Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da damuwa amma ban gama gane kan damuwar ba. Ina da abin faɗi, amma zuciyata na kwaɓa ta a koyaushe akan bai kai abin magana ba nayi shiru kawai. Na rasa meke damuna, idan na ce zan zurfafa tunani sai jikina ya hau rawa, kaina ya hau sarawa. Watakila iyakar abin da zan iya faɗa kenan. Nidai ki dinga sanya ni a addu'a."

Ummita ta ɗan rungumeta suna kuka. Kowannensu da kalar tunaninsa, dakyar suka rarrashi junansu suka share hawayen.

Sai kuma Humaira ta cigaba da karfafa mata gwuiwa akan ta bari Sahabi ya fito a yi magana. Ta kara da fadin.

"Kinga itama Raihana zan ce ta amince ta bar Imran ya turo. Shikenan sai ku bar min gida na huta."

Ummita ta harareta, ita kuma ta yi dariya tana kokarin danne radadin ciwon kan da take ji gudun kar ta kefa Ummita a wata sabuwar damuwar. Koda Ummita ta fita don amsa kiran Mami wacce ta turo Muhsin, sai ta zame ta kwanta ta runtse idanu tana tauna maganganun da suka yi da Ummitar, hannuwanta riƙe da kan da ke faman sara mata. Tana nan kwance har bacci ya sure ta, Raihana ta zo ta tashe ta akan ta je Mami na kira. Ta ci sa'a zuwa lokacin ya rage ciwon, don haka dankwalinta da ya zame ta maida ya rufe kan ta fita. Anan fa Mamin ta mata umarnin ta shirya za ta bi Futuha don ta taimaka mata da girki abokan mijinta za su je gidan nan zuwa jibi. Kamar ta cewa Mamin a bari mana sai jibin ta je ta dawo, amma ba ta son jan musu da ita kawai sai ta ce toh. Ranta na zafi haka ta shirya ta bi Futuha suka tafi. Tana ji Futuhar na yiwa Tasleem waya wai gatanan a hanyar gidanta, ita dai ba ta ce mata uffan ba sai kallon window da take yi zuciyarta na zafi, wani sashi na zuciyar na kokarin ce mata Mami ba ta kyauta mata ba yayinda wani gefen ke kwaɓarta yana nusar da ita irin kirki da mutuncin Mamin. Bai kyautu ta munana mata zato ba. Da haka suka karasa gidan Tasleem.

***
A yau Murja ta yi niyyar zuwa sashin Fadeel don ta rantse ko ta yaya sai ya saurareta ya ba ta damar amayar da abin da ke ranta ido da ido. Kwanakinnan ko bacci kwakkwara ba ta iya yi tsabar so da tunaninsa da ke neman zautar da ita, wannan ya sa ta zuri takalmanta kawai ganin an yi Magrib tana kuma da tabbacin yana nan ta nufi sashinsa.

Yana zaune ya kafe manyan frames guda biyu da aka yi mishi na hoton Humaira da idanu yana kallo. Ta yi kyau matuka, daya tana tsaye ne a farfajiyar Manal Event Centre ranar bikin su Futuha, dayan kuwa wanda ta dauka da sallah ne ba ta san ma an yi hoton ba ta rike kafaɗar Ummita tana dariya mai bayyana wushiryarta. Ta yi kyau ainun, masifar son da yake yiwa hotunan ne ya sanya aka wanko da zummar zai adana duk radda suka yi aure ya kafe su a ɗakin baccinsa. Uzurin bandaki ya kama shi, ya mike ya shige ƙuryar dakin don kama ruwa. Daidai lokacin Murja ta hau kwankwasa ƙofar dakin, tana ji kamar ta tura kanta ciki ko ba izninsa. A yau ta kai maƙura a so da kauna da begen ganinsa.

