Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

din ya aura. Ta kwantar da Mamin hankali akan Futuha fa kyakkyawa ce son kowa ƙin wanda ya rasa, ta kwantar da hankalinta komai zai tafi daidai.

Aikuwa cikin ikon Allah dai ga wani matashin ɗan chanji Alhaji Yakubu ya zo takanas ya samu Abba akan yana son aurenta. Mutumin ya jima yana ganin fuskar Futuha a Tiktok, kasancewarsa ɗan duniya, yana son mace mai irin wayewarta ya kuma jima yana bibiyarta akan ta amince ya aure ta, tana wulaƙatanshi. Tashi guda da ya ga abin da Sa'a ta yi mata ya ga dama ta samu da zai yi wuf da ita. Yana da mata ɗaya da yara uku, ya kuma tabbatarwa Abba koda Futuha ba ta son zama da matansa shi ɗin zai nema mata wani muhallin daban cikin waɗanda ya mallaka. Abba ya yaba da salon nutsuwa da ladabin da ya zo mishi da ita don haka ya ce ya je nan da kwanaki uku ya turo iyayensa. Wannan lamarin ya yiwa Yakubu daɗi sosai. Ya yi ta godiya.

Bayan tafiyarsa Abba ya yiwa Mami zancen, ta yi murna da hakan a fili musamman ganin yana da rufin asiri. Abba ya san shi don Alhaji Yakubu ba ɓoyayye ba ne, yaro ne abokin tafiyar manya. Yana da kuɗi sosai sannan akwai shi da kyauta. Ko kusa abin hannunsa bai rufe mishi idanu ba. Ya samu kyakkyawar shaida wajen jama'a da suka san shi a waje, a halayyarsa kuwa na baɗini wannan daga shi sai Mahaliccinsa sai kuwa wadanda ya buɗamusu suka sani.

Futuha fashewa ta yi da kuka sadda Abba ya yi mata zancen.

"Wallahi Abba bana sonsa, mutumin yana da son mata kuma..."

Wurgin da Abba ya kai mata da carbin dake gefensa ya sanya ta saurin yin gum da bakinta.

"Rufemin baki nace! Ke har kina da fuskar da za'a gani a aureki da ita, ban da ma shi so ba ruwansa, mutum mai mutunci da ƙima irin Yakubu mai zai yi da ƴar rawa? Macen da ba ta killace jikinta ba ta sake shi ko'ina yana yawo ana kallonta? Toh bari ki ji, muddin ni dai mahaifinki ina raye, ba ki da miji sai Yakubu. Na kuma ba shi damar turo magabatansa nan da kwanaki uku, karatu idan ya amince maki ki cigaba wannan shi ya ga zai iya, nidai ubanki ba da yawuna ba saboda ni yanzu tsoro kike ba ni, nema kike ki fi karfinmu. Wannan wayewar ta banza kuma da kika ɗaukarwa kanki, ki je can ki ƙarata da ita, Allah ya shiryeki idan ke mai ganewa ce. Tashi ki fice ki ban wuri, saura ki je ki kai ƙarata tun da ban isa da ke ba."


Yana nufin kai ƙara wurin surukarsa Anna kamar yanda ta yi a farko da ya yi batun auren har sai da Annar ta tako sashinsa da zummar lallaɓashi ya janye. Cike kuma da ba ta girma ya ce ta yi hakuri amma ba zai zuba idanu tarbiyyar yaransa su lalace ba. Ganin ba ta taɓa neman alfarma a wurinsa bai yi ba sai wannan ne ya sanya ta kama mutuncinta ta yi shiru da baki.

***
Su Humaira na ɗaki sai ganinta suka yi ta shigo tana aikin da ta saba kullum, wato aikin kuka. Humaira kukan yanzu kam ko a jikinta, ai tsuntsun da ya ja ruwa shi ruwa kan doka, ta lura hatta Tasleem itama abin ya bar sosa ranta, kowa ya fice a harkarta ya gaji da rarrashi. Tasleem dai waya take amsawa da Hamza, ganin ihun kukan Futuha ya cika dakin kawai sai ta ja guntun tsaki ta fice. Su din ma hirarsu ta tsaya, kowa ya shiga danna waya, su kansu Abba ya ja musu kunne sosai ya kuma rantse duk wacce a cikinsu ta yi irin gangancin Futuha ba zai duba komai ba zai aurar da su. Wannan ya sa bakinsu ya mutu murus.

