Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tunda mukayi haka dashi ya sanja lokacin dawowa gida sai can dare yake shigowa kuma kafin na tashi ya fita yau dai na zauna a falo dole ya dawo akan idona domin ba zan kwanta ba sai naji matsayina a gurinsa.


Sai goma da arba'in da biyar ya shigo gidan Ganina a zaune a falo yasa yayi kici kici da fuska ya kauda kansa hade da kama hanyar dakinsa......."Yaya Aminu sannu da zuwa." Ko kallona beyi ba ya cigaba da kokarin bude d'akinsa.

Sai da na bari ya shiga dakin tukkuna na mike nabi bayansa.


Yana kokarin cire rigarsa na tsaya a gabansa fuskata a mugun hade......Rai a bace yace."Lafiya zaki zo ki sani a gaba."? Tsaki naja nace."Ina so naji matsayi na ne? ina so nasan zaman me nake a gidanka."

Shuru yayi min ya cire rigar tare da ratse ni zai wuce da sauri na tari gabansa na bude baki kenan zanyi magana ya gaura min mari!

Dafe kunci na nayi ina kallonsa idanuwa sunyi jajawur! Yace."Baki san haushin ki nake ji ba ko."? Jikina na kyarma nace."Kana jin haushina kamar yanda nake jin haushinka wallahi na tsanake bana kaunar kallon wannan bakar fuskar taka."

Murmushi yayi yace."Duk na gane akan abinda yasa kike min rashin kunya kina so ki tunzura zuciya na sake ki ko."? shuru nayi ina kallonsa ya cigaba da cewa."To ba zan sake ki ba sai kin wahala a hannuna tunda ke baki da mutunci."

Hawaye na share nace."Komai abinka idan zamana ya kare da kai dole ka sake ni ai ba'a dole na gaji da zama da kai babu lafiya gashi baka san mutunci ba."

Ture ni yayi na fadi a gurin ya shige toliet din yana fadin."Hukunci saki a hannuna yake zanga wanda ya isa ya sani na sake ki."


Cikin mutuwar jiki na mike na fita daga dakin......Gefan gado na zauna ina kuka na dauki waya ta number Umma Habiba na nemo gabadaya na manta da dare burina kawai na samu wanda zai rarrashe ni Yaya Aminu so yake yasa zuciyata tayi bundiga."


Umma Habiba na kokarin kashe wayarta taga kira gabanta na faduwa ta daga........."Innalillahi wa'ina ilahi raji'un! wannan kalmar ta fad'a hankali a tashe tace."Sa'ida ya isa ki daina kuka haka kiyi shuru kiyi min bayanin abinda ya faru shin fada kukayi da mijin naki."?

Cikin shaqewar murya tace."Umma na gaji da wannan masifar na gaji wallahi So nake ku raba ni da wannan wahala Yaya Aminu yana azabtar dani zuciyata daf take data buga saboda abubuwan da take had'iya."


Alhaji Shamsu ya miqa hannunsa da fadin."Bani wayar." Jiki a mace ta mika masa wayar yasa a kunnensa a nutse yace."Sa'ida yi shuru kinji ko ki daina kuka haka ya isa duk naji k'orafin ki kuma duk abinda kika ce Aminu yayi miki ba zanyi musu ba domin ba'a shaidar mutumin yau wannan auran dama ni tuntuni ya fice min daga raina saboda wannan gagarimar matsalar ba zan zama mara adalci ba insha Allahu ni zan tsaya miki akan hakkin ki Aminu zai sake ki kamar yanda kika bukata Allah yasa haka shi yafi alkairi."

Jikina ne kuma yayi sanyi sai tausayin mutumin ya lullu'be ni a sanyaye nace."Alhaji wallahi ba laifi na bane nayi dukkanin bakin kokari na al'amarin yaci tura Yaya Aminu yaki fahimtata kullum babu nutsuwa da kwanciyar hankali shiyasa kawai na yanke wannan shawarar domin ina ganin kamar itace maslaha."