*LITTAFIN NAN NA KUƊI NE. SIYA AKAN NAIRA ₦400 KI KARANTA BA TARE DA SHIGA HAKKI BA.*


*5407827015*
*FCMB*
*Farida Abdullahi*

09034973645



A can kuwa, Wizzy yana kammala magana da Abba ya fidda layin a wayarsa ya kakkarya ya zubar, lokaci guda kuma ya mayar da layinsa. Suka dubi juna suka kwashe da muguwar dariya. Humaira da Ummita aka titsa ƙeyarsu zuwa cikin ɗakin. Babu laifi wajen da suka sauya ya fi wancan kyau, komai tsaf sai ƙura kuma ga dukkan alamu sabon gida ne da ba a kammala aikinsa ba. Banɗakin akwai ruwa har da butar alwala. Wajen dai ya fiye musu ɗayan amma kuma hankulansu ba a kwance suke ba. Ai babu wani gata da za a yi musu alhalin su na hannun azzalumai abin ya yi musu daɗi su samu kwanciyar hankali. Daga Ummita har Humaira tun sadda aka garƙame su a ɗakin ba sa aikin komai sai kuka hakan na da nasaba da jin muryar Abba da suka yi wanda gaba ɗaya sun fitar da ran ƙara ji ko ganin wani cikin fuskokin da suka sani.

Wizzy kuwa bayan dawowar Badboy daga rufe ƙofar ya dube su ya ce.

"Aski fa idan ya zo gaban goshi ya fi zafi, wannan lokaci ne da zamu ƙara zage damtse kuma mu yi takatsantsan don cik umarninta, a ƙarshe mu ma mu kwashi rabonmu, ta sallame mu."

Babba wanda ke faman hura hanci yana fitar da huci ya soma magana a kausashe.

"Wai ni fa bana son rainin hankalin da take yi mana! Matar nan tun da ta bamu aiki ba ta yarda ayi waya da uta sai rubutun saƙo. Ita ba ta san hatsarin da ke tattare da hakan ba? Idan fa ta yi sakaci har wani ya yi ya gani to fa akwai matsala. Sannan ta ƙi ta bayyana kanta sai ɗan aiken da ta ke turowa, ita kenan ko kama mu za a yi ta tsira kenan? Ba mu san wace ce ba, kuma ba mu san komai a kai ba, namu kawai aiwatarwa idan an cafke mu ta ci bulus kenan?!"

Wizzy ya ɗaure fuska bai ce komai ba, ganin haka Badboy ya cafe.

"Kai Babba ka iya kalamanka, ka sani koda wasa idan har ba mu ne muka so ba, toh fa ba za mu taɓa kamuwa ba. Mun fi ta iya shege ai kai ka sani. Ni fa duk ba wannan ne damuwata ba, yarannan su na hargitsa lissafina amma kai Oga ka ƙi bani damar gwangwajewa. Kenan haka muna ji muna kallo za mu bar su shikenan sun sha?"

Sai a sannan Wizzy ya kalle shi.

"Ba wannan aka umarcemu  da yi ba, asalima don horo ne ya sanya muka kai su tsohon gidan gonar can don kawai su shiha taitayinsu amma tun farko ba ya daga cikin bajat dinmu. Kai ne ka fiye garaje, ai na ce maka akwai lokacin da hakan za ta kasance, mu bari mana har mu samu tabbacin kuɗaɗen nan za su faɗo hannunmu tukunna mana, sai mu yi duk abin da muka ga zamu iya. Mu dai tabbatar ba mu kashe su ba don ba shi aka sanya mu ba."

Suka yi shiru babu wanda ya tanka masa musamman Badboy da ke jin haƙurinsa na dab da ƙarewa akan ƴanmatan musamman Humaira da surarta ke fisgarta.

***
  Hankalin Anti Maijidda (babbar yayar mahaifiyar Ummita ta Bichi) a tashe ta shigo babban falon na Mami da jama'a ke zaune ana jajanta wannan lamari na su Humaira. Ba ta ƙasar gaba daya ta je Umarah sai a jiya ta diro Kanon, ko gida ba ta je ba kai tsaye ta ce a sauke ta a gidan. Tana shiga ta zube jikin ƙanwar Abba, Baba Amina  da suka saba tun a baya tana kuka sosai ana ba ta haƙuri. A lokacin ne kuma Mami ta shigo daga ɓangaren Abba cikin dogon hijabinta, ta gama jin yadda aka yi da Abba da kidnappers din akan kuɗin fansa. Jin muryarta su na gaisawa da makwaftan da ba su jima da leƙowa gidan ba ya sa Anti Maijidda miƙewa kamar wacce aka tsiƙara ta hau tafi raf raf har sau uku, wannan ya ja hankulan kowa kanta yayinda wasu suka shiga tunanin kodai ɓatan Ummita ya girgiza kwakwalwarta har haka? Mami kuwa cak ta tsaya kawai tana mai zubamata idanu. Maijidda kenan, macen da ba su taɓa raɓar juna da alheri ba, babu wata jituwa da ta ƙara haɗa su tun bayan rasuwar Fatima mahaifiyar Humaira.

