Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wacce tuni ta yi wanka ta sauya shiga cikin riga da siket ƴan kanti ta yi murmushi daidai sadda ta motsa tukunyar miya ta rufe gami da rage wuta. Juyowa ta yi tana kallon Ummita da ta mayar da hankali tana juye farar shinkafar da ta dafa a cikin ƙaton warmer.

"Ban damu da abin da kowannensu zai ce ba, ban kuma damu ko Raihana ta sauya ba ko aa, abin da na sani shi ne, ko a gaban waye, kuma a ko'ina ne, su din ko naƙi ko na so, ƴan uwana ne na jini, ba zan taɓa ganin abin da zai cutar da su na yi shiru na zuba ido ba, sai inda karfina ya kare. Kar mu ja zancen Ummita, ni yanzu damuwata Mami, ta ina zan soma wanke kaina a wajenta? Na mari diyarta har shatin yatsuna sun bayyana ƙarara a saman fuskarta, anya kuwa za ta karɓi dukkan hanzarina? Ni dai na san soyayyar uwa akan nata, dagaske ne Mami na yi mana so na hakika, amma wace uwa ce za ta kara kallonka da ƙima alhalin ka sa hannu ka daki nata?"

"Sai ni nan, Maryam."

Gaba daya suka kalli bakin ƙofar shigowa kicin din, Mami ce wacce ta tsinkayi zantukan Humaira na karshe. Humaira ta zuba mata idanu tana so ta ga ko za ta fahimci yanayinta, ba ta gane komai ba sai murmushin da ta gani kwance saman fuskarta. Kicin din ta karasa shigowa sosai ta ce.

"Sai ni nan Maryam, haba Humaira, kina zaton ba ni da hankali ne? Na sani duk yadda aka yi akwai wani abu da Raihana ta yi kika yi mata wannan hukuncin. Kar ki manta tazarr fitarku ba nisa, da nayi nazari sai na ga kodai wani wurin za ta je da bai kyautu ba kika bi bayanta? Kar ki sa komai a ranki, koda ba ki faɗi komai ba ni na fahimceki kinji ko?"

Humaira ta sauke nannauyan ajiyar zuciya na samun nutsuwa. Wai mami wace iri ce acikin matan uba? Komai nata daban ne, kirkinta da kawaicinta akwai mugun yawa. Sai kunya ta lulluɓe ta, ta sunkuyar da kai.

"Kiyi hakuri Mami. Ban yi..."

"Bana buƙatar ji ko sanin komai kinji ko? Komai ya wuce. Ku hanzarta shirya kayan abinci, Abbanku na jin yunwa."

Suka amsa da toh a gaggauce suka ci gaba da aiki, Mami ta fice daga kicin din fuskarta ba yabo ba fallasa.

***
Kwance take saman gadonta tana buga game a waya, hankalinta kacokam ya tafi a game din sai ga kira ya shigo. Ta yi tsam tana duban wayar, lamba ce da ba ta da masaniya a kanta. Ganin haka sai ta katse kiran ta ci gaba da game dinta, aka kara kira, ta katse, a na uku ta ɗaga a fusace amma sai ta danne ta yi sallama. Jin muryar namiji ya amsa sallamar ya sa ta jin wani abu tun daga tsakiyar kanta har zuwa yatsun ƙafa, ba ta san ma'anr hakan ba.

"Ina mai ba da hakurin yi maki katsalandan a rayuwa. Hope ba za ki damu ba idan na ce jiya na karɓi numbernki wurin Ibb Gusau."

Shiru ya biyo baya, ita ba ta fahimci komai ba don har ga Allah ta mance da su. Jin shiru ya sa Fadeel ƙara magana a tausashe.

"Ok, ba ki gane ba ko? Jiya ni da abokina da ya ba ki numbernsa akan wannan saurayin ƙanwartaki, Musaddam nake tunanin sunansa ko?"

Nan da nan ta tuna komai, wannan me kama da aljanun ne mai shegen kallo. Ta ja guntun tsaki kaɗan.

"Uhm, na gane. Ina fatan lafiya?"

