Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nace." Zazza'bi ne ya rufe ni wallahi."

Yace."Sannu ki daure ki tashi ki wanke najasar dake jikin ki ina falo ina jiran ki." Hanyar fita ya kama Idona na bude ina kallonsa yana kokarin bude kofa nace." Kazo ka taimaka min mana kaina yayi min nauyi sosai."

Dawo wa yayi ya mikar dani tsaye ya kalleni da fadin."Ko na d'auke ki ne.''? girgiza kaina nayi kawai nasa hannuna a kafadarsa ya rike ni muka nufi toilet din. sai da ya tabbatar ta fara wankan sannan ya fita daga bandakin.


Koda na fito daga toilet din kayan bacci kawai nasa nasha paracetamol na nemi guri na kwanta bacci mai nauyi ne ya dauke ni.............Can cikin bacci na dinga jin magana da sauri na bude idona yana tsaye a kaina magana yake akan na tashi na bashi abinci.

Takaici kamar ya kashe ni nace."Don Allah yau d'aya kaje ka zuba abincinka da kanka wai kai ba kai wa mutane uziri ne.''?

A hasale yace."Ni kike wa tsawa."!? Na daga masa hannu da fadin." Kaga yanzu dare ne bana bukatar hayaniya bayan haka kuma nace maka bani da lafiya me yasa ba zaka tausaya min ba." Wani irin kallo ya watsa min kafin yaja tsaki mai karfi ya bar gurin. kallon mamaki nake masa har ya fita daga dakin.
Washe gari da safe da rashin karfin jiki na tashi amma dai hakan bai hana ni yin ayyuka na ba yana kwance yana bacci na kammala komai na zauna ina tashinsa.

Ido ya bude da fadin."Malama ki kyaleni na huta bacci nakeji." Daure zuciyata nayi nace."Ba zaka fita ba kenan."? banza yayi min yaja bargo ya rufe jikinsa.

Nace."Jiya Gwaggo tazo ta bani sa'ko gurin ka.'' Kallona yayi da lumassaun idanunsa, nace."Gwaggo tace lallai kaje tana neman ka." Idonsa ya rufe da fadin."Naji sai na tashi a bacci zanje." Ba tare da nace uffan ba na mike... ina kokarin fita kira ya shigo wayarsa. " Zo ki miko min waya ta." Yafad'a ba tare da ya bude idonsa ba, ko kallonsa banyi ba na bude kofa na futa daga dakin.

Ransa ya 'baci sosai da abinda tayi masa ya mike cikin kasala da bacci ya dauki wayar yana dubawa sai yaga Jamila ce. Wayar yasa a kunnansa da sallama ciki-ciki a bakinsa.

"Yaya Khalid kazo baby naso yaji d'umin ka." Jamila ce ke wannan maganar.

Cikin yanayi na me jin bacci yace."Ki bashi hakuri kafin nazo yanzu bacci ne a idona amma daga na tashi zan shigo na gaisa dashi.

Fashewa tayi da kukan shagwaba da fad'in."Ni dai don Allah kazo yanzu muke so mu ganka." Ajiyar zuciya ya sauke yace." To daina kuka gani nan zuwa." Kashe wayar yayi ya lalubi singlet dinsa yasa.....Ina zaune a daining ina karyawa ganin ya kama hanyar fita yasa na bishi da kallo koda ya fita din kasa hakuri nayi sai da naje na daga labulan window ina lekansa nan naga ya nufi Side din Jamila, girgiza kaina kawai nayi na koma na zauna Wato na fad'a masa Gwaggo na nemansa yana masifa amma yanzu gashi matarsa ta kirashi ya tafi Allah ya kyauta.

Ita kuwa Jamila dama da wata manufa ta kirashi koda ya shiga gurin nata rikeshi tayi ta dinga tsokano masa da sha'awa dama me neman kuka ne nan take ya turmushe ta a gado ya shiga biyan bukatarsa ya manta da sharad'in Likitansu.



Sai waje sha d'aya ya shigo ko kallon inda nake zaune beyi ba ya bude dakinsa ya shiga ya kwanta ya cigaba da baccinsa.

