Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ki zaunar dashi ki rarrashe shi ki nuna masa cewa samu da rashi duk na Allah ne idan yayi hakuri sai Allah ya bashi wacce ta fini.

Tace."Zanyi iyakacin bakin kokarina Sa'ida Allah ya sanya masa dangana." na amsa da ameeen ina kokarin fita daga dakin.




*Littafin na kudi ne....Kada ki siya ki fita dashi...idan kika ganshi a gruops kada kiyi sharing......Idan kika karanta baki biya ba na biki bashi.....Idan kina so ki biya kudin littafin ga yanda abin yake... Vip gruop#600 normal gruop#300...account.. 0542382124...Binta umar gtbank....Idan kati zaki turo #400 ne sai kiyi min magana ta WhatsApp da wannan numbers*
*07084653262*
*08089965176*
*BINTA UMAR ABBALE*

*SADAUKARWA NE GA IYAYE NA BIYU*

*FATIMA MUSA (MOMMY NIJAR)*
*TARE DA*
*USAINA ABDUL-MALIK ISA (KAITA)*
*(HAJIYA BABBAH)*

*_Ha'kika ina Alfahari daku da irin kaunar da kuke min.🥰🤝🏻💜_*





*39&40*
Sai daf da magariba Khalid suka fito daga filin wasa, hannunsa rike da karamin towel yana goge zufar dake jikinsa ya nemi guri ya zauna yana mayar da numfashi, Salmanu ya zauna kusa dashi shima da k'aramin towel din a hannunsa yana goge fuskarsa, Oga Labaran ya karaso gurin fuskarsa yawalce da fara'a yace."Khalid a gaskiya kana burgeni da kwazon ka babu shakka nan gaba kad'an za kayi fice a duniya zata san da zamanka."

Khalid murmushi kawai yayi ya kar'bi goran ruwan faro dake hannunsa ya bude ya sha ya mikawa Salmanu sauran. Oga Labaran ya mika masa wayarsa da fad'in "Kana filin wasa aka kira wayar ka ka duba ka gani.''

Da sauri ya kar'bi wayar yana dubawa ganin sunan auntynsa yasa shi sakin murmushi ya mike da sauri ya bar gurin, Salmanu ya bishi da kallo yana girgiza kansa.

Number ta ya shiga kira cikin zumud'i da bukatar son yaji muryarta.

Lokacin da ya kira wayar tana sallah Gwaggo kuma ta idar da tana jan carbi, da sauri ta dauko wayar tana dawurwura domin bata san inda zata ta'ba ba.

Sai kawai tasa wayar a kunnanta ta dinga zabga sallama tana fad'in " Halo Khalid kana jina ko? Halo Khalid nice Gwaggon ka nake magana." Da karfi take maganar gashi wayar sai 'kara take yi kafin kiran ya katse! ta shiga duba fuskar wayar tana surutai da fad'in "To ko dai babu nethook ne." Saura kad'an dariya ta su'bcewa Sa'ida da sauri ta kori shed'an ta cigaba da sallarta.

Gwaggo ta cigaba da surutai da fad'in "Babu shakka yaron nan ne ya kira waya amma saboda abin nasara bashi da tabbas yayi mana rashin mutunci.

Tana rufe bakinta wani kiran ya sake shigowa, da sauri tasa wayar a kunnanta ba tare da ta ta'ba wani guri ba Fad'i take."Halo Khalid kayi min magana mana nice Gwaggonka."

Ummatu dake gurin ta a zaune ta dinga jin shouting din Gwaggo tana kiran sunan Khalid da saurin gaske ta fito ta tsaya a bakin kofar dakin tana fadin"Gwaggo Khalid din ne."?

Da sauri ta mika mata wayar da fad'in "Eh ina tsammanin shine kinga tun dazu yake kira inata magana babu amsa shine nace ko matsalar nethook ne."

Itama Ummatu sai da ta kusa dariya ta kar'bi wayar tana fad'in "Gwaggo ai baki d'aga wayar ba ba zaiji maganarki ba."

