Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

tsaneshi hakan? Oho, ta ba kanta amsa, sai kuma ta ja tsaki cikin jin zafin rai, to meye nata ma na tsayawa tunaninsa? Don haka sai ta miƙe ta shimfiɗa darduma jin an soma kiraye-kirayen sallah. Koda ta idar sai da ta yi nafila sannan ta yi salati da istigfari. A karshe ta yi addu'a sosai. Sai kuma ta tsinci zuciyarta da yin wani sanyi tamkar an yayemata wata damuwar. Sabuwar wayarta ƙirar Huawei da Abba ya damƙa musu bayan fitowarsu daga hannun ƴan ta'adda ta yi ƙara sauti mai dadi shaidar shigowar saƙo. Ta ɗauka ta duba.

*_Babu wata damuwa ko baƙin ciki da Allah ba zai iya magancewa ɗan adam ita ba. Ki miƙa dukkan lamuranki gareshi, ki kusanceshi, zai kusanceki. Allah yana son masu ambatonsa safe, rana da kuma dare. Ina miki fatan alheri koyaushe._*

Ta karanta fiye da sau uku, ya yi mata dadi sosai, ta kuma kasa barin murmushi. Fadeel ne, koda babu suna a lambar tana da haddarta saboda kira na yau da gobe da yake yi kuma duk da ita ne. Ta sauke ajiyar zuciya, kwankwasa ƙofar da Futuha ta yi da shigowarta da sallama ya sanya ta ajiye wayar ta dube ta. Murmushi Futuha ta yi mata.

"Yauwa Humaira idan kin huta ki fito ki ɗebi abinci a kicin. Daga gobe za ki soma gwadawa Hafsatu yanda kike tsara abinci da komai, yau kinga sai ki huta ko? Ni zan shiga ciki ba lallai kuma mu haɗu ba sai da safe."

Ita dai ta amsa da toh kawai, bayan fitar Futuhar ta girgiza kai. Mamakin wannan rayuwa ta yaran Mami take, tabbas albasa ba ta yi halin ruwa ba, da ace sun biyo Mami hatta da girkin ba su da matsalarsa. Ta rasa menene ribar ɗiya mace idan ta zauna har ta yi aure ba ta iya girki ba. Banda shiriritar Futuha, ta gwammace a koyawa Hafsatu girki ta cigaba da yi mata bauta ita kuwa ta zauna ta miƙe ƙafa. A ƙarshe dai ta watsar da tunane-tunanen da ta tabbatar ba za su yi mata wani amfani ba ta cigaba da ambaton sunayen Allah har aka kira sallar isha'i ta gabatar ta kuma haɗa da nafila ta yi addu'a anan ma sannan ta ninke dardumar ta fita, abincin sam bai yi mata ba. Shinkafa ce dafaduka ta dai ji kaji wadanda daga ka kai saman hancinka sai ƙarni ya bugeka, da sauri ta mayar ta ajiye. Sanin da ta yi idan ta zauna sai ta kwana da yunwa ne ya sanya ta daukar indomie kanana biyu ta dafa ta ci ta sha ruwa.
Saita alarm ta yi ya tashe ta karfe uku, dakyar ta tashi saboda ba ta saba ba ga bacci dake neman fin ƙarfinta, sai da har uku da rabi ta buga sannan ta iya miƙewa firgigit tana ambaton sunan Allah. Hakan ya ba ta wani ƙarfi ta kuwa ɗauro alwala ta dawo ta yi nafiloli ta karanta alƙur'ani bacci na ɗaukarta, dakyar ta daure ta yi sallar asuba sannan ta kwanta anan bacci mai karfi ya kwashe ta.
Sai wuraren takwas na safe ta tashi ta yi wanka ta shirya tsaf ta dora hijabinta ta nufi kicin. Ta sani mutanen gidan ba sa tashi da wuri, maigidan kansa sai ya kai goma bai fita ba. A kicin ta tarar da Hafsatu na zaman jiranta har ta yi gyara ta wanke kwanuka. Suka gaisa fuska a sake, nan suka shiga haɗa kayan kari, kasancewarta babbar mace kuma mai basira tana hankalta kwarai da yanda Humaira ke sarrafa girkinta. Suyar dankali da agada suka yi sai ko sauce da ta haɗa, sai ruwan shayi da ya ji citta da kanumfari. Sai ko farfesun nama da ta yi da ya ji kayan lambu. Kicin din ban da ƙamshi ba abinda ke tashi, komai ta yi daidai gwargwado yanda ta tabbatar ba za'a yi almubazzarancinsa ba. Hafsatu ta fita da shi zuwa dinningtable na Futuha, ita kuwa Humaira bayan ta zuba wa Hafsatu ta ɗebi nata ta yi ɗaki don ba za ta iya jurar har sai su Futuha sun tashi ta karya ba saboda yunwar da ya addabe ta, a ranar kuma ta tashi da wani irin karfin jiki da walwala. Ta ƙara gasƙata cewar Fadeel, babu abin da ibada ba ta ɗaukewa na daga damuwa da ma ƙuncin zuciya. Hamdala kawai ta ke yi bisa yanayin da ta tsinci kanta a ciki.

