Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kamar ma ba shi da niyyar motsawa.

Bayan fitarsu Abba ya yi tagumi cike da tunani, a yanzu duka-duka dai abin da ya haɗa bai fi miliyan shida ba, ya kuma sani muddin ba gidansa da suke ciki zai siyar ba bayan motocin da ya sa kasuwa ya siyar, to fa babu ta inda zai samu cikon miliyan goma na fansar yaransa. Yana wannan halin ne Mami ta yi sallama ya amsa gami da ba ta damar shigowa. Ta shigo sanye da hijabinta ta zauna gefensa fuskarta dauke da damuwa ta ce.

"Baƙi ka yi ne?"

Ya numfasa.

"Eh, yaron nan Fadeel ne ya zo da abokinsa, ba su jima da tafiya ba."

Ta ɗan yi jim sai kuma ta numfasa ta ce.
 
"Allah Sarki."

Daga haka ba ta ɗora komai ba, shiru ya biyo baya kafin Abba ya girgiza kai ya ce.

"Maryam, an zo gaɓar da dole sai na siyar da gidannan na cika kuɗin fansar yarannan. Idan ya so sai mu koma wanda bai fi shi ba, lokaci na ƙurewa sosai, kaina ya ƙulle gaba ɗaya, dole na tashi na nemi mai siya ko kaɗan a kuɗin ne aka ba ni zai isa na cika na kaiwa wadannan mutanen."

Murmushi Mami ta yi.

"Kamar ka san shawarar da na zo na ba ka kenan Abban yara, sai kuma naji dadi da ka kasance mai yarda da ƙaddara. Siyar da gidan zai fiye mana alheri matuƙar dai za su bar yaranmu su dawo garemu."

Abba ya jinjina kai.

"Hakane Maryam, dama na riga da na yi magana da lauyana, na kuma bada damar an sa gidannan a kasuwa, ina ta tunanin ta yadda zan sanar maki kada ki ji abin daga sama shi..."

"Haba Abban yara, wace irin magana kake yi ne? Mene ne ciki don ka sadaukar da abin da yake mallakinka don fansar yarana? Idan da ace yau nima na mallaki wata dukiya kana tunanin ba zan iya sadaukar da ita domin ceto ransu ba? Don Allah kada ka sa naji kamar kana bambanta Humaira da Ummita da yan uwansu."

Tun faruwar al'amarin na su Humaira, Abba bai yi koda murmushi ba sai a yanzun, ya kamo hannun Mami ya riƙe gam cikin nashi.

"Ina kaunarki Maryam, Allah ya yi maki albarka. Nagode da kika fahimce ni."

Itama murmushinta ta faɗaɗa gami da shafar gefen fuskarsa.

"Nima ina kaunarka. Yanzu ajiye godiyarnan, ka daure ka sa abu a cikinka sai a je a san ya za'a yi. Ina fatan dai ba ka faɗawa  D.P.O yadda ku ka yi ba ko?"

Abba har ya buɗe baki zai magana sai ya tuna yadda suka yi da D.P.O da safe. Sun tattauna ya sanar da shi komai bai rufe ba akan batun kuɗaɗen fansa da aka nema.

*_Koda wasa Yallaɓai kar ka nunawa kowa ka faɗamin yadda ake ciki. Komai kusancinka da mutum, ka ɓoye wannan tattaunawarmu saboda mutane su na da ban tsoro, koda ace ka faɗawa wanda ka yarda da shi yadda muka yi, to fa zai iya sanar da wani maƙiyin. Kaf duniya tun da dai daga ni sai Alhaji Bashir (Daddy) muka san da hakan, to ya tsaya iyakar nan, koda ace sun ƙara kiranka a waya kar ka bari wani cikin iyalinka ko ma waje ya sani.  Mu kuma zamu yi iyakar yin mu, mu yi kokari mu cafke su duk sadda ka tashi kai musu kuɗin._*

"Ya naji ka yi shiru?"

Mami ta nemi sani tana mai ƙuramasa idanu. Ya numfasa.

"Babu komai Maryam. Ina tsoron na furta masa su ji labari tunda sun gargaɗe ni. Bana fatan a samu matsalar da yarannan za su rasa rayukansu."