Misalin karfe biyu da rabi na rana Uwale tazo gidan cikin girma da mutunci na tar'be ta muka gaisa sosai na bata abinci taci ta koshi nan take sheda min cewa tazo duba jikin Jamila ne da yake kwana biyu taje kauye ziyara sai jiya ta dawo shine data shiga gidan Gwaggo take fada mata shine tace yana da kyau tazo ta dubata tunda an zama d'aya.

Nace."Kwarai kuwa hakan yana da kyau bari na dauko hijabi na raka ki gurin nata.

Lokacin dana shiga dakin yana zaune akan dadduma da alamar sallah yayi ba tare dana kalleshi ba nace."Uwale ce tazo yanzu.'' Kallona yayi fuska a hade yace."Me tazo tayi ."?

Nace."Duba jikin Jamila tazo wai jiya Gwaggo take fada mata shine tazo ta dubata."

Tsaki yaja da fadin." Munafurci ne dai ya kawo ta yanzu zan korata dan ni bana son gulma da had'a husuma a gida."

Mikewa yayi zai fita na tare hanyar da fadin."Wai kai don Allah me yake damunka? me yasa dik wanda zaiyi maka alkairi sai ka mayar masa da sharri ina laifin Uwale don tazo duba matarka."


Ture ni yayi da fad'in." Uwale ba mutuniyar arziki bace shiyasa bana son mu'amularta da Gwaggo yanzu ma na tabbata sharri ne ya kawo ta gidan ba alkairi ba."

Nace."To don Allah kayi hakuri kada ka wulakantata koda ta nufe ka da sharri zai koma kanta kayi hakuri ka kyaleta."

Ba tare da ya sake magana ba ya bude kofar ya fita da sauri nabi bayansa da hijabi a jikina.

Uwale na ganinsa ta washe bakinta da fadin."Au Ashe ma maigidan yana nan Khalidu Jarumin maza na Gwaggo mijin Sa'ida da Jamila."

Duk wannan rawar jikin da take masa bai sa ya saki fuskarsa ba a dakile ya gaisheta ya kama hanyar fita Uwale jikinta yayi sanyi da wulakancin da yayi mata..........Nace."Kiyi hakuri Uwale daga bacci ya tashi shiyasa babu walwala a tare dashi.'' Ya'ke tayi tace."Aifa naga alamun haka to yanzu wannan soyayyiyar gyad'ar dana kawo muku ya zakuyi da ita.

Nace."Bari na d'an d'ibi kad'an sai ki bawa Jamila sauran nasan zata fi ni bukatarta saboda cikin jikinta."

Tace."To shikkenan kema Allah ya baki naki musha suna." murmushi nayi na amsa a cikin zuciyata.



To a takaice dai Khalid bai je kiran da Gwaggo take masa ba sai bayan kwana hudu da zuwanta gidan........Koda yaje gidan Gwaggo kin kallonsa tayi sai da ya rarrasheta sannan ta saurareshi Tace."Khalid ka watsar dani kana nuna min ban isa da kai ba ko? yanzu tun yaushe nake nemanka ba kazo ba sai yau da kayi ra'ayi.

Yace."Gwaggo don Allah kuyi hakuri kuyi min uziri Abubuwa da yawa suka sha kaina itama Ummatu rabona da zuwa inda take kwana hudu kenan.

Tace."Ko ba kaje inda take ba ai kana waya da ita.'' Murmushi yayi yace."Eh hakane kema ai na baki daya daga cikin wayoyina kince bakya so." Tace." Yo ni me zanyi da wannan waya ai wahala zata bani gwara irin wacce ta lalace tafi sauki."

Yace."To insha Allahu kuwa yau zan siya miki in yaso duk sanda banzo ba sai na dinga kiran ki muna gaisawa." Tace."To hakan yayi daidai.

Shuru tayi na minti biyu kafin tace." Khalid me yasa kullum baka bukatar zaman lafiya da iyalinka."?

Cike da mamaki yake kallonta "Gwaggo bangane maganarki ba." Tace." Lokacin da naje duba Jamila hankalina ya tashi da naga Sa'ida cikin halin damuwa duk ta rame ta lalace haba Khalid ya zakayi min haka kuma." Murya na rawa ta karasa maganar.


