Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sai ya zuba ruwa a kasa yasha.


Gwaggo ta dinga girgiza kai tana fadin."Kai amma wannan al'amari beyi dadi ba Khalid kuma bai kyauta duk da khalid ya kasance dan uwanki amma ai bai cancanta yana baligi irin wannan ba ya shiga gidan matan aure ba tare da neman izina ba dik abinda Alhaji Nura yayi masa na hukunci daidai ne tunda shi ya taka sharia.

Nace."Gwaggo to me yasa kin san gaskiya kike takewa me yasa bakya ganin Laifin Khalid kuma me yasa kike fifitashi akaina."

Cikin nutsuwa tace."Sa'ida kada ki fassarani da wata manufa mara kyau ni dake da Khalid dik daya kuke a gurina babu wanda yafi wani hakika kuma naji bakin ciki da takaicin abinda yayi saboda haka an jima idan ya kira ni a wayar daya siya min zan nuna masa 'bacin raina."

Shuru nayi ina sha'kar bakin ciki! ta girgiza kanta tana jimanta al'amarin tace."Wai saki uku a gaskiya wannan mutumin bashi da hankali ko kad'an wallahi naji ciwon abinda yayi."

Nace."Gwaggo kiyi min addua kawai Allah yasa haka shi yafi alkairi Allah ya za'ba min miji nagari."

A sanyaye ta amsa da ameeen ya rabbi. dakin ya sake daukar shuru na 'yan mintina kafin nace."Gwaggo kin tuna asibitin da kika rakani a washe garin ranar da Khalid yayi min fyad'e."?

Kallonta tayi a sanyaye tace."Sa'ida bana so naji kina wannan maganar wallahi babu dadin ji.'' Cike da takaici nace."Gwaggo har duniya ta nad'e ba zan daina maganar nan ba kuma ba zan fasa neman sakayya gurin Ubangiji ba."

Babu walwala a tare da ita tace."To naji ya isa haka magana dai tuntuni ta wuce tayar da ita bashi da amfani yanzu sai ki fuskanci abinda yake gabanki.

Nace."Magana ai tuntuni na barwa Allah yanzu ma dalili tayi shiyasa na fada miki abinda yake zuciyata.

Shuru tayi ba tai magana ba, nace."Wannan likitar data duba ni ashe kawar aunty Murja ce."

Kallona tayi da mamaki a tare da ita, na cigaba da cewa "Itace duk ta warware masa komai shi kuma ya fusata ya yanke min wannan hukuncin kafin na fito daga gidan ba kiji irin zagi da cin mutuncin da Yayi min ba."

Hawaye ta goge tace."Ki rabu dashi daga shi har ita likitan Allah zai saka miki kuma duk wanda ya tona asirin wani shima sai Allah ya tona nasa yanzu ni tsorana Allah da Annabi kada maganar ta fita jama'ar gari su dinga yi mana wani irin kallo." Tana kuka take maganar.

Gabadaya naji zuciyata ta karye zafafan hawaye suka fara zubo min nace."Gwaggo insha Allahu hakan ba zata kasance ba idan kuwa maganar ta fita to zan tattara kayana na gudu gurin mahaifiyata."

Kuka takeyi sosai tana kallona had'e da girgiza kanta, Kaina na sunkuyar kasa ina shakar hanci tare da jin tsananin tausayinta a cikin raina.


"Gwaggo ba'kuwa kikayi ne na fito domin d'ibar ruwa naji magana a dakin ki.'' Maganar Ummatu ce ta dawo damu nutsuwarmu tana tsaye a bakin kofar dakin hannunta ri'ke da labule.


Ido muka had'a tace."Au ashe Sa'ida ce." Nace."Eh Ummatu Ina wuni ya gida."?


Ta amsa a sake tana tambayata maigidana....Gwaggo tace."Rabi wane maigida kike tambaya bayan ya sake ta.

Da sauri tace."Gwaggo ban gane maganarki ba." Tace."Ina nufin Alhaji Nura ya saki Sa"ida saki uku."

Da sauru tace."Subahannallahi Sa'ida garin ya haka ta faru me kikayi masa."?