Tace."Ayya to ya ake yi."? Ummatu na kokarin magana Na idar da sallar wanda kuma yayi daidai da sake shigowar wani kiran.


Ta miko min wayar da sauri! Kar'ba nayi na d'aga tare da sawa a kunnena.

A dan sanyaye yace."Aunty barka da dare ina ta kiran waya baki daga ba." nace."Barka dai Khalid ina sallah ne.'' Yace."Okey to ina Gwaggo."? Nace."Gata a zaune ita da Ummatu.'' Kafin yayi magana na mikawa Gwaggo wayar yaji sautin muryarta a kunnansa.

Ajiyar zuciya mai sanyi ya sauke yace."Gwaggo ki gafarce ni akan abinda nai muku." Murya na rawa tace."Khalid mun yafe maka dan Allah ka dawo gida gabad'aya mun galabaita da rashin ka.''

Yace."Gwaggo insha Allahu sati mai zuwa zan zo gida amma hakan ba yana nufin na dawo kenan ba zan koma insha Allahu."

Tace."Khalid yanzu kana wane gari ne."? Yace.''Ina legos kuma na samu aiki Gwaggo kada ku damu akwai alamun nasara a inda nake.

Tace."Khalid daka hakura da Lego's din nan ka dawo gida ka cigaba da harkokin ka dan d'azu da Sa'ida ta kira wayarka wani 'katon mutum ya dauka yake fadin wai kana filin wasa Khalid kasan na tsani buga 'kwallon nan ko."

Yace."Gwaggo idan anan abinci na yake dole kiyi hakuri dan babu irin fafutukar da banyi ba akan na samu aiki abun yaci tura dole tasa na mayar da hankalina gurin buga kwallo.

Tace."To ka dawo gida kayi anan mana." Yace."Gwaggo zan duba maganarki." Tace."To shikkenan ga mahaifiyarka ma tana so tayi magana da kai."

Ummatu hannu na rawa ta kar'bi wayar tasa a kunnenta,

Gaisheta yayi ta amsa a sanyaye tana jin kewarsa tace."Khalid me yasa ka aikata wannan abu." A raunane yace." Ummatu rashin jin magana ne kin gargade ni akan na fita harkar aunty Sa'ida ni kuma na'ki bin umarninki shiyasa Allah ya jarrabe ni nima nayi nadama."


Hawaye ta share tace."Khalid ka dawo gida nima bana son zaman Lego's din nan."

Yace."Ummatu zan dawo gida amma kiyi min alkawarin amince min auran Auntyna."

Magana za tayi Gwaggo ta d'aga mata hannu, da yake wayar handsfree take duk muna jin maganarsa.

Gwaggo a hankali tace "Kice masa kin amince."

Ummatu ta dinga kallonta tana mamakin maganarta wace irin magana ce wannan bayan gobe daurin auranta

Yace."Ummatu kinyi shuru har yanzu baki bani amsa ba." a sanyaye tace."Khalid ka dawo na amince maka.

Hamdala yayi ga Allah cikin tsananin farin ciki yace."Nagode Umma Allah ya tabbatar mana da alkairi." a sanyaye ta amsa da ameeen tana mamakin al'amarin ko me yasa Gwaggon ta fadi haka.


Bayan sunyi sallama sai ta mikawa Sa'ida wayar da fadin"Gwaggo nifa wallahi duk jikina yayi sanyi da wannan maganar taki gobe i yanzu Sa'ida na dakinta ya za'ayi kuma a yaudari yaron nan yanzu idan ya zo ya tarar tayi aure mai zai biyo baya.

Gwaggo tace."Rabi komai mai sauki ne mutukar dai an samu ya dawo gida ai ni a ganina duk abinda zai biyo baya mai sauki ne ni zan zauna dashi na rarrashe shi ya hakura da kaddara matar mutum kabarin sa."

