Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sameku lafiya." Tace."Lafiya kalau alhamdulillhi Ya iyalin naka."?

Yace." Duk suna nan kalau." Tace." To masha Allah sai ka tashi ka tafi gurinsu su ganka kada ka shiga hakkinsu."

Yace." Tom ki bani abinci naci." Girgiza kanta tayi tace."Aa babu ruwana ba zan baka abinci ba mai girki taji haushina.

Yar dariya yayi yace." Gwaggo bana sha'awar komai sai abincin ki kawai ki bani idan da akwai."

Jim tayi tana nazari tace." Bari na baka kadan idan kaje gida sai ka 'kara wani."

Yace." To ki had'a min bari na shiga gurin Ummatu mu gaisa na fito." Tace." Tom shikkenan sai ki fito.


Da 'Kyar Gwaggo ta kore shi ya tafi dan bayan ya gama cin abincin kwanciya yayi kusa da ita tana bashi labarai sai dariya yake kyalkyalawa ganin dare yayi beda niyyar tafiya gida yasa tace ita kwanciya za tayi ya tashi ya tafi gurin iyalinsa da kyar ya tashi ya tafi cike da 'kaunarta a cikin ransa.


Sai da ya fara duba Jamila tukkuna ya nufi Gurin ta.

Duk da nasan yau zai dawo gida Ban yi tsammanin zai shigo inda nake ba wannan dalilin yasa ban zauna zaman jiransa ba na shige daki nayi kwanciyata.

Maganarsa kawai naji a kaina, da sauri na bude idona ina kallonsa, ganin fuskarsa a murtuke yasa gabana faduwa ni kam Allah yana jarrabata da masifaffun maza.

Zaune na mike a sanyaye nace." Khalid ka dawo ashe."? a dakile yace." Na dawo ina fatan kuna lafiya."? Nace." Lafiya kalau Ya hanya."? shuru yayi min kawai ya zuba min ido." Nace." Kana bukatar wanka na had'a maka ruwa."?
"A'a idan ina bukata zan shiga na had'a da kaina yanzu inaso nayi magana dake ne." Yanda yake magana a harzu'ke yasa na gane cewa lallai da tashin hankali ya shigo gidan.

*103*
A nutse nace."To Allah yasa alkairi ne ina sauraranka." Cikin sigar tuhuma yace."Har yanzu akwai sauran alaqa a tsakanin ki da Alhaji Nura ko."? Gabana yayi wani irin fad'uwa! Ido na tsira masa raina idan yayi dubu ya 'baci nace."Khalid wace irin magana ce wannan."?

Hannu ya d'aga min "Kinga tambayarki nayi yana da kyau ki bani amsa ba ki tambaye ni ba." Ajiyar zuciya na sauke tare da bawa zuciyata hakuri nace."Tunda nayi aure alaqa ta yanke a tsakanimu.''
"To mai yasa yake bibiyarki har yanzu."? Kallonsa nayi duk ya tsareni da ido Nace." A'ina zan ganshi da har zai bini."

Tsaki yaja cikin tsananin kishi yace."Yau yaje can Mandawari ya samu Kawu yana cin mutuncinsa har da fad'in ba ayi masa adalci ba kin san Allah wannan mutumin yana cin darajar abu guda ne da ba don haka ba da tuni na dauki mataki mai tsauri a kansa sabida haka ki fad'a masa cewa komai maitar sa dole ya hakura dake idan kuma yaqi zai k'are rayuwarsa a prison."

"Ka daina wannan maganar Khalid yanzu ni a ina zan sameshi har na fad'a masa sa'kon ka a kansa don Allah ka rage kishi ba abune mai kyau ba.''


" Wannan abun da nake ba kishi bane gyara ne na lura dake dashi baku da Ilimin addini ba kusan menene hakkin aure ba shiyasa kuke abinda kuka ga dama to ke d'in ma tsatstsauran mataki zan dauka a kanki mutukar baki daidaita sahun ki ba."