Maijidda ta soma magana murya a ɗage kuma a kausashe.

"Ki zuba ruwa a ƙasa ki sha Maryam! Ki tara jama'arki ku yi kiɗa ku yi rawa har da juyi! Yau burinki ya cika! Abin da kika jima kina ƙullawa akan yarannan yau kin cika shi!"

Jin haka Baba Amina ta miƙe a firgice cikin kaɗuwa ta fisgo hannun Maijidda.

"Maijidda ki shiga hankalinki mana! Ki yarda da ƙaddara ki yi imani da ita. Wannan wane irin zantukan banza ki ke yi akan baiwar Allahn da ta riƙi amanar ɗiyar ƴar uwarki da amana da kulawa tsawon shekarunnan koda wasa Ummita ba ta taɓa kokawa da ita ba? Wane irin baƙin ƙazafi kike shirin yiwa baiwar Allahn nan?!"

Anti Maijidda ta fashe da kuka sosai tana nuna Mami da yatsa.

"Har abada ni Maijidda ba zan taɓa kaunarta ba, kuma ba na jin zan yarda da ita koda ace gaba ɗaya mutanen duniyar nan za su taru su yi mata kyakkyawar shaida! Baƙar azzaluma ce! Amina ni nasan wacece Maryam, ni zan ba da labarinta! Don haka idan har bincike ake son yi na gaske daga cikin gida, a soma daga kanta da kuma azzalumar uwarta!"

Wannan ƙazamin furucin ya sa Mami ta fusata sosai.  Hannunta na rawa kamar yadda dukkan gaɓɓan jikinta suke yi ta nuna ta da yatsa, daƙyar maganarta ke fita saboda zuciyar da ta taso mata da kuma ruwan hawayen da suka wanke mata fuska lokaci guda.

"Na shanye dukkan baƙaƙen maganganunki na tsawon shekarunnan ba don komai ba sai domin albarkacin ƴar uwarki marigayiya Maimuna da muka yi zaman mutunci da ita! Na kuma cigaba da jure duk wani cin kashinki a dalilin Ummita jinin Maimuna ce da Naziru. Ban da haka ba ki da wata ƙima ko daraja a idanuna!"

Baba Amina da mutanen ɗakin dakyar suka tsawatar aka kashe zancen inda Mami ta fice daga falon cikin ƙunar rai zuwa ɗakinta inda Anna ke zaune kuma tsaf ta ji dukkan abin da ya faru. Allah ya taƙaita lamarin Jannat ba ta gidan, ta fita dubiyar wata ƙawarta da aka yiwa aiki a asibiti, da abin zai fi haka ɓaci.

Anna ta dube ta sai kuma ta yi dariya.

"Maryama kenan, wannan shi ne sakamakon bautar da ki ka yi na riƙon Ummita ko? Wannan ranar nake jira dama, ban kuma zaci zan gani nan kusa ba. Shashashar yarinya! Ga shi nan tun ba a je ko'ina ba kin kwashi kashinki a hannu. Da ace tun a farko kin ji maganata hakan da bai faru ba. Yanzu sai kiyi kuka da kanki akan duk abin da ya faru."

Mami ba ta ce da Anna komai ba, sai ta fidda hijabin da ta zumɓula ta ɗauki wayarta kawai ta zauna ta yi shiru tana aikin dannawa, Anna ta cigaba da zabga ruwan bala'i, da Mami ta ga abin ba na ƙare ba ne, kawai sai ta fice zuwa ɗakin su Raihana ta bar mata ɗakin.

