Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da mutunci baya jin maganata sai ta kakarsa duk abinda Gwaggo tace shine daidai a gurinsa ni ya raina ni alhalin ni na haifeshi kuma mutukar za'a zagi Sa'ida a gabansa sai ya nuna 'bacin ransa saboda haka dole na nemi taimako a gurin malamai su karkarto da hankalinsa kaina dan na rantse ba zai auri Yarinyar nan ba."


Baito tace."Abinda ya kamata kiyi kenan kada kiyi sanya idan anjima ki shirya sai muje gurin Malam Saminu zai taimaka miki akan lamarin."

_Allah kasa mu dace jama'a wai uwa ce take d'ora 'yarta a hanyar zuwa gurin malami a maimakon tayi wa d'anta kyakykyawar addua sai mugun baki take masa 'karshe ma zata kaishi gurin malami Allah ya kyauta yasa mu gane_

Khalid na daf da fita sukayi karo da Jamila zata shiga gidan washe baki tayi da fadin"Laa Yaya Khalid ina wuni."? Kallon banza yayi mata kafin ya ratseta ya wuce ba tare da ya amsa gaisuwarta ba, haushinta yake ji sosai akan k'azafin da tayi wa auntynsa.....Jamila a sanyaye tabi bayansa da kallo gabanta na faduwa itakam ya zatayi ne Allah ya d'ora mata kaunarsa a cikin ranta...jiki a mace ta shiga cikin gidan.



Gwaggo na zaune a tsakar gida ita kad'ai tayi suguri abin duniya duk ya isheta Sa'ida kawai take tunani idonta akan kofar shigowa gidan daga taji motsi zata zabura ta kalli kofa.....Uwale ta rangad'a sallama cikin gidan.

Gwaggo ta amsa mata tare da gyara mata gefanta ta zauna suka shiga gaisawa....Uwale tace."Dama nazo ne naji inda aka kwana shin ina fatan kuna ganin kyawun maganin nan."?

Gwaggo ta sauke ajiyar zuciya rai a 'bace! tace." Ai Uwale Yarinyar nan ta'ki bani had'in kai wallahi da 'kyar ma ta bari aka turara maganin sau biyu daga nasa turaran a wuta zata dinga masifa ta fita daga dakin ta barni a ciki ina shakar haya'kin ke a takaice ma ta gudu daga gidan tun jiya."


Uwale ta rike ha'ba cikin mamaki tace."Kinji ko ai alamun da akwai iska a tare da ita kenan tunda gashi sun hanata zama a gidan saboda turaran da kikeyi musu."


Gwaggo tace."To hakan zata iya kasancewa amma ni ina tunanin abinda Rabi tai mata ne yasa ta tattara kayanta ta gudu."

Cikin son jin gulma Uwale tace."Oh! me kuma Rabin take mata."? Gwaggo ta shiga bata labarin abinda ya faru...Uwale tace."Ai kinga Rabi ko gado tayi dan mahaifiyarta Baito mara mutunci ce babu irin sharri da kazafin da ba tayi wa kishiyoyinta ba ni dama tuntuni nasan Baito ba mutuniyar kirki bace."


Gwaggo tace.''Kice dai Rabi gadon mugun hali tayi."? Uwale ta 'bantari gora ta mi'ke kafarta a kan tabarmar tace"Wallahi kuwa Sau nawa muna had'uwa da ita a zauran malam ai shiyasa kullum nake fad'a miki cewar sai kin tashi a tsaye akan Rabi domin ita da mahaifiyarta biye-biyen malamai suke."

Gwaggo tayi shuru tana jimanta al'marin.....Uwale ta yunkura da fad'in "Gwaggo ni zan tafi dama unguwa zani nace bari na shigo mu gaisa na kuma tambayeki halin da ake ciki."

Gwaggo tace."To Uwale nagode sosai sai kin dawo nazo gidan naki domin mu yanke shawarar yanda za'ayi domi gaskiya maganar Rabi da mahaifiyarta ya tsaya min a rai."


Uwale tace."To shikkenan ai babu damuwa sai kinzo din." Sallama sukayi da juna...Uwale na kokarin fita daga gidan Khalid ya shigo da kyar ya gaisheta yana dauke kansa ya shige gidan.