"Khalid ni kake kira da suna jahila har kana fadin ban san hakkin aure ba har yaushe aka haife ka? yaushe kazo duniyar da zaka dinga yi wa mutune rashin kunya ko ka manta cewa a gabana aka haife k..........Kafin ta 'kara maganar ya kifa mata lafiyayyan mari! yana wani irin huci yace." Kada ki kuskura kice zaki min wannan haukan! ranki ne zai 'baci wallahi ina ruwana da wani shekarun ki duk girman ki a k'arkashina kike dole kibi umarnina idan ba haka ba ki fuskanci bacin raina."

Yana gama maganar ya bar gurin yana numfarfashi na bacin rai.

Hannu dafe da fuska na bishi da kallo har ya bude kofar toilet din ya shige.

Wasu hawaye masu tsananin zafi ne suka tsinke min wai yau yaron nan ni yake mari ikon Allah! wani abu mai nauyi ne yazo ya tsaya min a makogwaro shin wai menene mafita? ta yaya zan daidaita alaka ta dashi wai shin gabad'aya haka halin maza yake? babu shakka idan duk haka halinsu yake dole aure ya dinga saurin mutuwa babu uziri a cikin al'amuransu duk mazan data aura hakan suke da irin wannan halin.

Ina jin motsin fitowarsa nayi saurin Kwanciya ido na rintse ina nanata kalmar innalillahi wa'ina ilahi raji'un a cikin zuciyata.......Ina jinsa ya gama shirye-shiryen sa yazo ya kwanta gefe na amma ko da wasa baiyi kuskuran ta'ba wani sashe na jiki na ba......Cikin mintinan da basu wuce goma ba naji saukar numfashinsa bacci har ya daukeshi, ajiyar zuciya na sauke a hankali na lalla'ba na sauka daga gadon toilet na nufa domin daura alwala Nafila zanyi domin na kaiwa Allah kuka na.''


Alhaji Nura kuwa tsabar tension ya sanya sitiyarin mota ya k'wace daga hannunsa a take motar ta dinga walagigi a kan titi abinka da daran sanyi sahun mutane ya dauke sai jefi-jefi Cikin tashin hankali ya dinga kokarin kashe motar domin ta tsaya abun yaci tura sai kawai ya shiga kalmar shahada Mussaman daya hango wata katuwar akori kura cike da katako tayo kansa. hannu na karkarwa ya fara kokarin bude motar domun ya fita daga ciki sai kawai yaji motar ta hantsila dashi 'kasa......"Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un." A take motar tashi ta fara hayaki wuta na kokarin tashi, hayaniyar jama'a ya dinga ji sama-sama a kunnenshi ya dinga kiran sunan Allah yana kalmar shahada wutar ce ta tashi a daidai lokacin da jama'a ke kokarin taimakon sa ganin haka yasa kowa ya watse daga gurin wuta ta tashi a motarsa da motar katakon da suka had'u. da kyar 'yan a gaji suka samu nasarar kashe wutar gurin ya turnuke da haya'ki Alhaji Nura k'urmus aka fito dashi duk wani mai imani idan ya ganshi sai ya zubar da hawaye Allah sarki duniya ashe dama Alhaji Nura daf yake da barin duniya babu wanda ya san gaibu sai Allah....Labarin mutuwarsa ya zagaye garin Kano saboda shi din sanannan mutum wanda duk mutumin da yake shiga kasuwar Kwari ya san da zaman shi Abokan kasuwancin sa suka shiga alhini da damuwa.

Gwaggo kuwa kuka ta dinga yi tana fad'in "Allah Sarki Alhaji Nura Allah ya jikan ka mutumin arziki babu kai babu shiga wutar jahannama Allah ya jikan ka ya kar'bi shahadar ka." Rigima tasa akan lallai sai Kawu ya shirya ya kaita gidan mutuwar domin ayi jana'iza da ita.

Kawu da yake shima a cikin alhini yake bai mata gardama ba ta shirya ya d'auketa a motarsa domin zuwa gidan jana'izar DUNIYA KENAN ALLAH KASA MU CIKA DA KYAU DA IMANI.


