Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta miƙe, Futuha ba ta kawo komai ba ta ƙarasa da sauri ta rungumeta ta fashe da wani irin kuka mai tsuma zuciya.
Mami wacce ta ji kirjinta ya yi wani irin bugu da ƙarfi ta ɗago kai da azama ta kalle ta har hannuwanta a rawa.
"Ke mene ne ya faru ne? Ina Yakubun?"

Gaba ɗaya ta ruɗar da cikin Mami wanda ta ji har wata ƴar ƙara ma yake yi.

"Mami ƙarya yake yimin, ashe matarsa tana gidansa cikin wata irin ƙasƙantacciyar rayuwa?"

"Toh ina ruwanki da ita! Ke ba kanki kika sani ba?!"

Yadda Mamin ta yi furucin a zafafe ya sa Futuha shiru tana kallonta da ɗan mamaki saman fuskarta, kamar dai ba Mamin da ta saba karo da ita ba. Sai kuma ta tuno labarin ƴanmatancin Mamin da Anna ta ba su, mace ce da a tarihin soyayyarta ba ta taɓa kallon mai mata balle ta ji zuciyarta za ta iya ɗaukar zaman kishi da ita ba, har tana jinjina mamakin zaman da ta amince suka yi da Fatima ta kuma ƙaunace ta. A baya dai Mami ba ta san kowa da komai ba sai kanta da kuma nata. Wannan tunanin da Futuha ta yi ne na tsohon tarihin Mamin ya sanya ta sauke ajiyar zuciya lokaci guda kuma mamakinta na farko ya gogu tas daga kwanyarta.
"Nifa ba wannan ƙaryar ce ta tada hankalina ba, tun kafin mu dawo likita ya bayyanamin ina da ciki bayan ƴar rashin lafiya. Na bar abin na ɓoye ban sanar mishi ba akan zan ba shi labari mai dadi, sai yau da muka dawo ne nake sanar da shi toh kawai sai ya sauya fuska. Ya kuma rantsemin shi bai aure ni don na haifarmasa, daga uwargidansa kawai yake da kwaɗayin samun yara. To fa shi ne da faɗa ya kaure tsakaninmu, ya ce na zubar ni kuma na ce ba zan zubar ba tunda ba shege ba ne, kawai Mami sai ya ja hannuna ya kai ni ɓangaren Uwargidansa. Nayi mamakin ganin ashe yaransa takwas har da budurwar da za ta yi sa'ar Raihana. Komai nata ya ci uwarsa a falon. Goyon ɗa take yi ma, a gabanta da na yaran ya nunamin yaranta sun ishe shi ba ya kaunar haihuwa daga kowace mace. Ya kuma aure ni don ya ci duniyarsa ganin da ya yi ni ƴar rawa ce wai a Tiktok na kuma san ta kan rayuwa sai ya ɗauka zan san dabarun family planning kafin aure."

Kawai sai ta fashe da kuka. Mami zuciyarta har wani tafarfasa yake yi. Ta ji kukan Futuhar tamkar yana ƙara tafarfasa ƙwaƙwalwarta don haka ta dakamata tsawa.

"Ya isa! Nace maki ya ishe ni haka! Haba! Da wanne ku ke son na ji? Da mummunan albishir din da Babandi ya faɗamin ko kuwa da hargitsinku?! Ke ba za ki iya cin uban shege ba?! Ba za ki iya yadda za ki yi ki ga kin fitar da yar iska daga gidanki ba?! Shashasha kai marar wayo!"

Tana kaiwa nan ta nemi bakin gado ta zauna kirjinta na dukan tara-tara tana maida numfashin gajiya. Futuha kuwa ai sai ta ƙara yin mutuwar tsaye don mamaki. Toh Mamin nan dai ta tabbata ita ce ainahin Mamin can baya lokutan yanmatancinta, ita ce Mamin da Anna ta yi mugun kewarta. Faɗa, zagi kuma duk akan kishi? Yau Mami dai da bakinta ta mata iznin daukar kowane mugun mataki ne akan kishiyarta da mijinta. Futuha ta juya cikin sassarfa tana kukan har lokacin ta fice zuwa ɗakin Anna.