Gwaggo na ganinsa shi kadai fuskarsa kuma babu annuri sai tasha jinin jikinta.....Ya zaune kusa da ita yana matse gumin goshinta a sanyaye tace."Jarumi ya ake ciki ne ina Sa'idar.''?

Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke kafin yace."Gwaggo lokacin da muka isa gidan Alhajin ya fita sai na yanke shawarar kiran wayarta Gwaggo nayi nayi ta daga ta'ki haka na hakura na kyaleta.

Tace."Yanzu dai baku samu nasarar daukota ba." Kansa kawai ya daga mata ya lumshe idonsa damuwa ce mai tsanani take damunsa.

Gwaggo shuru tayi na minti biyu kafin tace."Idan anjima da yamma zanje gidan ayi wacce za'ayi."

Idonsa ya bude da sauri yace."Kada kije musu gida ki bari Baba yace zai koma da daddare insha Allahu komai zaizo da sauki amma ni bana so kije gidan kiyi wani abu suji haushinki ko kuma daga baya kiyi nadama kiyi hakuri abi komai a hankali."


Shuru tayi ba dan maganarsa ta gamsar da ita ba, yace." kin san gobe ni zan koma skull ko."? Girgiza kanta tayi tace."Bani da labari aini na dauka ka gama karatun ganin wannan karan ka dade a gida."

Yace."Yajin aiki malamai suka tafi karatu kuma da yardar Allah na kusa kammalawa ki cigaba dayi min addua idan na gama na samu aiki."

Tace."Insha Allahu zan cigaba dayi maka addua."

Mikewa yake kokarin yi tace."Zaka ci abinci ko."? kallonta yayi kafin yace."Idan yanzu kika girka zanci." Tace."Sai dai na dauki taliya d'aya a cikin kayan abincin Sa'ida nayi maka dafaduka da daddawa irin wacce kakeso."

Girgiza kansa yayi yace."Kada ki ta'ba mata kayan abinci bari nai wanka na fita na siyo sai kiyi min." Tace."Khalid kada ka 'batar da kudinka zasuyi maka amfani a makaranta ka bari a d'auka tunda da akwai."


Yace."Gwaggo bana bukata na fad'a miki ki kyaleni naci aljihuna bana fatan wata mace ta ciyar dani." Tace."To shikkenan bari naje na siyo kayan miyar da zanyi maka girkin."

Yace."Ki zauna ki huta duk zan had'o komai da zaki bukata gurin girkin." Shuru tayi tana kallonsa har ya shige gurinsu....Ta sauke ajiyar zuciya cikin ranta take masa fatan alkairi.

Tsaf tayi masa jallop din taliya irin ta mutanan da taji daddawa da manja da kifi sosai yaji dadin abincin ya dinga ci yana santi ita kuma sai dariya take masa dama haka take so ya sake ya cika cikinsa da abinci......Bayan ya kammala cin abincin a nutse ya kalleta da fad'in "Gwaggo ni zan fita nayi sallama da abokaina dan gobe da wuri nake so na tafi."

Tace."To shikkenan Jarumi sai ka dawo." Khalid yasa takalmansa ya fice daga gidan ita kuma ta juye ruwan zafin dake kan wuta ta surka ta shiga bandaki tayi wanka a gurguje ta shirya jikinta cikin atamfa (nicam) riga da zani da mayafi ta daura dankwalin (disco) a kanta pose dinta da dan mukkuli ta dauka ta fito ta kulle dakin takalmanta na dan'ko tasa a 'kafafunta ta fita daga gidan......Bakin titi ta fita tana addua akan Allah yasa kada ta hadu da Khalid din cikin ikon Allah kuwa har ta shiga adaidaita sahu bata ganshi ba.

Har bakin gate din gidan Alhaji Shamsu aka ajiyeta ta fito tana gyara lullu'bin mayafin atamfar dake jikinta, Pose din ta bude ta dauko dari biyu ta mika masa ya kar'ba tare da dauko hamsin ya bata a matsayin canjin ta.. karba tayi da sauri tasa a cikin jakarta tana masa godiya yaja babur dinsa yayi gaba.

