Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya aro dauriya yasa a ransa ya cigaba da driving din yana nanata kalmar innalillahi wa'ina ilaihi raji'un.!


"Hakika Sa'ida banji dad'in wannan abubuwan da suke faruwa da rayuwarki ba amma kuma bai kamata ki yanke wannan hukuncin ba dalili kuwa shine kin san halin Gwaggo baud'ad'd'iyar macace zata iya zargina kan cewa ni nake zugaki ki bijire musu."

Ajiyar zuciya na sauke a raunane nace"Umma wallahi hakuri na ya 'kare a gidan nan dan saboda bana so watarana su tunzura zuciyata na fad'a musu magana mara dad'i shiyasa kawai na yanke wannan hukuncin."

Girgixa kanta tayi tace."To shikkenan ai Allah yasa hakan shi yafi alkairi bari da safe sai na shedawa Alhaji halin da ake ciki idan yaso duk hukuncin da ya yanke miki sai kiyi hakuri dashi."


A sanyaye Nace."Tom shikkenan Umma Allah ya kaimu lafiya." kallona tayi cikin tausayawa tace."Naga duk kin rame ko duk fargabar ce."? Murmushin takaici nayi nace."Umma zama da Gwaggo da Ummatu ai sai jarumi mai kuma hakuri sosai suke takurawa rayuwata."

Murmushi tayi tace."Ba tun yau ba na san halin Gwaggo macace wata iri wacce baka gane gabanta da bayanta haka nima nai hakurin zama da ita Ummatu kuwa dama can ba muyi wani zaman arziki da ita ba."

Nace."Hakane Umma tace." to saboda haka sai kiyi hakuri ki cire damuwa daga cikin ranki ki fuskanci abinda yake gabanki aure idan Allah ya kawo lokacinsa babu wanda ya isa ya hana."

Nace."Kwarai kuwa hakane." Ta kalli kwanukan abincin dake gabana a nutse tace."Da alama ba ki bude abincin nan ba."? Nace."Eh ban ci ba tukunna." Tace."To ni zan shige na tafi dakin Alhaji sai ki nutsu kici abincin ki kwanta." nace."Tom shikkenan Umma sai da safe." Ta mike a nutse ta fita daga dakin, cikin nutsuwa na bud'e kwanukan abincin towon farar shinkafa ne da miyar taushe taji gyada sai kamshi take.....dama tsabar fargaba da tashin hankali bata bari naci wani abincin kirki ba saboda haka lokaci guda yunwa ta taso min nasa towon a plate na zuba miya akai a nutse na fara ci ina tunanin halin da Gwaggo zata shiga idan ta farka daga bacci taga bana nan.....



*Masoya a taimaka da sharing👏🏼🥰*


*IDAN KINA BUKATAR BIYAN KUDIN LITTAFIN GA YANDA ABIN YAKE....VIP GRUOP#600 NORMAL GROUP #300 ACCOUNT... 0542382124.....BINTA UMAR GTBANK...IDAN KATI ZAKI TURO #400 SAI KIYI MIN MAGANA TA WHATSAPP DA WANNAN NUMBER.*
*07084653262*
*08089965176*
*BINTA UMAR ABBALE*
[3/6, 2:04 PM] Umm Muhammad: *GA IRINTA NAN!!!🙆🏼‍♀️*
_(LOVE STORY🌺)_
*NA*
_BINTU UMAR ABBALE🍒_
*MANAZARTA WRITES ASSO🖊️📚*


*11*
Ina zaune da plate din indomee a gabana ya shigo gidan, kallo guda nayi masa na kauda kaina, gani nayi ya tsaya yana kallon kayan wanki na dana jibge a bakin rijiya, minti biyu ya wuce daga gurin..... mikewa na share tsakar gidan sannan na shiga dakin na harhad'o kayan wanke-wanke na fito dashi bakin rija. d'akin na koma na sameta ta fara kad'in lagwani nace." Gwaggo zan fara wanki inaso na share miki dakin." Tace."Kije kiyi wankin ki idan na tashi na share." Ba tare da nace mata komai ba na fita daga dakin, samun sa nayi zaune a bakin rijiya daga shi sai gajeran wando yana wanke kayan ball d'insa.