Ta jinjina kai.

"Ina ji a jikina za su dawo gida cikin aminci."

Daga haka ta jawo kayan abinci ta shiga zubamasa tana mai lallaɓa shi don ya ci. Dakyar ya tsakuri kaɗan ya miƙe ya yi shiri ya fita don ganin ya kammala kafin ya kai.

Cikin rashin nasara, aka rasa mai siyan gidan Abba, a karshe dai tayin da ya ƙi karɓa a farko na iyayen Fadeel hakanan ya karɓi cikon miliyan huɗu ya haɗa aka tashi kuɗin fansa, babu abin da ya rage sai jiran waya daga kidnappers don a ji lokaci da kuma wurin da za a miƙa kuɗin. Mami ba ta san ya aka yi da batun gida ba, Abba dai ya ce mata an samu an haɗa kudade. Daga nan bai ƙara ko harafin A ba.

***
Humaira da Ummita na rakuɓe a lungu guda na ɗakin sun yi shiru don zuwa lokacin kukan ma ya ƙi fita, aka banko ƙofar ɗakin aka shigo. Su ukun dai da suka zame musu tamkar baƙaƙen kumurci su ne suka shigo. Suka ƙura musu idanu tamkar za su lashe su, Wizzy kamar koyaushe sigari ne a hannunsa, ya fesar da hayaƙin ya dubi Babba da Badboy cikin murmushi ya ce.
  "Ni zan fara, ku kuma sai ku biyo baya."

Ba su ji dadin wannan hukuncin ba amma babu yadda suka iya, hakanan suka lashi lebbansu suka ja gefe. Shi kuwa kai tsaye ya ƙarasa ya finciko Ummita wacce ta ƙanƙame jiki guri guda ga jikinta dake masifar rawa.

"Ina za ku kai ta? Ku yiwa girman Allah ku yi hakuri."

Humaira ke zancen cikin ruɗu da tashin hankali. Suka kwashe da dariya.

"Haba Baby, kema ai zan zo kanki. Duk inda zan kai ƴar uwarki kema za ki je. Kuɗin fansarku aka kawo, za a tafi da ku gida."

Humaira sam zancen bai shige ta ba balle Ummita da ba ta san lokacin da ta shiga kuka sosai ba, su na jan ta tana tirjewa, Humaira na zabga uban ihu suka dauke ta da mari suka fidda kyalle suka rufemata baki da idanu. Wizzy haka ya ja Ummita har sai da ya dangana ta da wani ɗakin.

Humaira da suka fita suka rufe kamar ta yi hauka haka ta dinga bugun ƙofar tana gurnani tamkar wacce ake  zarewa rai. Babban fatanta bai wuce su ceto Ummita da ko ihunta ba a ji ba sakamakon rufemata baki da aka yi da kyalle.

Ummita na ji tana gani Wizzy ya keta alfarmarta. Tsananin azaba ya sanya ta sumewa ba tare da sanin inda kanta yake ba. Shi kuwa ya fito yana sharɓar gumi, ya dubi su Badboy cikin annashuwa ya ce.

"Ku bari shegiyar ta farfaɗo sai ku ƙara farr mata, suman dadi ta yi."

Suka kwashe da muguwar dariya. Yana kai wa nan ya shige wurin Humaira.

Tana ji an bude ƙofar ta yi saurin karasawa gami da shaƙe wuyan rigar Wizzy tana um um saboda bakinta da ke ƙulle ta ma kasa magana. Ya yi dariya gami da tura ƙofar da ƙafarsa ta baya ya damƙe hannunta.

"Haba my love? Kokawarnan da kike wani sanyamin ƙarfi ai sai ki jigatar da kanki tun ma ba a je ko'ina ba."

