Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yanda na san shi. Wato yanzun ya ci moriyar ganga ya yar da koren, ke yanzu ban da ke sakara ce wawiya, kina tunanin har wani karfin iko kike da shi a wajensa? Mutumin da ya dubi tsabar idon mahaifiyarki ya ce ba zai janye kudurinsa na aurar da Futuha ba? Toh wallahi Maryama ki shiga taitayinki tun kafin dare ya yi maki, mazan nan dai babu amana bar ganin wai girma ya soma kama shi, don ya dankaro maki kishiya ƴar zamani ba komai ba ne. Tun wuri ki ƙwatarwa yaranki ƴanci a wajen mahaifinsu, ki murje idanunki dakyau ki daina bari yana wulaƙanta min jikokina akan wasu bare can. Ban da ma mutum mai shegen mantuwa, Isuhu ko kare ne ya fito daga gidan su Fatima zai kalla da daraja? Matar da ta nunawa duniya cewa ta tsane shi har kwanciya ciwo take akan sai ya sauwaƙe mata ta koma garinsu? Mts, Allah ya wadaran naka ya lalace."

Har Anna ta kai aya ita dai Mami ba ta ce komai ba banda huci da take furzarwa, daga ita sai zuciyarta ta bar wa sanin abin da take tunani. Dakyar ta taushi zuciyar ta soma magana bayan sakin ajiyar zuciya mai nauyi.

"Anna ki yi hakuri, babu amfanin mayar da hannun agogo baya tunda mai afkuwa ya riga da ya afku. Na ba ki wuƙa da nama akan ƙwatarwa jikokinki ƴanci, ki yi abin da kika ga ya dace. Sai dai ki sani, ni Maryam ba da yawuna ba saboda daidai gwargwado yarannan su na kyautatamin, ba ni na haife su ba amma su na bi na sau da ƙafa fiye da ma yaran da na haifa a cikina. Kiyi hakuri idan maganata ta maki zafi."

Anna ta wurga mata harara.

"Au haka kika ce ko? Toh shikenan, ni zan san abin yi a kai kamar yanda kika ce. Koda kuwa zan rasa kwabo a asusuna, zan kwatarwa jikokina ƴancinsu, sai ya zama Isuhu ba ya ganin kowame ɗa a gabansa idan ba su ba. Mu zuba ni da ku."

Mami ganin yanda ta ɗauki zafi kawai sai ta miƙe itama ranta a jagule ta bar mata ɗakin. Da ace Anna ta san damuwar da ke cin ranta da ba ta soma ƙara mata fetur a kan wutar da ta riga ta soma babbaka a zuciya da kwakwalwarta ba. Ta ja tsaki ya fi a ƙirga a hanya har ta ƙarasa ɗakinta.

