Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

*TARE DA*
*USAINA ABDUL-MALIK ISA (KAITA)*

_*Ina kaunar ku iyayena ina kuma alfahari da irin kaunar da kuke nuna min💜🥰*_




*45&46*
Raina ne ya 'baci ganin yanda yake daga murya sama kamar zai doke ni nace."Kayi hakuri dan Allah ni banga abin daukar zafi ba idan kana so kasan wacce tazo guri na sai kaje ka tambayi wacce ta fada maka cewa yau nayi bakuwa."
Wani irin kallo yake min yana girgiza kansa yace."Sa'ida ashe baki da kunya dama? ni kike fadawa wannan maganar?
Hawaye na share nace."Alhaji wace magana na fada maka mai zafi! al'amarin ne ai ya bani mamaki kuma banta'ba tsammanin aunty Murja fuska biyu gare ta ba."
Yace."Okey yanzu mai kike nufi."? kai tsaye nace."Ina nufin abubuwa da yawa." Girgiza kansa yayi kafin yace."Ni ban hana wani naki yazo gidan nan ba kawai dai sintiri ne bana so inace duka-duka yau kwanan ki biyu da tarewa a gidan nan mai zai sanya a fara yi min sallama a gida.

Fuskata na goge nace."Babu wanda zan hana shi zuwa cikin gidan nan tunda dai kasan ina da jama'a bayan haka kuma ina da 'yan uwa da dangi masu yawa saboda haka ni dik wanda yazo gurina ina maraba dashi."


Rai a 'bace yace."Ni kike d'aga wa murya ko."? shuru nayi yace."To bari ki ji abinda baki sani ba Murja da kike gani ta fiki 'yan uwa da dangi da jama'a amma saboda tana bukatar zaman lafiya dani tabi doka ta a kan dauki dogon lokacin kafin kiga wani dan uwanta a cikin gidan nan saboda haka kema yana da kyau ki kiyaye.

Nace." 'Karya take aunt Murjan." cike da mamaki yake kallona.

Na cigaba da cewa" D'azu itama ai tayi bak'uwa mai yasa bata fada maka ba saboda ita ta cika munafukace magulmaciya."

"Murjar kike kira da wannan sunaye." ? a hasale nace."Eh ita din fa ai ta amsa duka sunayen."

Rai a 'bace ya juya ya fita daga dakin. tsaki naja mai karfi da fadin"Mijin tace kawai."

Koda ya fita daga dakin kai tsaye bene ya hau ya sameta a kwance da wayarta a hannunta tana latsawa, ganin shigowarsa yasa tayi saurin kashe wayar ta ajiyeta ta mike zaune tana kallonsa.

Zama yayi kusa da ita rai a dagule! ta dafa kafadarsa da fadin "Abban Yusura ya akayi ne naga ka shigo fuska a 'bace."


Ajiyar zuciya ya sauke yace."Murja na lura yarinyar nan Sa'ida bata shigo gidan nan da sigar son zaman lafiya ba kamar ni zata tsaya tana jayayya dani akan hukuncin dana yanke a gidana saboda na kawo mata misali dake shine take zagin ki."


Murmushi tayi alamun abun bai mata ciwo ba tace."Sai hakuri Abban Yusura kasan ko wace mace da irin halinta wallahi nima yau haka ta yini tana yar min da habaici ban san meye dalili ba amma dai ka cigaba da hakuri da halinta.''


Yace."Ai kuwa zata gane kuskuranta Murja babu wata mace da zan aura ta taka martabarki ban nuna mata kuskuranta ba saboda haka na bar dakinta har sai na koya mata hankali."


Murmushin samun nasara tayi tace."Haba Abban Yusura kayi hakuri dan Allah ka koma dakin kaga amarya ce ka cigaba da rarrashinta.


Hannu ya daga mata yace."Murja kin san bana magana biyu ko saboda haka ki bar maganar kawai ni nake auran Sa'ida ba ita ke aurena ba dan haka zan nuna mata cewa ni cikakken namiji ne."


