Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

uwan mahaifinsa kowa ya fito zuwa falon. Murna kam ba a magana. Yayyunsa mata waɗanda kaf dinsu su na da aure sai guda ɗaya bazawara da aurenta ya mutu take zaune a gidan da yaranta, su din ma kowaccensu ta halarci falon. Kallonsu kawai yake yi yadda kowacce ke haba-haba da shi, murmushi kawai ya ke yi don ba shi da tabbacin ko abin nasu ya kai zuci ko aa. Sanin da ya yi musu daban a baya, ba shi da masaniya akan yanzu.

***
  Raihana ce zaune a can lungun gadon Tasleem ta maƙure a gefe tana zuba kuka ga waya saman kunnenta. Musaddam take ta ba hakuri adalilin ya ƙi ya huce tun sadda Humaira ta gasa mishi zafafan maganganu. Ya kuma ci alwashin ko don ya nuna wa Humaira ba ta isa ta tsaida shi daga abin da ya yi niyya ba, sai ya kusanci Raihana ko ta ƙarfi kuma ya yi hotuna don ya shayar da ita mamaki. Yana sane da gangan ya ƙi ya huce saboda kawai ya ƙara fahimtar irin matowar da Raihanan ta yi a kansa.

Sati ɗaya kenan da dawowar Yayannasu amma ko kaɗan walwalwarta ba ta dawo daidai ba ga wani irin tsanar Humairar da take ji a ƙoƙon rai amma shakkar kada ta tona mata asiri da ma tsoron ita kanta Humairar ya hana ta labartawa koda Tasleem ce balle Futuha. Sai ƙawarta da ta ba labarin, ita kuwa ƙara hure mata kunne ta yi akan kar ta yarda wata can bare ta raba ta da abin sonta. Da wannan huɗubar da kuma mahaukacin son da take yiwa Musaddam idanunta suka rufe ruf. A wannan yanayin walwalarta ba ta dawo ba sai da ta tabbatar ya haƙura bisa alƙawarin za ta zo gidan su Munirat su gaisa.

Humaira ta shigo ɗakin daidai sadda Raihanan ke fadin. "Shikenan zan zo goben idan har ganina zai samar maka da nutsuwa."

Wannan kalmar ta daki zuciyarta, sai dai ta dake ba ta ko kalle ta ba ta ƙarasa ciki, dama mayafin abayarta za ta ɗauka zasu je Shoprite ita da Ummita, Mami ta aike su.

Raihana kuwa ganin Humaira ya sa ta shan jinin jikinta. Ta kasa magana kwakkwara sai um da humm ina jinka. Guntun tsaki Humairar ta ja ta fice, ta sha alwashin ko ina ne a goben sai ta bi bayanta ta kuma kama ɗan iskan dumu-dumu ta ci uwashi.

  A falon ta haɗu da Ummita, har suka soma tafiya ta ga dai hira suke amma ita ke kiɗa da rawarta hakan yasa ta dube ta.

"Wai ke lafiyarki kin wani haɗe rai kamar wacce aka aikowa saƙon mutuwa? Koda dai ɓata bakina nake dama ai halinki ne. Amma naga ai yanzun ba kiciɓus kika yi da maƙiyinki naki ba ko?"
Tana nufin saurayi, Humaira ta ja tsaki ta girgiza kai.

"Ba komai fa."

Taɓe baki Ummita ta yi ba ta ƙara magana ba sanin hali. Sai kuma can don kanta ta saki fuska suka hau hira. Kayan maƙulashe irin su Jam, Ketchup, Mayonnaise da sauransu, shi Mami ta bada su siyo na Yaya Mubarak. Sun kammala suna dab da ficewa suka tsinkayi sallama a gefensu. Lokaci guda suka juya ga mai shi, wani matashin saurayi ne gajere mai ƙiba. Irin ƙibar da ba ta da muni. Daga yanayin yadda ya saki fuska za ka fahimci mutum ne mai fara'a. Humaira wacce kallo ɗaya ta mishi ta dauke kai gami da ci gaba da tafiya, ganin haka itama Ummita ta mara mata baya, ya kuma bin bayansu da sauri ya sha gaban Humaira.

