Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

soma magana.

"Lamarin ita Ummita na buƙatar rarrashi da ja a jiki. Kaso casa'in na ire-irenta da hakan ke afkuwa a kansu sukan samu matsala ta rudani, firgici da kuma rashin yarda ga kowa. Wasu kuma yakan taɓa musu kwakwalwa. Zamu yi mata gwajin kwakwalwa don a tabbatar da komai na ta lafiya kalau yake."

Abba ya share fuskarsa.

"Toh Likita, nidai babban burina lafiyarsu. Allah ya sa komai lafiya."

"Ameen." Ya amsa cikin tausayawa yana mai lallaɓar Abba.

***
Cikin iko na Ubangiji an yiwa Ummita gwajin kwakwalwa kuma an tabbatar da komai lafiya. Wannan ya kwantar da hankulansu. Humaira dai ba ta dogon magana tun farkawarta, kowa ta gani sai dai ta ambaci sunansa, idan an rungumeta an sa kuka itama ta soma. Da daddare ba bacci sai razana, ga Ummita haka. Wannan yasa aka raba musu ɗaki. Fadeel na zuwa, kuma abin mamaki Humaira na ganinsa ta kira sunansa, abin sosai ya ji dadinsa ya kuma tsaya a ransa.

Sai da suka kwashe sati biyu a asibiti kafin su tattara su dawo gida. Babu laifi sosai zuwa lokacin sun samu nutsuwa ba kamar farko ba. Sai dai daga Ummitan har Humaira duk sadda tunanin cin zarafin da aka yi musu da kuma keta haddin da aka yiwa Ummitan sai su yi ta kuka. Har zuwa lokacin babu wanda ya san da mummunan labarin sai ko Anti Maijidda da Mami wadanda Abban ya faɗawa.

Anti Maijidda nan fa ta dage akan lallai sai a ba ta Ummita su tafi Bichi, Abba ya ƙi amincewa. A dole ta haƙura ta tafi tana ƙunar rai da jin tsanar Mami har cikin ƙoƙon ranta.

Jannat ko a fuska sai ka rantse nan jimamin duniya take yi akan lamarin don ba ta nuna komai wanda zai sa wanda bai sani ba ya fahimci takun saƙarta da su. Hakanan Anna wacce ta daurewa zuciyarta ta taka har ɗakinsu ta duba lafiyarsu bayan ta je asibitin a baya har sau uku. Wannan ya wanke ta daga zargin mutane da rashin nuna kauna ga su Humaira a baya.

***

*LITTAFIN NAN NA KUƊI NE. SIYA AKAN NAIRA ₦400 KI KARANTA BA TARE DA SHIGA HAKKI BA.*


*5407827015*
*FCMB*
*Farida Abdullahi*

09034973645



Sai da su Humaira suka samu sati hudu cif kafin su ɗan maido da jikinsu, da kuma walwala kaɗan. Sukan zauna cikin jama'a, a taɓa hira da su idan ka cire Ummita da har lokacin ta tuno aika-aikar da aka yi mata sai kawai ta fashe da kuka wanda hakan ke tayarwa Humaira hankali itama ta sa nata kukan sai su haɗu su yi ta yi. Kawun Humaira ya so su koma can Nijar da ita amma nan ma Abba ya nuna sam bai amince ba dole haka ya tattara matarsa suka koma gida.

  Su na zaune a ɗaki, Ummita riƙe da Alƙur'ani tana karantawa zuciyarta na yin sanyi yayinda Humaira ke kwance saman katifa ta yi shiru gami da zubamata idanu kusan ma hankalinta ba a kanta yake ba, ta lula wata duniya ta daban na tunani. Raihana ta shigo ta iske su haka, dawowarta kenan daga makarantar boko wanda har lokacin Ummita ta ƙi amincewa ta koma ganin haka babu wanda ya takura mata shi ma mai makarantarsu da ya zo har gida ya jajanta ya ce a kyale ta zuwa wani lokacin.

"Wash! Wallahi na gaji! Ke kuma kina da baƙo a falon Abba."

Ta faɗi da murmushi tana duban Humaira duk a ƙokarinta na son ta ga komai ya dawo daidai a mu'amalarsu. Humaira ta ɗan dube ta gami da ɗan haɗe gira kaɗan.