Tace."To shikkenan tunda kace haka sai dai nace Allah ya kyauta ya rufa asiri." shuru yayi bai amsa ba ya nata wani muzurai kamar gaske.


Nayi ta tsammanin dawowarsa dakin naji shuru cikin takaici da bakin ciki na kwanta da kyar bacci ya dauke ni.

Na d'auka da safe zai shigo mu gaisa naji shuru har goma da rabi babu labarinsa, falon na fita shuru matar gidan na sama yara kuma sun tafi makaranta.

Jiki a sa'bule na zauna gurin cikin abincin.

haka na yini cikin 'kunci da damuwa ga Khalid ya ishe ni da kiran waya lallai sai na bashi Gwaggo sun gaisa sai da nayi masa jan ido sannan ya rabu dani muka rabu cikin Jin haushin juna.


Haka na cigaba da kasancewa a gidan Alhaji Nura tsayin sati guda babu wani zaman Arziki a tsakanina dashi, tun ranar da mukayi musayar yawu dashi bai sake shigowa dakina ba haka nan kuma idan zan ganshi a falo na gaishe shi baya ko kallon inda nake ballantana ya amsa min gaisuwata.

Sosai na shiga cikin tsaka mai wuya nadama mara amfani duk ta buwaye ni gabadaya kaina ya kulle na rasa wane irin tunani zanyi.


Ranar Lahadi nasan baya fita kasuwa da wuri sai na fito falon na samesu suna zaune suna hira na zauna kan kujerar dake fuskantarsu a nutse nace."Aunty Murja kin tashi lafiya ya kwanan su Yusura."
Ta amsa fuska a sake kamar ko da yaushe....kallonsa nayi yana duba jarida wanda zama na a gurin ne yasa shi daukar jaridar "Barka da asubah Alhaji."
Ciki ciki ya amsa hankalinsa nakan jaridar nace."Ina so zanyi magana da kai." ba tare da ya kalle ni ba yace."Ki fada ina sauraranki.

Shuru nayi na minti biyu kafin nace."Akan maganar aiki na ne dama hutun sati biyu suka bani to kaga yau sati na uku ban je ba shine nake so insha Allahu gobe zan koma bakin aiki."


Ba tare da ya kalleni ba yace."Babu maganar aiki a gidana tunda da ban gaza da komai ba saboda haka ki ajiye maganar aiki a gefe mutukar ni nake auranki na soke maganar zuwa gurin aiki."


Wani irin gumi! ya shiga yanko min murya na rawa nace."Alhaji wannan wace irin magana ce? kada ka zama 'karamin mutum mai magana biyu mana ya za'ayi muyi da wajewa da kai kafin muyi aure amma sai bayan bukatarka ta biya sai kuma ka sanja magana."


A fusace! ya daga min hannu da fad'in "Sa'ida me kike so ki mayar dani ne? wato nine ma nake magana biyu."? Cikin rawar baki nace" Eh hak.......'Barin makauniya yayi a fuskata! nasa hannu na dafe kumatuna ina mamakin sanda yazo inda nake har ya samu nasarar mari na.

Yana tsaye a kaina yana huci da kumfar baki sai bambami yake Ita kuma gwanar tasa tana rirrikeshi tana bashi hakuri da fad'in "Haba Sa'ida ashe haka kike da tsayayya me ya sanya zaki dinga jayayya da mijinki."

Cikin b'acin rai na mike tsaye da fad'in "Kinga saurara aunty Murja nifa ba 'kan'kanuwar yarinya bace ballanatana ki dinga wasa da hankalina duk abinda yake faruwa a gidan nan da sanya hannuki a ciki saboda haka kiyi shuru da bakin ki bana son munafurci."

Kalar tausayi ta koma da fad'in "Sa'ida ni kike kira munafuka." Cikin rawa murya nace."Idan ba ita bace mecec....Marin dai ya k'ara kawo min na kauce da sauri ina kallonsa hawaye na ambaliya a fuskata nace."Wallahi dana san kai mijin tace ne a gidanka da ban aureka ba."