Gwaggo a d'an hasale tace."Rabi har kin manta ashe."? Kallonta tayi jikinta duk yayi sanyi Gwaggo ta cigaba da cewa"Ko wane namiji dai yana kulafucin wannan abu (budurci) to da Alhaji Nura ya tabbatar da cewa Sa'ida bata dashi shine ya yanke shawarar sakin ta."


Ummatu shuru tayi jikinta duk yayi la'asar Tace."To amma me yasa tun farko beyi magana ba sai da tayi wattani a gidansa Gwaggo anya wannan ce matsalar."

Girgiza kanta tayi tace."Rabi wannan ce matsalar ko kinqi ki kin so sai matsala ta biyu ashe Khalid duk jan kunnansa da nayi akan kada yaje gidan mutumin nan sai da yaje saboda tsabar wuce gona da irin nasa har 'kuryar daki ya shiga.

Ummatu gabanta na fad'uwa tace."Gwaggo a yaushe Khalid din yaje gidan bayan yau satin sa uku da tafiya.

Tace."A ranar da zai tafi yaje da safe kuma Alhaji Nuran ya ritsa shi a dakin baccin sa Rabi wace irin masifa yaron nan yake so ya janyo mana


Ummatu taji 'kwalla ta cika idonta Itakam ta rasa wace irin masifa ce wannan wane irin kwadayi da kulafuci yaron keyi akan wacce bata dace dashi ba, aranar da Gwaggo take masa fada akan kada ya kuskura yace zaije gidan tana jinsu har ta shiga dakin tasa baki tayi masa gargadi sosai ashe jinsu kawai yake da kunne ya mayar dasu shashashai sai da yaje ya dauko musu magana.



Kai ta kad'a ta bar gurin ba tare da tace komai ba, Gwaggo tace."Duk kauce-kaucen da za kiyi dole sunan Khalid ya fito a cikin mutuwar auran Sa'ida."


Koda kawu ya dawo ya sameni a gidan bai kawo komai ba a cikin ransa muka gaisa a nutse ya shiga gurin sa domin cin abinci da hutawa.

Gwaggo bayan ta tabbatar da cewa yaci abinci ya huta sai ta fito tsakar gida tana 'kwala masa kira, da sauri ya bude kofar gurun nasu ya fito yana fadin"Gwaggo lafiya dai ko? Ina S'ida ina fatan ta tafi gidanta.


Tace."Sa'ida tana nan ai kuma ta dawo kenan sabida saki ukun da mijin nata ya rattaba mata."

Kawu wani irin gumi! ne ya jika masa riga baki na rawa yace."Gwaggo me yasa mutumin nan zaiyi mana haka? me yarinyar nan tayi masa da har zaiyi mata irin wannan hukuncin

Kai tsaye tace "Munafurtar sa akayi Ibrahim me yasa tun farko baka sameshi ka fada masa abinda ya faru ba.

Yace." Gwaggo ya za'ayi na tonawa yarinyar nan asiri? wane namiji ne kike gani zai ji wannan al'amari ya yarda da auran."

Tace."To ai *"GA IRINTA NAN!* An yanka ta tashi domin dai likitar data duba ta a washe garin ranan da al'amarin ya faru To itace ta tabbatar masa da gaskiyar lamarin bayan haka kuma ashe Khalid a ranar da zai tafi sai da yaje gidan saboda kuma wace gona da iri irin nasa har uwar daki ya b ita a takaice ma dai sai da maigidan ya shiga ya same shi Ibrahim ka fad'a min shin Khalid me yake nufi da aikata hakan."?