Tsigar jikina ta tashi na tsani na ganshi babu suttura a jikinsa nakan ji wani irin yanayi a tare dani, kamar na koma d'aki na zauna idan ya gama abinda yake nazo nayi wankin, sai dai na daure kawai naja bokiti da ruwa a ciki na zuba omo na sunkuya na fara cud'a wankin....Shuru gurin yayi yana ta cud'a kayansa nima ina cud'a nawa.

Sunkuyo na d'an gyara karaf! na kama shi yana satar kallon kirjina. cikin dubara na duba sai naga ashe gurin sunkuyo din wuyan rigata ya zame gabad'aya breast dina ana ganinsu.

Girgiza kaina kawai nayi na mi'ke. kujera 'yar tsuguno naje na dauko na zauna akai na cigaba da abinda nake........ Hannunsa ya mi'ka ya d'auki briziyata yasa a cikin ruwan omon dake gabansa ya fara cud'awa.

Rai a 'bace! na kalleshi da fad'in "Ranka zai 'baci idan baka mi'ko min rigar nan ba."

Uffan bai ce min ba ya cigaba da cud'a breziyar yana gyarata, Nace."Khalid ko bakyaji abinda nace ba."? Babu walwala a tare dashi yace."Naji ashe akwai sauran wani abu da zakiyi min bayan wanda kikayi min d'azu."

A zafafe! Nace."Nayi maka d'in ai kai ka janyo meye ruwanka da wayata ko kuma Alhaji Nuran sa'anka ne wallahi ka nutsu ka shiga hankalinka idan ba hakaba kana tare da 'bacin rai."

Cike da nuna rashin damuwa yace."Mutukar akanki ne a shirye nake da kowane irin 'bacin rai kuma wallahi sai inda karfina ya 'kare zaki gane baki da wayo."


Da sauri nace." Ni kake fad'awa wannan maganar."? Shiru yayi ya cigaba da abinda yake a fusace! na kai hannu zan fuzge rigar ya murd'e min hannu har sai da yayi 'kas! cike da mamaki nake kallonsa! Yace."Ki kyaleni na cigaba da wankewa hakan na rage min rad'ad'i!

Gabana ya fad'i! wanke breziyya har wani jin dad'i ne lallai Khalid fitinanne ne........Kallona yayi da wani munafikin murmushi a fuskarsa yace."Naga kamar ma tayi miki kad'an idan na tashi had'a miki lefe wacce ta fita girma zan sa miki."

Naji wani irin takaici ya rufe ni wai ni ya zanyi da yaron nan ne? shamtarsa nayi na zubar da ruwan oman dake gabansa.

Sai yayi murmushi ya cire breziyar a cikin bokitin kawai naga yana marmatsa 'ko'konta kamar yana ta'ba nono sai lumshe ido yake yana cizar lips d'insa....Ruwan Oman dake gabana na d'aga na kwara masa a jikinsa, hakan yayi daidai da fitowar Ummatu daga gurinta, ya mi'ke tsaye da breziyyar a hannunsa.....Ganin mahaifiyarsa yasa yayi saurin mayar da fuskarsa ta salihai "Aunty Sa'ida me nai miki kika watsa min ruwan wanki."

Shuru nayi jikina yayi sanyi da irin kallon banzan da mahaifiyarsa keyi min....ta kalleshi rai a 'bace tace."Khalid meye wannan a hannunka."? da sauri ya kalli hannunsa sai kuma ya jefo min breziyyar da fad'in."Ummatu ban san na rike ba mybe a cikin ruwan wanki data watsa min ta had'o da ita."


Ta kalleni da rai a 'bace "Sa'ida wane tsabar rashin mutunci ne wannan? me yayi miki dan wulakanci zaki watsa masa ruwan wanki a jiki."

Shuru nai mata ba wai dan bani da amsar da zan bata ba sai dan sanin da nayi cewa duk abinda zan fad'a mata yayi min ba yarda za tayi ba.

Gwaggo ta fito daga dakin tana fad'in "Me kuma yake faruwa nake jin hayaniya."? Ummatu da sauri tace." Gwaggo duba jikin Khalid ki gani sabida tsabar ita ta cika ishashshiya ta dauki ruwan wankinta ta watsa masa a jikinsa.