***
A ɓangaren Fadeel kuwa, sosai suke shirin bikin Ibb da Dakta Salma wanda bai fi sati ya rage a yi ba. Abokansu duk wanda ya ji zancen auren Ibb sai ya tambaya ko an yi na Fadeel? Amsar dai bai wuce nan kusa shima zai yi ba. Kamar koyaushe a kwanakin nan, yau ma su na tare bayan ya raka Ibb wurin Dakta Salma jin tsarin events din da za ta gudanar, Ibb sai faman mita yake yi mishi akan kawai ya kai kudi a sanya aurensu lokaci guda shi kuwa murmushi kawai ya ke yi. Girgiza kai Ibb ya yi.

"Fadeel na sanka, kana da ƙoƙari sosai gun ɓoye damuwa, ba ka fiye son ɗorawa mutane nauyin damuwarka ba, amma ba yanda ka iya, mun taso tare kuma kai ɗin aminina ne dan uwana na maka sanin da wani mafi kusa da kai ɗin bai yi ba. Yanzu a ture zancen wasa, please and please ka yi abin da muke da tabbacin yiwuwarsa, idan yin a yi, idan barin a bari."

Tuƙi yake yi amma sai da ya ɗan juyo ya dube shi.

"Ban fahimceka ba. Me za a bari?"

Ibb ya kauda fuska yana ɗan shan ƙamshi.

"Auren mana, ko dole ne sai ita? Lamarinta ya fara kai ni bango, ita ba ƴar kowa ba a ƙasarnan sai ji da kai da taƙama. Matan da suka fi ta sun nuna su na yi da kai sun kuma nuna sun ji sun gani kowane yanayi ma a tafi da su amma ka nace mata, ka maƙale sai ita. Haba Fadeel, yaushe duk wannan zai wuce? Har yanzu kana da hope din cewa za ta amince da aurenka da bakinta?"

Fadeel bai ce komai ba, amma zuciyarsa zafi take. A duniya bai taɓa yin so ba sai akan Humaira, kuma da son ya tashi kama shi, sai ya yi mishi wani irin kamun dabaibayi wanda ko ya ƙi ko ya so, hakanan zai rayu da shi. Bai dai san abin da gaba za ta haifar ba.

"Ban iya ƙiyayya ba, kamar yanda ban iya soyayya ba ka san da haka ko? Meyasa ka ke tunanin akwai ranar da zan iya haƙura da Humaira alhalin ba ta yimin laifin da zan ƙi ta ba har yau? Ko ka yi zaton ta taɓa wulaƙantani ko zagina? Toh Humaira ba ni ta wulaƙanta ba, soyayyar da na furta ina yi mata ta wulaƙanta, amma na yi mata uzurin kasancewarta daga jinsin Dan Adam wanda muka riga muka san ajizancinsa. Ka yi hakuri, na sani kana jin babu dadi yadda ake maka ƙorafi akan aurena har da masu nemana da sharri. Please ina son ka toshe kunnuwanka daga garesu. Duk radda ni Fadeel na furta maka cewa na bar Humaira, toh ka sani ina nufin rabuwa ta har abada, amma yanzu bana jin ko ɓurɓushin hakan a zuciyata. Ba na jin kuma wannan mafarki naka mai tabbatuwa ne saboda ba ta yimin kamun wasa ba. Ka bi wannan ɗan uwannaka da addu'a Ya Sheikh, komai zai zamo tarihi fa in sha Allahu."

