Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

adaidaita sahu Gwaggo ke tambayata nace ta kwantar da hankalinta babu matsala, ajiyar zuciya ta sauke tana godewa Allah....har kofar gida nace da direban ya kai mu sai cewa tayi ita ya sauke ta a bakin hanya domin tana so ta shiga gidan Uwale su gaisa.

Nace."Gwaggo me zakiji kiyi a gidan Uwale da rana gatse-gatse haka." d'an 'bata fuska tayi tace."Zanje ne mu tattauna al'amuran da suka shafe mu Sa'ida kin san abokin kuka shi ake fad'awa mutuwa."

Idanuwa na suka kawo ruwa nace."Wallahi Gwaggo kika kuskura kika fad'awa Uwale abinda yake faruwa kin kashe kanki domin dai ni nasan Uwale ba zata ta'ba barin maganar nan a cikin ranta ba sai ta fad'awa wani kinga daga haka shikkenan labarin abinda ya faru ya bazu a duniya ko ya sani."

Shuru tayi tana nazari tace."Sa'ida Uwale tana da amana kuma mun jima muna aminta nasan zata ri'ke min amanata.

Nace."Ni dai dan Allah dan Annabi kada kije gidan matar nan wallahi bata da kirki ko kad'an yanda take kawo miki gulmar mutane haka kema zata kai gulmarki gurin wasu.


Tace."To naji dan Allah maganar ta isa haka na fasa zuwa shikkenan ko."

Na kalli direban da fad'in "Shiga damu cikin layin ka ajiye mu a kofar gida.
Da sauri yace." To hajiya.


Koda muka shiga gidan shuru babu motsin kowa kofar gurin Ummatu a rufe da kwado Gwaggo tace."Sarkin yawo kenan wato har ta kulle kofa ta fita."

Nace."Kika sani ko wani uzirin ne ya fita da ita." tace."babu wani uziri ta tafi yawon malamai ne."

Ashe hakane Ummatu bayan fitarsu gwaggo daga gidan itama sai ta shirya a gurguje ta tafi gurin malamin da suke zuwa gurinsa yana musu duba tana kuka duk ta sheda masa abinda yake faruwa.


Malam Sammani ya jima yana zane-zane kafin ya dago kansa ya kalleta da fadin"Rabi yaron nan naki abinda ya aikata gaskiya ne ba sharri akayi masa ba kamar yanda kike zargi! kuma na duba na gani cewa lallai akwai ibtila'in da zai sameshi a cikin 'yan kwanakin nan amma kuma akwai wani tauraro da yake haska shi watakila nan gaba akwai wata daukaka da zai samu sannan maganar surukar ki sai dai kiyi hakuri domin 'kwan'kwaman! da suke kanta sunfi karfin ki itama sunfi 'karfin ta iyayen aljanu ne a jikinta dole kiyi hakuri da duk abinda za tayi miki sai dai akwai wani taimako da zanyi miki akanta zan gwada daure mata baki mu gani idan zai yuwu."


Ummatu ta sharce gumin goshinta hankali a tashe tace."Malam Sammani dan Allah ka taimaka min akan yaron nan hankalina ya tashi da jin abinda kace yayi nisa da gari bayan haka kuma ga ibtila'in da zai hadu dashi ka taimaka min kayi aikin da zai sanya ya dawo gida babu shiri.


Malam Sammani yayi zane-zane a karo na biyu ya duba yaga abinda Allah ya haska masa tabbas duk abinda ya gani a dubansa zai faru amma bari kawai ya sanja mata magana domun ya kar'bi kud'inta ya biya bukatarsa.


"Shikkenan Rabi za'ayi miki kokari akan bukatarki amma kema zaki bayar da sadaka mai auki.''

Tace." To kamar nawa ne abin sadakar."? yace."Dubu bakwai zaki bayar ya isa." jim tayi tana nazari kafin tace."Malam a yanzu dai wallahi bani da dubu bakwai bani da dalilinta amma ina da kayan kudi a gida insha Allahu gobe zanzo maka da kudin sai ka fara gudanar da aikin."