Koda Khalid yazo gidan Ummatu ke sheda masa mutuwar jikinsa ne yayi sanyi damuwa da nadama suka baibayeshi ashe ma dik wannan hargitsin mutumin saura kad'an ya mutu kai gaskiya al'amarin ya girgiza shi mutuka, adduar samun rahamar Allah yayi masa yayi mata sallama domin tafiya harkokinsa.


To koda ya dawo da daddara kasa fad'a mata mutuwar yayi ya dai sassauta fuskarsa Sa'i da lokaci kuma yana satar kallonta da tunanin yanda zaiyi ya fad'a mata mutuwar mutumin.


Washe gari da safe yana shiryawa na shiga dakin cikin rashin kuzari nace." Amma Zaka tsaya kayi break fast ko."? Ya kalleta da fadin." Ba zanci abu mai nauyi ba don bana so jikina ya mutu za muyi wasa da abokaina sai dai idan na dawo.

Nace."Ai ko tea kasha ka gasa cikin ka ko." Yace." To shikkenan muje ki had'a min.'' Gaba nayi ya biyo bayana, tea din na had'a masa ya dauka yana sha yana kallona ni kam gabad'aya jikina a mace yake na rasa abinda yake damuna.


"Kina da labarin mutuwar.....Kasa 'karasawa yayi kawai ya zuba min ido.

Cikin fad'uwar gaba nace." Mutuwa waye ya mutu."?

Sunkuyar da kansa yayi yana motsa tea din gabansa yace." Sai hakuri dukkanin mai rai mamaci ne Alhaji Nura ya rigamu gidan gaskiya kwana biyu da suka wuce."


Wani irin kallo nake masa kafin wasu zafafan hawaye su wanke min fuska nace." Yanzu Alhaji Nura ya mutu har anyi kwana biyu amma a rasa wanda zai fad'a min."

Haushi ta bashi ganin tana kuka, sai kawai yaja bakinsa yayi shuru ya cigaba da kur'bar tea d'insa.

"Khalid me yasa kasan da mutuwar baka fad'a mun ba ashe shiyasa kwana biyu gabad'aya na rasa abinda ke damuna Allah Sarki Alhaji Nura ya mutu ya bar wannan duniyar mai cike da rud'ani."

Ya kalleta da fad'in." Wannan kukan dai da kike bashi da fa'ida addua zaki masa idan kuma zaki bishi lahirar dama hanya a bud'e take."


Cikin hawaye tace." Eh idan lokaci na yayi dole na tafi ko inaso ko bana so babu wanda zai zauna ya dawwama a duniya can ne gidan gaskiya sabida haka dik wanda ya dauki zafi da duniya to gwara ya sauke domin ba matabbata bace."

'Bata rai yayi yace." Sa'ida maganar nan ta isa haka bana bukatar ta." Miqewa nayi na bashi gurun, ina jin sanda yake jan dogon tsaki a kaina.


Bayan Kwana uku da faruwar al'amarin Hauwwa har gida tazo tayi min gaisuwa muka jima muna jajanta al'amarin yanda take bani labarin irin mutuwar da yayi yasa na dinga zubar da hawaye nace." Hauwwa aini gabadaya Khalid bai fada min ba yace kawai ya mutu amma bece dani accident yayi ba."

Tace." Aikuwa yana da kyau kije gaisuwa domin a ranar da mukaje gaisuwa da jama'ar gidanmu Mahaifiyarsa da matarsa Murja sai tambayarki suke."


Nace."Allah Sarki Insha Allahu zanje nai musu gaisuwa Hauwwa amma bana tsammanin har ya mutu da aure a tsakaninsa da Murja kin san tunda asirinta ya tuno shikkenan suka rabu."

Hauwwa tace." Allah sarki amma ba kiga yanda ta shiga damuwa ba ni dai har muka fito daga gidan bata daina kuka ba.''

