Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ido da gwaggo da Babana naci amanarsu na tozartasu a idon duniya dalilin da yasa kenan na yanke shawarar barin gari gabadaya.

Gabanta ne ya fad'i da sauri tace."Khalid ba'a kan ka aka fara ba kuma ba za'a 'kare a kanka ba saboda haka ka dawo gida shine kwanciyar hankalina.


"Ummatu kiyi hakuri ki gafarce ni ba zan dawo gida na zauna cikin takaici da damuwa ba ki yafe min kuma kiyi min fatan alkairi a duk inda nake."
Yana gama maganar ya kashe wayar kansa na wani irin sarawa

Ummatu baki a sake take kallon mahaifiyarta Baito tace."Wai me yake faruwa ne."?


Bude baki tayi za tayi magana sai kuma kuka ya kufce mata!


baito hankali a tashe ta dinga tambayarta abunda ya faru Ummatu sai da taci kukunta ta koshi ta fada mata yanda sukayi da Khalid din.

Baito tace."Amma nayi mamakin hakan saboda nasan aikin malam Sammanin kamar yankan wuka haka yake to me yasa wannan karon aikin yayi gardama."


Ummatu tace."Ni babban tashin hankalina ma katifa ta dana siyar gashi yaron nan yana tabbatar min da cewa ba zai dawo gida a wannan lokacin ba


Baito tace"Share hawayen ki ki daina kuka akwai malamai a gari saboda haka yanzu sauran kudin da suka rage a hannunki dasu zamuyi amfani zaki tashi yanzu muje mu nemi inda za'ayi aiki mai zafi akan yaron nan."

Ummatu a sanyaye tace."To shikkenan Baito Allah yasa a dace." Baito ta amsa da cewa "Za'a dace da yardar Allah bari na shirya mu tafi."
Mikewa tayi ta hau shiryawa suna sake tattauna maganar.



Sai daf da magariba suka gama yawace yawacen gurin malaman tun a hanya suka rabu da juna....Ummatu ana kiran sallah ta shigo gidan lokacin Gwaggo na zaune a kan kujera tana alwala sallama tayi Gwaggo ta kalleta kafafunta sunyi fururu! duk tayi firgai-firgai da ita! Gwaggo ta amsa sallamar da fad'in "Rabi daga ina kike haka kinyi fururu dake kamar an haqo ki daga rami."

Ummatu shuru tayi bata tanka mata ba ta bude kofarta ta shige...Gwaggo ta bita da kallo tana girgiza kanta.

Ummatu abubuwan hannunta ta ajiye da sauri ta fito ta shiga kicin ta hura wuta ta dora tukunya ta fito a gurguje tayi alwala azahur la'asar magriba ta had'a a lokaci guda tana idar da sallar ta mike ta dauko kaskon wuta kicin ta shiga ta d'ebo garwashi da yawa tazo ta bude ledojin data shigo dasu wani magani ta dauko daure a leda ta kwance ai kafin kice kwabo ta rikice da atishawa maganin jajawur dashi kamar barkono tana zabga atishawar ta zuba maganin cikin wutar ta mike da saurin gaske ta fito babban tsakar gidan tasa a tsakiya ta tsaya kan maganin tana kiran sunan Khalid.

Gwaggo dake sallah atishawa da majina suka cika mata hanci hawaye kawai take a jigace! ta idar da sallar ni kuwa tunda na leqa tsakar gidan naga Ummatu a tsaye gaban kaskon sai kace soja na koma dakin na kwanta tare da toshe hancina daya cika da majina tsinkakkiya.....Tana idar da sallar ta hau sababi da fad'in "Wace irin jaraba kuma aka shigo mana da ita gida." Zaune na mike ina kokarin hana ta fita ta fizge hannunta da fad'in "Ke sakar min hannu na fita naga jarabar da matar nan take." Fita tayi daga dakin tana surutai....har yanzu Ummatu na tsaye a tsakiyar tsakar gidan da kaskon wuta a gabanta yana hayaki tana kiran sunan Khalid fuskarta tayi gaja-gaja da majina da gumi da hawaye sai nishi take tana sakin atishawa.....Gwaggo da sauri ta 'karasa gurin tasa kafa tayi wurgi da kaskon wutar da fad'in "Rabi wane irin surkulle ne wannan........!