Humaira ta bude saƙon da ya faɗo wayarta a lokacin. Ta sani, shi kadai ne zai yi mata saƙo don haka ta buɗe.

_"Ko kinsan mai hakuri ba ya taɓa karo da rashin nasara a rayuwarsa? Ki sani ni ɗin masoyi ne a gareki, ba kuma hakan zai sauya komai ba. Ma'ana, koda ace zamu shekara kina wahalar da zuciyata, Humaira ki sani, Fadeel bai fara sonki domin ya daina ba. Muddin rai ba zan fasa neman soyayyarki ba."_

Ta karanta kusan sau uku, ta rasa dalilin da yasa ba zai taɓa turo kata saƙo ta karanta sau ɗaya ba, kuma ko kadan ba ta iya goge saƙonninsa. Abin da yake ba ta mamaki shi ne, ta ga yana hawa whatapp amma ko sau daya bai taɓa yunkurin yi mata magana ta can ba. Kira ma da ya ga ba ta ɗagawa ya bari. Sai dai akwai lambar da take zargin ko shi ke kiranta da shi. Za a kira ta ɗaga amma ba za a ce komai ba sai dai ta yi ta sallama tana sababin anƙi magana ƙarshe kuma ta ji ɗif an katse kiran. Wannan abu na ba ta mamaki, tana kuma zargin Fadeel ne. Ta yi shiru tana so ta hasaso dalilin wannan ƙiyayya da ta ke yiwa Fadeel amma duk iyakar tunaninta ta kasa, karshe ta ja guntun tsaki. Ta bar shi akan kawai ita ba ta kaunar soyayya, ba ta kaunar kowace mu'amala da za ta haɗata da namiji. Da wannan ta watsar da tunaninta.

***
BAYAN SATI UKU...

Garin aka tashi da shirye-shiryen shiga wata mai alfarma wato Ramadan, wanda ake kyautata zaton ganin wata a ranar ko washegari hakan yasa Mami suka yi dogon list na cefane ita da Humaira. Mamin ta dube ta bayan sun kammala tana murmushi.

"Wannan azumin a daɗinmu, girkinki zamu ci. Kin ga kina yi idan kin shirya komai sai ki yi hoto, Raihana ta buɗemaki account a instagram kina ɗorawa da sunan tallah, idan Allah ya taimaka zuwa sallah sai mu samu odar girkin sallah ko su samosa da sauransu. Da kaɗan-kaɗan kuma ki ji an soma neman ki yi na biki. Ina mai tabbatar maki da wannan iya girkin naki za ki samu alheri mai yawa da zai yi maki amfani har na kusa da ke."

Humaira cike da jin dadi ta hau murmushinta mai bayyana wushiryarta ya kara fiddo da usulin kyanta. Ta ma kasa magana don murna. Mami ta yi dariya.

"Allah ya kyauta, wannan dariyar duk ta murna ce? Tashi dai maza ki je kar yamma ta kawo kai. Kinga siyayyar da yawa."

"Toh Mami." Ta mike ta gyara zaman mayafin doguwar abayar dake jikinta ruwan madara mai dark brown din mayafi. Ƙafarta sanye da safe ba ka ganin komai sai tafin hannunta sai kuwa fuskarta da ta shafa hoda ta zizira kwalli. Ta yi kyau tsaf duk kuwa da cewa ba kwalliya ta yi ba. Irin matan nan ne wadanda ko ba kwalliya su na kyau. Har ta fice a ɗakin Mamin na bin ta da kallo tana murmushin da ta ba kanta sanin ma'anarsa.