Nace."Hauwwa ai dole aunty Murja tayi kuka Uban 'ya'yanta ne fa kuma ta cutar dashi sosai ta yaudareshi ya dauki amana da yarda ya bata amma ta zalince shi take masa fasikanci a gida."

Hauwwa tace." To Allah ya shiryeta yasa mutuwar tasa ta zama silar shiryuwarta Allah kuma ya raya abin da ya bari."

Hawaye na share da fad'in." Ameeen ameeen Ya Allah."


Mun jima tare da Hauwwa muna hira nan take bani labarin tsakaninta da Yaya Aminu sun fahimci juna sosai amma kuma tana jin tsoron auransa saboda kada ya kasa biya mata bukata.

Kwantar mata da hankali nayi nace." Hauwwa insha Allahu ba zaki samu matsala ba domin kuwa ina ji a jikina cewar Yaya Aminu ya samu lafiya saboda haka ki aureshi da kyakykyawar manufa."
Tace."To shikkenan Sa'ida ki taya ni da addua akan al'amarin." Nace."Insha Allahu zan miki addua Hauwwa Allah ya baku zaman lafiya."
Ta amsa da "Ameen ya Allah 'kawata."

Duk da nasan ba a gurina yake ba sai da na zauna zaman jiran shigowarsa domin sheda masa uziri na na zuwa gidan gaisuwar Alhaji Nura, to har wajen goma da Rabi na dare ina zaune a falo bai shigo ba mikewa nayi na nufi bakin window domin na duba naga ya dawo ko kuwa wani sa'in haka yake yi ko ya dawo baya shigowa yayi min sallama sai da safe idan zai fita, duka motocinsa suna nan alamu ya nuna ya jima da dawowa, girgiza kaina kawai nayi na saki labulan window din daki na nufa domin na kwanta na samu nutsuwa amma a zahirin gaskiya al'amarin yaron ya soma isa ta.

Washe gari
Da wuri na kammala komai na shirya tsaf na zauna zaman jiran shigowarsa...........Cikin 'kananun kaya ya shigo ya shirya tsaf da shirin futa amma babu walwala a tare dashi.

Kauda 'bacin raina nayi na gaishe ya amsa yana gyara wuyan rigarsa Yace."Za muje asibiti da Jamila yanzu." A nutse nace."Me yake damunta."?

'Dan ya mutsa fuska yayi yace."Zazza'bin dare take sai kasala da rashin kwarin jiki." Nace." Allah sarki Allah ya bata lafiya ." Ya amsa da ameen yana kokarin fita.......Sunansa na kira yaja ya tsaya yana kallona.

Nace."Inaso naje gidan gaisuwar nan."? Shuru yayi yana kokarin bude kofar dakin. Nace." Kaga yau sadakar bakwai zan samu jama'a sosai sai nayi musu gaisuwa."

Cikin takaici yace."Ke yanzu idan akace dake kije sai kije."?

Rai a 'bace nace." Wace irin magana ce wannan ko babu haihuwa a tsakanina da mutumin akwai ala'kar aure data had'amu kada kuma ka manta irin hidimar da yayi mana nida Gwaggo wannan mutumin bai cancanci wulakanci ba."


A harzu'ke yace." Ke komai qabli da ba'adin da zaki kawo min babu inda zakije mutu'kar ni ne zan baki umarni idan kikayi masa addua ma a gida ta isa.

Yana gama maganarsa yasa kai ya fice daga dakin....Rasa bakin magana nayi kawai na tsirawa guri guda ido ina mamakin al'amarin.



Jamila ashe ciki ta samu sai bayan sun je asibitin likita ya tabbatar musu dashi Khalid yayi farin ciki sosai sai dai kuma likita ya kafa sharad'ai domin ingantuwar cikin nasu mahaifar Jamila bata da k'wari tana saurin budewa likitan yace kada ta dinga daukar abu mai nauyi babu zurga-zurga sannan shima Khalid din kada ya takura mata da fitina. duk abinda za suyi su bari cikin yayi 'kwari tukkuna.