Harara Ibb ya wurga masa jin ya ambace shi da sunan zolaya, Fadeel kuwa murmushi ya yi mishi yana ƙara yi mishi kirari da Angon Salma. Nan kuma ya saki fuska aka bar maganar gaba ɗaya.

***
Cikin hukuncin Allah, a kwana a tashi har tsawon lokacin da su Abba suka ƙara roƙar alfarma a yi bikin Ummita da Sahabi ya kusa cika, a sannan Humaira ta tattara ta bar gidan Futuha adalilin mijin Futuhar da ko kallo suke sai ya dinga kiran Humaira wai ta fito su yi kar ta ƙumshe a ɗaka. Ko kuma ya yi ta santin girki yana fadin ai kaf gidan su Futuha ta fi su iya girki, Futuha tun tana yaƙe har ta zo ta kasa jure ɓacin ranta ganin tashi guda ya siyo wani rantsetsen leshi dan dubu arba'in ya kawo wa Humaira matsayin ladan girki da take yi musu. Anan ne gaba daya ta sauya fuskarta ta ce Humaira ta tattara ta koma gida, ta sa direba ya kai ta bayan ta karɓe leshin. Ba tare da sanin cewa ita Humaira hakan ya fiye mata komai dadi ba don dama ta gaji da zaman gidan, dadinta daya bai wuce na ibadar da take yawan yi yanzu ba sosai, kuma abin mamaki koda Fadeel ya kira ta ta rage jin wannan tsanar da ɓacin ran sai dai ba yabo ba fallasa.

Tashin hankalin daake gudu dai shi ne ya afku, Abba ya zaunar da Sahabi da wani Kawunsa a dakin baƙi ya sanar da su abin da ke faruwa. Sahabi da yake jin wai wai a gari bai yarda ba ji ya yi har wani jiri na neman kwashe shi daga zaune. Kawunsa kuwa ya jinjina lamarin, ya kuma yi addu'ar Allah ya sauki Ummitan lafiya a karshe ya ce idan ta haihu ta yi aure ban da Sahabi don tuni dama sun yi mishi mata ganin ana ta yawo da hankalinsu akan Ummita. Sahabi ya kasa cewa uffan, idanunsa sun kaɗa. Tsakani da Allah yake son Ummita, ya kuma so aurenta, amma bisa gargadi iyayensa ga Kawu, matukar idan sun je ta tabbata ciki ne a jikin Ummita toh lallai su faɗi hakan. Sun kuma yi barazanar saɓawa Sahabi muddin ya musa zancen. Da wannan aka ƙulle mishi baki ya kasa cewa komai. Sai ma da zai tafi ne ya roƙi arziƙin ganin Ummita, nan Abba ya ba shi hakuri gami da nunamasa ba za ta iya jure ganinsa ba. Ya yi hakuri dai ya bi umarnin iyayensa. Daga wannan Sahabi ya ja jikinsa suka bar gidan bayan Abba ya damƙa musu dukkan wani abu da suka kawo da sunan aure.

Ummita na ɗaki ban da kuka babu abin da take yi, Humaira wannan karon ta ma kasa rarrashinta, ga ciki ya fito ras ana gani kasancewar bai fi watanni biyu ya yi mata saura ta haihu ba. Ta shiga watanni bakwai cif. Ita kanta Humairar hawayen take yi tana gogewa. Ta dai tabbata shikenan Sahabi ya rabu da Ummita duk kuwa da irin dogon wayar da suke yi da soyayyar da suke nunawa juna.

"Kaddararki ce Ummita, kiyi hakuri mu rungumeta da hannu bibbiyu. Watarana komai zai zama tarihi."