"Wa kenan?"

"Fadeel."

Ta yi shiru, ita ba ta ce uffan ba balle ta yi wani yunƙurin kawai sai ta maida kai ta kwanta ta yi shiru. A karan kanta ba za ta ce ga abin da take ji game da Fadeel din ba, lamarin dai ba yabo balle kuma fallasa. Ummita na ji ba ta iya cewa komai ba, Raihanar ma ba ta sake magana ba sai ta miƙe ta rage kayan jikinta ta shiga wanka, ba ta son duk abin da zai takurawa rayuwar ƴan uwannata da ta ƙara sanin girman ƙauna da shaƙuwar da ke tsakaninta da su bayan sun yi mata nisan da ta zaci har abada ba za ta ƙara sanya su cikin kwayar idanunta ba.
  Ummita tana kai wa ƙarshen surar da take karantawa ta juya ta dubi Humaira.

   "Ki je ku gaisa mana."

Humaira ta yi mamakin jin wannan furucin naga bakin Ummita, tun bayan dawowarsu ba ta wani magana kwakkwara, ko hirar Raihana ke jansu da shi, sai dai ta basar ta yi shiru. Wannan murmushin da ba ya barin fuskar Ummita, babu shi babu labarinsa tun dawowarsu. Ita ɗinma ƙarfin hali take yi don faranta ran Mami da su Raihana ga kuma Ƙasim waɗanda gaba ɗaya suke nuna musu kulawa da ƙoƙarin ganin sun saki jikinsu.

"Kin ji?"

Maganar Ummitan ya ƙara katse mata  tunani. Tana so ta ja musu amma a yanzun duk duniya babu abin da ta ke so irin ta ga ƴar uwarta ta dawo tamkar yadda ta ke rayuwa a baya. Abu na  biyu kuma ta sani ba ta jin za ta iya ɗaukar waya ta kira shi da zummar godiya bisa hidimar da ya yi akan fitowarsu, don ko cikon da suka bayar na kuɓutar da su a hannun ƴan fansa ƙin karɓa suka yi da Abban ya maida musu, ta sani wannan ita ce damar ta amma hakanan ba ta son Fadeel din ya cigaba da shigemata shiyasa.

Abban har gidansu ya je ya ƙara godiya sosai shi da Mami wacce a sannan ne ta ga gidan da ya kere na Aminiyarta Hajiya Lubna.

Ganin Ummitan ta zubamata idanu ya sanya ta miƙewa.

"Toh, na ji Ummita."

Ta faɗi kamar ta fashe da kuka sai ta miƙe ta ɗora hijabi akan doguwar rigar atamfar da ke jikinta.

Suka ci karo da Mami a falon wannan ya sanya ta tsayawa.
Gidan yanzu duk an watse sai su kadai, Jannat ta tattara ta koma bayan dogon kiran da mijin ya dinga danno mata har abin ya kusan zame musu rikici sannan ta tafi ba don ta so ba. Tasleem kuwa tun fitowarsu da kwana biyu Hamza ya zo suka koma gida.
 
  Cikin sakin fuska Mami ta dubi Humaira.

"Ina zuwa haka?"

Ta sunkuyar da kai sannan ta ce.

"Wai Fadeel ne ya zo za mu gaisa."

Nan da nan fara'ar dake saman fuskar Mamin ya ragu.

"Zuwan me yake ta yi haka ne alhalin jinyar ta ƙare? Ina ce na muku iyaka da shi tun a baya?"

Humaira ta jinjina kai.

"Hakane Mami, kiyi hakuri. Ai gaisawa kawai zamu yi. Ya yi abin da ko maƙiyina ne ya cancanci na ƙara yi mishi godiya."

Mami ba ƙaramin mamakin furucin Humairar ta yi ba wanda daidai da fuskarta ta nuna. Sai kuma ta jinjina kai.

"Shikenan, ki je amma kar ki ɗau lokaci."