Gwaggo da sauri ta kalli Khalid jikinsa jagab! da ruwan daud'a! cike da mamaki! tace."Jarumi me ya had'a ku nasan dai ruwa baya tsami banza."?

Girgiza kansa yayi yace.''Gwaggo daka kawai zan taimaka mata da wanki shine tayi min wannan wulakancin.''

Tace."Haba Sa'ida me yasa kika aikata haka."? Rai a 'bace na d'ago ina kallonsu nace." Lokacib dana fito da wanki na bance kowa ya taimaka min ba akan me zai zo yasa min hannu sai kace sa'arsa dan wulakaci ya d'auki breziyata yace zai wanke."


Gwaggo ta ri'ke bakinta tana yi masa wani irin kallo mai kama da harara.....Ummatu tace"Ke Sa'ida kada kiyi masa sharri yaushe ya dauki rigar nonan naki bayan ke kika watsa masa ruwan daud'a da ita a ciki."

Nace."Ummatu kenan ba sharri nai masa ba da idonki fa kin gani amma zaki ce nai masa sharri."

Gwaggo tace."To duk dai magana ta wuce kada a 'kara tayar da ita kai kuma Khalid babu ruwanka da ita." Yace."Yanzu ke Gwaggo kin yarda zan aikata hakan? okey idan ma breziyar ta na d'auka domin na wanke mata meye a ciki? ai ba k'irjinta na ta'ba ba ballantana tayi min sharri ." Gwaggo tace."Aikuwa dai babu laifi a ciki tunda tace bata so sai ka kyaleta.

Tsaki yaja ya bar gurin yana fad'in "Daga Abin alkairi sharri ya biyo baya wataran ma cewa zakiyi na turmushe ki." Ummatu tayi saurin fad'in "Allah ya kiyaye." Bayansa tabi tana surutai itama Gwaggo dakinta ta koma ta cigaba da abinda take.


Tana zaune a d'an tsakar gidanta ya fito daga dakinsa cikin shirin fita yayi gayu cikin 'kananun kaya sai kamshin turare yake, Khalid akwai tsabta da kwalisa kayansa kullum a goge gashi bai yarda da fesa turare me arha ba.

"Khalid zo nan ina so nai magana da kai." A nutse yaje ya samu gefanta ya zauna. tace." Kana jina ko."? yace."Eh Umma ina jinki." Tace."Ni ba zan raba ka da 'yar uwarka Sa'ida ba amma inaso kayi nesa da ita dan gabad'aya ni yarinyar bata kwanta min a raina ba ina jin tsoro taje tayi lalata a waje ta laqaba maka sharri ka daina shiga sabgarta."

A sanyaye yace."Ummatu me yasa kike mata irin wannan zargin." ? Tace."Kai Khalid yaro ne kai baka san me duniya take ciki ba gabad'aya jama'ar gari kallon lalatacciya suke mata dan ni akwai wacce ta kawo min magana kancewa babu irin lalatar da ba tayi da maza a gurin aikinta wannan dalilin yasa nace kayi nesa da ita bana so taje tayo cikin shege ta d'ora maka."

Cike da mamaki! yake kallonta kafin yace."Ummatu amma banji dadin wannan magana ba dan Allah ki daina yarda da surutan mutane bana tsammanin Aunty Sa'ida zata zubar da martabar gidan nan."

Tace."Oho! dai Sa'ida tana bin maza bata bin maza ni dai nace ka rabu da ita dan naga kaima tana so taja hankali ka gashinan baka san laifinta.''

Shuru yayi yana girgiza kansa! Tace."Yaushe ne zaku koma makaranta."? Yace."Ai kin san da tuni mun koma wannan yajin aikin da aka tafi ne ya janyo amma naji gwamnati tayi magana cewa kowane dalibi ya koma makaranta ranar mondy."

Tace."Jibi kenan zaka tafi."? Yace."Eh insha Allahu." Tace."To shikkenan kafin ka tafi kaje can babban gida ka gaishe su." Yana kokarin mi'kewa yace "To insha Allahu zanje."


