Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sake zuwa inda take da niyyar zawarcin ta to zamu tsaya gaban hukuma dani kai.''


Alhaji Nura ya kalleshi sheqeqe! yace."Aminu kayi shuru ka daina wata fuffuka ka bari mazaje suyi magana anan gurin kai ka san kanka nima nasan kaina saboda haka dama tsautsayi da kaddara ne yasa har na saketa ka aura yanzu kuma na dawo zan mayar da ita dakinta dan haka kai zan jawa kunne ba kai zaka ja min kunne ba."

Hannu na daga musu murya na rawa nace."Ni dai yanzu dik cikin ku babu wani wanda zan komawa auransa dan haka fad'a da cece kuce bai kamace ku ba kuyi hakuri kowa Allah ya bashi daidai dashi."

Gabad'ayansu suka zuba min ido suna kallona nace."Ni zan shiga gida sai an jima." Yaya Aminu sarkin zuciya a fusace! ya bude mota ya shiga da gudu ya bar gurin.....

Shi kuma da sauri ya tare ni "Haba Sa'ida don Allah kada ki tafi ki tsaya mu fahimci juna mana wallahi nayi nadama na gane kece matar rufin asiri na."


Kallonsa nayi a sanyaye nace."Ni dai yanzu bani da wata magana da kai Alhaji nasan dai kasan babu kyau neman aure a cikin iddah saboda haka ko na 'kare iddah bana tsammanin zan komawa auranka."

Da sauri yace."Idan saboda Murja kike wannan maganar tuntuni na saketa saboda na gane cewa ita din ba matar rufin asiri bace kece matar arziki Sa'ida shiyasa lokacin dana samun labarin mutuwar auranki raina yayi fari tas saboda nasan Allah ne ya amsa addua ta akan ki."

Murmushi nayi nace."Amma naji dadi sosai daka gane gaskiya akan abinda nake fad'a maka dama irin wannan ranar nake so tazo sai dai ina so na tabbatar maka da cewa ni ba zan komawa auranka ba kayi hakuri kaje ka sasanta da matarka."

A marairace yace."Babu maganar sasanci a tsakani na da Murja domin shaidaniya ce ina nadamar auranta."

Ta'be baki nayi nace."To Allah ya kyauta zan shiga gida a gaishe da yara." Da sauri ya sake tare min hanya cikin faduwar gabana nake kallonsa.

Yana kokarin magana motar Khalid ta shigo layin.....A hankali motar take tafiya saboda yanda matasa da yara suka kewaye ta hayaniya gabadaya ta cika gurin da kyar suka bashi guri yayi parking ai yana fitowa suka rufu a kansa hannu kawai yake d'aga musu Salmanu da Salim suka bud'a masa hanya ya wuce duk da haka sai da aka samu wa'inda suka bi bayansu.

Kallo guda yayi mana ya kauda kansa sai da suka karasa bakin kofar gidan ya tsaya suka d'anyi magana da abokansa kafin ya shige su kuma suka bar kofar gidan.

Ajiyar zuciya na sauke gabad'aya jikina yayi sanyi da al'amarin yaron.........Muryarsa naji yana fadin."Sa'ida wannan yaron nan ne ko."? A sanyaye nace."Eh.'' Yace." Duk da ban kasance ma'abocin kallon k'wallon 'kafa ba na samu labarin dau'ka'kar da Allah yayi masa kuma ashe shine ya zama Gwarzon shekara ko."?

Nace."Eh shine kam." Yace."Masha Allah gaskiya na taya shi murna amma yayi aure kuwa.''? Girgiza kaina nayi nace."Beyi ba har yanzu."

Yanayinsa ne ya sauya yace."Don Allah kada kice zaki aureshi domin ke yanzu kin wuce tsaran auransa."

Da mamaki a fuskata na kalleshi da fadin."Ashe dama mace tana wuce sa'ar auran Namiji."?