Yace."Kwarai kuwa Wannan shine Maslaha kuma kinyi tunani mai kyau Sa'ida ba zaki kashe kan ki akan bukatar wani ba tabbas kinyi hakuri kuma kinyi namijin kokari akan al'amarin auranki duk wanda zai budi baki ya fadi laifin ki to yaso kansa domin ita gaskiya duk inda take sai ta tona kanta saboda haka kada ki damu kinji ko gobe da safe kizo gida da kayan ki." A sanyaye nace."Tom shikkenan Alhaji nagode sosai Allah yasa haka shi yafi alkairi" Cike da kulawa ya amsa da "Ameeen ya Allah." Kwanciyar rigingine nayi ina kallon rufin dakin......."Yanzu idan na rabu da auran Yaya Aminu wane irin namiji zan aura? Shin Sa'ida anya kuwa zaki samu nasarar auran wanda zuciyarki take hasashe."? Zuciyata ce take min wannan zancan.....Idona na rintse gabana ya shiga bugawa! kawai sai na tsinci kaina da addua akan Allah yasa Khalid ya dawo da soyayyarsa a gare ni........
[5/14, 11:48 AM] NAFEE Alwasa: *SADAUKARWA NE GA IYAYE NA BIYU*

*FATIMA MUSA (MOMMY NIJAR)*
*TARE DA*
*USAINA ABDUL-MALIK ISA (KAITA)*
*(HAJIYA BABBAH)*

*_Ha'kika ina Alfahari daku da irin kaunar da kuke min.🥰🤝🏻💜_*





*92*
Da wannan tunanin bacci mai nauyi ya d'auke ni da asubah sai da na fara wanka tukkuna na dauro alwala na fito na tayar da sallah bayan na idar na jima ina rokon Allah ya kawo min mafita a rayuwa amma a zahirin gaskiya auran Yaya Aminu ya fice min daga raina. jikina na shirya na nemi guri na kwanta ina jiran gari ya waye sosai na fita daga gidan.

Waya ta dake kan bedside na dauka na kunna time na duba shida da rabi na safe, ajiyar zuciya na sauke ina jin wani irin zazzafan feelings na taso min wani irin so nake wa yaron bana tunanin zan iya auran wani idan bashi din ba tunda yanzu na gane cewa shine daidai rayuwa ta, na jima ina shawarwari da zuciyata kafin na yanke shawarar kiran wayar shi muryarshi kawai nake so naji ko zan samu sassaucin abinda ke damuna a zuciyata......Number shi ta kasar waje bata shiga sai na kira number shi ta Asali cikin ikon Allah kuwa tana fara ringing ya daga.
Ajiyar zuciya na sauke hade da kiran sunansa. cikin alamun bacci ya amsa da wacece."? saboda bacci ne a idonsa sam be duba wayar ba.

Gabana na faduwa nace."Khalid nice fa.'' Jin muryarta yasa ya bude idonsa tare da gyara kwanciyarsa a kasalance yace."Aunty Sa'ida kin tashi lafiya."? Cikin kasala nace."Lafiya Khalid bacci kake na tashe ka ko."? k'aramar ajiyar zuciya ya sauke yace."Eh wallahi tunda nayi sallar asubah na kwanta baccin ya dauke ni kiran wayar ki ya tashe ni." Cikin taushin murya nace."Kayi hakuri don Allah." Murmushi ya saki yace."Auntyna ai ke bakya laifi ina fata dai lafiya ko."? shuru nayi ina dawurwura.

Yace."Kinyi shuru Aunty Sa'ida ke nake saurare." Cikin mutuwar jiki nace."Khalid na kasa nutsuwa saboda tunaninka yaushe zaka dawo gida ne."?

Jim yayi na minti biyu yace."Gobe ko jibi zan zo gida insha Allahu kada ku damu ina cikin koshin lafiya da nasarori masu yawa."

