Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da Humairar za ta dawo hannunsa, sai dai ya so ace ko na faransancin ne ta yi, da irin haka biyu babu. Ya tuna shawarar da Mami ta ba shi a daren jiya da suke maganar karatun Humairan.

_"Zai fi dai ka sanya ta a inda za ta koyi sana'a koda kuwa na girke-girke ne, kasan can idan ma ta yi karatun faransanci ne, nan kuwa turanci ake. Zai iya ba ta wahala."_

Toh shi ɗin ma dai ya ga hakan ya fi mishi sauƙi, yanzun ma dubunnan da yake fitarwa na karatun yaran kaɗai sai godiyar Allah kawai, ina kuma da ace ya sanya Humaira wacce ya tabbatar kafin ta fara sai an yi mata lesson a gida sosai, ɗaukar karatun ne ma abin tunani, bai san ya kaifin kwakwalwarta yake ba.

"Abba."

Ya tsinci muryarta wanda  hakan ya katsemishi tunani.

"Na'am Mamana."

"Abba meyasa ba ka taɓa zuwa ka gan ni ba? Meyasa ko a waya ba ka damu da kira mu gaisa ba idan ma aiki ne ya tsare ka?"

Ya tsare ta da ido, yanzun ya gama raina kaifin kwakwalwar yarinyar, sai dai ya sha mamakin tambayoyinta duk kuwa da ya sani lallai ne dama watarana ta yi mishi su. Sai dai bai tsammace su nan kusa ba. Dogon numfashi ya ja ya furzar.

"Kiyi hakuri Humaira, eh na yi maki laifi amma hakan ba wai yana nufin ban damu dake ba ne. Sai dai nayi hakan bisa alƙawarin da na ɗaukarwa mahaifiyarki wanda hatta da bayan mutuwarta ban karya shi ba."

Cikin sauri ta ce.

"Wane alƙawari?"

Ya yi shiru sai kuma ya ɗago da niyyar magana, muryar Mami ta katse hanzarinsa.

"Wai nikam dai yau Abban yara ba ka da niyyar fita ko? Gashinan har goma ta gota."

Suka dubeta, a ɓangaren Humaira ji ta yi gaba ɗaya zuwan Mamin bai burgeta ba, sai da aski ya zo gaban goshi tana shirin ta san ta ya ya aka haihu a ragaya lokaci guda kuma Mami ta yi mata katsalandan. Mami kuwa ganin hankalin Humaira ba ya kanta sai ta girgizawa Abban kai cike da damuwa. Abba shi din ma jinjina kan ya yi, ya fahimci manufarta. Don haka ya dubi Humaira da murmushin yaƙe.

"Af, kinga na sha'afa har lokaci ya ja, kar ki damu Mamana, muna tare ai yanzu, a kowane lokaci idan na samu dama da kaina zan yi kiranki mu yi hirar nan kin ji ko? Yauwa Maminki ma ta ba da shawarar a sanyaki a makarantar koyon girke-girkenku na zamani, ina fatan za ki so hakan?"

Duk da yanayin rashin jin dadin da take ciki sai da ta yi farin ciki da hakan. Dama tana da son girki, ko a can gida ita ke yiwa Dada dahuwa daga lokacin da ta soma zama budurwa. Ta kuwa saki fuskarta har wushiryarta na fitowa muraran.

"Eh Abba ina so."

Abba ya dubi Mami suka yi murmushi, Mamin ta karaso ta dubi Humaira.

"Yauwa ƴar Abbanta, kin ga da girki adon mace ce. Kuma na tabbatar za ki iya sosai idan kika mayar da hankali. Ana samun alheri sosai da girki. Kar ki wani damu idan ba ki yi boko ba, da yawa babu bokon amma sun samu ci gaba ta fanni da dama a rayuwarsu."

Humaira ta jinjina kai, tabbas haka ne don ta ga mijin Mammati wata ƴar uwarsu a Maine, shi ma babu bokon amma yanzu kaf ƙauyen nasu babu mai kuɗinsa. Idan ya zo hutu da yaransa kowa sai ya san ya zo saboda alherin da yake yi musu.