"Ranki ya dade, kiyi hakuri na tsayar da ke. Nima kuma na san darajarki da ƙima ta zarce a tsayar da ke a hanya a..."

"Kai Malam saurara don Allah! Ni nan da ka ke gani da mijina a hannu don haka kama kanka. Muje."

Ta fisgi hannun Ummita ta bi gefe suka fice a nan. Hakan da ta yi ba karamin ɓatawa Ummita rai ya yi ba, ba yau farau ba, idan da sabo ya ci ace ta saba da ganin irin cin kashin da yar uwarta ke yiwa samari. Ita har mamaki take yadda gaba daya Humairar ke sauyawa kamar ba ta taɓa zama haɗa hanya  da wani abu wai shi mutunci ba. Ta fara gasƙata zancen Raihana da ta ce jinnu ne da ita. Kamar kuma ba ita ba, sai ga shi a hanya ta saki rai sun ci gaba da hirarsu lafiya lau.

***
  Washegari tun safe take dakon Raihana tana jira ta ga sadda za ta fita ta mara mata baya. Aikuwa wuraren karfe biyu tana zaune a falon da littafi a hannunta na koyon rubutun hausa tana ɗan duba inda muhsin ya biyamata, Mami kuwa na gefe tana yankewa Muhsin farce sai ga Raihanar,  ta tambayi Mamin zuwa gidan ƙawarta Munirat. Farko Mamin ta hana sai can kuma da ta dage da naci ta samu Mamin ta aminta. Humaira ba ta ko ɗaga kai ba balle ta yi yunkurin miƙewa, har sai da Mami ta soma barin falon, tana nan zaune ba ta ko motsa ba har Raihana ta fito cikin shigar fita, ta ci wani arnen kwalliya ta sanya riga da siket da ya yi matuƙar kama ta sai ta dora afterdress a sama wanda da shi da babu duk ɗaya. Tana fita Humaira ta yi wuf ta miƙe ta zari hijabinta dake hannun kujera. Tuni ta yi shirinta dama ta sa kuɗi a bayan gidan wayarta. Bayan Raihana ta bi, sai da ta kai ƙarshen layin ta nemi can jikin wata  bishiya ta ɓoye fuskarta cikin facemask. Haka ta shiga ɗan sahu ta bi bayanta har gidan su Munirat. Kamar yanda ta zata kuwa hakan ne, wani saurayi matashi ne tsaye jikin wata mota suna hira da wata budurwa. Raihana na karasawa ta cafke da budurwar da bayan ta matso ta gane Munirat ce saboda ta taɓa zuwa can gidannasu ba sau ɗaya ba ba biyu ba.
    Can kuma sai Munirat ta shige gida ita kuwa  saurayin ya buɗe mata gidan gaba ta shiga ya maida ƙofa ya rufe. Baƙar mercedez ce mai baƙin tinted wanda duk iyaka hangen mutum bai isa ya ga na ciki ba.

Humaira ta ji ƙirjinta na dukan tara-tara da wani irin sauri ta soma takawa ta nufi wajen kai ka ce kafin ta karasa abin da take tsoron afkuwarsa ya afku.

Da tsayuwarsu a wajen, da shigar budurwar motar, duka ya faru ne akan idanun Ibb da Fadeel wadanda ke tsaye a ƙofar gidan su Fadeel ɗin su na taɓa hira. Ya rako Ibb ne zai wuce gida suka tsaya. Ganin shigar budurwar ya sa Ibb jan tsaki.

"Wallahi ina mamakin rayuwar ƴan matan yanzu da ba su da kunya kuma ba su san mutuncin kansu ba. Yau da ƙanwata ce daga ita har shi sai sun raina kansu."

Ya faɗi ransa na wani irin ƙuna, Fadeel kuwa da zuciya ta kai mai wuya bai san sadda ya soma takawa ba da sassarfa hakan da ya yi ya sa Ibb bin bayansa da sauri ya dakatar da shi sanin hali.

"Aa Fadeel, please don't, ba ka san waye ba a.."