Daga nan ya soma kiciniyar raba ta da kayanta yana taɓa wasu ɓangare na jikinta, nan da nan ta ji kanta ya soma wani irin sarawa, wani irin baƙin ciki da ba ta za ta iya kimantawa ba ya tsaya mata cak a ƙahon zuci. A sadda Wizzy ya yi nasarar keta rigar dake jikinta, a lokacin ne gaba ɗaya tsikokin jikinta suka mimmiƙe. Idanunta suka ƙara turuwa suka yi ja, ba ta san lokacin da ta shaƙo wuyansa ba har ya shiga kakarin mutuwa. Duk iya ƙarfin da ya sa da zummar ƙwatar kansa ya kasa, ga shi ba damar ihu saboda koda ya yi abokan aikinnasa za su yi zaton na lafiya ne. Haka suka ƙarasa har jikin ƙofar da ba ta rufe gaba ɗaya ba.

Anan ne Badboy da ke zaune saitin ƙofar ya hangi hannun Wizzy na lilo, da wani irin gudu-gudu ya tunkari ƙofar, shima Babba ya mara mishi baya. Daƙyar suka tura ƙofar ta buɗe. Abin da suka gani ya yi mugun rikita su, Humaira dai ta zame musu tamkar wata ƙaƙƙarfar damisa, daƙyar da suɗin goshi suka ƙwace Wizzy a hannunta, Babba ya fice da shi daga dakin yayinda Badboy ya tunkareta da niyyar kifamata mari sai dai yanayin da ya ga ta taso ta yi kansa ne ya sa shi ficewa babu shiri. Nan ta kife zaune tana rirriƙe kanta dake azabar sarawa tana huci ga uban gumi kuma ga baki a ƙulle. Kukan nan da ta saba yi ta shiga rerawa mai mugun tsuma zuciya, ta fi rabin awa a haka har ba ta san an shigo da Ummita an watsa ta a kusa da ita ba.
  Abin da Humaira ta aikata ne ya sanya Wizzy dakatar da su daga ketawa Ummita haddi, ya ce su kyale su kafin su kashe su labari ya sauya tunda gobe za su cafki kuɗadensu. Da wannan suka rufe su gam suka bar gidan su Babba da Badboy na ɗacin ran ganin samu da kuma rashi lokaci guda. Ganin haka Wizzy ya yi musu alƙawarin zai ba su sabuwar yarinyarsa da ya yi a wurin mashayarsu kowannensu ya more da ita, sun ɗan ji dadin hakan tunda ko ba komai ita bariki ke yayi a lokacin. Kowa kuma mararinta yake.

Ummita da har lokacin ba ta da kuzari, kusan ma yanzun suman zaune ta yi. Ga uban azaba da ta ke ji a ƙasanta, gaba ɗaya hawayenta ya kafe ta ma kasa koda kukan, tun shigo da ita abu ɗaya ne a bakinta take furtawa sanadiyyar ƙyallen da aka ciremata, Innalillahi kawai take ambato daga farko har ƙarshe, wannan daren babu wanda ya runtsa sai Humaira da bayan gama koke-koken wani bacci marar dalili ya ɗauketa kamar yadda ta saba.

***
A firgice Raihana ta farka daga mummunan mafarkin da ta yi wai an soka wuƙa a wuyan Ummita, Humaira kuma tana kwance cikin jini. Wani ƙara ta saki mai firgitarwa ta zabura ta miƙe daga gadon Mami ta nufi hanyar fita daga ɗakin. A hanyar ƙofa ta ci karo da Mami kasncewae asuba ta kawo kai, Abba ya fita masallaci. Cikin tsananin ruɗani Mami ta riƙe ta.

"Meyafaru Raihana?"

Ta ruƙunƙume Mamin sai kawai ta fashe da kuka mai tsanani. Mami ba ta ce mata komai ba ta shiga shafar kanta. Don kanta Raihanar ta sassauta kukan sannan ta ɗago kai ta ce.

"Mami nayi mafarki marar daɗi akan su Humaira. Har yanzu ba su kira Abba a waya ba? Mami a kai kuɗaɗennan a dawomin da ƴan uwana yanzu kafin lokaci ya ƙure. Kar su kashemin su."

Mami ta riƙe hannuwanta.

"Kar ki damu da mafarkin da ba lallai ya kasance gaskiya ba. Ki yi addu'a da fatan alheri. Ina mai tabbatar maki babu abin da zai faru da su, lafiya kalau za su dawo gidannan ki gan su."