Mamin kuwa sai bayan da kwanyarta ta ɗan samu nutsuwa, tashin hankalin dake ƙasan ranta ya ɗan lafa sai ta soma tunano irin maganganun da ta faɗawa Futuha. Ta lumshe idanu ta ja guntun tsaki. Ta san yarinyar dole mamaki ya kashe ta, amma ita ta san azabtuwar da take yi ko kuma ta yi a shekarun baya da suka gushe. Ta tsani kishiya tsana mafi munin gaske.

'Ciki har da Fatima?'

Wani ɓangare na zuciyarta ta watso mata wannan tuni. A fili ta ɗaure fuska tamau, idanunta nan da nan suka kaɗa tsabar masifa da kuma abin da ta tuna na daga rayuwar Fatima da Yusuf a baya.

"Har da Fatima." Ta furta a zahiri, can kuma ta miƙe ta shiga banɗaki ta wanke fuskarta. Sai bayan ta dawo daidai ne sannan ta fito zuwa ɓangaren Abba. Ta iske shi zaune yana kallon labarai, itama wuri ta nema ta zauna da wani irin sanyin jiki.

Abba ya maido hankali gareta.

"Maryama, na ganki wani iri, Futuhar ba su dawo ba ne?"

Mami ta girgiza kai.

"Sun dawo, tana wajen Anna ma suna gaisawa."

"To ko jikin Tasleem din ne? Ni me ma ya faru ne da ita ta yi rauni?"

Ko kusa ba ta sanar da Abban gaskiyar abin da ya yi sanadin kwanciyar Tasleem din a asibiti ba. Ta sani muddin ya ji to faɗa zai yi wannan ya sa ta gyara batun.

"Zamewa ta yi ta faɗi a banɗaki. Amma ai da sauki tunda jinin ya tsaya."

Jinjina kai Abban ya yi.

"Allah ya raba su lafiya. Sai ta ƙara kula."

Ta yi shiru tana kallon gefe guda ta kasa amsa mishi, ya riƙo hannunta cike da kulawa murya a tausashe ya ce.

"Faɗamin, meke damunki?"

Ƙasa ta yi da idanunta sai hawaye, suka zubo saman hannun Abba da ya ɗora bisa nata. Nan da nan ya ƙara shiga tashin hankali.

"Kinsan bana son kuka ko? Taimaka ki faɗamin damuwarki Maryam. Zuciyata ba za ta ɗauki wani sabon tashin hankalin ba bayan wanda na fuskanta kwanakin nan."

Ta jinjina kai ta dube shi.

"Abban yara tunanin yarannan ya kasa barin zuciyata ta huta. Tun dawowarsu zan iya ce maka Ummita har yau ta ƙi dawowa cikin nutsuwarta. Yarinya mai fara'a da son jama'a marar hayaniya, ta koma wata iriya. Babu doguwar magana balle hira, koyaushe zaman tunani da shiru. Wannan abu yana damuna matuƙa."

Shima Abban hakan da ta faɗi sai ya ƙara taso mishi da nasa damuwar.

"Hakane Maryama. Toh a shawarce me kike tunanin za'a yi? Mece ce mafita?"

Mami ta numfasa.

"Mafita a samar mata abin da zai dawo da walwalarta. Abin nufi, madadin lokacin da aka sa na aurenta da Sahabi, me zai hana a yi mishi magana idan sun shirya kawai ya kawo lefe a sanya bikin nan da kamar sati biyu?"

Ɗan jim Abba ya yi cikin hali na tunani. Sai kuma ya ce.

"Kina tunanin idan an yi hakan ba a tauye ta ba kuma. Bana jin yarinyar nan ta samu nutsuwar da za ta karɓi aure a yanzu. Kada ki manta fa, keta haddinta aka yi ta ƙarfi. Aa Maryama, mu dai yi hakuri tun da abinda ya rage cikin shekarar bai wuce watanni biyar ba, ki jira mu ga abin da Allah zai yi a gaba."

Ba haka ta so ba sam, ba kuma ta taɓa tunanin Abban zai watsamata ƙasa a ido ba. Kai ta mance rabon ma da ta bada shawara irin haka dangane da abin da ya shafi yaran ya musanta. Ganin sauyin dake saman fuskarta ne ya sa Abban ƙara riƙo hannunta ya ɗan matsa.

