Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

saboda haka sai ki tashi kije ki karya ko." ba tare da nayi mata musu ba na mike a nutse na nufi gurin cin abincin.


A ranar haka muka yini da Aunty Murja muna hira na dinga mamakin saukin halinta kamar bata da damuwa akaina domin daidai da 'kwayar zarrah banga ta nuna wani kishi a kaina ba wannan dalilin yasa na saki jikina da ita sosai muka shiga kicin a tare mukayi aiki tsaf muka kammala komai muna hira cikin fahimtar juna

Koda yaran suka dawo daga makaranta a daki suka sameni ina shiryawa suka gaisheni suna nuna farin cikin su da zuwana cikinsu nima na dinga jansu a jikina ina duba litattafansu na makaranta.

Sai da mukayi sallar isha'i tukkuna suka fita suka barni ni kadai a dakin.....sai kawai na yanke shawarar fita falon. abin mamaki da al'ajabi maigidan na samu zaune a gurin cin abinci iyalin nasa suna zaune ko wanne da kujerarsa suna cin abinci....sosai na shiga mamakin al'amarin yaushe ya shigo gidan babu labari kuma me yasa basu nemi ni gurin cin abincin ba.?

Gwiwa a sanyaye na juya zan koma daki muryar Yusura ta daki kunnena...."Aunty kizo muci abinci." a sanyaye na juyo ina kallonsu naga shi gogan ko kallona ma beyi ba sai abincinsa yake ci itama aunty Murjar haka.... hakan da sukayi sai ya nuna min cewa basa bukatata a gurin.....jiki a mace na bude kofar dakina na shiga na rufe tare da jingina jikina jikin kofar gabana sai wani irin faduwa yake....wace irin rayuwa ce wannan? shin wai me Alhaji Nura yake nufi dani ne? ganin bani da mai bani amsa yasa na sulale nayi zaman durshan a gurin hawayen bakin ciki ya shiga karakaina a fuskata.

Na jima a zaune a bakin kofar dakin ina kuka kafin na bawa kaina hakuri na mike a sanyaye na shiga bandaki na wanke fuskata na fito ina kallon agogo goma har ta gota bai shigo dakin ba ga yunwa na kokarin cinye min 'ya'yan hanji a sanyaye na mike na fita falon sai na gansu a zaune yaran suna kasan kafet suna duba littafansu na makaranta su kuma suna zaune a kan kujera a tare yana nane da jikinta sai soyayya sukeyi. fitowa ta bai hana su abinda sukeyi ba, ta kalle ni na kalleta ina mamakin iya sharrin ta wai ni za tayi wa dariya na tsaya kawai ina kallonta da jin abinda take fad'a...."Sa'ida kina ji Yusura nayi miki maganar abinci kika share ta.''

Kai tsaye nace."Aunt Murja naga kamar bakwa bukatata a gurin ne."

'Yar dariya tayi tana kallonsa tace."Abban Yusura kaji amaryar ka da wata magana ko."?

Murmushi yayi irin na dole yace." Ina jinta ai na fahimci neman fitina take."

Kallon banza na watsa masa a zuciyata nace"Lusari mijin tace kawai."
Daga ita har shi sunga abinda nayi kuma na lura sunyi mamaki. nace."Ai idan an damu da naci abincin kira na Za'ayi ba kawai sai na fito na tarar daku kuna ci ba.''

Fuskarta ce ta sanja da yanayi na 'bacin rai kafin tayi magana ya rigata da fad'in "Ke wace irin banzar magana ce wannan? kina so ki rusa min tsarin gidana ne."? shuru nayi masa ya cigaba da fuffuka yana kumfar baki.

Nace." Dan Allah kayi hakuri naga kamar maganata ta fusata ka kasan ita gaskiya d'aci gareta."