Shuru yayi yana kallona. Nace." Idan Allah ya kaddara aurena da yaron babu mahalukin da ya isa ya hana ayi saboda haka kai dai kawai kayi addua akan al'amarin." Ba tare da na tsaya na saurari maganarsa ba nayi saurin barin gurin.

Tunda na shiga soron gidan nake jin sautin muryarsa na tashi sama-sama da alama shi da Gwaggo ne domin itama naji muryarta........." Ni wallahi ban ta'ba ganin mara hankalin mace irinta ba me za tayi da wannan shashashan mutumin da har zata fita tana magana dashi." Wannan maganar kunnuwa suka ji "Mara hankali." sunan da ya kira ni dashi ya masifar 'bata min rai.

Muryarta naji tana fad'in "Ai kasan halinta ba'a bata shawara ta dauka ni ai cewa tayi dani Aminu ne ashe bashi bane Alhaji Nura to idan gidansa take so ta koma sai ta d'aura niyya."

Yana kokarin magana na kasara gurin. tsaki yaja da sauri ya bar gurin yana wani irin huci! Kallo na bishi dashi ina mamakin sa.

Magana take kokarin yi na daga mata hannu da fadin."Gwaggo don Allah bar maganar nan raina a 'bace yake a halin yanzu."

Da sauri tace."Ai dole kiyi bacin rai tunda ke ba zaki dinga fad'ar gaskiya ba.

Murya na rawa nace."Wai ke Gwaggo dan Allah duk abinda Khalid yayi daidai ne a gurin ki kina jifa yana kirana da shashasha mara hankali sa'ar sa ce ni kome."?

Shuru tayi min nace."To idan baki masa magana ba wallahi ransa zai 'baci dan ba zan kyaleshi ba.'' Tace." Ai gaskiya ya fad'a me kike kufalaci a gurin Alhaji Nura bayan kin san irin zaman da kikayi dashi a baya."


Nace." Ni dai kawai addua zaki min bana son k'ananun magana ki nema min alkairi a gurin Allah."


Tace."To Allah ya za'ba miki abinda yafi alkairi.'' amsawa nayi da ameeen Na shiga d'akin raina duk a 'bace Gwaggo duk cika bakinta akan Yaron na banza ne zaiyi mata laifi ta gama surutai da cin alwashi a kansa amma daga zarar yazo shikkenan sai ta manta. tayi tai masa rawar jiki tamkar wanda ya sammace ta.


Khalid da asubar fari ya fita motsa jiki can filin wasa na Sharad'a Har muka gama shirye-shiryen mu muka had'a tsaraba muka tafi k'auyen D'ambatta bai dawo gidan ba......Ummatu kuwa yini tayi cikin walwala da farin ciki danginta suka cika gidan suna d'orawa da saukewa.

Sosai ranshi ya 'baci da ya dawo ya tarar da basa nan wayarsa ya dauko ya lalubi number ta ya shiga gurin kira.


Ina kallon kiran nashi naqu d'aga wa domin yayi masifar bani haushi jiya da daddare ya kira ya kai sau hudu ban daga ba ya hakura da kiran. Kwanciya na gyara kan gadon bunun Baba Ladidi ina jiyo hirarsu a tsakar gidan Gwaggo ta samu 'yan uwa sai fara'a da farin ciki takeyi su kuma sun ke waye ta kowanne da kwanon abincinsa suna farin ciki da zuwanta garin nasu na gado.


"Sa'ida wai Gwaggo tace ki fito kici abinci." muryar Jikar Baba Ladadi naji a kunnena.

Ba tare dana tashi zaune ba nace."Kice gani nan zuwa.'' Yarinyar ta juya da sauri ta fita.


Zaune na mike ina gyara dankwalina ya sake kiran wayar......Dauka nayi a hasale nace."Wai menene."? Ajiyar zuciya ya sauke yace."Ki had'ani da Gwaggo za muyi magana."

"Okey." abinda nace kenan na kashe wayar gabadaya na ajiyeta. fita nayi tsakar gidan na samesu suna hira sai raha suke a tsakaninsu.