***
Azumi yana ta tafiya har a yau sun kai goma sha shida, lamarin su Tasleem da Abba ya ƙara tsauri musamman da ya fahimci ba su bi zancensa ba na shiga kicin. Futuhar da ta soma shiga, tun bayan faɗan da Abban ya yi ya goyi bayan Humaira sai ba ta ƙara leƙawa ba. Cikin ikon Allah wataran kwatsam sai ga shi a kicin din abin da Humaira za ta ce tun zuwanta gidan banda ranar da ya ji fitar gas ya cika gidan ya shigo, ba ta taɓa ganinsa a ciki ba. Ganin daga ita sai Ladidi da Ummita a kicin din ya shiga bambamin faɗa, a sannan Raihana na fama da Malaria mai zafi har allurai ta sha. Aikuwa har ɗakin ya shiga ya titsa ƙeyar Tasleem da Futuha zuwa kicin din yana gargadin Humaira akan lallai duk sadda ba su shiga ba ta sanar mishi. Tun daga wannan ranar ba su ƙara fashin shiga ba. Sai dai shigar da rashinsa ba amfani don kusan zama suke yi kawai ba sa komai.
Abba ya yi siyayyar kayan sallah, kamar kowace shekara wannan ma da kansa ya yiwa kowa zaɓi idan ka cire samarin da ya ba kowannensu kudi su siya shadda. Yanmatan kuwa atamfa ce iri ɗaya sai dai bambancin kala, sai dubu uku da ya ba kowace budurwa a siya takalmin sallah. Shikenan bai ƙara daga haka ba, su Futuha aka dinga kauɗi ganin Alhajinta ya kawo mata shadda da atamfa har da leshi masu tsada sai kuwa dubu ashirin na mayafi da jaka da kuma ɗan kunne. Tasleem kuwa dayake ta soma shaƙa sai ta budewa Hamza wuta akan ko kyautar biyar bai taɓa ratsawa tsakaninsu ba. Ranar shi kansa ya yi mamaki da ta iya karya bille ta tambaye shi kuɗi, aikuwa ya ce ta turo acc no, take ya yi mata transfer dubu goma sha biyar. Tsabar rainin da ta yiwa kyautar ko faɗawa su Mami ba ta yi ba sai dai sun mata amfani ta siya abin da take so. Su Humaira kuwa Mami da kanta ta kara musu dinki, leshi mai kyau na ɗankwarai ta siya musu su uku kala ɗaya. Ana saura kwana biyar sallah sai ga Anti Jannat a gidan. Zuwanta ya yiwa su Futuha daɗi ko ba komai mace ce mai sakin bakin aljihu ga fankama. Burinta ta buɗa ko don ta nunawa Mami ita fa mijinta mai bayarwa ne, yana da kyauta sosai. Daidai da Anna ta fi ji da ita, abinda ya hana ta zama wajen Jannat din bai wuce na ganin surukanta sun nuna ba su kaunar hakan ba. A farko ta gwada amma aka so samun matsala, dole ta tattara ta dawo gidan da ta raina, gidan Abba.
Suna zaune a ɗaki bayan sun kammala gwada dinkunansu na sallah, ya yi musu cif da cif, washegari kuma sai tafiya kitso da ƙunshi. Sai faman tsokanar Ummita suke yi ganin saurayinta ya kira tana kashe murya a waya, koda ta ajiye Raihana ta dube ta.

"Wai ni yaushe za ki ba Ya Sayyadi damar zuwa gidannan?"

Kasancewar zuwa lokacin sun sani ba kowa Ummitan ke soyayya da shi ba face Ya Sayyadinsu na makaranta hakan yasa suka samu abin tsokanarta. Ashe wai dama yawan tashinta da yake yi ta biya musu karatu mai dalili ne. Ummita ta ɗan harareta.

"Ke me ya hana ki ba Jafar daman zuwa gida? Ni ai mun kashe magana da shi, na ce ya bari sai nan da shekaru biyu ko ma ince ɗaya da rabi idan mun yi candy, tunda yanzu muna SS2."

"Kai Ummita, shekara ɗaya da rabi fa? Gaskiya sun yi yawa ina laifin ma shekara ɗaya?" Faɗin Humaira dake tsaye tana maida kayanta sif. Raihana ta tari numfashinta da sauri ta ce.

"Wai ke ce mai yiwa wata faɗan shekaru sun yi yawa? Allah ya ba Fadeel hakuri. Wallahi idan na tuna abinda kika yi masa sai na ji kamar na yi maki dukan tsiya."

Ummita ma kwafa ta yi cikin kunar rai ta ce.

"Bar ta kawai Raihana, nima ba ki ji raina ba. Kuma babu kunya ba tsoron Allah har faɗamana take yi ya hakura sai nan da shekara. Shi marar zuciyar ina ne da zai biyemaki ya yi zaman jiranki? Ai tana sane, kora da hali ne kawai ta yi mishi. Ba fata nake maki ba, amma wallahi kafin ki samu kamar Fadeel a maza sai dai tsananin rabo."

Humaira ta taɓe baki gami da jan guntun tsaki.

"Kanku ake ji, ni na faɗamaku ina so nayi auren ne? Auren ku yake burgewa ba ni ba. Sai me? Idan ba auren zan fasa rayuwata yanda ya kamata ne? Ya yi ma gangancin zaman jirana ya gani idan haƙansa zai cimma ruwa. Ya ƙare rayuwarsa a tuzuru."

