Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zuciyarki ki bada sadakar magani tunda dai ke kikaji kika gani sai ki daura d'amarar neman magani."


"Uwale dan Allah kada naji maganar nan a wani guri." hankalina a kanta nayi maganar .

Gabad'ayansu suka rike baki Uwale cikin jin haushi tace"Sa'ida munafuka kika mayar dani kome."?


Da sauri nace"Aa ni ba haka nake nufi ba halinki na sani idan labari yayi miki dadi sai ki manta ki fadi abinda bai kamata kowa yaji ba."


Cikin takaici Gwaggo tace."Uwale tashi kiyi tafiyarki ina dalilin wannan abu yarinya ta dinga kokarin cin fuskarki a banza a wofi."

Da sauri nace."Gwaggo kinga don Allah ki tsame kanki daga cikin maganar nan tunda dai ke kinqi taimakawa ai sai kija bakin ki kiyi shuru ki kyale wanda zasuyi.

Tsaki taja ta bar gurin.

Handbag d'ina na bude na dauko kudi dubu dubu guda biyar na bata da fadin "Uwale ga sadaka Allah ubangiji yasa a dace." Hannu tasa ta 'karba da fadin."ameeen ameeen." Na mika mata dubu daya da fadin."Ga wannan sai ki kara kudin mota." tasa hannu ta kar'ba da fadin."To nagode a na tashi na tafi kada naje na samu layi a gurin.''

Nace."To shikkenan Allah yasa a dace."Takalmanta tasa tana amsawa ta leqa kicin a gurguje tayi sallama da Gwaggo ta fita daga gidan.


Mikewa nayi jiki a sanyaye naje na kwanta gadon gwaggo ina tunanin wautar dana tafka sai yanzu da na zauna nayi tunani da nazari na gane manufar Khalid wato ya bugi cikina yaji dukkanin sirri na yana min dariya idan banda tsabar iskanci a ina zai samo maganin da yake magana gabadaya kaina ya daure tunani na ya ta'allaqa gurin ganin na samu mafita akan abinda yake damuna shiyasa na saki jikina dashi na fada masa abinda ke damuna dariyar da yake itace ta tabbatar min da cewa kawai tsabar iskanci ne babu wani taimako da zaiyi mana.

Kwanciya na gyara a kan gadon ina addua akan Allah yasa dai a dace da magani idan hakan ta faru itama Uwale dole a samu kyauta ta mussaman ayi mata mutukar ta kasance wacce tayi sanadiyar samuwar abinda muke bukata.


Motsin shigowarta naji dakin nayi saurin rufe idona "Sa'ida kinyi bacci ne."? Shuru nayi mata sai naji tana cewa" Allah sarki watakila tayi bacci oh! ko wane bawa dai da irin jarrabawarsa a rayuwa." Fita tayi daga dakin na bude idona ina kallon bakin kofar da tunanin maganarta ashe tasan kaddara ce amma idan rigimar ta tashi sai ta mayar da laifin kaina.

Jin ana kiran sallah yasa na sauko daga gadon fita nayi domin daura alwala lokacin har ta kammala aikinta tana kashe wuta.

Kallonta banyi ba na shiga bandaki na fito ina daura alwala tace."Ai na shiga dakin naga kina bacci."

"Umm." abinda nace kenan na cigaba da abinda nake tace."Idan kinyi sallar ai sai kici abinci ko gashinan na kammala." Ina kokarin mikewa nace."Nifa Gwaggo ba cin abinci ne ya kawo ni gidan nan ba zaman da kika ga nayi ina jiran Uwale ta dawo na kar'bi magani nayi tafiyata." Ina gama maganata na bar gurin ba tare dana saurari abinda za tace ba.


Ina zaune akan dadduma ta shigo dakin, na kauda da kaina da fadin."Gwaggo na tashi a hannunki nayi wayo a hannunki kiyi min aure amma ace ba zaki rufe sirri na ba shin wannan wace irin rayuwa ce Shikkenan tunda abin naki ya zama haka dukkanin matsala ta zan dinga tunkarar mahaifiyata da ita nasan tunda ita ta haife ni zata rufa min asiri kuma ta taimake ni."