Ya yi shiru yana jin amsarta a wata kala na daban, madadin ta ba shi haushi sai kuma ya ji bai ji haushin nata ba.

"Lafiyar ce ta sa na kiraki. Suna na Fadeel, magana nake son mu yi amma ta fi ƙarfin waya, idan kin ba ni dama ko zan iya sanin kwatancen gidanku?"

Ranta ya soma ɓaci, ta ji wani abu na taso mata.

"Idan maganar ba za ka iya yinta a waya ba don Allah kada ka ƙara gangancin kirana. Hakan zai fi maka alheri, sannan ina bukatar ka goge lamba ta a wayarka, tunda ba wani muhimmin abu ne ya sa ka kira ba."

Tana kai wa nan ta katse kiran, ta yi wurgi da wayar saman gado, game din ma ya fice a kanta. Ita kaɗai ce a ɗakin, sai ga Raihana ta shigo. Ko kallonta ba ta yi ba ta mike ta faɗa banɗaki, koda ta fito ganin Raihanan zaune saman gadonnata yasa ta mamaki. Fuska a ɗaure ta ƙarasa.

"Malama lafiya?"

Jiki a sanyaye Raihana ta soma magana.

"Kiyi hakuri Humaira, na ja an maki faɗa an kuma zalunceki. Don Allah ki yi hakuri. Ina neman gafararki bisa dukkan abin da na taɓa yi maki a gidannan. Ban kara gasƙata kaunarki gareni ba sai a jiya da kika shanye faɗan Abba ba ki faɗi ainahin abin da ya faru ba. Wallahi na ji kunyarki sosai, kiyi hakuri ki yafemin."

Taɓe baki Humaira ta yi tana fadin.

"Ya wuce. Kar ki damu."

"Dagaske kike?"

Ta tambaya da sauri kamar za ta yi kuka don muryarta ta karye, Humaira ta zauna a gefe.

"Ni ban taɓa binku da kallon maƙiyana ba, kallon da nake maku na ƴan uwana ya bambanta da irin wanda ku ke yimin. Sai dai dukkan wannan ba zai sa na ga abin da zai cutar da ku na kasa magana ba. Idan na yi hakan na ci amanar kaunar da Mami ke nunamin. Raihana mutunci da darajar mace ya fi gaban ta tsaya ta siyarwa wani ƙaton banza a waje. Musaddam da kike gani wallahi ba zai taɓa aurenki ba matuƙar kika yarda kika ba shi kanki a waje, ke koda ba ki bayar ba, yaron ba aure ne a ransa ba face iskanci. Idan kuma dagasken auren yake sonki da shi, meyasa bai taɓa zuwa nan ƙofar gidanku da sunan zance ba, kema kin san karya ne kawai. Tun wuri ki yiwa kanki faɗa ki rabu da shi zai fiye maki alheri."

Raihana da tuni ta soma hawaye ta kamo hannun Humaira.

"Toh naji Humaira, amma wallahi ina sonsa, wani irin so ne da ban san yanda zan fara yakice shi ba a rai. So ne da ya rufemin ido naji ko me Musaddam zai nema a wurina zan iya yi mishi."

Sai kuma tausayinta ya lulluɓe ta, tana kuma godewa Allah da bai ɗora mata son kowane ɗa namiji ba balle har ya wahalar da ita.

"Wannan son za ki yaƙa, domin halaka ne a wajenki. Musaddam ba sonki yake yi ba muna nan da ke watarana za ki ban labari. Ki kai kukanki wurin Allah sannan ki shagaltar da kanki wajen duk abin da kika san zai dauke maki hankali daga tunaninsa. Nima kuma zan tayaki addu'a har sai Allah ya amsa, ya rabaki da wannan makahon son. Ke ina kika hango dacewarki da shi wai? Wallahi ta ko'ina ke din ba ajinsa ba ce, ban da ma dai shi son da kike ikrari bai san inda zai je ba, ai sawun giwa ya shafe na raƙumi."