Yana numfarfashi yace."Ki fice min daga gidana." da sauri tace."Subahanallahi Abban Yusura kada ka yanke wannan hukuncin.


Rai a 'bace yace."Murja na fada miki babu wata mace da zan aura ta ta'ba martabarki na 'kyaleta saboda haka mutukar Sa'ida tana bukatar ta zauna lafiya dani to sai ta baki hakuri."


Na dinga kallonsa ina mamakin maganarsa wato sai na bata hakuri sannan zai zauna dani lafiya. kallona yayi yace."Ki bata hakuri ko bakya ji ne."


Kaina kawai na girgiza ba tare da nace komai ba na kad'a kaina na bar gurin.


Dakina na shiga na samu gefan gado na zauna kuke ne ya 'kwace min na dinga yi ina girgiza kaina wannan takaici da bakin ciki har inaa! lallai babu shakka dole na bar masa gidansa domin ba zan zauna bawa wata 'yar iska hakuri ba.


Sai da naci kuka na na koshi tukkuna na shiga toilet na wanke fuskata kaya na na hada cikin akwati nasa hijabi na na fito.

Har yanzu suna zaune a falon suna mayar da magana kai tsaye hanyar fita na nufa. ina kokarin bude kofa tazo ta rike akwatin hannuna. "Haba Sa'ida mai yayi zafi haka dan Allah kiyi hakuri kada ki tafi abun kunya ne ace aure sati uku kacal har an fara yaji sam bai dace ba.


Akwatin kaya na na fizge daga hannunta nace." Aunty Murja ai zama da Alhaji Nura sai ke kamar yanda ya fada cewa komai naku a tsare yake keda shi to bai kamata wani yazo ya rusa muku tsari ba kamata yayi ace ku biyu kacal zaku zauna sai 'ya'yanku.

Girgiza kanta ta shiga yi kamar wata mutuniyar arziki sai hakuri take bani shi kuma yana zaune 'kwam akan kujera na d'an hango nadama a fuskarsa amma tsabar girman kai ya hanashi yayi magana.


Ganin ta juya ta nai masa magana yasa da sauri na kwace akwatina a hannunta na bude kofa da sauri na fita.



Gwaggo na zaune a tsakar gida da kayan kad'i a gabanta gefe guda kuma tana sauraran redio tashar freedom suna gabatar da shirin barka da hantsi....Ummatu na bakin rijiya tana wanke-wanke suna hira yanzu tsakanin Gwaggo da Ummatu an samu daidaito sun daina fad'a kullum suka zauna hirar Khalid da Sa'ida suke gabadayansu suna cikin alhinin rabuwa dasu.......Gwara Khalid suna gaisawa dashi dan da ya gaji da kiran wayar Sa'ida tana yi masa yawo da hankali kawai sai ya yanke shawarar kiran wayar mahaifiyarsa su gaisa sannan ta bawa Gwaggo itama su gaisa.

Khalid bai samu damar zuwa gidan ba sabida yanda Oga Laraban da sauran abokanansa suka taushe shi gami da nuna masa muhimmacin abinda ke gabansu, a cikin satin daya gabata Mr William yazo daga america aka gabatar da shahararran wasan daya daukaka 'kungiyar kano pillars Khalid dashi da Ahamad Musa sunyi kokari sosai kuma sun zama zakaran gwajin dafi domin sune suka cinye kofin da ko wane team suke 'kwa'kwa Oga Laraban tamkar ya zuba ruwa a kasa yasha sabida tsabar murna da farin cikin kungiyarsa ta cinye kofi......To wannan dalilin ne yasa bai samu damar zuwa gidan ba a lokacin daya fad'a zai zo sai yanzu da hankalinsu ya kwanta suka shirya tafiyar shida Salmanu.


Sallamar ta a cikin gidan itace ta katse musu hirar da suke. gabadaya suka bita da kallo a lokacin da take shiga gidan da akwatin kayanta a hannunta.

Gwaggo a sa'bule ta amsa sallamar ta cigaba da bin ta da kallo har ta cire takalmanta ta shiga daki ba tare da tace musu komai ba.