A sanyaye Ummatu tace."To shikkenan Allah ya kawo shi lafiya yasa kuma ya d'auki kaddara kamar yanda itama Sa'idan ta dauka." Gwaggo ta amsa da ameeen ya Allah. Ummatu sallama tayi mana ta nufi gurin ta tana dan jin sassauci a cikin zuciyarta.


Gwaggo bata kwanta bacci ba har sai da Kawu ya shigo ta sheda masa abunda yake faruwa. to shima da yake ya huce fushinsa akan d'an nasa sai yayi ta murna da farin ciki yana adduar Allah ya dawo dashi gidan lafiya.

****
To cikin ikon Allah da hukuncinsa a ka daura auran Sa'ida da Alhaji Nura daurin auran da ya samu hallatar mutane da dama ta 'bangaran Ango da kuma Alhaji Shamsu da Kawu Ibrahim anyi taro an gama lafiya amarya tayi ado sosai tai kyau k'awayenta na gurin aiki sunyi mata kara sun hallaci taron bikin sunyi mata gudumawa sosai mussaman Hauwwa dan itace ta dauki nauyin gyara mata jikinta da nau'in magungunan mata masu kyawun gaske mahaifiyarta ma tayi nata kokarin dan tun kafin bikin take gyara ta ita dai Sa'ida kallonsu kawai take fargabar abunda zai biyo baya kawai ke damunta tabbas tasan idan Alhaji Nura ya fuskanci ita din ba budurwa bace dole ya tuhumeta wannan dalilin yasa har aka gama taron bikin aka kaita dakinta ta kasa sakewa bini bini gabanta zai fad'i....Yanzu ma tana zaune ita kadai a dakinta bayan tafiyar Hauwwa sai tunanin yanda zata kaya take tasan Alhaji Nura yana sonta watakila idan ta fada masa abinda ta tanada ba zai kalubanceta ba.

Ya shigo dakin cikin manyan kaya kamshin turaransa ya game dakin ledojin hannunsa ya ajiye kan teble tun kafin ya zauna a kusa da ita ya cire babbar rigar jikinsa da murmushi a fuskarsa ya kira sunanta had'e dayi mata kirarin da ya saba. "Amarya bakya laifi ko da kin kashe d'an masu gida."

Mayafin dake rufe da fuskarta ta cire tana d'an mirmushi tace."Alhaji kenan." yace."Aa inaso ki kira ni da angon gimbiya Sa'ida."

'yar dariya tayi cikin jin nauyi ta kauda kanta yace."Alhamdulillahi nagode Allah daya nuna min wannan rana Sa'ida auran nan namu anyi kamar ba za'ayi ba sai gashi Alkwarin Allah ya cika."

Tace."Hakane Alhaji dama komai yana da lokacinsa ina rokon Allah ya tabbatar mana da alkairi."

Ya amsa da ameeen ya rabbi yanzu zaki tashi muje falo domin inaso na zauna daku keda 'Yar uwarki."

Nace."To shikkenan." kokarin mikewa nake ya rike hannuna muka mike a tare falon muka fito ya zaunar dani akan kujera da fadin."Bari na kira ta ko." kai kurrum na daga masa na bishi da kallo a lokacin da yake kokarin hawa sama.

Tv na tsirawa ido ina kallon film din da akeyi a tashar Mbc action...........Ina zaune tsayi mintina talatin ina tsammanin su shuru babu labari na dauke kaina daga kan tv din na tsirawa matattakalar benan ido jikina yayi bala'in mutuwa da al'amarin anya kuwa mutumin nan zai fito minti arba'in ko motsinsu nayi kasa da kaina hawayen takaici na nema ya kufce min............Motsinsu naji da sauri na daga kaina ina kallon steps din ya riko hannunta suna saukowa na dauke kaina raina yayi masifar 'baci da abinda sukayi min.

A nutse ta zauna kan kujera shima ya zauna kusa da ita da fad'in "Sa'ida kinji shuru ko afuwa tana d'an uziri ne shiyasa na jira ta gama.