*SADAUKARWA NE GA IYAYE NA BIYU*

*FATIMA MUSA (MOMMY NIJAR)*
*TARE DA*
*USAINA ABDUL-MALIK ISA (KAITA)*
*(HAJIYA BABBAH)*

*_Ha'kika ina Alfahari daku da irin kaunar da kuke min.🥰🤝🏻💜_*




*33&34*
Ummatu da sauri ta d'aga kaskon dake cike da wutar ta gyarashi haya'kin ya cigaba da tashi a gurin tana me cigaba da kiran sunan Khalid a bayyane .........Gwaggo ta tsorata sosai da sauri ta bar gurin tana toshe hancinta dakin ta dawo ta same ni da tissue ina goge hanci gabad'aya majina ta tsinke min wannan wace irin jaraba ce...Hannuna ta kamo muka fito daga dakin har yanzu Ummatu na tsaye akan maganin tana aiki ita kanta sauri take ta gama kiran sunan Khalid din iya adadin da aka gindaya mata .

Kofar gida muka fita muka tsaitsaya muna mayar da numfashi..Gwaggo ta kalli cikin soron gidan tasa gefen hijabinta ta goge hawayen dake sauka a fuskarta tace."Sa'ida kinga yanda haya'kin nan yake fitowa kuwa."

Soron na le'ke na gani nace."Gwaggo matsa daga gurin ki bashi hanya ya fice idan gidan ya sarara sai mu koma.

Kusa dani ta tsaya tana zazzare ido kafin tace."Sa'ida kiga jaraba mutum da gidansa an koro shi waje kai gaskiya Rabi shaid'aniya ce wallahi tana azabtar damu."

Nace."Gwaggo addua zakiyi mata Allah ya shiryeta." tace."Sa'ida idan da Rabi zata shiryu da tuntuni ta shiryu kullum fa a tafe take to daga yau ta daina fita daga gida domin zan sa Ibrahim ya gindaya mata sharad'ai."

Tana rufe bakinta Kawun ya karyo kwana nace"Alhamdulillahi gashinan ma.'' Ajiyar zuciya ta sauke dukkaninmu muka tsira masa ido har ya karaso gurin.


Hankali a tashe yace."Gwaggo lafiya na ganku da magariba a tsaye a waje."

Da sauri tace."Ibrahim ai gidan yafi karfin mu le'ka kaga abinda yake fitowa daga cikin gidan.

Le'ka kansa yayi soron ya hango haya'ki da sauri yace."Subahanallahi Gwaggo ba dai wuta ce ta tashi a gidan ba.'' Yana kokarin kutsa kansa gidan yake magana.

Gwaggo ta hana shi shiga da fadin"Oh o! ko d'aya Rabi ce take haya'ki a gidan ko na barkono ne oho! dan a jigace muka fito daga gidan.

Kawu ransa ya 'baci sosai shi kam Allah ya jarrabeshi da fitinanniyar mata kafin Gwaggo tayi aune ya fad'a cikin gidan.


Lokacin da ya shiga gidan Ummatu ta gama aikin tana sunkuye gaban kaskon wutar tana karkad'eshi duk tayi wujiga wujiga fuskarta tayi jawur! d'ago kan da za tayi sai taga mijin nata a tsaye a kanta shima hawayen haya'kin na zuba a fuskarsa Kawu Iro bai damu ba saboda yasan dole yayi hawaye saboda zafin maganin da yake fitar da haya'kin.


A sanyaye take kallonsa tana share fuska yace."Rabi wane irin haya'ki ne wannan kika turni'ke gida dashi saboda tsabar iskanci da wulakanci na dawo na tarar da mahaifiyata a waje a tsaye Rabi wai me yasa bakya ganin girman Gwaggo ne me tayi miki kika raina ta."


Ummatu kuka ta fashe dashi tace."Wallahi ni bance su fita daga gida ba da kansu suka fita dama nasan dole a k'ulla min sharri a gurinka.