Gate din gidan ta nufa ta bubbuga maigadin ya bude ganin kamar yasan fuskarta yasa ya gaisheta tace."Ina fata ka sheda ni ko."? Maigadin yace."Eh na sheda ki Gwaggo bisimillah shigo mana."

Gwaggo ta shiga gidan tana hamdala a cikin zuciyarta...............Gyaran kayan miya mukeyi da Asabe kawai naji sallamarta nai saurin daga kaina ina kallon bakin kofa. Ido muka had'a da ita tace."Babu shakka Sa'ida wato ke kina nan hankalin ki a kwance kin bar mu cikin damuwa ko."?

Bagarar da maganarta nayi nace."Gwaggo sannu da zuwa ki shigo mana." Tace."Ai ko baki fad'a ba." Asabe na murmushi ta gaisheta ta amsa tana bin gurin da kallo sai ta'be baki take.

Sanin halinta yasa nayi saurin mi'kewa da fad'in "Shigo mana." Ba tare da tace komai ba ta biyo bayana...Ummah kawai sai ganin mu tayi a tare.

Da sauri tace."Gwaggo kece kike tafe da yamma haka."?

Tana kokarin cire takalmanta domin shiga falon tace."Aikuwa dai nice nake tafe ko dai ba'a maraba dani."?

Ummah Habiba tace."Aa Gwaggo ana maraba dake shigo ga guri ki zauna." Ta shiga ta zauna kan kujera tana gyara yafan mayafinta.

Cikin mutunci da girmawa Ummah ta gaisheta ta amsa babu cikakkiyar walwala a tare da ita.

Nace."Gwaggo sannu da hanya." tayi saurin fad'in "Ai bazan amsa gaisuwarki ba Sa'ida tunda kin nuna mana iyakarmu."

Nace."Gwaggo wace irin magana ce wannan."? Fashawa tayi da kuka tace."Wato Sa'ida saboda Ibrahim bashi da kudi baya baki shayi da biredi baya siyo kayan miya da nama shine kika tattaro kayan ki kika gudo gidan mijin mahaifiyarki to komai talaucin mu mune gatanki sabida haka 'kafata k'afarki zamu koma gida dan ba zan zauna ayi min 'karfa-'karfa ba."

Cikin aljabi da mamaki nake kallonta lallai Gwaggo ta iya sauya lamari wato tanan ta 'bullo kenan."

Umma Habiba tace."Haba Gwaggo banji dad'in wannan magana ba wallahi Sa'ida bata da gata sai ku kuma duk rashi da taulacin Kawunta bai gaza da ita ba yana iyakacin bakin kokarinsa akanta to me zai sanya kiyi wannan maganar."

Shuru tayi bata tanka ba.Umma Habiba ta cigaba da cewa" Sa'ida tazo gidan nan jiya da daddare cikin damuwa da tashin hankali ta sheda min irin cin mutuncin da Ummatu take mata wannan dalilin yasa nace ta zauna ta huta idan ta samu nutsuwa sai ta koma."

Gwaggo tace."Eh hakane abinda tazo ta fad'a miki Ummatu taci mutuncin ta amma kuma Kawunta Ibrahim ya dauki mataki dan yanzu zancan da nake miki Rabi tana gidansu kuma yace ba zata dawo ba sai Sa'ida ta dawo saboda haka idan ke 'yar halak ce sai ki had'a kayanki mu tafi gida idan kuma kikayi sanadiyar raba auran Ibrahim da matarsa to zaki shiga bakin duniya."

Sa'ida da mahaifiyarta jikinsu yayi sanyi! Gwaggo ganin duk jikinsu ya mutu sai taji dadin hakan ta cigaba da zuzuta al'amarin.....Ummah Habiba tace."To shikkenan Gwaggo magana ta 'kare Sa'ida zata biki amma sai mun jira Maigidan ya dawo."

