Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sallah.

Nafila tayi raka'a biyu tayi sallama sai ta daga hannunta sama hawaye ya 'kwace mata tana kuka take fad'in "Ya Ubangiji Allah ka karkato da hankalin yaron nan gida Allah ka yafe masa kada ka d'ora masa mummunar kaddara Allah Khalidu mai laifi ne a gurinka Allah ka sassauta masa Allah kada ka jarrabe mu da abinda ba zamu iya ba." Kuka ne yaci k'arfinta hannuwanta a sama ta kasa saukewa.

A tsorace na mike zaune ina kallonta gabana na faduwa nace"Gwaggo lafiya meye kike kuka me ya faru."?


Adduar ta shafa a fuskarta murya a dushe tace."Sa'ida dan Allah da Annabi ki yafe wa Khalid abinda yayi miki kaddara ce ki yafewa dan uwanki ko ya samu sassauci.


A sanyaye nace."Gwaggo me ya faru dashi.?

Tana rawar murya tace."Mummunan mafarki nayi dashi Sa'ida amma kafin na farka daga baccin na manta ni dai nasan na ganshi cikin mawuyacin hali jina jina da jini.

Gabana ya fad'i! nace."Gwaggo mafarki ba gaskiya bane ki daina gazgazata shi." Girgiza kanta tayi tace."Sa'ida ni bazan kira kaina waliyyiya ba ba kuma zan kira kaina 'yar baiwa ba amma Allah yakan nuna min abu a mafarkina mai dadi ko mara dadi kuma mafarkin yakan zama gaskiya ko mutuwa za'ayi Allah yakan nuna min a mafarkina shiyasa hankalina ya tashi da yin wannan mummunan mafarkin.

Shuru nayi har yanzu kuma ban daina jin faduwar gaba. ta cigaba da cewa "Dan Allah kice kin yafe masa ko ya samu sassauci." A sanyaye nace"Gwaggo tuntuni na yafe masa ki kwantar da hankalin ki."


Tace."To nagode sosai Allah yayi miki albarka na amsa da ameeen ya rabbi.

Kasa komawa bacci mukayi har asubah tayi mukayi sallah muna idarwa tace lallai wai sai na kira mata shi a waya, to nima nawa 'bangaran jikina yayi sanyi da al'amarin ban yi mata musu ba na kunna wayata na fara laluben number sa.


Na kira sau kusan biyar bata shiga, nace"Gwaggo kin dai ji da kunnanki wayar taki shiga ko."


A sanyaye tace."Watak'ila sun kashe shi." naji gabana ya yanke ya fad'i!

Kallonta nayi hawaye na kwarara a fuskarta tace."Sa'ida na d'an tuno mafarkin ganin sa nayi wasu mutane masu baka'ken kaya sun zagaye shi da bundigogi a hannunsu suna ta dukansa."


Nace"Gwaggo ki samu nutsuwa dan Allah in sha Allahu Khalid na raye cikin koshin lafiya."


"Kayya! Sa'ida bana tsammanin yaron nan nada rai.'' nace" Bari gari ya waye sai a sake kiran wayar tashi."

Tace."to shikkenan." tagumi! ta zabga har yanzu hawaye take cikin zuciyata nace ko wane irin so da kauna take masa.....Nace"Gwaggo yau ba zaki kunna redio ba."?


Kanta ta girgiza min na dauki redion na kunna mata na ajiye mata kusa da ita.

Dauka tayi tana kokarin kashewa tace."Sa'ida rabu dani nayi salati a zuciyata yau bana sha'awar jin redio nafi bukatar na samu nutsuwar zuciya nayi wa yaron nan addua.

Nace"Hakane Allah ya kare shi." ta amsa da ameeen ya rabbi.'' Mikewa nayi na fita tsakar gida domin d'ora ruwan wanka, sai naji motsin fitowarta na jiyo ina kallonta naga tana sa takalmanta da kudi a hannunta.


Nace"Ina kuma zakije da sassafe haka'' Tace."Zanje gidan Marka mai waina na siya domin nayi wa almajirai sadaka."