Ta yi tafiya daga gidan zuwa titi na ɗan mintuna sannan ta fito babban titi. Garin akwai rana sosai duk kuwa da cewar an yi sallar azahar amma hakan bai sa ya ɗan yi sanyi ba. Dakyar ta samu abin hawa ta shiga. Sun yi tafiya mai ɗan tazara sun tsaya a daidai junction din sabon titi wayarta ta ɗau ƙara. Ta ji gabanta ya fadi don tsoro, Ummita ta ce mata ana satar waya a ɗan sahu wannan yasa kodayaushe idan za ta fita ta ke sanya ta a vibration amma yau sauri ya mantar da ita. Ta ɗan kalli mata biyun da ke gefenta sai ta ga ba su yi mata kama da ɓarayi ba don haka ta ciro ta da sauri, ganin sabuwar lamba ya sa ta ɗagawa da sallama. Madadin ta ji shiru an yi kamar yanda aka saba yi mata, sai ta ji wannan karon an amsa. Duk da ta ɗau muryar hakan bai sa ta tambayar "Wa ke magana." ba.

"Wallahi ina sonki."
Ya furta cike da kasala, abinda bai taɓa faruwa ne ba gareta ta afku a sannan. Ji ta yi tsikar jikinta ya tashi, ta ji lebbanta sun mata nauyi ta kasa buɗe baki balle ta rufe shi da faɗan da ta saba. Sai kawai ta zame wayar daga kunnenta ta katse kiran. Daidai lokacin da aka ba su hannu, juyawar da za ta yi suka yi ido hudu da shi, kallonta ya ke bilhakki har sai da na bayansa suka cikamasa kunne da hon, ta yi saurin kauda kanta. Kallon ya dawo mata da sabuwar tsanarsa, ta ji ranta ya ɓaci, ta kuma rasa dalili. Ba ta kara juyawa ba har suka yi mishi nisa, ba ta kuma san inda shi ya yi ba. Ƙarar shigowar saƙo wayarta ya sanya ta buɗewa.

_"Kin min kyau. Ina roƙon Allah ya nunamin ranar da Fadeel zai mulki zuciyarki gaba ɗaya. Ya zame maki haske maganin kowane duhu. Ameen."_

Ta yi saurin maimaitawa sau ɗaya ta jefa cikin jakarta. Ana zuwa kasuwar rimi ta sauka bayan ta fidda facemask dinta a jaka ta rufe hanci da baki. Haka ta dinga kutsawa ta kammala siyayyar Mami, ba ita ta bar kasuwarnan ba sai yamma lis duk ta jiga ta. Washegari ma haka ta kara tashi ta fita zuwa haɗo kayan kwalam na yin Snacks iri-iri. Hatta da kayayyakin haɗin salad sai da ta siyo. Wannan karon dai Abba ya saki bakin aljihu domin shi dai idan har watan azumi ne yakan yi bakin kokarinsa wajen wadata gidansa, hakanan da sallah. Ya kuma ce lallai lallai su Tasleem da Futuha su dinga shiga kicin su koyi girki wajen Humaira. Rana ɗaya idan suka yi fashi, za su yi karo da fushinsa.

***
Murja ce durkushe gaban Alhaji, ya kalleta dakyau jin ta kasa magana. Da murmushi dauke a saman fuskarsa ya ce.
"Kin yi shiru Murjanatu, kiyi magana."

Ta ga dai shirunta zai sa ta cuci kanta don haka ta muskuta ta soma cewa.
"Dama Yaya Fadeel nake so a auramin."
Jin haka kan Alhaji ya ɗaure, ya yi sakato yana kallonta.

*LITTAFIN NAN NA KUƊI NE. SIYA AKAN NAIRA ₦400 KI KARANTA BA TARE DA SHIGA HAKKI BA.*


*5407827015*
*FCMB*
*Farida Abdullahi*

09034973645


"Shi Fadeel din ya sani?"

Ta girgiza kai tana kara sunne wa kamar mai jin kunya.
Alhaji ya yi shiru sai kuma ya ce.

"Shikenan, ni dai b na yiwa yarana dole balle kuma namiji. Zamu yi maganar da Fadeel duk amsar da ya bayar za ki ji daga Antinki."