"Allah ya kiyaye wallahi, bakinki ya sari ɗanyen kashi. Fadeel ya wuce nan, kuma ina masa fatan alheri, ya samu haɗaɗɗiyar da ta fi ki komai ƴar kwalisa in sha Allahu." Cewar Raihana.

Haka kawai sai ta ji zafi a ranta, ta ji tana son yin kukan da ta rasa dalili, kawai sai ta fashe da kukan ba tare da ta yi shawara da zuciyarta ba. Raihana ta dubi Ummita kafin su dube ta jiki a sanyaye. Tun tana kukan su na ganin kamar wasa su na rarrashinta, har dai suka ga kamar kukan ba na lafiya ba ne suka fita da sauri suka yiwa Mami magana. Kai abin tsoro Humaira duk iyakar rarrashin Mami ba ta yi shiru ba, hakanan harafi ɗaya ya kasa fita a bakinta. Mami ta juya garesu.

"Meyafaru ta soma kukan?" Nan suka ba ta labarin komai, ta ja hannun Humaira kawai suka fice a ɗakin. Su Raihana za su biyo bayansu ta dakatar da su, can falo suka tsaya yayinda Mamin ta shige ɗaki da ita. Sun yi jugum kuma sai ga Mamin ta fito ta dube su ranta a ɓace.

"Don me za ku dinga yi mata batun saurayin da ba ta so?! Ina gargadinku daga rana irin ta yau koda wasa kada wanda ya kara kuskuren ko ambaton sunansa balle ya yi mata zancensa. Fadeel ko? Daga yau sunan nan ya fice a bakinku." Suka ce toh, su ma abin ya tsorata su, sun kuma kara gaskata zancensu, Humaira na da aljanu musamman da suka ji Mami ta mike tana fadin wai ta samu bacci idan ta tashi komai zai wuce a ranta. Tabbas zarginsu ya tabbata gaskiya, aikuwa ga mamaki Humaira sumul ta tashi tamkar babu abin da ya faru. Yanda ba ta yi zancen ba hakanan su ma ba su kara tada shi ba. Ba ma kamar Raihana mai shegen tsoron aljanu, Ummita sai dariya take mata ciki-ciki ganin ko zama kusa da Humairar ta ɗan rage yi a ranar. A gefe guda kuma ta yi alƙawarin muddin ta je Bichi za ta yiwa mijin yar uwar mahaifiyarta magana akan lamarin Humaira, yana ba da hayaki da maganin jinnu, in sha Allahu za ta karɓo mata.

***


    
 

*LITTAFIN NAN NA KUƊI NE. SIYA AKAN NAIRA ₦400 KI KARANTA BA TARE DA SHIGA HAKKI BA.*


*5407827015*
*FCMB*
*Farida Abdullahi*

09034973645

Assalamu alaikum, ina mika saqon taaziyyar rashin member makaranciyar Dukan Ruwa kuma masoyiyata ta don Allah, Aysha Salisu. Allah ya gafarta zunubanta. Ya sa aljanna makoma, ameen.



****

Malamin ya jinjina kai.

"Aa Murjanatu, kar ki zo gaba kiyi kuka da ni, jimawar da muka yi da da yar uwarki da irin alherin da nake samu a wajenta, ba zan yi abin da zai cutar da ke ba. Ki je nan da kwanaki uku ki kara nazari, idan kin shirya fuskantar kowane ƙalubale da zai biyo bayan aikin, sai ki dawo."

Murja ta yi jim, a yanda ta ke jin Fadeel gani take babu wani abu da ba za ta iya jurewa ba. Can ta nisa ta ce.

"Malam, idan har dai ba hauka ba ne ko wata nakasa naji na gani zan jure."

Ya yi wani murmushi.