Yanda ya fadi maganar kai tsaye babu kulawa yasa naji wani irin sam bai saba yi min magana gatsar-gatsar ba tunda nake dashi idan zaiyi min magana ko a waya ne sai ya tausasa murya amma yanzu magana yake min kamar baya so.

Cikin kokarin danne damuwa ta nace " Ayya ai babu damuwa. kallonta nayi a nutse nace."Aunt Murja ina fata kin wuni lafiya."?


A sake ta amsa min da "Lafiya lau Alhamdulillahi Sa'ida ya taro.''? Nace."Alhamdulillahi." falon yayi shuru na minti biyu kafin yayi gyaran murya kamar me tsoron magana yace."Sa'ida ga Uwargidana Murja Uwar Yasir da Yusura kenan inaso ki zauna da ita lafiya ki mutuntata a matsayinta na uwargidanki kada naji kada na gani tunda nake da ita wani sa'bani bai ta'ba shiga tsakaninmu ba sabida haka bana so zuwanki ya hargitsa min gidana kada kiyi kishi da ita tunda itama ba tayi dake ki dauketa a matsayin 'yar uwa kamar yanda ta daukeki."


Kaina ya dinga juyawa ina jin maganganunsa suna amsa kuwwa! a kunnena........Wannan wasu irin banzayen maganganu ne."?

"Sa'ida ko bakya ji ne.'' Muryarsa ta dawo dani hayyacina, nace." Naji Alhaji Allah ya sa'ba halaye a tsakaninmu." Ya amsa da ameeen ya Allah.

Muryart a naji tana fad'in "Abban Yusura ni zan shiga na kwanta .'' da sauri ya mike da fadin" Haba gimbiya ai ni zan mayar dake d'akin ki kamar yanda na dauko ki."

Kafin na ankara naga ya rike k'ugunta sun fara hawa steps suna magana 'kasa-'kasa, kaina ya dinga juyawa a gurin na nemi yawun a bakina na rasa hawayen dai da nake dannewa sai da suka kufce na mike da saurin gaske na shiga dakina na zauna bakin gado hawaye masu zafin gaske suna shatata a fuskata...."Shin ni d'in wace irin amarya ce ne? tambayar kaina nake Wace irin wulakantacciyar amarya ce wacce ba'a zumud'in ta? ashe Alhaji Nura mijin tace ne a gidansa? shin me hakan yake nufi ne ? yana so ya nuna min cewa matarsa ta fini daraja a gurinsa? tambayoyin da nake tayi wa kaina kenan ina wani irin kukan bakin ciki a yanzu Alhaji Nura ya fifita matarsa a kaina to kuma ina ga ya fahimci abinda yake lullu'be! innalillahi wa'ina ilahi raji'un!
Ita na dinga nanatawa a cikin raina ina addua akan Allah yasa duk abunda zai faru dani na kaddara yazo min da sauki tabbas nasan zan fuskanci tashin hankali a zamantakewar aurana.

Dakin ya shigo kamar wani mutumin kirki ya mayar da kofa ya rufe dauke kaina nayi har ya karaso kusa dani ya tsaya da fadin"Gimbiyar mata kiyi hakuri na barki ke kadai ko Maman Yusura ce take fama da mura shiyasa na dan jima a gurinta na tabbatar tasha magani ta kwanta.

Shuru nai masa yace." Ki tashi kije ki dauro alwala mu gabatar da sallar godiya ga Allah." ba tare da nace komai ba na mike na nufi toilet din dake cikin dakin, ina daura alwalar ya shigo na dauke kaina ina gamawa na fita na bashi guri.


Addua yayi sosai muka shafa na mike na koma bakin gado na zauna...ledojin da ya shigo dasu ya hau budewa da fadin" Amarya ki sauki kici abinci ko."

Nace."A koshe nake ni." jim yayi yana kallona kafin yace."Kin san fa yau tsakanina dake a kwai harka yana da kyau ki cika cikin ki kada ki galabaita."