A takaice dai sai da waya ta tayi kwana hudu a kashe sannan na kunna ina sane nayi masa haka saboda na kuntukawa zuciyarsa.

Text messages d'insa ne suka shigo har uku ko wanne sai da na bud'e na karanta dukkaninsu ba'kar magana ce dan zagi na ne kawai beyi ba ya kira ni da shashasha ya kai sau nawa har da fadin Ban san inda yake min ciwo ba. tsabar bakin ciki da takaici ya sani zubar da hawaye.....nasa hannu na goge da fadin.'"Yaron nan ya gama raina min hankali Allah ka cire min jarabar sonsa a zuciyata.


Aikin gidan ake gadan-gadan domin k'wararrun ma'aikata ya d'auko suka ruguje gidan abinka da tsohon gini irin nada sosai aka samu fili ba tare da 'bata lokaci ba ma'aikata suka fitar da Foundation na zamani aka shiga aikin gidan babu kama hannun yaro........ cikin sati biyu anyi an gama sai abinda ba'a rasa ba gida yayi kyau mutuka ya haske layin Khalid ya kashe kudi sosai gurin aikin gidan Kofar Gwaggo daban Kofar Ummatu daban komai iri daya ya sa musu set na gado da kujeru da sauran abubuwan bukata Ummatu ta dawo amarya gwaggo ma haka. Ummatu ta dinga jin haushin hakan 'yan uwanta na zugata dan kakarsa Baito kishin Gwaggo take sosai ta turkeshi da masifa akan lallai itama sai ya gyara mata gidanta ya sanja mata kayan daki.'' Yace."Shikkenan ta bari idan an kwana biyu zaiyi mata. Hankalinta ne ya kwanta jin abinda yace.


Muna can bamu san abinda ke faruwa ba domin tuntuni ya daina kiran waya ta tunda ba dauka nake ba, kwanan mu ashirin da biyar muka fara shirye-shiryen tafiya.
Tsarabar da mutan kauyen suka had'a mana har taso tayi yawa nace."Baba Ladidi a wace mota zaku kaimu gida da wannan uban kayan." Tace."Ai ba za'a rasa a kori kura ba yanzu idan na fita zan shiga gidan Dije mijinta a kori kura yake ja sai ta fada masa cewa gobe zai dauki kaya ya kai birni.'' Gwaggo tace."To hakan yayi Allah ya kaimu goben." Ta amsa da ameeen ya Allah.


Da daddare ina shirye-shiryen kwanciya ya kira wayar cikin mamaki na dauka ina dubawa ina so naji muryarsa amma kuma ina gudun ya 'bata min rai da ba'kar maganarsa.

Daga wayar nayi a nutse nayi sallama. ya amsa a cunkushe da fad'in." Yaushe zaku dawo gida.''? "Gobe idan Allah ya kaimu." Yace."Okey to kada ku biyo motar haya zan zo na dauke ku domin nima inaso na gaisa da dangi na kuma nuna musu matar da zan aura.''


Nace."Okey to sai kazo din." da sauri na kashe wayar gabana na wani irin fad'uwa! Zai zo ya nuna musu matar da zai aura lallai Khalid wato yana so ya kuntukawa rayuwata tunda ya gane inda na dosa a kansa.

Da kyar bacci ya dauke ni na tashi sukuku don da kyar ma na karya nayi wanka na kimtsa jikina jama'ar garin sai shigowa sallama sukeyi.......Gwaggo kuwa sai share hawaye take sam bata so ta tafi ta bar 'yan uwanta.


Kiran wayarsa ya tabbatar min da cewa ya shigo garin....da kyar nace."Idan ka tambayi gidan Malam mai doki kazo gidan ai babu wuyar kwatance." Yana kokarin magana na datse wayar ina jan tsaki!

Ransa ya 'baci da abinda tayi masa ya ajiye wayar ya cigaba da tafiya da motar a hankali a hankali yana taka busassun kararen ice.

Jamila dake gefensa a zaune tace." Ya Khalid baka ta'ba zuwa bane naji kana tambayar kwatancen gidan."?