Ummatu tace."Gwaggo anya lafiya kuwa Sa'ida ta shigo jiki a sab'ule ga kuma a kwati a hannunta.


Gwaggo ta ajiye makad'in hannunta ta yunkura da nufin mi'kewa tace"Aa Rabi ai wannan zuwan na Sa'ida ba na lafiya bane kina ganin ta shigo gidan kai tsaye ta shiga daki bari nabi bayanta.

Ummatu shuru tayi jikinta duk ya mutu........Kuka ta shiga ta same ni inayi. a sanyaye ta tsaya kaina da fad'in "Sa'ida me yake faruwa? kada kice min Alhaji Nura ya sake ki bayan ya tabbatar da babu budurci a tare dake."?


Kaina na girgiza nace." Gwaggo Alhaji Nura Bashi da kirki ashe mijin tace ne a gidansa sai abinda matarsa tace dashi."


Ajiyar zuciya ta sauke ta nemi guri ta zauna da fad'in "Wallahi na dauka ko saboda rashin budurci ne ya koro ki gida ashe ba wannan matsalar bace.''


Girgiza kaina nayi nace" Ba wannan matsalar bace Gwaggo........Tiryan tiryan na fad'a mata dukkanin abubuwan da suke faruwa ban rage mata komai ba


Gwaggo ta dinga mamaki tana girgiza kanta tace."Ashe duk kirkin matar nan da jama'a suke fad'a na gaibu ne ashe fuska biyu gare ta.''

Nace."Wallahi kuwa Gwaggo aunty Murja muguwar makira ce shi kuma kamar tsoronta yake duk abinda tace shine daidai wai dole sai na bata hakuri sannan zan zauna a gidan Gwaggo babban abinda yafi tayar min da hankalina shine maganar gurin aikina wai bai yarda na k'ara zuwa ba."
Gwaggo shuru tayi tana girgiza kanta gami da jajanta al'amarin.



*Kuyi manege babu yawa ana bikin 'yar yar Mamana sannan yau ma kuyi min uziri ba zaku samu na dare ba nagode*
*47&48*
Gwaggo tace.''Yanzu dai kiyi hakuri ki daina kuka zamu jira Ibrahim ya dawo domin muji hukuncin da zai yanke amma gaskiya Alhaji Nura ya bani mamaki ashe mace ke juya shi." Nace."Gwaggo ai ba kiji mamaki da takaici ba sai kinga abin da idonki." Tace."To Allah ya sawake yasa ya zama jajurtacce a gidansa.
shuru kawai nayi ina tunanin abinda zai biyo baya.

To koda Kawu ya dawo ya samu labarin a binda yake faruwa shima ransa ya 'baci sosai da irin abinda Alhaji Nuran yake a gidansa ya kalleni cikin kulawa yace."Kiyi hakuri kinji ko yanzu za mu jira zuwan sa domin shime muji da abinda zai zo amma maganar zuwa aiki ki ajiye ta tunda dai baya so sai ki hakura.''

Cikin kuka nace."Kawu ya za'ayi na saki aiki na bayan kafin auranmu sai da mukayi da wajewa dashi ya amince zan cigaba da aiki na sai kuma yanzu yazo ya sanja magana."


Yace."Sa'ida aikin nan ba dole bane tunda Allah ya rufawa mijinki asiri baki da wata matsala sai ki hakura ki zauna kiyi zaman auranki lafiya."


Hawaye na share ina jin wani irin d'aci a ma'kogwarona anya kuwa zan iya hakura da aiki na kuwa."


Washe gari da sassafe Ummatu ta shigo da waya a hannunta tana fad'in "Gwaggo Khalid ne ya kira yanzu yanzu yake sheda min cewa yana kan hanya."

Cikin farin ciki ta mike zaune tare da kar'bar wayar tana dubawa kamar wacce za ta ganshi a cikin wayar sai washe baki take da fadin"Allah ya sauke shi lafiya kamo min shi mu gaisa." Ummatu ta karbi wayar da fadin"Lokacin da ya kira babu network sosai da 'kyar ma naji abinda yake fada amma bari na sake kiransa naji.