"Kina da gaggawa Murjanatu, eh ba nakasa ba ne, amma rushe maganar wannan yarinya a zuciyar Fadeel ba zai amfaneki da komai ba sai halaka. Abin nufi, har abada kema ba lallai ki aureshi ba, idan kuwa aurenku ya tabbata toh fa har ki mutu ba zai kusanceki ba. Ke za ki kasance kare ma ya fiki daraja a rayuwarsa. Ki yi hakuri, ita gaskiya ɗaci gareta kuma kin fi kowa sanin ni Malam Tanimu ba na ɓoyewa mutum koda kuwa idan ya aikata abun zai haɗu da mummunan bala'i sai na sanarmaka idan ka ji ka gani a tafi a haka, sai a tafi. Kin yarda kin amince?"

Ta ji zufa na karyomata, ita da take burin rayuwa mai kyau da inganci da shi? Take burin ta mallake shi su ji dadin tarayyar aure? Kai sam ba ta yi imani da faɗar Malamin nan ba duk kuwa da sanin da ta yi mishi ba na yau ba don haka kawai sai ta ce ya ba ta lokacin shawara, daga haka ta miƙe ta bar wajensa da nufin sauya sheƙa. Wannan Malamin ba abokin tafiya ba ne, ba zai mata yanda take so ba.

***
Sun yi yawo sosai gidan ƴan uwan Abba, wannan kam ita da Ummita ne sai ko Raihana da ta jera da su. Si Futuha kuwa daga gidajen ƙawaye sai ko ƴan makarantarsu na sakandire da suka haɗa reunion aka ci aka sha. Sun je hawan sallah Humaira ta sha kallo, abin ya yi matukar burgeta. Ta dauki hotuna sosai a wayanta, ita kuwa Raihana babu kwalliyar Humairar da ba ta ɗaukarwa Fadeel ba, daidai da bidiyonta a wurin kallon hawa sadda take murmushi da haska bidiyon sarki ta ɗauka ta tura wa Fadeel. Sosai sallar ta yi mata dadi, ta kuma yaba da kalar wasannin da aka yi.

***

Zaune take a falo tana ta kallon yanda a hankali ta soma samun mabiya a shafin Instagram, hakanan hatta a facebook da Raihana ta budemata ta sanya ta a shafukan tallace-tallace na sana'o'i nan ma ta samu abokantaka da mutane da dama, sai dai babu wanda suka taɓa hira a akwatin sirri (inbox). Ita kaɗai tana ta murmushi ganin yanda hotunan girke-girken da ta yi yake samun likes da kuma comment. Jannat ta shigo falon da rawar jikinta, dawowarta kenan daga gyaran gashi. Su Futuha sun fice shoprite sun kai yara, Ummita ta je albarkacin yaran Jannat da suka sa rigimar su sai an tafi da ita don ba karamin shaƙuwa suka yi ba.
Humaira ta ɗago tana dubanta don har ta tsorata ta, sam ba ta tunanin ta yi sallama. Su na cikin sati na uku ga sallah, a yanda ta ji daga Ummita, bai fi kwanaki uku ya rage Jannat ta bar gidan ba wannan yasa take ta shirye-shirye. Kallo ɗaya Jannat din ta yi mata ba ta ko amsa sannu da zuwan da take mata ba ta yi gaba, har ta ɗan yi nisa ta dawo baya tana yatsine fuska.

"Ke, ki dafamin abu marar nauyi yanzu."

Humaira ta amsa da toh, daga haka ta watsa mata harara ta shige. Taɓe baki Humaira ta yi, ko kaɗan ta daina jin ciwon ƙiyayyar da suke mata, ta lura ba ƙasa suka kwasa ba. Jinin Anna ne dole su kwatanta halinta. Ban da ma rashin ta ido, ina uwar mace da zuwa gidan surukai ta tare ko tuna asalinta ba ta yi? Mami ce dai ta sha bamban da su.

Tana wannan saƙe-saƙen zucin wayarta ta ɗauki ƙara. Ganin baƙuwar lamba ya sanya ta yin jim tana tunani, tana da tabbacin ba shi ba ne. Mutumin da gaba ɗaya ya sauya bai ko ƙara kiranta ba, ganin wayar na shirin katsewa ya sa ta ɗauka. Muryar mace ce, ta amsa sallamarta suka gaisa.