"Ki je ciki nasan zaman da kaɗaici ke kadai, ki sa Ladidi ta kunna maki kallo a wayarta sai ki yi."

Ta fadi hakan saboda babu wuta, ƙa'idar Abba tun sha biyun dare ake kashe masa inji, sai ko idan aka ci sa'a Kedco sun hasko wuta.  Humaira ta fice a falon bisa bin umarni. 

Bayan fitarta Mami ta ƙarasa ga Abba fuska dauke da damuwa.

"Ya haka? Kana son ka karyawa yarinya zuciya daga zuwanta? Ko kuwa so ka ke ta riƙi mahaifiyarta da mugun zato a ranta alhalin ba ta ji ba ba ta gani ba? Don Allah kar ka fara, kar ka yi wannan kuskuren. Tabo ne da yaro kan yiwa gurguwar fahimta."

Abba ya numfasa.

"Hakane, sai dai ki sani ba karamin taimakona ki ka yi ba don ba ki da masaniyar abin da zan ce a sannan. Na gama iyakar nazari ban san ƙaryar da zan shirga don rufe zancen ba. Na gode maki mace ta gari."

Ya karashe yana jifanta da murmushi, ta rausaya  kyawawan idanunta tana maida mishi martani.

"Nima na gode da wannan yabon, muje ka shirya lokaci na ƙurewa. Idan ka dawo ni kuma kafin nan na bincika wurin wacce ya dace a kai Humaira ta fara daukar darasi."

"Hakane, amma zan fi so ta gama shiga ta san ƴan uwana. Kafin a durfafi wannan."

Mami ta ɗan yi jim sai kuma ta amsa da toh. Bayan shigar su ɗakin yana cikin shiri ta sanyo zancen kaya.

"Ka ga ya kamata a ɗan ɗinka mata suturu ko ba yawa, mutumin da ya zo daga ƙauye na tabbata ba wasu kayan kirki ne da ita ba."

"Ke dai wato burinki kawai na karya bakin aljihu, toh wannan na jikinta ba sutura ba ce? Kin fi kowa sanin ba na son kashe-kashen kuɗi ko?"

Ta yi ƴar dariya, an zo wajen. Ai idan har batu na fitar da kuɗi ne toh nan suke kai ruwa rana, a karshe dai hakanan ta ke cin nasara a kanshi, kafin ya botsare akan jima.

"Haba Abban yara, Humaira fa uwa guda ce, idan ba ka yi mata ba wa za ka yiwa?"

Ta ƙarashe murya a narke kamar wata matashiyar budurwa, hakan ya tuna mishi zamanin tashen soyayyarsu. Ya yi dariya gami da girgiza kai.

"Maryam kenan, ke kam ba a kayar da ke a magana. Shikenan idan na dawo zamu ga yadda za'a yi. Na fita ai ko?"

"Eh ka fita kam, Allah ya kara buɗi." Ta ba shi amsa tana dariyar itama.

Ya amsa da amin.

***
  Washegari kuwa Mami da kanta ta bada aka siyowa Humaira atamfa da leshin sai kuwa kananun kaya dogayen riguna duka dai ba masu yawa ba, hatta da takalmin shiga taro ƙafa biyu da mayafai kala uku sai da Mami ta siya mata, ba kuma ta tsaya anan ba sai da aka haɗo da kayan shafe-shafen mata da na kwalliya da kuma undies.

Abba ya kalli kayan sannan ya kalli Mami.

"Yanzu dukkan kayan nan a dubu talatin?"

Mami ta ɗan bishi da hararar wasa.

"Au, ka yi zaton kowa irinka ne? Wannan dai ya fi ƙarfin abin da ka bayar, Mami ta cika ta siyawa ɗiyarta. Wanda ka bayar ma mun gode."

Ya yi ƴar dariya.

"Maryam mai halin girma, ai shikenan, wannan tsakaninku kun fi kusa. Allah ya saka da alheri."

Ta amsa da amin.  Sannan ta umarci Ummita dake zaune wadda ita ce ta dauko kayan zuwa sashin Abban akan ta ɗauka ta ba Humaira na shafe-shafen, suturun kuwa ta sa a leda Humairar ga shirya su kai wurin telansu.