Shuru nai ina kallonta har ta fita daga gidan na girgiza kaina tare da cigaba da abinda nake.


Har nayi wanka na fito nasa kaya na Gwaggo bata dawo gidan ba, na zauna cikin damuwa na dauki mai ina shafawa a jikina Kawu Iro ya daga labulan dakin, da sauri na gaisheshi ya amsa cikin kulawa yana fad'in "Gwaggo tana bandaki ne."?

Nace." Aa ta d'an jima da fita wai taje gidan Marka siyo wainar gero."

Yana kokarin magana ta shigo gidan. Kawu Iro Kallo guda yayi wa mahaifiyar tasa jikinsa ya mutu ganin yanda ta zabge idunuwanta sunyi fululu.

Yace."Gwaggo lafiya me yake faruwa."? Hawaye suka 'kwace mata tace."Ibrahim babu lafiya domin kuwa Jiya a zaune na kwana tunda nayi mummunan mafarki da yaron nan Khalid na kasa rintsawa.

Yace."Gwaggo dan Allah ki cire damuwar Khalid daga cikin ranki kada ki janyo wa kanki ciwo mai tsanani.


Tace."Ibrahim idan kaga na cire Khalid a raina to mutuwa nayi amma ba zan ta'ba daina damuwa dashi ba.''


Tana gama maganarta ta wuce gurin Ummatu.

Ummatu na tsaka da dama kunu ta ganta ta shigo kicin din, gabanta ya fadi! tunda suke a gidan sai ta irga iya adadin shigowarta gurinta bai fi uku ko hudu ba Allah dai yasa ba wata masifar bace.

"Gwaggo ina kwana."? tafada babu cikakkiyar sakewa.

Gwaggo cikin kulawa ta amsa da fadin" Rabi gurin ki nazo.'' Ummatu ta saki ludayin da take dama kunu dashi tana kallonta .


Gwaggo ta 'kas'kantar da kanta da fad'in "Dan Allah Rabi'atu ki gafarci yaron nan kiyi hakuri ki masa addua Akan Allah ya sassauta masa domin jiya ni nasan mummunan halin dana ganshi a mafarkina.


Ummatu jikinta yayi sanyi tace." Gwaggo dama ai ni ban 'kullaci Khalid ba tunda dama ban yarda da zargin da kuke masa ba.

Tace."To hakane to amma dan Allah ki dage dayi masa addua saboda bakin uwa albarka gare shi ki daina zuwa kina asarar kudin ki a banza addua zaki masa da kyakykyawan fata."


Ummatu tace."To shikkenan Gwaggo insha Allahu zan cigaba dayi masa addua.

Tace."Bari na tsaya na tafi da kunun tunda naga kin gama damawa." Ummatu tace."Aa Gwaggo kije kawai zan kawo muku." Gwaggo 'kin tafiya tayi har sai da Ummatu ta zuba musu kunun a jug ta zuba musu awara mai yawa a silba Gwaggo ta dinga shi mata albarka kamar basu ta'ba samun sa'bani da juna ba Ummatu ta dinga mamakin al'amarin domin tunda suke da Gwaggon bata ta'ba kwantar mata da kai irin yau ba gashi har da ya sanya mata albarka gaskiya dole al'amarin ya bata mamaki.


'Dakin ta shigo ta same ni na gama shiryawa tace."Sa'ida ga kunu nan da zafin sa ki zauna kisha kafin ki tafi.''


Da mamaki! a tare dani nake kallonta kafin nace."Yau da kanki kika kar'bo kunun."? Tace."Eh gani nayi ta gama damawa shiyasa na tsaya na tawo dashi.

Shuru nayi na samu cup na tsiyayi kad'an a warar ma uku na dauka na zauna ina kur'ba, tace"Ki sake kiran wayar tasa mana.

Ba tare dana ce komai ba na dauki wayar na shiga duba number tashi....Kamar dazu wayar ta katse ta'ki shiga.

Nace."Gwaggo sai dai kiyi hakuri fa domin wayar nan ta'ki shiga.kallona take nace." Dan Allah ki daina wannan kukan Gwaggo mutuwa dai ake Jin tsoro idan Kwanan sa ne ya 'kare Allah ya jikansa.