"Sai nasan waye? Idan ƙanwartaka ce za ka zuba ido kana kallo rayuwarta ta ɓaci!"

Yana kai wa nan ya fisge hannunsa, sai dai kafin ya kai ga tafiya suka hangi Humaira wacce gadan gadan ta nufo motar a fusace.

  
 


 

09

Zuciyar Humaira har wani tafarfasa ta ke yi, tana isa ta sa hannu ta ja murfin motar cikin sa'a kuwa ƙofar ta buɗe. Raihana wacce yatsunta ke sarƙe da na Musaddam gaba ɗaya ta kasa sukuni amma ƙarfin soyayyarsa a ruhinta ya sa ta daurewa ranta, daidai sadda ya kai bakinsa ne da nufin sumbatar hannun aka wangale ƙofar hakan ya sa a firgice gaba ɗaya suka juya. Humaira ta fisgo Raihana, ba shiri ta fito har tana tuntsirawa. Ba ta yi wata wata ba ta ɗauke ta da mari hagu da dama ga wasu zafafan hawaye da suka zubo saman fuskarta lokaci guda. Musaddam tuni ya fito ya zagayo wurinta, hannu ya ɗaga shi ga marar kunya zai ramawa Raihana marin, amma tuni Humaira ta riƙe hannunsa ta ba shi nasa rabon. Hannunta har rawa yake ta sa hannu ta fisge facemask din da ke rufe a hanci da bakinta.

Fadeel ya yi mata ƙuri da idanu babu ko kyaftawa yana jin tamkar gangar jikinsa ne kawai tsaye a wurin, hannu ya sarƙe a kirji yana so ya ga matakin da za ta ɗauka. Humaira da ba ta san wainar da ake toyawa ba, gaba ɗaya ba ta tattare da nutsuwa hankalinta kacokam a tashe yake, yana kan Musaddam da take jin kamar ta shaƙe shi. Ɗan firit da shi sai sirantaka, fari ne yayinda lebbansa suke baƙake wuluk shaidar yana shan sigari. Hannunsa dafe da ƙunci yake duban Humaira rai ɓace ya ce.

"Ke! Ni kika mara?"

Bai yi aune ba ta kara wanke shi da mari.

"Yanzun ka daina tantama? Eh marinka nayi! Da kuma ace ni wata mai ikon ce, abin da ya fi mari shi zan maka. Ɗan iska marar tarbiyya! Ka yi amfani da son da ka ga yarinya na maka za ka cutar da ita saboda a gidanku ba a baka isassan tarbiyyar islama ba sai na bokon da bai amfaneka da komai ba. Idan har ba ka raba kanka da kanwata ba ina maka rantsuwa da Allah sai na yi maganinka ta yadda rayuwarka za ta ƙare a kurkuku. Ke kuma..."

Ta juya gaba ɗaya ga Raihana wacce ke kuka ga dukkan ilahirin jikinta na rawa. Ba ta jin an taɓa tozarta ta irin yau, a gaban saurayin da take yiwa son duniya? Lallai Humaira ba ta da kirki ko kaɗan. Aljanun nata ma ƴan iska ne na ƙarshe da alama.

"Kin ɗauka ba shi jikinki shi ne zai sa ya ga mutuncinki ya gane irin son da kike mishi har ta aureki? Toh kin yi kuskure, wallahi wallahi duk sadda kila bari wannan ɗan akuyan ya kusanceki kin cuci rayuwarki har abada Raihana, za kuma ki yi kukan nadamar da babu mai share maki hawaye. A haka kuke kirana da ƴar kauye, wannan ita ce wayewar? Toh wannan birnin naku na jahilai ku ke ciki, idan za ki farka tun wuri ki farka idan kuwa ba haka ba wallahi muddin irin haka ta ƙara faruwa a kunnen Abba. Wuce kuma mu tafi tun ban kakkaryaki ba."

Raihana ta dubi Musaddam da ya haɗe girar sama da ta kasa yana kallonta, ta maida duba ga Humaira wacce ke cika da batsewa kiris take jira ta fashe ga hawaye kace-kace a fuskarta. Ta lura ma jikin Humairar har rawa yake.