Ba tare da ya kalleta ba yace."Tun ina yaro k'arami rabo na da garin kinga kuwa dole kaina ya juye.''


Tace."Eh gaskiya ne kuma amma garin ya burgeni wallahi idan mukayi aure zamu dinga zuwa akai akai muna shan iska." Murmushi kawai yayi ya cigaba da juya sitiyarin motar.

Da kyar suka samu gidan yara yaran k'auyen suka cika bakin motar suna shafawa.

Gwaggo da kanta ta fito domin tar'bar sa sai dai ganinsa tare da Jamila yasa fara'ar fuskarta tayi rauni kadaran kadahan ta amsa gaisuwarta ta jagorance su shiga cikin gidan.

Tsakar gidan akayi musu shimfid'a jama'a maza da mata suka shiga turereniyar zuwa gaisuwa........Ya fito da kudi ya dinda basu yana Jin dadin yanda suke masa addua da fatan alkairi.


Duk abinda ke faruwa ina daki a kwance ina jinsu inaso na fito domin nayi tozali dashi ina jin takaicin na had'a idona da yarinyar.


Baba Larai ta kalli Jamila da fadin" Wato shine kika biyo shi saboda kada na riqeshi na hanashi tafiya ko to komai dai abinki nice Uwargidansa domin itama Gwaggon baya na take bi saboda haka duk ado da kwalliyar ki baki kama kafafuna ba."

Jamila ta dinga Dariya tana 'boye fuskarta ina jinsa yana tare mata da fadin." Ni me zanyi daku duk kun tsufa mussaman ke Baba Ladidi jikin ki duk jijiya da kai duk furfura babu abinda zaki burgeni dashi." Baba Ladidi ta riqe baki tana fadin."Wato wulakanci zakayi min kenan to ai da tsohuwar zuma ake magani kuma dame matar taka tafi ni itama ai bata da wani kumarin kirki dubeta kamar ka busheta tafad'i."

Gwaggo ta ta'be baki da fad'in "Aikuwa haka yaji ya gani sai yaje yayi ta fama watakila kuma a gaba za tayi qiba." Jamila shuru tayi jikinta duk yayi sanyi gabadaya taji wani irin tsanar Gwaggo a cikin ranta.


Sai da zamu tafi tukkuna na fito daga d'akin Uffan bance musu ba na kama hanyar fita Baba Ladidi tace.''Ke kuma ta bizaro babu sallama kinyi gaba na lura da akwai abinda ke damunki domin tun jiya kike nukufurci."


Kallonta nayi da fadin."Baba Ladidi sau dubu kike so nayi miki sallama ne.'' Tace."Ai wannan salamar daban take da sauran wacce mukayi." Nace."To shikkenan mu zamu tafi sai an kwana biyu." Tace."To Allah ya sadamu da alkairi muna jiran tsammani Allah ya kawo miki miji nagari muzo musha biki."
A zucci na amsa da ameeen nayi saurin ficewa daga gidan....

*96*
Jikin motar suka same ni a jingine kauda kaina nayi har suka karaso gurin 'yan uwa da abokanan arziki sun kewaye motar sai bankwana suke mana Gwaggo sai hawaye take sharewa Baba Ladidi na taya ta nace."Dan Allah sallamar ta isa haka Gwaggo shigo mota mu tafi idan kuma baki gaji da zama a garin ba sai ki koma ki zauna mu dai tafiya zamuyi." Baba Ladidi tace."Rufe min baki ja'ira kawai dama ai ke na lura kamar dole akayi miki kika zauna damu komai abinki garin Dambatta shine tushen ki."

Yanda take masifa tana tada jijiyar wuya abin ya bani dariya gaban motar na bude na zauna da fadin."To ni dai na shiga mota Allah ya kaddara saduwarmu." Jamila tayi kicin-kicin da fuska ganin na zauna mata a mazauni ni kuwa ina sane nayi hakan domin da ita dashi dik neman rigima nake dasu.