Murmushi Raihana ta yi cikin jin salama, sai kuma hira ta buɗe tsakaninsu, tana ba ta labarin ainahin yanda aka yi ta hadu da Musaddam din. Humaira ta gefen ido na kallon wayarta da ke silent tana ta haske alamar shigowar waya amma ta yi biris da ita. Su na a haka Futuha ta dawo daga makaranta ta iske su, mamaki ya dabaibayeta, ta cire facemask din da ta sa don ɓoye kumburin gefen bakinta da Humaira ta daka, ba ta cewa Raihanan komai ba sai zama da ta yi gefen nata gadon tana ci gaba da kallon ikon Allah. Ita kuwa Humaira ko ta nuna ta san da wanzuwar wata a dakin bayan su. Can kuma Raihana na juyawa tana yiwa Futuha magana ta ga hasken wayar Humaira ta jawo.

"Lah, kinga fa kiranki ake ta yi. Lamba ce. Kodai Ibb ne?"

Jin sunan da ya fito bakin Raihana ya sa Futuha zaro ido waje a razane. Ita kuwa Humaira fuska ta yamutse.

"Waya sani, tun dazu ya kira wai wani kwatancen gidanmu."

"Wane Ibb din kika nufi Raihana?"

Suka dube ta, sam Raihana ta mance, yanzu me za ta ce idan Futuha ta dage akan son sanin komai? Kada dai allura ta tono garma. Ita kuwa Humaira sai a sannan ta tuno ashe fa a hirarsu tana jin Futuha na yawan maganar son da take yiwa Ibb Gusau da haduwarsa. Kodai shi ne Ibb din da take magana?

"Ibb Gusau wanda kika sani."

Humaira ta furta da murmushi saman fuskarta, ta karbi wayarta a hannun Raihana ta katse kiran amma sai ta sa a kunnenta kamar gaske ta hau fadin.

"Assalamu Alaikum, ina neman afuwa ka kira bana kusa. Fatan ka karasa gida lafiya?" Tana kaiwa nan ta sa kai ta fice daga dakin, sai da ta isa falo sannan ta kwashe da dariyar ganin yanda Futuha ta cika tayi tam har gefen bakinta da ya kumbura sumtum yana kyalli. Ta dai san ta harba mata bomb a zuciya.

10

Dariya take yi har ta shiga kicin ɗin, Ummita dake amsa waya tana lumshe idanu ta yi azamar katsewa tana dubanta. Humaira kuwa ganin haka ta karasa fuska dauke da walwala tana bin ta da kallon tsokana.

"Waya kike amsawa ko? Shi ne ina shigowa kika yi saurin katsewa. Nidai ya kamata zuwa yanzu na san waye wannan majnun ɗin naki."

Ummita dai ba ta tanka mata ba sai maida hankalin da ta yi wajen ɓarar tafarnuwa tana murmushi, sai kuma ta share zancen da hanyar fadin.

"Wai dariyar me kike yi ne?"

Sai a sannan ta tuna abin da ta yiwa Futuha, dariyar ta kuma taso mata. Ta fayyacewa Ummita labarin, baki buɗe take kallonta.

"Ke kuma ina kika samu lambar shi?"

Ita shaf ta mance Ummita ba ta da labarin komai, ta yi ajiyar zuciya. Labarin da ba ta so bayarwa ba amma ya zama dole ta sanarwa Ummita don ba ta da yar uwa kuma aminiya sama da ita. Ta labarta mata duk abin da ya faru da sanadiyyar marin Raihana ta kara da jan tsaki da fadin.

"Shi ne wannan mayen ya takuramin da kira fa, toh ita Raihana ta yi zaton ma Ibb din ne. Ni kuma don na shaƙawa ƴar banza shi ne na sa wayar a kunne ina wayar gangan na soyayya."

Ummita da iyakar burgewa yar  uwar ta burgeta sai ta shiga murmushi kawai da mamakin kaifin hankali da tunaninta, ta sani ko ita ba lallai ta iya shiru a irin wannan gaɓar ba. Amma ta gwammace kowa ya yi mata kallon rashin kyautatawa akan dai ta bayyana gaskiyar abin da Raihana ta aikata. Sai kuma karar wayar Ummitan ya katse tunaninta. Da sauri har su na rige-rigen ɗauka ita da Humairar, sai dai a karshe wayar ta faɗa hannun Humaira tana dariya, ga nata wayar ta na ta haske shaidar faɗowar saƙo amma ko a jikinta.