Da sauri tace."Sa'ida kiyi hakuri anyi miki ba daidai ba kai kuma ka daina wannan kumfar bakin haka.'' Kamar anyi ruwa an dauke yayi shuru sai wani muzurai yake.....naja tsaki cikin raina na bar gurun

Gurin cin abincin na zauna na zuba daidai cikina naci na tashi na bar gurin......nesa dasu na tsaya da fad'in "Aunt Murja sai da safe." Fuskarta kamar gonar audiga ta amsa da fad'in "Allah ya tashe mu lafiya.

Dakina na bude na shiga takaici kamar ya kashe ni cikakken mutum a zahiri mai haiba da kamala uwa uba kudi amma saboda lusaranci mace na juya shi a gida wani irin tsanarsa naji a cikin raina.

Wanka nayi na shirya jikina na kwanta kan gado da waya ta a hannuna.......Misscall din Khalid na gani gabana ya fadi da sauri na mike zaune hannuna sai rawa yake.

Wani kiran ne ya sake shigowa, kamar kada na daga sai wata zuciyar tace " ki daga kiji abinda zai ce."

A hankali nayi sallama naji sanyayar muryarsa yana amsa wa. kafin yace."Aunty ya kike ina fatan kin wuni lafiya." ?

Nace."Lafiya khalid fadi abinda yake bakin ka inada uzuri.'' murmushi yayi wanda yasa tsigar jikina tashi. na lumshe idona ina sauraransa.

Yace."Wato aunty Sa'ida idan bani na kira wayarki ba ban isa ki kira ni kiji lafiya ta ba ko."?

Shuru nai masa yace."Yau so nake nayi hira dake inaso na rage feeling's ne auntyna ina nan sha'awar ki duk ta addabe ni kiyi min wani taimako mana." yakarasa maganar a sanyaye.

Wani irin yanayi na shiga na tsantsar tashin hankali da fargaba nace."Khalid yaushe zaka dawo gida." Ajiyar zuciya ya sauke yace."Na fada miki cikin satin nan zan zo kuma da sadaki na domin ba zan koma ba sai an daura mana aure.

Shuru nayi kaina yana wani irin sarawa nace."To kayi kokari ka dawo kaji ko." Yace."Insha Allahu ki bani Gwaggo mu gaisa.'' da sauri nace."Ta riga tayi bacci." yace."Okey da safe zamu gaisa insha Allahu yanzu meye labari auntyna ki fad'a min kinyi kewa ta ko."?

Ina kokarin magana ya shigo dakin, da sauri na datse wayar na ajiyeta, ya karaso kusa dani a daida lokacin da ya 'kara kira, sai kawai na dauki wayar na kashe ta gabadaya na ajiye saman bedside.

Jallabiyar jikinsa ya cire na dauke kaina daga kansa toilet naga ya nufa da gashi sai gajeran wando naja tsaki da fadin"Shashashan namiji kawai.

Minti biyar ya fito daga toilet din ya kashe wutar dakin, kusa dani ya zauna na sunkuyar da kaina ina jin wani irin haushin sa.

Shuru yayi yana tunanin da abinda zai fara "Sa'ida." ya kira sunana kallonsa nayi a kaurare yace."Kada ki sake ganin wani abu a cikin gidan nan ki tanka kome kika gani yana tafiya ne akan tsari mun riga mun tsara gidanmu nida Murja saboda haka abinda kika zo kika tarar dashi zakiyi amfani."

Na dinga kallonsa ina mamakin maganarsa......"Alhaji wannan ai ba tsari bane kwana na daya kacal gidan ka na fahimci abubuwa da yawa a gaskiya dole da kai da matarka ku canja tsari tunda yanzu na shigo gidan kuma a matsayin matar gida nake."

Hannu ya d'aga min da fad'in "Bana bukatar canza wani tsari a gidana wanda yake kai shine daidai saboda haka idan kina bukatar zama tare dani dole kibi abinda nace."