Dauke kaina nayi bance masa komai ba, yayi murmushi a nutse ya fara cin kazar amarcin yana hadawa da lemo, cikinsa ya cika sosai kafin ya d'an gyara gurin duk ina zaune ina kallonsa ya nufi toilet ya wanke bakinsa ya fito..

Hasken dakin ya kashe ya mayar dashi Dark gabana ya tsananta faduwa ganin ya cire rigar shaddar jikinsa ya hayo gadon na dan ja baya ina kallonsa ya janyo ni jikinsa yana kokarin cire mayafin jikina.

Jikina ya dinga karkarwa na dinga no'kewa ina kare jikina, Alhaji Nura gabadaya ficewa yayi daga hayyacinsa ganin zahirin ta sai ya shiga sambatu yana wasa da sassan jikinta mussaman Brest d'inta da suke masifar tafiya da imaninsa.

Ni dai ina kwance ina kallonsa da jinsa yana sarrafa ni gabana na cigaba da faduwar abinda zai faru, jin yana karanto adduar saduwa da iyali yasa na rintse idona kawai sai jikina ya shiga karkawa tun kafin ya shige ni na fara zubar da hawayen bakin ciki da takaici.


Ya jima kafin ya shiga ramin amma duk da hakan sai da ya gane matar tasa ba budurwa bace, ransa idan yayi dubu ya 'baci! ya cigaba da abinda yake yi yana bukatar ya samu satisfaction ya sauka a gaskiya yayi mamakin yarinyar ashe dai duk irin maganganun da ake kawo masa akanta gaskiya ne gashi yanzu ya gazagata tunda ya sameta a bude.

Ni'imar ta da dad'in ta sune suka sanya yaji dan sassauci a cikin ransa amma dai duk da haka sai ya tuhumeta akan cin amanarsa da tayi......sau biyu yana kawo wa amma abin mamaki a duk kawowar da zaiyi baya ta'ba yarda yayi a cikin ramin fita yake da jijiyar tasa ya zubar da sperm din a kan bedshirt kafin ya koma ya cigaba da biyan bukatarsa, shin to meye manufarsa tayi hakan.?

*SADAUKARWA NE GA IYAYE NA BIYU*

*FATIMA MUSA (MOMMY NIJAR)*
*TARE DA*
*USAINA ABDUL-MALIK ISA (KAITA)*
*(HAJIYA BABBAH)*

*_Ha'kika ina Alfahari daku da irin kaunar da kuke min.🥰🤝🏻💜_*



*41&42*
Cikin tsananin bushewar ma'kogwaro na mike zaune tare da kare jikina da bedshirt din daya cukurkud'e sabida dabdalar da akayi akansa. Gajeran wandonsa ya dauka yasa a jikinsa ba tare da ya ko kalli inda nake ba ya sauka daga gadon bandaki ya nufa

Cikin mutuwar jiki gami da nadamar rayuwa nabi bayansa da kallo wata masifaffiyar fargaba ce ta tsaya min a raina hakika ya fahimci abinda yake da akwai ko ga yanayin yanda ya sauka daga gadon yana d'acin rai.

Motsin fitowarsa naji daga toilet din sai nayi saurin sunkuyar da kaina kasa jikina duk ya mutu tsabar nadama da kunya tasa kwata-kwata bana kaunar na hada ido dashi.

Ganin ya nufi wardorbe ne yasa na mike a hankali na nufi toilet jikina duk a sab'ule... Tsuganawa nayi na takure kaina guri guda mahaukacin kuka ya kufce min. hannu nasa na rufe bakina ina so na had'iye kukan amma yaki haka na hakura nayi tayi ina shar'be majina Khalid Khalid ya cuce ni ya kassara min rayuwa wannan rana itace ranar da ko wace mace take alfahari da ita mutukar ta yarda da kanta ita din cikakkiya budurwa ce dole tayi tunkaho da ranar daran amarcinta amma ni na kasance cikin kunci da bakin ciki sakamakon abinda Dan uwana na jini yayi min Khalid baya sona domin da yana sona ba zai keta min rigar mutunci ba.

