ko kadan ba ta ji ta amince da zancen ba, da hakan ne ai ta san iyayen Ummitan masu dattako ne ba za su ɓoye musu ba. Wannan yasa inda ta ji zancen anan wurin ta bar shi kuma a cewarta ai ciki ba ya ɓuya, idan har akwai to fa zai fito.

Mami ta yi nasarar samun wayar WIZZY. Wayarsu ta farko ya nuna bai ma san zancen da take yi ba don gaba daya hankalinsa ba a nutse yake ba gani yake kamar an hada baki ne don a kai musu cafka.

Sai da aka kwashi lokaci mai tsawo sannan ta kara nemansa a waya ganin dai cikin dake tattare da Ummita ya ƙi fita uwa uba ga wani irin kulawa da Mubarak ke yiwa Ummita wacce har gobe ba ta da walwala. Wannan abu ya tashi hankalinta ya kuma jefa ta cikin rudani da tsoro. Ya tabbata kenan idan ciki bai fita a cikin Ummita ba za ta iya zama rabon ɗanta nan gaba. Ta kuwa gwammace gwara ta sanar da Wizzy cewa Ummitan na dauke da cikinsa har na watanni hudu don su ga matakin da za a dauka a kai.

Cikin sa'a ya ɗaga wayar.

"Wai Malama ba mun gama aikin da kika sanya mu ba? Kiran da kike yimin na mene ne bayan kin jaza mana asarar maƙudai?"

"Kaga Wizzy, kar ka yimin rashin kunyar banza da wofi! Ni na jazamaku asara ko kuwa ku ne kuka jazamin? Da na ba ku aiki na ce ku ketawa yarinya haddi ne? Shegen halin akuyancinku ya sanya kun afkamata yanzu yarinya tana dauke da ciki har tsayin watanni hudu."

Wizzy ya kantamo wata ashariya ya saki.

"Ciki kuma?!! Don uwarta ita din akuya ce daga yi sau daya sai ciki!"

Mami itama ji tayi tamkar ta sakar masa ashar, da kusa da ita yake a yadda take ji za ta iya shaƙar wuyansa har lahira.

"Ko mece ce ni ba wannan ne ya sa nayi kiranka ba. Mafita nake so, idan kuma babu to lallai kuɗina ya dawo. Sadik shi ne sunanka na gaskiya, kai din haifaffen Katsina ne. Ina da kaf tarihinka na kuma san inda zan sameka, wallahi muddin ka bani matsala sai na yi maganinka."

Shiru ya ɗan biyo baya tamkar ba zai ce komai ba don ba karamin dauremasa baki ta yi ba, ita kuwa Mami ta san komai bisa shawarar Hajiya Lubna, tun ma basu kai ga ba da aiki ba sai da suka sanya aka nemi dukkan bayanan sirri na wadanda suka ba aikin sannan suka amince.


"Hajiya bai kai ga nan ba. Ni dai yanzu kudi mun ci ubansu. Kawai dai

5 Comments On DUKAN RUWA
avatar
daiy drop

2 years ago

Reply

hhh

avatar
daiy drop

2 years ago

Reply

sss

avatar
daiy drop

2 years ago

Reply

sss

avatar
daiy drop

2 years ago

Reply

sss

avatar
north

2 years ago

Reply

hhhhh

Please Login or Register in order to submit comment