Tace."Sa'ida amma baki da tausayi da imani yanzu sai kiso Khalid ya mutu a wani guri ai idan ma lokacinsa ne yazo nafi bukatar ya mutu a gabana hankali na sai yafi kwanciya idan naga gawarsa.

Nace."Yanzu ma idan mutuwar yayi kina zaune labari zai same ki kuma za'a kawo miki gawar sa har gida.

Ta dinga kuka tana watsa min harara, dariya na kunshe a gurguje na gama abinda nake nayi mata sallama uffan ba tace min ba har na fita daga gidan.


Sai da gari ya waye tukkuna suka samu damar komawa cikin motar kowa ya zauna a gurin zamansa jikinsu duk yayi sanyi da irin 'barnar da 'yan fashi sukayi musu Khalid baiji takaici sosai ba saboda yasan ya tsira da sim card dinsa da 'yan tufafinsa amma duk guzurin kudin da Sukayi shi da Salmanu 'Yan fashin nan sun hargitsa musu kaya sun kwashe a yanzu ko sun sauka a garin na legos sai Sunyi fafutuka tukkuna.


Motar tayi shuru kowa na sake-sake a cikin ransa yayin da direben ke ta sharara guda akan kwalta, tun kafin su karasa inda matar take kwance a gefen titi Mijin nata yake ihu! da fadin"Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un gatacan a kwance sun kasheta.''


Direban suna karasawa inda take ya fara kokarin parking ko kafin ya 'karasa mutumin ya fit ya fito a take ya gangara k'asan wani rami mai Mugun zurfi! gaske.


Hankalin su Khalid ya tashi mutuka hakika tunda yake bai ta'ba ganin masifa da tashin hankali irin na yau ba wannan mugun ramin da mutumin ya fad'a ciki ai sai dai wani kuma, wasu suka nufi inda matar take kwance wasu kuma Sukayi dafifi! a bakin ramin da mutumin ke ciki sai salati suke suna tunanin ita ina zasu taimakeshi.


Khalid yayi masifar tsorata da ganin matar da babu rai a tare da ita har ta fara kumbura ga jini duk ya bushe a jikinta kud'aje da 'kwarika sai bin jikinta sukeyi.......Yarinyar ta na gani uwarta sai ta tsandara ihu!! ta shiga tsakanin mutanan tana so taje inda take...Khalid yayi gaggawar daukarta yana rarrashin ta hawayen tausayi na nema ya kufce masa..


Da yake sun shiga cikin gari yasa basu sha wata wahala ba mazauna gurin suka kawo musu dauki 'yan agaji suka shiga cikin ramin suka fito da mutumin a mace duk ya karkarye, da yawa daga cikin mutanan gurin sai da suka tsorata da wannan tashin hankali masu rauni a ciki suka dinga faduwa suna suma wasu kuwa gefe suke nema su zauna suyi ta share hawaye suna kad'aita Allah shi d'aya.


Khalid wata irin nadama mai tsanani ta rufe shi ya dinga jin kamar ya juya ya koma gida ya nemi gafarar iyayensa da wacce ya zalin ta yanzu idan da 'karar kwana da tuni shima ya zama tarihi ya mutu da fushin iyaye a tare dashi.



Jakar mutumin aka duba akayi sa'ar samun wallet dinsa nan Suka shiga binkicen in da yake a jikin IDcard d'insa aka samu cikakken address dinsa da inda yake aiki. Mutumin dai dan kano ne kuma yana aiki asibitin Koroda dake karkashin gomnati. ba tare da 'bata lokaci ba jami'an tsaron dake gurin suka shiga aikinsu Gawarwakin aka d'aure suka sa a mota suka dauki hanya Khalid ya dinga jin kamar ya tsayar dasu ya bisu ya koma gida suna tsaye a gurin har motar Police din ta 'bacewa ganinsu kafin su koma cikin motar ko wanne da mataccan jiki motar tayi tsit! shima direban duk da ya saba ganin tashin hankali irin wannan amma gaskiya wannan karon ya firgita mutuka jiki a mace ya shiga ya zauna ya kunna motar suka bar gurin...
*SADAUKARWA NE GA IYAYE NA GUDA BIYU*