Mari ya kwada mata yace."Rabi kina nufin mahaifiyata ce za tayi miki sharri.'' hannu da dafe da kumatu tace "Aa ni ba haka nake nufi ba. Yace." To wannan azababben haya'kin na magani da menene.'' ?

Tana kuka tace."Kiranye Malam ya sani nayi wa Khalid saboda d'azu da Rana Ya kira ni a waya yake sheda min cewa shida gida har abadah. shine Baito tace na tashi muje ayi mana taimako akan al'amarin shine wani malami ya had'a min wannan maganin yace nasa a wuta na tsaya a kai na kira sunan Khalid in sau dari ba d'aya."

Fuskarsa ta sanja da yanayi na 'bacin rai yace."Rabi yanzu akan yaron nan Khalid kike nema ki kauce hanya wane irin mushirikin malami ne wannan kikeje gurinsa da ya baki irin wannan hayakin."?

Tana hawaye tace." Kandala 'Kawar Baito ce ta kaimu gurinsa a can cikin k'yauyen Janguza."


A karaf a kunne gwaggo a lokacin da suke kokarin shiga gidan ita da Sa'ida.


Tace."Umhum! kaji maganar Uwale ta fito ko Ibrahim."? da sauri ya juya yana kallonta ta cigaba da cewa." Ibrahim ba zan ta'ba mantawa ba kafin ka auri Rabi babu irin abinda ba a fada maka ba a kanta da mahaifiyarta amma ka rufe ido to yanzu ai sai ka gazgata maganar mutane tunda gashinan da bakinta tana fada maka cewa ita da mahaifiyarta sukeje Janguza gurin malami.

Kawu Iro jikinsa yayi sanyi tabbas hakane babu irin shawarwarin da ba'a bashi ba akan ya hakura da Rabi ya nemi wata ya rufe idonsa a lokacin saboda masifar son da yake mata ya aureta gashinan tana azbatar masa da mahaifiyarsa.

Yace."Gwaggo dan Allah kiyi hakuri wallahi tuntuni na gazgata maganar mutane akan Rabi ba mutuniyar kirki bace."


Tace."Ai ni tuntuni magana ta wuce a gurina amma inaso na sanar da kai cewa Yau tsayin kwana biyar kenan Kullum matarka bata yini a gida haka take fita tana barin mu da yunwa ga kayan abincin Sa'ida ya kare muyi ta kame-kame! to sabida haka nake umartaka cewa ka hana ta zuwa ko'ina idan kuma ta'ki to ka gindaya mata sharadi cewa duk sanda ta sake fita a bakin auranta.


Ido jawur yake kallon Ummatu da tayi muzu-muzu a tsaye sabida tsabar zurga-zurga har ta rame yace."Rabi ina kike zuwa babu izini na sannan kuma ina kike kai kudin cefanan da nake baki a kullum."

Murya na rawa tace."Wai shin ya za'ayi na zauna a gida na kwantar da hankalina rayuwar yaro na na cikin garari ai dole naje inda za'a taimaka min."


Gwaggo tace."Shiyasa kika dauki katifar dake shimfid'e a gadon ki kika siyar saboda kiyi yawon malamai."

Da sauri Kawu Iro ya kalleta dan shi bai da labarin siyar da katifa tunda a dakinsa yake kwana sai da Ummatun ta kai kanta gurinsa.


Gwaggo tace."Eh Ibrahim maganata gaskiya ce Kwana hudu da suka wuce Rabi ta siyarwa da Lantana katifar ta.....Kawu Iro kamar yayi kuka yace."Rabi me na gaza dayi a gidana yunwa ko ishirwa."? shuru tayi tana dauke kanta

Yace." To bari kiji Rabi bani kika tozarta ba kanki kika tozarta kuma shi yaron da kike kashe kudi a kansa ko ya dawo ba zai zauna mana a gida ba sai dai ya nemi gurin zama yawon bin malamai kuma kada ki fasa kece a wahale sannan maganata ta karshe dake ita wallahi tallahi duk sanda kika sake fita daga gidan nan bada sani na ba a bakin auranki dan na gaji da wannan munanan d'abi'un naki."