Gwaggo da kyar 'yan uwa suka barta ta shiga motar Shi kuma ya tsaya yana sallamarsu sosai yayi musu rabon kudi tamkar wanda bai san ciwonsa ba.

Kokarin bude motar yake ya ganta a tsaye tasha kunu yace."Jamila shiga mota mu tafi mana."

A marairace tace."Yaya Khalid ai ta zauna min a mazaunina."

Cikin motar ya duba ya ga yanda na wani 'kame a zaune kaina na dauke ina sake cin magani......Wani irin kwarjini tayi masa ya kalleta da fadin."Ki bata guri ta zauna mana."

Ko kallonsa banyi ba, Gwaggo tace."Jarumi wai tsayuwar me kukeyi ne kai da ita."?

Yace."Gwaggo gata nan tayi mata fin karfi ta zauna mata a gurinta."

Gwaggo tace."Aa ban gane ba wane irin fin karfi kuma."?

Yace."Gwaggo kamata yayi ace Matata itace a kusa dani to ita kuma aunty Sa'ida saboda neman fad'a ta zauna mata a guri."

Gwaggo rai a bace tace."Au motar daga gidansu tazo da ita kenan? ashe har an daura auran naku babu labari to ai shikkenan ke Sa'ida fito mata daga gurin zama sai muje mu samu motar haya inace dai duk mota mota ce kuma zamuje gida kalau."

Kokarin fitowa take daga motar yayi sauri mayar da ita da fadin." Yi hakuri ki zauna." Gwaggo taja tsaki da fadin." Yo idan ba tsiya ba ya za'ayi tace lallai sai ta zauna a kusa da kai inace da ita da Sa'idar duk daya suke.''


Girgiza kansa yayi yace."Aa ba daya suke ba wannan auntyna ce ita kuma wannan wife d'ina."

Tace."Kai kasan wani Wife ka shiga mota mu tafi kawai." Juyawa yayi ya kalleta duk jikinta yayi sanyi yace."Yi hakuri ki shiga ki zauna kusa da kishiyarki Gwaggo muje gida."

Rai a bace tasa hannu zata bude motar yayi saurin bude mata yana rarrashinta hakan yasa taji sassauci a cikin zuciyarta.

Sai da ya tabbatar ta zauna sosai sannan ya rufe motar ya bud'e mazauninsa ya zauna da bisimillah a bakinsa...........A hankali na sauke ajiyar zuciya a cikin raina dama babban burina na kuntatawa yarinyar naji dadi sosai da ranta ya 'baci.


Shuru motar babu mai magana sai dai shi jefe-jefi yana amsa waya tinda ya zauna nake satar kallonsa gabad'aya yaron ya gama tafiya da imani na yau yayi ado cikin manya kaya riga tazarce ta shadda kanshi da hula irin ta kanawa yayi wani kwarjini da kamala babu wanda zai ce bashi da iyali saboda yanda Allah yayi masa suttura ta kowane bangare.


Kasuwar 'yan kaba yayi parking gilashin motar ya sauke yayi magana da daya daga cikin masu siyar da kayan miya yace."Yana son kayan miya masu kyau." Motar ya bude ya fita sukayi magana ya bashi kudin yana tsaye yasa masa komai buhu a bayan motar motar ya kunna muka bar gurun.

Gwaggo tace."Kai kuma me za kayi da uban kayan miya haka."? Yace."Gwaggo ke na siya wa kina min miyar ki mai dadi."


Murmushi tayi tace."Aikuwa nagode za kuwa kasha miya." Yace."Tom nagode Gwaggo yanzu idan mun isa gida zan tura kasuwar Janguza a siyo kaji da zabi ko."

Tace."Aa sai dai ka bari a kwana biyu tukkuna domin mutanan Dambatta sun bamu kaji masu yawa motar tsarabar mu nasan ta isa gida tunda tun safe direban ya tashi."


