Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fadin."Anya kuwa Sa'ida."? zuciyata ce ta karye dama neman wanda zai rarrashe ni nake ina kuka nace."Uwale mutumin nan yaki bani had'in kai tunda yayi amfani da maganin nan na kwana uku ya daina amfani dashi karshe ma sai ya kasance a duk sanda zanyi masa magana akan maganin sai munyi fada wannan dalilin yasa gabadaya na tattara maganin na zubar dasu."

Uwale ta dinga girgiza kanta tana mamakin al'amarin tace"Anya Sa'ida wannan mijin naki zai amince ku rufawa kanku asiri kuwa? wace irin rayuwa ce wannan ace namiji babu lafiya amma ba zai sha magani ba wane irin hali yake so ki shiga."?

Hawaye na share nace."Uwale wai cewa yayi maganin yana kashe masa jiki yayi ta sashi bacci." Uwale tace"To idan banda abinsa ai haka ake so alamun maganin yana tasiri a jikinsa."
Nace"To wallahi babu yanda banyi dashi ba ya'ki sha sai fad'a yake wai maganin cutar dashi yake."

Tsaki taja tace."To ai shikkenan kansa yayi wa ke yanzu wace shawara kika yankewa kanki."? Hawaye na zuba nace "Uwale wace shawara zan cigaba da hakuri kawai." Girgiza kanta tayi tace."Aa ba za'ayi haka ba Sa'ida ai yana da magabata saboda haka kije ki samu iyayensa da maganar idan kika ce zaki cigaba da hakuri to zaki cutar da kanki saboda haka kije ki shedawa mahaifiyarsa halin da ake ciki." Ajiyar zuciya na sauke nace."Shikkenan Uwale zanyi kokarin zuwa insha Allahu amma don Allah kada naji maganar nan a bakin kowa Uwale ni bana so sirri na ya fita ko'ina."

Tace."Haba kada ki damu Sa'ida babu wanda zaiji maganar nan." Mikewa nayi na shiga daki na dauko mata kudi, ta kar'ba tana ta godiya direba nasa ya dauketa a mota domin ya kaita inda ta nufa.
*SADAUKARWA NE GA IYAYE NA BIYU*

*FATIMA MUSA (MOMMY NIJAR)*
*TARE DA*
*USAINA ABDUL-MALIK ISA (KAITA)*
*(HAJIYA BABBAH)*

*_Ha'kika ina Alfahari daku da irin kaunar da kuke min.🥰🤝🏻💜_*




*82&83*
Bayan tafiyar Uwale na jima a zaune ina nazari akan shawararta tabbas dole manya su shiga cikin al'amarin tunda duk iya bakin k'okari nayi akan kada maganar ta fita waje wani yaji ya'ki bani had'in kai ni naso ace daga ni sai shi muka kashe matsalarmu amma rashin fahimtarsa yasa ya mayar da al'amarin wani iri mutukar kuwa nace zan cigaba da zama dashi a haka to rayuwata tana cikin garari tunda ni Allah ya hallice ni cikin masu tsabanin bukata wannan dalilin ya sanya kawai na yanke shawarar tunkarar iyayensa da maganar sai dai kuma ban san ya za'ayi na iya fad'a musu maganar ba........''Kawai idan kinje gidan ki samu mahaifiyarki ki sheda mata halin da kike ciki a gidan auranki." zuciyata ce ke tunasar dani abinda ya dace, ajiyar zuciya na sauke na amince da shawarar Uwale da kuma shawarar da zuciyata ta bani akan al'amarin.

Bai dawo gidan ba sai bayan tara na dare koda ya dawo din bayan yayi wanka falo ya fito ya zauna yana abinda ya saba lissafi da amsa kiran waya duk yabi ya wani murtuke fuskarsa dan kada nayi masa maganar magani. sai kawai na tashi na bar masa falon na shiga dakina nayi wanka na kimtsa na kwanta kan gado ina tunanin yanayi na rayuwa bacci ne ya dauke ni na dinga wani mummunan mafarkin da ya sani tashi a firgice ina takure jiki na bedlamp na kunna ina wulkita idona a dakin gani nake kamar yaron yana dakin ya 'buya a wani gurin a sanyaye na sauko daga gadon na shiga duba bayan labule gani nake kamar ya 'boya a wani gurin.