Yace."To babu damuwa insha Allahu zan ajiye aikin kowa na durfafi naki sabida ni kaina al'amarin ya firgita ni amma babu komai za dage da addua muyi masa kiranye ya dawo gida babu shiri itama surukar taki aiki mai kyau zanyi akanta.


Ummatu ta dinga zabga masa godiya kafin tayi masa sallama ta tafi gida .

*Shashashar Uwa kawai a maimakon ta gyara kuskuranta ta sake tafka wani*


Kafin ta shiga gida sai da ta tsaya gidan Lantana Dillaliyi tayi mata bayani kancewa idan tana son siyan katifar gado tazo ta gani.

Lantana ta kalleta da mamaki a tare da ita tace."Ke kuwa Rabi me yayi miki zafi zaki siyar da katifar gadon ki shin rashin ci ko rashin sha ne ya janyo haka."?


Ummatu a sanyaye tace."Ko d'aya Lantana wata 'yar matsala ce dani wallahi sabida haka nazo nayi miki tallah idan kina so kawai muje ki gani bana san doguwar magana."


Lantana ta yafa mahaifinta da fad'in "To shikkenan muje naga katifar." suka fito daga gidan a tare.


Muna zaune nida Gwaggo a tsakar gida muna hira gwaggo na gyara wake za tayi mana alala Ummatu da Lantana suka shigo.....Lantana cikin mutunci ta tsaya suka gaisa da Gwaggo ita kuwa Ummatu ko kallonmu ba tayi ba ta bude gurinta ta shiga Lantana tabi bayanta.


Gwaggo da bakinta baya shuru tace."Sa'ida mai Ummatu zata siyar ta kawo dillaliya gidan nan."?

Nace."Gwaggo dan Allah ki daina shiga abinda babu ruwan ki kiyi shuru da bakin ki shi yafi miki alkairi."


Shuru tayi bata sake cewa komai ba sai dai sa'i da lokaci takan daga kai ta kalli kofar Ummatun nasan jira take su fito.


"To shikkenan Lantana sai ki aiko yaro da akori kura ya daukar miki na siyar miki akan dubu ashirin da biyar din." Ummatu ce ke wannan maganar a lokacin da suke fitowa daga gurin nata.


Lantana tace."To shikkenan yanzu yanzu ina komawa gida zan turo a dauka tare da kudin naki." Ummatu tace."To ina saurare."


Lantana ta kalli Gwaggo da fad'in "Gwaggo Allah ya bamu alkairi ni na tafi." Gwaggo tace."To ki gai da gida." Lantana na fita Ummatu da sauri ta juya zata bar gurin.


"Rabi." Gwaggo ta dakatar da ita ta hanyar kiran sunanta. Fuska a murtuke ta juyo tana amsawa Gwaggo tace."Me zaki siyar ne."? Da sauri na kalleta ina jin masifar takaicin abinda take ina ruwanta Ummatu ko kanta da kanta zata siyar ido ne nata.



"Gwaggo ba abinda ya shafeki bane'' Ummatu ta mayar mata da amsa daidai da tambayarta. Gwaggo taji ciwo sosai tace." Duk abinda zaki siyar kije kiyi ta siyarwa ni dai nasan ba za'a zagi Ibrahim ba ace ya gaza a gidansa wannan ai cin mutunci ne rana gatse-gatse kije ki dauko dillaliya ta shigo mana gida me aka gaza dayi miki a gidan."?

Itama cikin rashin tausasa harshe tace." Ai dama ni bance Ibrahim ya gaza a gidansa ba tunda daidai gwargwado yana kawo abinci amma kuma suttura sai shekara shekara sannan ni na dauko Lantana ne domin tazo ta siyi katifar gadona saboda inada bukatar kudi."
Tana gama maganarta ta kad'a kanta ta shige gurinta.

Gwaggo ta bude bakinta cike da mamaki tana kallona.

Nace"Ai dama baki in yasan abinda zai fada bai san abinda za'a mayar masa ba tun farko sai da nace kiyi shuru kika k'i ai gashinan kin janyowa kanki cin mutunci.'"