Ji ta yi kamar Alhajin ya harba mata mashi a ƙahon zuciya, da irin wannan amsar ai gwara kawai ya ce mata aa kansa tsaye. Abu ne da ya sani kamar yanda ta sani, zai wahala Fadeel ya amince da shi, ta yi zaton yanda Alhajin ke yabawa da nutsuwarta zai ce ya amince ya zaɓawa Fadeel din ita matsayin matarsa. Haka ta mike ta fice gwuiwa a sake. Bayan fitarta Alhaji ya yi shiru, ta ina zai soma ɓata ran ɗannasa wanda a baya ya sha baƙar wuya a dalilinsa da mahaifiyar Fu'ad? Ya musguna mishi, bai duba maraicinsa ba na rashin uwa ya yi watsi da shi. Karshe don kansa da ya gaji bayan ya yi hankali ya fice ya koma dangin mahaifiyarsa a can ƙasar Kamaru. Sai kuma bayan da ya kwashe dogon shekaru har kusan biyar ya dawo yanzun kuma ya hargitsa shi komai ya ƙara hargitse mai? Yaransa biyar kacal a duniya, Fadeel ne babba sai Fu'ad sai kuwa ƙanwar Fadeel uwa ɗaya uba ɗaya Hannatu dake aure a can Adamawa, sai yaran Anti Amarya biyu, Khadija da Abdulmaleek. Shi hakanan Allah ya yi shi ba mai yawan haihuwa ba, matansa babu me yin tsarin iyali.
  A ƙarshe dai ya yanke zai mishi maganar auren don shi kansa yana damuwa kwarai akan zaman yaran haka(wato Ibb da Fadeel) ba tare da iyali ba. Har ga ƙaninsu Fu'ad ya yi auren ya bar su.

***
  Fadeel ya nutsu a gaban mahaifinsa, bai katse shi ba har ya kai aya. Sai a lokacin ya yi magana.

  "Na ji bayananka Alhaji, ina neman addu'arka musamman a wannan wata mai alfarma da za mu shiga akan neman zaɓin Allah. Sai dai kuma ba na kaunar Murja, ba na sonta matsayin matar aure. Don Allah abar zancenta."

Jinjina kai Alhaji ya yi, ya ɗan murmusa kaɗan.

"Shikenan, Allah ya sa hakan ya fi alheri. In sha Allahu zan tayaku kai da ɗan uwanka. Ya kamata ku maida hankali."

Fadeel ya amsa a ladabce. Daga nan suka rufe wannan babin suka cigaba da tattaunawa akan abubuwan alheri na sadaka da neman lada da Alhaji ke yi duk shekara idan watan azumi ya kama. Kamar yin kunu da abincin sadaka, kyautar butoci, ruwa, dabino da ma sauransu a masallatai., daukar nauyin tafsir, sai kuwa idan sallah ta matso ya yiwa ƴan uwansa marasa ƙarfi da marayu da dama sutura. Da wannan suka rufe babin Murja da ma batun aure. Anti Amarya dake laɓe a bayan labulen ɗakin Alhaji, ta ji ciwon cewa da Fadeel ya yi ba ya son ƙanwarta. Ta yi ƙwafa, ai idan ya san wata bai san wata ba.

***
A daren ranar Lahadi gaba ɗaya garin aka dau murnar ganin watan Ramadan. Lokacin Sahur gaba ɗaya gidan suka tashi aka yi idan ka cire Tasleem wacce ba ta da sallah.
  Lokacin shan ruwa na kawo kai, Humaira da Ummita har Raihana ana kicin ana faman kai da kawowa, Tasleem ba ta shiga ba don langaɓewa ta yi wai mararta na ciwo. Ita kuwa Futuha tana tsaye kawai tana yatsine-yatsine da gwatsale wani abun idan Humaira ta yi wai ba haka ake yi ba. Ita dai ba ta tanka mata ba albarkacin watan da suke ciki na ibada. Sai da suka kammala komai sannan suka jera a tsakar falon bayan shimfiɗa ƙatuwar ledar cin abinci. Na Abba kuwa can ɓangarensa suka kai aka shirya komai. Itama Anna, Raihana ta kai mata komai ta bar ta tare da su Muhsin don a duniya Anna ba ta fiye son zuwa falon Mamin ba sai da kwakkwarar dalili.