Na dinga kallonsa ina me mamakin al'amarin.... matsowa jikina yayi yasa hannunsa ya janyo ni jikinsa ya matse gam! raina ya 'baci! nayi yunkurin tureshi ya rike ni sosai ya sa min nauyinsa, hakura nayi na kyaleshi ya cigaba da budurunsa yana sambatu sai lugudar breast d'ina yake yana sha kamar zai tsinke nippels d'in, yanayin jikina gabadaya ya sanja zazzafar sha'awa mai zafi ta taso min.

Sakar masa jikin yayi ya dinga sarrafa ni iya son ransa.. Daf da zan samu satisfied ya zare jijiyar daga ramin ya dinga mutsika brest d'ina yana wani irin sambatu kafin naji saukar ruwa mai d'umi a tsakanin cinyoyina duk ya 'bata min jiki da sperm d'in shi, kafin nayi wani motsi naji saukarsa daga gadon, cikin mawuyacin hali na bude idona na bishi da wani irin kallon mamaki a lokacin da yake kokarin shiga toilet.

*SADAUKARWA NE GA IYAYE NA BIYU*

*FATIMA MUSA (MOMMY NIJAR)*
*TARE DA*
*USAINA ABDUL-MALIK ISA (KAITA)*
*(HAJIYA BABBAH)*

*_Ha'kika ina Alfahari daku da irin kaunar da kuke min.🥰🤝🏻💜_*




*43&44*
Wani irin azababben ciwo mara ta take min ta dinga wani irin d'aurewa tana murd'awa . fillo na janyo na matse shi tsam-tsam a kirjina ina cigaba murkususu da birgima a gadon gabad'aya hankali na a tashe yake ina jin wani irin azababben feelings yayin da mara ta ke sake turnukewa da ciwo mai zafi.
Zafafan hawaye ne suka shiga sauka a fuskata na rintse idanuwana ina kiran sunan Allah a fili da zucci motsin sa naji ya fito daga toilet din na bude idona dishi-dishi nake ganinsa sakamakon k'an'kancewar da sukayi,

Ni kaina nasan ina da tsananin bukata shiyasa sam ban fiye kallon india film ba dan wannan rungume rungumen da suke yakan tayar min da hankali na uwa uba kuma a yanzu na kai matakin da dole sai da d'a namiji zanyi rayuwa kamata yayi ace na samu jarumin namiji da zai dauke min dukkanin lalurata ta tsayin shekarun da nayi babu aure kwata-kwata ban tsammaci haka daga gurin Alhaji Nura ba saboda ni inayi masa kallon namiji cikakke wanda zai biya min bukatuna ashe ba haka bane *Kallon kitse na kewa rogo* Alhaji Nura ta ko'ina yana da matsala mai girma.

Zaman sa kusa dani yasa na kalleshi naga yana jan bargo zai kwanta duk ya tuje bedshirt din da ya 'bata yana so ya kwanta kan katifar a haka, raina ne ya 'baci na miqe zaune ina kallonsa.

Ya kalle ni babu wata cikakkiyar kulawa yace."Ko da akwai wata bukatar ne."? Kai tsaye nace."Eh da akwai." yace."Okey bukata mutukar ta kudi ce ki fada kawai."

Jikina yayi sanyi da jin maganarsa nace"Ni bana bukatar kudi Alhaji." kallona yayi yana neman 'karin bayani.


Kunya da tsoro na cire nace "Alhaji ni fa
Bangane abinda kake nufi ba."

Yayi shuru yana kallona na cigaba da cewa" Me yasa kake min haka ne sai ina daf da samun satisfaction sai ka rabu dani jiya haka kayi yau ma haka meye amfanin zubar da sperm din da kake a waje."


Jim yayi kafin yayi gyaran murya da fad'in "Sa'ida bana bukatar haihuwa a yanzu Yusura da Yasir sun ishe mu itama Murja abinda mukeyi kenan ni da ita tuntuni mukayi tsarin mu.