Ummita ta amsa da toh, sannan ta kwashi kayan ta fice.

A falon Mami kuwa, Tasleem ce zaune a gefe daga ita sai vest sai kuwa wandon makarantarta da ba ta cire ba, zaune take tana cin ɗan wake tana ba su Raihana labarin wata ƴar ajinsu Suhaima da kusan kullum ta Allah babu ranar da ba sa taɗinta. Sosai ta tsayawa Tasleem ɗin a ƙoƙon rai, a cewarta yarinyar ta fiye rawar kai, ga nunawa sauran ɗalibai kamar ta fi uban kowa ƙoƙari. Tasleem ta cusa loma a bakinta sannan ta dube su.

"Kun san yau wallahi ta ci arzikin Babandi da ya shiga tsakaninmu amma da sai na gwabje bakinta. Ƴar iskar yarinya ta dubi tsabar idona ta ce wai ina mata katsalandan a harkokinta saboda kawai tana yin tutorial din sanya kai na ce ita kanta ba ta gane ba shikenan fa ta tasomin, su kuwa ƴan korenta su Teema Small saboda na taɓa Hajiyarsu me zuwa da mota nan suka goyi bayanta."

"Ke dai Tasleem ina raba ki da nuna bakin cikinki a fili ga Suhaima, kin kasa ɓoyewa har sun harbo jirginki, ke ba ki iya kwantar da kai ba? Ai irinsu da sannu za ki shige mata har ta yarda dake ki zama aminiyarta, kika san wane Don ɗin za ki samu ta hanyarta? Ko kin mance cewa ubanta fa ya fi naki arziki, koda dai namun akwai sai maƙo." Faɗin Futuha tana ƙarashewa da murya a ƙasa gudun kar ta yi shuka a idon makarwa. Suka kwashe da dariya, shiru Tasleem ta ɗan yi sai kuma ta ce.

"Ke kuma fa haka ne wallahi, don ba ki ga wani arnen gaye da ya taba zuwa wajenta a makarantar ba, wallahi ƙarshen dai haɗuwa ya haɗu, ba wai kyawun fuska ba aa, motarsa ma kanta abin a kalla ce."

"Ahaf, to kin gani. Ai kinga kakarki ta yanke saƙa muddin ki ka samu irinsa. Bare ma yanzu da Abba ya yi sanyi da batun auren, da ace ban da Mami ta shawo kansa ya bari ai da yanzun mun haihu. Taɓ ni nasan da yarana biyu."

Suka yi dariya, hankalinsu ya koma ga niƙi-niƙin kayan da Ummita ta shigo da su daga bangaren Abba.

"Ke." Cewar Futuha. Ummita yarinya mai sanyi da hakuri, ta juyo ta kalle ta. Da yatsa ta nuna ledojin kafin ta ce.

"Wannan fa? Daga ina zuwa ina?"

Duk da tambayar ta rainin hankali ne, amma ta amsa.

"Aiken Mami ne, ta ce a kai wa Humaira."

Daga haka ta ci gaba da tafiya, dukkan su ukun ba wacce ta tanka sai faman furzar da hucin ɓacin rai da baƙin ciki. Can sai Tasleem ta ja tsaki tana ture kwanon da ta ci ɗanwake da ƙafa.

"Mami! Mami!! Wallahi ban taba ganin uwa irin tamu ba wacce ba ta damu da lamarin yaranta ba. Kunsan Allah, ba don kamanni da kuma Ann dake ƙara ba mu tabbacin cewa ita din mahaifiyarmu ce dagasken ba da zai yi wuya na yarda."

Cikin taɓe baki Futuha ta amshe zancen.

"Uhum, kema dai kya fada. Ai shiyasa nake so mu samu mazan kece raini da za'a kalla a ƙara kalla. Ko ba komai za mu huta da baƙin cikin Abba da Mami."

Tsaki Tasleem ta ja ranta na zafi, sai dai ta kasa magana karshe kawai ta mike ba ta ko kara kallon kwanon ba kuma babu niyyar ɗaukewa. Bayan wucewarta kallon Futuha ya koma kan Raihana wacce ta maida hankalinta ga waya tana  murmushi.