  Sai a sannan Tasleem ta shiga kicin din ta ɗibi abinci ta dawo falon tana ci ta a yatsine fuska wai gishiri ya yi yawa. Ba ta ko jin nauyin yan uwanta maza dake zaune a falon su na taɓa hira. Haka aka sha ruwa aka yi zaman cin abinci bayan kowa ya yi sallah. Mazan suka dinga santin girkin amma da zarar sun yi ido da Humaira su watsa mata harara idan ka cire Ƙasim wanda tun wata rana da ya shiga ɗakin Mami zai ɗau kuɗi ta gan shi kuma ta rufamasa asiri ba ta faɗawa kowa ba, tun a ranar ya soma ganin ta da ƙima a idanunsa. Ya ke kuma jin kunyarta. Yassar kuwa faɗi yake ai ba basirarta ba ce, koyamata aka yi. Futuha  ta ja tsaki.
  "Wai kai kana wani zance, ina abin yake? Ni ba abin da ya kara ɓatan rai wai sai da Abba ya ce wani mu shiga kicin mu koyi girki wajenta. Don Allah ku ji wani abu."

Dariya suka yi idan ka cire Ƙasim dake faman cin sandwich da ya ji kaza da su cheese yana santi.

"So ya ke ki je ki yiwa Alhaji Yakubu kar a ji kunya mana."

Jin an ambaci Alhaji Yakubu nan da nan ta ɗaure fuska. A duniya yanzu babu wanda ta tsana irinsa, mutum dai kamar maye. Abu daya da ta sani shi ne, daga maganar zuwa kamawar watan da suke ciki na azumi ya yi mata ɓarin kuɗi sama da dubu ɗari, wannan kaɗai shi ne ya burgeta musamman ganin cewa Tasleem ba  ta samu hakan ba. Rabu dai da Hamza akwai kulawa a baki amma babu ko asi da ya taɓa kawomata. Wannan abu na yiwa Tasleem ciwo kuma yana fasawa Futuha kai, tana son ta ga ba ta son mutum yana bibiyarta kamar jela.

"Kar ka sa na tashi, har wani tsami na ji abincin ya soma yimin a baki."

Yassar da Dawud suka kwashe da dariya. Tasleem ta yamutse fuska ta ce.

"Gulma, a bakya so kike kwace ƴan chanjinsa. Fuska biyu."

Futuha ta dire fork din hannunta da ta ke cin haɗin salad da shi, tun ba ta kai ga haɗiyar wanda ta ke tauna ba ta soma balbaleta da masifa.

"An kwata ɗin, ina ce albarkacin kaza dai ƙadangare ke shan ruwan kasko? Ko kin manta abin da Mami ta ce akan amfanin kudin?"

Tasleem ta hadiye zancenta, ta tuna Mamin cewa ta yi Futuhar ta saki jiki da Alhajin ta dinga nuna masa kulawar koda iyaka baki ne, muddin dai zai bayar da kuɗin ba za a ji kunya a auren ba tunda ba su da tabbacin samun yanda ake so daga wajen Abba. Wato na siyayyar kayan ɗaki da sauransu. Maganar Futuha ta katse ta.

"Kuma ko banza gwara Yakubu tun daga nan an san zai iya riƙe mata biyu, wani kuwa da ko ɗayar ma ya kasa nunawa zai iya sai afkin waya da ƙalƙalar  turanci kamar tsatson sarauniyar Ingila." Suka kwashe da dariya. Ran Tasleem ta kai kololuwa a ɓaci, su Humaira na zaune su dai su na shan ruwa abin su daga gefe suna kallon ikon Allah. Raihana ce ta tofa.

"Kai Adda Futuha, ramuwar gayya fa akwai zafi kar ki kai Adda Tasleem bango."

Aikuwa tana cewa haka kamar ta kara zuga Tasleem sai kuwa ta yi caraf ta ba ta amsa.