Ta girgiza kai.

"Humaira na sani ƙaddarata ce, amma wallahi Humaira na tsani cikin jikina da abin da ke cikin. Ba zan taɓa sonsa ba. Humaira duk sadda cikina ya yi motsi ji nake kamar na ɗauki wuƙa na caka a cikin abin da ke cikin ya mutu gaba daya koda ace nima nawa ajalin kenan. Allah ya isa, Humaira ba zan taɓa yafewa azzaluman nan ba. Har gobe mummunan fuskokinsu na nan a kwakwalwata, wallahi yau idan Allah zai nunamin su, sai na raba su da numfashinsu."

Hawaye sosai itama Humaira take yi, balle kuma Raihana wacce shigowarta kenan dakin sanye da Uniform ta dawo daga makaranta ta tsinci labarin fasa auren Sahabi da Ummita kwata kwata a bakin Mami, kuka sosai take yi sanin irin kaunar da suke yiwa juna. Ta karaso ta rungume kafadar Ummita tana kuka tamkar ranta zai fita ta ma kasa magana. Sai Humaira ke aikin rarrashinsu cikin ƙarfin hali duk da itama hawayen ne ke zubomata.

"Humaira! Raihana!! Kuna ina?!"

Jin muryar Mubarak yana kiran sunansu murya a sama ya sanya su duban juna kafin su fito zuwa falon gaba daya ban da Ummita da ko motsi ta kasa. Kirjinta ne kawai ke dukan tara-tara, zai wahala ta yi mafarki bai afku ba, tana tsoron kuma yanzun ace mafarkin nata ne ya tabbata. Sai ta hau ambaton Innalillahi a ƙasan ranta.

Ba Mubarak ne kaɗai a falon ba, har da Mami da Abba wanda bai je kasuwa ba saboda lamarin fasa auren Ummita sosai ya taɓa ransa, dama kuma ya san da zuwan ranar, amma babu yanda iya.

"Kai Mubarak, mene ne haka kake ihu a gida?"

Mubarak da idanunsa suka kaɗa gaba daya ba cikin nutsuwarsa yake ba, daga shi sai singilet da wando three quarter, fuskarsa ta yi jazur abinka da farin mutum. Waya kawai ya miƙawa Abba, Mami da su Humaira har su na rige rigen zuwa leƙa saman wayar. Rubutu ne a ka yi dogo, headline din rubutun mai jan hankali sai ko rubutun.

_*GASKIYA TA YI HALINTA..._*

_*Rahina Sani da Humaira Yusuf wadanda kwanakin baya ake tunanin sace su aka yi, a yanzu gaskiya ta yi halinta._* _*Yan matan sun bi samarinsu ne yawon sharholiya inda a karshe har ɗaya ta zubar da cikin da ta yi yayinda ɗayar kuwa Allah ya tona asirinta cikin ya ƙi zubewa tana nan yanzu haihuwa yau ko gobe. Bincikenmu ya tabbatar da cewa ba sace su aka yi ba, dama ƴan hannu ne suka bi abokan watsewarsu ganin asirinsu zai tonu ne ya yi sanadin da suka haɗa baki suka yi ƙaryar an sace su._* *_Tabbas inda ranka za ka sha kallo da mamaki._*

Sakin wayar Abba ya yi har yana taga-taga zai fadi, da taimakon su Mami dake kusa da shi ya samu ya zauna a kujera mafi kusa saboda rawar jiki. Humaira kuwa zuciyarta ke wani irin tafarfasa ranta idan ya yi dubu ya ɓaci, waye wannan ke kokarin ɓata musu suna a idon duniya? Mene ne ribarsa?

"Wannan wace irin rayuwa ce? Daga wannan sai wannan? Waye da wannan aikin? Kai Mubarak a ina ka samo mummunan labari haka?"

Duka wannan zantukan Abba ke yinsu lokaci guda cikin rawar murya mai nuni da zallar ɓacin rai. Mubarak da ya dauki wayarsa ya amsa.