Ummatu tana kuka na fitar hankali ta shige gurin....Ya juyo cikin tausasawa yake rarrashin mahaifiyartasa Gwaggo tace."Ibrahim kada ka damu kaji ko kaje kayi sallah nayi abinci kazo kaci mu tattauna muhimmiyar magana."

Yace."To shikkenan Gwaggo bari na shiga na daura alwala." tace"To babu laifi." Kawu Iro ya bude kofar gurinsu ya shiga ita kuma ta shigo dakin ta sameni a zaune a bakin tabarmar ta.

Zama tayi tana fad'in "Haba jama'a mata duk ta zame mana annoba a gida wallahi Sa'ida da Ibrahim yana da iko aure zan sa shi yayi domin kuwa sam bai dace da mace ta gari ba."


Nace."Gwaggo kema fa da laifinki kina shiga abin da babu ruwanki a gaskiyar magana Ummatu tana hakuri dake da halin ki shiyasa wani lokacin idan tana mayar miki da magana bana jin haushi sabida nasan ke kika janyo."

Tace."Sa'ida nifa ba zan ga ba daidai ba nayi shuru haka halina yake tunda can bana shuru kawai na zuba ido akan mutum yana abinda yake so ban gyara masa kuskuransa ba."


Nace."To Gwaggo kada dai kisa Kawu yayi wani aure a yanzu dan Allah ki kyaleshi yaji da d'aya idan ya 'karo aure gidan nan sansanin ya'ki zai zama gaki ke kuma a gefe kina 'kara ruru wutar al'amarin sabida haka ki kyautata zamanki da surukar ki shima Kawu Ibrahim sai yaji dadin tafiya neman sa."

Tace."To ai shikkenan Sa'ida tunda laifi na kike gani a kan na Rabi." Nace."Aa Gwaggo bance ke kadai kike da laifi kowa yana dashi."

Shuru tayi bata tanka ba ta dauki redio tana murdawa. Kawu ya shigo dakin na gaisheshi a nutse ya amsa Gwaggo ta ajiye redion a kusa da ita bayan ta kama tashar da take so.

Abincin ta zuba masa tasa masa da yawa, yaci ya koshi yasha ruwa. tace."Ka gani sai Rabi taci kayanta idan ta dafa dan Allah Ibrahim ko tayi maka tayi kada kaci ka nuna mata kuskuranta.".......kallonta nayi ina mamakin 'karfin halinta ko waye ya fad'a mata ana shiga tsakanin miji da mata oho.

Zamansa ya gyara da fad'in"Gwaggo kada ki damu ai sai na sake nuna mata kuskuranta idan na shiga gurin." Tace."Yauwa to ka tauna mata tsakuwa sosai." yace."Insha Allah Gwaggo ke nake saurare akan maganar da zamu tattauna.

Gyara zama tayi ta fuskance shi sosai tace."Ibrahim akwai wani bayani dana saurara daga Malam Aminu Daurawa inda yake cewa................Bayani tayi masa sosai kamar a gabanta malam din yayi tambihin...Kawu Iro ya dago kansa a hankali yace."Gwaggo wallahi ni kaina na sha'afa da wannan al'amari nasan tabbas hakane gaskiya malam ya fad'a akan wannan al'amarin kuma dole ne a dakata da daurin aure tukkuna aga abinda ubangiji ya lullube amma ni yanzu tunanin ta inda zan tunkari Alhaji Nura da maganar nake."

Gwaggo tace."Muma dai tun dazu muke wannan nazarin mutumin nan fa ya riga ya gama duk wani shirye-shiyen sa lokaci kawai yake jira idan anje masa da wata magana dole yayi zargin wani abu.

Kafin Kawu yace wani abu kira ya shigo waya ta Alhajin ne da sauri na fita daga dakin da wayar a kunnena.

Soro na tsaya muka gaisa kamar ko da yaushe kafin yace."Sa'ida wasu harkoki ne na kasuwanci suka taso min a yanzu dama kuma tun watanni uku da suka wuce nake tsammanin gudanar da harkokin sai yanzu Allah ya bani iko sabida haka nake baki hakuri akan abinda zakiji na fada miki a yanzu." a sanyaye nace."Haba Alhaji ai babu komai ina sauraranka.''