Murmushi kaɗan Humaira ta yi sannan ta amsa da toh ta cigaba da tafiya. Ban da abin Mami, ita ba ta tunanin ma za ta yi auren, wane namijin ne zai aure ta bayan ta gama wulaƙanta duk masu kaunarta domin Allahn? Ta rasa dalilin da a ƴan kwanakin nan take jin sauyi a jiki da kuma kwakwalwarta. Wannan ne ya sa Fadeel samun rangwame daga wurinta.

Ɓangaren Mami kuwa ji ta yi kirjinta ya yi wani irin bugu. Meke shirin faruwa haka? A duniya ba ta kaunar Fadeel ya raɓi Humaira kamar yanda bai raɓi Tasleem ba. Kai ba ma shi ba... Sai kuma tunaninta ya katse, ta haɗiyi miyau da ta ji yana mata zafi. Sai kawai ta nufi ɗakinta a gaggauce. Tabbas ta yi sake a kwanakin da suka shuɗe ba ta bayar an ɗoramata sabon aiki ba.  Wayarta ta fiddo ta shiga zarya a tsakar ɗakin tana jira a ɗauka daga ɗaya ɓangaren. Doguwar magana suka yi sai kuma ta hau murmushi hankali a kwance ta katse kiran ta shiga danna wayar karo na biyu inda ta tura kuɗi ga wani akawun lamba. Daga nan kuma ta ji wata irin nutsuwa ya saukar mata.

***
  Ya kwashi mintoci  masu yawa a zaune anan, shigowar su Waleed ne ma ya ɗauki hankalinsa suke hirar makaranta yana biyemusu. Ya gama fidda rai daga ganinta, gefe guda ga tsoron kada a koma ƴar gidan jiya, tunanin da ya sanya gumi tsastsafo masa a goshi duk kuwa da iskar dake kaɗawa a falon har tana kaɗa labule. Sai dai kuma ba zato ya tsinci sallamarta, cikin sauri ya kalli hanyar yana mai amsawa da rawar murya.
  
'Please Fadeel, Control.' Zuciyarsa ta ba shi shawara, ya sauke nannauyan ajiyar zuciya. Ya zubamata idanu, ta  fara dawowa ainahin Humairarsa, fuskar ta ɗan ciko ba kamar farkon dawowarsu ba. Hakanan ta yi haske fayau dama can a bayan har da rashin samun wanka ga uban cizon sauron da tabonsa ya yi ja a jiki da fuskarta.

  Ita kuwa kanta a ƙasa ta ƙarasa ta zauna ɗan nesa da shi, tana ji ya kaɗa su Waleed ciki akan su je su cire uniform dinsu.

"Barka da rana."

Ya yi furucin yana dubanta tamkar ya haɗiye ta. Sai a sannn ta ɗan ɗaga kai ta dube shi. Ganin yanda ya zubamata idanunsa ya sanya ta maida kanta ƙasa ta na jin wani yaam a jikin da ba ta saba ba a baya.

"Ina wuni, ya wajen su Baba?"

Fadeel da ke jin kamar an tsoma shi a aljanna ya faɗaɗa murmushin fuskarsa yana hamdala a ƙasan ransa. Dama komai ɗan hakuri ne, idan ka yi to fa zai wuce. Ya shanye wulakancin da zagin, yanzu ga shi nan ya soma cin galaba.

"Kowa lafiya kalau Alhamdulillah, Sisterna ma ta zo daga Adamawa. In sha Allah zuwa gobe za ta zo ku gaisa."

Sai ba ta watsa masa ƙasa a ido ba ta amsa da toh. Shiru ya biyo baya, a ɓangaren Fadeel ba ya so ya faɗi abin da bai yi daidai da ra'ayinta ba ta sauya fuska ta miƙe ta bar shi anan, ita kuwa godiya take son yi mishi don su yi sallama ta koma ciki amma ta rasa ma ta inda za ta fara sai can da ta ga ba shi da niyyar ce mata uffan sai aikin kallon da ba za ta ce yana ba ta haushi ko kuma faranta mata ba a lokacin, ta daure ta soma magana.

"Mun gode bisa dukkan ɗawainiyar da ku ka yi mana, Allah ya ƙara arziki."

"Ban yi abin da za ki godemin ba. Ke kika yi wanda zan godemaki. Nagode sosai and I..."