Jamila rawar kai ya 'karu sai langwa'bewa take miji na rarrashinta Baito kakarsu 'kullo kaya tayi ta tare a gidan wai tazo tayi jinyar ta zuwan ta ne ma yasa nasan da samuwar cikin dan har sashena ta shigo tana yar min da habaici ni dai uffan ban ce mata ba ta gaji da surutan ta ta tashi ta tafi.


Tun da likita ya kafa masa wannan sharad'in ya takura min da fitina babu dare babu rana gajiya nayi na daina yarda yana wahalar dani da yake makiri ne sai wani shagwa'be wani sa'in har kuka yake min yayi ta rarrashina amma fa idan rashin mutuncinsa yazo sai ya sauke min sama da kwando goma hakuri kawai nake da zaman aure domin nasan ibadah ne.


Gwaggo tazo duba Jamila da 'yan kayan dubiyarta...... guri na ta fara yada zango muka gaisa sosai na bata abinci taci ta koshi sai bayan tayi sallar azuhur ne ta kalle ni cikin alhini tace."Ke kuma Sa'ida me yake damunki naga kinyi rama dubi kashin wuya ko dai kishi kika sa a ranki."

Girgiza kaina kawai nayi nace."Gwaggo wane irin kishi kuma Khalid ne kawai yake azabtar dani yaki bari mu zauna lafiya masifar yau daban ta gobe daban kullum babu sassauci."


Tace."Me yasa kin san halinsa ba zakiyi hakurin zama dashi ba ina nufin kiyi kokarin ganin kin kauda abinda zai kawo muku sa'bani a tsakaninku."


Girgiza kaina nayi nace." Gwaggo kenan ban san me zance miki ba amma ni nasan ta kowane 'bangare bana zalintar yaron nan shine kawai ya kasa kwantar da hankalinsa."


Tace."To kuwa idan hakane zaizo ya sameni ni bana son rashin adalci na lura dama kamar yafi karkata gurin kishiyarki to mutukar yace ba zaiyi adalci a tsakaninku ba yana tare da fushin Ubangiji."

Nace."Yana dai da kyau ki zaunar dashi ki masa fad'a ni na gaji da wannan masifar wallahi.'' Tace."Kada ki damu tashi ki rakani na duba jikin nata.

Hijabi nasa muka fita tare.........Kaca-kaca muka samu falon Baito da Ummatu da mahaifiyar Jamilan suna zaune sai hira suke sun ci abinci dik sun baja-baja dashi a kasan kafet Jamilan kuma na kwance akan doguwar kujera tana bacci.

Gwaggo ta samu guri ta zauna tana kallon Ummatu tace."Ashe nan kika nufo kema."? Cikin inda-inda tace."Eh wallahi nazo duba jikin nata ne " Tace."Ai babu laifi.''

A nutse na gaisa dasu suka amsa babu yabo babu fallasa Gwaggo kuwa babu wacce ta gaisar a cikinsu ya mutsa fuskarta tayi tace." Ku kuwa don Allah bakwa jin tsami da karni a falon nan wace irin rayuwa ce wannan kuzo gidan yara kuna 'barna a maimakon gyara."

Falon yayi tsit! cikin zuciyata nace."Gwaggo ba'a ci miki bashi........Ta cigaba da cewa." Ai amfanin zuwanku shine kuyi mata gyare-gyare ku sata tayi wanka ku kwantar mata da hankali amma duba don Allah sai hayaniya kuke kunyi kaca-kaca da gurin Haba Baito a wannan zamanin da ake saurin daukar ciwo ai idan su basu da hankali ke kina dashi sai ki tsawatar musu."

Baito ta 'bata rai da fad'in"Gwaggo Matsalata dake kenan shiga sabgar da bata shafe ki ba ina ruwanki da abinda idonki ya gane miki."

Tace."Babu ruwa na amma ni bazan ga abunda bai dace ba nayi shuru dole sai na fadi gaskiya koda zaku tsire da tsinken tsire ." Nace."Gwaggo dan Allah maganar ta isa haka.