Uffan ba tace dani ba ta hau kan dadduma ta tayar da sallah, koda ta idar da sallar sai da taja carbi kafin ta ajiye ta mike ta fita.

Kwanonin abincin ta shigo dasu dakin ta ajiye daidai lokacin Ya shigo dakin ya tsaya daga bakin kofa da fadin."Gwaggo Ummatu bata dawo bane."?

Tace."Khalid yaushe Rabi zata dawo gidan nan ka manta 'Yar gidan yayarta ce ta haihu ko bata fada maka ba."?

Kansa ya sosa yace."Wallahi ranar da akayi haihuwar ma ta fada min na manta ne gabad'aya okey ina tsammanin yanzu idan naci abinci zanje can Dalan nayi sallama dasu."

Tace."To hakan yayi daidai sai ka shigo kaci abincin." Yace."Bari tukkuna na watsa ruwa zafi akeyi wallahi." Tace."Ai dama kai ko babu zafi a gari baka gajiya da kuzawa kanka ruwa.

Dariya kawai yayi ya bar gurin.

Kallona tayi da fadin."Sa'ida kin gama cin mutuncin.''? A hasale nace."Gwaggo wane irin cin mutumci gaskiya ce na fada miki tunda dai kin kasa rufa min asiri zan koma gurin uwar data haife ni."

Kuka ta fashe dashi tana nuna kirjinta tace."Ni kike fadawa wannan maganar."? dauke kaina nayi na 'bata rai sosai! ta cigaba da share hawaye tana fadin."Ai shikkenan tunda fahimtar da kikayi min kenan babu komai akwai Allah."

"Gwaggo laifin me nayi miki da zaki had'a ni da Allah nifa wallahi Uwale nake jira ta dawo na bar muku gidanku."!

Baki ta rike tana kallona a tsorace! nace." Eh ba zan zauna a gidan da ake nuna min wariya ba a zahiri kina nunawa kin fi son Khalid dani."

Hawaye ta share ta saisaita kanta a nutse tace."Sa'ida maganar nan ta wuce kada kisa jinina ya hau dake da Khalid duk daya kuke a gurina saboda haka kiyi hakuri ki daina wannan maganar dazu ma raina ne ya 'baci shiyasa kikaji ina surutai amma tunda bakya so na daina Allah yasa a dace da magani mai kyau."

Uffan bance mata ba ta cigaba da maganganunta nace."Gwaggo bafa zanci abincin nan ba ki daina wani damuwa a koshe nake."

Ta dinga kallona tana girgiza kanta dauke kaina nayi dan ko kadan bata bani tausayi ba saboda halinta.

Shigowa yayi ya ganta cikin damuwa....."Gwaggo menene naga kamar kinyi kuka idonki yayi jawur."
Kallonsa nayi na ganshi daga shi sai short Neckar ko arzikin singlet babu a jikinsa, gabadaya hankalina ya tashi na sunkuyar da kaina kasa gabana na bugawa.


Dakin ya shigo sosai ya zauna kusa dani ina jin kamshin sabulun da yayi wanka wani masifaffen feeling's ya dinga taso min.


"Aunty Sa'ida me ya faru.''? ba tare dana kalleshi ba nace." Gaka gata ka tambaye ta mana." Murmushi yayi yace."Gwaggo menene."?

Ajiyar zuciya ta sauke tace."Khalid wai ba za taci abincin nan ba shine nake mamaki." Ya kalle ni da fadin."Akan wane dalili."? Tsaki naja na mike na fita na bar musu dakin. ita dashi gabadaya suka bini da kallo.


Tsakar gida na zauna ina duba waya ta ina jinsu suna magana 'kasa-'kasa sam bai dame ni ba babban burina naji sallamar Uwale da magani a hannunta.


To sai daf da magariba Uwale ta dawo a jigace hannunta rike da wani katon buhu cike da itacen magani da saiwowi.