Sai kuma ya yi saurin haɗiye zancensa, ya san komai na tarihin Humaira a sannan daga bakin Raihana, ya san ba ta jin turanci amma kuma dai kalmar I Love You ko yaro ƙarami da bai je makaranta ba ya sani. Shirun da ya yi ganin zai yi taɓargaza ne, gaba ɗaya ji yake da ace Humaira za ta ba shi dama, zancen aurensu kawai za a yi. Ya sani hatta da Abbanta ya buƙaci a ba shi lokaci kaɗan yaransa su dawo cikin nutsuwa sai a haɗa auren Ummita da na su, shi ne a karon kansa ya roƙi alfarma a kyale Humaira ta amince da batun aurensa da kanta. Yana kuma ji a jikinsa hakan ce za ta kasance daga yanayin sauyin da ya gani tattare da ita.

"Shikenan?"

Ta katse mishi tunani, ya ɗan lumshe idanu sannan ya buɗe su a cikin nata, ta kauda fuska ta yi shiru.

"Toh, zan koma bakin aiki, dama zuwa nayi na duba lafiyarku. Ki gaishemin da Ummita da mutan gidan. Allah ya ƙara lafiya."

Ta amsa da amin, cikin sanyin muryar ta ce.

"Zan fadamusu. Nima ka gaidamin ƴar uwarmu, sai ta zo goben in sha Allahu."

Ambaton ƙanwarsa Hannatu da ƴar uwarmu da ta yi ya sanya shi jin tamkar yana tafiya a iska tsabar mamaki da farin ciki. Ya ji dadin wannan lamarin sosai.

"Nagode."

Hakan ya furta kawai sannan suka miƙe kusan lokaci guda, sai da ya ga shigewarta sannan shima ya juya yana murmushin da har haƙoransa suka bayyana, ga duk wanda ya ga fuskarsa ya san yana cikin farin ciki da annashuwa.

***
Washegari Mami ta tashi da aikin girki na tarbar Futuha wacce ta yi waya ta sanarmata dawowarsu a ranar. Daga Dubai sai da suka je Saudia suka yi Umarah kafin su juyo. Humaira ba ta yi ƙasa a gwuiwa ba wajen shiga kicin ɗin din taimaka mata da aiki, zaman kaɗaicin babu abin da yake jefa ta ciki sai kogin tunani. Ummita ma ta fito falo kasancewar akwai wuta ta kunna tashar Saudia tana kallo.
Gaba ɗaya samarin gidan sun dawo, Mubarak da ya kammala shima yana gida hakanan Yassar da Dawud wadanda sun fi sati da dawowa daga Camp suna nan tare da su. Anan Kano aka yi posting ɗinsu inda zasu yi service.
Daga Humairar har Ummita ba su ƙara samun matsala da su Yassar ba, musamman Humaira wacce a baya suke ƙi sosai, ita hakan ma har mamaki yake ba ta. Tsakaninsu gaisuwar mutunci, wasu lokutan har su ɗan tsoma ta a ciki idan suna ƴar hira. Har a lokacin ba ta saki jikinta da su ba don ba ta saba da hakan ba.

Suna girkin Ladidi na taya ta murnar yanda ta soma sakin jikinta tamkar a baya. Raihana ta shigo kicin din kamar an jefo ta har Mami na mata faɗa.

"Ku yi hakuri. Humaira, Yaya Fadeel ya kira Sister dinsa Hannatu tana hanyar zuwa."

Gaba ɗaya ta manta da wani batun zuwansu, Mami kuwa haɗe rai ta yi ba ta ce uffan ba har sai da Raihana ta ƙara magana.

"Ki je ki ɗan sauya kaya don Allah. Kar ta ganki da Tshirt."

Ladidi ta yi dariya Humaira kuwa ta maka mata harara ta rasa dalilin kuma da aka yi ta ɗan dawo da jin haushi-haushin Fadeel, sai lokacin kuma Mami ta yi magana.

"Toh uwarta, ke kuma Humaira meyasa ba ki faɗamin kina da baƙuwa yau ba?"

Cikin sanyin murya da kuma rashin jin dadin ɓatawa Mamin rai da ta yi ta ce.

"Kiyi hakuri Mami, gaba daya na manta ma ya faɗamin."