Raihana ta ɗauki maganganun Mami kawai don ta kwantar mata da hankali ta faɗi, amma ina da ta ke da tabbacin ganin ƴan uwannata cikin kwanciyar hankali? Haka dai ta dinga lallaɓa ta ƙarshe ta samu nutsuwa ta fice ta ɗora alwala ta tayar da sallah amma har sannan kirjinta na dukan tara tara. Wannan dalilin ne ya sanya ta tsaya ta yi addu'a sosai har ta jawo Alƙur'ani ta karanta ta roƙarwa yan uwanta tsari daga sharrin dukkan masu sharri.

***
Ƙarfe shida na safe daidai sai ga kiran Wizzy ya shigo wayar Abba.  Abba ya ɗaga jiki na rawa. Nan yake tambayar ko kuɗaden sun samu, ya amsa da eh. Daga nan ya yi mishi kwatancen inda za su haɗu, ya ƙara da faɗin.

"Ina ƙara gargaɗinka, kar ka sake ka yi kuskuren zuwa da jami'an tsaro idan ba haka ba a gabanka zan yanka wuyan ƴaƴanka."

Abba ya hau girgiza kai tamkar Wizzy na gabansa.

"Aa aa, ni kadai zan zo. Ba zan saɓa alƙawarinku ba."

Daga nan kit aka kashe wayar, ya ɗaga kai ya dubi lokaci, yanzun shida da mintuna, an kuma ce mishi bakwai daidai ya isa wannan dalilin ne ya sanya shi miƙewa ba shiri ya janyo jakar kuɗaɗen. Tunanin ya kira D.P.O ya sanar masa yake amma kuma yana jin tsoron kar su cutar da su Humaira sai dai ya ɗan yi shahada ya dannawa D.P.O kira, suna cikin magana Mami ta iso, Abba bai ko lura da ita ba don hankalinsa ya yi gaba. D.P.O ya ce za su fito su ma cikin kayan gida da kuma motar da ba ta aiki ba, ya kwantarwa da Abban hankali ya nunamasa kar ya damu su Humaira za su kuɓuta a hannun ko ma su waye.

Mami ta dubi Abban a rikice bayan ya gama wayarsa.

"Abban yara sun kiraka ne naji kana sanar da D.P.O?"

Bai kalle ta ba ya ja akwatin jiki na tsuma ya ce.

"Eh Maryama mun yi waya da su. Bari naje kar lokacin ya ƙure mintuna kawai suka ba ni."

Mami ta sha gabansa.

"Meyasa za ka yi ganganci da rayuwar yarana? Mene dalilin sanar da D.P.O? Ba ka tsoron su cutarmin da su?"

Sai ta fashe da kuka jikinta babu inda ba ya rawa.

Abba bai da lokacin rarrashinta sai kawai ya ce.

"Kiyi hakuri, babu abin da zai faru da su lafiya kalau zan maidomaki su in sha Allahu. Ku sanya ni addu'a har na dawo dai."

Yana kaiwa nan ya fice riƙe da muƙullin motar Jannat da Mamin ta aro masa tun jiya an kuma zuba mai dama jiran su kira kawai ake. Tasleem dake laɓe ta yi baya da sauri zuwa dakin Anna jikinta har tsuma yake.


Abba yana hanya ma sai ga kiran Fadeel, Abban ya kwantar masa da hankali ya ce sun yi waya yanzun yana hanyar fita amsar su. Ya tambayi Abban inda suka ce, kamar ba zai faɗi ba sai dai ya faɗamasa. Fadeel ya ce zai biyo bayansa. Dakyar Abban ya hana shi gudun samun matsala.

***
  Bakwai da mintuna uku Abba ya iso dab da kogin da suka yi masa umarni. Yana tsayuwa ya ji wayarsa na ringing. Jiki na rawa ya fiddo ya ɗaga.

"Mun ganka, ka fito da jakar ka ajiye gefen wannan kogin, mu kuma za mu turomaka yaranka. Ba ruwanka da kalle-kalle, ka saukar da kanka ƙasa har ka ajiye ka bar wurin."

"Toh."

Yana faɗin haka a gaggauce ya ja jakar ya fita.  Bisa bin umarnin nasu kansa yana ƙasa amma fa ta ƴan maza kawai yake sai dai zuciyarsa na ta harbawa da ƙarfi. Sunayen Allah ya shiga ambato da fatan samun matsaya.