"Ina magana da Humaira? Humaira Yusuf mai yin snacks?"

Ai sai ta miƙe tsaye ta hau washe haƙora. Ta amsa cikin zaƙuwa.

"Eh, ita ce."

"Masha Allahu, ina bibiyarki a shafinki na instagram, na ga tallace-tallacenki. Ina son snacks ne, za'a iya samu nan da kwanaki hudu haka zuwa biyar?"

Humaira ta ɗan yi tsallen murna sai ta ɗan toshe baki gudun kar dariyar farin ciki ya suɓuce mata, wannan kusan shi ne order din farko tun da suka soma talla. Nan ta tambayeta kalolin snacks din da take so, ta yi mata bayani, a karshe suka yi sallama da zummar Humaira ta lissafa adadin kuɗinta sannan ta turo acc number. Ai don murna tuni ta mance da batun wata Jannat, gudu-gudu ta nufi falon Mami tana kwala mata kira. Amma ina! Ba ta nan tana bangaren Anna, tsabar rufewar idanu kawai sai ta sa kai har cikin dakin Anna tana kwala kiran Mami. Su na zaune su na hira sai ganinta suka yi. Mamin ta nemi ba'asi nan ta hau sanar da ita yanda suka yi da mai order. Itama sai murna da hamdala.

"Kai Alhamdulillah. Dole kiyi murna, maza muje ayi lissafin sai a turamata."

Da murmushinta mai bayyana kyawunta da tsantsar kamanninta da Abba ta amsa da toh. Har ta juya za ta fice ta ji tsawar Anna.

"Ke!"

A firgice ta juyo kuwa, har ga Allah sai a sannan idanunta suka buɗe. Ta tuna inda ta faɗo da kuma kuskuren da ta yi na rashin sallama ballantana gaisuwa. Kawai sai ta durkushe ta gaida Annar, Jannat ta karasa ta ja kunnenta har sai da ta saki ƙara.

"Don ubanki dayake kin raina mutane uwarmu sa'arki ce da har ki faɗo ɗakinta kamar na uwarki?! Ba aiki na sanyaki a kicin ba? Kema kuma Mami laifinki ne."

Daga nan ta juya harshe zuwa buzanci ta cigaba da sababin faɗa, Anna itama tana taya ta. Daga yanda Mami ta yi shiru ta haɗe girar sama da ta ƙasa Humaira ta fahimci magana suke gasamata. Nan da nan jikinta ya yi sanyi, a gefe guda ga na gorin ɗakin uwa da aka yi mata, ba don darajar Mami dake a idanunta ba sai ta faɗamusu mai zafin da ba zasu ƙara mararin daɗa kwana ko ɗaya a gidan ba idan har su na da sauran kunya.

"Humaira, tashi ki je, ki yi aikin da ta sanyaki kafin na zo." Muryar Mamin ta katse ta. Ta mike tana mai amsawa da toh gami da share kwallar da ta cika idanunta. Bayan fitarta Anna ta ce.

"Maryama ban san irinki ba, ban san wa kike son ki burge ba. Wato har wani girki za ta fara na harkar kuɗi? Wannan naki salon uƙubar ce ko kuwa dai son yarinyar ne fiye da naki yaran ya rufemaki idanu kike son ta kere su a komai ta yi musu zarra? Idan bacci kike ki farka, kin nemawa yarinya har ya zama mai arziki, a kuma yanda naji zaƙin miyarta ina mai tabbatar maki watarana sai ta fi ki kuɗi. Tukunna ma, kuɗaɗen kina nufin ita za ki dinga damƙawa?"

Mami ta yi shiru na ƴan sakanni har Anna ta ƙara tankawa yayinda Jannat kuwa ta ja tsaki don tana jin haushin yayarta sosai, tana abu tamkar a duniya su Humaira ta haifa ba su Futuha ba. Can dai Mamin ta yi magana.

"Ta asusuna kuɗin za su shigo."