Nace."Alhamdulillah dama haka ake so ai duk na samu labarin irin daukakar da ka samu Khalid na taya ka murna ina rokon Allah ya tsare gabanka da bayanka." Ya amsa da ameeen Auntyna nagode sosai."

Shiru mukayi kowa yana sake-sake a zuciyarsa......Murya kasa-kasa yace."Aunty ya labarin maigidan ki ina fata dai komai yayi normal."

Murmushin takaici nayi nace."Yana nan Khalid ai mun rabu da juna." Kawai na tsinci kaina da fada masa haka.

Yace."Ai gwara hakan yafi amfani tunda zaman da kike a gidansa na cutar da kai ne Allah ya za'ba miki abinda yafi alkairi."

Cikin jin dadin maganarsa na amsa da "Ameeen ya Allah nagode k'anina.'' Yace." Yanzu kina ina hotoro ko gidan Gwaggo."? Nace." Ina can hotoro amma dai zan dawo gidan Gwaggo idan an kwana biyu." Yace."To shikkenan idan na sauka a gari zan kira wayarki." Cikin farin ciki nace."To shikkenan Allah ya kawo ka lafiya.'' Ya amsa da ameeen ya Allah ." Kashe wayarsa yayi ya barni da tawa a hannu sai murmushin jin dadi nake a zuciyata nace da alama ba zan sha wahala da yaron ba tunda har yanzu akwai kaunata a cikin zuciyarsa.........Kaina na dago sai muka hada ido dashi yana tsaye a bakin kofar shigowa fuskarsa a mugun 'bace! Gabana na faduwa na mike zaune ina kallonsa, cikin wani irin taku ya karaso inda nake sai na sunkuyar da kaina kasa ina addua a cikin zuciyata ha'ki'kanin gaskiya Yaya Aminu ya zame min mijin jaraba bala'in tsoron masifarsa nake.

"Da wane namiji kike waya."? maganarsa ta daki kunnena. kai a sunkuye nace.''Khalid ne."? Waye Khalid.''? ya fada cikin sigar zargi Dauriya na aro na kalleshi da fadin." Yaya Aminu Khalid din ne baka sani ba."? A zafafe ya daga min hannu da fad'in."Kada ki mayar dani shashasha mana kina waya da wani d'an iskan kice Khalid ne.'' Nace."To ai sai ka duba wayar ka gani ni bana munafurci mutukar nasan nayi abu to zan fad'a." Wayar hannuna ya fizge yana dubawa yake fadin."Na lura dake baki da mutunci da sanin ya kamata ba to zan sanya ido sosai a kanki domin ba zan lamunci ki zubar min da mutunci ba."
Murmushin takaici nayi nace."Wane irin mutunci kuma? Yaya Aminu ai kai zaka siyawa kanka mutunci ni wallahi daidai da 'kwayar zarrah bana ganin mutuncin ka." Ido ya tsira min nasan mamakin maganata yake dauke kaina nayi ina sake tamke fuskata 'kwafa yayi cikin bacin rai yace."Saboda kin kasa samun abinda kike so daga guri na shine kike bibiyar mazan waje ko.'' ? Da sauri na kalleshi idanuwa na sun tara ruwa nace."Sharrin da za kayi min kenan."? Cikin sigar rashin mutunci yace." Ke baki isa ayi miki sharri ba gaskiya ce wannan kada kiyi tsammanin ban san dalilin da yasa tsohon mijinki ya sake ki ba kada kuma kiyi tunanin cewa ba san irin iskancin da kike da maza a gurin aikin ki ba nasan komai nayi binkice sosai a kanki kafin na amince a d'aura min aure dake wannan dalilin ne yasa naqi mayar da hankali gurin shan magani domin kuwa banga amfanin had'a zuria dake ba.''

Wasu irin hawaye ne suka kwace min kallonsa kawai nake bakina na rawa na kasa magana tsabar mamaki da al'ajabi.

Yace." Tunda na gane abinda kike so to ba zanyi ba sai na galabaitar dake tukkuna zaki san wanda kike wa rashin kunya.''