*SADAUKARWA NE GA IYAYE NA BIYU*

*FATIMA MUSA (MOMMY NIJAR)*
*TARE DA*
*USAINA ABDUL-MALIK ISA (KAITA)*
*(HAJIYA BABBAH)*

*_Ha'kika ina Alfahari daku da irin kaunar da kuke min.🥰🤝🏻💜_*




*60&61*
Kawu Iro shuru yayi a gurin tamkar ruwa ya cinyeshi gabadaya al'amarin ya daure masa kai ya rasa ma bakin magana shi kam ya rasa wane irin yaro Allah ya bashi. Gwaggo ta kalleshi da fadin"Ibrahim kayi shuru ka kasa magana." Zazzafar ajiyar zuciya ya sauke yace."Gwaggo al'amarin ne ya daure min kai shiyasa kikaji nayi shuru na kasa cewa komai wato Khalid yayi hakane domin ya kashe mata aure ta fito daga gidanta shi ya aureta hakane ko ba haka bane." ? Gwaggo tace."Ato nima abinda nake zargi kenan.....Ummatu ta karaso gurun da fad'in "Dan Allah Gwaggo kuyi wa al'amarin nan kyakykyawar fahimta kada ku zargeshi da mummunar manufa tunda kun san dai maganar auransa da Jamila tayi nisa to mai zai sanya ya kashe auran Sa'ida wannan magana tuntuni ta mutu domin ya hakura ya kar'bi Jamila a matsayin matar auransa.

Kawu yace." Rabi ke kika haifi Khalid amma har yanzu baki san halinsa ba yaron mugun Hatsabibi ne." Cikin bacin rai yayi maganar....Gwaggo tace."Kada kayi masa baki Ibrahim ka daina kiransa da wannan suna addua za'ayi masa.

Yace."Gwaggo idan wannan ce manufar Khalid akan Sa'ida to ni mutukar ni na haifeshi ba zan lamunce masa auranta ba Allah zai kawo mata miji daidai da ita ta aura."

Jin abinda ya fada Yasa Ummatu jin dadi a zuciyarta gurin ta bari tana godewa Allah. Gwaggo jiki a sanyaye tace." Allah ya kyauta ya za'ba mana abinda yafi alkairi." amsawa yayi da amin ya kama hanyar fita yana kokarin fito da wayarsa.


Kofar gida ya zauna yana goge gumi hankalinsa a tashe ya nemo number wayar Alhaji Shamsu ya kirashi domin ya sheda masa halin da ake ciki.


Alhaji Shamsu hankalinsa ya tashi jin irin bayanin da Kawu Iron ke masa yace."Ibrahim na jima ban ji 'bacin rai irin na yau ba kuma banta'ba tsammanin Alhaji Nura zaiyi mana wannan wulakancin ba shin me yarinyar nan tayi masa da har zaiyi mata saki uku."?

Kawu ya goge gumi yana dawurwura hakika yana jin nauyi da kunyar fada masa dalilin da ya janyo sakin....Alhaji Shamsu yace."Ibrahim ka kwantar da hankalinka Alhaji Nura bamu ya tozarta ba kansa ya tozarta kuma abinda kayi wa d'an wani kaima sai anyi wa naka.

Kawu yace."Kwarai da gaske Alhaji maganarka haka take." Yace."Yanzu yanzu zan kirashi a waya dole ya fad'a min dalilin da yasa ya saki yarinyar nan domin hankalina gabadaya ya kasa Kwanciya inata tunani babu shakka ruwa baya tsami banza.


Jiki a mace Kawu yace."To shikkenan Alhaji duk yanda kukayi dashi sai ka kira wayata ka sanar dani."


Alhaji Shamsu yace."Insha Allahu zan kaji daga zarar mun tattauna magana dashi."
Sallama sukayi kowanne ya kashe wayarsa.


Washe gari da safe Alhaji Shamsu ya zaunar da matarsa kafin ya fada mata abinda yake faruwa sai da yayi mata nasiha mai ratsa jiki sannan ya sheda mata abunda ya faru da 'yarta.


UmmuHabiba fashewa tayi da kuka tana girgiza kanta take fadin."Innalillahi wa'ina ilaihi raji'una Alhaji wannan wane irin wulakanci ne? saki uku a lokaci guda akan wane dalili ashe dama mutumin nan auran sha'awa yayi."

Alhaji Shamsu ganin hankalinta ya tashi tana kuka ya shiga rarrashinta yana bata baki har sai da tayi shuru tana goge fuskarta yace." Dama yanzu nake tunanin kiransa a waya naji bayani daga bakinsa domin tabbas akwai dalili mai karfi da ya janyo hakan."