Jikinsa a sanyaye yace."Gwaggo tace dake inayi mata wani abu ne.''?

Girgiza kanta tayi tace."Aa ba tace ba amma dai tace kullum babu kwanciyar hankali a tsakaninku." Shuru yayi yana dan tunani.....Tace."don Allah idan da wani hali da kake mara kyau ka daina ka zauna lafiya da iyalinka Khalid ka tausayawa 'yar uwarka mana ko baka ganin ramar da tayi."

Yace."Gwaggo ni yanzu ban san abinda zance miki ba nasan ni ina kokari a cikin gidana kuma duk wani abu da zan fito nayi magana a kai mai muhimmanci ne to amma tunda kince haka zan kara kiyayewa.

Tace."To nagode sosai Khalid ina rokon Allah yayi riko da hannuwanka Allah ya baka ikon adalci a gidanka." Ya amsa da ameeeen ya rabbi Gwaggo nagode sosai.


Fuskarsa kadai na kalla na gane akwai damuwa kama kaina nayi ban shiga sabgarsa ba, hakan da nayi sai ya sake tunzura masa zuciya yazo ya tsaya a kaina da fadin." Me nake miki kika kai 'karata gurin Gwaggo shin na hana ki ci ko na hana ki sha a gidana."?

Girgiza kaina nayi a murtuke nace."Babu rashin ci babu rashin sha a gidanka sai dai akwai rashin nutsuwa da kwanciyar hankali.'' Ya kalleni da jajayen idonsa yace." Ko zaki fada min abinda ya janyo miki rashin nutsuwa da kwanciyar hankalin."?

"Wannan kuma kai za'a tambaya namiji shike kawo nutsuwa da zaman lafiya a gidansa idan yaso idan kuma beso ba zai iya kawo akasin haka."


Tsaki yaja da karfi yace."Tun sanda kika fahimci cewa Jamila nada juna biyu kike fushi da b'acin rai shin waye yake bada haihuwa idan ba Allah ba me yasa Zaki sanya kanki a cikin damuwa saboda kawai kishiyarki nada ciki ke baki dashi gashi kin janyo jamaa nayi min wani irin kallo.


Cike da takaici da bacin rai nace." Khalid cikin matarka baya gabana ballanatana na damu dashi haihuwa da rashinta duk Allah ne yake yi saboda haka idan ma tunanin da kake kenan to ka daina domun ni nayi imani da Allah da manzonsa."


Yace."Idan kinyi Imani da Allah da Manzonsa kuma kin dauki Jamila a matsayin 'Yar uwarki me yasa har yanzu baki saki jiki da ita ba? me yasa kullum kike cikin damuwa da 'bacin rai."

Girgiza kaina kawai nayi na mike da niyyar bar masa gurin.....Ya tare ni da gangar jikinsa kallonsa nayi da fadin."Bani hanya na wuce.'' Yace."Wato kin mayar dani mahaukaci kenan." dauke kaina nayi yasa hannu ya juyo da fuskata ina kallonsa......"Kada ki sake zuwa ki kai 'kara ta gurin Tsohuwa bana bukatar 'bacin ranta." fuskata na fuzge da fadin." Dallah malami matsa ka bani guri kullum kana 'kara girma da shekaru amma ka'ki kayi hankali."

Baki ya bud'e yana kallona na buge kirjinsa da ya tare ni dashi bedroom d'ina na bude na shiga na kwanta kan gado bakin cikin duniya ya isheni.
Tunda ranar ya dauke min wuta ya daina kula ni ko shigowa sashen yayi baya shiga sabgata zaiyi abinda ya zaiyi ya fita gabadaya ya tare a gurin Jamila ya ma daina kwana a gurina hakan yayi min dadi sosai dama takura min yake gashi ba cikakkiyar lafiya gare ni ba.