Tace."Sa'ida ni ba wannan ne ya dame ni ba saboda cin mutuncin Rabi kuma wane iri ne ban sani ba ko ba kiji abinda tace ba wai zata siyar da katifar gadonta to a 'ina Ibrahim zai dinga kwanciya."?


Nace."Gwaggo babu ruwanki katifa dai ta Ummatu ce baki isa ki hana ta siyarwa ba saboda haka kiyi shuru da bakinki shi yafi miki alkairi Kawu kuma insha Allahu ba zai rasa gurin kwanciya ba ni nayi alkawarin siya masa katifa yasa a dakinsa shikkenan magana ta mutu."

Girgiza kanta tayi da fad'in "Lallai Rabi tayi nisa ko da yake ai nasan idan ta kar'bi kudin katifar gurin malamai zata kai asararriya kawai."

Shuru nayi ban tanka mata ba saboda bana so maganar tayi tsayi da dai naji taki tayi shuru sai na mike na shige daki na kwanta ina jira ta gama mana alalan nasha magani bacci mai nauyi ne ya dauke ni.

Gwaggo kuwa har akazo ka dauki katifar ba ta daina surutai ba tamkar ma wacce ake ingizawa Lantana da Ummatu sun sha habaici amma sai akayi sa'a cikinsu babu wacce ta tanka mata Lantana ta tafi da katifa ita kuma Ummatu ta shige gurinta da kudinta a hannu



****
*BAYAN SATI DAYA*
Khalid ya dan samu nutsuwa a gidansu Salmanu sai dai baya sakewa sosai a unguwar gudun kada yaga idon sani kullum yana dakin Salmanu a kwance yana shawarwari da zuciyarsa.


Salmanu ya shigo dakin da fad'in "Khalid ka tashi ga shawara nazo mana da ita."

Zaune ya miqe yana kallonsa da fadin" Nima kwanciyar nan da nayi shawarwari nake da zuciyata.

Salmanu yace."Legos zamu tattara mu tafi akwai wata 'kungiyar 'yan ball ta 'yan kano mai taken kano Pillas inaso muje mu fara gudanar da harkokinmu na ball a can Khalid ka iya buga 'kwallo jikina na bani kana da abinci a harkar.


'Karamin tsaki yaja yace."Wallahi na dauka zaka ce akawai company da yake bukatar irinmu a legos din wace irin ball kuma Salmanu mu fuskanci abinda yake gabanmu ina ganin tunda aikin ya'ki samuwa anan me zai hana mu tafi da takardun mu can mu gwada mu gani."


Salmanu yace."Eh dama haka za'ayi Khalid ai ba zamu dogara da abu guda ba idan aikin ya'ki samuwa ba sai mu mayar da hankalinmu gurin harkar k'wallo ba ko ya kaga ni."

Khalid yace."Salmanu nifa a halin yanzu aikin da zai ri'ke ni nake nema bana so nayi ta zama da girmana wani na dawainiya dani 'Kwallo tana kawo kudi amma sai mutum yana da hanya a harkar sannan duniya zata san dashi har ya samu wani abu."


Salmanu yace."Khalid ka kasa gane maganata dama ai ba wai zamu zauna a guri daya bane idan munje zamu dinga buge-buge nufi na duk inda ta fad'i daidai ne."

Ajiyar zuciya ya sauke yace."To shikkenan Salmanu amma dai akwai guziri mai yawa a gurinka ko dan ni ba wasu kudi masu yawa gare ni ba.


Salmanu yace."Babu damuwa insha Allahu zan tambayi kanin mahaifina zai taimaka min sannan Mamana ma zata bani goyon baya kuma zata taimaka mana.

Yace."To shikkenan Allah yasa muje a sa'a." Salmanu ya amsa da ameeen tare da fadin"Khalid ya kamata ka kunna wayarka ka kira gidanku ka shedawa mahaifinka yasa maka albarka ka kuma nemi gafararsa.