"Ki yiwa girman Allah kada ki ɗaga." Gwalo ta yi mata suka hau zagaye a kicin din.

"Sai kin rantse cewar za ki fadamin ko wane ne mai kiran."

Da sauri ta amsa.

"Eh wallahi zan fadamaki, yanzu dai ban wayar."

Ba musu ta ba ta tana dariya, ta ja kujera ƴar tsugunno ta zauna tana duba nata wayar da saƙon ya faɗo tun ɗazun.

_*Kar ki yi tunanin akwai abin da zai sa Fadeel ja baya ko tsoro. Ki tambayi wadanda suka san waye shi, yana da naci akan abun da zuciya da gangar jikinsa suka yi na'am da shi. Ba shi da saurin karaya, ba kuma ya jin zai soma daga kan ɗiya mace. Ina kuma farin ciki shaida maki ke ce halittar farko a mata da na ji zuciyata ta yi na'am da kasancewarta rabin jiki kuma abokiyar rayuwata. Nasara tana tare da wanda ya miƙa lamarinsa ga Allah. Have a nice day.*_

Ta karanta har da karkata kai kusan sau uku, sai ta ji ma abin kamar irin a fina-finan da ake haskowa a tashar Hausa da su Tasleem ke kunnawa. Ranta na wani irin huci da zafi, a gefe guda kuma duk da wannan radadin wai sai ta ji tana so ta san ma'anar kalmomin karshen da ya rubuta mai kama da farasanci da turanci.

"Lafiya ki ka ba waya hankalinki?"

Muryar Ummita ya katse mata tunani, ta isa wajenta ta miƙa mata waya. Har a sannan hausarta ba ta dawo daidai irin ta Kanawa ba.

"Ɗan fassaramin ƙarashen saƙon nan, me yake nufi?"

Ummita ta karanta tun daga farko, tun kuma somawarta take zabga murmushi don ba ƙaramin burgeta ya yi ba.

"Fatan alheri ya yi maki a wannan rana. Kai Humaira wannan mutumin akwai iya tsara kalami, ina ji a jikina kin samu mijin aure."

Guntun tsaki Humaira ta ja gami da warce wayarta tana ƴar harararta.

"Ai ke ce mijin, ni raba ni da wannan shirmen soyayyar kin ji ko. Ba ni da lokacinsu."

"Anya Humaira kalau kike kuwa? Ko dai sai an haɗa da addu'a?"

Yamutse fuska ta yi kawai ta kwashi tafarnuwar ta dauraye ta watsa a turmi ta hau daka. Ganin haka itama Ummita ta share batun.

A gefen Futuha kuwa, gaba daya ta yo kan Raihana.

"Ke! Wane Ibb din ki ke nufi ne?"

Raihana ta yi jim, ba ta son ta ce Ibb Malaminta allura ta tono garma don haka sai ta kife ta da fadin.

"Ba fa wanda kike zato ba ne, wannan wani Ibb ne Ibrahim sunansa suka hadu da ita a hanyar islamiyya."

Nannauyan ajiyar zuciya Futuha ta yi kafin ta juya ta koma gadonta tana jan tsaki.

"Toh barkanta, amma da ace Ibb da nake mutuwar so da kauna ne wallahi sai na koyamata hankali. Ke kuma wani sabon salon gulma da munafunci tun da ta wanke maki fuska da mari kike wani shakkarta har da taya ta hira. Ke kika sani."

Raihana dai ba ta tanka ba ta mime ta bar mata ɗakin. Amma ta sa a ranta babu wani abu da zai sa ta kara biye musu wurin nunawa baiwar Allah da ba ta ji ba kuma ba ta gani ba ƙiyayya kawai saboda don zuciya irin nasu.