Gwaggo ta gyara mata tabarma tana mata sannu.....Tace."Gwaggo bani ruwa nasha yau nasha bakar wuya kafin na samu ganin mai daburau."

Gwaggo da sauri ta mike ta ciko kofi da ruwan randa ta bata tasha sosai ta ajiye kofin tana sauke numfashi.....Sai da hankalinta ya dawo tukkuna nayi mata sannu ta amsa da yawwa Sa'ida ai tafiya tayi kyau sosai tunda anyi dace an samo magani gashinan cikun buhu.


Nace."To Alhamdulillahi Nagode sosai sai kiyi min bayanin maganin." Tana kwance buhun tace."Ai dama yanzu zanyi miki bayanin yanda zakuyi amfani dashi."

Tsaf ta zazzage itacen maganin da wasu gari a daure a leda da saiwa ta shiga yi min bayani nace."To insha Allahu zanyi kokarin bin ka'ida. Tace."Kuma mai maganin yace."Bayan sati biyu a koma masa da bayanin yanda mara lafiyar yaji a jikinsa." Nace."To shikkenan Uwale insha Allah zanzo har gidanki da bayanin." Ta shiga mayar da maganin cikin buhu tana cigaba da magana da 'kawar ta.

Gwaggo ta mike da fadin."Bari na kawo miki abinci nasan dai kinsha yunwa acan." Tace."Aikuwa dai dama kin san babu masu siyar da abinci da kyar na samu mai awara na siya na toshe wata kafar."

Tace."Ai dama dubara akeyi idan mutum zashi irin wannan guri sai yayi abincinsa ya zuba a fulas ya tafi dashi maganin yunwa." Tace."Wallahi kuwa ai na dauka ba zan dade ba shiyasa ban tafi da abinci ba sai kuma naje na tarar da layi jamaa kowa lalura ta ishe shi."
Gwaggo dake kicin tace."Ai fa abinda ake ta fama dashi kenan Ubangiji Allah yayi mana magani." Gabadaya muka amsa da ''Ameeen Ya Allah."
*SADAUKARWA NE GA IYAYE NA BIYU*

*FATIMA MUSA (MOMMY NIJAR)*
*TARE DA*
*USAINA ABDUL-MALIK ISA (KAITA)*
*(HAJIYA BABBAH)*

*_Ha'kika ina Alfahari daku da irin kaunar da kuke min.🥰🤝🏻💜_*



*81&82*
Gwaggo abinci mai yawa ta had'awa Uwale tasa mata miya da nama sosai ta ajiye mata a gabanta ta dauki kofin silban gabanta ta debo mata ruwa a randa ta ajiye mata tare da zama kusa da ita. Uwale tace."Sannu da aiki Gwaggo nagode sosai da hidima." Gwaggo tace."Haba Uwale ai babu komai an riga an zama d'aya muma mun gode sosai da taimakon ki muna rokon Allah yasa kwaliya ta biya kudin sabulu." Uwale na kokarin kai lomar abinci bakinta tace."Insha Allahu za'a dace domin mutane da yawa sun sheda kyawun maganin mai daburau shiyasa jama'a keta rububin zuwa gurinsa kar'bar magani."

Gwaggo tana kokarin magana Ummatu ta shigo gidan kafafunta fururu! gabadaya muka bita da kallo gani na a zaune yasa ta washe baki da fadin."Aa ashe amarya ce a gidan.''? babu yabo babu fallasa na gaisheta ina satar kallon jikinta. ta kalli su gwaggo da fadin."Sannunku da gida." Uwale ce kawai ta amsa Gwaggo a dakile tace."Yanzu Rabi ki fita tun farar safiya sai ana kiran magariba zaki dawo."? Shan kunu tayi da fadin."Gwaggo kafin na fita sai da na sheda miki cewa Hamara'u ce ta haihu 'yar dan uwana kuma mune iyaye dole muje da wurwuri muyi mata ayyuka." Gwaggo tace."Wane ayyuka Rabi ke dai kin biya yawon da kika saba dubi kafafunki."? Ummatu tabi kafafunta da kallo na minti biyu girgiza kanta tayi ta bar gurin.......aikuwa suka dasa gulmarta ita da Uwale sai magana suke kasa - kasa nace."Kuna dai rage mata zunubi duk inda taje ita da Allah ku dai babu ruwanku da wannan surutan da kuke gwara ku tashi kuyi alwala dan lokacin sallah yayi.