Jiki a mace na shiga toilet na wanke jikina na fito na zauna gefan gado tare da zabga tagumi! yanayin yanda mukayi mu'amula da yaron a cikin mafarkin tamkar a zahiri shine al'amarin yayi masifar gigita ni gabadaya nipples dina sun mi'ke sun dame bu da kyaikyayi ga wani irin ruwa dake fita daga jikina. zazzafar ajiyar zuciya na sauke na koma na kwanta tare da rungume filo rintse idona nayi ina sake tunano yanda yaron yake sarrafa ni a mafarkin babu abinda yafi gigita ni sai girman joystick d'inshi sosai ta cika min mara ta cif-cif! yanda kuma yake buguna yana sucking d'in breast d'ina shi ya dinga sanya ni sakin ihu ina rungumeshi da kiran sunansa, ina daf da samun gamsuwa mafarkin ya katse...."Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un ! Astagafirullah ya Allah." abinda nake ta nanatawa kenan ina birgima a gadon masifaffen feelings na taso min.

Ganin ina neman mutuwa ne yasa na mike a jigace na nufi dakin Yaya Aminu duk da nasan ba wani abun zan samu ba ina ganin dai ko rungume ni yayi ya tatta'ba ni zan samu saukin wani abun.

A bude kofar take na shiga tare da mayar da kofar na rufe, yana kwance a gadonsa yana bacci hankalinsa a kwance.

Ajiyar zuciya na sauke na karasa a hankali na kwanta a kusa dashi tare da dora kaina a kirjinsa......Ajiyar zuciya dai na sake saukewa a hankali na shiga kiran sunansa, shuru be amsa ba sai kawai na shiga shashshafa sassan jikinsa gabana na fad'uwa na fara ko'karin sa hannuna a cikin wandonsa.

A firgice ya tashi zaune ya wani ture ni na matsa gefe guda.

Bedlamp ya kunna yana kallona hade da matsawa baya....na kalleshi da idanuwa na da suka k'ankance saboda fitinar dake damuna.

"Yaya Aminu ina cikin wani yanayi ka taimak.........Hannu ya daga min tun kafin na karasa yace." Sa'ida wane irin taimako zanyi miki kamar baki san komai ba me yake damun ki ne."?


Murya na rawa nace."Sha'awa ce ta taso min cikin dare Yaya Aminu mara ta ciwo take na rasa yanda zanyi dan Allah kayi wani abu."


Kansa ya dafe yana cijar lips d'inshi. jikinsa na matsa na dora hannuna a cinyarsa da sauri ya ture ni yana hararata yace."Kada ki janyo wa kanki 'bacin rai Sa'ida ni ba zan iya aikata miki komai ba a yanzu ki rabu dani nayi bacci."


Raina ne ya soma 'baci nace."Haba Yaya Aminu ya kake wannan maganar kamar ba namiji ba kayi min dabaru dan Allah na samu satisfaction ko yaya ne."

"Sa'ida idan nayi miki dabaru kin samu gamsuwa ni kuma fa? zaki barni cikin halin damuwa kiyi hakuri nima ina bukatar naji dadi amma babu hali shiyasa gabadaya na ajiye maganar aure a gabana saboda lalura ta ina ganin zan iya kare rayuwata a haka saboda haka ki cigaba da hakuri insha Allahu komai yana da karshe."
Yana gama maganarsa ya mike ya shiga toilet ya barni da baki a sake ina binsa da kallo.

Ya jima a ciki kafin ya fito ya kalle ni da fadin."Ashe baki je kin kwanta ba kina zaune."? Ba tare da nace masa komai ba na sauko daga gadon na kama hanya na fita daga dakin zuciyata tamkar zata fashe sabida tsabar takaici da bakin ciki.


Ruf da ciki nayi kan gado na dinga rizgar kuka ina rokon Allah ya kawo min dauki!! jaraba sai k'ara nunnukuwa takeyi al'amarin da ya gigita ni mutuka ba tare da nayi tunanin abinda ka iya zuwa ya dawo ba na dauki waya ta na kunna number Khalid na lalabo na shiga gurin kira.............Muryar wani naji ta doki kunnena da sauri na cire wayar ina dubawa tabbas number sa ce to ya akayi wayarsa taje hannun wani.

"Da wa nake magana ne."? Mutumin yayi magana. a sanyaye nace." Sunana Sa'ida daga kano inaso nayi magana da Khalid.

Yace."Eh naga sunanki akan wayar sai dai kiyi hakuri fa Domin Khalid baya kasar nan sun tafi wasa kasar america."