Hanya ya kama zai fita nace."Tsaya ka saurare ni." Tsayawa yayi yana watsa min kallon banza Nasa hannu na goge hawayen fuskata nace."Yaya Aminu nagode da irin sakayyar da kayi min inaso na sanar maka da cewa shi Ubangiji baya bacci kuma shine alkalin kowa na rantse da girman zatin sa ba zan yafe maka k'azafin da kayi min ba."

Tsaki yaja ya bude kofa zai fita nace." Kuma zan cigaba da rokon sa akan ya raba ni da kai tunda kai ka kasance azzalimi mara tsoron Allah." Da sauri ya dawo inda nake yana huci! yace." Idan kika sake magana a gurin nan sai na baki mamaki wallahi." shuru nayi ina kallonsa hawaye na sauka a saman fuskata ko a mafarki ban ta'ba tsammanin mutumin zaiyi min haka ba.
Sosai ya tsaya a kaina yaci min mutumci iya son ransa ya kad'a kansa ya fita yana fad'in zai ga wanda ya isa yasa shi ya sake ni.
Hakika na tsorata da al'amarin mutuka saboda haka yana fita na tashi da sauri na harhad'a kaya na a kwati na dauka da sauri na kama hanyar hotoro ina addua akan Allah ya bani rinjaye a kansa.
Kici'bus nayi dashi a lokacin da nake kokarin shiga gidan shi kuma yana fitowa fuskarsa kawai na kalla gabana ya fadi da sauri na dauke kaina nayi gaggawar jan akwatin kaya na domin barin gurin.

Ido jawur ya tare min hanya "Sa'ida ni zakiyi wa haka ko."? Yanda ya fadi maganar a kufule shi ya nuna min cewar a cikin bacin rai yake.

Cikin jarumta nace." Me nayi maka."? Da kyar ya hadiyi wani yawu mai d'acin gaske yace."Me yasa kika kasa hakuri kika fad'awa mahaifina tsakaninmu."

Dauke kaina nayi nace."Saboda na gaji da zama da kai ina bukatar rabuwa da kai shiyasa na shedawa mahaifinka domin hausawa suna cewa ta inda aka hau ta nan ake sauka."

Zazzafar ajiyar zuciya ya sauke yace."To bukatar ki ta biya Alhaji ya tursasa ni na sake ki ba dan raina yaso ba."

Wani irin sanyi naji a zuciyata nace."Alhamdulillahi Allah nagode maka nasan yanzu dai ka gazgata cewa Allah na kowa ne ba naka bane kai kad'ai."

Shuru yayi yana kallona idanunsa sunyi jawur.....Ratse shi nayi zan wuce ya rike hannuna yana marairaice fuska yace."Don Allah kiyi hakuri ki dawo mu zauna ina son ki sosai zan nemi magani a duk inda yake."

Murmushin takaici nayi nace." Yaya Aminu kenan ai da wannan matsalar ce kad'ai da kai to da da sauki amma bari na fada maka cewa kai duk macan da ka aura to ba zaka ta'ba zaman lafiya da ita ba saboda halayenka."


Cikin sanyin murya yace."Wane irin halaye ne dani Sa'ida duk fa wasu abubuwa da nake miki kece kika janyo amma bana miki mugunta.

Girgiza kaina kawai nayi na ja akwatin kayana na barshi a gurin.......Jiki a mugun mace ya bude motarsa ya shiga yana mamakin yanda al'amarin ya sauya a yanda yaga mahaifin nasa na son auran bai ta'ba tsammanin zai yanke musu irin wannan hukuncin ba, sai bayan ya rubuta sakin ne yaji wani masifar kaunarta a cikin zuciyarsa shi kansa yasan yayi babban rashi duk da bai cika cikakken namiji ba amma yasan yarinyar zata zame masa garkuwa ko babu komai jamaa zasu dinga yi masa kallon cikakken mutum tunda yana da iyali shin yanzu wace mace zai aura da lalurarsa ta zauna dashi a haka a gaskiya abun da kamar wuya.