Yace."Yauwa 'yar albarka inaso za'a d'aga daurin auran mu sai nan da wata uku ko hudu saboda a cikin satin nan nake so na tafi chana domin company da muke harkokin mu a tare suna bukatata a kusa wannan dalilin yasa nace bari na kira ki a waya na fada miki kafin nazo.'' Ajiyar zuciya na sauke ina godewa Allah a raina babu shakka dukkanin abinda yake faruwa da ikon Allah ne.


Nace."To babu komai Alhaji kada ka damu ai kamar yau ne kaje ka dawo insha Allahu ina zaman jiranka kuma inayi maka fatan alkairi da nasara a rayuwarka."

cikin jin dadi ya amsa da ameeen Sa'ida insha Allahu a satin dana dawo za'a daura auran ki tare a dakin ki.'' mirmushi nayi nace"To Alhaji Allah ya nuna mana lafiya." Ya amsa da ameeen Gimbiya bari na barki ki huta ko insha Allahu gobe zan shigo da wuri muyi sallama."

Nace."To shikkenan sai kazo din a gaishe min da yarana." ya amsa da fadin"Zasuji da kyau insha Allah." sallama mukayi da juna na kashe wayar na koma cikin gidan.

Cikin nutsuwa na nemi guri na zauna ina kallonsu duk sun shiga yanayi na damuwa nace."Gwaggo ku kwantar da hankalin ku Allah ya kawo mana mafita domin kuwa yanzu muka gama waya da Alhaji Nuran yake sheda min cewa tafiya ta taso masa zuwa chana sabida haka za'a daga daurin aure sai bayan ya dawo wata uku zaiyi a can ko hud'u insha Allahu yace cikin satin da ya dawo sai a daura auran.

Gwaggo tace."Kai alhamdulilahi amma naji dadin wannan magana wallahi dama bayan fitar ki muna ta tararrabin yanda za'ayi a tunkareshi da maganar sai gashi cikin sauki Allah ya kawo mana mafita."

Kawu yace."amma kuma kamata yayi yazo ya same ni mu tattauna maganar a tsakaninmu.

Nace."Eh hakan yace insha Allahu gobe zai zo kuyi maganar." Gwaggo tace."To kaga shikkenan sai ka jira zuwansa kada ka fita kuma kuyi sa'bani."

Yace."Insha Allahu zan zauna nayi jiran zuwan nasa. Mi'kewa yayi da fad'in zai fita ya sha iska a waje." Gwaggo tace."Haba ai zafin ya isa muma yau kwanciyar tsakar gida zamuyi ai." Kawu yana kokarin saka takalmansa yace."Hakan yayi gwaggo ke Sa'ida sai ki fito ki dan gyara muku inda zaku kwanta din." Nace."To shikkenan." mikewa nayi na fito tsakar gidan domin na gyara mana inda zamu kwanta.


To kamar yanda dai Alhaji Nura yayi alias a run zuwa gurin Kawu su tattauna maganar haka din ne ya kasance domin Kawu a daran ranar ya kira wayar Alhaji Shamsu mijin mahaifiyata ya sheda masa dukkanin abinda yake da akwai Alhaji Shamsu yace babu damuwa insha Allahu zai fito da wuri ayi zaman dashi.

Sun tattauna abinda ya dace a tsakaninsu tinda dukkaninsu ba yara bane sun san harkokin kasuwanci mussaman Alhaji Shamsu shi ya 'kara karfafawa Alhaji Nura gwiwa akan tafiyar tasa amma kuma sai yace mai zai hana kawai a daura auran idan yaso in ya dawo sai ayi maganar tarewa.

Lokacin da yayi wannan maganar Kawu Iro hankalinsa ne ya tashi yayi shuru yana sauraran yaji amsar da zai bashi Alhaji Nuran yace yafi so ayi komai a lokacin da yake nan." Alhaji Shamsun yace to shikkenan babu damuwa Allah yasa hakan shi yafi alkairi."