***
Gidansu cike taf da jama'a sakamakon daurin auren Fu'ad da aka yi a ranar, haka ya dinga kutsawa ransa duk a ɓace har ya shige bangarensu, kai tsaye dakinsa ya nufa, tun daga falo ya cire hularsa ya yi jifa da ita, hakanan babbar rigarsa blue itama ya ajiye saman kujera kafin ya zauna ya shiga kokarin cire covershoe din da ke a ƙafarsa da kuma safa. A duniya Fadeel ya tsani hayaniyar jama'a, wannan ta sa kansa har wani sarawa yake yi. Ya ja guntun tsaki gami da kwantar da kai jikin kujerar ya lumshe idanu. Zafi biyu ya haɗe mishi, ga na rashin samun haɗin kan yarinyar da yake jin ta a ƙoƙon rai, ga kuma wata irin yunwa da yake ji domin ko karin kumallo bai yi ba suka fice masallaci wurin daurin aure. Kowa kuma a dangin sai ya yo kansa da tsokana a wajen, su na fadin saura kai babban yaya. Wadanda ba su da labarin dawowarsa kuwa, sai a ranar suka gan shi. A hankali ya bude lumsassun idanunsa ya murza yatsunsa suka yi ƙara, har wani zogi suke yi mishi saboda gaisuwar da ya dinga yi da jama'a. Lokaci guda kuma ya miƙe ya nufi bandaki, hannun ya wanke tas da hand sanitizer sannan ya fito rike da karamin tawul yana gogewa. Ya yi daidai da shigowar Ibb tare da wani dan uwansu Imran.

Sallamarsu ya amsa ya koma mazauninsa har da kwanciya wannan karon. Kafin Ibb ya yi magana ya riga shi.

"Wai so ku ke na mutu? Yunwa fa nake ji."

Harararsa ya yi.

"Kai dai an yi ɗan iska, muna can Alhaji ya sa mu nemoka ku gaisa da abokansa ashe kai nan ka yo? To sai ka tashi ka shirya muje idan ya so kafin mu dawo na yiwa Anti Amarya magana a kawo mana abinci."

Fadeel ya lumshe idanu.

"Kasan Allah ba zan iya fita ko'ina ba, ni fa ji nake idan ma na kara sa ƙafa na fita cikin wannan ranar hanjin cikina za su fito waje."

Imran ya kwashe da dariya, shi kuwa Ibb kamar ya shaƙo amininnasa haka yake ji. Yana niyyar magana kuma sai ga kiran Alhaji karo na uku. Ya ɗaga ya mishi bayani, dama bai tsammaci faɗan Alhajin ba, cewa ya yi babu komai maza ya yi waya a kawomusu abinci. Da wannan suka yi sallama shi kuma a nan take ya yi kiran Anti Amarya ya sanar da ita.

A bangaren Anti Amarya wacce ta ci ado cikin arnen leshi ruwan toka da ya sha adon stones, ga ƙunshi ta yi sai baza ƙamshi take, jin wayar Ibb ya sa  da rawar jiki ta amsa ta ba ɗaya daga cikin hadiman gidan Larai umarnin haɗawa Fadeel da abokansa abinci za ta turo a kai musu. Ta shiga falonta inda yan uwanta hudu ke zaune su na shan hira. Uku a cikinsu matan aure ne, ɗaya yayarta sai sauran gaba daya ƙannenta. Ƙanwarta Murja dake kwance tana danna waya ta kai wa duka a ƙafa.  Ba shiri ta mike zaune.

"Ke tashi maza ga dama ta samu, jeki wurin Larai na sa ta haɗa abincin su Fadeel ki kai musu, kika sani ko Allah zai sa a dace ko cikin abokansa wani ma ya ce yana so?"

Jin haka babbar yayarta Saddika ta amshe.

"Ke wallahi hakane kam, tashi Murja, Allah ya ɗora ki akan su."

Murja ta haɗe girar sama da ƙasa.

"Nikam wallahi Fadeel nake so. Shi dai za ku taya ni addu'a ya ce yana sona."