"Kiyi hakuri Maryama, ba fa watsa maki ƙasa a idanu nayi akan al'amarin yaranki ba. Aa, ki dai daure na sani da zafi ka dinga ganin ɗanka cikin yanayi mai firgitarwa. Amma a shawarce, me zai hana ta je Bichi ko sati biyu ta yi kinga za ta samu nutsuwa da kwanciyar hankali."

Daure fuska Mami ta yi.

"Shikenan, ɗauke ta a yau ka kai ta sai Maijidda ta zuba ruwa a ƙasa ta sha tunda ta ga gazawata a kula da Ummita. Nagode."

Tana kaiwa nan ta zame hannunta cikin na Abban ta soma kokarin miƙewa tsaye. Ya yi saurin dakatar da ita.

"Haba Maryama, to kiyi hakuri naji na yi laifi a kalamaina. Ba zan kai Ummita ba face da izninki. Kiyi hakuri, shikenan? Yanzu me kike tunanin za'a yi don sama mata nutsuwa?"

Ta sauke ajiyar zuciya.

"Tunda har shawarar da na bayar bai yi ba, toh na fi tunanin ka bayar da kudi muje da su ukun nayi musu ƴar siyayya sai kuma ita Humaira da ka riga ka san matsalarta akan maza. Ganin wannan abu da ya afku ga Ummitan ya ƙara sanyawa ta tsani al'amarinsu. Daidai da Fadeel din da muke murnar ta soma sakin jiki da shi suna ƴar hira yanzun ko muryarsa ba ta wani son ji. Tun wuri gwara a yi mata maganinsa. Na kuma fadamaka labarin wani mai magani, idan har ka amince sai na kai ta a karɓo a gani ko za'a dace."

Abba ya kurawa Mami idanu, a duniya bai taɓa ganin matar da ba ta damu da nata ba sai na wasu. Ba ruwanta da damuwar yaranta sai abin ya ci tura. Matar da ɗiyarta ke kwance a gadon asibiti amma ba ta ko zancenta, burinta ta samar da farin ciki ga yaran wasu. Kaunarta ya ƙara mamaye zuciyarsa, ya riƙo hannuwanta ya sumbata sannan ya sakarmata murmushinsa da ya san yana daga cikin abin da yake ƙara dulmiyar da ita cikin kogin sonsa. Ita kuwa sai ta ɗan kauda kai tana murmushi.

"Ina kaunarki Maryam, Allah ya yi maki albarka ya bar mu tare. Kin cikemin gurbin mace hudu a duniya. Babu abin da zan ce maki sai fatan alheri. Yanda kika ce haka za'a yi, gobe ki shirya zan baku kudi, ku fara da siyayyar, koda zuwa jibi ne kuma sai ki kai ɗiyartaki wurin mai maganin. Ina fatan hakan ya yi maki?"

Har lokacin tana murmushi ta gyaɗa mishi kai.

"Ya yi ranka ya daɗe. Fatanmu Allah ya maidowa yaranmu farin cikinsu."

Cikin jin dadi Abba ya amsa da amin amin.

***
Washegari kuwa hakan aka yi, tamkar ba Mamin da Tasleem ɗiyarta ke kwance gadon asibiti ba, tamkar kuma ba wacce ɗiyarta mace ta farko ba (Futuha) ta kawo mata ƙorafin tashin hankalin da take ciki. Daga fuskarta za ka fahimci kamar a duniya ba ta da wata aba wai ita matsala ko kuma damuwa. Ta saki ranta suka zagaye shoprite da su Humaira da Raihana. Ummita sosai kuwa ta sake ɗin kamar yanda Mamin take buƙata, su kansu sun ji dadin yadda yanayinta ya sauya. A ɓangaren Ummitan kuwa, ta tabbatar domin ta saki jiki ne aka yi duk wannan shiri hakan ya sa ba ta watsawa Mamin ƙasa a ido ba, ta daure ta yakice damuwarta ta saki jiki. A ɓangare guda shima Sahabi na nashi iyakar kokarin ganin ya faranta ran abar kaunartasa. Wannan ma ya yi tasiri kwarai a zuciyarta amma har lokacin wannan baƙar ranar ta ƙi ɓacewa a tunaninta da mafarkanta. Su ne har gidan Hajiya Lubna, sun ɗan jima tare da yaranta a ƙasa inda Mami ta haye saman kafin daga bisani ta sauko su wuce.