Murmushi Anna ta yi mai tarin ma'ana kafin ta ce.

"Na sanki Maryama, ni na haifeki. Kar ki zo mini da rainin hankali da wayo kinji ko? Wato ni ga sakara shi ne za ki rufe ni ruf, to ai koda ta asusunki kuɗaɗen suka shigo a yanda kike nunawa yarinyarnan kamar ki lashe ta, ke me iya yin hidimar ta ce ba naki ko yaranki ba. Kaiconki Maryama, lallai idan ba bi a hankali ba yarinyar nan watarana sai ta watsa maki borkono a idanu. Kina wasa da wuta."

Janant ta kalli Mami, sai kuma ta girgiza kai.

"Anna, zai fi kyau ki bar wahalar da bakinki a kan wannan saboda ɗiyarki ta yi nisan da ba ta jin kira. Ita mai miji, burinta ta nunawa duniya ta fi kaunar ɗa wani sama da nata yaran. Idan kin ji yanda yarannan ke ƙorafin nuna halin ko in kula da take yi musu sai ki rantse ba ita ce ta yi naƙudar su ba a bola ta tsinto su. Babu ma kamar su Yassar wadanda su ubansu bai sakarmusu sun ji dadin rayuwa irin na matasa sa'anninsu ba, su ba su sami wata kyakkyawar kulawa a wurin uwar ba. Ni na rasa irin wannan gidan da rayuwar cikinsa. Ba haka nake rayuwa a gidan nawa mijin ba, shi koyaushe burinsa ya wadata mu da abinda za mu huta ni da yaransa, amma tun da na rayu a gidannan har na yi aure, mijinta bana jin ya kashemin sama da dubu ɗari biyar a rayuwa."

Mami ta miƙe tsaye tana duban Jannat, zuwa yanzu ranta idan ya yi dubu to ya ɓaci.

"Ya isheki hakanan! Ke tsabar rashin kunya har kya kalli kwayar idanuna ki faɗan magana? A gidan dai da kika raina nan kika rayu sannan ko Yusuf bai kashe maki sama da kuɗaɗen ƙaryar da kika buga lissafinsu ba, ai kin ci kin sha daga jikinsa. Ke yanzu idan da kina can wannan dajin kina rayuwa, har kin isa ki ga shi mijin da kike tutiya da shi ki aura? Ni na isheki! Nan da kike ganina kar nake, na fi ku sanin inda ke mini ciwo. Ba damuwarki ba ce kuma balle ki sani, idan har ba za ki dauke idanu daga lamuran gidana ba, ki tattara ki..."

"Maryama!" Tsawar da Annan ta bugamata ne yasa ta yin shiru tana fesar da huci mai zafi, ta kalli Anna sai kuma ta juya ta fice daga ɗakin. Jannat nan ta haukacewa Anna wai Mami ta yi musu gorin zama a gidan don haka su tattara su bar mata gidanta. Anna dai ta dinga lallaɓa Jannat, ta sani muddin ta bi cewarta ta bar gidan to fa komawa can wani ƙauyensu dake garin Agadez ya kamata, yanda ta fito ta ɗanɗani rayuwar daula koda ace bai kai yanda ta ke so ba, ta gwammace ta cigaba da rayuwa a nan. Ta sani babu ta yanda za'a yi shegiyar surukar zamani irin ta Jannat ta amince da zamanta a gidan ɗanta. Dakyar dai ta samu Jannat ta janye ƙudurinta, tsana da haushin Humaira ya ƙara ninkuwa a ƙasan ranta.

***
Humaira kuwa sai ta nemi murnar da take yi na Oda ta rasa, jiki a saluɓe ta yi mata dahuwar dafadukan macaroni mai busasshen kifi. Ƙamshinsa ya karaɗe kicin ɗin da falo. Koda ta kammala ta haɗa komai a ƙaton faranti ta kai mata babu godiya ba kallon arziki, itama ba ta sa a ka ba kawai ta jya da zummar tafiya.

"Ke zo nan!"