***
Fadeel ya farka gami da ƙurawa silin idanu, shiru ya yi yana ƙoƙarin tunano dalilin kwanciyarsa ciwo, a hankali kuma ya juya kansa ya dubi ɗakin. Ibb ne kaɗai a zaune yana danna waya bai ma lura da farkawarsa ba. Ya lumshe idanunsa lokaci guda komai ya dawo kwanyar kansa, a firgice ya miƙe zaune.

"Ya Salam!" Ya faɗi da ƙarfi yana mai fisge drip din da aka sa mishi. Furucinsa ya sa Ibb mikewa da sauri ya nufo shi gami da riƙe kafaɗunsa.

"Fadeel yi a hankali mana."

Jin haka ya dube shi da rashin kwarin jiki.

"No Ibb, kwana nawa nayi a nan? Humaira na hannun kidnappers, za su kashemin ita. Ka bar ni na je nemanta."

Daidai nan Alhaji da Daddy suka shigo. Fadeel ya miƙe jiri na kwasarsa yayinda Ibb ke ɗan riƙe shi, Daddy da sauri ya tarbe shi ganin kamar zai faɗi ya ce.

"Fadeel kwantar da hankalinka, in sha Allahu za'a ga Humaira."

Kawai sai ya ji hawaye sun zubomasa, wato za ma a gan ta ba wai an ganta ba? Ya girgiza kai yana kallon Daddy amma sai ya kasa magana.

Suka taimaka suka mayar da shi mazauninsa. Daddy a nutse ya karanta masa duk yadda suka yi da Abba ya kuma ƙara da faɗin.

"Yanzu haka ba mu jima da waya da shi ba, ya tabbatar mana da cewar sun samu kira daga mutanen, sun kuma buƙaci kuɗi. Wannan damuwar ba zai magance maka kowacce matsalar ba, addu'a da kuma sadaka ita zamu duƙufa yi. Yanzu idan ka ce za ka fita nemanta, ta ina za ka fara? Ka san a inda suke ne? Daji, cikin gari, kasuwa, ƙauye, kai ko ma ba a garin suke ba gaba ɗaya wannan sanin Allah ne kaɗai don haka ka samarwa kanka ƙarfin zuciya ka dage da kai wa Allah kukanka. Babu abin da ba ya magancewa."

Daddy ya cigaba da kwantar masa da hankali har da cewa koda ace kudaden da Abban za su haɗa ba za su kai ba, shi ya ji ya gani zai san yadda za'a yi a cika a bayar don su kuɓuta, balle kuma shi Fadeel din wanda yake jin zai iya sadaukar da dukkan abin da ya mallaka a doron ƙasa don kuɓutar rabin jikinsa daga hannun azzaluman nan. Sosai ya ji dadin zantukan Daddy, da wannan ya lallaɓa ya yi wanka, brush, da alwala, Ibb ya ba shi kaya ya sauya. Daga nan ya hau ramuwar sallolin dake kansa.

Bai kai ga idarwa ba sai ga Anti Amarya tare da Murja sai ko Fu'ad da ya kawo su, hannun Murja riƙe da kwandon abinci. Ta gaida su Abban sannan ta karasa ta ajiye gefen gadon. Gefe ta koma tana satar kallon Fadeel ɗin da a kwana ɗaya kawai ya zabge. Zuciyarta na wata iriyar tafarfasa.
  'Ka yi ka gama Fadeel, na rantse maka koda ace Humaira ta fito ni Murja sai na kashe ta da hannuna. Ballantana ma ba za ka ƙara ganinta ba.'

Ta yi maganar a zuci, su Alhaji suka tafi saboda yamma ta kawo kai yayinda Ibb suka fita don yi musu rakiya. Fadeel na idarwa ya dubi Anti Amarya ya gaishe ta, ta amsa tana mishi sannu. Ido ta ɗan yiwa Murja hakan ya sa ta saurin gaida Fadeel, ya amsa ba tare da ya kalleta ba.