"Mami ba zamu leƙa Anti Tasleem ba?" Cewar Raihana. Mamin ta yi shiru. Ganin haka sai Ummita ta sa baki.

"Mami don Allah muje a duba ta."

Humaira kuwa uffan ba ta ce ba, asalima kallon shuke-shuken dake farfajiyar gidan Hajiya Lubna kawai take.

"Shikenan, muje. Yarinyar ce ta ban takaici, kina da ciki don sakarci ki tsaya wani faɗa akan kishin banza da wofi."

Su dai babu abin da suka ce. Humaira ta buɗe bayan mota ƙarama ƙirar KIA da Abba ya tsiya ta shiga. Mami ta ɗan bita da kallo sai kuma ta murmusa ba ta ce uffan ba. Ta dubi Hajiya Lubna.

"Shikenan Hajjaju, sai mun yi waya."

Ƴar dariya Hajiya Lubna ta yi.

"Toh Hajiya Mamin yara. A gaida Tasleem din ki ce mata ta sha kuruminta zan zo."

"Ai shikenan. Za ta ji."

Daga haka suka yi sallama.

***
Malamin ya yi shiru yana duban ƙasa, can kuma ya ɗago ya kalli Murja ya girgiza kai.
"Abin da kike so ba zai taɓa kasancewa ba."
Wani malolon baƙin ciki ya turnuƙe zuciyarta. Daƙyar ta haɗiyi miyau mai ɗaci ta ce.

"A yanzu kake nufi ko har a gaba? Kenan Humaira ba za ta kasu ba?"

Malamin ya yi ƴar dariya.

"Wane mutum! Inji mutuwar. Ai Hajiya Murja babu wanda ba zai mutu ba. Kuma ni da na isa na duba mutuwar wani ai da nawa zan fara dubawa. Abin nufi kina son ta mutu kada ta auri Fadeel din ko? Toh hakan ba zai taɓa yiwuwa ba."

Ji tayi wani abu mai nauyi ya tsaya a ƙahon zuciyarta. Malamin ya zubamata idanu, ya lura ba ta saduda ba don haka ya sauya zancen.

"Amma fa idan kina so za'a iya nakasata rayuwarta. Zamu iya nakasta ta gaba ɗayanta. Amma da sharaɗi, matukar aikin bai ci ba, zai dawo kanki. Kin amince?"

Ba tare da dogon tunani ba ta amsa.

"Eh na amince."

"Murja, ko za ki yi shawara?"

Ranta ya ɓaci sosai.

"Wancan karon haka ka ce min, wannan karon ma kana nema ka tauye ni da faɗin haka ko? Toh yanzu ba shawarar da zan yi, ga kudi nan ka yi duk abin da ya kamata."

Ta bude jaka ta ciro bandir na dubu ta dire mishi.

Ya yi murmushi.

"Shikenan, ni nawa aiki. Sauran ke za ki yi da kanki. Dole kina bukatar zuwa inda ita yarinyar take. Ki je ki dawo nan da kwanaki uku."

Murja ta ji kwanakin tamkar watanni a wurinta. Tana jin zuciyarta za ta iya bugawa na yanda Fadeel ke rawar ƙafa akan Humaira, kullum ya zauna da Hannatu a falon Anti to fa hirarta ne kawai.

"Babu wani aiki da za ka yimin akan Fadeel?"

"Aiki kai, ga wannan layar ki tabbatar kin saka a ƙarƙashin katifarsa, muddin ya kwana ya tashi ki ɗauke ki binne. Wannan kwallin kuma ki zizira ki tabbatar kun yi ido hudu."

Ta yi murmushi, duk da cewa ta yi abubuwa da dama ba ta yi nasara a kan Fadeel ba amma hakan ba zai sa ta karaya ba. Ta karɓa ta sa a jaka ta mishi sallama ta tafi zuciyarta sol.