"Ke kuma ke da wa? Mu gani."

Raihana kamar wacce aka tsikara ta mike tana ja baya da dariya.

"Toh sa ido, ina ruwanki da wayata?"

Futuha ta taɓe baki.

"Kya ji da gulmarki dai, kullum latse-latsen waya, wayarki ta munafukai babu wanda kika taɓa bari ya ga meke ciki. Ni ban san irinki ba, ko hoto za ki nunawa mutum sai dai ya kalla haka tana dunkule hannunki kamar wacce za'a sacewa."

Raihana na dariya ta yi hanyar waje gami da fadin.

"Eh ɗin dai, wasu ma ba a san me suke shukawa ba. Gwara ni ko failed ban taɓa samu ba sai ku masu C.O."

Futuha ta yi kwafa kawai tana huci, zafi biyu ya haɗe mata.

***

Murna sosai Humaira ta yi da wannan kyautar ban girman. Ta ɗaga wata riga ja mai adon fulawa ruwan madara tana mannawa a jikinta. Haƙora a buɗe ta dubi Ummita.

"Kinga kamar Mami ta auna, daidai da ni."

Ummita ta yi dariya.

"Eh mana, sai ki sa hijabi su na falon Abba kiyi musu godiya. Kinsan Allah, Mami tana ban mamaki. Wai fa har cikawa ta yi da kudinta ta ƙarasa yi maki siyayya, nidai ban taɓa ganin mace mai kirkinta ba."

Humaira ta jinjina kai tana murmushi cike da gamsuwa da zantukan Ummita. Tabbas itama a farko ta yiwa Mamin gurguwar fahimta, amma yanzu kam ta ga saɓanin tunaninta. Sai kuma da sauri ta dubi Ummita.

"Wai anya ban yi wauta ba? Kin ga ban je na gaida Anna ba tun da na zo."

Ummita ta ɗan yi shiru alamar damuwa, har dai Humaira ta ce.

"Lafiya kika yi shiru?"

Girgiza kai ta yi.

"Anna fa ba ta wani murna da zuwanki, ta cewa Mami koda wasa kar ta sake ta turo ki ɓangarenta. Ki share kawai, ni nasan Mami za ta shawo kanta, kuma tunda kuna tare a gidan dole watarana ku haɗu ai. Zance ne kawai irin na Anna. Kinga jeki ki yiwa su Abban godiya mu wuce, yamma na yi."

Humaira ta gyada kai kawai ta numfasa, dama ba dole ne kowa ya ƙaunaceka ba. Ba tare da damuwa ba ta zura hijabin ta fice a ɗakin.

04

Humaira ta ware idanu tana ƙarewa garin Kano kallo a hanyarsu ta komawa gida bayan sun kai wa telan Mami dinkunan an kuma auna ta, sosai akwai bambanci da inda ta fito koda dai dama ita din a ƙauye take. Sai dai kuma hatta da titunan garin burgeta suke yi. Ummita ta kalleta ganin yanda gaba ɗaya hankalinta ke a waje, murmushi ta yi.

"Humaira kenan, idan dai garin nan ne har sai kin gaji da shi ina tabbatar maki."

Jin haka sai ta yi dariya.

"Anya kuwa? Nidai sosai ya burgeni wallahi. Ji nake tamkar kada mu koma gida."

Dariya Ummita itama ta ɗan yi.

"Shiyasa ai na ce a bi da mu ta wannan hanyar ba ta farko ba, kinga sai ki ƙara kalle garin sosai ko?"

Jinjina kai Humaira ta yi tana murmushi sannan ta jefo mata tambaya.

"Ni kuwa yar uwa su Abba su nawa ne a wajen Umma? Umman na raye?"

"Umman su Abba tun ina firamare, yaranta uku kawai Allah ya ba ta daga nan ba ta ƙara haihuwa ba sai ko yaran ƴan uwa da ta riƙe ta aurar. Kinga Abba shi ne babba sannan Babana, sai autar ɗakinsu Baba Amina, ita a can gadon kaya take zaune da mijinta. Kuma Kakanmu wanda ya haifi Abba shi ya riga ma Umma rasuwa, ita kadai ce matarsa har ya bar duniya. Kar ki damu kedai, tun da kika zo garin nan babu gidan da ba zamu je ki ga ƴan uwanki ba in sha Allahu."