Uwale tana kokarin mikewa take fadin."Gaskiyarki Sa'ida Allah dai ya yafe mana amma a zahirin gaskiya abinda Rabi takeyi a gidan nan dole ne a taka mata burki."

Shuru nayi ban tanka ba suka mike tare da daukar butoci domin daura alwala.

Uwale sai da tayi sallar isha'i tukkuna ta tayi mana sallama ta tafi bayan ta sake jadadda min yanda za'ayi amfani da maganin data kar'bo.

Karfe takwas da rabi Yaya Aminu ya kira waya ta yace mani gashinan a waje na fito domin nayi masa jagora cikin gidan.

Na kalleta tana fama da redio a hannunta nace."Gwaggo Yaya Aminu yazo yana so ya shigo ku gaisa." Redion ta ajiye da fadin."To ai babu komai ya shigo mana." Mikewa nayi domin naje na shigo dashi.

Ina kokarin fita Kawu ya shigo zubewa nayi gwiwa a kasa ina gaisheshi cike da kulawa ya amsa yana ta farin ciki yace."Sa'ida ashe anan kika yini yanzu yanzu mijin naki yake sheda min."

Nace."Eh wallahi Kawu tun safe ina nan yace nazo na gaishe ku lokacin kuma da nazo kai ka fita dama inata addua Allah yasa kafin na tafi ka dawo mu gaisa."


Yace."Aikuwa ya kyauta sosai kuma naji dadin ganinku keda mijinki kicin koshin lafiya ina rokon Allah ya dawwamar miki da zaman lafiya da kwanciyar hankali a gidan auranki."


A sanyaye na amsa da ameeen ya Allah Kawu." Yace."Kiyi maza kije ki shigo dashi yace yana so ya gaisa da Gwaggo." Nace."To Kawu." Hanya ya bani na wuce shi kuma ya karasa bakin kofar dakin mahaifiyarsa.


Gwaggo cikin girma da mutunci suka gaisa da Yaya Aminu kamar ba itace mai zagin sa da ganin aibun sa ba sai wasa take masa tana masa adduar fatan alkairi. Yaya Aminu da yake mutum ne mai saurin sabo ya saki jikinsa sosai suka dinga hira har ta zuba masa abinci ya zage ciki yana ci harda cire hula ita kuwa sai tsokanarsa take wai kada dai garin santi ya manta hularsa....Cikin wannan halin Khalid ya daga labulan dakin, ganin mu cikin raha da annushuwa yasa ya kirne fuskarsa kamar baya so ya miqa masa hannu da fadin"Barka da dare Alhaji." Yaya Aminu da sauri ya amsa da "Barka dai abokina ya kake ya al'amura."
Babu wani sakewa ya amsa da "Alhamdulillahi." Labulan dakin ya saki zai bar gurin Gwaggo da sauri tace."Jarumi ka shigo kaci abinci mana." Yana kokarin barin gurin yace."Sai an jima yanzu inada uziri." Gwaggo kasa'ke tayi tana tunani yanayin yanda yayi maganar a cunkushe ya nuna mata lallai akwai abinda yake damunsa.

Yaya Aminu sai da ya cika cikinsa tsaf da abinci Gwaggo yasha ruwa babu wani kyankyami ya goge bakinsa da hankici ya kalleta a tsanake yace."Uwargida ran gida nagode sosai yau naci abincin tsofaffi wanda na jima banci irinsa ba.

Gwaggo na dariya tace."To masha Allah ai haka nake so naji kana kira na da uwargida domin dama so nake na kar'be gidan gabadaya.'"