Mami ta sauke ajiyar zuciya, ta sauya yanayinta na farko sannan a sanyaye ta ce.

"Ai shikenan, ba don girkin da ake na Futuha ba da sai dai ta zo ba a yi nata tanadin komai ba kenan. Ladidi ƙaro shinkafar nan kafin ki wanke."

Ladidi dake shirin wanke ɗanyar shinkafa ta zuba a ruwa ta amsa da toh, sai da ta ƙara ruwan tukunyar sannan ta ƙara awon shinkafar da ajiye. Raihana dai ta tsaya jiran Humaira ta dage lallai sai ta sauya shigar jikinta. Mami ba ta sa musu baki ko kadan ba, Humaira har haushin Raihanar ta dinga ji saboda irin wannan nacin ba ta ko fuskantar yanayin fuskar Mamin.

"Ki rabu da ni don Allah." Faɗin Humaira cikin haɗe gira. Sai lokacin Mami ta sa baki ta hanyar bin Humaira da murmushi.

"Aa Humaira, da gaskiyarta. Maza je ki sauya suturar jikinki. Bai kyautu baƙuwarki ta ganki a hakan ba. Jeki."

Ganin yanayin Mamin har a sannan ba ta gamsu ba, amma ta bi umarninta suka fice da Raihana zuwa nasu ɗakin. Ta iske Raihanar ta fiddo mata wata atamfarta purple mai ratsin fara da baƙi, ta kalle ta. Raihana ta murmusa.

"Ya aka yi? Da magana ne? Ko na sauyamaki kayan?"

Guntun tsaki Humaira ta ja.

"Ke dai yadda kika damu da wannan Fadeel din da ma ke kika aure shi."

Raihana ta ji ba dadi jikinta kuma ya yi sanyi, tana tunanin Humaira ta fara sauyawa daga lamarin nata da na Fadeel sai ta ga abin ba haka ba.

"Allah ya huci zuciyarki tawan." Ta fadi tana riƙo hannun Humaira, sai itama ta ji ba dadi.

"Shikenan. Bari na watsa ruwa na sauya ko don ke."

Sosai Raihana ta ji dadin kalamanta. Ta yi dariya.

"Toh."

Daga haka ta fice ta bar Humairar da shiga bandaki.

***
Murja tana zaune gaban motar ta hakimce yayinda Hannatu da yarinyarta mai shekaru uku da ta ci suna Husna suke a baya zaune.
Tun da Murjar ta ji inda Hannatun ta nufa ta kafe akan sai ta bi ta, a farko Hannatu ba ta so ba don tana da labarin irin son da Murjar ke yiwa Fadeel daga bakin Kausar. Shi Fadeel dayake bai ɗauki maganar da muhimmanci ba ya sa bai ce mata komai a kai ba. A karshe dai ganin yadda Anti Amarya ta nuna ta yi na'am Murja ta raka su ya sa itama ɓoye nata rashin yardar suka tafi tare ba da sanin Fadeel ba.
Karfe biyar na yamma suka shiga gidan. Raihana ta tare su da fara'arta zuwa ciki. Murja sai raba idanu ta ke ta ga inda Humaira za ta ɓullo kuma ta ga yanda ta sauya. Ummita itama ta fito suka gaisa da su, nan suka jajanta musu da addu'ar Allah ya kiyaye gaba. Ba ta amsa ba sai ta mike sakamakon idanunta da suka cicciko da kwalla ta nufi daki.

A duniyarta yanzu babu abin da ta tsani ta tuna kamar abin da ta faru gareta a hannun Kidnappers. Gani take duk ranar da aka ɗaura mata aure da Sahabi babu abin da zai hana shi gano komai, Abba ya yi niyyar sanar da shi amma Mami ta nuna kar ya yi hakan. Ita kuma a karan kanta ta rasa ta ina za ta fara gayamishi. Ga wata sabuwar kauna da yake nunamata tun bayan fitowarsu duk domin ya kwantar mata da hankali.
Ganin da ta yi Humaira na ɗakin, ta yi saurin share fuskarta ta dubeta fuskar a ɗan sake duk da ba kamar can baya da take Ummitarta ba.