Gwaggo wani irin kallo ta watsa mata a fusace tace.....
*GA IRINTA NAN!!!🙆🏼‍♀️*
_(LOVE STORY🌺)_
*NA*
_BINTU UMAR ABBALE🍒_
*MANAZARTA WRITES ASSO🖊️📚*

*MUTANAN NIJAR IDAN KUNA BUKATAR BIYAN KUDIN LITTAFIN GA NUMBER DA ZAKU NEMA......22790899076*


*SADAUKAWA NE GA IYAYE BIYU*

*FATIMA MUSA (MOMMY NIJAR)*
*TARE DA*
*USAINA ABDUL-MALIK ISA (KAITA)*
*(HAJIYA BABBAH)*

_*Hakika ina alfahari dadu Iyayena🤝🏻🥰*_



*16&17*
*'KARSHEN FREE PEGE*
"Wane irin sai maigidan ya dawo kuma Habiba kina nufin zanyi ta zama a gidan nan har sai mijinki ya dawo ya bada umarni."? ta'karashe maganar tana hararar ta.

Umma Habiba taji rashin dadin maganar Gwaggon amma sai ta daure ko a fuska bata nuna ba tace."Gwaggo abinda nake nufi kenan a bari ya dawo a bashi hakkinsa a matsayinsa na mijina tunda tamkar uba yake a gurinta saboda haka dan Allah kiyi hakuri kada ki dauki maganata da wata manufa ta daban."

Ta'be bakinta tayi tace."Saboda kawai nice sarkin zargi sai na dauki maganarki da wata manufa shikkenan ai tunda kince haka sai na zauna na jira shi ya dawo na dai fad'a miki 'kafata 'kafar Sa'ida dan ba zan yarda da raina da lafiyata jinina yayi agolanci a wani guri ba."

Cikin takaici nace."Wai Gwaggo wace irin magana ce wannan kike yi dan Allah kiyi shuru haka ki daina d'aga mirya da tada jijiyar wuya magana ta 'kare zan koma gidan ko dan saboda Ummatu ta dawo d'akinta."

Shuru tayi min ba tanka ba. Umma ta sauke ajiyar zuciya da fad'in "Ai maigidan ma yana kan hanya shida na yamma suke dawowa daga kasuwa."

Tace."To Allah ya kawo su lafiya." Umma Habiba ta amsa da "ameen tare da mi'kewa domin fita daga falon Gwaggo ta dakatar da ita, da fadin " Nace ko kina da goro ki bani wallahi garin sauri na manta nawa a gida." Tace."Gwaggo ni bana cin goro amma bari na tambayar miki Hajia Hansatu.'' tana nufin uwargidansu. tace."To nagode Habiba ina jira wallahi sha'awar cinsa ce ta taso min a yanzu idan ma babu a gurinta ga kudina a siyo min."

Umma Habiba tace."Ba za'a rasa ba insha Allahu bari na tambayar miki ita." Fita tayi daga dakin da sauri.

Nace."Gwaggo ba zaki daina cin goro ba ko."? Kallona tayi cikin kulawa tace."Sa'ida ai ina jin sai ranar da numfashi ya bar gangar jikina zan hakura da goro ya zame min masifa ni kaina so nake na daina amma na kasa."

Nace."Abu ne da kuka sanyawa ranku wanda kuke ganin idan baku ci ba wata matsalar zata iya faruwa daku kuma ba haka bane da zaku yi sati guda baku ci ba babu abinda zai same ku sai ma lafiya da kuzari da zakuyi amma dan jaraba kuyi ta cin abinda zai cutar daku."

Shuru tayi bata ce komai ba. nasan duk surutan da zanyi akan al'amarin ba zata d'auka ba cin goro ya zame mata jinin jikinta.

"Gwaggo zan koma gida amma da akwai sharad'i." Da sauri ta kalleni, na sha kunu da fad'in "Kiyi min tsakani da Khalid babu ni babu shi yaron bai da kirki da tarbiya akwai abubuwan da suka faru a tsakaninmu wanda idan na fito na fad'a miki hankalinki zai tashi ko kuma ma kice nai masa sharri to wannan dalilin yasa nayi shuru da bakina inaso ki zauna dashi kija masa kunne sosai ya fita daga sabgata maganar yana sona ya ajiyeta a gefe guda dan na rantse ba zan aureshi ba koda kuwa zan rasa mijin aure keda kike goya masa baya akan lamarin ki cire kanki domin ke zakiji kunya. abu na biyu kuma kina d'ora min lalurar aljanu ni lafiyata kalau kamar yanda nasha fada miki aure lokaci ne sabida haka Uwale ta daina janki gurin masu magani kina asarar kud'in ki bayan haka kuma idan kin san akwai ragowar wannan turaran da kike turnuk'awa a daki to da mun koma ki zubar dashi dan wallahi duk ranar da kika sake kunnawa zan bar gidan kuma komai abinki ba zan dawo ba guduwa ma zanyi ku rasa inda na nake.