Jiki a mace nace."Dan Allah babu yanda za'ayi ka bani number da yake amfani da ita a can din.........Yace."Zan iya baki mana sai dai ko na baki number be zama lallai ki samu amsa akan lokaci ba saboda kullum yana busy. " Nace."Babu matsala ka bani number."

Yace."Okey bari na miki text. " ajiyar zuciya na sauke da fadin."Nagode sosai. wayar na kashe ina dan jin sauki a cikin zuciyata.

Number ya tura min nayi sauri nayi serving agogo na duba karfe goma sha biyu da minti arba'in inaso na kira shi amma kuma ban san me zan ce dashi ba.

Gwada kiran wayar nayi cikin ikon Allah ta shiga sai dai har ta karaci ringing ta katse bai dauka ba, text na tura masa na sheda masa cewa nice nake kira ya dauka.

Lokacin suna dakin hutu shida abokansa domun basu jima da fitowa daga filin wasa ba, koda ya duba text din sai kawai ya share yaki kiran ta akan wane dalili zata kirasa da daddare ta tayar masa da hankali ta hanashi gudanar da abinda ke gabansa wayar ya ajiye kan drowar ya shiga toilet daidai lokacin dana sake kiran wayar tayi ta ringing babu wanda ya daga a cikin jama'ar dake dakin kowa harkar gabansa yake.....sai bayan ya fito daga toilet din yana tsane jikinsa da towel Salmanu yace."Khalid an kira wayarka kana wanka kuma da alama daga gida Najeria ne."

Yace."Salmanu rabu da ita don Allah aunty Sa'ida ce me za tayi min da daddare salon ta jaza min masifa ta kuma hanani gabadatar da uzurina."

Salmanu yace."Amma nayi mamaki fa to me zata ce maka bayan tana gidan auranta." Yace."Nima abinda na gani kenan."


Salmanu yayi jim yana nazari yace."Baka kuma tunanin ko wata matsalar ce ta faru a gida ka kira ta kaji ko menene."? Girgiza kansa yayi yace."Aa ba zan kira ta ba Salmanu idan wata matsalar ce Babana zai kira ni ya fad'a min tunda yana da number ta." Salmanu yace."To shikkenan Allah yasa alkairi ne." Yana kokari sanya short nickar a jikinsa ya amsa da "Ameeen Ya Allah."

Jikina a mace na ajiye wayar na kwanta rigingine idona na kallon rufin dakin hawaye kawai yake zuba a fuskata duk yanda naso da na samu bacci a daran abin ya gagara yanda naga rana haka naga dare na tashi da wata irin kasala da mutuwar jiki! da kyar na shirya break fast na samu nayi wanka na kimtsa jikina na fito falo na zauna ina jiran fitowarsa.

A shirye ya fito da shirin fita kamar yanda ya saba babu yabo babu fallasa muka gaisa da juna na mike na nufi gurin cin abincin ya biyo bayana.

Haka mukayi zaman kurame a gurin babu wanda yayi magana da dan uwansa tun bayan gaisuwar data shiga tsakanin mu.

Kallonsa nayi yana goge bakinsa da tissue nace."Yaya Aminu ina so ka ajiye ni a hotoro mu gaisa da mutan gida."

Jim yayi na minti biyu kafin yace."Ina fatan a kimtse kike."? nace."Eh mayafi na kawai zan dauko." ya mike da fadin."Okey to kiyi sauri ki fito ki same ni a bakin mota."

Da sauri na mike da fadin."To shikkenan." hanyar fita ya kama ni kuma da sauri na shiga dakina domin dauko mayafi na.

Ko a motar ma haka mukayi zaman kurame sai jefi-jefi muke magana da juna waya kuwa ban san iya adadin nawa ya amsa ba duk wayoyinsa a lokaci guda sai a kira sai ya gama da wannan sai ya dauki wannan.


A tsaitsaye ya shiga gidan suka gaisa da mutanan gidan ya wuce ya tafi kasuwa, ni kuwa ko wane daki sai da nabi daya bayan daya muka gaisa sai dai na jima a dakin mahaifiyarsa muna hira sama-sama kafin na fito.

Ummu Habiba ta kalle ni da fadin."Ina fatan dai kuna zaune lafiya babu wata matsala." ?

Shuru nayi ina wasa sa hannuwana. tace."Sa'ida idan da akwai matsala ki fada min baki da wacce ta kaini a duniya.