*LITTAFIN NAN NA KUƊI NE. SIYA AKAN NAIRA ₦400 KI KARANTA BA TARE DA SHIGA HAKKI BA.*


*5407827015*
*FCMB*
*Farida Abdullahi*

09034973645



Misalin bakwai da mintoci ne, Fadeel ne zaune a falon Alhaji tare da Hannatu da Alhajin. Wannan damar Murja ta yi amfani da shi wajen kokarin ganin ta ƙaddamar da shirinta, sai da ta fakaici idanun su Khadija da Abdulmaleek wadanda suke kallo ta nufi ɓangaren Fadeel. Sai dai ta yi mugun mamakin jinsa a garƙame da muƙulli. Ta ciji leɓɓa don takaici kamar ta haɗiyi zuciya ta mutu haka ta ke ji, sai kuma ta tuno duk abinsa da safe yana barin mukullin ɗakin ya fice don a yi mishi gyara. Wannan ya sa ta yi murmushin mugunta ta juya tana mai kara cin alwashi.

***
Futuha na zaune tana faman cika da batsewa kamar ta fashe, Alhaji Yakubu ya shigo fuskarnan a murtuke ya zauna yana dubanta gami da jefamata ledar dake hannunsa.

"Idan har kina son mu cigaba da rayuwar farin ciki da ke, to ki gaggauta shan magungunan nan, an tabbatarmin zasu yi sanadin zubewar cikin dake jikinki. Idan kuwa har ki ka ƙi, kika dage sai kin haihu da ni, toh shakka babu baƙar rayuwar da za ki fuskanta sai kin sha mamakinsa. Sannan rashin bin umarnina zai yi sanadin da zan yi aure."

"Wallahi ba zan sha ba! Idan kuma aure ne ka yi idan ka isa! Kuma wallahi ka ji na rantse maka matukar ka ce za ka wulakantani ba zan zauna ba sai dai ka sakeni!"

Ya yi wata muguwar kyakyacewa da dariya. Ya nunata da yatsa.

"Ke Futuha, ba ki da hankali ashe? An fadamaki ni Yakubu zan saki mace? Ai babu wannan ranar a duniyata. Zaman aure da ni ya zamar maki dole. Koda bakya so kuwa sai kin zauna da ni. Na dai fadamaki, muddin rayuwarnan mai dadi da na ɗanɗana maki kina so ya ɗore, to sai kin bi umarnina. Idan kuwa kin ƙi zan auro..."

Sai kuma ya yi shiru yana jinjina kai duk a kokarinsa na shanye sirrin dake ransa. Tun su na Dubai ya yi wani irin sabo da ɗinkewa da Sa'a Ƴar Snow, kullum yana shafinta yana jifanta da likes da kuma chatting da suke yi a ɓoye. Tsantsar kalaman iskanci da ma hotunan tsiraicin da take turomasa ya yi mugun hargitsa shi, ba ya fatan ya kusanci zina amma ya sha alwashin aurenta. Ta kuma amince sannan ta ba shi lokaci ya gama cin angoncinsa kamar yanda ta buƙata. Ya fi kowa sanin ƴar tsamar dake tsakaninta da Futuha, ya tabbatar idan zancen ya fasu to fa ba za su kwashe da dadi ba hakan ya sanya shi zaɓar yin shiru.

"Ka auro wa?! Ka faɗamata ko ma wacece don ubanta ta yi kaɗan ta shigo gidannan!"

Ya mike ya watsamata harara.

"Saboda ke kika haife ni kenan? Titse ni za ki yi na faɗamaki ko? Toh sai ki yi da wani."

Yana kaiwa nan ya kama hanyar fita, aikuwa ta yi tsalle ta dire gabansa idanunta har sun kaɗa tsabar kishi da ɓacin rai, cakumar wuyan rigarsa ta yi tun ma ba ta kai ga furta ƙala ba ya cire hannu sai ji kake tas a saman fuskarta.

"Ke! Ashe iskancin naki ya kai haka? Ni kike cakumarwa wuya?! Wannan ya zama na ƙarshe idan kika ƙara mugun gangancin nan sai na nunamaki ba ki da wayo! Banza marar tarbiyya ƴar rawar Tiktok kawai! Mtsw."

Yana kai wa nan ya fice yana gyara zaman babbar rigarsa, dama dawowarsa kenan daga wurin Ƴar Snow, don dai kalamai da rungume rungume wadannan ya sha su kamar ba gobe, ita ta yi mishi rakiyar siyan magani kafin ya maida ta gida da siyayya mai yawa sannan ya dawo gidan.