Yace."Salmanu wallahi tuntuni nake wannan tunanin amma na rasa ta ina zan fara ina jin kunyar abinda na aikata.

Salmanu yace."Daurewa kawai za kayi ita qaddara ai ba'a guje mata zuwa yanzu dai nasan zuciyoyinsu sunyi sanyi sai ka tausasa harshe gurin neman afuwarsu mussaman ita wacce ka 'batawa."


Shuru yayi yana me sunkuyar da kansa, Salmanu yace.''Bari na shiga gida na dauko mana abinci." Bayan fitar Salmanu daga dakin Khalid ya janyo jakarsa ya bude a nutse ya dauko wayarsa ya kunna kai tsaye number auntyn nasa ya lalubo ya shiga gurin kira.


Lokacin muna hanyar dawowa gida ni da 'kawata Hauwwa kiran ya shigo waya ta gabadaya hankalina ya dauke gurin hirar da muke shi yasa ban duba mai kiran ba na daga tare da sa wayar a kunne na.


A sanyaye naji maganarsa...."Auntyna barka da rana." Gabana ya yanke ya fad'i wayar ta kusa su'bcewa daga hannuna.....shuru nayi masa yace."Ina fatan kin warware ko."? nayi shuru ban tanka masa ba yayi d'an murmushi da fad'in "Kiyi hakuri sharrin shed'an ne ki gafarce ni dan Allah."

Ajiyar zuciya na sauke na kashe wayar na ajiye gabadaya yanayi na ya sanja.

Hauwwa na driving ta kalleni da fad'in "Kawata ina fata dai lafiya." da sauri nace"Lafiya mai kika gani."?

Tana 'kokarin magana ya sake kira kamar kada na dauka sai kawai na yanke shawarar dagawa sabida kada ta zargi wani abu.


Zazzafar ajiyar zuciyarsa naji a cikin kunnena kafin yace."Ya maganar wacan 'katon mutumin mai k'aton tumbi." Yana nufin Alhaji Nura. Nace."Khalid kada ka sake kiran waya ta kaji ko ba kaji ba."?

Jin sanyayyar muryarta yasa shi sake sauke ajiyar zuciya ya lumshe idonsa yana sake gyara kwanciya 'kasa-'kasa yace."Aunty Sa'ida idan kin janye maganar Alhaji Nura zan dawo gida idan kuma baki janye ba to ina mai tabbatar miki da cewa sai dai kuyi hakuri dani domin zanyi nisa kuma ba zan dawo ba.''

Nace."Khalid ka tafi 'karshen duniya kaji ko ba abinda ya dame ni bane aurena da Alhaji Nura yana nan yanda ka sani ranar Juma'a mai zuwa daurin aure."


Ya fesar da wani zazzafan huci! ya mi'ke zaune gumi! na yanko masa yace."Okey ina fata dai kin sheda masa cewa saura na zai samu domin duk na kwashe roman sai da ya samu sud'i."

Da sauri na kashe wayar gabana na dukan uku-uku addua nake a zuciyata akan Allah yasa Hauwwa ba taji komai ba.

Kiran wayar ya sakeyi na dauka da sauri na kasheta gabadaya, Hauwwa tayi dariya da fad'in "Khalid kenan kice dai har yanzu bai hakura ba."

Cikin basarwa nace" Hauwwa rabu da shashasha dan Allah idan ya gaji zai hakura."

Tayi dariya da fad'in "Ni kam ina sha'awar yanda yake nuna miki so hakan yana burgeni wallahi."

Nace."Hauwwa ke kin fiye budurwar zuciya wallahi ina abun yake a gurin Khalid me ya iya a soyayya sam baya burge ni wallahi."

Ta kalleni tana so ta gazgata maganata nace."Kwarai kuwa Hauwwa soyayya sai babban mutum wanda yasan abinda yake amma irin wannan soyayya tasu Khalid ai shirme ce."


Tace."Ni kam a gani na Sa'ida soyayya duk soyayya ce babu babba babu yaro a cikin ta na tabbatar da cewa babu abinda Alhaji Nura zai nunawa Khalid d'an zamani ne sai dai ma ya nuna masa wani abun."