Tace."Eh ai gwara ka kirasa a wayar yayi mana bayani muji abinda ya janyo wannan cin mutuncin.

Wayarsa ya dauka ya nemo number Alhaji Nuran ya shiga gurin kira.

Yana kokarin fita kasuwa kiran wayar ya sameshi ya fito da ita daga aljihu yana dubawa, ganin number Alhaji Shamsu yasa yaja tsaki! aunty Murja ta kalleshi da fadin"Lafiya dai.''? Yace.''Mahaifin yarinyar nan ne Sa'ida." shuru tayi bata ce uffan ba har wayar ta katse wani kiran ya sake shigowa.

Tace."Kayi hakuri ka dauka mana kaji abinda yake tafe dashi a yanzu dai ai babu wata magana tunda saki uku kayi mata."


Wayar ya daga yasa a kunnensa had'a da sallama.....Alhaji Shamsu ya amsa masa a nutse suka gaisa da juna kafin yace."Alhaji Nura wane gagarimin laifi yarinyar nan tayi maka kayi mata saki uku a lokaci guda."?

A tur'bune yace."Kana so kasan dalili kenan."? Da sauri yace."Eh ai sabida inaso nasan dalilin yasa na kira wayarka domin dai nasan babu shakka ruwa baya tsami banza."


Ajiyar zuciya ya sauke kafin yace."Ai Alhaji kune da laifi kuma banta'ba tsammanin zaku munafurce ni ba ashe yarinyar nan sai da ta gama watsewa da lalattatun maza a waje ku rufe min na aureta.

Cike da mamaki yace."Wace irin magana kake Alhaji Nura ban fahimci inda ka dosa ba yarinyar nan Sa'ida da kima da mutuncinta muka aura maka ita."


Da sauri yace." Waye ya fada maka haka? bari ma dai na daina rufe maka magana a ranar dana kusanci yarinyar nan na gane ba budurwa bace fanko ce. lokacin dana turketa ina tuhumarta tana kuka ta kawo min wasu hojojji wanda suka kashe min jiki har na yarda da ita na cigaba da zama da ita, a kwanakin baya yaron da nake zargin shi ya lalata ta yazo har cikin gidana sabida tsabar cin fuska har cikin d'akina na same su nan ma raina ya 'baci sosai na nuna mata kuskuranta hakuri ta bani ta nuna min babu wata alaqa a tsakaninsu sai gashi jiya Dr Maryam likitan ta ta tabbatar min da gaskiyar magana kuma itama Sa'idar ba tayi musu ba akan abinda ake zarginta dashi al'amari ya fusata ni sosai kuma naji takaicin abinda kukayi min na ha'inci wannan dalilin yasa na yanke alaqar aurena da ita."


Alhaji Shamsu ji yayi gumi na tsatstsafo masa bakinsa ya bushe qamas da kyar yace."Alhaji Nura ka dai fad'i wata hujjar amma ba wannan ba yarinyar nan Sa'ida bata san ko wane namiji ba lafiya lau muka aura maka ita kadai kara binkice akan maganarka."

Alhaji Nura yace."Alhaji a yanzu dai babu batun tashin-tashina a tsakaninmu tunda dai na yanke alaqar data had'a mu shikkenan magana ta 'kare dan Allah kada ka 'kara kiran wayata kazo min da maganar Sa'ida na sake ta saki uku babu ni babu ita."

A fusace! Yace."To sai me don ka saketa Alhaji Nura akwai maza a duniya da zasu aureta kuma wallahi ina mai tabbatar maka da cewa sai kayi nadamar abinda ka aikata."
Yana gama maganarsa ya kashe wayar sam baya bukatar sake jin wata magana daga bakinsa sabida yayi masifar 'bata masa rai."

Ummu Habiba kallonsa kawai take ko beyi mata bayani ba ta fahimci komai tunda wayar a hands free take.....Gumin goshinsa ya goge yace."Saboda kawai yana so ya rabu da yarinya sai yayi mata kazafin zina Habiba kina jin abinda mutumin nan yake fada akan yarinyar nan Sa'ida wai bai sameta da budurci ba to bai samu budurcinta ba me yasa tun farko bai fada ba sai yanzu da tayi watanni a gidansa ni nafi tunanin cewa ya gaji da zama da ita ne shiyasa ya shirya wannan maganar."