"Kyale ta Raihana, ai mugun abu ya ƙare a gindinta tunda ko ba komai nidai auren soyayya zan yi, Hamza gani ya yi yana so a mutunce. Wata kuwa sai bayan an jefe ta da kalmar karuwanci, ƴar rawar Tiktok sannan ta yi na'am da Alhaji mai zubin moɗa."

Lallai, baki idan ya san me zai faɗi bai san me za a mayar masa ba. Aikuwa Futuha ta yi kukan kura har ta na cilli da bowl din salad dake saman cinyarta zuwa ƙasa, ta yi kan Tasleem da kokawa. Itama Tasleem kasancewar a wuya ta ke kawai sai ta biye mata suka hau jibgar juna. Dakyar Yassar ya shiga tsakaninsu gudun kar Abba ya ji.

Tasleem na  huci ta ce.

"Ni kuɗi bai dameni ba tunda zan auri wanda yake sona nake sonsa. Arzikin dai ai na Allah ne, kuma ko makaho ya shafa ya san Hamza ba talaka ba ne. Alhamdulillah ba a taɓa yimin wannan mugun ƙazafin na karuwanci  ba."

"Shegiya! Ni kike kira karuwa, ai gwara ni sharri ne, ke kuwa sau nawa kina yiwa Mami sata? Ko ranar da aka yi na Humaira, ina ce ke ce kika kawo shawarar a yi mata wannan sharrin don ki wanke kanki. Ke ce kika ɗauki kuɗaɗen, ganin Yassar ya kama ki sai aka shiryawa Humaira tuggu don kar Mami ta zarge mu."

Humaira da ke shirin kai kofin kunu bakinta ta yi saurin ajiyewa, ashe ma ɓarayin biyu ne? Ba ma wannan kadai ba sai ganin yau dai Allah ya karɓi addu'arta gaskiya ta yi halinta. Tasleem gaba ɗaya ta yi wuri-wuri da idanu, ko kaɗan ba ta zaci Futuhar za ta yi mata wannan tonon sililin ba. Yassar ya dakamusu tsawa amma kasancewar girma ya faɗi ko a jikinsu, sai dai tsawar farko daga Abba ya sanya gaba daya suka yi tsit. Ashe yana tsaye a bakin ƙofar falon tun sadda suka soma kokawa, Mami na biye da shi a baya. Gaba ɗaya hankalinta a tashe, wato dai ya allura ta tono garma? Ba wannan ba ma, babu uwar da za ta so ganin yaranta kansu a rabe. Gaba daya falon ya yi tsit su Tasleem sai rarraba idanu ake.

Ya shigo tsakiyar falon ya wanke su ganin ba su duba girman watan da ake ciki ba na ibada su na yi mishi faɗa a falo. Daga nan ya nemi sanin abin da ya faru da Humaira a baya, nan fa Raihana kamar wacce ake tsikara ta ba shi labari. Humaira kanta a ƙasa tana hawayen farin ciki, wato da Allah ya tashi wanke ta sai ya sa Abba da kansa ya ji zancen ba iyaka Mami ba. A ranar su Yassar da Futuha sun ga tashin hankalin Abba, ya kuma ci alwashin saɓawa duk wanda ya ƙara jarraba musgunawa Humaira. Hatta da Mami mai kokari akan Humaira a ranar har da ita ya haɗa ya ce ai laifinta ne da ba ta tsawatar musu shiyasa suka samu sake. Haka Abba ya yi faɗan da ba su zata ba har Humairar daga nan ya fice daga falon. Mami ta bi yaran da kallo sai kawai ta juya ta bi bayan mijinta. Humaira ta mike ta kalle su fuskarta dauke da murmushi ta juya zuwa ɗaki.  Ranar jin ta take ranta babu ko ɗigon bakin ciki sai dai ba ta ji dadin dorawa Mami laifin su Yassar da Abba ya yi ba. Amma ta yi mamakin Abban, a baya tana tunanin ko sonta ne ya daina, ko ya manta ma da ita a lissafin ƴan gidan sai kuma abin da ya yi yau ɗin ta fahimci tana nan daram a zuciyarsa kawai dai ba shi da lokacin kansa balle na hira saboda yanayin kasuwa.  Banɗaki ta shige ta ɗora alwala ta dawo ta zura hijabinta ta shiga lazimi. Ta na nan zaune ta yi shiru, wani lokaci can take tunowa ita da Dada musamman a wata irin na azumi yanda suke zama bayan shan ruwa a yi hira kafin lokacin sallar isha'i.
  Ƙarar wayarta ya katse mata tunani, ta sa hannu ta ɗauka. Fadeel, shi ne  sunan da ya bayyana saman screen din, haka Raihana ta adana mata lambar ba da son rai ba. Albarkacin watan da suke ciki ya ci ta ɗaga da sallama. Ya amsa daga can ransa fari sol.
   "Ina fatan kin sha ruwa lafiya?"