Jamila ta mike zaune tana hamma! Gwaggo ta zuba mata ido tana kallo magana ce a bakinta amma dai tayi shuru.....Jamila kamar bata so ta gaisheta ni kuwa ai ko kallon inda nake bata yi ba." Gwaggo tace." Jamila ga kayan Lambu nan na kawo miki Allah ya kara sauki ya raba lafiya."

Gabadaya suka amsa da ameeen ya Allah." Ta mike tana gyara lullu'bin mayafin ta "To ni zan tafi." mikewa nayi Baito da Ummatu suka ce "To shikkenan muma yanzu zamu tawo."
Tace."Oh!o kuna iya kwanciyar ku tunda zaman ku a gurin shine zai bata lafiya ciki dai ba akanta a kafara ba kuma ba za'a k'are a kanta ba."

Baito tace."Ramatu wannan habaicin ya isa haka ko don kinga nayi miki shuru ne ? ciki dai Allah ne ya bawa Jamila kuma babu mahalu'kin da ya isa yace ciki ba na Khalid bane."
Gwaggo tana kokarin magana na rufe mata baki da sauri na rike hannunta na jata muka fita daga falon........

*104*
Kamar 'Yar jagora haka nake jan hannunta ta fizge da fadin."Sakar min hannu ni ba makauniya ba sai jana kikeyi ina zaki kaini." ? Kallonta nayi tana gyara mayafinta nace."Gwaggo don Allah ki dinga hakuri da rayuwa wannan cacar bakin da kuke yi sam bai dace ba yanzu an riga an zama daya ni wallahi zuciya daya nake zaune da Jamila shiyasa kwata-kwata bana daukarta a matsayin kishiya sai 'yar uwa."

Ajiyar zuciya ta sauke tace."To naji dadi da kika fad'i haka saboda haka sai ki cigaba da zama da ita da zuciya daya idan ma ita ta nufe ki da sharri zai koma kanta, sannan kina magana akan su Baito kin dai san halina ni ba zan ga ana ba daidai ba nayi shuru da bakina sai na fad'a musu gaskiya sai dai duk abinda zasuyi suyi.'' Nace."To gurin fadar gaskiyar ki san irin maganar da zaki dinga fad'a dan Allah." Shuru tayi nace."Muje nasa driver ya kai ki gida ko."

Tace."To dama zaman me zanyi tunda nayi abinda zanyi sai dai idan Jarumi ya dawo ki fada masa cewa ina nemansa domin da kyar idan zai je inda nake tunda ba kullum yake zuwa ba."

Nace."To shikkenan Insha Allahu zan fad'a masa." Ina tsaye dravar yaja motar maigadi ya bude gate suka fita daga gidan, ajiyar zuciya na sauke tare da juya da niyyar komawa cikin gidan.


"Baito wai menene naga tunda na shigo kike shan kunu ko kin gaji da zaman jiyyar kina so ki tafi gida."? Khalid ne yake wannan maganar a lokacin daya dawo gidan.

Cikin b'acin rai tace." Khalid raina ne a 'bace wallahi saboda bayan fitarka daga gida kakar ka Gwaggo da matarka suka zo har nan inda nake suka ci mana mutunci harda kiran zuriarmu da makwad'aita matalauta 'kazamai kai babu irin cin mutuncin da ba suyi mana ba 'Karara suka nuna bakin cikinsu akan cikin dake jikin Jamila Al'amarin ya bani mamaki sosai."

Shuru yayi yana kallonta da nazarin maganarta yasan halin Gwaggo da fadin gaskiya da kuma rashin hakuri amma baya tsammanin za tayi irin wannan cin mutuncin kuma tunda ta samu labarin cikin Jamila take farin ciki da adduar sauka lafiya shiyasa yake nazarin maganar.


Baito tace."Ai dama nasan ba yarda za kayi ba tunda kai kullum baka son laifin kakar ka 'kiri-'kiri ka nuna mana cewa tafi mu muhimmanci a rayuwarka."