Wayar ta dinga katsewa ta kalleta da fadin" Taqi shiga wayar bari idan anjima sai mu sake gwada kiransa.'' Tace."To shikkenan." Ummatu fita tayi daga dakin cike da farin ciki. Ita kuma ta shiga kiran sunana "Sa'ida kina ji ko Khalid na kan hanya." Shuru nayi mata gabana in banda faduwa babu abinda yake sam! bana so yaron nan yazo ya same ni a gidan ba.

Ido na bude da fadin"Gwaggo naji Allah ya kawoshi lafiya." Ta amsa tana 'yar dariya had'e da fadin "Ni kuwa dame zan tar'bi yaron nan."?

Shuru nayi mata tace." Sa'ida kina jina ina magana ko nace me kike gani zan shiryawa Khalid na tar'ba."?

Nace"Kiyi masa girki mai dadi mana amma kisa nama kin san halinsa kamar kure haka yake."

Dariya tasa da fad'in "Ni kuwa yaushe zan kasa fito da kudi na siyi naman miya bari anjima kadan sai naje gurin Isiyaku mai kayan miya nayi cefane."

Cikin zuciya ta nace."Aiki ya same ki. Kawu ne ya daga labulan dakin da sallama a bakinsa gabad'aya muka amsa na mike zaune ina gaisheshi so kawai nake naji yayi magana akan Alhaji Nura.

Kayan tea din dake Hannunsa ya ajiye kusa da Gwaggo da fadin" Gwaggo ga kayan shayi nan yanzu Rabi zata kawo muku ruwan zafin sai ku had'a ku karya.


Tace."Ibrahim me zai sanya kayi asarar kudin ka kasan ni fa bana ra'ayin cin wannan fulawar d'aure min ciki take."

Yace."Gwaggo yau dai d'aya ai sai ki daure kisha saboda Sa'ida yasa nace yau Rabi tayi muku shayi.''

Nace."Kawu nima zanfi sha'awar kunun ai.'' Yace."To babu laifi Allah ya kaimu gobe sai ayi miki."

Kokarin fita yake Gwaggo tace." Ibrahim d'azu Khalid fa ya kira wayar uwarsa yace yana kan hanya.''


Babu yabo babu fallasa yace."To Allah ya sauke su lafiya." ta amsa da ameen tana dariyar farin ciki. har ya fita daga dakin ba tayi masa maganar data dangance ni da aurena ba, raina ya 'baci sosai da kyar na iya had'a tea din nasha na koma na kwanta ina tunanin mafita.........Wato dai dama Alhaji Nura ba wani sona yake ba sha'awata yake tunda gashi tun ba'aje ko'ina ba har gishiri ya salance daga jiki kaza, zuciyata tace dani yanzu da ya samu budurcin ki ma wannan wulakancin zaiyi miki, kawai sai naji ina jin dadi da Allah yasa bashi ya samu budurcina ba domin akwai takaici ace ya samu abu mai muhimmanci a tare dani amma ya dinga wulakanta ni akan matarsa.

Ina can duniyar tunani Gwaggo ta gama kujigaba-kujigabarta tasa hijabi ta tafi cefane, sai fitowa tsakar gida nayi na sameta ta baza kayan miya a gaba gefe guda kuma ta hura huta a kurfoti (mangal) ta d'ora kasko tana ta soya nama. cikin takaici da bacin rai na dauki buta na shiga bandaki nayi uzirina na fito ta kalleni da fadin"Sa'ida kina gani aiki ya cakud'e min ba zaki taimaka min ba."

Ba tare dana kalleta ba nace."Gwaggo kaina ne yake ciwo.'' bina tayi da kallo kafin tace."Dole kanki yayi ciwo mana tun jiya kike kuka sai kace Alhaji Nura ne autan maza a duniya duk kin damu kan ki."



Nace."Gwaggo dole nayi kuka na shiga damuwa mana tun jiya mutumin nan bai kira waya ba kuma bai zo ba ai dole hankalina ya tashi gashi Kawu yace dole sai na hakura da aikina."