Raina ne ya 'baci nace." To ni me kake nufi dani kenan kana nufin ba zaka haihu dani ba."?

Ba tare da damuwar komai ba yace."Eh haka nake nufi ai na fada miki yara biyu kacal sun isheni rayuwa ga Murja nan munfi shekara bakwai muna haka da ita bata samu ciki ba kuma ba ta ta'ba cewa bata gamsuwa ba sai ke sarkin jaraba ko."

Hawaye suka zubo min nace." Alhaji wannan Wace irin magana ce ni kake kira da jarababbiya.''

Yace."To idan ba ita bace me yasa zaki sani a gaba kina min kuka okey kina so na jigata kaina a kanki ko? na yini a kasuwa ina nema da daddare sai na 'kare a gindin ki ko ? to ni ba haka nake ba idan nayi sau d'aya shikkenan na gamsu matata Murja bata da matsala dani .


Wani irin kallo nake masa ina mamakin maganganunsa wato dai Alhaji Nura yaudarata yayi Ashe bashi da mutunci dama."? Zuciya tace "Aa Sa'ida ke kika cutar da kanki yanzu da Khalid kika aura ai bakin ki alaikum zai cika miki mara ya dauke miki dukkanin bukatunki.

Ajiyar zuciya na sauke na kalleshi ya juya min baya ya rufe jikinsa da bargo babu abinda ya dameshi baccin sa kawai yake.

A tsananin bukace na matsa kusa dashi ina dan shafa jikinsa, ya juyo da saurin gaske ya ture ni da fad'in " Sa'ida bafa ki isa kisa nayi abinda banyi niyya ba ni na gaji ki kyale ni nayi bacci na huta gajiya."

Sakato nayi da baki ina kallonsa yaja tsaki mai karfi ya koma ya kwanta.

Shuru nayi a zaune a gadon ina sa'kawa da kwancewa, nafi karfin rabin a wa a zaune ina tunani shin ya za'ayi na warware wannan gagarimar matsalar da nake fuskanta. Hakuri kawai na bawa kaina na cire abin daga raina na mike da mataccen jiki na shiga bandaki na tsarkake kaina har na fito daga toilet din gabana bai daina tsut-tsut ba babu shakka har yanzu gurin bai daina bukatar a gaji ba.

Ban kwanta kusa dashi ba sai na dauki fillo na ajiye kasan kafet na kwanta na takure jikina cikin hijab ina addua akan Allah yasa bacci ya dauke ni......Cikin ikon Allah kuwa bacci mai nauyin gaske ya dauke ni.

Sai wajejen shida na safe na tashi, lokacin shi tuni ya fice daga dakin na dinga mamakin yanda akayi bai tashe ni nayi sallah ba. a sanyaye na mike na shiga bandaki wanka nayi a gurguje na daura alwala na fito sai da nayi sallah tukkuna na shirya jikina gabad'aya auran Alhaji Nura ya fice min daga raina, gefan gado na zauna na kunna waya ta ina dube dube so nake na kira k'awata Hauwwa na fada mata halin da nake ciki ko da akwai shawarar da zata bani....Ina kokarin kiran wayar ta Khalid ya kira babu kwari na daga wayar gami da sawa kunnena.

"Auntyna kin tashi lafiya." A sanyaye nace."Lafiya Khalid." Yace."Ya na jiki wani iri ko baki da lafiya ne."? 'Kwallah ce take kokarin zubo min na daure nace."Lafiya ta lau." Yace."Okey ki bawa Gwaggo mu gaisa a gurguje zan fita gurin wasa ne." Nace."Khalid Gwaggo tana bacci." Jim yayi kafin yace." Tunda nake banta'ba ganin Gwaggo na bacci da safe ba a daidai wannan lokacin take zaman kad'i tana sauraran redio aunt Sa'ida ko dai da akwai abinda kike 'boye min."?