"Muddin kika bi umarninta ki sani daga yau babu ni babu ke Raihana, alaƙarmu ya zo karshe. Sannan ke kuma ba ki san waye ubana a ƙasar nan ba ko? Zan nunamaki daga kaina ba za ki ƙara gangancin marin wani namijin ba."

"Musaddam ɗan gidan Alhaji Jafar Nababa, right?"

Gaba daya har Humaira suka juya a inda suka tsinci muryar, Raihana ta yi mutuwar tsaye ganin Ibb Gusau mutumin da yar uwarta Futuha ke mahaukacin so tare da wani haɗaɗɗen guy wanda ko fuskarsa da take a haɗe ka kalla, sai ya burgeka. Kunyar da ta ji ne ya sa ta saurin amfani da gefen mayafinta ta rufe baki da hancinta gudun kar su gane ta. Humaira kuwa kallo ɗaya ta musu ta maida duba ga Musaddam ɗin fuskarta har lokacin a mugun ɗaure tana jiran ta ji amsar da zai ba da.

Musaddam ya kai duba ga me maganar, nan da nan ya ji gumi ya karyo masa, Malaminsa ne a jami'a da ya taɓa yiwa gadara da matsayin Ubansa, shi kuwa ya nuna masa nashi Uban da matsayi sun kere na babansa. A sanadin wani rikicinsu sai da Musaddam din ya yi kwanaki uku a ofishin ƴan sanda kafin a fiddo shi. Ya kasa cewa komai sai shafar ƙeya, Ibb Gusau ya nuna shi da yatsa.

"Kai ba za ka taɓa nutsuwa ba kenan a rayuwa ko? Ina mai gargadinka, wannan ya zama na ƙarshe, ke kuma zan ba ki lambata duk sadda kika ƙara ganinsa da ƙanwarki ki kirani kai tsaye nasan maganinsa. Ke kuma ki yiwa kanki faɗa ƴanmata, kar ki bari shaiɗan ya kaɗa maki ganga, irin su Musaddam ba su dace da ke ba. Daga ganin yanayin ƴar uwarki an san daga gidan mutunci ki ka fito saboda haka please be careful."

Raihana da ta yi mutuwar tsaye da mamakin mutumin da Futuha ta ce ba ya magana mai tsawo yana zuba zance ta gyada kai. Ga kuma wani iri da ta ji cewa wai zai ba Humaira lambarsa. Aikuwa Humaira ta miƙa mishi wayarta ya sanya mata lambar ya danna kira ta fito kan wayarsa sannan ya miƙa mata. Musaddam dai na tsaye kamar an kafe shi a wurin ya kasa motsi sai wani ɗaci da ya ke ji a maƙoshi ganin an dake shi an kuma hana shi kuka. Ya yi biyu babu kenan.

"Ko za su bi ka ka sauke su a gida?" Ya yi furucin da sassanyar murya. Sai a sannan ma hankalin Humairar ya kai gareshi karo na biyu don ta mance ma  da wanzuwarsa, ranta ya yi fari sol da taimakon da Ibb ya yi mata, ko ba komai ta ga tsoro fal a saman fuskar Musaddam wanda hakan ya fi komai faranta mata. Ganin irin kallon da Fadeel ke jifanta da shi ya sa ta kauda kai.

"Aa mun gode, zamu hau ɗan sahu."

Fadeel kamar ya tanka sai kuma kawai ya basar bai ce uffan ba. Humaira ta kalle su, kalmar godiya ce kadai ta fito a bakinta kafin ta juya ta dubi Raihana.

"Muje." Ba musu kuwa Raihana ta bi umarninta, zuwa yanzu jikinta a mugun sanyaye yake. Ta dai tabbata Humaira ta fi ƙarfinta. Ba kuma ta son tada wani borin su Ibb su ƙara ganin rashin kunyarta ƙarara.

Bayan tafiyarsu, Ibb ya shiga yiwa Musaddam faɗa mai haɗeda nasiha, a karshe  ya ba shi damar tafiya. Sai da ya bar wurin sannan ya dafa kafaɗar Fadeel yana murmushi.