'Kamshin turaransa ne yasa nayi saurin juyowa muka had'a ido dashi, saurin dauke kaina nayi ina mamakin a'inda ya samu kudi ya siyi turare mai tsada irin wannan nafi jin 'kamshinsa a jikin Alhaji Nura. Cigaba da shanya kayana nayi har ya fice daga gidan sai kawai na tsinci kaina da bin bayansa da kallo gaskiya dressing din yayi masa kyau sosai. kawar da tunaninsa nayi daga cikin raina na cigaba da abinda yake gabana.


Ina tsaka da share inda nayi wanki yaro ya shigo."Wai Salisu mai kanti yace a bashi lagwanin." Nace."Shiga dakin ka fad'a mata. muryarta naji tana fad'in "Bama sai ya shigo ba naji bari na kawo maka ka kai masa."

Yaron yace."To gwaggo." ta fito hannunta rike da leda viva ta mika masa da fadin"Kace dan Allah yayi hakuri banyi masa akan lokaci ba." Yace."To Gwaggo zan fada masa."

Fita yaron yayi ta kalleni da fadin"Sa'ida yau sha'awar sakwara nake ko zakiyi mana da ragowar doyar can." Nace."Banda kudi da zan sarrafa.''

Tace." 'Dari biyu zata isa ayi miyar."? Kaina na girgiza mata alamun ba zata isa ba, tace."Aikuwa dari biyu zan iya bayarwa ayi cefane." tafada tana kokarin shiga daki sallamar Almajirin gidan Alhaji Nura ta dakatar da ita.
Washe bakinta tayi tana kallonsa ya 'karaso inda nake hannunsa ri'ke da ledoji yace."Aunty Sa'ida ina wuni."? na amsa ina kokarin wanke hannuna yace."Daga kasuwa nake Alhaji yace na kawo miki wannan." Hannu nasa na kar'bi ledojin da fadin."To Rabi'u kace masa nagode sosai." Ya amsa da ameen tare da juyawa Gwaggo tace." Rabi'u babu gaisuwa ka shigo kawai ka wuce gurin uwar dakinka."Murmushi yayi yana kallonta yace."Gwaggo Dan Allah kiyi hakuri wallahi hankalina ne yayi gaba ina fatan kin wuni lafiya."?

Tace."Lafiya lau Rabi'u ya Alhajin ina fata dai lafiya dan Allah kace masa muna godiya da hidima." Rabi'u yace."Insha Allah zan fad'a masa."

Yana fita ta karaso inda nake tana fad'in "Kai amma naji dad'in wannan aiken wallahi nasan harda nama da kayan miya a ciki kinga na huta 'batar da kudina.

A nutse nace." Gwaggo wai dan Allah me yasa kike da san abin duniya ne inace d'azu kika gama zagin mutumin nan amma yanzu kinga kayansa duk kin gigice."

"Sa'ida kada ki fad'a min magana mana kin san dai ba zan bar nawa na na za'be shi ba, ni nafi kaunar ki auri Khalid amma da babu maganarsa a tsakani zan baki goyan baya d'ari bisa d'ari ki auri Alhaji Nura domin ya cancanta.''

Nace."Wallahi har mamaki kike bani idan naji kina cewa wai na auri Khalid gwaggo kina tunanin ko maza sun'kare a duniya zan auri wannan yaron........"Shima ba zai aureki ba tsohuwar guzama dake." Muryar Ummatu ce ta katse maganar da nake. duk muka juya muna kallonta....Fuska a murtuke ta karaso inda muke tsaye tace."Sa'ida ke har wata cikakkiya ce da har zaki dinga k'yamatar auran Khalid me kike dashi na matantaka bayan duk kin gama rabawa abokanan aikin ki maza."

Gwaggo tace."Rabi wannan wace irin banzar magana ce."? Da sauri tace."Gwaggo ranar wanka fa ba'a 'boyan cibi ke kin sani kuma kin fad'a da bakinki hakanan kuma jama'ar gari sun sani Sa'ida bata da kamun kai to me zai sanya kice lallai sai Khalid ya aureta."

Rai a 'bace Gwaggo tace."Rabi kada ki 'kara yi mata 'kazafi ni kaf zuriyata babu lalatacce idan Allah ya kaddara auran Sa'ida da Khalid babu yanda zakiyi sai hakuri."