A raunane nace."Hakane Umma sanin hakan ne ma yasa nazo gurin ki domin na sheda miki abinda yake faruwa."


Zama ta gyara tana kallona a nutse tace."To ina sauraranki." Na jima kaina a sunkuye kafin nace."Ummu ashe Yaya Aminu bashi da lafiya."?

Tace."Bangane ba idan Aminu bashi da lafiya ai zaki fi kowa sani ya za'ayi kuma ni da nake gefe guda ki tambaye ni."


Ajiyar zuciya na sauke nace."Ummu ki fahimci maganata mana Yaya Aminu a zahiri lafiyayye ne amma a bad'ini nakasashshe ne."!

Ta dinga kallona tana neman karin baya ni. Murya na rawa nace."Ummu ranar wanka ba'a boyan cibi kamar yanda kika fada hakane bani da wanda zan kaiwa matsalata ya saurare ni sai ke da kika haife ni To inaso na sanar miki da cewa tsayin watannin aurena da Yaya Aminu wata mu'amular aure bata ta'ba shiga tsakani na dashi ba gabadaya bashi da kuzari bashi da girma irin na maza haka nake zaman hakuri har aka kawo wannan lokacin da na kasa hakuri nazo na sheda muku koda taimakon da zakuyi a matsayin ku na iyayenmu tunda nima nayi iyakacin bakin kokari na akan matsalar."

Ido ta tsira min tana girgiza kanta daka ganin yanayin ta al'amarin ya bata mamaki! "Sa'ida yanzu tsayin wata hudu da kwanakin auranku babu wata mu'amula ashe."?

Kaina na daga mata hawaye na kokarin kwace min." Tace."Amma al'amarin ya bani mamaki mutuka kuma babu kama ko kad'an to shin me yake damun wannan yaron haka."?

Nace."Wallahi nima ban sani ba gashi baya son shan magani dan har zuwa nayi gidan Gwaggo Uwale taje can kauyen daburau ta samo masa magani amma sau uku kacal yasha yace a zubar dashi ba zai kara amfani dashi ba."

Ummu Habiba tace."Ai to hakan ba zata yiwu ba dole ya nemi magani domun rayuwa ba zata ta'ba tafiya a hakaba wace macace zata zauna dashi a haka babu shakka dole yau mahaifinsa yasan halin da ake ciki domin yasan matakin da zai dauka.

Nace."Ummu ni wallahi da Ya bani hadin kai a gida babu wanda zaiji ko ya gani tunda dai wannan maganar ta sirri ce be kamata a fad'a ba amma duk kokari na akan hakan be samu ba gabadaya ma yanda na fahimce shi matsalar bata damunsa."

Ummu tayi shuru tana nazari kafin tace."Ko shiyasa ya'ki aure ne saboda yasan bashi da lafiya." Nace."To ina jin dai hakane manufarsa." tace."To ai shikkenan Allah yayi mana magani kuma naji dadi da baki rufe maganar ba kika fito kika fad'a domin a san matakin dauka saboda haka kada ki damu insha yau idan Alhaji ya dawo zan isar masa da maganar." Ajiyar zuciya na sauke da fadi."To shikkenan Umma Allah yayi mana magani." ta amsa da "Ameeen Ya Allah."

*SADAUKARWA NE GA IYAYE NA BIYU*

*FATIMA MUSA (MOMMY NIJAR)*
*TARE DA*
*USAINA ABDUL-MALIK ISA (KAITA)*
*(HAJIYA BABBAH)*

*_Ha'kika ina Alfahari daku da irin kaunar da kuke min.🥰🤝🏻💜_*




*84&85*
Koda Alhaji Shamsu ya samu labarin abinda yake faruwa sai ya rasa bakin magana yayi shuru yana mamakin al'amarin da kyar ya iya d'aga kansa ya kalli inda nake zaune kaina a kasa yace."Sa'ida ina neman gafara a gurinki a bisa wannan al'amari da ya faru wallahi dana san yaron nan yana da matsala da ban tilasta ki auransa ba ni duk abinda yake faruwa ban sani ba bani da labari shi bai fada min ba kuma mahaifiyarsa ma haka saboda haka kiyi hakuri da wannan al'amari nasan anyi miki laifi amma mutukar al'amarin nan ya zama da akwai cutuwa a ciki to zan sanya Aminu ya sawwake miki sai kiyi auran da hankalin ki zai kwanta."