Nace."Hauwwa wai ko son yaron nan kike ne." ? tasa dariya da fad'in "Ai abun so ne yaro ingarma namiji mai 'kwazo ai wallahi ni idan na sameshi to bakina alaikum."

Na dinga kallonta ina mamakin maganarta ita kuma sai kyalkyala dariya take tana 'kara tabbatar min da gaskiyar maganarta...


*30&31*
Cikin wani irin yanayi na damuwa Salmanu ya shiga dakin ya same shi.....Ya ajiye fulas din abincin a gabansa da fadin"Abokina yane na ganka a cikin wani irin yanayi dubi yanda kake zabga gumi sai kace wanda yayi tsere." Ajiyar zuciya ya sauke ido jawur yace."Salmanu dole ne ma na bar garin kano domin mutukar ina zaune a cikinsa hankalina ba zai ta'ba kwanciya ba yanzu nan na kira aunty Sa'ida a waya ta farfad'a min maganar da take so akan wannan mutumin da zata aura Allah Salmanu yanda na tsani Alhaji Nura haka na tsani mutuwa ta idan ina ganinsa zan iya aikata mummunan abu akansa domin sosai nake kishin sa."

Salmanu yace."Dan Allah Khalid ka cire soyayya a cikin ranka kayi abinda yake gabanka wai shin me kake nema ne a gurin aunty Sa'ida bayan ka samu biyan bukatarka duk fa namijin da ya aureta a yanzu sauranka zai samu to meye na damuwa kuma ka cire soyayyarta a ranka ka fuskanci abinda yake gabanka.


"Salmanu bana jin zai ta'ba daina son aunty Sa'ida a cikin jini na yake ko yaya nayi motsi sai na jita a rai na ina yi mata so da kaunar da ban san iya adadinsa ba saboda haka ka daina wannan maganar bana tsammanin zan cire sonta a cikin raina.

Salmanu yace." To ai aure za tayi bai kamata ka cigaba da bibiyarta ba dan Allah tunda dai ka samu abunda kake so a tare da ita to ka rabu da ita ta zauna da mijinta lafiya.

Murmushin takaici yayi yace.''Idan ni ne na auri mace babu budurci wallahi a daran ranar zan saketa to ina fatan hakan ta kasance a kanta Alhaji Nura ya koro ta gida a daran ranar da aka daura musu aure."

A tsorace Salmanu yake kallonsa yace."Khalid wace irin muguwar zuciya gareka wai shin kai baka kaunar zaman lafiya ne kake irin wannan mugwayen kalaman akan 'yar uwarka gaskiya ba sonta kake ba domin duk wanda kake so ba zaka dinga yi masa mummunan fata irin wannan ba."

'Karamin tsaki yaja yace"Salmanu dan Allah maganar nan ta isa haka ni kadai ne nasan abinda yake cikin xuciyata sai kuma wanda ya hallice ni duk da na samu abinda nake so a tare da ita to ba zan daina bibiyar rayuwarta ba."


Salmanu ya dinga girgiza kansa yana mamakin karfin halin abokin nasa.

Yace."Kenan yanzu daka kira wayarta ba hakuri ka bata ba."

Yace."Ganin ina karyar da kaina gurin bata hakuri yasa ta samu damar fad'a min ba'kar magana wannan dalilin ne yasa ka shigo ka tarar dani a burkice Salmanu wai dan Allah dame Alhaji Nura fini da har zata dinga fifitashi a kaina."

Salmanu yace."Watakila kud'insa take so amma bayan haka babu macen da zata dubeka tace bata so Khalid kasan matan yanzu suna so su auri mai kudi ko dan su huta shiyasa kaji nace ka watsar da komai kazo muje mu nemi kudi ko dan mu huce takaici.


"Salmanu bana tsammanin aunty Sa'ida za tayi auran kudi kawai dai nine bata ra'ayi tunda tasha fad'a cewa ita ba zata auri yaro ba sai mai shekaru shin wai wane abu ne take nema da bukata a gurin Alhaji Nura wanda ni bani dashi na zauna nayi tunani sosai na kasa gane mai take hangowa a tattare da mutumin."