  Nan suka zauna har sai da Fadeel ya ɗan sha ruwan shayi dakyar amma sam ya ƙi yarda da cin abinci, tunaninsa ko a wane yanayin Humaira take? Watakila ma ko abincin ita ba a ba su sun ci ba. Wannan ya daƙilar da shi daga ci.

***
  Sahabi saurayin Ummita kullum sai ya zo gidan ya gaida Abba da Mami, gaba daya ya komaɗe ya rame tsabar tunanin Ummita. Iyaye da ƴan uwansa babu wanda bai shigo jajantawa ba. Hakanan ƴan makarantar islamiyyar su sun zo sun kuma yi saukar Alkur'ani akan Allah ya bayyana su. Hatta da yan makarantar su Ummita na boko sun zo har da malaman makarantar an jajanta. Aka yi addu'a suka tafi.

  Labarin dai yana ta yaɗuwa don har waɗanda su Abban ba su ma sani ba sun zo sun taya su jaje, da yawansu a social media suka ci karo da shi. Mubarak dake Ghana yana jarrabawar ƙarshe hankalinsa gaba daya yana Kanon, ba don Abba ya ce kar ya zo ba ya zauna har ya kammala da tuni ya dawo. Hakanan su Yassar ba su zo ba. Amma sosai abin ya taɓa su duk da ƙiyayyar da suke yi musu. 
   
   Ɓangaren Futuha kuwa ƴar Dubai, kasancewarta mai mu'amala sosai da yanar gizo sai ga abin nema kuma ya samu. Bidiyo sosai ta yi tana kuka ga hotunan Ummita da Humaira daga ƙasa ta ɗora a shafinta tana addu'ar Allah ya bayyana su a ƙarshe ma har da sanya muryar shahararren Malamin nan wato Sudais yana addu'a. Koda ta ɗora hankalinta kwance ta shiga duba yadda ba a ɗauki dogon lokaci ba bidiyon ya yaɗu, nan fa jama'arta suka fara jajanta mata su na tambayar dama Humaira mai shafin Deelsha's Delicacies yar uwarta ce? Da yawa ma wadanda ba su san Humairar ba ko shafinta sai lokacin suka dinga followinh dinta, lokaci guda shafinta ya yi jama'a fiye da dubu talatin. Hakanan shafin Ummita ma ya yi jama'a.

Raihana tana kallon duk abin da ke wakana amma ba ta magana, karshe ma sai ta kashe wayarta gaba daya ta ajiye.  Tun da Abba ya shaida musu da kuɗaɗen da aka ce a bayar na fansar Humaira da Ummita ta ke jin ƴar nutsuwa, ko ba komai kenan su na lafiya kuma Abban ma ya tabbatar musu ya ji muryoyinsu amma bai ce musu ga a yanayin da ya ji ba gudun tayar musu da hankula.

***
  Fadeel da Ibb suka shirya tsaf a washegari zuwa gidan su Humaira kamar yanda Fadeel din ya nema. Hankalinsa ya kasa kwanciya da zamansa a asibiti alhalin ba a ga Humaira ba, kuma bai je ga iyayenta ba. Wannan ne ya sanya su Alhaji goyamishi baya don haka ana ba shi takardar sallama ya kama hanyar gidan.

Sun samu tarba na mutunci daga Abba, Tasleem tun ganin da ta yiwa Fadeel matsayin saurayin Humaira ya zo jajantawa ta ji hankalinta ya yi mummunan tashi. Kishin nan daɗaɗɗe na Humaira ya taso ya soma  cin zuciyarta. Har gobe akwai son Fadeel a ƙirjinta, ta kuma tabbata da ace shi ta aura da yanzu wani labarin ake ba wannan ba.

Kusan lokaci guda suka shigo gidan da Fadeel anan ta gan shi, shi kuwa bangaren Abba suka nufa inda Ƙasim da ya yi musu iso ya raka su ciki. Fauziyya ce ta yi mata rakiya gidan, tana kuma lura da sauyin da ya zo mata lokaci guda sadda Ƙasim ya dawo yana shaida mata ai manemin auren Humaira ne. Ta yi shiru ba ta ce mata komai ba tana ƙara nazarinta.
  A falon ta bar Fauziyya ta faɗa ɓangaren Anna tana huci. Nan ta tarar da ita zaune da Jannat wacce ke zaune tana taunar gasasshiyar kazar da ta siyo suna hira da Anna kai ka ce babu wani tashin hankalin da ake yi a gidan. Ganin yanayinta ya sanya su dubanta.