Dukkaninsu suka amsa da ameen ya Allah ." suka rabu cikin mutumci da girmama junansu.


****
*Bayan sati biyu*
Khalid da Salmanu mota suka bi da kayansu da kuma guzirin su domin zuwa Lego's dan su nemi aikin yi su kuma cigaba da gudanar da harkokinsu na buga kwallo a cewarsu duk inda ta fad'i sha ne, Salmanu lafiya lau suka rabu da mahaifiyarsa da da sauran 'yan uwansa shi kuwa Khalid babu sa albarka uwa da uba ya d'auki irin wannan tafiya aikuwa cikin dare suna tsakiyar titi motarsu na sharara gudu *da'u fataken dare!* ('Yan fashi) suka tare musu mota yana ganin haka yayi saurin bude wayarsa ya cire sim card dinsa yasa a bakinsa ya danne a kasan harshen sa......'Yan fashin suka dinga sakin harbi! ta ko'ina suka sanya dik wa'inda suke motar mata da maza suka fito suka kwanta a tsakiyar titi duk motar da ta karaso gurin sai sun tsayar da ita sun fito da mutanan ciki.....Daya bayan d'aya suka dinga binsu suna kar'be musu wayoyinsu wa'inda sukayi gardama a cikinsu suyi musu dukan mutuwa ganin haka yasa mutane suka tsorata domin tsira da ransu da lafiyarsu suka dinga mika musu wayoyinsu da jakkunan kayansu da guzurinsu.

Sai da suka kwace musu komai suka loda cikin motocinsu sannan suka dawo gurin da suke kwance suna haskasu.........Babban cikinsu ya tsuguna kusa da wata mata ta rungume d'anta sai kuka take ta hada uban gumi jikinta sai karkawa yake.

Fuskarta ya haska sosai yake 'karewa jikinta kallo ya sauke ajiyar zuciya ganin akwai mamora a jikinta yasa ya kira daya daga cikin 'yan uwansa ya nuna masa ita da fad'in "Zamuje da ita mu biya bukatarmu."

Matar ta fashe da kuka tana waiwayen bayanta mijinta take nema can ta hangoshi ya rarrafo gurin cikin fitar hayyaci yace."Oga dan Allah kada kuyi mata wani mummunan abu ni ne mijinta tunda dai kun samu abunda kuke bukata shikkenan."

Wani wawan mari ya kwad'a masa a take hancinsa ya fashe da Jini yasa kan bindigar dake hannunsa ya dinga dukan kansa da mugun karfi har sai da yaga galabaitar dashi tukkuna ya kyaleshi ya fad'i a gurin jina jina dashi! matarsa da 'yarsa sai kuka suke a kansa.........Fizgo hannunta yayi ya hau janta a k'asa ta dinga ihu tana fad'in "Ku taimaka min kada ku bari ayi zina dani." 'Kwakkwaran motsi babu wanda yayi a gurin mijin nata ya rarrafa ya mike domin ceton matarsa dan fashin ya kai masa wawan duka ya fadi a gurin a sume.

Khalid yayi shahada ya mike da saurin gaske yace."Kai bawan Allah kaji tsoron Allah kuji tsoron ranar had'uwa dashi shin wai baka san matar aure ce ba kada kuyi zina da ita da nauyin aure a kanta Allah ba zai barku ba.

A sukwane! sukayo kansa dukkaninsu! Salmanu ya shiga tsananin tashin hankali ya dinga jan hannun Khalid din wai ya tsuguna ya basu hakuri Khalid ko gezau beyi ba yana tsaye suka karaso gurin babban cikinsu ya daga hannunsa zai kwada masa mari Khalid da sauri ya rike hannun.......Cike da mamaki jama'ar gurin suke kallonsa. Kafin kiftawar ido yaji saukar wani mugun duka a tsakiyar kansa...ihu! ya kurma yayin da lokaci guda yaji wani dummmm! a kunnesa tangad'i ya farayi Salmanu ya mike a zabure! yayi nufin rikeshi Danfashin da yake bayansa ya bangajeshi ya fad'i! 'katon dutsen dake hannunsa ya sake bugawa Khalid a kansa a take ya fad'i a gurin ya suma gefen kansa ya fashe sai zubar da jini yake........Fitilolinsu suka kashe gurin yayi duhu! dumd'um! suka ja matar nan tana kurma ihu! suka sanyata a motarsu suka tafi da ita.....