Umma Habiba ta sauke ajiyar zuciya a sanyaye tace."A'a Alhaji ba za'ayi gaggawar yanke hukuncin rabuwa ba kamata yayi shi Aminun ya nemi magani domin a duniya babu cutar da bata da magani amma kada kace zaka raba auran."

Yace."Habiba yaron nan ya bani mamaki mutuka wato ashe yasan yana da dauke da lalura irin wannan amma bai ta'ba zama tare dani munyi maganar ba to Habiba ta yaya za'ayi rayuwar aure babu wannan mu'amular akwai cutuwa a ciki dole a raba auran.

Murya na rawa nace."Aa Alhaji ka dai kira shi kayi masa magana ya mayar da hankalinsa gurin neman lafiyarsa nima bana so a kashe min aurena ina tausaya masa halin da yake ciki.

Kallona yayi yana girgiza kansa yace."Sa'ida hakika ke 'yar halak ce kuma hakika ke din matar rufin asiri ce duk namijin da yayi dace da samun mace kamar ki ya samu jin dadin duniya ina rokon Allah yayi miki albarka ya azurtaki da 'ya'ya masu albarka kuma insha Allahu kamar yanda kika bukata cewa ba kya so a raba auranki da Aminu to bazan raba ba amma dole duk inda magani yake yaje ya nema kuma yatsa tsayin daka gurin amfani dashi."

Umma Habiba tace."Eh dama hakan shine maslaha a tsakaninsu Ubangiji Allah ya bashi lafiya kamar ko wane da namiji." Cikin alhini da damuwa ya amsa da ameeen ya Allah."


Tunda na shiga motar naga fuskarsa kamar hadari nasha jinin jikina, a sanyaye nace."Yaya Aminu ya kasuwa da Jama'a."? Shuru yayi min a zafafe yaja motar muka bar gurin.
Sunkuyar da kaina nayi gabana na fad'uwa! wato saboda mahaifinsa yayi masa fad'an gaskiya yake jin haushi na akan gaskiya ni ina ganin idan da mutunci ban cancanci wannan sakamakon daga gurinsa ba tunda duk abinda nake saboda da lafiyarsa nake babu laifi domin iyayensa sun san halin da yake ciki.

A haka muka isa gida kamar kurame! yana gama parking ya bude motar da sauri ya fita barni a ciki....Na jima ina mamakin al'amarin kafin na fito da sanyayyan jiki nabi bayanshi.

Kasa shiga dakina nayi na yanke shawarar bin sa dakinsa, tsaye na sameshi da towel a jikinsa wanka zai shiga sai kawai ya daga min hannu a fusace yace."Ki fita ki bani guri bana bukatar ganin ki a dakina tunda dai ke kin kasance mace mara sirri."

A sanyaye nace."Yaya Aminu kada kayi min mummunar fahimta dan Allah ka tsaya ka fahimce ni."


"Sa'ida babu wata fahimta da zanyi miki nagode da abinda kikayi min."

Rai a 'bace nace." Yaya Aminu laifi ne dan mahaifinka yasan lalurarka kada fa ka manta shine silar samuwar ka a duniya me yasa kake 'bacin rai akan yaji matsalarka."


"Ki rufe min baki munufaka kawai tunda nake ban ta'ba samun sa'bani da mahaifina ba sai ta dalilin ki dama bani nace ina sonki ba tilas ta min akayi idan kika takura min zan iya sawak'e miki babu lallai babu dole."


Wani irin gumi ne ya shiga yanko min na dinga kallonsa ina mamakin furucinsa ashe dama alkairi yana zama sharri! ban ta'ba tsammanin shima yana da mugun hali ba sai yau.

"Yaya Aminu na fahimci kai baka san abinda ya dace ba kuma kana da son kanka da yawa a wannan rayuwar da kake ciki duk kudin ka da kima da mu'kamin ka wace macace kake tsammanin zata zauna da kai da mugun halinka da lalurarka to gaskiya ni na gaji da wannan masifar taka nima zaman hakuri nake idan rabuwar itace alkairi meye a ciki."

"Kada dai kice zaki zage ni ranki zai mummunan baci yanzu yanzu." Cikin fushi yayi maganar, hawaye na share na juya da sauri na fita daga dakin ba'kin ciki kamar ya dagargaza min zuciyata.


Yau kusan kwana goma kenan baya yi min magana ko gaishe shi nayi baya amsawa abinci kuwa idan na ajiye haka nake dauke abuna daga ya dawo daga kasuwa zai shiga daki ya kulle kansa sai dai kuma na fahimci yana shan magani amma na asibiti ne sabida nagansu akan drowar d'akin shi.