A sanyaye tace."Ni kaina al'amarin ya daure min kai kuma duk bayanin da yayi maka naji da kunnena dama can ba son Allah da annabi yake mata ba sha'awarta yake."

Ya dauki hularsa yasa da fad'in "Ai babu komai duk wanda yayi nagari kansa kiyi hakuri kuma ki cigaba dayi wa yarinyarki addua insha Allahu Allah zai za'ba mata abunda yafi alkairi a rayuwarta.

A sanyaye ta amsa da " Ameeen Alhaji nagode sosai da kulawar ka akan yarinyar nan." Yace."Habiba ni na dauki Sa'ida tamkar ni na haifeta saboda ina tausayawa maraicinta ina kuma kwadayin ladan kula da maraya sabida haka kada ki damu zan tsaya tsayin daka akan yarinyar nan."
Tace."To shikkenan Alhaji Allah ya shige mana gaba kai kuma abinda kakeyi na alkairi Allah ya baka lada." ya amsa da ameeen ya Allah yana kokarin fita sai ta mike a nutse tabi bayansa domin taka masa.

Koda ta dawo gidan dakinta ta shiga ta zauna kan kujera babu kuzari a tare da ita ta dauki wayarta number 'yar tata ta nema ta shiga gurin kira.

Lokacin data kira ina bandaki ita kuma Gwaggo bata iya da waya ta ba kira ta dinga kwala min da fadin na fito ana kiran wayata.

A gugurje na fito daga bandakin na ajiye butar hannuna, wayar ta miko min da fadin."Kinga har ta katse sai ki duba kiga ko wanene idan Khalid ne kada ki daga ki shareshi kamar yanda nake masa idan ya kira ni."

Murmushi kawai nayi ba tare da nace mata komai ba na nufi dakin da wayar a hannuna ina dubawa

Ganin number Ummana yasa da sauri na zauna gefan gado na shiga gurin kira da alama wayar tana hannunta domin sau daya tayi ringing ta daga, yanda naji muryarta a sanyaye yasa nima jikina ya mutu a nutse na gaisheta ta amsa tare da fadin."Ya mukaji da wannan abu."

Nace."Alhamdulillahi Umma." Tace."Kiyi hakuri kinji ko kowane mutum akwai irin kaddararsa kisa a ranki cewa dukkanin abinda ya faru da rayuwarki kaddara ce insha Allahu wataran sai labari."

Hawayen da suka zubo min na share murya na rawa nace."Insha Allahu Umma ki taya ni da addua akan Allah ya za'ba min abinda yafi alkairi."

Tace."Sa'ida addua kullum akanta muke Ubangiji Allah ya amsa mana adduo'inmu na alkairi." cikin sanyin murya na amsa da ameeen Ummana." Tace."Ki gaishe min da Gwaggo da kyau." nace."To zataji insha Allahu.'' Sallama mukayi da juna......Gwaggo ta shigo dakin tana fadin."Dawa kike waya ne."? Nace."Umma Habiba ce tace ma a gaisheki.''

Kallona tayi da fadin."Ita kuma a ina ta samu labarin abinda yake faruwa."? Nace."Watakila ko Kawu ya sanar da mijinta ne.''

Tace."Eh hakan zata iya yuwu wa Allah dai ya kyauta.'' cikin mutuwar jiki na amsa da "ameeen ya Allah.


*BAYAN SATI DAYA*
Na d'an samu nutsuwa hankalina ya dawo jikina sai nayi tunanin kiran Hauwwa a waya domun na sheda mata abinda yake faruwa..........Sosai Hauwwa tayi mamakin al'amarin daga bisa ni tace." Yanzu dai kinga ne abinda ke da akwai ko? a yanzu dai kin fahimci cewa auran Babban mutum bashi bane tunda gashinan wata shida har anyi an gama ya rattaba miki saki uku wallahi da Khalid kika aura ba zaki fuskanci wannan matsalar ba babban tashin hankalin ma mutumin nan yayi miki sanadin aikin ki."