*****
Sati na biyu a gidan Alhaji hankali ya kwanta sosai kullum ina tare da mahaifiyata tana kwantar min da hankali akan irin kaddarar rayuwa ta.............Gwaggo kuwa data samu labarin mutuwar auran sam bata nuna damuwa da alhini ba koda tazo gidan Alhajin ma cewa tayi Allah yasa haka shi yafi alkairi Kawu Iro ne kawai ya nuna damuwarsa tamkar ya zubar da hawaye saboda damuwa rayuwar yarinyar ce take bashi tausayi har yanzu Allah bai bata nagartaccen namiji ba......Kasa hakuri nayi da zata tafi nace."Gwaggo kwanaki da mukayi waya da Khalid yace zai zo gida ko."
Tace."Eh ai yazo yau kwanansa goma sha biyu da zuwa sai da kullum baya zama jama'a sun takura masa sun mayar mana da kofar gida sansani su cika mana kunne da ihu! bayan 'yan maula wanda suke dako mana sammako da sassafe ya basu kudi dangin Rabi ma suyi ta damunsa da bani-bani."

Dariya ce ta kwace min ina yi nace."Haba Gwaggo sai kace tsohowar redio daga tambaya kin saki baki sai zuba kike kamar kanya."


Tsaki taja ta kalli Umma Habiba da fadin."Habiba ki duba magana ta da kyau akwai gaskiya a ciki wallahi tunda yaron nan ya dawo jama'a sun'ki barinsa ya huta wai daga jin labarin yaci kofin gold da miliyoyin kudi da motoci shine fa aketa cika mana kofar gida ni kaina idan na fito matasan layi kamar zasuyi min sujjada saboda tsabar kwadayi.


Umma Habiba na murmushi tace."Gwaggo ai arziki ne amma dai suma abinda suke bai dace ba haba ai sa barshi ya huta tukkuna.

Tace."Wallahi kuwa ai abin da takaici sai kinga yanda Dangin uwarsa suke tururuwar zuwa gidan kamar marasa hankali."

Nace."Gwaggo ki kyalesu don Allah babu ruwanki saboda nasan halinki da shiga sabgar da bata shafe ki ba."


Tace."Oh! o dama ni ina ruwa na abun ne dai yake ban haushi." Umma Habiba tace."To Allah dai ya kyauta shi kuma Allah ya kara masa daukaka ya kareshi daga sharri masu sharri." Gabadaya muka amsa da "ameeen ya Allah."


Tace."Sa'ida ki tashi ki shirya mu tafi gida." Umma Habiba sunkuyar da kanta tayi domin ba taso Gwaggon taga kamar dasa hannunta a gurin zaman Sa'idan a gidan.

Nace."Gwaggo kije kawai insha Allahu gobe ko jibi zan biyo bayan ki."

Tsaki taja tace."In banda rashin zuciya irin naki namiji ya sake ki amma ki zauna musu a gida kamar wacce ta rasa gurin zama to idan sha'awar gidan bulo da bulo kike ki kwantar da hankalin Khalid yana nan yana shirye-shiryen ruguje gidan ya sanja mana gini na zamani."

Umma Habiba tace."Haba Gwaggo ai Sa'ida bata da inda ya kai gidan ubanta komai lalacewarsa nan ne tushenta sabida haka don Allah ki daina wannan maganar."


Ta'be bakinta tayi tace."To ai nima abinda na gani kenan gashi ke da kika haife ta kin kasa tsawatar mata ta dawo inda take da gado."