Na jima tsugune a toilet din ina kuka kafin nayi wankan tsarki na fito na samu dakin duhu sosai ya kashe hasken. da lalube na dauki waya ta kan mirror na kunna toch sai na ganshi kwance a kan gadon ya jefar da bedshirt din ya 'bata a kasa ya shimfida wani.

Babu kuzari a tare dani na duba doguwar rigar bacci mai hula nasa a jikina tare da pant. a sanyaye naje na kwanta kusa dashi sai ya matsa can gefe tare da juya min baya.

Na tsirawa bayan nasa ido ina ayyana abubuwa masu yawa yanzu ko wane irin hukunci zai yanke akaina tabbas al'amarin yayi masa zafi koga yanayin yanda yayi shakulatun 'bangaro dani ko banza nasan da ya samu budurci a tare dani zai taimaka min da wani abu amma saboda yasan ban cika mace ba ya biya bukatarsa ya juya min baya banga laifinsa ba akan abinda yake ko wane namiji abinda yake kulafuci kenan mutukar yasan budurwa ya aura zai so ace shine zai fasa tantanin budurcinta.

zazzafar ajiyar zuciya na sauke na gyara kwanciya tare da tsirawa rufin dakin do.


Yanda naga dare haka naga rana tsabar fargaba ta hana ni rintsawa shi kuwa baccin sa kawai yake yana sakin munshari babu abinda ya dameshi.


Asubah nayi ya tashi ko gefe na bai kallah ba ya sauka daga gadon ya shiga bandaki, na mike zaune tare da saukar da kafafuna kasa, ido muka hada a lokacin da ya fito nayi gaggawar yin kasa da kaina kunyarsa nake Ji wallahi.

Fita yayi daga dakin daure da alwala. na sauke ajiyar zuciya jiki a mace na mike na nufi toilet domin na daura alwala.


To har gari ya waye sosai nayi wanka na shirya jikina babu labarinsa na daga kaina na kalli agogon bangon dake kafe a dakin tara da rabi na safe tunda ya fita sallah bai dawo ba. cikin rauni da sarewa na sauke kaina kasa ina addua a cikin zuciya ta akan Allah ya sassauta min.

Da sauri na dago kaina jin motsin shigowarsa dakin. wannan karon dakewa nayi a lokacin da muka hada ido dashi ban nuna tsorona ba, har ya karaso inda nake ban dauke idona daga kansa ba mamaki nake lokacin da ya fita daga dakin jallabiya ce a jikinsa amma abin mamaki yanzu ya shigo cikin sabuwar shadda(wagambari) sai zabga kamshi yake yi shin a ina yayi wanka ya kimtsa? zuciyata ce keyi min wannan tambayar.

Kusa dani ya zauna yana yi min wani irin kallo jikina ya sake mutuwa a hankali nace."Alhaji Barka da asubah fatan ka tashi lafiya."?

Bai amsa ba kuma bai fasa watsa min kallon tuhuma ba.

Sai kawai na shiga wasa da hannuwana ina jiran abunda zai biyo bayan kallon.

"Sa'ida mai yasa kika yaudare ni kika sa na aure ki a matsayin budurwa." ? tambayar da yayi min kenan wacce ta kusa sa zuciyata ta faso kirjina ta fito waje.
jarumta na aro nace."Alhaji wace irin magana ce wannan."? Ido ya zuba min fuskarsa a had'e yace." Kada ki mayar dani shashasha mana ba'a kanki na fara auran budurwa ba matata Murja da budurci na aureta kuma akanta nasan ya yake saboda haka jiya na tabbatar da cewa ke ba cikakkiya bace dan duk wasu gyare-gyare da kikayi a gurin sai da na gane budurci ya bambamta da komai."