"Kin ji wawiya, ke kanki kinsan kaf abokansa ma babu na yar wa musamman Ibb. Ai dai kinga irin jama'arsa da suka kawo masa ziyara muna nan dake a gidannan tun zuwansa ko?"

Murja wacce ta zo hutun makaranta gidan ƴar uwarta ta, ta mike tana gyara zaman ɗaurin dankwalinta.

"Nidai kam shi nake so, ai duk kyawunsu ba su kai shi ba. Malam ga aji na musamman. Kiga fa ko sadda su Sholy suka zo gidannan ko kallo basu ishe shi balle su ga haƙoransa. Nima din ba.."

"Ki yi zaman hira har sai ya gaji ya turo wani ya karɓar musu abincin. Shashasha marar wayo kawai. Ana kai ki kina ƙin zuwa. Ke kika sani. Zauna har ki yi biyu babu."

Jin haka da sauri ta fice daga falon tana dariyar maganar Zuwaira, mai bi wa Anti Amarya.

A kwando ta ga Larai ta haɗa komai har da cokula da farantai, ta kinkima ta yi gaba inda ta tsallake yan uwan Alhaji da suka zo daga ƙauye ko kallo ba su ishe ta ba ballantana ta yi tunanin gaishe su. Su kam suna hau gulmarta da harshen fulatanci. A ƙasan ranta ta ja Allah ya isa.

Tana zuwa ƙofar ta kwankwasa, Ibb ya ba da umarnin a shigo. Lokacin dukkansu har Imran sun cire babbar riga ana shan iskar fanka ana hira, sun zama su biyar a ɗakin sakamakon shigowar abokan Ibb biyu, Saifullahi da Idris. Da sallama a bakinta ta shiga, kasancewar Fadeel ne a saitin ƙofa ya bi ta da kallo ɗaya ya kauda kai ya maida saman kwandon dake hannunta. Dama abin da yake jira kenan, ita kuwa kusan zaucewa ta kusa yi sakamakon kwayar idanun Fadeel da suka haɗu da nata, gaba daya ta ji ta ƙara narkewa a tekun sonsa. A ranta tana ayyana ba gudu ba ja baya shi din dai ranta ke so. Babu wani abokinsa da ta ga ya burge ta, gwara ma Ibb don a baya tana mishi kallon hadadden saurayi duk sadda suka hadu ya zo gaida Alhaji, ita kuma ta zo gidan, yanzu kuwa ta fahimci Fadeel ya kere shi.

"Ba sai kin zuba ba, bar shi za mu yi serving da juna." Fadin Ibb fuska a sake ganin ta sauke kwandon ta hau fito da kayayyakin tana shirin buɗe warmer.

Ta kalle shi kadan tana dan murmushi.

"Lah ba komai, bari na zubamaku, wannan ai aikinmu ne mata."

Bai kara magana ba sai mayar da hankali ya yi ga Imran dake nuna mishi wani hoto a waya. Shi kansa Ibb ba mai yawan zance ba ne sai ta kama, don haka bai hanata ba. Shi kuwa gogan kallonta bai kara ba, sai Idris da ya zuba mata ido kamar ya haɗiye ta. Shi dai kam lokaci guda ya ji ta kwanta masa a ƙoƙon rai. Don haka bai yi ƙasa a gwuiwa ba ya dubi Fadeel.

"Wannan ƙanwarmu ce?"

Tsaf Fadeel ya karance shi, don haka ya gyada kai kawai fuska ɗaure. Ita kuwa da rawar jiki ta miƙa kwanon abinci ga Fadeel. Madadin ya karɓa sai ya dube ta. Ta ji kallon tun daga tsakar kanta har tafukan sawayenta.

"No, ki fara ba su tukunna."

"Kai Malam, idan za ka karɓa ka soma ci ka karɓa. Tun ɗazu ka ke mana raki da kukan yunwa kamar wanda ya shekara bai ci ba. Wannan ta ya ya kake azumtar watan Ramadan?"