Murmushi ya suɓucewa Humaira har ta ɗan lumshe idanu ta buɗe su, ranta ya yi fari sol, burinta ya cika. Yadda ta san kaf ƴan uwan Mamarta, yau Allah ya nufa za ta san na Abbanta. Haka suka karasa su na tafe Ummita na mata nuni da wuraren ƙayatarwa a garin.

***
   
Dattijuwar mace ce hakimce saman kujera ta haɗe girar sama da ta ƙasa. Banda tsufanta da ya fito muraran, kallo ɗaya idan ka yi mata za ka ga tsantsar kamannin da ta yi da Mami har ta so ta fi Mami hasken fata. Ta gyara zama gilashinta gami da amsa sallamar da Mami ta yi mata ciki-ciki. Anna sam ba ta iya ɓoye abin da ke ranta wannan ya sanya a kallo daya Mami ta gane fushi take da ita. Da harshen buzanci ta ce.

"Anna yanzu zancen nan ba zai wuce ba? Ina ce na yi maki bayanin komai?"

Anna da sai a sannan ta dubeta ta ba ta amsa cikin yare don ba kasafai take yin hausa ba, kaɗan-kaɗan take ji.

"Ki ka ce bayani? Yanzu ke har kina tunanin zan gamsu da bayananki na wofi Maryam? Kina da masaniyar irin
wahalar da aka ci a baya? Wato ke dadi miji ko?"

Mami gaba ɗaya ta dube ta fuskarta duk a jagule.

"Haba Anna, idan ban godewa bawan Allahn nan ba  bai kamata na watsa mishi ƙasa a ido ba. Mutumin da ya amince na zauna tare da ku, muke rayuwa. Duk da irin son abin hannunsa, hakan bai sanya shi watsi da lamarinki ba. Duk wata kulawar da mai shekarunki ya dace ta samu, babu ɗaya da ya taɓa nuna gajiyawarsa wajen yi. Toh mene ne aibu a ciki don ɗiyarsa guda ɗaya ta zauna a hannuna?"

"Shashashar banza da wofi, dama nasan ba alheri ne zai fito a bakinki ba. Wato dai gori za ki yimin ko? Dama nasan akwai ranar ƙin dillanci ai, dadin abin da baza  ta kike rawa. Shikenan zan sa maki ido na ga inda wannan rashin hankalin naki zai kai ki. Kin fi kowa sanin wahalar da aka sha a baya ai."

Mami dai ba ta ce komai ba, ta so a bar maganar a sanyo wata amma sam ba ta samu fuska wurin Anna ba dole haka ta miƙe ta kama hanyar barin ɗakin, daidai ƙofa ta ɗan dakata kafin ta juyo ta sakarwa Anna wani murmushi da ita kanta Anna ya ba ta ɗumbin mamaki da baƙin ciki, to wannan sabon raini ne ya gifta tsakaninta da Maryam din ko kuwa dai kishi ya taɓa kwakwalwarta tun a shekarun baya? Haka Anna ta cigaba da saƙe-saƙenta da babu mai warware mata.