"Toh ya aka yi?"

Fadeel ya zura hannuwansa cikin aljihu ya fiddo hannunsa na dama riƙe da waya ya miƙawa Ibb gami da ɗan ɗara  gira kaɗan. Dariya Ibb ya yi ya girgiza kai.

"No, haba Malam, da wuri haka?"

Ya narkar da wuya.

"Please, ina rantsuwa da Allah ban taɓa jin abin da na ji a kan wata ba sai ita."

Murmushi Ibb ya faɗaɗa.

"Alhaji da sannu dai Allah zai cika masa burikansa."

Guntun murmushi Fadeel ya yi.

"Ko? Kai kuma kana neman ka dakile faruwar hakan."

"Ah wane ni? Ba ni na sanya maka."

Ya karɓi wayar Fadeel da tuni ya buɗe, lambar Humaira ya sa a ciki sai kuma anan ya dafe goshi.

"Oh no, ka ga ko sunanta ba mu sani ba. Da me zan maka saving?"

Jin haka ya lumshe idanunsa yana hasko kyakkyawar fuskar Humaira wacce kumatunta har wani sheƙi suke saboda fushi, ya kuma lura ko ya ya ta buɗe bakinta sai wushiyarta ta bayyana. A hankali ya ce.

"Mrs Fadeel."

"What?" Ibb da kunnuwansa kamar ba su ji ba ya tambaya. Buɗe idanunsa ya yi ya dube shi dakyau.

"Yes, haka za ka yi saving lambar."

"Aa, riƙe ka yi da hannunka. Ka gani koda wani abun ya je ya zo, ba za ka kalle ni da shi ba."

"Babu abin da zai je ya zo face alheri. Da yardar Allah ba ta da miji sai Fadeel."

Ya ba wa Ibb amsa sa'ilin da ya sa hannu ya karɓi wayar. Aikuwa da hakan ya yi saving sunan. Ibb dai mamaki ma yake, to kodai ɗan lokacin da ya kwashe ba ya tattare da su ya sauya ne daga yadda ya san shi? Mutum da zancen aure ma ba ya so a yi mishi, daidai da hira idan ta budurwa ce aka ɗauko cikin abokai yanzun gayyar za ta watse a wurinsa don tsam yake tashi ya bar musu wurin yana mitar ba shi da lokacin shirme.

"Sai goben?"

Maganar Fadeel ta katse mishi tunanin, ya sauke ajiyar zuciya.

"Allah ya kaimu. Amma ina mai ba ka shawarar kada ka zurfafa, duk abin da aka zurfafa ana shan wuya a cikinsa. Balle kuma irin wannan faɗawar da ka yi lokaci guda."

Madadin ya amsa sai ya yi murmushi ya soma tafiya kawai, sanin da Ibb ya yi shikenan sallamar tasu ya sa shima ya nufi motarsa cike da fatan shi din ma Allah ya kawo mishi mace ta gari ya huta da gorin ƙannensa sun yi aure sun bar shi da Mahaifiyarsa ke yawon mishi.

***
  A can gida kuwa, Mami tun da ta ji wai Humaira ta fita ba da saninta ba gaba daya ta ji ta kasa sukuni. Har ta kasa ɓoye ɓacin ranta ta hau faɗa a falon.

"Wannan wani sabon salo ne da har Humaira za ta sa ƙafa ta fice a gidannan ba tare da neman iznina ba? Me take so na faɗawa Abbanku idan ya tambaye ta?"

Tasleem da Futuha suka kalli juna suka taɓe baki, yayinda Ummita da aka kira tuhumar ko ta san inda take, ta ke gefen kujera a zaune.

"Toh wai Mami, ba Humairar na da waya ba? A kira mana." Faɗin Mubarak wanda ke shigowa falon daga masallaci, tun kafin fitarsa Mamin ke faɗan fitar har dai ya dawo ba ta chanja zani ba. Ganinsa ne ya sanya su Tasleem nutsuwa. Mamin kuwa dubansa ta yi kafin ta kauda kai ta ja guntun tsaki na takaici.