Dariya yayi ya sunkuyar da kansa minti biyu a tsakani ya kalleta da fadin."Gwaggo insha Allahu sha biyar ga azimi zaki je umara k'asa mai tsarki inaso kiyi min addua akan wasu bukatuna."

Gwaggo ta kalleshi cikin farin ciki da kuma tausayi tace."Aminu Allah ya yaye maka damuwarka nagode sosai daka za'be ni a matsayin me maka addua nagode da wannan karamcin.

Na kalleshi a sanyaye nace."Yaya Aminu Gwaggo ta gode sosai Allah ya saka da alkairi." Ya amsa da ameeen ai babu komai Sa'ida insha Allahu tare dani dake zamuje mu dawo." Nace."To Allah ya yarda Allah kuma ya amsa adduarmu.

Yaya Aminu mikewa yayi bayan ya duba agogon hannunsa ya kalleta da fadin."Gwaggo mu zamu tafi sai kinji kira ko."? Ta mike da sauri tana fadin.''To shikkenan Allah ya kaimu lokacin nagode.

Mayafi na na gyara na fito na same su a tsakar gida suna magana har Ummatu ta fito daga gurinta ya dauko kudi masu yawa ya bawa kowacce Ummatu bakinta ya kasa rufuwa sai juya kudin take a hannunta tana zabga godiya, Khalid kuwa na bakin rijiya a zaune yana gyaran fuskarsa uffan bece ba sai da muka zo fita Yaya Aminu ya tsaya yana masa magana Da kyar yace."A sauka lafiya." Tsabar bacin ran abinda yake yasa na watsa masa harara tare da jan tsaki nabi bayan mijina da sauri Gwaggo har soro ta rako mu tana mana fatan alkairi da godiyar abin alkairi.

Koda ta koma cikin gidan Khalid rufe ta yayi da masifa ta inda yake shiga bata nan yake fita ba, Gwaggo dai tasan akan abinda yasa yake bala'i da ta gaji da bashi hakuri sai kawai ta shiga daki ta barshi a gurin.........Bayan ya gama gyaran fuskar zuwa yayi ya tsaya bakin kofar dakin da fadin."Sabida kawai ya biya miki umara sai wani rawar jiki kike masa harda bashi abinci da kawo shi daki har nawa umarar take to ni insha Allahu aikin hajji zan kai ki wata shekarar wannan shashashan mutumin kudinsa na banza ne tunda ba'a hanyar halak ya samesu ba.

Gwaggo tace."Aa Khalid bana san sharri da kazafi Yaron nan Aminu dukiyarsa ta halas ce." a zabure! yace."Waye ya fada miki haka? kina zaune a gida kike masa sheda duk 'yan kasuwar nan macuta ne mutsiyata kawai." Gwaggo baki ta rike tana kallonsa mamaki fal a zuciyarta.

Khalid ya cigaba da masifa da fadin."Shashashan namiji hotiho kawai kullum yana yawo cikin galla-gallan shadda da hula a saman a kansa amma gidansa hoto ne Allah ya tsinewa wannan auran."!

Gwaggo gumi ya dinga tsatstsafo mata ita kam wannan masifa ta isheta wallahi ta dauka yaron tuntuni ya hakura ashe bai hakura ba....Khalid bai saurara dayi wa Gwaggo rashin kunya ba sai da ubansa ya fito tukkuna ya bar gurin yana huci!! koda Kawu ya tambaye ta abinda yake faruwa kasa fada masa tayi ta dinga Kare Khalid din tana fadin."Aa ni ba wani laifin yayi min ba muna mayar da magana ne." Kawu yace."Amma nake jiyo shi yana daga murya kamar wanda yake magana da sa'arsa."

Murmushi tayi cikin kokarin bagarar da maganar tace."Ibrahim kasan Halin Khalid wani lokacin baya abu cikin kintsi amma ni babu wani abu da yayi min na bacin rai."

Kawu girgiza kansa kawai yayi domin yasan kawai ta fadi maganar ne domin ta kare yaron amma babu shakka akwai abinda yake faruwa. Yace."To Allah ya sawake shi kuma wannan yaro da ya biya miki umara Allah yayi masa albarka ya sake daukaka darajarsa." cikin farin ciki ta amsa da ameeen ya rabbi.