Yace."Baito kiyi hakuri don Allah zanyi binkice akan maganarki idan na gano da sanya hannun Sa'ida a cikin al'amarin zan dauki mataki domin ni babu wata mace da zan aura ta raina min dangi."


Baito tace."Ai shikkenan tunda ka 'karya ta maganata sai kaje kayi ta binkicen." Shuru yayi mata ya mayar da hankalinsa kan Jamila dake xaune a gefansa tana faman ya mutsa fuska......"Ya jikin naki ina fatan dai lafiya."? a shagwabe tace."Lafiya lau amma fa babyn nan naka yana wahalar dani ko ba haka bane Baito.''?

Tace."Kwarai kuwa hakane wannan cikin ai tsirfar sa yawa gare ta." Yace."To ko zakuje asibiti idan Allah ya kaimu." Baito tace."Aa ai ba sai anje asibiti ba laulayi ne kawai kuma duk mai yaron ciki tana irinshi mu dai babban fatan mu yarinya ta haihu lafiya." Yace."To shikkenan Allah ya kara lafiya ya kuma sauketa lafiya." Gabadaya suka amsa da Ameeen.

Mi'kewa yayi da wayoyinsa a hannu yace."Ni zan shiga na watsa ruwa na kwanta na huta sai da safe in Allah ya kaimu." Baito tace."To Allah ya tashe mu lafiya." Jamila kuwa shuru tayi tana bin shi da kallo wani irin bakin kishi yana taso mata gaskiya ta kusa ta karya dokar likita dan ba zata iya jure rashin mijinta ba.


Jin motsin shigowarsa yasa nayi saurin kallon bakin kofar..........Ido muka had'a dashi a lokacin da ya shigo falon. a nutse nayi masa barka da zuwa ya amsa tare da nufar bedroom d'inshi.

Kamar kada nabi bayansa sai da na mike na shiga dakin na sameshi zaune a bakin gado yana kwance necktie din wuyanshi. kallona yayi nan naga yanda kwayoyin idanunsa suka sanja a nutse nace." Da alama dai ba kajin dadi." Shuru yayi baice min komai ba ya kwance agogon hannunsa ya ajiye kan bedside trouser din jikinsa ya cire ya kwanta daga shi sai gajeran wando. Zama nayi kusa dashi da fadin." Ba za kayi wanka ba zaka kwanta ga abinci can yana jiran ka."

"Babu wani abu da zan iya gabatarwa a halin yanzu." A nutse nace."Saboda me ko wani abu na damunka." ?

Ido ya 'kura min yana min wani irin kallo lokaci guda na fahimci abinda yake da akwai. 'Bata raina nayi na fara kokarin barin gurin. da sauri ya janyo hannuna na afka kanshi, rungumeni yayi tsam-tsam a jikinsa yana shashshafa ni! "Kada kice zaki hana ni don Allah ki bari nayi koda sau d'aya ne wallahi da masifar sha'awa na yini da kyar na dinga gabatar da al'amura na ki taimaka min kinji Auntyna."

Ajiyar zuciya na sauke nace."Khalid ka iya dad'in baki idan kana neman biyan bukatarka ko me yasa wai baka ganin mutuncina sai sanda kake bukata ta."

Yana kesses din fuskata yace."Aa ni kinyi min mummunar fassara sam ba haka nake ba mutukar kinga ina miki fad'a akan wani dalili ne na daban amma ba wannan ba."

Shuru kawai nayi masa sabida nasan duk tawayen da zanyi masa ba zanci riba ba tunda ya riga ya matseni nasan sai ya biya bukatarsa.

Sosai naji jiki a hannunsa kafin ya saurara min ina kallonsa yasa wandonsa ya nufi toilet domin tsarkake jikinsa.........Har ya fito ban motsa ba ina kwance a gadon zazzafan zazzabi ya rufe ni.

Sai da ya kimtsa jikinsa yazo ya tsaya a kaina da fadin." Har yanzu baki tashi ba ko dai sai na kara wani." ? Ido a rufe

Please Login or Register in order to submit comment