Jin haka ya ja filo ya jefawa Imran a fuska, gaba daya aka sa dariya shi kuwa ya shafi sumar kansa yana mai lumshe idanu lokaci daya ya bude su akan Murja, wannan karon sai da ta ji miyan bakinta ya sarƙe ta sai ga shi ta soma tari ba ƙakƙautawa. Idris da sauri ya miƙa mata ruwan roba dake gefensa saman kafet. Ta karba ta sha tana satar kallon Fadeel da bai ƙara dubanta ba sai waya da ya ke faman dannawa. A haka da rawar jiki ta zuba kowa ta miƙa mishi. Friedrice ne da hadin coslow sai chicken pepper. Ta bude firij ta ciro musu lemuka ta ajiye. Daga haka ta sa kai ta fita. Tana fita Idris ya gyara zama ya shiga rantse musu akan ya ga matar aure shi dai yana sonta idan za'a ba shi. Fadeel ba ya fahimtar komai ban da ta cikinsa da ya ke yi, ganin duk da fankar da ke busawa yana gumi kawai sai ya mike ya cire rigarsa daga shi sai dogon wandon shadda da vest ya koma ya zauna. Sai da ya tashi da abincin tas kafin ya ɗauki ruwa ya kora ya dubesu. Kowannensu bai kai ga kammala ci ba, suka kwashe masa da dariya, shi kansa murmushi da tsaki ya yi lokaci guda kuma yana sa hankicif ya goge fuska.

"Ku na da matsala wallahi, ba za ku gane illar da yunwa ke min ba. Yanzu sai ta tayarmin da ulcer."

"Ai mun gane komai ranka ya daɗe. Ko za ka ƙara?"

Saifullah ya faɗi da zolaya. Fadeel ya ɗan harareshi.

"Saboda na zama rumbu ko?"

Haka suka yi ta zolayarsa shi kuwa tuni ya maida kai kan wayarsa yana kiran abu na biyu da ya tsaya mishi a ƙoƙon rai amma har ta kammala ringing ba a ɗaga ba. Haka ya kira har sau uku, sai a na huɗun, aka ɗaga. Kafin ya kai ga cewa komai ta soma faɗa.

"Wai Malam kai din maye ne?! Na ce ka bar kirana ka ƙi! Dole ne zuwanka gidan namu? Haba, wannan jaraba da naci har ina wai? Mtsw."

Daga haka kit, aka kashe kiran, nan da nan kansa ya yi wata irin sarawa, dama ga ciwon kan da tun ɗazun yake ji. Gumi ya karyo masa saboda tsananin ɓacin rai, idanunsa tuni suka kaɗa. Sauyawar yanayinsa ya sa Ibb ƙuramasa idanu. Sai dai bai ce komai ba ganin ba su kaɗai ne a falon ba. Sai bayan da gaba daya suka fice don gaisawa da Alhaji sannan Ibb ya dube shi, lokacin ya mayar da kai jikin kujera ya lumshe idanu don har su Imran suka fita sun yi zaton bacci ne ya kwashe shi su na mishi tsiya. Shi kuwa duk yana jin su ba shi dai da karfin biyewa shirmensu.

"Fadeel, wai meke faruwa haka?"

Jin muryar Ibb yasa shi bude idanun, ya mike zaune sosai.

"Yarinyarnan nema take ta kashe ni, daga ranar da na gan ta har zuwa yau ban huta ba."

Cikin rashin fahimta Ibb ya dan wurga hannu.

"Wace yarinya ce haka? A rayuwarka har ta hanaka sakat? Wace ce?" Tsakaninsa da Allah ya yi furucin don shi gaba ɗaya ma ya manta da wata Humaira.

"Wacce muka haɗu da su tare da wannan ɗan iskan yaron."

Shiru Ibb ya yi cikin nazari sannan ya dube shi a hanzarce.

"Are you serious?

5 Comments On DUKAN RUWA
avatar
daiy drop

2 years ago

Reply

hhh

avatar
daiy drop

2 years ago

Reply

sss

avatar
daiy drop

2 years ago

Reply

sss

avatar
daiy drop

2 years ago

Reply

sss

avatar
north

2 years ago

Reply

hhhhh

Please Login or Register in order to submit comment