  "Toh mai ciki, yau kuma wa ya taɓo ki?"

Ta zauna idanunta suka cicciko da kwalla yayinda zuciyarta ke faman tafarfasa. Kwafa ta yi kana ta amsa.

"Wai Fadeel na gani ya zo jajantawa Abba fa? Har yanzu dama yana tare da Humaira? Shi ne don munafunci Humaira ta ci amanar Mami ta ɓoye zancen?"

Murmushi Jannat ta yi.

"Ke ban da abinki ina Humairar take a yanzu? Kina tunanin shirin na wasa ne za ta dawo, ai daga can inda take sai wata duniyar kuma ba wannan da muke ciki ba. Duk fa wanda ya samu dama ya dama.  Kuma da kike wannan maganar ba yanzu gashinan kin auri Hamza ba? Ba kya sonsa kika bari ciki ya shige ki?"

Tasleem ranta ya ɗan yi sanyi jin yadda Anti Jannat ke fadin kaddarar Humaira kai ka ce ita ta rubuta hakan. Batun cikinta ya ƙara jefata damuwa, dama ba da son ranta ta samu ba kuma Hamza ya rantse sai ya yi mugun saɓa mata idan ta zubar.

"Wallahi Anti idan har zan samu na auri Fadeel zan iya kashe ko nawa ne a yimin aiki a kan Hamza ya sake ni. Anti wai kin taɓa ganin Fadeel kuwa da irin yadda ya haɗu? Wallahi ba zan iya zuba idanu wata ta kwacemin shi ba."

Anna tsohuwar banza ta kwashe da dariya madadin ta yi kwaɓa akan wannan haramcin da ake aikatawa sai ma ta ce.

"Kina da Jannat Firdausi ai babu ke babu fargaba. Yadda aka yi wancan haka wannan ma zai kasance labari."

Suka yi dariya. Can kuma Jannat ta ɗan jinjina kai.

"Ko wane ne wanda ya aikata wannan kidnapping din ya yi matuƙar burgeni, da ace ina da damar ganinsa sai na mishi babbar kyauta. Sai hakan ya zo mana da nasara kuma akan gaɓa, Boka ya tabbatarmin da cewa Humaira a can za ta haɗu da ajalinta. Itama Ummita babu tunanin za ta rayu balle har su samu damar kuɓuta su dawo. Kawai dai zan so dawowar ita Ummita, yarinyar ta iya bauta."

Tasleem ta yi murmushi.

"Nima dai Ummita ba ta yimin komai ba, ba ni da wani ƙulli da ita kamar Humaira. Wallahi Anti na tsane ta na kuma tsani duk wani mai sonta."

"Har da ni kenan!"

Suka juya don ganin mai furucin a razane.

®️Rufaida Umar

*LITTAFIN NAN NA KUƊI NE. SIYA AKAN NAIRA ₦400 KI KARANTA BA TARE DA SHIGA HAKKI BA.*


*5407827015*
*FCMB*
*Farida Abdullahi*

09034973645


*TALLAH!* *TALLAH!!*


*Ina ma'abota ƙamshi, su yi ƙamshi suna birge kansu suna birge wanda ya shaƙa*

*Ku danna wa.me/2347010137848 ku ce ta yi saving lambar ku watarana zaku ga garabasan ƙamshin da ba za ku iya Bari ba*








Tasleem ce ta soma  kauda kanta gami da jan guntun tsaki ciki-ciki ba tare da ta ce uffan ba.

Raihana wacce ta gama jin dukkan munanan maganganunsu  ta tako tsakiyar dakin sosai ta cigaba da magana.