Nace."Khalid Gwaggo ba ta jin dadi ne shiyasa tana karya kummalo tasha magani ta kwanta bacci ya dauketa." Cikin jimami yace."Allah sarki Gwaggo ki gaishe min da ita idan mun fito daga wasa zan sake kira." Nace."Tom shikkenan." Kokarin kashe wayar nake ya shigo dakin cikin dakakkiyar shaddar galila kamshin turaransa ya game ko'ina har ya karaso inda nake ban dauke idona daga kansa ba cikin zuciyata nace"A zahiri cikakken mutum amma a bad'ini malalaci ne.

Gaishe shi nayi ba tare dana kalleshi ba, ya amsa yana duba agogon hannunsa da fad'in "Dawa kike waya ne."? Gabana ne ya fad'i ! nace" Khalid ne."? Jim! yayi yana kallona da fad'in "Menene zai kira ki da sassafe haka."? Nace." Wai yana so su gaisa da Gwaggo ne." Yace."Ita Gwaggon bata da waya."? kaina na daga masa.

Ya wani 'bata rai da fad'in "Kada ki kuskura ki sake d'aga wayarsa a cikin gidana." Kai tsaye nace "Sabida me."? yace." Tambaya ta kike."? na kalleshi ido cikin ido nace."Eh." girgiza kansa yayi yace."Yaron nan fa nasan mun had'a takara dashi gurin neman auranki to mai zai sanya na zuba ido na barki kina mu'amula dashi."

Cikin takaici Nace."Alhaji da kuka had'a takara da Khalid wa na za'ba a cikin ku."? 'Kirjinsa ya nuna da hannu da fad'in "Ni kika za'ba."

Nace."To meye naka na kishi da damuwa Khalid dan uwana ne na jini ba zaka rabamu ba."


Rai a 'bace yace."Yanzu dai nasan kin san da cewa a karkashina kike ko."? Nace."Eh yace."To idan na isa kada ki sake daga wayar yaron nan." cike da d'umbin mamaki nake kallonsa. ya girgiza kansa da fad'in "Ni zan tafi kasuwa." shuru nai masa. yayi murmushi wanda shi kadai yasan manufarsa ya kama hanya ya fita daga dakin ya barni cikin d'umbun mamakin sa.

Bayan fitar sa na jima
ina sa'ke-sa'ke kafin na yanke shawarar kiran Hauwwa a waya idan da hali tazo mu tattauna domin a gaskiya ina bukatar mai bani shawara akan wannan gagarimar matsalar

Jin yanda nake magana a sanyaye yasa itama tasha jinin jikinta tace."Sa'ida lafiyarki kalau kuwa.'' Nace."Hauwwa lafiya ba lafiya ba dan Allah idan an tashi kizo zamuyi magana."

Tace."Sa'ida kina ganin babu matsala ko? bana so ina zuwa gidan mata biyu gudun zargi kin san dai yanda rayuwar nan take wata matsalar tana iya faruwa ace ni ce''

Nace."Haba Hauwwa wace irin magana ce wannan me zai faru da har sunanki zai fito dan Allah kizo babu damuwa Aunty Murja tana da saukin kai.

Tace."To shikkenan idan an tashi zan shigo." nace."Okey to ina sauraranki."

Kashe wayar nayi na ajiyeta kan mirror na futa falon, shuru babu kowa da alama yaran sun tafi makaranta tunda litinin ce. gurin cin abinci na nufa naja kujera na zauna wato dai nice bare a gidan nice wacce bata da mutunci da galihu ban isa a zauna tare dani a ciki abinci ba tabbas badan kada na cutar da kaina da yunwa ba to da babu abinda zai sanya na zauna naci abincin gidan amma babu komai karshen wata na dauki albashina zan sayi komai nawa na dinga ciyar da kaina wannan shawarar na yanke a cikin raina.

To har na gama breakfast din Aunty Murja bata sauko ba sai kawai na yanke shawarar hawa saman na gaisheta.