***
  A kwana a tashi babu wuya a wurin Allah, har a yau Humaira ke cika sati uku cif a garin Kano. Abubuwa da dama sun faru na alheri a rayuwarta da suka rinjayi sharrukan ciki. Ɗaya daga ciki har da ƙarin suturu da ta samu, sai kuwa gadonta da sif din kayanta da Abba ya sa aka yi mata. A gefe guda Abba ya mallaka mata wata ƙaramar waya ƙirar Vivo sai dai tana yin whatsapp, kuɗin wayar dai dakyar suka  fito daga aljihun Abban nan ma sai da Mami ta sha fama har ta nuna ɓacin rai ƙarara, a duniya kuwa babu abin da Abba ya tsana kamar ganin Mami ta sauya mishi, nan da nan take cin galaba a ka sa muddin buƙatarta bai shallake tunaninsa ba.
  Ummita ta yi mata rakiya wurin dangin Abbansu na kusa, sun yi murna kwarai da ganinta. Sun kuma karɓe ta da hannu bibbiyu, babu abin da ya fi faranta ran Humaira irin shaidar kirki da suka yiwa mahaifiyarta. Ta kuma ji dadin hakan ba kaɗan ba. Rashin abin yi ne ya sa kusan koyaushe idan ba ta komai tana kan wayar tana danne-dannenta ganin ta riƙe abubuwan da Ummita ta koyamata tunda dai harshen turanci ne, ta kuma sani koda faransancin aka mayar ba za ta tsinci abin kirki ba. Abba ya sanya mata lambar Kawunta, sun gaisa sau ɗaya ta waya don ita kam ko whatsapp ma cewa Ummita tayi kada ta buɗe mata, ba ta ga wanda za ta yi hira da shi ba. Ta dai gwammace ta kunna rediyo ta yi ta saurare don hatta da waƙoƙi iri-iri na soyayya da Ummitan ta sanya mata ba ta damu da su ba.

  A wannan yammacin kamar koyaushe tana zaune a ɗakinsu gefen gado ta buɗe labule iska mai daɗi na dukanta, garin wuni aka yi cikin zafi yanzu kuwa sai ya ɗan huce. Rabin hankalinta yana ga farfajiyar gidan inda take hango Yassar tsaye da abokinsa wanda ta ji ana kira da Affan su na hira, a gefe ɗaya Muhsin ne da ball yana wasansa tare da Waleed, daidai nan Futuha ta buɗe gidan ta shigo, dawowarta kenan daga makaranta, Humaira na lura Affan na mata magana ko kallonsa ba ta yi ba, daga yanayin tafiyarta za ka fahimci ba a nutse take ba, har ta gifta hankalin Humaira na kanta, ta san dai babu lafiya, tana kuma fatan ba gurguwar shawarar da ta ji jiyan wata aminiyarta Aina'u da ta zo tana ba ta ba shi ta gwada a yau ɗin, gabanta ya faɗi. Ba ta mance kalaman da suka fito daga bakin Aina'un bayan Futuha ta gama amayar mata da damuwarta akan mahaukacin soyayyar da take yiwa Ibb Gusau.

   _"Ke ki na ban mamaki wallahi Futuha, ki na da kyawun da babu namijin da zai kalleki bai ƙara ba. Da ace ni ce ke, wallahi babu abin da zai hana na kai wa Ibb Gusau kaina. Kina da sura irin wadda da zarar kin tallata mishi kanki zai ji nan duniya babu wata sai ke. Ke idan ma wannan bai yi ba, ki zo na raka ki wurin Malam Aci Bulus, na rantse maki ko me kike so za ki samu. Ke wallahi sai kin mallaki malamin nan kin juya shi kamar waina a tanda."_

Gaban Humaira ya yi wata iriyar faduwa, ta ambaci Allah a ranta, ta yi nisa da saƙe-saƙen zuci ta ji an banko ƙofar ɗakin an shigo, ta juyo da sauri, Futuha ce. Ba ta ko lura da ita ba ta kife a saman gadon Tasleem tana kuka har da sheshsheƙa. Humaira ta yi shiru, kafin ta lalubo abin faɗi duk kuwa da cewar ba shiga sabgar juna suke yi ba, Tasleem ta shigo ɗakin da sauri a bayanta kuma Raihana. Za ta soma magana amma idanunta na sauka kan Humaira ta fasa, cikin haɗe rai ta ce.
 
"Malama ba mu waje za mu yi magana."

Jin haka tsam, Humaira ta miƙe ta kama hanyar barin ɗakin, bayan fitarta Raihana ta karasa ta rufe ƙofar har da sanya muƙulli sannan ta dawo. Futuha suka ɗago su na magiyar ta sanar da su abin da ya faru. Dakyar ta iya tsaida hawayenta ta shiga ba su labari.

"Ai na faɗamaku yadda muka yi da Aina ko?"

Suka gyaɗa kai duk sun ƙagu su ji komai.

"Shi ne..shi ne.."

Sai kuma ta yi shiru ta rasa me ma za ta ce. Tasleem ta zaro ido.