Sati guda da faruwar al'amarin Jamila ta tashi da ciwon mara mai tsananin gaske kafin ma suyi wani yunkuri jini ya yanke mata hankali a tashe suka nufi asibiti suna zuwa cikin ya fita sosai tasha wuya kuma ta zubar da jini mai yawa........Baito ta dinga kuka saboda rashin tawakali sai suka d'orawa Uwale sharri suka ce ai gyad'ar data kawo ce tayi sanadiyar zubar da cikin wai had'a baki sukayi da Gwaggo tunda 'kawarta ce......Shima khalid din da yake bashi da tsinkaye sai ya yarda da maganarsu ya dinga cika yana batsewa da fadin." Sai yayi sharia da ita.......Gwaggo tare da Uwale suka je asibitin domin duba Jamilan Baito da sauran 'ya'yanta suka dinga sakin habaici dan wata mara kunya ma a cikinsu har sai da ta zagi Uwale da fadin." Duk sharrin da suka k'ulla cikin ya zube sai Allah ya tona musu asiri.....Uwale ta dinga share hawaye tana fadin." Ni kuwa me Jamila za tayi min da zan bata guba a cikin gyada." Gwaggo ranta a bace ta kalli Baito da fadin." Wallahi ku dai 'kananun mutane ne marasa tawakalli masu yarda da jita-jita kawai." Baito tace."Asiri dai ya tonu baku da bakin magana."

Rai a 'bace suka bar asibitin.....Bayan sun koma gida da daddare Khalid yaje gidan yana tashin hankali wai wallahi Sai ya daure Uwale tunda ta bawa matarsa gubar da tasa cikinsa ya zube .

Tashin hankali yasa Gwaggo ta fad'i hawan jininta ne ya tashi, hankali a tashe suka nufi asibiti ganin halin da Gwaggon nashi take ciki yasa jikinsa yayi mugun sanyi.

Ni kam in banda share hawaye babu abunda nake masifar yau daban ta gobe daban gashinan garin rashin hakurinsa matsala ta afku gabad'ayanmu hankalinmu bai kwanta ba sai da aka sallami gwaggo daga asibiti.......Kawu ya dinga yi masa fad'a da fadin." Mutukar 'bacin ransa ya kashe masa mahaifiyarsa sai ya hukuntashi. Khalid dai hakuri kawai yake bashi yana fadin." Insha Allahu hakan ba zata sake faruwa ba.


****
Hajiya Aziza a gurin harkar lesbian ta hadu da wata mata mai suna Elizabeth suka kulla abota ashe 'yar mafiya ce bata sani ba ta saki jikinta da ita sosai suke sha'aninsu matar na sakar mata kudi sosai Hajiya Aziza ta dinga cin duniya da tsinke tana jin dadin duniya..........Rana tsaka k'ungiyarsu ta mafiya ta 'bukaci da Elizabeth ta bada mutum dodon tsafinsu na bukata ba tare da tunanin komai ba ta mika musu Hajiya Aziza a daran ranar dodon tsafin ya shanye mata jini tas Aka wayi gari da gawar ta, Elizabeth ta dinga kuka tana kiran Jesus 'Yan uwanta arna suka taimaka mata gurin had'a gawar ba tare da sun sallace ta ba suka sa a akwati sukaje suka binne suna wa'ke-wa'ke.......
*Duniya kenan Allah kasa mu gama lafiya*