"Abba ina zaune naga an turo group din da nake har da masu bibiyata ta inbox su na tambayar ko dagaske ne. Da na duba naga an yi forwarding sama da sau hamsin. Wannan ya sa na fahimci koda ace ba a jima da baza labarin ba, toh ya samu karɓuwa ainun."

"Innalillahi wa inna ilaihir raaji'un! A duniya ba ka sanin cewa kana da maƙiya sai irin hakan ta kasance. Ina so maganar nan ta tsaya iya mu da wadanda suka sani a gidan, koda wasa kar a faɗawa yarinyarnan ko don yanayin da take ciki. Mu rufe duk wata ƙofa da za ta tsinci labarin. A karɓe wayarta, ku kuma ku kiyayi tayar da zancen a gabanta. Ni kuma in sha Allahu sai inda ƙarfina ya ƙare wajen ganin an bi maku hakkinku, koda ace abin da na mallaka zai ƙare sai na sanya an bincikomin me wannan aika-aikar an hukuntashi ya kuma faɗi dalilinsa na aikata wannan abu."

Kowa a wurin ya gamsu da batun Abban, Mami kuwa tunani kawai take yi na waye wannan da ya fi ta nuna ƙiyayya ga yaran? Fatanta kar ya kasance wacce take zargi. Ta sani tunda har Abba ya ci akwashin ɗaukar mataki akan al'amarin to fa babu fashi.

Da wannan aka kashe zancen amma fa ran kowa a ɓace, koda su Humaira suka koma ɗaki, sun tarar Ummita ta shiga bandaki wannan ya sanya da sauri ta ɗauke wayarta ta kashe ta jefa a sif, da Ummitan ta fito ma babu wani a cikinsu da ya nuna mata komai. Ita ɗin ma ba ta lura da yanayinsu ba balle ta mayar da hankali, damuwar rashin Sahabi ya rinjayi komai. Tana buƙatar ganin ta samu nutsuwa ko ya ya ne, tana tsoron ciwon da damuwa za ta haifar mata. Wannan dalilin ne ya sanya ta jin tsoron tambayarsu dalilin kiran da Mubarak din ya yi musu, sai ta zaɓi yin shiru gami da kwanciya ta hau jan carbi.

***
Wasa-wasa sai ga zance ya yaɗu a duniya. Abinka da soshal midiya masu jran ƙiris sai ga labari salo-salo ana juyawa har da masu fitowa su na ƙara nasu gishirin su na ƙara yaɗawa. Abin mamaki da tsoron shi ne har asalin su Humaira da Ummita na kasancewarsu yaran riƙo a gidan da suke haka aka dinga yaɗawa ana faɗin watakila musguna musu ake yi ya yi sanadin shigarsu karuwanci yayinda a wani gefen wasu ke cewa mai yiwuwa son duniya ne ya kai su ga faɗawa halin da suka tsinci kansu. Har da kuma wadanda suka ce koda ace ba karuwancin suka fita da zummar yi ba, zai iya yiwuwa sun yi ne domin su samu maƙudan kuɗaɗe amm a ƙarshe abokan ta'addar nasu suka cutar da su ta hanyar yi musu fyaɗe. Labaru dai iri-iri akan bayin Allahn nan biyu Humaira da Ummita babu irin wanda bai yaɗu ba. Mafi rinjaye sun fi aminta da cewar da haɗin bakinsu aka sace su hakan ta kasance. Ƙalilan ne masu tsoron Allah wadanda ba su yarda da wannan labaran ƙanzon kurege da ake ta fafutukar yaɗawa ba.
  Tsintar wannan labari a wurin dangin Ummita da ma Humaira sam bai zo musu ta daɗi ba. Hankali tashe Anti Maijidda ta diro Kano, ko kaɗan ba su da labarin wai Ummita na da ciki, a hakan ma ba ta amince ba sai da ta zo don kanta ta ga Ummita da tulelan ciki, wannan baƙin ciki yasa har suma ta yi ta kuma tiƙe lallai sai dai Abba ya ba ta Ummita su tafi. Mami kuwa tashin hankalinta bai wuce na wayar da Wizzy ya ƙara yi mata bayan bayyanar labarun da ake ta yayatawa ba akan lallai Ummita na haihuwa ta ba shi ɗansa yana so zai kai wa gyatumarsa idan kuwa ta saɓa zai iya tona asirinta. Wannan dalilin ne yasa itama ta kafe akan Ummita ba za ta tafi ba.