*FATIMA MUSA (MOMY NIJAR)*
*TARE DA*
*USAINA ABDUL-MALIK ISA (KAITA)*

_*Ina kaunar ku iyayena ina kuma alfahari da irin kaunar da kuke nuna min💜🥰*_


*37&38*
Khalid da Salmanu sun sha matukar wahala kafin wani bayerabe ya tausaya musu ya basu gurin kwana a jikin gidansa, tunda suka sauka a garin suke buge-buge a kasuwanni domin su samu abinda zasu ci idan dare yayi su shiga 'kar'kashin gada su kwanta asuba nayi suke futowa daga karkashin gadar suyi sallah su shiga buge-buge kamar yanda suka saba Akande beyerabe ne kullum yana ganinsu a kasuwa suna bulayi da daukar dako sai ya tausaya musu ya dinga jansu a jikinsa yana nuna musu gurin da zasu shiga su samu aiki cikin ikon Allah kuwa suka kutsa cikin kasuwar su shiga cikin kanikawa masu gyaran abubuwan hawa suka fara taimaka musu da yake duk yawanci masu aiki a gurin 'yan jahar kano ne shiyasa suka saki jikinsu dasu suka basu gurin zama suna nuna musu yanda zasuyi sati hudu sun zama 'yan gari domin gyaran mota kona babur babu wanda basu iya ba.
Idan sun tashi daga aiki sai su nufi shagon da suke kwana wanda yake jikin gidan Akande, watansu biyu a legos suka siyi waya Khalid yasa Sim card dinsa a wayar shi kuwa Salmanu sai da ya siyi wani akai masa rigistar Allah yasa yana da number wayar mahaifiyarsa saboda haka kai tsaye ita ya fara kira.

Khalid kuwa babu wanda yayi tunanin kira sai aunty shi domin kullum da ita yake kwana a cikin ransa zuciyarsa na fada masa cewa ta riga tayi auranta fa sai dai ka hakura duk sanda zuciyarsa tayi masa wannan tunin yini yake cikin damuwa da bakin kishi.



Muna tare da Hauwwa a gidanta mai lalle nayi min na biki kiran wayar tashi ya shigo waya ta a lokacin da naga sunansa yana yawo a fuskar waya ta sai da na zabura! mai lallen tayi saurin rike kafata nace."Dan saurara na amsa waya.

Kafata ta saki na kalli Hauwwa a sanyaye nace."Khalid ne."? Baki ta bude da sauri tace."Ikon Allah dama yana raye a duniya.?

Hannu na daga mata nasa wayar a kunnena.

sanyayyar ajiyar zuciyarsa naji a kunnena kafin naji sautin muryarsa yana kiran sunana.

Na amsa a nutse da fad'in "Khalid tsayin wattanin hudu kana ina ne? shin kasan halin damuwar ka jefe iyayen ka a ciki kuwa? Uwa uba Gwaggo na nan ta'ki lafiya kullum sai tayi kuka kafin ta kwanta bacci tana ganin kamar baka raye a duniya dan Allah ka dawo gida ni idan saboda ni ka tafi to ka dawo na yafe maka.''

A sanyaye yace." Aunty Sa'ida idan na dawo gida zaki aure ni."? Gabana ya fad'i nace."Khalid ashe har yau baka daina wannan tatsuniyar ba."?

Ransa ya 'baci yace."Ki daina kiran soyayyata da ta tsuniya insha Allahu sai ta zama gaske."

Nace."Okey to naji yanzu dai yaushe zaka dawo gida."? Yace."Kina so na dawo ne."? Nace."Eh ka dawo ka nemi afuwar iyayenka ni kuma na yafe maka."

Yace."Aunt Sa'ida idan na dawo gida zan takura miki fa." Nace."Khalid na amince zan aureka ka dawo gida."