Khalid kuwa haka ya kwana da yunwa tsabar bakin ciki da takaici bai ta'ba tsammanin Gwaggo fuska biyu gare ta ba sai yau ashe duk goyon bayan da take nuna masa na gaibu ne tunda gashi yazo ya tarar tana hira da abokin adawarsa a daki har da bashi abinci.......da wannan takaicin ya kwanta ya kuma tashi dashi, a gurguje yayi shirinsa ya fito da jakar kayansa yana kokarin kulle dakinsa kira ya shigo wayarsa.....Oga Labaran ne ya daga wayar suka gaisa cikin mutumci kafin yace."Gani nan na fito Oga kada ka damu." Daga daya bangaran oga labaran yace."To Alhamdulillahi Allah ya kawoka lafiya " ya amsa da ameeen tare da kashe wayar.

Bakin kicin ya nufa inda mahaifiyarsa take ya tsuguna har kasa suka gaisa tace."Khalid har ka fito kenan." Yana duba agogon dake daure a hannunsa yace "Eh Wallahi Ummana inaso na sauka da wuri ne." Tace."To ka tsaya ka karya kummalo mana." Ya mike da fadin."Umma kiyi hakuri zan samu wani abu a mota nasa a cikina kiyi min fatan alkairi." Ummatu tace "To shikkenan Khalid Allah ya kiyaye hanya ya baku nasara akan abinda kasa a gaba.""

Ya amsa da ameeen Ummatu nagode sosai inaso ki cigaba dayi min irin wannan adduar har karshen numfashina." Tace."Insha Allahu Khalid zan cigaba dayi maka kyawawan addua mutukar ina numfashi a duniya." Khalid ya saki fuskarsa sosai yana mata godiya yaji dadi matuka da suka rabu lafiya ba tare da yayi mata wani abu na bacin rai ba. koda ya fito babban tsakar gidan Mahaifinsa ya samu a tsaye a bakin kofar dakin Gwaggo suna magana, hannu ya mika masa sukayi musabaha da juna Kawu yace."Har ka fito kenan."? Yace."Eh wallahi da wuri nake so na sauka. Yace."To Allah ya tsare sai ka kiyaye da abinda na fada maka Khalid kada kaje kasar waje ka hadu da arna ka watsar da addininka ka kula da sallah da salati da istigifari." Yace."Insha Allahu zan kula." Gwaggo ta fito daga dakin tana kallonsa duk tayi kalar tausayi

Kauda kansa yayi yana jin tausayinta kadan a ransa da kyar yace."Gwaggo ni na tafi.'' Murya na rawa tace."Khalid Allah ya tsare dan Allah ka buga kwallo a hankali kada su karya ka kasan kafuran nan basa kaunar musulunmi da gayya ma zasu jefar da kai ka karye."

Duk d'aurewar da yake sai da yayi dariya ya kalleta tana goge hawaye yace."Idan sun karya ni ai ai sai na dawo gida kiyi jinyyata."
Girgiza kanta tayi tace "Bana fatan haka Khalid na fiso kaje ka dawo lafiya." Yana kokarin magana kira ya shigo wayarsa Salmanu ne sai yayi sauri ya daga wayar tare da sawa a kunnensa hanyar fita ya nufa yana amsa wayar hade da jan jakar kayansa....Gwaggo da Kawu suka bishi da kallo tare da bin shi da kyawawan addua gami da fatan alkairi.
[
******
Tun bayan kwanaki uku da suka wuce Yaya Aminu ya daina amfani da maganin gurin Uwale da farko dai kamar gaske duk sanda zan kawo masa maganin zai kar'ba yasha yana ya mutsa fuskarsa sannan idan dare yayi yakan kar'bi na shafawar wanda aka had'a da manshanu ya shafa a gabanshi wani lokacin ma ni yake sawa ina shafa masa maganin a gurin....amma kuma yanzu ban san abinda yasa ba duk sanda zanyi masa maganar maganin sai rai na da nasa ya 'baci! gabad'aya hankalina ya tashi da abinda yake yi na rashin arziki.