"Kira na nawa kuma? Wayarta idan ba a kashe take ba to na fi tunanin babu network."

Ya kai duba ga Ummita.

"Ke ba ta faɗamaki komai ba?"

Kafin Ummita ta amsa, Futuha ta yi caraf.

"Nima dai ita nake zargi don babu ta yadda za ta fita ace ba ta sanar mata ba. Bakinsu daya wallahi Yaya."

Kallon da ya watsa mata ya sa ba ta ƙara cewa uffan ba, Mami ta ja tsaki karo na ba adadi ta nufi ɗakinta. Ganin haka Ummita ta miƙe ta yi nasu dakin da zummar gabatar da sallar La'asar, ita kanta tunanin da take yi bai wuce na inda Humaira ta je ba tare da neman iznin Mamin ba kamar koyaushe. Tsoronta kar Abba ya dawo ya tambaye ta ace ta fita alhalin ba ta da makaranta yau.

Aikuwa dai sai wuraren biyar da mintoci suka shigo gidan, ko ci kanki ba wanda ya cewa wani a cikinsu. Su Yassar dake zaune cikin abokansu a kofar gidan su ka bi su da kallo.

"Ga uwar girman kan gidannan ta dawo." Faɗin wani abokin Yassar yana nuni da Humaira. Tun ranar da ya yi gangancin kulata da sunan so ta ci mishi mutunci yake jin tsanarta. Yassar tsaki ya ja.

"Kai ka so ai dama ka ga kalar nata girman kan, amma ga mata a gari kamar ƙasa ka rasa ta kulawa sai wannan ƴar ƙauyen nijar din?"

Sauran suka yi dariya. Shi kuwa Yassar miƙewa ya yi ya bi bayansu ganin kamar Raihana na sharce hawaye, jikinsa har mazari yake don muddin ya kasance Humaira ce sila to ya rantse sai ya rama mata koda kuwa gaban Abba ne ba Mubarak ba.

***
A falon gidan suka iske su Futuha zaune, sallamar Humaira ta dakatar da Ummita daga shiga kicin, ta dawo cikin falon da sauri don ta ganewa idonta ko ita ɗin ce. Futuha da Yasmeen kuwa ido suka bi Raihama da shi ganin yadda fuskarta ta yi ja ga shatin yatsu kwance saman fuskarta.

"Ke, Raihat, me nake gani haka? Uban waye ya mareki?!" Tasleem ta faɗi da buɗaɗɗiyar murya tana kallon Humaira. Humaira da ita dinma kiris take jira ta dube ta dakyau.

"Ni ce nan, ko za ki rama mata ne?"

Aikuwa jin haka gaba daya Tasleem da Futuha suka yo kanta, ta kuwa shiga tarewa, duk wacce ta bugeta sai ta sa hannu ta rama da iyakar ƙarfinta, duk da cewar su biyu ne a kanta, ta yi iyakar kokarinta amma itama ta ji jiki. Ummita ta hau kwala ihun kiran Mami, ga Yassar a gefe da ya ƙi ya tsawatar don dama ya jima da haushin Humaira a ƙoƙon ransa. Raihana na ihun su kyaleta akan ba ita ce ta mare ta ba amma inaa dama sun jima su na dakon rana mai kamar ta yau din hakan ya sa da gayya suka yi biris da ita. Yayinda a ɓangarenta shakkar tonuwar asirinta take musamman da ya kasance Yaya Mubarak na gari, ta sani koda ace Abba bai taɓa lafiyarta ba, shi kam ban da lafiya ma, hatta da wayar da take tunƙaho da ita sai ya raba ta da shi.

Kusan a tare Abba da Mami suka shigo falon. Wata tsawa Abba ya daka da ta sa gaba daya suka saki juna, Humaira gefen kumatunta na fidda jini sakamakon yakushi da ta sha da dogayen faratan Futuha. Su kuwa daga mai riƙe baya, sai mai riƙe gefen fuska da naushin Humaira ya kumbura har ya tasa. Mami zuciyarta ta yi wani iri, ta kasa magana ta yi shiru tana kokarin hadiye abin da ke cinta. Abba ya karaso falon ya dube su gaba daya. Humaira tuni ta durkusa, ganin haka su ma suka durƙusa.