Salmanu yace."Son sa take shiyasa take ganin kowane namiji a bayansa yake saboda haka ni dai shawarar da zan baka shine ka tattara lamarinta ka watsa a kwandon shara ka fuskanci a binda yake gabanka.
Murmushin takaici kawai yayi yace."Salmanu duk abinda zan fada maka a yanzu ba zaka gamsu ba saboda kai baka ta'ba soyayya ba sabida haka zanyi kokarin ganin na dauki shawararka amma inaso na sheda maka cewa ba zan ta'ba iya cire son aunty Sa'ida daga zuciyata ba."

Salmanu yace."To Allah yayi maka magani abokina." ya amsa da ameeen yana goge fuskarsa da hankici Salmanu abincin ya zuba musu a plate cikin ikon Allah aka kawo wuta dama zafi ya ishesu sai kawai suka kunna fanka suka fara cin abincin suna tattauna yanda tafiyar tasu zata kasance.


Ina komawa gida na kunna waya ta saboda nasan Alhaji Nura zai iya kirana a cikin ko wane lokaci.....sai da nayi wanka tukkuna na zauna domin cin abinci Gwaggo tace."Sa'ida yau ma sai hakuri domin dai tun safe Rabi tasa kafa ta fita daga gidan nan bayan fitar mijinta.

Nace."Ba ayi abinci ba kenan."? Tace."Sauran taliyar ki na dauka na dafa gatanan a cikin fulas sai dai babu yaji dan nayi ta neman yaro ya siyo min barkono ban samu ba duk suna makaranta.

Nace."Gwaggo taliya da man gyada ina laifin da manja.'' Tace."To nima dai har yanzu ban ci ba dan na tsani taliya ina jiran yara su dawo daga makaranta a siyo min d'an wake a gidansu Mamu."

Nace."Yau kuma d'an wake kike sha'awa."'? Tana cigaba da kad'i tace.Aikam kin san rai da marmari." Girgiza kaina kawai nayi cikin zuciyata nace."Gwaggo sar'ka kenan mai rikicin gangan.

Mikewa nayi zan fita tace."Ina kuma zakije da ina so muyi wata magana mai muhimmanci.

Nace."Zan duba almajiri ne ya siyo min kayan miya nayi miya dan ba zanci farar taliya da mai ulcer zata tayar min.

Tace."Yawwa to tunda hakane nima na fasa siyan d'anwaken Allah yasa a samu almajirin."

Ameen nace na fita daga dakin....daga cikin soron na tsaya ina le'kawa can na hango almajirai su uku hannu na daga musu gabad'ayansu suka 'karaso inda nake na mikawa daya daga cikinsu dari biyu da fad'in "Dan Allah kayan miya zaku siyo min na duka.''

Da sauri suka ce to suka tafi ni kuma na koma cikin gidan


Tana zaune a inda take na nemi guri na zauna ina kallonta da fad'in " Wace magana za muyi."

Ta dago a nutse tace."Ya jikin naki ina fatan gurin ya daina ciwo.'' nace."Eh alhamdulillahi." Tace."Masha Allah haka ake so."

Dakin yayi shuru na minti biyar kafin tace." Dazu bayan tafiyar ki makaranta Ina sauraran shirin *TAMBAYA MABUDIN ILIMI* wanda Malam *AMINU DAURAWA* yake gabatarwa a tashar freedom redio naji yana amsa wata tambaya da akayi masa akan budurwar da akayi mata fyad'e ko kuma karuwar da ta tuba ta dawo gida domin tayi tsarkakken aure shine yake cewa ba kai tsaye za'a daura aure ba sai mace tayi tsarki uku an tabbatar da cewa babu ciki a tare da ita sai a d'aura auran wannan shine daidai da abinda addinin musulunci ya tanada sai duk jikina yayi sanyi Sa'ida ina so kiyi tsarkakken aure gashi yau saura kwana biyar daurin auranki yanzu ya kike ganin za'ayi me zamu cewa da Alhaji Nura nasan dai shi yanzu ya gama shirye-shiryensa lokaci kawai yake jira yanzu ya kike ganin za'ayi."?