Da sauri yace."Da gaske kike.''? Ajiyar zuciya na sauke cikin yaudara nace "Eh da gaske nake kana dawowa za'a daura aure."

Yana dariyar farin ciki yace."Okey ki bani Gwaggo mu gaisa insha Allahu zan dawo gida a satin nan.

Nace."To yanzu dai bana gida ina gidan 'kawata Hauwwa insha Allahu idan na koma gida zan kira ka sai ku gaisa."

Yace."Nagode auntyna insha Allahu zakiyi alfaharin aurena zan jiyar dake dadin duniya auntyna zan kula dake zan zama bawanki zan kwanta ki taka ni zan zama d'an aiken ki zan......Katse shi nayi nace."To duk naji na kuma gamsu da maganarka Ka bari idan ka dawo sai ka 'karasa.

Yar dariya yayi yace."Okey to shikkenan zan kira anjima idan kin koma gida." Ina kokarin kashe wayar nace"babu damuwa.

Hauwwa ta zuba min ido tana kallona tace."Sa'ida babu kyau yaudara fa ban so kikayi masa haka ba ya za'ayi kice zaki aureshi bayan kin san gobe daurin auranki."?

A sanyaye nace."Hauwwa ni nasan halin Khalid idan ba haka nai masa ba wallahi ba zai dawo ba ga Gwaggo taki kwantar da hankalinta dan har fargaba nake na tafi na barta cikin halin damuwa kullum da daddare sai na lalla'bata take bacci.'

Hauwwa tace."To yanzu idan yazo ya tarar kinyi aure fa wane hali kike so ya shiga."?

Kai tsaye nace."Sai yayi hakuri ya kaddara cewa ni d'in ba matarsa bace."

Hauwwa tace." A gaskiya da kamar wuya ya iya wannan hakurin dan yaron yana miki mahaukacin so." Nace."To hauwwa idan ba zai yi hakuri ba sai yayi abinda zaiyi." ta bini da kallon mamaki! na Kalli mai kunshin nace."Baiwar Allah ki cigaba." Ta kama kafata da sauri ta cigaba da akinta.

Khalid cike da farin ciki yake shedawa abokinsa Salmanu abinda ke faruwa. Salmanu na washe baki yace."Kai amma naji dadi wallahi to yanzu ya za'ayi naji kace a cikin wannan satin zaka tafi kuma gashi zamu fara buga wasa a Club kasan kana da mutukar mahimmanci a 'kungiyar nan ko zaka bari mu gama wasan in yaso wani satin sai ka tafi."

Girgixa kansa yayi yace."Salmanu hankalina gabadaya yayi gida wallahi kafin na tafi zan nemi shugaban kungiyar na fada masa uziri na idan za'a d'aga wasan nan da sati uku sai ayi min uziri idan kuma yana ganin da akwai wanda zai kawo a madadi na sai ya kawo dan gaskiya babu abinda zai hana ni tafiya gida.

Salmanu jikinsa yayi sanyi sam baya so abokin nasa ya tafi yana ganin kamar damar da suka samu zata iya kufcewa gashi ogan nasu kullum sukaje training yakan fad'a musu cewa yana so su mayar da hankali sosai domin a wannan karon ne yake so ya za'bi za'kwa'kurai a cikinsu da zasuje america su buga wasa to
wannan dalilin yasa gabad'aya Salmanu baya so a bokin nasa ya tafi domin jikinsa na bashi kamar zasu samu nasara.

Khalid yace."Tashi ma muje chamber d'in Allah yasa mu sameshi." Salmanu ya mike yana kokarin cire kayan jikinsa ya sanja wasu.


Sun ci sa'a sun sameshi yana horar da wasu suka samu kujeru suka zauna bayan sun gaisa....Oga Labaran yace."Khalid me yasa yau baku shigo da wuri ba."?


Yace."Wallahi oga mun je gurin aiki ne kasan dama sai da mukayi maka bayani cewa asabar da lahadi ba zamu dinga zuwa da wuri ba saboda muna zuwa gurin aiki da wuri.