Anti Maijidda ta fusata ainun ta dubi Mami da hawaye jage-jage saman fuskarta tana kai nunata da yatsa.

"Ke Maryam! Ni ba sakara ba ce ki dube ni dakyau! Idan idanun kowa ya rufe ba a ganin aibunki ni kuwa Maijidda ko ruwan teku za ki shiga ki wanke jikinki ki fito ba za ki taɓa sauyawa daga yanda nake kallonki ba. Don haka tun wuri ki fita idanuna na runtse, idan kuma ke kika yi naƙudar Ummita a yau sai ki hana ni tafiya da ita mu gani!"

Jin haka sai kawai Mami ta sa kuka sosai, Abba ransa ya ɓaci yayinda Ummita ta kwantar da kai a kafaɗar Humaira tana nata kukan.

"Hajiya Maijidda ina ganin ƙimarki kuma albarkacin Jamila da abin da ta haifa ya sa ban taɓa ɗaga idanu na faɗamaki maganganu ba. Ko ba komai kina ganina da wannan girman, amma fa ba zai yiwu ace koyaushe ki zauna kina kushe Maryama ba. Haba, duk ƙoƙarin da take yi akan Ummita bakya gani? Meyasa kike nema ki yanke zumuncin da ke tsakanina da ɗiyar ɗan uwana? Ke a ganinki idan ace yau Maryama na cutar da ita zan zuba idanu ne nayi shiru? Ni ga sakarai?"

Mami ta ɗan dube shi ta gefen idanu kawai, yayinda Maijidda ta ji zafin maganganunsa.

"Alhaji Yusuf, na ji Maryam ba ta cutar da Ummita, amma yau idan har ni na isa da Ummita matsayin yaya ga mahaifiyarta ina neman alfarma a wurinka ka bar ni na tafi da ita Bichi. Ka ga dai yadda abubuwa suka rincaɓe, sunanmu gaba daya ya gama ɓaci, ba naku ba, ba kuma ga namu ba ƴan uwan mahaifiyarta. Don haka ina  roƙon arziki ka bar ni na wuce da ita."

Ummita ko kusa ba ta gane ɓacin sunan da Antinta ke magana a kai ba, sai ta yi tunanin ko don cikin dake jikinta ne kuma ga shi nan an soma sani a gari. Abba kuwa, ya yi shiru yana nazarin maganganunta, da alama sun yi tasiri a zuciyarsa. Ganin haka da sauri Mami ta dube shi.

"Yau kenan kana ƙoƙari ka nuna ba ni na haifi Ummita ba? Kokari ka ke yi ka sallamawa Maijidda Ummita ta wuce da ita ko? Kana son nunamin ba ni na haifeta ba, ashe Raihana idan ace ita hakan ya faru a kanta ba zamu yi hakurin duk abin da zai je ya zo ba mu bar ta karkashin kulawarmu ba? Lallai ka sani Yusuf, a yau idan ka amince da dauke Ummita daga hannuna toh ka sani cewa ta tafi kenan har abada ba za ta dawo wurina ba. Na kuma gode da nunamin iyakata da ku ka yi."

Tana kai wanan ta juya ta soma tafiya cikin zubar hawaye, wannan ya tashi hankalin Abba da ma su Ummitan.  Abban na kiran sunanta ta yi banza da shi, ita dai Anti Maijidda na tsaye riƙe da hannuwa a kirji tana kallon irin salon makirci na Mami mai ban mamaki. Ummita cikin sauri ta miƙe ta riƙo hannun Mami tana kuka  kamar ranta zai fita lokaci guda tana girgiza kai amma kalma ɗaya ta kasa fita daga bakinta. Mami ta dube ta cikin hawayen sai kuma ta shafi gefen fuskarta ta yi murmushin yaudara. Cikin karyar da murya ta ce.