"Mene ne hakan? Wane sabon shashanci ne haka? Ke Humaira wadannan ba su girmeki ba? Ku kuma manyan wofi ba kanwarku ce ba? Duk me ya kawo rigimar ne?"

Humaira ba ta ce uffan ba, Yassar ya yi saurin sa baki.

"Abba ba fa wani abu ba ne, Humaira ce ta mari Raihana har fuskarta ya yi shatin yatsu, shi ne don Tasleem ta yi magana kawai sai ta taso mata da faɗa wai ta mara ko akwai shegen da zai rama mata. Kalmar shege ya fusata su suka yi kanta da duka." Murmushi mai ciwo Humaira ta yi lokaci guda hawayen da take dannewa suka zubo samam fuskarta, zubar hawayen a inda Futuha ta mata rauni ya sa ta jin zafi amma ba ta ko damu da sharewa ba don wata azabar ta fi wata, ita daya ta san me take ji a zuciyarta. Ummita ma hawayen take na ganin yadda gaba daya Yassar ya juya magana. Ita kuwa Mami, karasowa ta yi ta ɗaga fuskar Raihana tana kallo. Tabbas mari ne, fuskar ta yi ja, ga yatsu kwance ta ko'ina a gefen fuskar.

"Mari?! Mamana dagaske ne kin mari ƴar uwarki? Me ta yi maki da zafi har haka da kika ɗau hukunci da kanki?"

Raihana nan fa ta shiga zare-zaren ido, Humaira ta kalleta na ɗan dakiku, har abada ba za ta tona mata asiri gaban iyayensu ba. Mami ta kai matsayin da ko laifin ɗiyarta ta gani za ta iya rufa mata asiri don haka dakyar ta haɗo abin fadi.

"Ka yi hakuri Abba. In sha Allah ba zan kara ba."

Nan kuma Abba ya kara fusata.

"Oh, dagasken kenan kin mare ta ko?! Wannan ai hauka ne! Kamar babu manya a gidan? Ke waye ya mare ki?"

Nan ya shiga bude mata wuta, sai da ya gama sannan ya maida hankali ga su Futuha wadanda duniyarsu ta yi dadi, ko babu komai wacce suke yiwa kallon ta fi su a wurin Abban yau ya rufe ido ya wanketa tas kamar zai kai duka. Hakan yasa ba su ji zafin nasu faɗan sosai ba. Sai da Mami ta sa baki sannan ya bar wurin. Humaira na ta kallon fuskar Mamin don ta hasaso yanayinta amma ba ta fahimci komai ba sai dai jikinta ya yi sanyi ganin ko kallonta Mamin ba ta yi ba. Hakan na nufin ba ta ji dadin hukuncin da ta yiwa Raihanan ba?

***
"Ban da abinki Humaira, duk son da Mami za ta nuna mana ai ba zai kai son ƴaƴan da ta haifa da kanta ba. Ni ba abin sa ya fi ban haushi irin yadda ba a damu da tambayar inda ku ka je ba. A jikina nake ji ba hakanan kawai za ki mari Raihana ba, akwai abin da kike ɓoyewa. Amma wace rana zai maki? Zai siya maki daraja ne a gun Raihana da yan uwanta kike zato? Babu ɗaya fa, halinsu ne ba na jin za su taɓa sauyawa."

Ummita ke zubo mata zance sa'ilin da suke kicin su na gudanar da girkin dare, awanni kusan biyu bayan afkuwar komai, Humaira
DOWNLOAD
DOWNLOAD

5 Comments On DUKAN RUWA
avatar
daiy drop

1 year ago

Reply

hhh

avatar
daiy drop

1 year ago

Reply

sss

avatar
daiy drop

1 year ago

Reply

sss

avatar
daiy drop

1 year ago

Reply

sss

avatar
north

1 year ago

Reply

hhhhh

Please Login or Register in order to submit comment