Yace."Tom mungode kwarai." shuru motar babu wanda ya sake magana ringing din waya ta ya katse shurun.......Alhaji Nura ne saboda mugun haushin yaron yasa na daga wayar murya ta na gyara yanda za tayi dadi na fara magana a hankali-hankali wanda duk 'kwa'kwar mutum ba yanda za'ayi ya ji.


"Eh wallahi nayi tafiya ne zuwa kauye amma yanzu gamu a kan hanya okey kada ka damu Alhaji kasan komai nufin Allah ne." Shuru nayi ina sauraran kalaman da yake min mirmushi nayi ina sake yin k'asa da murya nace." Haba dai yaushe zan wahalar da kai kazo d'auka na ka huta kawai tunda yanzu gani tare da direba."


Wani irin cin birki motar tayi! Gwaggo da take gyangyadi ta bude ido da sauri tana salati.

Kallonsa nayi sai huci! yake yana zufa(gumi) "Fitar min a mota."! abinda ya fada kenan idonsa yayi jajawur!! Gwaggo tace." Lafiya me yake faruwa ne."?


Bai saurareta ba ya bude min mota kokarin tura ni waje yake sai kyarmar jiki yake.


"Khalid wai meye haka bana son wulakanci fa.''

''Kin san Allah sai kin fitar min a mota tunda dai ni ba direban ki bane."

Shuru nai ina kallonsa nace."Idan na fita a mota a nan gurin wace motar ce zata d'auke ni.'' ?

"Ke kika sani malama ki fita tun kafin nayi miki rashin mutunci wallahi."

Dariya nayi ina kallonsa kawai naji ya angiza ni waje nayi saurin dafe motar raina yayi masifar 'baci!


Gwaggo kuka tasa da fadin."To tunda ka kore ta a motar ka nima ka bude min mota na fita mara mutunci kawai."

Ko kallonta beyi ba ya figi motar da karfi suka bar gurin......Sakin baki nayi ina kallon hanyar da suka wuce ikon Allah kenan mirmushin takaici nayi na girgixa kaina. waya ta na dauka number Alhaji Nura na laluba kiransa nayi akan yazo ya dauke ni na bashi kwatancen gurin.

Ranar da ake 'kwallara wa itace ta dame ni na samu inuwa na zauna ina mamakin rashin mutumin yaron nasan kishi ne ya rufe masa ido har yasa ya yi min wannan rashin mutuncin.



"Mara mutunci kawai wato har kayi arziki da zaka dinga wulakanta 'yan uwanka to shikkenan zamu isa gidan Wallahi sai na samu Ubanka duk na sheda masa abinda kake yi ni mai zanyi da Rabi da Uwarta ai sun cutar dani tunda suka had'a ka aure da wannan afiruwar yarinyar da ido sai kace na tsaka nasan itace ta zuga ka ka kori 'yar uwarka a motar ka.


Jamila ta fashe da kuka da fadin." Wallahi Gwaggo babu ruwa na ni ban san abinda ya had'a su ba kawai naji suna mayar da magana a tsakaninsu.


A fusace! tace." Rufe min baki munafuka kawai ai duk sharrin ku sai dai ya koma kanku masu mugun hali kawai." Jamila kuka kawai take tana shar'be majina.......Yana jinsu yayi musu shuru abinda ya dameshi shi ya dameshi wai kamar shi zata kira shi da direba abin yayi masa zafi mutuka. wani irin tsanarta yake ji a zuciyarsa ita da bazawarin nata.


Koda suka isa gidan Gwaggo taga yanda ya sauya bai burgeta ba zaginsa kawai take tana cin mutuncinsa sosai tayi masa tatas sannan tace ita bai burgeta ba tunda arzikinsa ya zama na izgilanci.

Tana shiga gidan taga kayan tsarabar su jibgi guda a kicin ajiyar zuciya ta sauke ta shiga dakinta ta zauna tana bin ko'ina da kallo sam hakan be burgeta ba hankalinta na kan Sa'ida hawaye suka shararo mata tace."Allah kayi min maganin Rabi da Uwarta Baito.