Na jima a bakin kofar ina knocking kafin naji motsinta ta bude kofar dakin muka had'a ido da juna.

Fuskarta a sake tace."Aa Sa'ida kece ashe shigo mana." Kasa shiga nayi sabida nauyi tana sanye da wani gajeran wando da riga mai kamar breziya da madauri a wuya nonowanta duk a waje bayan ta ma haka.

Na tsaya daga bakin kofar da fadin"Dama naji shuru baki sauko ba nace bari nazo mu gaisa." Murmushi tayi tace."Kin ga ni wallahi tunda nasha maganin mura ya kashe min jiki nake ta bacci mijinki ma ban san lokacin daya fita ba."

Nace."Ayya sannu Allah ya sawa'ke." ta amsa da "ameeen da fad'in " Ki shigo mana." cikin ya'ke nace"Aa aunty zanje nayi ayyuka a dakina ne anjima idan na gama sai nazo muyi hira."

Tace."Tom shikkenan babu damuwa." sallama nayi mata na sauka ina kokarin shiga dakina naji sallama da sauri na juya domin na dauka Hauwwa ce. wata hamsha'kiyar mata ce taci kwalliya har ta gaji kana kallonta kasan naira ta zauna..


Nace"Sannu da zuwa hajiya." ta amsa fuska a sake tana min wani irin kallo kafin tace."Kece amaryar Murja ko.''? nace."Eh nice amma ke d'in 'yar uwarta ce ko dan naga kuna kama."

'Yar dariya tayi tace"Haka mutane suke fada Aa Murja ba 'yar uwata bace ta jini 'Kawata ce dai." Nace."Ayya sannu da zuwa tana sama sai ki hau ki sameta."

Tace."Okey babu damuwa.'' Juyawa nayi domin bude dakina naga ta bini da kallo tana murmushi, al'amarin ya dinga bani mamaki! irin murmushin da Aunt Murja takeyi min matar ma irinsa take........Gefen gado na zauna abun na cigaba daure min kai.

'Karfe biyu shaura Hauwwa ta karaso gidan, bayan mun gaisa ta dinga bina da kallo tana girgiza kanta kafin tace."Sa'ida kwana biyu kacal naga duk kin sanja kin wani hargitse dan Allah me yake damunki.'?


Ajiyar zuciya na sauke nace."Hauwwa matsala mai girma nake fuskata a gidan nan." Zama ta gyara tana kallona, idanuwa na suka ciko da ruwan hawaye na shiga bata labarin abunda ke faruwa.

Kanta kawai take girgizawa kafin tace." *AI GA IRINTA NAN!* Sa'ida babu irin shawarar da ban baki ba akan mutumin nan kika rufe idonki kika aureshi gashinan kwana biyu kacal ya nuna miki akuyanci me ake da auran irinsu Alhaji Nura kayan ba'kin ciki da takaici ai wallahi gwara na auri 'karamin yaro na raine shi nasan komai rintsi ni zan mora amma duba dan Allah kwana biyu da yin aure kin zama tamkar wata zautacciya."

Nace."Hauwwa dan Allah ki bar wannan maganar Alhaji Nura fa lafiyarsa lau tsabar iskanci ne da wulakanci yasa yake min haka tunda ai na fad'a miki hujjarsa ta 'kin sakin jiki dani saboda kada na haihu bayan sun tsara rayuwarsu shi da matarsa."


Tsaki taja tace."Eh ai na fahimta mayaudarin banza da wofi kawai to ke yanzu wace shawara kika yankewa kanki ko kina nufin a haka zaki cigaba da zama da sha'awa."


Nace."Shine ai na kira ki domin ki bani shawara."

Shuru tayi na minti biyu kafin tace." Sa'ida ki rabu da mutumin nan shine alkairi a gare ki ni dai wannan shawarar ita zan baki."


Gabana na wani irin fad'uwa nace."Hauwwa wace irin magana ce wannan? aure kwana biyu ki fadi irin wannan maganar gaskiya bata dace ba ki bani shawarar arziki mana."