Nace."Ni wallahi a yanzu shine babban abinda yake damuna wata shida bai zama lallai idan na koma aiki su kar'be ni ba......Hauwwa tace ko zasu kar'be ki sai an kai ruwa rana amma babu matsala ni zanyi miki kokari kin san Shugaban makarantar yana zawarcina zanje har ofis d'insa na lalla'ba shi." Nace."Yawwa aminiyata nagode kwarai dan Allah kiyi min kokari." Tace."Kada ki damu mybe ma gobe idan mun tashi na shigo domin mu tattauna." Nace."To shikkenan sai kin shigo Hauwwa nagode Allah ya bar zumunci." ta amsa da ameeen ya Allah ki gaishe min da Gwaggo." nace."Za taji insha Allahu."

Wayar na kashe ina jin sassauci a cikin zuciyata.....Gwaggo dake kad'i ta kalleni da fad'in." Naji kina magana komawa gurin aiki Sa'ida ke yanzu sai ki koma cikin maza bayan zargin da ake miki."?

Nace."Gwaggo kina so kenan na zauna a gida babu aikin fari bare na baki ko."? tace."Oh!o ni nafi so ki samu miji kiyi aure Sa'ida.'' Nace."Gwaggo kada kiyi min maganar aure a yanzu domin dai bashi ne a gabana ba'' Tace."To ai shikkenan idan lokacin auran yazo sai ki hana Allah ikonsa." shuru nayi mata domun nasan neman magana take.....Ummatu ta daga labulan dakin da waya a hannunta tana fadin."Gwaggo ga d'an d'akinki ya kira waya wai yana so ku gaisa.'"

Tace."Ke Rabi raba ni da wannan yaron ki fada masa ni bana bukatar magana dashi a yanzu." Tace."Gwaggo me yayi zafi."? Tace."Rabi duk irin kulawa da rarrashin da nakewa yaron nan besa yaji maganata ba to ni kam me zaice dani ai na daina wahalar da kaina a kansa."
Ummatu jikinta a mace ta bar gurin...Gwaggo taja tsaki da fad'in "Kawai kin d'auko wata kod'add'iyar yarinya kin nana masa ya aura yarinya sai kace zabiya tana yawo sai kace takand'a babu kumari babu 'kira da cika irin na mata.'"

Dariya nasa ina kallonta nace."Gwaggo kefa naji kina kod'a yarinyar kina cewa sun dace da juna gata kyakkyawa mai kuruciya."

Tace."Ai ni banta'ba 'karewa yarinyar kallo ba sai ranar da ta zo gaishe ni lokacin yana nan be tafi ba ranar nayi azimin litinin yaje ya dauko ta wai tazo tayi min sannu da shan ruwa tsabar haushi ko kayan data kawo min ban duba ba na bawa al'amajirai."

Nace."Yanzu dai kina nufin bakya kaunar al'amarin kenan."? Tace."Yo Sa'ida me Jarumi zai samu a jikin yarinyar nan jiki a bushe ko'ina babu kumari sai qashi shi kuwa kato dashi tubarkallah ai yana da kyau ya samu 'koshashshiyar mace yanda zai more kuruciyarsa.

Dariya nayi sosai ina kallonta nace."Gwaggo wai dan Allah me yasa bakya kunyar fadar magana ne? Tace."Sa'ida wace kunya kuma ai gaskiya na fad'a.'' Nace."To Allah dai kyauta Gwaggo ni dai shawarar da zan baki ki kauda kanki daga al'amarin nan idan kika ce zaki zuga Khalid ya bijirewa umarnin mahaifiyarsa zaki jefe shi a masifa sannan Ummatu da 'yan uwanta zasu dinga jin haushinki."

Tace."To dama Sa'ida ni ina ruwana yaje ya aureta nasan duk daran dad'ewa sai ya sake aure tinda ni nasan halin fitinarsa wannan siririyar yarinyar ba iyawa za tayi dashi ba."