"Sun ƙaraso su na falo. Ki je ku gaisa, mace mai kirki da ita."

Taɓe baki Humaira ta yi.

"Toh." Shi ne abin da ta iya cewa, daga haka ta sa kai ta fice. Bayan fitarta Ummita ta tura kai a filo ta yi kuka mai isarta tana mai tausayawa kanta. Wannan baƙin ciki na keta alfarmarta da aka yi ta kasa gogeshi daga kirjinta, ta dai san an gogamata baƙin fentin da har abada ba za ta iya gogewa ba. Amsar da ta kasa ba wa kanta har yau shi ne, wane ne wanda ya sa a yi kidnapping dinsu.

*_Ba don kar asirinmu da na Boss ɗinmu ya tonu ba, da sai na nemi aurenki na killaceki saboda kin haɗu ƙarshe._*

Ta tuna wannan ƙazamin zancen da ya fito daga bakin Wizzy a sadda yake kam ganiyar raba ta da mutuncinta. Kenan dai akwai wanda ya sanya su wannan aika-aikar. Waye shi? Kuma a ina yake? Allah ne kaɗai masani. A karshe dai ta yakice wannan tunanin ta mike ta shiga bandaki.

***
Hannatu ta dubi Humaira har ta ƙaraso ta zauna tana mata ɗan murmushi. Murja kuwa kallon Humaira kawai take yi cikin tafarfasar zuciya tana mai kuma cin alwashin ganin bayanta. Babu wani abu da ya sauya daga kyawunta wannan ne ya ƙara wa Murja baƙinciki a ƙasan rai. Ta kauda fuska tana amsa gaisuwar da Humaira ke yi mata a yatsine. Ita kuwa Humaira mamaki take na dama Murjar ta san Fadeel amma sai ta bar wa cikinta ba ta tambaya ba. Hannatu ta saki jikinta ta yi ta jan Humaira da hira, kasancewar da Raihana a falon ta samu ƴar tayi, tun dai Humaira ba ta saki jiki ba har sai gatanan ta soma murmusawa haƙoranta na bayyana.

Raihana ta kawomusu abin motsa baki da kuma abinci. Husna ta maƙalewa Humaira tana mata hira iri iri na yara. Itama ta dinga biyemata. Can dai Murja ta kasa jurewa ko Mami ba ta tsaya sun gaisa ba ta amsa wayar ƙarya sannan ta dubi Hannatu.

"Ni zan wuce sai kun taho. Ƙawata ce ta zo."

Suka dube ta har Raihana da ta fahimci sauyin fuskar Murjar da irin harare-hararen da take wurgawa Humaira jifa-jifa.

"Shikenan, sai mun taho."

Ranta ya ƙara ɓaci, wato dama so take ta tafi ɗin don haka ta dauki jakarta ko sallama ba ta tsaya yi da su ba ta fice a fusace.

Ba jimawa kuwa da fitarta Mami ta fito cikin shirin fita. Daga ganin yanayinta sauri take kuma fuskarta ya nuna rashin nutsuwa. Hannatu ta gaida ta, ta amsa da ɗan sauri. Ganin haka Raihana da Humaira suka tarbi Mamin da neman ba'asi. Guntun tsaki ta ja fuskarta dauke da tsantsar damuwa.

"Wajen Tasleem zan je, sun yi dambe da wannan Fauziyar shi ne fa jini ya ɓalle mata amma sun wuce asibiti."

Hankalinsu su din ma ya tashi. Suka nuna za su bi ta amma fir ta ce aa su zauna da baƙuwarsu sannan ga Futuha dake hanyar zuwa kada a bar gidan babu ƴan tarbarta. Dole suka jajanta suka dawo ga Hannatu aka cigaba da hira. Ba ita ta bar gidan ba sai bayan Magriba. Ta kuwa ajiyewa Humaira leda babba ta kayan kwalam sai ko turarukan da ta yo mata tsarabarsu. Firr Humaira ta ƙi karɓa sai daƙyar sannan ta yi godiya. Lokacin itama Ummita ta fito falon, tare suka yi mata rakiya har gaban motar da suka zo cikinta.