Murmushi takaici tayi tace."Gwaggo sai dai kuwa idan bani na haifi Khalid ba." Tana gama maganarta ta bar gurin tana wani irin huci!

Ido jawur! na kalleta nace."Kinga abinda kika janyo min ko."? ''Kinga Sa'ida rabu da Rabi bata da cikakken hankali kuma wallahi sai na fad'awa Ibrahim ayi muku tsakani da ita kada ta 'kara jifanki da mummunar kalma."

Nace.''Gwaggo da Ummatu ba taji kina fad'a min haka ba to ba zata fad'a ba tun farko ke kika nuna kina zargina da iskanci a gurinki taji gashinan kin janyo min cin mutumci."

Tace."Kiyi hakuri na fad'a miki zan had'ata da Ibrahim zata gane bata da wayo." nace"Gwaggo kada ki had'ata da mijinta a kaina ki kyaleta kawai ni zan yanke hukunci da zakuyi farin ciki."

Tace."Sa'ida wane irin hukunci zaki yanke."? Murmushin takaici nayi nace."Idan na yanke zaki gani." barin gurin nayi naje ina duba abinda yake cikin ledojin .....kayan tea ne komai da komai sai uban kayan miya da nama mai yawan gaske a cikin wata katuwar takarda.
Kallonta nayi nace.'' Kinga nayi wanki na gaji ba zan iya dukan sakwara ba zan dafa miki ita kawai kici da miya."

Tace."To shikkenan had'a kayan miyan ni da kaina sai na miqa markad'an gidan Lubabatu." Mi'kewa nayi na dauko d'an maidaidaicin baho da wuka na zauna ina gyara kayan miya ta nufi daki tana fadin" bari na 'karasa d'an abinda nake kafin ki gama."



To duk k'ulafucin Gwaggo ba taci doyar da yawa ba duka -duka uku taci ta ajiye wa mutumin nata miya cikin silba duk ta kwashe masa naman 'kyaleta kawai nayi domin ni nasan abinda na shirya mata.

Ganin tana gyangyad'i nace."Gwaggo ki gyara kwanciyarki mana." Da sauri ta bude ido tana kallona tace."Ina jiran Ibrahim ya shigo ne shiyasa ki kaga bankwanta."

Nace."Gwaggo Ummatu ni ta ciwa fuska kuma gani tayi ki nayi min saboda haka dan Allah kada kice zaki fad'awa mijinta ki had'asu." Ta'be bakinta tayi tace."Ai sai kiyi Sa'ida Sai fa na fad'a masa fa Ummatu zata san da ni take zancan."
Shuru nai ina kallonta.........ta cigaba da gyangyadin tana nema ta tintsira nace."To ki kwanta idan ya shigo zan tashe ki." Ajiyar zuciya ta sauke tace."To mi'ko min fillo na d'an matse." da sauri na mi'ka mata ta kwanta tana kiran sunan Allah.

Shuru dakin yayi na tsayin minti goma sha biyar na tabbatar tayi bacci na mike a tsanake nasa hijabina jakar dana san na had'a dukkanin kayana na dauka a hankali na fita daga d'akin.......Kai tsaye babban titi na nufa ina addua a kan Allah yasa ina fita na samu adaidaita sahun da zai kaini hotoro gidan Mahaifiyata......

?‍♀️*
_(LOVE STORY🌺)_
*NA*
_BINTU UMAR ABBALE🍒_
*MANAZARTA WRITES ASSO🖊️📚*



*SADAUKARWA NE GA IYAYE NA GUDA BIYU*

*FATIMA MUSA (MOMY NIJAR)*
*TARE DA*
*USAINA ABDUL-MALIK ISA (KAITA)*

_*Ina kaunar ku iyayena ina kuma alfahari da irin kaunar da kuke nuna min💜🥰*_


*14&15*
Wayarsa ya d'auko daga aljihun shart din dake jikinsa sai ya nemo number ta ya shiga kira.

lokacin ni kadaice zaune a falon Ummah ina karyawa, jin kira ya shigo wayata dake gefena a ajiye yasa da sauri na kai hannuna kan wayar kwata-kwata ban kawo shi bane sai da na duba naga number sa akan wayar. tsaki naja na mayar da ita na ajiye a nutse na cigaba da abinda nake.