"Kar ki damu Ummita. Da nan din da can duk ɗaya ne."

Sai a sannan Ummitan ta magantu.

"Aa Mami, kiyi hakuri. Wallahi babu inda zan je, ke din tamkar uwa kike a gareni. Idan har a duniya za iya barin mahaifiyata toh kuwa zan iya rabuwa da ke. Kin rungumeni a sadda na buɗi idanuna babu iyaye, kin maida ni tamkar ɗiyar cikinki, kin kaunace ni ta kowace fuska. Ni kuwa me zai sa na zama mai butulci a gareki? Kiyi hakuri da kalaman Anti Maijidda, ta yi su ne saboda tsantsar tausayi da kuma ganin kamar zan fi samun kwanciyar hankali a can, amma na tabbata ita kanta ta sani kina nunamin kaunar da ba don kar nayi wauta ba, zan ce ta fi na Raihana da su Anti Tasleem."

Anti Maijidda ta kasa cewa komai tayi gum sai kallo, Abba kuwa sai kalaman Ummita suka kashe mishi jiki, shakka babu gaskiya ta fadi kuma ba zai so a yiwa Mami butulcin nan ba. Ya dai so a farko ya amince da batun Anti Maijidda idan har sauya wurin zai dawo da walwala da farin cikin Ummita. Humaira sosai ta ji dadin kalaman da Ummita ta yi ga Mami, ta tabbata hakan ne kawai zai sanyaya zuciyar Mamin, sai kawai ta ji Anti Maijidda ta sire a ranta. Ita a duniya yanzu ba ta da maƙiyi irin mutumin da zai kushe Mami da ƙoƙarinta a kansu, abin da dai ta fahimta shi ne, ba a iyawa DAN ADAM, wannan sai mahaliccinsa. Ba ta san mene ne ribarta na aibata Mami ba.

Murmushi Mami ta yi tana dubanta kafin ta dubi Anti Maijidda da ta yi mutuwar tsaye. Sai a lokacin Anti Maijidda zuciya ta tunzurota ta soma magana tana duban Ummita.

"Yau kin watsamin ƙasa a ido ko Ummita? Ni kika nuna bani da wani matsayi ko ƙarfin iko a wajenki? Wa.."

"Anti please. Ki duba yanayin da take ciki mana ki rabu da zancen nan haka. Ina haɗa ki da Allah ki bar komai har ta rabu da abin da ke jikinta lafiya idan har dagaske farin cikin kike nema mata."

Mubarak ke wannan tun soma zancen ya shigo yana kuma sauraronsu. Ransa ya ɓaci ba kaɗan ba da yanda Anti Maijidda ke kushe masa uwa kuma mahaifiya amma ya fi jin zafin yadda take neman haifarwa da Ummita wai sabon ɓacin ran na daban. Jinjina kai Anti Maijidda ta yi, ta hadiye ɓacin ran nata kamar yanda ya nema. Dagaske ta fi kaunar samun lafiyar Ummita a yanzun da kuma kwanciyar hankalinta wannan yasa ta taka zuwa ga Ummita ta janyota ta rungume. Yadda Ummitan ke kuka hakanan itama take yi.

"Kiyi hakuri ya isa hakanan, shikenan magana ta wuce. Kiyi zamanki anan zamu dinga waya kin ji?"

Ummita ta gyada mata kai, daga haka kuma aka kashe zancen. Abba da Mubarak suka fita don haɗuwa da D.P.O don tsaurara bincike akan wanda ya yi wannan aika-aikar da ma neman alfarma gurin D.P.O akan ya fito gidajen yaɗa labarai ya faɗi abin da ya sani kan satar
DOWNLOAD
DOWNLOAD

5 Comments On DUKAN RUWA
avatar
daiy drop

1 year ago

Reply

hhh

avatar
daiy drop

1 year ago

Reply

sss

avatar
daiy drop

1 year ago

Reply

sss

avatar
daiy drop

1 year ago

Reply

sss

avatar
north

1 year ago

Reply

hhhhh

Please Login or Register in order to submit comment