Gwaggo gabanta ya fad'i! ta tsira min ido nace." Wallahi Gwaggo wannan maganar da nake miki har cikin zuciyata nake miki ita Khalid ba tsaran aure na bane ki daina tatsuniya ba zan aureshi ba sannan ni lafiyata kalau aure kuma lokaci ne insha Allah cikin satin nan Alhaji Nura zai turo da magabatansa.

"Sa'ida meye aibun Khalid da zaki dinga gudunsa ko dan bashi da kudi ne."? A sanyaye take magana dan na lura jikinta yayi sanyi da maganata.

Girgixa kaina nayi ina kokarin magana Umma ta shigo falon hannunta da farar leda cike da goro manya masu kyau Gwaggo da sauri tasa hannu ta kar'ba da fad'in " Kai amma naji dadi sosai Habiba Allah yayi miki albarka."

Umma Habiba ta amsa da "ameeen ya Allah." Ta fita daga falon.

Ledar ta kwance ta dauko daya ta 'bantara ta fara taunawa. Nace."Gwaggo Khalid ko ya kai *Dangwate* kud'i a duniya baya cikin tsarina yaje can ya auri daidai dashi nima na auri daidai dani magana ta mutu a gidan nan kada ki Sake yi min maganar Khalid."

Tace."Ai shikkenan Sa'ida tunda kinqi Khalid har kina kokarin yi masa sharri zanyi masa magana ya rabu dake tunda bakye kad'ai ce autar mata ba insha Allahu Allah zai bashi wacce ta fiki kyau da 'kuruciya."

Nace "Nima zan taya shi da adduar samun macan data fini."

Shuru tayi min ta cigaba da tauna goronta kallonta kawai nayi na gane maganata ta kashe mata jikinta, nace."Ko na kawo miki abinci."?

Girgiza kanta tayi tace."Bana bukata saboda inda na baro da akwai abinci." Nasan magana ta fad'a min a fakaice oho! ni dai na fad'a mata abinda yake raina sabida haka ita da Khalid din duk su shiga hankalinsu.

Tace."Khalid d'in ma gobe zai koma makaranta." Nace."Allah ya bada sa'a." ta amsa da "ameeen ya Allah."

Umma ce ta shigo dakin da fad'in "Gwaggo Alhajin ya dawo tashi muje nayi miki jagora ku gaisa." Da sauri ta miqe tana gyara yafan mayafinta suka fita tare.

Alhaji Shamsu yana zaune a kan kujera yana lissafi da wayar hannunsa sukayi sallama a dakin nasa....cikin kulawa ya amsa da fad'in"Gwaggo sannu da zuwa ga guri nan zauna."yafada yana nuna mata kujerar dake kallonsa

Gwaggo ta zauna kan kujerar tana amsawa tare da fad'in "Ai na jima a gidan ina jiranka da fatan ka dawo lafiya."? Yace." Lafiya lau gwaggo ai ban sani ba da tuntuni na dawo gidan sabida ke koda na shigo ma maigadi yake sanar dani zuwan Ibrahim bayan fita ta hakika banji dadin faruwar hakan ba."

Tace."Aikam dole kaji rashin dadi dan muma jiya haka muka kwana zuciyoyinmu Babu dadi wannan dalilin ne ma yasa shi Ibrahim dako sammako yazo gurinka domin ku tattauna magana sai kuma akayi rashin sa'a ka fita kasuwa shine nace to ni bari idan rana tayi sanyi sai nazo gidan na sameka mu tattauna maganar dan nazo tafiya da Sa'ida ne matarka Habiba tace lallai sai ka dawo ka bada umarni shine nace to komai dare kuwa zan zauna har ka dawo domin naji uzirinka akan yarinyar."