Ya kira kusan sau hudu bata dauka ba jikinsa yayi sanyi sosai kuma ransa ya 'baci da abinda tai masa yanke shawarar tura mata text yayi kamar haka."

_*Aunty Sa'ida ina fatan kin tashi lafiya na kira wayarki babu adadi sabida wulakanci kin'ki dauka kin tafi kin bar baya da kura a gida saboda ke Baba ya kori Ummatu gidansu bayan haka kuma Gwaggo tana nan cikin damuwa ko abinci ta kasa ci kiyi hakuri ki dawo gida idan ni nake takura miki to ina mai tabbatar miki da cewa gobe i yanzu ina skull saboda haka ki dawo gida saboda farin cikin masu kaunarki.*_

Text din na duba jikina yayi sanyi jin cewar Ummatu na gidansu me yayi zafi da Kawu Iro zai yanke irin wannan hukuncin sai duk naji banji dadin al'amarin ba.

Dakin ta shigo ta sameni a zaune ga kayan break din a gabana na kasa ci tace."Lafiya kika zabga tagumi haka."?

A sanyaye nace."Umma wai kinji Ummatu tana gidansu saboda abinda tayi min Kawu Iro ya yanke mata wannan hukuncin."

Cikin rashin jin dadi tace."Ikon Allah me yayi zafi shi kuwa da zai yanke irin wannan hukuncin a gaskiya ban Ji dadi ba wallahi."


Nace."Nima gabadaya jikina ya mutu wallahi a cewarsa wai ba zata dawo ba har sai na koma gidan.''


Umma shuru tayi tana girgiza kanta kafin tace."A gaskiya Ibrahim ya yanke hukuncin da bai da dace ba ai bai kamata da girmanta da komai yayi mata haka ba."A sanyaye nace." Nima dai haka na gani." tana kokarin bud'e wardrobe d'inta tace."To Allah ya shiga cikin al'amarin ya sasanta tsakaninsu." na amsa da "ameeen ya Allah."



Khalid kai tsaye can babban gida ya nufa gidansu mahaifiyar tasa dake unguwar dala gidan yawa ne irin na gado duk wanda ya tashi a gidan yake aure ya zauna kafin Allah yayi masa nasa shiyasa gidan kullum yake a cike da yara kowanne da nasa .

Kai tsaye bangaran su Mahaifiyarsa ya nufa ya same su suna karyawa da koko da awara zama yayi kusa da kakarsa mai suna Baito yana tsokanarta ganin yanda ta tasa bokitin koko a gabanta tana sha. Tace."Kai ma idan kana sha sai na zuba maka badan halin Ubanka ba."

Yace."Aa bana shan koko kashe min jiki yake." shuru tayi ta cigaba da kur'bar kokonta yace."Baito naga kamar haushina kike ji."

A fusace! tace" Ba dole naji haushi ba Khalid jiya da bakin cikin kakarka da babanka na kwana saboda tsabar rashin mutunci su koro min yarinya cikin dare mai tayi musu da zafi da har zasu yanke mata wannan hukuncin."?


Yace."Baito dan Allah ki samu nutsuwa muyi magana ta fahimta yanzu ina Ummatu take."?

Tace."Tana Bandaki." shuru yayi na minti biyu kafin yace." Baito Ummatu bata fad'a miki laifinta ba ko."?

Tace."Ta fad'a min akan wannan lalatacciyar yarinyar ubanka ya koro ta.''

Khalid yaji kamar ta soka masa wu'ka a ma'koshi yace."Baito bai kamata ba abinda kukeyi kuma fa kun haifa kina da 'ya'ya da jikoki bai kamata ki dinga aibata d'an wani ba yau ko gaskiya ne zargin da kukewa auntyn Sa'ida bai kamata ku dinga zaginta kuna la'antar ta ba kamata yayi kuyi mata adduar shiriya.''

"Allahu akbar! Khalid ka gama nasihar ko baka gama ba."? Tafad'a tana masa wani kallo. yace." Da alama maganata bata gamsar dake ba."