****
Aunty Murja bata sare da al'amarin duniya ba sai da ta samu labarin irin mutuwar da Aziza tayi ta dinga kuka tana nadamar rayuwa tunda tsohon mijinta ya mutu ta zama saliha ta kasance kullum cikin addua da nema afuwa gurin Ubangiji babban burinta ta daidaita da 'ya'yanta domin ta gane sune farin cikinta yayin da su kuma yaran suke masifar nadama fitowa ta tsatsonta suna jin bakin ciki a nuna ta a matsayin mahaifiyarsu......
*105* Bayan sati uku Al'amura sun d'anyi sauki Ya rage wulakanci dalilin rashin lafiyar Gwaggo ya sanya kullum burinshi bai wuce mu samu zaman lafiya ba ni kuma a lokacin ne nake jin mugun haushinsa tunda na fahimci ina da ciki shikkenan na tsane shi duk sanda ya kusance ni sai munyi rigima na tsani kamshin turaransa gashi ya'ki ya daina amfani dashi duk da na fada masa cewar bana so amma kamar kara tunzura shi nake......B'angaran sa kuwa shi sam be san tana da ciki ba tunda bata fada masa ba kawai dai yaji gabad'aya ta sauya masa ni'imar ta tafi ta da yana masifar jin dad'inta duk sanda yake gurin Jamila ya dinga bacin rai kenan sai yayi ta neman ta da rigima idan ta biye masa sukayi fad'a sai ta kulle masa kofa wanda dama shi hakan yake so sai kawai ya tafi gurin auntyn nashi ya dameta da fitina Khalid sam baya gajiya da sex kullum kamar kara masa karfi da kuzari ake..............Yau Yini nayi ina bacci sai bayan la'asar na tashi nai wanka da salolina doguwar riga mai hula nasa kai tsaye kicin na nufa domin samawa cikina abinci, daidai cikina nayi tunda bani ke da girki ba a kicin din na zauna naci na rage wanda zanci da daddare, falon na fito na zauna ina duba waya ta text messages dinshi na gani yana tambayata gida wai ya kasa aikata komai sai tunani na. 'Karamin tsaki naja ina mamakinsa tunda mukayi aure bai ta'ba fad'a min kalmar so ba sai yau da alama akwai abinda yake bukata aikuwa yau da rigima kenan domin ba zan lamunci shiga hakkin wani ba......Kafin magariba ya dawo gidan a maimakon ya wuce gurin mai girki sai ganinsa nayi ya shigo ido jawur sai kace wani bugagge. babu fuska nayi masa sannu ya zauna kusa dani yana ya mutse fuskarsa, Jin zuciyata tana tashi yasa na mike da sauri na bar gurin. dakin ya biyo ni rai a bace yace."Wai meya sa kike min hakane." ? Ba tare dana kalleshi ba nace."Bana son warin turaranka." Babu sukuni yace." Wannan ba hujja bace me yasa tunda nake amfani da turarena baki ta'ba gudu na ba sai yanzu." Shuru nayi masa Ya matso jikina da fadin ." Tunda na fita nake tunaninki gabadaya na kasa aikata komai kinzo kin tsaya min a raina." Kallonsa nayi da fad'in." Ina fatan baka mance cewa ba girki na bane.'' Yace." Ina sane auntyna ke kadai nake bukata Wallahi manège kawai nake da Jamila bata gamsar da ni." Nace."Hakanan za kayi hakuri kaje gurinta." hannuna ya rike murya na rawa yace."Ba zata iya ba wallahi kece zaki iya ki taimaka min." Nace." To jeka tambayeta idan ta amince sai kazo." Shuru yayi yana kallona nace." Ko tsoronta kake.'' Murmushin takaici yayi yace." Ni nafi karfin naji tsoron macan dake karkashina kema ba karfi na kikafi ba kawai ina lallaba'ki ne.'' Nace."Okey to kaje kawai." Mikewa yayi ya fita minti biyar da fitarsa naje na kulle kofar palon na shige daki nai kwanciyata.............Jamila tana zauna a falon ta ya shigo dauke kanta tayi tana kumbura fuska shima bai kula ta ba ya bude dakinsa ya shiga ya watsa ruwa ya shirya jikinsa ya fito massalaci ya nufa sai bayan isha'i ya dawo gidan. Gurin cin abinci ya nufa yaga babu komai akai falon ya sameta tana kallo yace."Ke baki abinci bane."? A kumbure tace." Nayi daidai cikina na cinye." Yace."Saboda me."? Cikin tsiwa tace." Saboda bana bukatar kaci kaje gurin matar so ta baka." Ransa a bace yace."Ke zanci ubanki wallahi ni kike d'agawa murya." Sai ta fashe da kuka tana nuna kirjinta take fadin." Yaya Khalid ni kake zagi."