Tace." Sa'ida nifa wani sa'in bana jin haushin abinda Alhaji Nura yayi miki dama hausawa suna cewa duk wanda ya sayi rariya yasan zata zubda ruwa haka kurrum kika 'ki d'an uwanki kika za'be shi *AI GA IRINTA NAN!* Tun kafin aje ko'ina ya nuna miki halinsa."


Hawaye na share nace''Gwaggo dan Allah ki daina wannan maganar kada ki sake tunzura min zuciyata Khalid yana d'aya daga cikin mutanan da suka hana ni samun kwanciyar hankali a gidan aure na."

Kallonta tayi baki a bude tace."Au! tana nan kuma kika 'bullo.''? Da sauri nace."Eh Mana Gwaggo da Khalid bai raba ni da martaba ta ba, to bana tsammanin Alhaji Nura zai yi min irin wannan wulakancin."


Shuru tayi ba tace komai ba ta cigaba da gyara kayan miya, labulan dakin na daga na shiga na zaune tare da daukar waya ta ina duba gurin text burina kawai naga wani sa'ko daya dangace shi, abin takaici text din Khalid na gani har biyu inda yake sheda min cewa zuwa La'asar zasu sauka.
Ajiye wayar nayi ba tare dana bashi amsa ba.


Kafin La'asar Gwaggo da Ummatu sun gama aiki tsaf sun shirya masa abinci har kala uku da zo'bo wanda suka sa masa k'ankara Gwaggo sabbin kwanikan ta na silba ta dauko aka jere masa kayan abincin a guri guda yanzu shi kadai kawai ake jira.....Al'amarin ya dinga bani mamaki yana daure min kai ganin yanda suka shirya masa guri sai kace wani cikakken mutun magidanci gabadaya tsabar haushi da kishi naji zaman gidan ya fita min a rai sai kawai na hau shirye shirye ta kalle ni da fad'in "Ina kuma zakije da yamma."?

Nace." Zanje can gidan Ummana ne." Girgiza kanta tayi fuska a 'bace tace."Aa Sa'ida ba zaki mayar damu 'kananun mutane ba da auran mutum akanki ki dinga yawo."

Nace."Gwaggo gidan Ummana fa nace zani ba wani guri ba."

Tace."Eh ai na fahimta babu inda zakije har sai munji ta bakin mijinki tukkuna."

Takaici yasa kawai na zuba mata ido ina kallonta. Kayan kad'inta ta dauka tana gyarawa mukaji sallamar yara a cikin gidan.

Gwaggo da sauri ta amsa tare da daga labulan dakin........Yaran sun kai su hudu biyu buhu ne a kawunan su biyu kuma jarkokin manja da man gyada ne a hannuwansu.

Gwaggo tace."Waye ya aiko ko da wa'innan kayan." Daya daga cikinsu yace."Khalid ne ya dawo yana waje shida abokanansa."

Da sauri ta cilar da kayan kad'in ta miqe tana fadin"Alhamdullilahi Allah nagode maka." Hijabi tasa ta kama hanyar fita Nace."Gwaggo ai kya bari ya shigo ko."

"Aa Sa'ida gwara naje na tar'beshi." tafada tana kokarin fita, kallo na bita dashi ina girgixa kaina.

Gwaggo na kokarin fita suka buga karo. rungumeshi tayi sai kuma ta fashe da kuka tana kiran sunansa....Hannunta ya rik'e yana rarrashinta suka shiga gidan

Ummatu na tsaye a bakin kofar ta fuskarta yawalce da fara'a take kallon yaron nata sai taga duk ya sanja ya kara girma da hasken fata....Yace."Ummana kina mamakin ganina ko." Murmushi tayi tace."Khalid dole nayi mamaki." Cikin jin nauyi ya sunkuyar da kansa kasa yana gaisheta ta amsa cike da kulawa.

Ya shiga gogewa gwaggo hawaye yana fad'in "Gwaggo dan Allah ki daina kuka haka ai gani na dawo cikin koshin lafiya dan Allah ku gafarce ni."