Da sauri tace."Ta ina kuwa zata gamsar dani bayan nasan karya kake kana fada ne kawai dan ka kareta nan Jamila take sheda mana irin lalatar da takeyi da maza a makarantarsu saboda haka maganar Jamila ba karya bace Sa'ida bata da kintsi da kamun kai."

Jamila 'yar yayan Ummatu ce da suke zaune a cikin gidan Jamila budurwace 'yar kimanin shekara goma sha takwas tana zuwa makarantar da Sa'ida take koyarwa ta *Hajara Buhari* dake goran dutse.

Khalid yace."Jamilan ce tazo tana fad'in wannan maganar."? Baito na kokarin yin magana Ummatu ta karaso gurin da sauri tace."Rabi kinga Khalid daga zuwansa ya soma kalubalantata akan na fadi gaskiya ashe har Sa'ida ta fiki kima da mutumci a gurinsa."


Ummatu ta ajiye butar dake hannunta rai a 'bace tace."Baito aini tuntuni na gama magana wallahi tallahi duk ranar da yaron nan ya sake shiga sabgar Sa'ida to sai yaga abinda zai faru dashi."

Khalid yace."Ummatu dan Allah ki daina wannan maganar aunty Sa'ida 'yar uwata ce bai kamata ki raba zumuncin dake tsakanina da ita ba."


Tace."Ai nima dama ba zumuncin ku nace zan raba ba abinda nake nufi shine ka raba kanka da ita tunda duk wasu alamu ka nuna kana sonta in banda rashin hankali irin naka Khalid me zakayi da wannan yarinyar tsohuwa gata mara daraja da kamun kai kai yanzu ba zakaji kunyar auranta ba."

Yace."Ummatu babu kunya a cikin abinda ya zamanto halas dan aunty Sa'ida ta girme ni hakan ba zai hanani na aureta ba tunda ba haramun bane.''


Baito tace."To ba zaka aureta ba d'in Khalid ba zaka lalata mana zuria ba kaje ka nemo wata ka aura idan baka samu ba kazo gida ka duba gamu nan da 'yan mata kyawawa masu da kyau da duk abinda ake bukata."

Shuru yayi ransa duk a 'bace ya tsani yaga suna nuna k'yamarsu akan auntynsa a ganinsa sam bata cancanci haka a gurinsu ba.

A cunkushe yace."Dama ni nazo ne domin nayi muku sallama idan Allah ya kaimu gobe zan koma makaranta''

Baito tace."Wace makaranta kuma? dama baka gama karatun ba."?

Yace." Akwai sauran kad'an." Tace."To Ubangiji Allah yasa daga ka gama ka samu aiki kaga sai kayi auranka da hujja ni nafi so ma kazo gida ka duba wallahi ina yi maka sha'awar Jamila." tana 'yar dariya ta 'karasa maganar.

Hararar gefan ido yayi mata yana kokarin mi'kewa yace."Baito ni dai Namiji ne babu wanda zai yi min auran dole."

Ummatu tace."Khalid magana kake so ka fad'a mata saboda baka da kunya."?

Girgiza kansa yayi yace."Aa Ummatu kiyi hakuri dan Allah abar maganar amma ni kada a 'kara yi min maganar wata Jamila bana ra'ayinta."

Ummatu ta fusata sosai tace." 'Yar d'an uwan nawa kake k'yamata? meye aibun Jamila yarinya kyakykyawa fara mai kuruciya a jika."

Shuru yayi bai tanka ba yasa takalmansa Baito tace."Ai ni mamaki ma ya hana ni magana 'kiri-'kiri yaron nan yana nuna yafi kaunar dangin Ubansa akan na uwarsa."

Khalid dai baice komai ba ya kama hanya ya fita daga gidan gabad'ayansu suka bishi da kallon mamaki!! bayan fitarsa Baito tace."Rabi hak'ika zama bai ganki ba tilas ki fara neman taimako akan yaron nan idan ba hakaba anan gaba cewa zaiyi ba ke kika haifeshi ba."

Ummatu ta sunkuyar da kanta ranta idan yayi dubu ya 'baci tace."Baito maganarki gaskiya ce Khalid kwata-kwata baya ganina

Please Login or Register in order to submit comment