Umma Habiba tace."Kiyi hakuri dan Allah Sa'ida ki tashi ki had'a kayan ki ku tafi." Ajiyar zuciya kawai na sauke na mike domin shirya kayana Gwaggo farin ciki yasa ta zauna kan kujera tana jan Umma Habiba da hira duk Rabi ta Khalid ce Umma Habiba murmushi kawai take dama ba tun yau ba tasan matar da jarabar son jikoki komai nata na Sa'ida da Khalid ne....
: *93*
A bakin kofar gidan adaidaita sahu ta ajiye mu ganin tarin mutane a kofar gidan yasa gabana ya yanke ya fadi kallonta nayi ina kokarin magana tace."Ai kada kiyi mamakin ganin jama'a a kofar gidan dama ai na fad'a miki haka suke damun mutane watakila ai Khalid din ya dawo tunda ga motarsa can a tsallaken hanya". ajiyar zuciya na sauke nace."Wallahi Gwaggo ba kiji yanda gabana ya fadi ba ganin mutane a kofar gidan ya tuna min da mutuwar mahaifina." Girgiza kanta kawai tayi ba tare da tace komai ba ta fita daga babur din tana gyara lullu'binta fitowa nayi ina kokarin daukar akwatin kaya na dake can baya da sauri wasu matasa suka karaso gurin suna fadin."Gwaggo sannu da zuwa unguwa kika je."? Tace."Eh naje hotoro ne." Sannu da zuwa sukayi mata kafin daya daga cikinsu ya dauko min akwatina sai sannu da hanya suke mana, idona ne ya sauka kan motar tasa dake can gefe a ajiye na dan tsaya ina kallon motar da mamakin k'ayatuwar ta duk irin tarin motocin Yaya Aminu banta'ba ganin shi da irinta ba da alama dai motar sabuwa ce kuma ba tayi yawa a gari ba, ajiyar zuciya na sauke cikin zuciyata nace."Lallai Khalid ya samu duniya lokaci guda ya tara dukiya da jama'a gashi ya zama super star kowa sai ji yake dashi......... Hayaniya ce ta cika gidan Gwaggo ta kalleni da fadin."Kin gani ko ai kullum gidan nan a cike yake dangin Rabi maza da mata harda masu aure suzo suci na rana dana dare saboda tsabar rashin tunani uwar tasu Baito tana kallonsu ba zata ha nasu ba.

Nace."Gwaggo dan Allah kiyi abinda yake gabanki kada ki shiga sabgarsu rai yazo yana b'aci."! Tace."Aikuwa sai na shiga na fito dashi watakila yana ciki sun tasa shi a gaba ko abinci basa bari yaci a nutse."

Kafin nayi magana ta tura kofar gurin ta shige sai surutai take, ni dai sakin bakina nayi kawai ina bin ta da kallo na rasa yaushe Gwaggo zata daina shiga abinda be shafe ta ba.


"Eh ai dama wannan dalilin ne yasa ta kashe auranta taji yaro yayi kudi ya zama attajiri duniya tasan dashi shine ta kashe auranta domun ta aureshi to mutukar ni na haifi Khalid ba zan bari ya aureta ba taje can ta auri daidai da ita." Maganar Ummatu ce ta daki kunnan gwaggo sai tayi lamfo ta cigaba da saurarar tattaunar da sukeyi Baito tace." Ai ba zama zakiyi ki saki baki ba domin dai kin san wannan kakar tashi idan ta gindaya masa abu baya tsallakewa kiyi musu farraqu gabadaya yaji ya tsaneta dakinta ma ya daina shiga idan ba haka kikayi ba to babu shakka zata iya sanya shi ya auri 'yar iskar yarinyar nan mai kashin tsiya."
Ummatu tace."Ai yanzu bana fargaba tunda ina da kudin da zan zubewa ko wane irin malami yayi min taimako insha Allahu gobe ko jibi da wurwuri zan fito muje gurin taimakon." Baito tace."Yawwa to hakan shine dubara mai kyau."