Dariya tayi tace."Duk wata shawarar da zan baki bayan wannan take wallahi idan kika cigaba da zama da mutumin nan zuciyarki sai ta buga irinsu suna nan da yawa masu kashe matansu da bakin cikin su."


Shiru nayi ina kallonta tace."Idan kuma kinga ba zaki rabu dashi ba to sai ki dauki tsatstsauran mataki a duk lokacin daya kusance ki sai ki hana shi tunda zalinci baya barin sa ya biya miki bukatar ki."


Nace."To kinga wannan shawarar ita zan duba a cikin shawarwarin ki amma maganar kashe aure sam bata taso ba."


Tace."Tom shikkenan sai ki kwada ki gani mybe idan kikayi masa butsu ta wannan hanyar zai dinga dogon zango a kanki tunda kin ce lafiyarsa lau ba rashin kuzari bane wulakanci ne irin nasa.

Murmushi nayi nace."Hakane Hauwwa Alhaji Nura ragal yake kawai 'keta ce nima kuwa zan gwada masa tawa." Dariya tasa ta bani hannu muka tafa.


Sai da tayi sallah la'asar muka ci abinci sannan tayi shirin tafiya, tare muka fito falo wanda yayi daidai da saukowarsu daga sama.

Nace."Hauwwa ki tsaya ku gaisa da aunt Murja ko." Tace."Okey babu damuwa.

Muna tsaye suka 'karaso dukkaninsu fuskarsu a sake da walwala aunty Murja tace."Ashe kema bakuwa kikayi.''? Nace."Eh wallahi 'kawata ce Hauwwa gurin aikin mu daya."

Tace."Ayya Sannu.'' Hauwa ta amsa da "yawwa aunty ya gida ya yara."? tace."Alhamdulillahi." Hajiya Aziza na murmushi tace."Ai sai muje na rage miki hanya ko."?

Hauwwa tace."Nagoda hajiya amma nima ina da abin hawa.'' Tace."Okey to babu damuwa sai mu fita tare ko." Tace."Eh hakan yayi.'' Ta kalleni da fad'in "Sa'ida sai munyi waya kenan amma yaushe zaki koma gurin aiki."? Nace." Insha Allahu sati na sama." tace."Tom shikkenan Allah ya bamu alkairi." Nace."Ameeen ya Allah nagode k'awata." Aunt Murja tace."Muje mu taka musu." bayansu muka bi kowacce ta shiga motar ta suka fita daga gidan muna daga musu hannu da fatan alkairi.

Tare muka koma gidan ita ta hau sama ni kuma na bude dakina na shiga ina tunanin shawarar da na yanke akan abinda yake faruwa.


To yau ma dai ban san lokacin da ya dawo ba sai da na fito falo na same shi a zaune suna hira da ita ga yaran su suna wasa, tsabar haushi da takaici ya hana ni kulashi ballantana nai masa sannu da zuwa.

Gurin cin abinci na zauna naci na koshi na bar gurin ita kanta aunty Murjan haushinta nake ji sabida na gane itama fuska biyu gareta.

Sai da bacci ya soma daukata ya shigo dakin, na dinga kallonsa ina daga kwance har ya gama shirye shiryen sa yazo ya tsaya a kaina....."Sa'ida wacece tazo d'azu."? tambayar da yayi min kenan....Na mike zaune ina kallonsa ya sake maimaimata maganarsa." Wacece tazo gurin ki d'azu."? Nace."Kai waye ya fad'a maka wata tazo."? a fusace! ya daga min hannu da fad'in "Wace irin magana ce wannan a maimakon ki bani amsar tambayata sai kuma ki tambaye ni..

*SADAUKARWA NE GA IYAYE NA GUDA BIYU*

*FATIMA MUSA (MOMY NIJAR)*


Please Login or Register in order to submit comment