Futuha ta yi kuka mai isarta tamkar ranta zai fita sai dai ta ƙudurta a zuciyarta Alhaji Yakubu bai isa ya wulakanta ta ba. Sai ta ɗauki mummunan mataki a kansa kamar yanda Mami ta ba ta shawarar ta kwaci kanta da gidanta, to kuwa za ta ƙwata ta ƙarfin tsiya. Gama tunaninta kawai ta ciri waya ta kira wata tsohuwar aminiyarta Aneesa Jafar. Matar aure ce amma tantiriyar ƴar duniya ce domin ko a rayuwarsu ta makaranta tana cikin masu neman soyayyar Sir Ibb duk kuwa da auren dake kanta. Ita din shaida ce a yanda take juya mijinta a gida hakan yasa ta yanke shawarar tuntuɓarta. Tun sadda ta yi aure ba ta ƙara nemanta ba saboda a ganinta ajinta ya fi nata, sai a yanzun da buƙatarta ta taso.
Kasancewae Aneesa ta iya barikanci, ko kusa ba ta nunamata komai ba suka gaisa hannu bibbiyu. Sai kuma Futuha ta warware mata damuwarta. Dariya Aneesa ta yi kafin ta amsa.

"Ai wannan ba matsala ba ce yar uwa, amma ki yi yanda yace. Ke banda abinki mene ciki don kin zubar da cikin wanda ya nuna ba ya son haɗa zuri'ar da ke? Kuma wallahi kika yarda kika haihu da shi to ina mai tabbatar maki nan da nan za ki lalace ki zama wata daban. Ki daurewa ranki ki zubar da cikin idan ya so ki kawo kudi mu san hanyar da zamu bi ki mallake shi, yanda ko tsinke bai isa ya tsallake ba matukar ba ki yi mishi izini ba."

Cikin sanyin jiki da kuma ɗan nutsuwar da Futuha ta samu ta ce.

"Toh Aneesa. Ni dama tsoron mutuwa nake, kada na sha na mutu naji ance masu zubar da ciki mutuwa suke yi."

"Mutuwa ai sai lokaci ya yi, nidai ina ba ki shawarar ki zubar kuma ki je ki yi planning abinki hankali kwance. Matukar dai kina so mu cimma burinmu."

Ta sauke ajiyar zuciya ta jawo ledar magungunan sannan ta ba Aneesa amsa.

"Shikenan, yanzun nan zan sha. Nagode Aneesa, zuwa gobe duk yanda ake ciki zan kiraki mu ji abinda ya dace a yi."

"Shikenan, sai na ji ki."

Daga nan suka yi sallama. Ta ƙurawa magungunan idanu, a wata farar takarda suke, ta yi shiru can kuma kamar wacce aka tsikara ta mike ta dauko gorar ruwa ta bude, ta zazzaga magungunan a hannunta ta shanye su tas sai jiran sakamako.

***
Tana kwance tana juyi yayinda yan uwanta duka ke bacci abinsu. Ta mike zaune ta yi shiru, tashin zuciya take ji sai dai ta rasa yanda za ta yi ba ta kaunar ta yi amai motsin yunƙurin ya tashe su. Zuwa lokacin ta soma shan jinin jikinta, tsoro da firgici ya soma shigarta. Bai fi kwanaki uku watan da suke ciki ya mutu ba amma har yau babu labarin ganin al'adarta. Tsoro iyaka Ummita na cikinsa. Ta kasa jurewa tashin zuciyar da take ji sai ta bude dakin ta fita da sauri zuwa falon bandaki, nan fa ta shiga kelaye amai kamar hanjin cikinta za su zubo. Duk wani kayan kwalam da ta ci a ranar sai da ta dawo da shi. Ta kammala ta wanke fuska ta gyara wurin, ta kuma ɗauro alwala ta dawo falon ta zauna. Sai kawai ta fashe da kuka mai tsuma zuciya ga wani irin mugun sanyi da ya lulluɓe ta lokaci ɗaya. Ba ta son koda tuna kalmar da take tunanin shi ya zama damuwarta balle har ta furta.

'Idan ya tabbata haka din ne ya za ki yi da Sahabi?'