Ina dariya nace."Gwaggo ai ba'a nan take ba sai kiga mace mara qiba amma sai ki sameta da juriya da kuzari ita kuwa mai qibar sai ki sameta da raki da rashin juriya.''

"Ummm! tace ta cigaba da abinda takeyi a jiyar zuciya na sauke a hankali nace." Gwaggo ni dashi Allah ya za'ba mana abinda yafi alkairi ki tsananta dayi mana addua.'' Tace."Insha Allahu Addua ba zamu bari ba har sai ranar da numfashi ya fita daga gangar jikinmu."


[3/24, 11:39 AM] +234 703 008 7807: *SADAUKARWA NE GA IYAYE NA BIYU*

*FATIMA MUSA (MOMMY NIJAR)*
*TARE DA*
*USAINA ABDUL-MALIK ISA (KAITA)*
*(HAJIYA BABBAH)*

*_Ha'kika ina Alfahari daku da irin kaunar da kuke min.🥰🤝🏻💜_*




*66&67*
Gefan zaninta tasa ta share hawaye da fadin."Ai shikkenan Sa'ida tunda haka zaki ce dole nayi hakuri da hukuncin da kika yankewa kanki amma ni sam bana sha'awar ki da wannan mai ba'kar fuskar." Kallonta nayi ina mamakin maganarta Gwaggo idan bata son abu komai kyawun sa ta dinga kushe shi kenan amma in banda haka meye laifin Yaya Aminu kyakykyawa ne sosai Khalid din babu abinda zai nuna masa sai haske fata.

Nace."Gwaggo maganar nan ta wuce don Allah ki daina kuka da damuwa ki cigaba da addua ni da Khalid din Allah ya za'ba mana abunda yafi alkairi Gwaggo duk sonki da na auri Khalid idan Allah bai nufa ba dole ki hakuri kin san komai nufi ne na ubangiji mussaman sha'ani na aure ba'a katsalandan a ciki kawai ki roki Allah alkairi sai kiga ya tabbatar miki.

Tace."To me kika ji na k'ara cewa? ai magana kuma ta wuce wannan yaro Khalid kuma Allah ya sanya masa dangana."
Ameeen na amsa ina kokarin mi'kewa tsaye


*Bayan sati biyu*
A tsakanin kwanakin Yaya Aminu yazo guri na mun gaisa sosai kuma yanda yake nuna kulawarsa a kaina yasa na gane cewa lallai ba dole akayi masa ba domin 'karara yake nuna min so da kauna ga uwar hidimar da yake min sai kace hauka ya kawo min sabuwar waya mai kyau da tsada kudi kuwa duk bayan kwana uku ko hudu zan ga alert dubu ashirin dubu talatin har dubu hamsin turo min yake idan nayi masa magana sai yace shine yayi niyya idan inada bukatar ya 'kara min wasu sai nayi magana, al'amarin ya dinga bani mamaki mutuka gidan Hauwwa naje domin mu tattauna maganar dan gaskiya ni kudin da yake bani suna bani tsoro ni ba auran kudi nake so nayi dashi ba nafi bukatar idan na aureshi ya rike ni tsakani da Allah mu zauna lafiya.....Koda Hauwwa ta gama jin bayani na sai tayi dariya tana fadin."Sa'ida kenan ke yanzu saboda rashin wayo da dubara har magana kike masa ya daina baki kudi? to idan ya daina baki wa kike dashi wanda zai baki? komai fa da kika gani yana da lokacinsa saboda haka ki kwantar da hankali Idan kullum zai dinga sa miki million a accont dinki kada kice masa don me kiyi godiya kawai idan baki kar'ba ba wasu can a waje su za su kar'be Yana da kudi to me zaiyi dasu tunda dai shi bashi da nauyin kowa a kansa ke d'in dama ke zai bawa sai mahaifiyarsa da sauran 'yan uwansa saboda haka ki nutsu ki samu abinda kika samu kafin lokaci ya kure miki."

Shuru nayi ina ta nazarin maganarta tace."Ni wallahi nayi miki murnar auransa domin ta

Please Login or Register in order to submit comment