"Shi ne me Futuha? Kada dai ki cemin kin gwada aiwatarwa?"

Futuha ta runtse idanu gami da shafa gefen fuskarta tana kuka sosai. Sai a sannan idanunsu ya kai ga gefen fuskar, ya yi ja ya yi ruɗu-ruɗu alamun dai mari ta sha. Koda alama ma ba guda ɗaya ba.  Ba ta bari sun nemi ba'asi ba ta cigaba da maganarta.

"Na iske shi zaune a ofishinsa shi kaɗai yana aiki a system, koda na shiga bai ɗaga kai ya kalle ni ba, daga motsawar leɓɓansa na gane ya amsa sallamata. Duk da cewa gabana na faduwa hakan bai sa nayi ƙasa a gwuiwa ba na karasa ga teburinsa. Na sauke mayafina yanda rabin kirjina ya bayyana, na shagwabe murya ina mai batun ban gane abin da ya koyar a aji ba. Koda naga bai kalle ni ba, sai na yi gangancin kai hannu saman nasa, shi ne ya gaggauramin tagwayen maruka a kuncina. Ya kum rantse idan na ƙara shiga ofishinsa sai ya ɓalla ni kuma daga kaina masu tunani irin nawa za su dawo hayyacinsu."

Tana kaiwa nan ta ci gaba da kukanta. Tasleem da Raihana kusan a tare suka sauke ajiyar zuciya. Raihana ta ja tsaki.

'Kema dai Futuha wataran kina abu kamar Waleed marar wayo wallahi. Ke kin manta tun farko itama Aina'un sonsa take yi wai? Ko don ta ɓata ki a wurinsa ku yi biyu babu kinga ai za ta ba ki gurguwar shawara. Ai mun faɗamaki amma ke idanunki ya rufe."

Tasleem ta amshe.

"Yanzu shikenan koda ace wannan mutumin na ganinki da mutunci kin ɓarar da shi, yadda za'a yi ki gyara ma nikam ban sani ba. Kada dai garin gyaran a ƙara jagula abubuwan shi nake tsoro. Ke!!! Wai don uwaki shi kaɗai ne namiji a duniya ma? Aikin banza kawai! Ga samari ƴan kasuwa da ƴan bokon su na matowa a kanki a instagram amma kin tsaya biyewa wani so, so, ke fa kike ban shawarar na shigewa Suhaima don na samu na yi mata koda snatching ne, amma ke nan kin tsaya ɓata lokaci akan wani kuturu gurgu."

Jin haka ran Futuha ya ɓaci, ta harari Tasleem kafin ta ja tsaki.

"Da ace kun san mene so da duk baku ɓata bakunanku ba. Sannan Ibb Gusau lafiyayyan mutum ne kar ki kara aibata shi. Tunda kuma ba ku da shawarar da za ku ban, ni nasan me zan yi."

Tana kai wa nan ta miƙe ta yaye mayafin ta faɗa banɗaki ba tare da ta amsawa Raihana da ke jefomata tambaya akan abin da za ta aikata ba.

***
  Mami ce tsaye a farfajiyar gidan ta haɗa cikin atamfa ruwan ƙasa mai adon fari, ta sha mayafi ruwan ƙasa hakanan takalminta. Ta dai yi kyau ƙarshe, idan ka kalle ta ba za ka ce ita ta haifi yaran ba saboda daidai gwargwado ta iya ɗaukar wanka. A gefenta Yassar ne su na magana yana ƙorafin shi dai mota yake so tasan yadda zata yi Abba ya siya mishi. Mami jinsa kawai ta ke yi tana yi kuma tana duban gate, da ta gaji ta ja guntun tsaki.

"Wai ina Yakubu ya je ne? Daga jeka ka sha mai shikenan har yanzu

5 Comments On DUKAN RUWA
avatar
daiy drop

2 years ago

Reply

hhh

avatar
daiy drop

2 years ago

Reply

sss

avatar
daiy drop

2 years ago

Reply

sss

avatar
daiy drop

2 years ago

Reply

sss

avatar
north

2 years ago

Reply

hhhhh

Please Login or Register in order to submit comment