Gajiya nayi da zaman gabar na sameshi a d'akinsa yana shirya kudi a cikin akwati na samu kujera na zauna a nutse nace."Yaya Aminu barka da asubah."

Shuru yayi min bai amsa ba, nace."Kayi hakuri dan Allah babu kyau gaba gashi Azimi zamu shiga idan muka cigaba da irin wannan zaman to ibadar mu za tayi rauni Allah da mala'iku zasuyi fushi damu saboda haka naji ni mai laifi ce a gurina kayi hakuri ka yafe min."


Kallona yayi babu sassauci a tare dashi yace."Wallahi kada ki kuskura ki sake fita da sirrin gidana ban amince kowa sake jin matsala ta ba cikin kuwa harda iyayen da suka haife ni bana bukatar suji idan zaki zauna dani a haka ki zauna idan ba zaki zauna ba ga hanya nan a bude."
Hak'ika
Bai ta'ba 'bata min rai irin yau ba sai kawai na mike tsaye rai a bace nace."To sai me? babu d'a babu jika zaman me zanyi dole ne? kabar ganin kana da kud'i to ni ba sune a gabana ba kwanciyar hankali ce a gabana kudin ka na banza ne domin basa gabana zan tafi inda nafi wayo sai ka biyo ni da takarda sai me? idan mun rabu kanka kayi wa." Ina k'are maganata na juya da sauri zan fita daga dakin. tare hanya yayi fuska a tur'bu ne yace."Ni kike d'agawa murya Sa'ida."? Murya na rawa nace."Yaya Aminu duk abinda nayi maka kaina ka janyo mai yasa ba zaka tsaya mu fahimci juna ba? me yasa ba zaka tsaya mu kashe matsalar mu ba duk fa abinda nake saboda da kai nake amma saboda gadara! ka dinga fad'a min dik maganar da ranka yake so to shikkenan na hakura da zama da kai babu lallai babu dole a rayuwar aure."
Ajiyar zuciya ya sauke yace."Ke da kan ki kikayi wa mahaifina al'kawari cewa zaki cigaba da zama dani da lalura ta me yasa kuma yanzu kike wannan maganar." Dauke kaina nayi nace."Ai kai ne naji kana wata magana wacce bata dace ba shiyasa na nuna maka cewar idan mun rabu d'in bawai zan tagayyara bane watakila ma Allah yayi min kyakykyawan sakamako." Yace."To duk dai magana ta wuce magani dai naje asibiti sun bani gashi can ma ina kan amfani dashi insha Allahu za'a a dace kiyi hakuri raina ne ya 'baci."
Ajiyar zuciya na sauke tare da ratse shi na wuce na barshi a tsaye a gurin gabadaya al'amarinsa ya fice min daga rai.

Saura kwana uku a dauki Azimi Yaya Aminu ya k'are shan maganin asibitin da yake amfani dashi ganin bashi da niyyar komawa asibitin sai na yanke shawarar yi masa magana sai kawai yace dani ranar litinin zai koma asibitin nace.''To amma dai kana gananin sauyi ko."? shuru yayi min sai da na sake magana yace."Ni babu wani sauyi da nake gani kullum jiya i yau." Wani k'aton abu ya tokare min a kirji Nace."To ai sai kayi musu bayani idan kaje ko kuma kawai kayi na hausa shine daidai." girgiza kansa yayi yace."Aa ni duk magungunan hausan nan ban yarda dasu ba zan dai cigaba da neman maganin asibitin.'' Fita nayi daga dakin ba tare da na sake masa magana ba Yaya Aminu mugun d'an taurin kai ne wannan lalurar tashi dole sai an hada da maganin gargajiya sam na bature ba zaiyi ba amma ya'ki amincewa.


Kwanciya nayi da waya ta a hannuna cikin rashin zuciya na sake nemo number yaron so kawai nake naji muryarsa ko naji sanyi a cikin raina haka kawai kwana biyu yaron ya tsaya min a raina yanzu gabad'aya hankalina na kansa ina ganin a gurinsa kad'ai zan iya samun abinda nake bukata.

Wayar ce ta katse bai dauka sai na rubuta masa text hade da magiyar ya daga waya ta......Ina kokarin sake kiransa sai ya kira, hannuna na karkarwa na daga wayar tare da

Please Login or Register in order to submit comment