Muryar Anna ta ji, ta runtse idanu kirjinta na dukan tara-tara cike da tunanin da wanne kuma Annar ta zo yanzu ta juya ta koma ta durkusa ba tare da ta kalleta ba. Ta soma magana a kausashe.

"Ɗago ki kalleni nan, ni da kike gani dai na fi ƙarfinki. Mun ci dubu sai ceto, zuri'ar Mamman Ɗan Jika daidai nake da kowane bafillace mai taƙama da asiri. Har mu za a gayawa asiri? Tun wuri ina gargaɗinki ki fice a rayuwar ɗiyata, idan ma wani mugun ƙullin aka kawoki da shi don ki shiga tsakaninta da yaranta toh ahir ɗinku, ni dai na fi ƙarfinku balle kuma tsatsona. Ki kama kanki tun kafin na ɗau mummunan mataki a kanki. Ɗan girkin da kike taƙama kin iya ni mai iya juya lamarinki da shi ne, idan kuma kina da ja ki cigaba kar ki fasa. Asir dai ba za ki nunamana ba, mun saka Allah a gaba ne kawai shiyasa muka watsar. Amma muddin kika ce za ki cigaba da juya ɗiyata kamar waina da shiga tsakaninta da yaranta da ta haifa da cikinta ni nan zan nunamaki iyakarki."

Tana kaiwanan ta juyar da kai tana girgiza ƙafa na bala'i. Humaira ta dubi Anna dakyau, an zo gaɓar da ba za ta jure ba sai ta ba ta amsa ko yaya ne. Ƙazafin sihiri ba za ta jure shi ba don haka ta soma magana da wani irin ƙunar rai.

"Kiyi hakuri Anna, amma kalamanki laifi ne ko a wurin Ubangiji, kin yimin mummunan zato kin kuma yimin ƙazafi. Lallai Ubangiji zai yi mana hisabi a gobe ƙiyama. Na samu kyakkyawan tarbiyya a wurin Dada da Kawuna irin wanda nake da yaƙinin ko uwar da ta haife ni sai haka. Ban san boka ba balle mugun malamin da zan je ya yi min wani mugun aiki ba, asalima ban da a fina-finai da kuma labari ban taɓa karo da su ba. Wanda ya riƙi Allah, ai ba zai aikata abin da kuke yi ba. Kullum cikin zagi da aibata musulmi ɗan uwanku, ni Humaira babu wani mahaluƙi a duniyarnan da zan kai ya yimin aiki a kan wasu, kenan idan nayi hakan ma ban riƙi gaskiya ɗaya ba, ban yi imanin Allah zai iya amsamin addu'ata ba komai muninta komai kyawunta ba kenan. Ai Ubangiji ya wuce duk zatonku. Balle ma ban taɓa roƙo mai muni kan kowane ɗan uwana musulmi ba, kuma ba zan fara akan Mami ko yaranta ba. Tsakanina da Mami sai addu'a, ta yimin riƙon da ya sa nake jure dukkan wani abu da za ki yimin ke da jikokinki. Har abada kuma bisa darajar Mami ba zan taɓa daina ganin mutuncinki ba. Kiyi hakuri idan da abin da na faɗi mai zafi."

Tana kaiwa nan tuni ruwan hawaye sun wamke fuskarta, a bisa tilas ta kalli idanun babbar da ba ta riƙe girma da tsufanta ba ta gasamata maganganu. Ita ta fi Anna jin ciwon haka, sai dai haka take, ba ta iya hakuri idan aka kai ta bango musamman idan abin ya kasance ya haɗu da baƙin ƙazafi. Juyawarta ya yi daidai da saukar igiyar chaja a gadon bayanta, Jannat ce wacce a farko ta yi ɗif

5 Comments On DUKAN RUWA
avatar
daiy drop

2 years ago

Reply

hhh

avatar
daiy drop

2 years ago

Reply

sss

avatar
daiy drop

2 years ago

Reply

sss

avatar
daiy drop

2 years ago

Reply

sss

avatar
north

2 years ago

Reply

hhhhh

Please Login or Register in order to submit comment