"Lafiya kalau." Ta amsa a taƙaice. Shiru ya ɗan biyo baya, ya rasa me zai ce yana gudun ya yi furucin da zai sa ta katse wayar gaba ɗaya. Ya kasa hakuri balle ya danne don haka ya ce.

"Sai yaushe Humaira? Sai yaushe za ki samarwa wannan ɗan marayan gurbi a zuciyarki? Ba zan gaji da roƙo ba, ki ba ni dama Humaira. Wai kin san so kuwa?"

Nan da nan ta ji ya har ta soma harzuƙa a sanadin kalmar so da ya ambata, cike da gatse ta ce.

"Sai nan da shekara."

"Kin yi alƙawari nan da shekarar za ki amince ki yarjemin da batun aure?"

Ta dauki maganar a zancen banza, ta sani babu wahalallen da zai yi dakon shekara ya auri budurwar da ba ta ko son zancen auren balle auren. Don haka babu dogon tunani ta amsa.

"Eh, na yi muddin za ka rabu da kirana ka bar takuramin."

Shiru na wasu lokutan sai kuma ya sauke nannauyan ajiyar zuciya.

"Za ki same ni da bin umarninki, amma kiyi hakuri koda saƙo na dinga aikomaki ta waya. Ke kuma ki daure ko da sallama ki amsamin domin na san kina sane da ni."

"Naji."
Ta amsa gabanta na faɗuwa ba tare da ta san dalili ba, ta ji zufa ta keto mata. Tsanarsa ta ke ji yayinda a wani gefe can a ƙasan ranta ta ke jin wani abu da ba ta tantance ba.

"Na bar ki lafiya, ki yi hakuri na adana dukkan wayoyinmu, abin nufi nayi recording tun daga farkon wayarmu har na yau. Hakan kan ɗebemin kewa wasu lokutan idan son jin muryarki ya ci ƙarfin kwakwalwata. Ki dage da addu'a a wannan wata mai alfarma. Ina roƙon Allah ya yi maki zaɓin abokin rayuwa nagari, koda ba Fadeel ba."

Yana kaiwa nan bai jira cewarta ba ya katse kiran. Ta yi ƙuri tana duban wayar, hakan na nufin wayar ƙarshe ce tsakaninsu sai nan da shekara? Ta taɓe baki, ta sani cewa ta ba shi aiki mai wahala. Kuma ba zai ma iya shekara yana wahala a kanta ba. Watakila ma kafin sannan ya yi aurensa. Ta watsar da tunani ta yi jifa da wayar ta mike jin an soma kiraye-kirayen sallar isha'i.

***
Anna ce ke yiwa Mami faɗa kamar ta ari baki.

"Kin bari miji ya rainaki ya raina uwarki, dama tun akan batun auren Futuha na san cewa Isuhu ya sauya daga

5 Comments On DUKAN RUWA
avatar
daiy drop

2 years ago

Reply

hhh

avatar
daiy drop

2 years ago

Reply

sss

avatar
daiy drop

2 years ago

Reply

sss

avatar
daiy drop

2 years ago

Reply

sss

avatar
north

2 years ago

Reply

hhhhh

Please Login or Register in order to submit comment