Wizzy kuwa da suke can gefe ƙasan wata ƙatuwar bishiya, su na ganin fitar Abban ya sanya Badboy da Babba cicciɓar su Humaira da suka ba su kwayoyi suke ba a cikin hayyacinsu ba suka nufi motar Abban da nufin sanya su ciki. Kiran da Wizzy ya samj ne game da batun zuwan ƴan sanda wurin ya sanya shi fitowa gami da dakawa su Badboy tsawa.

"Ku dawo da su mu bar nan! Shegen ya kira ƴan sanda!"

Jin haka sai kuwa aka soma harbi, dayake Allah ba azzalumin bayinSa ba, sai kawai suka yashe su a wurin sakamakon harbin da aka yiwa Badboy a kafaɗa ya saki ƙara,  da gudu suka koma cikin motar kiii suka tayar suka soma yunkurin barin wajen.

Abba da sai kawai maganganu ya ji da ƙarar harbi bai san sadda ya juya ba a ruɗe hantar cikinsa na kaɗawa don ya gama saddaƙarwa su Ummita aka harba. Sai dai ganinsu a yashe a tsakar filin ya sa shi sakin jakar kuɗin ya nufe su da gudun da a shekarunsa bai san ma zai iya ba. Su Wizzy tuni sun bar nan su na cizon yatsar wannan babbar asarar da suka yi. Yayinda D.P.O da mutanensa suka ƙaraso cikin jin zafin kubcewar da suka yi musu.

"Yallaɓai ba kuka ya kamata ka yi, kamata ya yi mu miƙa su asibiti."

Jin haka sai Abban ya ji kamar an masa tuni, ya ɗaga Humaira, macen ƴar sandar da ta biyo su ta ɗaga Ummita suka sanya su a mota sai asibiti. Jakar kuɗaɗen kuma yana cikin motar ƴan sandan suka mara musu baya. Fadeel da ya kasa haƙuri ya biyo bayan Abban, kafin ya kai ga ƙarasawa ya hango Abba a mota kawai sai ya yi reverse ya bi bayansu jikinsa babu inda ba ya kaɗawa. Yana son ya kira Abban don jin ko an same su amma yana tsoron jin akasin haka daga gareshi wannan ne ya hana shi kiran gaba ɗaya.

Murja ta jima tsaye jikin tagar falo tana hangen fitar Fadeel a gigice. Ranta idan ya yi dubu toh ya ɓaci. Hankalinta kuwa idan akwai abin da ya fi gaban tashi toh ta ya yi wannan dalilin ne ya sanya ta komawa cikin daki da sauri-sauri ta ɗauko gyalenta sai ko waya da jaka ta fice daga gidan a birkice har Anti Amarya wacce ta fito daga nata ɗakin tana tambayar ko lafiya kuma ina za ta je amma babu amsa.

***
Kasancewar tare suka isa asibitin da ƴan sanda wannan ya sa a gaggauce aka karɓi Humaira da Ummita zuwa emergency. Abba ya kasa zaune balle tsaye, ban da hawaye babu abin da ke fita daga idanunsa, ga jiri na kwasarsa yana ta ambaton sunan Allah kamar zai ciri baki. Daidai lokacin Fadeel ya shigo a birkice ya ƙarasa ga Abba.

"Abba sun fito? Su na ina? Me ya same su?"

Dukkan waɗannan tambayoyin ba a hayyaci yake yin su ba. Abban ma da ba a wani nutse yake ba sai ya kasa tanka mishi kawai sai ajiyar zuciya da kallo ga lebban na motsi amman ko harafi guda ya kasa fitarwa sai D.P.O ne ya karɓi zancen ya yiwa Fadeel bayani.

"Ka kwantar da hankalinka, in sha Allahu babu abin da zai faru garesu. Likitan ya tabbatar mana ga dukkan alamu kwayoyi aka ɗura musu amman in sha Allah za su yi iyakar ƙoƙari a kansu."