Samun sa nayi a kwance a dakinsa na zauna kusa dashi, ya kalleni da fadin."Sa'ida kina da damuwa ne."? Girgiza kaina nayi raina a k'untace nace."Yaya Aminu shifa magani ko wane iri ne hakuri yake bukata babu yanda za'ayi ace daga fara shan maganin ka kwana uku kaga aikinsa a jikin ka dan Allah kayi hakuri ka daure ka cigaba da shan maganin nan."

Shuru yayi be tanka ba na kalleshi da fadin .''Yaya Aminu magana fa nake dan Allah dan Annabi kada ka bani kunya ka bani hadin kai gurin amfani da maganin nan."

Ido a rufe yace."Sa'ida bafa zan sake shan maganin nan ba domun kashe min jiki yake wai shin baki ga yanda na koma bane kullum ina kwance a gida ina bacci sai kace malalaci wannan wane irin banzan magani ne."?

Murya na rawa nace."Ai ko wane magani da irinsa watakila aiki yake a jikinka shiyasa yake kashe maka jiki kuma shi na shafawar kamar yana aiki ko."?

Shuru yayi min. na mike a nutse na dauko 'yar k'aramar robar maganin na zauna kusa dashi hannu na dora a jikinsa da fadin."Dan Allah ka bari na shafa maka kaga jiya da daddare ba'a shafa ba kuma mai maganin yace kada a tsallake ko wace rana kwana bakwai za'ayi ana shafa maganin.

A fusace! ya mike zaune da fadin."Shin wai me maganin nan Ubanki ne ko kuma Kawun ki."!? Sakin baki nayi ina kallonsa gabana na wani irin faduwa." fuska a tur'bune ya cigaba da cewa"Haba kin dame ni akan abinda yake cutar dani dole ne? idan kin damu kiji ki samo wani maganin amma bazan 'kara amfani da wannan ba domin baya amfana min komai sai wahala."

Murya na rawa nace."Yaya Aminu abun har ya kai da zagi kuma." Komawa yayi ya kwanta yana jan tsaki! hawaye suka zubo min kawai na zuba masa ido ina kallonsa takaici da bakin ciki kamar su kashe ni.
Bacci ne ya dauke shi na mike jiki a sanyaye na fita daga dakin ina tunanin ta inda zan 'bullowa al'amarin.


Sai bayan hudu na yamma ya fito tsaf dashi sai kamshi yake fuskarsa babu walwala ya tsaya a kaina yana magana. ''Yanzu idan banda lalaci da tasirin wannan maganin da kika kawo mai zai sanya ni kwanciya a gida nayi ta bacci har la'asar ban fita ba bayan akwai jama'ar dake jira na a waje."

Hannu na daga masa babu walwala a tare dani nace."Yaya Aminu ni dai yanzu ba wata magana nake nema ba kaje kawai Allah ya bada sa'a magani kuma zan zubar dashi tunda baka bukata."

Yace."Hakan shi yafi alkairi domin ba zanyi amfani da abinda zai cutar dani ba." shuru nayi masa. ya kalli agogon hannunsa da fadin."Ni na fita." kasa-kasa nace."Allah ya bada sa'a." Ya amsa da ameeen tare dayin gaba.


Bayan kwana goma da faruwar al'amarin sai ga Uwale tazo tunda na ganta ita kadai nasan akwai abinda ke tafe da ita bayan mun gaisa na kawo mata abinci taci ta koshi sai ta kalle ni a tsanake tace."Sa'ida shuru ina ta tsammanin zuwanki domin naji abinda yake faruwa shuru baki zo ba shine nace to idan zan koma gurin me maganin na shigo na tambayeki halin da ake ciki.

Jim nayi na minti biyu kafin nace."Uwale magani yayi kyau sosai." Yanda na fadi maganar cikin inda-inda yasa ta kalle ni da

Please Login or Register in order to submit comment