Oga Labaran yace."Eh hakane na manta da wannan bayanin dama inaso kuzo mu tattauna ina fata dai kuna cigaba da shirye-shirye kamar dai yanda na fada muku cewa Mr William zai zo a ranar da zamu buga wasa na k'arshe kuma a ranar za'a za'bi muzakkarai a cikinku domin kuje ku fatata da 'yan wasan dake can america.

Khalid yace."Oga sai da ni ayi min uziri wallahi cikin satin nan nake so naje ganin gida."

Oga Labaran da sauri ya kalleshi cikin yanayi na damuwa yace."Khalid me yasa zakayi mana haka? kana fa d'aya daga cikin 'yan wasan da nake alfahari dasu, ka iya buga 'kwallo sosai shiyasa nake so kai ka zama zakaran gwajin dafi nasan ko munje america ba zaka bani kunya ba sai kuma kazo min da wannan maganar.""


Yace."Oga wallahi uziri babba ne zai kai ni gida ayi min alfarma." Oga Labaran ya girgixa kansa da fad'in "Khalid dole fa kayi hakuri domin ba zaka sa nayi asara ba ka bari muyi wasan nan mu gama lafiya a za'bi wanda suka dace ayi dasu in yaso sai ka tafi kafin lokacin tafiya american ya tashi."

Khalid yayi shuru tare da sunkuyar da kansa tunani yake akan lamarin.....Yana son aunty Sa'ida baya so ta kufce masa gefe guda kuma ga wata babbar dama ta same shi wacce yake saka ran samun nasara wai shin ya zaiyi ne?

Oga Labaran ya kalleshi da fad'in "Khalid kayi shuru kada fa ka bani kunya khalid."

Ya dago kansa da fad'in "Oga zanyi nazari akan al'amarin insha Allahu kafin lokacin zan yanke shawara." Yace."To shikkenan Allah yasa naji alkairi."


Har sun miqe da niyyar tafiya ya hana su yace su sanya kaya suyi wasa. ba tare da 'bata lokaci ba suka bi umarninsa suka shiga d'akin da suke shiryawa suka sako kayan kwallo suka fito kai tsaye filin wasa suka nufa su shiga shiga cikin 'yan uwansu Oga Labaran ya mike yana zagaye gurin tare da addua akan Allah ya daukaka 'kungiyarsa ta Kano pillas.


****
Ina komawa gida na fad'awa Gwaggo cewa Khalid ya kira waya sai ta kwantar da hankalinta yana raye bai mutu ba, ba tare da tace min komai ba naga ta mike ta dauki buta ta fita, alwala ta dauro ta dawo dakin ta gyara dadduma ta tayar da sallah, ina zaune ina kallonta tayi raka biyu ta jima a sujjadar karshe tana addua kafin ta dago....ko bayan da tayi sallama ma sai da ta daga hannu sama ta dinga godewa Allah tana share hawaye.....na cika da d'umbin mamakin irin kaunar da takewa yaron


Mi'kewa tayi ta fita daga dakin minti uku suka dawo tare da Ummatu tana washe min baki tace."Sa'ida ashe Khalid ya kira ki a waya ko."? Nace."Eh wallahi d'azu da rana mun jima muna waya har yace yana so yayi magana daku nace ya bari na koma gida.

Gwaggo tace"Dan Allah ki kirasa 'yar albarka so nake naji miryarsa.

Nace."Gwaggo babu kudi a waya ta bari a samu yaro ya siyo kati.'' Da sauri Ummatu tace"Ga dari biyu a siyo katin." kokarin kwance bakin zaninta take nace"Haba dai bari ba sai kin bada kudi ba bari na duba yaro." Gwaggo tace."Sa'ida na dauka gurin siyar da katin babu nisa inace gurin Auwala ne." Nace."Eh tace."To bani na siyo da kaina." kallonta nayi naga duk ta tashi hankalinta na koma na zauna bakin gado ina gwada siyan kati ta banki babu network ko kad'an na mika mata kudin ta yafa mayafi da sauri ta fita.

Ummatu kuwa tsayawa tayi tana jana da hira na dinga mamakin matar ta saki jikinta dani a yanzu ta daina jin haushina kullum kuma na gaisheta da sauri take amsawa komeye dalili oho.