Zuciyarta ta watso mata tambayar, ta rike kai sai kawai ta fashe da kuka sosai. Ba ma Sahabin kawai ba, ta ina za ta soma karɓar wannan ƙaddara na rainon cikin da ta same shi ta hanyar fyaɗe? Fyaɗen ma daga ɗan ta'adda?

Tana wannan kukan mai tsuma zuciya ba tare da sanin irin ƙarfin buɗe muryar da ta ke yi ba har sai da ta ga hasken fitila a falon an kunna saboda akwai wuta. Mami ce, kafin Mamin ta ce wani abu sai ga Humaira a gigice ta fito itama. Kusan lokaci guda suka ƙaraso gareta.

"Mene ne ya faru Ummita?"

Humaira ta tambaya jikinta har yana rawa nan da nan itama ta soma hawaye ba tare da sanin ainahin dalilin kukan yar uwarta ba.

Ummita ta rungumeta tana kuka sosai.

"Ciki Humaira, Humaira zan haifi shege."

Da karfi kuma cikin daga murya Humaira ke girgizata kamar zararriya tana fadin.

"Wa ya fadamaki kina da ciki? Karya ne! Karya ne ba ki da ciki!!"

Mami ta dago Ummita.

"Wa ya fadamaki wannan mummunan labarin? Kin ga wasu alamomi ne?"

Mamin ta fadi nata hankalin itama a mugun tashe, nan da nan cikinta ya duri ruwa. Cikin sheshsheka Ummita ta ce.

"Ma..ma.mi, amai nake ta yi."

Ajiyar zuciya Mamin ta sauke.

"Haba Ummita, amai kuma sai aka ce maki yana nuni da cewa kina da ciki kenan? Amai ai alamun cutuka ne da dama, ba lallai sai ciki ba. Lokacin al'adarki ya yi ne?"

"Eh Mami, har ya wuce."

Gaban Mami ya buga da ƙarfi, Humaira sunan Allah ta shiga ambato sakamakon ji da ta yi tamkar an zare mata wani laka na jiki. A durkushe take amma kuma jiri ne ke kwasarta. Tana ji tamkar a mafarki ake wannan diramar ba a farke ba.

"Maryama, meke faruwa ne?"

Suka juya gaba daya, Abba ne sanye fa jallabiya a tsaye a ɗan rikice, ya tako ya ƙaraso ganin Ummita na kuka ya sanya shi ƙara jin rashin nutsuwa sosai.

"Ummita, meyafaru kike kuka?"

Mami ta yi saurin share hawayen da suka zubomata, ta miƙe tsaye.

"Babu komai, ba ta jin dadi ne. Humaira ku shiga ciki. Ki kwantar da hankalinki gobe idan Allah ya kaimu zamu yi test a gani."

Bayan wucewarsu Abba wanda ya daskare a tsaye cikin wani mugun faduwar gaba ya ce.

"Maryama, meye hakan kuma? Na kasa gano bakin zaren wannan tattaunawar da tsakar dare?! Me kike son ki ce?"

Gaba daya ma Abban ya diririce ko kadan ba ya cikin nutsuwarsa.

Mami ta dafe hannunsa.

"Babu komai Abban yara, muje zan maka bayani."

Zai ƙara magana ta hana shi ta hanyar roƙonsa akan su tafi dare ne kar a ji sai kuma ya hadiye maganar ba musu ya yi gaba zuwa ɗaki ta bishi a baya bayan ta kashe fitilun falon.

Ya ji zancen tamkar saukar aradu, nan da nan ya dafe kansa.

"Innalillahi wa inna ilaihir raaji'un! Maryama wannan mummunan labarin da me ya yi kama? Tashi tashi muje asibiti yanzu a dubamin ita."

Mami cikin hawaye ta yi saurin dakatar da shi ta hanyar dafe kafarsa gami da girgiza kai.

"Aa Abban yara, kar muyi haka. Yin hakan tamkar tonuwar

5 Comments On DUKAN RUWA
avatar
daiy drop

2 years ago

Reply

hhh

avatar
daiy drop

2 years ago

Reply

sss

avatar
daiy drop

2 years ago

Reply

sss

avatar
daiy drop

2 years ago

Reply

sss

avatar
north

2 years ago

Reply

hhhhh

Please Login or Register in order to submit comment