Alhaji Shamsu yayi gyaran murya yana kallonta ya riga yasan halinta 'yar taratsatsi ce yace."Hakane Gwaggo Sa'ida tazo gidan nan cikin halin damuwa tana kuka ta sheda mana abinda yake faruwa acan gidan al'amarin ya tayar min da hankalina sosai Gwaggo shi ai aure lokaci gareshi mai zai sanya ku tayar da hankalinku akan yarinyar nan har ku dinga d'ora mata lalura irin ta aljanu bayan haka kuma har a samu masu yi mata 'kazafi na zina wannan al'amari baiyi min dadi ba gaskiyar lamari raina ya 'baci dajin wannan magana shine dalilin da yasa ma na yanke hukunci kancewa ba zata koma gidan ba sai an kwana biyu kuma dole ne mu samu zama dashi Ibrahim din akan maganar yana da kyau ya jawa matarsa kunne ta guji jifan yarinyar nan da muna nan kalamai domin hakan bai dace ba."

Gwaggo tace."To ai Alhaji Ibrahim ya tauna tsakuwa dan aya taji tsoro inaso na sheda maka cewar duk yanda kake kaunar yarinyar ba kamar shi ba tunda Ubanta ne ya saki nono shi ya kuma ya kama kaga dole yayi kishinta ya kuma nunawa matarsa 'bacin rai dan yanzu maganar da nake maka Rabi tana gidansu tun jiya ya koreta daga gidansa yace mutukar ba Sa'ida ce ta dawo gidan ba to ya gama zama da ita."

Alhaji Shamsu yace."Subahanallahi Me yayi zafi Ibrahim zai yanke wannan hukunci." Ummah Habibatan tace."Nima haka na gani Alhaji Iro ya yanke hukuncin da bai kamata ba ai komai a sannu a hankali ake binsa."

Gwaggo tace."To ai shine nake so ku fahimta Ibrahim zai iya rabuwa da matarsa akan yarinyar nan to tun kafin hakan ta faru yasa nazo domin tafiya da ita."

Hankali a tashe ya dauki wayarsa da fad'in "Bari na kira wayarsa idan da hali sai yazo domin mu tattauna maganar a tsakanina dashi amma banji dadin wannan lamari ba."
Gwaggo tace."To shikkenan ai yanzu nasan ya dawo daga kasuwa idan ma bai dawo ba to babu shakka yana kan hanya.


Kawu Iro na adaidaita sahu kira ya shigo wayarsa ganin number Alhajin yasa da sauri ya daga suka gaisa a tsanake Alhaji Shamsu ya sheda masa uzirinsa....Kawu Iro yace."To babu damuwa Alhaji ganin zuwa insha Allahu." Wayar ya kashe ya umarci direban daya juya baya ya kaishi hotoro. Yace."Amma dai zaka 'kara min kudi ko."? Kawu Iro yace."Eh 'kwarai kuwa idan ma ka samu fasinja ka dauka." yace."to shikkenan.

Sai magariba Kawu Iro ya isa gidan kuma basu samu zama ba sai da suka gabatar da sallah tukkuna suka fito daga massalaci a tare wani 'kebantacan guri suka samu suka zauna suka sake gaisawa cikin mutumci kana suka shiga tattauna abinda ya had'asu.

Kawu Iro ya sauke ajiyar zuciya da fad'in "Alhaji ka kwantar da hankalinka insha Allahu hakan ba zata sake faruwa ba maganar mai d'akina kuma ni a ganina hukuncin dana dauka a kanta shine daidai kaga gaba zata kiyaye jifan yarinyar nan da wata mummunar kalma."

Alhaji Shamsu yace."Hakane Ibrahim to amma inaso dan Allah ka sake sanya ido akan yarinyar nan sannan idan da wani wanda kaga alamun da gaske yake sonta to kayi masa magana ya fito kawai domin hakan shine ya dace."

Kawu Iro yace."Insha Allahu hakan za'ayi akwai wani mutumin anan gaban inda muke yana son ta koga yanayin hidimar da yake mata to saboda haka idan na koma gida zan sameshi da maganar domin mu tattauna."

Alhaji Shamsu yace."To Alhamdulillahi Allah yasa sanya alkairi.'' Kawu Iro ya amsa da ameeen ya rabbi.''