Cikin wani irin yanayi nace."Gwaggo wallahi nima ban san ya za'ayi ba gabad'aya na mance da hakan kinga Amfanin sauraran redio kenan da tuni an daura aure akan kwamacala."

Tace." To Sa'ida ai ita redio tamkar makaranta take domin babu abinda basa koyawa mutane wallahi sauraran redio yafi mutum ya kalli akwatin talabijin mutukar ba tashoshin addinin musulunci mutum zai kalla ba."

Nace."Hakane maganarki Gwaggo yanzu wace shawara za 'a yanke."? Tace." Bari Babanki Iro ya dawo mu tattauna shima nasan hankalinsa ne ya dauke baiyi tunanin hakan ba nasan idan ya dawo yaji abinda yake da akwai dole a nemo mafita."

Ajiyar zuciya na sauke nace"Gwaggo Allah yayi mana maganin masifa.'' ta amsa da "ameen 'yan nan."

To kusan awa guda kenan da aiken da nayi wa almajirai shuru basu dawo ba, Nace"Gwaggo kinga awa guda almajiran nan basu kawo kayan miyan ba.

Tace."Sa'ida Ai almajiran unguwar nan su zama abinda suka zama Allah yasa dai basu gudu da kudin ba domin sau nawa suka gudar min da kudi shiyasa kika ina zuwa nayi uzirina da kaina.

Girgiza kaina nayi nace." Allah ya kyauta to.'' tace"Sai dai fa kiyi hakuri ki bada wani kudin a siyo kayan miyan." Nace."Bani dasu tunda kin san yanzu dai a karshen wata muke ki siyo ai nasan kina da kudi.

Tace."To bari na 'karasa abinda nake sai naje na siyo." Tana rufe baki naji alamar shigowar text wayata daukar wayar nayi ina dubawa, Khalid ne wai dan Allah yana so yayi magana da Gwaggo yanzu zai kira sai na bata wayar. takaici ya sani na kashe wayar gabadaya na ajiyeta.

'Bangaransa kuwa hankalinsa ne ya tashi sosai lokacin daya kira wayar yaji ta a kashe ya kalli Salmanu a raunane yace."Kaga ta kashe wayar gabadaya.'' Salmanu yace."Ka kira ta mahaifinka mana." shiru yayi yana tunani kafin ya yanke hukuncin kiran mahaifin nasa.


Baba Iro yana kasuwa yaga kiran D'an nasa 'kin daga wayar yayi har ta karaci ringing d'inta ta katse. Khalid sai da ya kira sau kusan biyar Kawu Ibrahim bai daga ba. sai ya yanke shawarar kiran ta mahaifiyarsa a lokacin ta dawo daga zauran Malam Sammani suna tattaunawa da mahaifiyarta Baito ganin Khalid din ke kiranta a waya sai farin ciki ya isheta hakika babu abinda za tace da malam sammani gashi tun kafin aje ko'ina aiki yayi kyau Khalid din ya kira wayarta.


Hannu na rawa ta dauki wayar tasa a kunnenta tana kiran sunansa.

Ajiyar zuciya ya sauke yace."Ummatu ku gafarce ni." sai kawai ta fashe da kuka da fadin."Khalid kana ina ne? me yasa ka gudu bayan baka ka aikata ba nasan ni yaro na kamili ne ba zai aikata abinda ake zarginsa ba.


Yace."Ummatu ni na aikata ba wani mahaluki ba wallahi nine." sai hawaye suka 'kwace mata tana rawar baki tace."Khalid kaine fa kace."

Yace."Eh Ummatu tsautsayi da qaddara ne ku gafarce ni." hannu tasa ta sharce gumin fuskarta tace."To yanzu kana ina."?

Yace."Ummatu ina gidansu abokina a halin yanzu domin ina jin kunyar sake hada

Please Login or Register in order to submit comment