Fadeel ya dafe kansa ya yi juyin, ya yi safar ya dawo ya kai marwar amma wannan kalmar ta ya kwantar da hankalinsa ya kasa samun matsaguni a zuciyarsa. Kwayoyi? Ya ma rasa inda zai jefa zancen a kwakwalwarsa ballanta ya samu ya yi aiki da shawarar D.P.O Salahuddeen. 

***
A can gida kuwa, Tasleem tun sadda ta kai labarin tafiyar Abba fanso su Humaira, Jannat ta dauki waya hankali tashe ta kira Bokanta. Kaca-kaca suka yi sosai tana zaginsa akan ita fa ba su yi haka ba. Wannan ya sa  Boka tun a wayar ya ci alwashin sai ta girbi wannan tozarcin da ta yi masa. Kasancewar idanunta sun rufe ruf sai kawai ta ja mugun tsaki ta katse kiran.

Awa bai fi ɗaya tsakani ba, sai ga wayar Abba zuwa ga Mami, a gaggauce ya sanar da ita kuɓutar su Ummita ya kara shaida mata cewar su na asibiti. Hankali a mugun tashe suka fice tare da Ƙasim da Raihana wacce lokaci guda wani mugun zazzaɓi ya rufe ta musamman jin cewar su na asibiti. Suka yi kiciɓus da Kawun Humaira da matarsa Hajjo wadanda isowarsu kenan garin. Ba su tsaya yi musu dogon bayani ba, Kawu ya bi su yayinda ya ce Hajjo ta tsaya ta jira dawowarsu a gida.

***
  BAYAN AWANNI...

Mummunan labarin da ya iske su Abba na keta alfarmar da aka yi ga Ummita ya sanya shi sumewa bai ko iya jin ƙarshen ba balle ya san ko har Humairar ma an taɓa. Nan aka kwashe shi shima don ba shi taimakon gaggawa. Raihana kuka kamar ranta zai fita yayinda Mami ke taya ta. Kawu da Fadeel kuwa tashin hankalin da suke ciki ba zai misaltu ba. A gabansu aka fiddo su bayan an yiwa Ummita ɗinki na mugun raunin da aka ji mata aka sauya musu ɗakunan zuwa na hutu, daki mai gado biyu. Fadeel ya ƙurawa Humaira idanu kamar kirjinsa zai fashe haka yake ji, nan take idanunsa suka kaɗa jawur. Gaba ɗaya ta lalace ta yi rama tamkar wata halittar ce ba ita ba sai ko hancinta da ya ƙara fitowa. Har aka shige da su bai iya kauda kansa ba. Shi ya yi ƙarfin halin biyan dukkan abin da aka kashe har da na kama ɗaki.

  Cikin ƙanƙanin lokaci labarin kuftowar su Humaira ya cika gari, mutane da waɗanda suke dangi da ma yan uwa na gari suka dinga tururuwar zuwa yi wa su Abba barka, babu wanda aka bari shiga wajensu, hakanan labarin abin da ya afku gare su bai fita ba. Yan jarida kuwa suka dinga yaɗa rahoto, hakanan social media ta dauka.  Futuha mutanen Dubai ta ƙara yin bidiyo mai nuni da damuwa da kuma farin ciki tana shaida wa jama'a cewa an ga ƙannenta. Nan aka hau taya ta murna sosai.
Mutanen Bichi da labari ya iske su su ma baa bar su a baya ba. Anti Maijidda ta yi kuka kamar ranta zai fita jin labarin keta haddin da aka yi ga Ummita, matsayinta na babbar yaya ga uwarta ya sa Abba sanar da ita a sirrance.

  Sahabi kuwa baki har kunne, sun zo shi da abokansa yayinda mahaifinsa takanas ya zo ya taya Abba murna da addu'ar Allah ya kiyaye gaba.

  Kwanakin su Humaira biyu suka dawo hayyacinsu. Ummita ce ta soma farfaɗowa, ranar Allah ya taƙaita Anti Maijidda na zaune tare da Baba Amina sun yi jugum su na dan hira jefi-jefi hannuwansu riƙe da casbaha. Wani gigitaccen ƙara Ummita ta saki da ya yi masifar tayar da hankulansu.

"Wayyo Allahna! Kar ka kashe ni! Ka rabu da ni! Na haɗa ka da Allah ka rabu da ni!! Wayyo Allahna!!!"