*SADAUKARWA NE GA IYAYE NA BIYU*

*FATIMA MUSA (MOMMY NIJAR)*
*TARE DA*
*USAINA ABDUL-MALIK ISA (KAITA)*
*(HAJIYA BABBAH)*

*_Ha'kika ina Alfahari daku da irin kaunar da kuke min.🥰🤝🏻💜_*





*35&36*
Cikin tsananin tashin hankali Salmanu ya nufi inda Khalid ke kwance ya tarairayoshi jikinsa yana kiran sunansa, Jama'ar dake gurin suka rufo kansu gurin ya hargitse da kace nace kowa yana fadar albarkacin bakinsa akan abinda ya faru Salmanu shi dai babban damuwarsa abokinsa ya farfado! direban motar ne ya karaso gurin hannunsa rike da jarkar ruwa ya bude da saurin gaske ya shiga tuttulawa khalid ruwan a jikinsa, yana gamawa dashi da sauri ya karasa inda mijin matar nan yake a kwance shima ya daga jakar ruwan ya kwara masa a jikinsa cikin ikon Allah gabad'ayansu suka farfad'o cikin jigata Khalid ya dinga kiran sunan Allah yana jin yanda kansa ke wani irin sarawa! hannu yasa saman goshinsa ya shafo jini Salmanu yace."Sannu Khalid ai ka auna arziki." kallonsa kawai yayi ya juya yana kallon jama'a dake gurin suna surutai da hayaniyar kowa sai gyara jakar kayansa yake Yace."Salmanu ina matar nan take bana so su cutar da ita."

Salmanu yace ."Sai dai hakuri ai sun tafi da ita."

Kansa ya dafe yana kiran sunan Allah! Ihu! mai karfi sukaji da sauri ya dago kansa mijin matar nan ne yake kurma ihu mutane na rirrikeshi wai sai ya tafi neman matarsa jamaa sun hana shi ga 'yarsa sai sandara ihu take itama.

Khalid cikin karfin hali ya mike Salmanu yace."Ina zakaje Khalid kai ma fa kana bukatar taimako.

Yace."Salmanu mutumin can ya bani tausayi zanje na rarrashe ne."

Kafin Salmanun yayi magana ya bar gurin Salmanu yabi bayansa zuwa inda mutumin ke zaune jamaa sun kewaye shi suna bashi hakuri.

Khalid ya dafa kafad'arsa ya dinga rarrashin sa kancewa yayi hakuri ya barwa Allah insha Allahu Allah ba zai basu nasara akan matarsa ba.....Yana kuka yace."Matata ciki ne da ita d'an wata uku gashi bata da cikakkiyar lafiya mahaifiyarta na Lego's ta matsa min da cewa tana so taje ta gaisheta hakika dana san wannan tsautsayin zamu hadu dashi to da ban amince da tafiyar nan ba.

Khalid yace."Kayi hakuri abokina dukkanin abinda kaga ya faru da kai da matarka rubutacce:ne daga Allah kayi mata addua kawai akan Allah ya ku'btar da ita.

Kansa ya sunkuyar kasa hawaye masu zafin gaske suna zubo masa hakika yana son matarsa so mai tsanani yana jin tsoron 'yan fashin nan su haike mata su kasheta da wahala.


A firgice ta tashi zaune tana rarraba idanuwanta a dakin kafin ta fara lalube kan shimfid'arta salati takeyi a zuciyarta tana kiran sunan Allah.

Fitilar ta ta kunna dakin yayi haske jiki a sanyaye ta mike ta dauki buta ta fita bandaki ta shiga ta kama ruwa ta fito garin yayi tsit Allah yana saukar da ikonsa.

Alwala ta d'aura ta shiga dakin ta gyara dadduma ta tayar da

Please Login or Register in order to submit comment