"Har da ni kenan! Wannan ba Ummita ko Humaira kaɗai ku ka tsana ba Anna, har mu jinin Abba. Na yi mamaki dama da Anti ba ki ɗau mataki akan abin da Humaira ta yi maki a kwanakin baya ba, ashe dama ke tarkon da kika ɗana babba ne? Ashe wannan damar kike jira? Kai duniya! Mutum ya ƙi mutum har ta kai yana mishi fatan mutuwa? Me suka tare maku? Ku ji tsoron ranar da haƙƙin su Humaira zai kama ku!"

"Me kika ji ance da za ki rufe mutane da faɗa tamkar kina magana da Muhsin ko Waleed?"

Jannat ta furta a ƙoƙarinta na shanye firgicin da ta ɗan shiga, toh koda ace ba su da hannu a satar Humaira da Ummita, ai wannan ɓarin zancen da suke yi zai iya jawomusu matsala tunda ana kan bincike ko yau ɗin da safe sai da D.P.O ya zo wurin Abba.

Raihana ta yi murmushin takaici.

"Kar ku yi tsammanin ban ji mugun ƙullin da ku ke yiwa bayin Allahn nan ba. Amma ku sani, Allah na tare da bayinSa a duk inda suke kuma cikin kowane hali. Na rantse muku, duk iya yinku, duk iya ƙoƙarinku, ba za ku iya kawo sanadin koda karta a fatarsu ba balle a kai ga rasa rayukansu ba face sai da iznin Allahn da ya halicce su. Ku yi dukkan kokarinku, akwai ranar ƙin dillaci."

Tana kaiwa nan ba ta ko ƙara kallonsu ba balle ta ji me zasu ce ta sa kai ta fice daga dakin a guje zuwa nasu ɗakin wanda suka mallaka da su Humaira a baya. Haka kawai sai ta buɗe sif din kayan Humairar da Ummita ta fiddo abin da ta san sun fi so cikin kayansu ta yi ta kuka. Lamarin da ya sanya Mami hana ta kwanan ɗakin sai dai nata ɗakin. Ba za ta iya misalta baƙin cikin da ta ke ciki ba sanadiyyar ɓatan ƴan uwannata. A gefe guda ga baƙin cikin kasancewar Jannat yar uwa ga Maminta ballantana a kai kan Tasleem da take ji kamar ta shaƙe ta. Sai ko Anna da har ba ta kaunar ganin fuskarta a kwanakin nan tun da ta nuna ba ta wani bakin ciki da ɓatan yan uwanta.

***
Abba ya yiwa su Fadeel tarba na mutunci da dattako, gaba ɗaya idan ka ga Abba sai ya mugun ba ka tausayi sakamakon yadda ya koɗe ga kuma rama.
 
"Ka yi hakuri Fadeel, in sha Allah ƙiris ya rage na kammala haɗa kuɗaɗen fansar su, lafiya kalau za su dawo hannunmu. Kai dai ka ci gaba da addu'a."

Fadeel ya ƙara yin ƙasa da kai, Abban da ya ke da burin ya wayi gari ya gan shi a gabansa da zummar neman auren Humaira, su yi hira da dariya tsakaninsu sai gashinan ganin da suka yiwa juna na farko ba mai daɗi ba ne ko kaɗan.  Zuciyarsa ta yi rauni nan da nan kuma ya ji idanunsa sun kawo ruwa daƙyar ya iya daurewa ya amsa.

"Toh Abba, Allah ya kuɓutar da su."

Abban ya amsa da amin, yana son ya ce idan da yadda zai tallafa, a ba shi dama amma ba ya so Abban ya ga kamar ya mishi katsalandan wannan ne dalilin da ya sa shi jan bakinsa ya yi shiru. Sun ɗan jima anan har Abban ke faɗamusu cewa Kawun Humaira suna hanya daga Maine, Ƙasar Nijar. Suka yi musu fatan isowa lafiya a karshe dai Ibb ya soma yiwa Abban sallama kan zasu wuce ganin Fadeel

5 Comments On DUKAN RUWA
avatar
daiy drop

2 years ago

Reply

hhh

avatar
daiy drop

2 years ago

Reply

sss

avatar
daiy drop

2 years ago

Reply

sss

avatar
daiy drop

2 years ago

Reply

sss

avatar
north

2 years ago

Reply

hhhhh

Please Login or Register in order to submit comment