Ta dinga kallonsa tana girgiza kai tace."Khalid na kuwa sheda haka tunda gashinan na ganka kayi girma ka sanja kayi haske sosai kamar wanda yake cikin hutu.''

Murmushi yayi yace."Gwaggo godiyar Allah ce kawai da kuma tasirin adduoin da kuke min shi ya janyo haka.'' Tace."To Alhamdulillahi Khalid naji dadin ganin ka cikin koshin lafiya gashinan harda abin arziki." Tafada tana bin kayan dake jibge a tsakar gidan.

Yace."Gwaggo na san ki da son doya shiyasa na siyo miki buhu guda.'' Dariya tasa da fadin"Aikuwa naji dadi d'an albarka Allah ya 'kara maka wadata." ya amsa da ameeen ya rabbi.

Tace."Muje daki kaci abinci ka huta ko."? yace."To uwagidana." murmushi tayi ta rike hannunsa suka kama hanyar dakin....Ummatu kuwa murmushi tayi cike da farin ciki ta shiga gurinta.

Jin motsin shigowarsu dakin yasa da sauri na daidaita nutsuwata ba tare dana dago kaina ba na amsa sallamar shi.

A jikina naji cewar kallona yake a fizge na daga kaina na kalleshi yana sanye da k'ananun kaya kamar ko da yaushe sai kawai na tsinci kaina da kasa dauke idona daka kansa mamakin girmansa nake wata biyar kacal yaro ya sanja ya zama 'kato dashi da gaske ya sake girma da hasken fata.

A nutse ya zauna inda aka tanadar masa Gwaggo sai wani ji dashi take tana gyara masa gurin zama, shi kuma gabadaya hankalinsa na kaina ina kallonsa ta gefan ido sai kallona yake.

"Auntyna ba zakiyi min barka da zuwa." maganarsa naji ta daki kunnena.

Na kalleshi babu yabo babu fallasa nace."Khalid ya hanya."? fuska a sake yace."Alhmdulillahi aunty ya fargaba da alhinin dana tafi na barki dashi.''?

Share maganar nayi na dauki waya ta ina dubawa.

Gwaggo ta hau bude kwanunkan dake gabansa tana fad'in "Jarumi kaci abinci gashinan." Yace."Gwaggo duk wannan nau'in abincin duk ni kadai."

Tana mirmushi tace."Khalid kafi karfin komai a gurina burina kullum ka kasance cikin farin ciki."

Yace."To gwaggo naji dadi sosai ina rokon Allah yaja min da ranki." Tana kokarin zuba masa abincin a plate ta amsa da ameen d'an albarka.

Abincin ta zuba masa da yawa tasa masa miya da uban nama. yace."Gwaggo abincin nan yayi min yawa." Tace."Ka dai ci ka koshi."

Kallona yayi cikin kulawa yace."Auntyna zo ki taya ni ci." Ko kallonsa banyi ba ballanatana na bashi amsa.

Tace."Khalid rabu da ita don Allah kaci abincin ka."

Girgiza kansa yayi yace."Gwaggo ya za'ayi amaryata tana fushi kice na rabu da ita ko dai kishi kike."?

Bani kadai ba Ita kanta Gwaggo sai da gabanta ya fadi! shuru tayi jikinta duk ya mutu data tuna da yaudarar da akayi masa.

Gani tayi ya mike daga inda yake ya dawo kusa dani ya zauna. ni da ita dik jikinmu ya mutu. a sanyaye yace."Auntyna menene? ki fad'a min matsalarki gani na dawo na share miki hawaye."

Kallonsa nayi zuciyata ta dinga tafarfasa! ina tuna irin cin mutuncin da yayi min a ranar da zai gudu! 'kwalla ta cika kwarmin idona! kansa ya girgiza min cikin sigar rarrashi yace."Kada kiyi min asarar hawaye domin yana da mutukar daraja a gurina ki gafarce ni auntyna nasan dole idan kika kalli fuskata ki tuna abinda nayi miki na rashin

Please Login or Register in order to submit comment