To muna zaune a falo har gwaggon muna hira ya shigo. gwaggo tayi saurin fad'in "Ina fatan Ibrahim din yazo." Yace."Eh Gwaggo yazo ina fita da niyyar shiga massalaci na hangi zuwansa tare ma mukayi sallah masha Allah mun tattauna magana dashi ta fahinta saboda haka ke Sa'ida zaki koma gida magana ta wuce insha Allahu hakan ba zata sake faruwa ba sannan kuma Ibrahim ya sheda min cewa akwai wani mutumi da yake sonki a Cikin unguwar to nace masa yayi magana dashi idan da gaske yake sai yayi magana ayi abinda za'ayi."
Gwaggo har ta bud'e baki za tayi magana sai kuma ta fasa.

Yace."Gwaggo kamar akwai magana a bakinki." girgixa kanta tayi tace."Aa babu magana Alhaji." Ya kalleni da fad'in "Kinji hukuncin dana yanke ko."? Nace." Eh naji Alhaji dama nima inaso nayi masa magana kan cewa ya turo magabatansa ayi maganar aure idan da gaske yake."

Alhaji yace."To Alhamdulillahi hakan yayi kiyi masa magana shima Ibrahim din yayi masa sai ya dauki maganar da muhimmanci." Nace."To shikkenan Alhaji." hannu yasa a aljihu ya dauko kudi kimanin dubu biyar ya mikawa Gwaggo da fadin "Gashi kya sayi goro." Babu yabo babu fallasa ta kar'bi kudin dan Taji masifar haushin yanda yake nuna ikonsa akan Jikarta wai duk muna nan maganganun data ya'ba masa ba suyi masa zafi ba sai wani za'kal'kalewa yake.

Bayan fitarsa daga falon Ummah Habiba tace"Gwaggo bari na kawo miki abinci kici sai ku taf......tun kafin ta 'karasa tayi saurin katseta da fad'in "Bayan wanda naci d'azu kuma zaki sake d'ubga min wani Aa bana bukata tafiya za muyi." kana jin yanda tayi maganar kasan a fusace take......mi'kewa tayi tana gyara yafan mayafinta, nida Umma muka bita da kallon mamaki.

A cunkushe tace."To gimbiya ina jakar kayan naki take na d'aukar miki.'' Murmushi takaici nayi ba tare dana tanka mata ba na mi'ke Umma ma ta mi'ke tana 'yar dariya nasan ita da gwaggo ne....Hijabina na gyara na dauki jakar kayana na ri'ke ta ta'be bakinta tai tayi gaba tana surutai! Umma tace."Gwaggo ga mayafi da takalmi kayi amfani dasu."

Juyowa tayi tana kallon ledar hannunta murmshi tayi wanda be kai ciki ba tace."Habiba kin manta ni tunda jajayen sawuna bana yafa wani gyale idan ba na atamfa ba."

Umma tace."Kwarai hakane na manta wallahi to ki kar'ba dai ko kyautarsa sai kiyi.....Nace."Umma ki ajiye mayafin ki zaiyi miki amfani idan ta kar'ba ma munafukar matar nan zata bawa Uwale."

Umma ta ri'ke bakinta cikin mamaki tana kallon Gwaggo tace."GwaggoAshe har yau kina tare da Uwale."?

Da sauri tace." 'Kwarai kuwa ba kuma mai rabani da ita sai mutuwa." Tana gama maganarta tasa takalmanta ta fita ta barmu...Umma tace."Sa'ida ki cigaba da hakuri kinji ko watarana sai labari." Nace."Umma Insha Allah zan cigaba dayi nasan Allah yana kallo."

Ta mi'ka min ledar da fad'in " 'Karbi ki ri'ke mata tunda nayi niyya bazan fasa ba babu ruwanki da wanda zata bawa." ledar na kar'ba da fad'in "To shikkenan." sallama mukayi da ita tace."Lallai idan na fita na shiga d'akunan kishiyoyinta nai musu sallama.
Nace."To insha Allah zan shiga.

bakin gate na same su a tsaye ita da Baba Iro suna jiran fitowa ta ina ta

Please Login or Register in order to submit comment