Zafafan hawaye suka kwace min murya na rawa nace."Haba Alhaji shedar da za kayi min kenan? ashe shiyasa naga kana ta 'kunci ka tashi ka fita tun asubah baka shigo ba sai yanzu to inaso ka sani ni ba 'yar iska bace ballanatana kayi zargin ko gurin yawon ta zubar na sarayar da mutunci na. Sabida haka ni ban san wata magana ba budurci na kai ne ka kar'ba ba wani ba." Cikin kame-kame nake magana gabana kuma na cigaba da faduwa

Yace."Ki saurare ni da kyau kiji abinda zan fada miki." Na kalleshi ina goge hawaye ya cigaba da cewa"Tun kafin na aureki jama'a suke kawo min suka akan ki cewa babu abinda kikeyi a gurin aiki sai lalata da maza wannan dalilin yasa na sake gazgata maganar mutane tunda naga zahiri kada ki mayar dani yaro nasan komai kin cuce ni kin yaudare ni ashe kin san baki da kamun kai kika sa na tsaya na 'batawa kaina lokaci gurin auranki."!

Ina wani irin kuka na zube gabansa hannunsa na rike nace."Wallahi Alhaji duk k'arya ce kada ka gazgata maganar mutane akaina sharri sukai min amma ni bana bin maza zan iya rantse maka da al'kur'ani ni ba karuwa bace budurci kuma da kake magana akansa watakila ya fita ne saboda tsayin lokacin dana dauka banyi aure ba bayan haka kuma kaga kullum bana zama ina zurga zurga zuwa gurin aiki hawa babur da Napep hakan zai iya janyowa na rasa budurcina.

Shuru yayi yana kallona da akwai alamun sassauci a tare dashi a sanyaye nace."Dan Allah ka yarda da maganata Alhaji ban yaudare ka ba kada ka amince da maganganun mutane a kaina sharri sukayi min."

Hannu yasa ya d'ago ni na zauna kusa dashi yace."Naji maganarki kuma na gamsu tabbas zaki iya rasa budurcin ki ta wad'annan hanyoyin da kike fad'a sabida haka ki share hawayen ki na amince da maganarki.

Ajiyar zuciya na sauke nace."Nagode sosai mijina ina rokon Allah ya kauda idanun makiya akanmu." ya amsa da ameeen yana kokarin miqewa yace."Ni zan tafi kasuwa saboda kin san bamu jima da shigo da kaya ba bana zama a gida sosai dan haka kina iya zuwa kiyi breakfast d'in ki."

A sanyaye nace"To shikkenan sai ka dawo Allah ya bada sa'a.'' ya amsa da ameeen ya kama hanya ya fice daga dakin.

Ajiyar zuciya na dinga saukewa ina godewa Allah da yasa ya yarda da maganata yanzu dama ashe kallon karuwa mutane keyi min? shin me nakeyi a makaranta da har mutane zasu sanya min ido su dinga zargi na da aikata fasikanci." hawaye na share a fili nace."Ya Allah kabi min hakkina akan dukkanin wanda ya d'ora min kazafi na zina.


Fuskata na wanke na d'an shafa hoda nasa kwalli a idanuwana kana na fita falon......a hakimce akan kujera na sameta tayi ado sosai kamar itace amaryar tafkekiyar wayarta ce a hannunta tana dubawa.

Gani na yasa ta saki fuskarta tana murmushi ta nuna min kusa da ita na zauna a nutse muna gaisawa.


Yaran na tambaya tace."Sun tafi makaranta sai biyar da rabi zasu dawo ai da har sun zauna suna jiran fitowarki sai kuma direbansu yazo daukarsu da kyar na lallabasu suka tafi.

Murmushi nayi nace."Ai idan sun dawo zamu gaisa da kyau." Tana tauna cingum! din bakinta tace." Kwarai hakane.

Falon ya sake daukar shuru na 'yan mintina kafin tayi magana "Sa'ida kije kiyi breakfast mana." Murmushi nayi ba tare da nace komai ba. tace."Dan Allah ki saki jikin ki dani ni bana kishi irin na jahilci kanwata na dauke ki.''

Nace."Nagode kwarai auntyn Murja. " tace."Nima nagode da kika fahimce ni

Please Login or Register in order to submit comment