Ya jima a motar a zaune kafin ya fito ya shiga gidan.......Dakin Gwaggon ya nufa ya sameta tana kuka duk ta rasa yanda za tayi.


Da hannu ta nuna masa kofa da fad'in."Ka fita bana son ganin ka aini duk mutumin da zai tozarta Sa'ida to babu ni babu shi har abadah kuma wannan gyaran gidan da kayi sam baka burge ni ba gwara zamana a Danbatta akan na zauna a karkashin inuwarka."


Juyawa yayi ya fita daga gidan....yana kokarin shiga motar shi mahaifiyarsa ta kirashi babu yanda ya iya haka yaje ya sameta itama ta rufe shi da fad'a dan Jamila tana kuka wurjajan ta shiga gidan.

Tace."Wato kana fifita Sa'ida akan matar da zaka aura ko? kada fa ka manta Jamila 'yar dan uwana ce kuma matsayi biyu take dashi a gurinka mai zai sanya a hada baki da kai aci mutuncin ta.

Rashin abin cewa yasa kawai ya bata hakuri Amma ranshi ya baci da abinda Jamilan tayi masa dole yaja mata kunne mutukar tana bukatar zaman lafiya dashi.



Yana fitowa ya shiga motar da sauri hanyar Dambatta ya nufa gabad'aya nadama ta baibayeshi sai tunanin halin da take ciki yake.


Alhaji Nura na isa da motarshi shima ya isa gurin Kusan a tare suka fito daga motar.......Kallon kallon aka shiga yi Khalid zuciyarsa ta sake yin duhu yana ji tamkar yaje ya sha'ke masa wuya ya huta da ganin fuskarsa .

Da sauri ya karasa inda take tsugune....."Ki tashi ki shiga mota mu tafi'' Mik'ewa nayi na ratse shi zan bar gurin.

Hannuna ya ri'ke da sauri na juyo rai a 'bace nace."Sakar min hannu ko kuma ranka ya 'baci yanzu."

"Me zaki min na 'bacin rai ki burge shi."? Ido jawur nake kallonsa yana wani irin huci! yace." Babu wani abu na 'bacin rai da zakiyi min ki burgeshi tunda nasan dake dashi na riga na gama yi muku illah a rayuwarku so duk wani abu da zakiyi min ba zan damu ba."



Hannuna na fizge da sauri nayi nufin barin gurin. sai yayi gaggawar kamo 'kuguna ya had'a bayana da 'kirjinsa ri'ke ni yayi sosai a jikinsa.

Alhaji Nura ya rintse idonsa yana jin wani irin d'aci a ma'kogwaronsa. wani irin kishin yaron ne ya taso masa.



Kokarin kwace jikina nake yana sake matse ni hankalina ya tashi gashi motoci na wuce wa a kan titi.


"Khalid bana son iskanci ka sake ni ko bakaji ba."

Sake rike ni yayi ya tsirawa abokin gamayyarsa ido.........Alhaji Nura jiki a sanyaye ya karaso gurin da fad'in." Kai Yaro ba sai kayi haka ba sannan zaka nunawa duniya cewa kai din mara tarbiya ne."

Sosai yaji ciwon maganarsa sai ya share cikin sigar 'kunsa bakin ciki yace."Ashe kai sai yanzu ka san bani da kunya ai na dauka ta fad'a maka cewa ita d'in saura nace sai da naci na rage ka samu so kaga k'arshen rashin kunya kenan."


Alhaji Nura ya goge gumi da hankicin rai a 'bace yace." Ta fad'a min yanda al'amura suka faru ai dama shaid'ani ne kuma don kayi mata fyad'e a farko hakan ba zai hanani auranta ba tunda ina mata sahihiyar k'auna."


Tsaki yaja yace."Kaga malam kaja motar ka kayi gaba wallahi ba zata shiga motarka ba na fada maka magana guda.


Alhaji Nura yace."Kai kada fa kayi min rashin kunya anan gurin ka sake

Please Login or Register in order to submit comment