Gwaggo kuwa gabad'aya gwiwarta ce tayi sanyi kalau ruwan hawaye ya taru a idonta wannan wace irin rayuwa ce Rabi da mahaifiyarta suka jefa kansu Hakikanin gaskiya Ibrahim beyi sa'ar mace ba hannu tasa tana goge hawaye ta juya da niyyar barin gurin shi kuma ya shigo dama lokacin da muka shiga gidan yana bandaki yana wanka.....Ganinta babu kuzari ga hawaye a idonta yasa gabad'aya ya shiga damuwa kafard'arta ya rike yana tambayarta Gwaggo tsabar tausayin kanta yasa ta fashe da kuka tana girgiza kanta, rungumeta yayi a jikinsa suka fito daga gurin.....Ni dai ina daki naji shashshekar kukanta da sauri na fito gabana na faduwa nasan dama ba zasu kwashe lafiya da Ummatu ba, ganinta rungume a jikinsa yasa da sauri na karasa inda suke amma ban kalleshi ba saboda yanayin yanda yake babu kaya a jikinsa sai wando iya gwiwa gashin kirjinsa ya jike jagab da ruwa fatarshi tayi wani irin haske sai kyalli takeyi sosai ya k'ara girma gabadaya jikinsa ya bud'e ya zama k'aton gaske, gabana ya dinga faduwa ina korar shed'an a zuciyata nake tambayarsa abinda yake faruwa.

Shima ba tare da yayi min cikakken kallo ba ya bani amsa da fadin."Ban san dalili ba kawai na fito daga wanka na ganta tana kuka."

Nace."Ya za'ayi kace baka san dalili ba bayan daga 'kofar ku ta fito." 'Bata rai yayi yace."Zanyi miki karya ne."? Nace." Aa ka wuce kayi karya ai tunda ka girma amma tilas kasan abinda ya faru kawai kana 'boyewa ne." Yace."Kina nufin Ummatu tayi mata wani abu kenan."? Nace."Ko Ummatu ba tayi mata ba wasu daga cikin gurin zasu iya yi mata. Kallonta yayi da fadin."Gwaggo me sukayi miki."? Tana numfarfashi tace."Babu komai." Kai ya girgiza da fadin."Akawai dalili Gwaggo ki fad'a min waye ya ta'ba min ke na dauki mataki."

Kallonsa tayi sai kawai zuciyarta ta karye hawaye suka dinga sharara a fuskarta ga jikinta sai karkarwa yake ya dauki zafi sosai.

Hankalina da nashi ya tashi jiki na rawa muka rirri'keta muka shiga da ita dakin muka zaunar da ita kan shimfid'arta......Hawaye na share na kalleta da fadin. "Kinga irin abinda nake gudu ko? shiyasa kafin ki shiga gurin nan sai da na hana ki amma kinqi Khalid dai ba yaro bane ballanatana kice dole sai kin taso shi a gaba yazo yaci abinci gashinan kin shiga sun tayar miki da hankali."


Ya kalleni da bacin rai a fuskarsa yace."Kada ki yanke hukunci sai kinyi binkice tukkuna." Nace."Babu wani binkice da zanyi gaskiya na fad'a matar nan tsohuwa ce ya kamata a dinga yi mata uziri a gidan nan kuma duk abinda take saboda kai takeyi me zai sanya a dinga kokarin kasheta da bakin ciki."

A zafafe yace."To ya isa haka bana bukatar k'ananun magana idan Gwaggo tayi min abu dama can ta saba babu ruwan ki zaman Gwaggo da Ummatu tuntuni haka suke abunsu kowa yana da laifi a cikinsu."

Nace."Ai a matsayin ta na uwar masu gida ya kamata ace ana rangwanta mata da wasu abubuwan me yasa ba'ayi mata adalaci."

Yace."Okey yanzu dai idan na fahimta kina so ki zagi Ummatu ko wani nata ko."? Murmushi nayi nace."Wannan ba halina bane da zan zagi Ummatu da tuntuni na zageta a matsayin uwa take a gurina amma kuma duk inda gaskiya take dole ne a fad'e ta.

"Yace." To kada ki sake sanya bakin ki akan abinda ya shafi zamantakewar Gwaggo da Ummatu mutukar kin dauketa a matsayin uwarki Bana son mu samu

Please Login or Register in order to submit comment