Cikin kuka da tashin hankali suka yi kanta su na riƙewa, aka bankaɗo ƙofar aka shigo, su Abba ne da  ihun Ummita ya iske su. Raihana a guje ta nufi wurin Nurses dake tahowa, kafin ta kai ga magana suka ce sun ji. An tafi kiran likitan. Su na shiga sai ga Likita, aka fitar da kowa a ɗakin.

Gaba ɗaya matan kuka sosai babu kamar Raihana da take jin kamar ta shiɗe. A yadda take jin zuciyarta za ta iya fille kan wanda ya aikata wa yan uwarta wannan tozarcin.

Koda likitan ya ƙarasa gareta flask din ruwan zafin dake ajiye a gefenta kawai ta ɗauka ta jefa masa. Ba don Allah ya sa shi kaucewa ba da babu abin da zai hana a same shi.

Tana cikin wannan gigitar Humaira ta farka a matukar firgice, ta kira sunan Ummita da karfi sannan a guje ta diro ta zo ta rungumeta tana kallon jama'ar ɗakin kamar wasu sabbin halittun da ba ta taɓa gani ba.

"Su waye ku? Me za ku yi mana?! Ku fice ku bar nan! Wallahi ku ka yi ƙoƙarin zuwa kusa da mu zan ji maku ciwo."

Sai kuma ta juya a mugun firgice tana tattaɓa jikin Ummita dake kuka kamar ranta zai fita.

"Ummita! Yi shiru, Abba zai zo. Naji suna cewa yana hanya. Yi shiru, sai mun kashe su."

"Kin.."

Likitan ya ƙaraso zai soma magana Humaira ta juya da azama tana nunashi da yatsa. A sannan su Abba gaba daya sun shigo sun kasa daurewa.

"Kar ka taɓamin ƴar uwa! Zan kashe ka!!"

"Humaira, Ummita."

Humaira na ganin Abba ba ta ko damu da sauran jama'ar Abba ta karasa a guje ta rungume Abba tana kuka mai tsuma zuciya.

"Abba za su kashe mu! Abba ka cece mu! Ka ɗauke mu mu bar nan!"

Irin riƙon da ta yiwa Abban ba na wasa ba ne har maɓallan wuyar rigarsa sai da suka fita.

Cikin hawaye ya ce.

"Mamana babu abinda za su yi maku, likitoci ne. Kun kuɓuta daga hannun azzalumai. Ki kalla dakyau, ga Maminki ga yar uwarki Raihana. Kin gane Kawunki?"

Ta tsaya cak kamar wata sokuwa tana kallonsu ɗaya bayan ɗaya, Ummita kuwa da nos ta lallaɓa ta yi mata allura tuni bacci ya kwasheta. Kawai sai ta soma ruwan wasu sabbin hawayen ta ma kasa cewa uffan. Zuciyarta ta gasƙata eh sun kuɓuta daga hannun azzaluman, amma kuma ta ji tana tantama tana gani ko mafarki ne. Wannan ya sa Raihana tahowa da sauri ta rungumeta ta kara sautin kukanta.
A hankali ta ɗaga hannunta ta ɗaga fuskar Raihana ta na kallo kamar wata baƙuwar halitta ce gabanta, sai kuma da rawar murya ta ce.

"Raihana ce?"

Raihana saboda ƙarfin kukan ma ta kasa magana sai kawai ta ɗagamata kai. Humaira ta rungumeta sosai suna kukan tare.

"Amm, don Allah a ragu a ɗakinnan. Alhaji ina son magana da kai."

Fadin Likita, ganin haka duk aka fice banda Raihana wacce Humaira ta riƙe hannunta gam tamkar ita kaɗai ta gani.

***
Likita ya dubi Abba cikin nutsuwa ya

5 Comments On DUKAN RUWA
avatar
daiy drop

2 years ago

Reply

hhh

avatar
daiy drop

2 years ago

Reply

sss

avatar
daiy drop

2 years ago

Reply

sss

avatar
daiy drop

2 years ago

Reply

sss

avatar
north

2 years ago

Reply

hhhhh

Please Login or Register in order to submit comment