Gwaggo ta dawo gidan da katin mtn a hannunta da sauri na kar'ba nasa a wayar.......Muryar wani mutum naji a kunne na. nace."Dan Allah Khalid fa."? Yace."A yanzu dai suna filin wasa sai dai idan sun fito." ko kafin nace komai ya kashe wayar.

Gwaggo a sanyaye tace."Ya akayi."? Nace."Wani mutum ne ya dauki wayar yake cewa wai khalid din yana filin wasa.

Gwaggo da Ummatu suka had'a baki gurin fad'in "Ina ne kuma filin wasa."? Nace"Watakila gurin ball yake nufi kun san dama Khalid akwai naci ball a lokacin da yake gida.

Gwaggo tace."Eh hakane kuwa to an jima sai a sake kiran wayar. shuru nayi ina duba waya ta Ummatu tace." To bari naje na karasa ayyukana."Gwaggo tace."To shikkenan daga zarar wayar ta shiga zan fito na fada miki." Ummatu tace to shikkenan a yayin da take kokarin barin gurin.


Kallonta nayi a nutse nace."Gwaggo a yau da daddare nake so naje gidan Ummana nayi sallama da ita." Gwaggo tace."Ba zaki bari ba gobe idan za'a kai ki dakin ki sai na raka ki." Nace."Aa Gwaggo gwara naje yau din." Tace."To shikkenan Sa'ida ai ni ban ta'ba ganin biki irin naki ba sam baiyi farin jini ba.

Nace"Saboda me kike ce haka."? Tace."Ai gani nayi gidan nan yaki cika da mutane makota ne kawai suke shigowa a tsaitsaye suyi Allah ya sanya alkairi su fita."

Nace."Gwaggo wannan kuma kanki zaki tuhuma ina dangin suke."? Tace." Sa'ida kenan ai ni dangina duk sun mutu saura qalilan dama bamu da yawan zuria ko baki gani bane."?

Nace."Hakane amma ai Ummana tana taro a gidanta ita da 'yan uwanta'' Tace."Aikuwa mu dai sai gobe idan an daura aure zamuyi namu taron."

Shuru nayi tace."Dan Allah ki zauna a dakin mijinki lafiya tunda dai Allah ya had'aki da kishiya mai mutunci to ki 'ki ji ki 'ki gani babu ruwanki da 'yan bani na iya kada 'kawar data zugaki ki dauka.

Nace."Insha Allahu Gwaggo zan bawa mara d'a kunya." Tace."Allah ya sanya alkairi Ya bada zuria dayyu'ba." a zuciya na amsa da ameeen.

Dakin yayi shuru na minti biyu kafin tace."Sa'ida Alhaji Shamsu mutumin kirki ne kwarai duk hidimar kayan daki ya dauke ya hana Ibrahim siyan komai duk abinda kika gani a dakin ki to Alhaji Shamsu ne ya siya miki saboda haka ki rike shi da kyau kinji ko."

Nace."To Gwaggo insha Allahu.....Ta dauki goro ta gutsira tana taunawa tace."Oh! yau dai zanji muryar Khalid a kunnena wallahi ni kadai nasan halin damuwar da nake ciki akansa, gashi lokaci guda Allah ya amsa addua ta.

Nace."Gwaggo kin san wani abu."? Girgiza kanta tayi tana kallona, nace."Khalid nayi masa dubara kancewa ya idan ya dawo gida zan aureshi koda zaiyi miki maganar to ki nuna masa hakane.

Shuru tayi tana kallona kafin tace."Sa'ida me yasa kike yaudareshi gobe fa za'a daura miki aure."

Nace."Gwaggo Khalid fa idan ba haka akayi masa ba ba zai dawo gida ba zai bar zuciyoyinku cikin damuwa shiyasa nayi masa haka.

Shuru tayi na minti biyu kafin tace."To Allah ya sanyaya masa zuciyarsa idan ya dawo ya iske abinda ba shikkenan ba.

Nace."Ameeen ya rabbi sai

Please Login or Register in order to submit comment