***
Karfe takwas da mintoci sai ga Futuha a gidan, tun yamma ta sauka a garin tana gidanta, Ƙasim ne ya kai musu girke-girken da aka yi musu. Ta shigo gidan gaba ɗaya jikinta a mugun sanyaye. Matasan samarin duka suna falo aka tarbe ta da murna, su Humaira su din ma duka ana zaune ana kallon film din Krissh da ake haskawa a mbcbollywood. Ganin yanayin yadda take amsa musu hirar ya sanya Yassar dibanta dakyau.

"Are you okay?" Ta yi murmushin yaƙe kai ka ce ba Futuhar nan ba ce mai ɗora hotuna iri-iri da murnar zuwa Dubai a tiktok.

"Yes. Mamin ba ta dawo ba?"

"Ta dawo tana ɗaki."

Faɗin Raihana. Ta kuwa nufi ɗakin, ban da gaisuwar su Humaira babu wani jimamin da ta yi musu na abin da ya faru. Ƙamshin turarenta da ya cika falon ne ya sanya Ummita jin kanta na juyawa, ta ji tamkar hanjin cikinta ke kaɗawa. Da sauri ta mike ta yi dakinsu, kafin ta ƙarasa shigewa banɗakin wani amai ya tahomata wanda sai da ta amayar da duk abincin da ta ci a ranar. Humaira da Raihana wadanda suka biyo bayanta ganin irin miƙewar da ta yi ta bar falon suka tsaya cak cike da fargaba mai tsanani su ke bin ta da kallo.

*LITTAFIN NAN NA KUƊI NE. SIYA AKAN NAIRA ₦400 KI KARANTA BA TARE DA SHIGA HAKKI BA.*


*5407827015*
*FCMB*
*Farida Abdullahi*

09034973645


Raihana ta karasa cikin sauri bayan fitowar Ummita daga banɗakin ta riƙe ta.

   "Lafiya? Meke damunki?"

Ummita ta yamutsa fuska kaɗan.

"Ban sani ba, kawai dai na ji zuciyata tana tashi."

"Allah ya sauwaƙe, ki ɗan kwanta ko za ki ji dadin jikin." Fadin Humaira cikin dauriya da ƙaryata zuciyarta har da jan istigfari bisa saƙe-saƙen da ta jefa mata. Ummita kuwa ɗan murmushi ta yi.

"Kar ku damu, kalau nake. Naga duk kun yi wani sukuku da ku."

Cikin kokarin basarwa Raihana ta zauna gami da jan guntun tsaki.

"Ai dole, ga Tasleem can kwance asibiti dakyar aka tsaida jinin. Wai kawai saboda ta kama Fauziyya na waya da tsohuwar budurwar Yaya Hamza kuma ƴar uwarta tana ba ta labarin rayuwar ita Tasleem din da Yaya Hamza shikenan fa daga cacar baki sai cibi ya zama ƙari. Nima Mami naji tana ba Anna labari. Yanzu dai Maman Hamza ta ƙi zuwa ko duba Tasleem ta ce wai kashe mata ɗiya ta so yi."

Humaira ba ta ce uffan ba, domin tun dawowarsu ta ƙara jin Tasleem ta fice a ranta, ta kuma ƙudurta ban da dai gaisuwa ta musulunci to fa babu abin da zai sa ta cigaba da tura kai ba kwarjini wurin waɗanda ba za su taɓa kaunarsu ba. Ko kaɗan Tasleem ba ta wani nuna farin cikin dawowarsu ba, ita kuwa me zai sa ta cigaba da shiga sabgar wacce ba ta yin ta?

"Allah Sarki, Allah ya kawomata da sauki."
Cewar Ummita sannan itama ta ja bakinta ta yi shiru.

***
Yanayin da Futuha ta shigar wa Mami ne ya sanya ta ɗago kai daga wayar da take amsawa har da hawayenta. Cikin wani sauri ta sallame wayar

5 Comments On DUKAN RUWA
avatar
daiy drop

2 years ago

Reply

hhh

avatar
daiy drop

2 years ago

Reply

sss

avatar
daiy drop

2 years ago

Reply

sss

avatar
daiy drop

2 years ago

Reply

sss

avatar
north

2 years ago

Reply

hhhhh

Please Login or Register in order to submit comment