? Yace." Ko zaki rama ne."? Tana share hawaye tace."Duk dai wanda ya zagi uban wani nasa ya zaga." Wani bahagon mari ya kwad'a mata yana huci! yace." Tuntuni na gaji da zama dake domin Baki da wani amfani a gurina saboda haka ki tashi ki fitar min a gida bana bukatarki tunda baki da mutunci." Gabanta na faduwa tana kuka take bashi hakuri rufe idonsa yayi yaki sauraranta yace maza ta tashi ta fitar masa daga gida sai ya neme ta. Jamila na kuka wurjajan ta hada kayanta cikin akwati ta yafa mayafi ta nufi gidansu cikin tsananin tashin hankali.......Ajiyar zuciya ya sauke bayan fitar ta ya kulle sashen kai tsaye gurin auntyn nasa ya nufa.
Ya jima a tsaye a kofar falon yana bugu da dai yaga bata da niyyar bude masa kofar sai ya yanke shawarar kiran wayarta nan yaji wayar a kashe takaici kamar ya kashe shi ransa a masifar bace yaje ya lalobo spire key yazo yana kokarin bude kofar falon yafi awa guda kafin ya samu wanda ya bude kofar shiga yayi ya mayar da kofar ya rufe.........Kai tsaye bedroom dinta ya nufa ya tura kofar ya shiga tana kwance tana bacci sadidan, gadon ya haye ya janyota jikinsa ya fara abinda yake muradi....Cikin wani irin yanayi na tureshi daga jikina zaune na mi'ke na kunna bedlamp dakin yayi haske, tsira masa ido nayi ina kallonsa zuciyata na wani irin tashi, jikinsa na kyarma yasa hannu zai janyo ni na janye ina watsa masa harara. a sarqe yace." Kince na tambayi Jamila idan ta amince to na tambaye ta ta amince min da biyan bukatata." Nace." Ban yarda ba." Zaune ya mike da fadin."Kada fa ki sanya na gwada miki karfina ba zakiji dadi ba." Mikewa nayi na shiga toilet nai uziri na na fito na kwanta kan Sofa na barshi zaune a gadon yana bina da kallo! Cikin kunar zuciya ya sauko daga gadon ya isa inda take. "Kina so na mutu ko? ki duba kiga yanda hallitata ta fito." kallon inda yake nuna min nayi na d'auke kaina da fadin." Bari na kira yarinyar a waya naji daga bakinta." da sauri yace."Baki isa ba." Nace." Ai dama nasan karya kake kana satar kwana kana kawo min saboda rashin tsoron Allah.'' " Kada ki sake k'aryata ni." yafadi maganar a kufule. Nace." To idan kana da gaskiya ka bari a kira ta a tambaye ta mana." Tsugunawa yayi a gabana a sanyaye yace." Ko kin kirata ba zata saurareki ba saboda tana cikin fushi." Nace."Khalid wallahi kaji tsoron Allah kana azabtar da iyalinka kana kuma dorawa kanka nauyin zunubi." Ya jima yana kallona kafin yace."Wace irin azaba nake muku? kuna so na kwanta a kasa ku takani kenan.''? Girgiza kaina kawai nayi Yace."To mu bar wannan maganar muyi wacce zata taimaka mana." Nace "Kasan Allah yau kome za kayi ba zaka samu abinda kake so ba bani ma da lafiya ta kaina nake." A marairaice yace."Don Allah ki bari nayi ko Allah zai sanya ki samu ciki wallahi haihuwa nake so." Kallonsa nayi ya wani langwab'e kai sai lumshe idanuwansa yake. " Kayi hakuri ka bari sai girki yazo hannu tukkuna." Wani irin kallo yake min fuskarsa ta rikid'e da bacin rai yace."Saboda kinga ina sonki kike wulakanta ni." ? Kokarin bar masa gurin nake ya rike min hannu "Ba zan kara tunkarar ki da wata bukata ba." cikin zuciyata nace." Dama haka nake so." Hannuna ya saki yaje ya kwanta kan bed komawa nayi kan Kujarar na kwanta ina sauke ajiyar zuciya sosai naji dadin yanda yayi zuciya dama haka nake so ya kyaleni na huta.......Washe gari da safe babu yabo babu fallasa muka gaisa cikin rashin kuzari ya zauna yayi breakfast, yana shiga wanka kira wayarsa dake samar mirror, Ina dubawa naga sunan Ummatu. ajiye wayar nayi yana fitowa na fad'a masa, daukar wayar yayi ya zauna kusa dani..............."Rai a b'ace naji maganarta "Khalid ni zaka tozarta ko? me Jamila tayi maka kace ta fice maka daga gida."? Yace." Ummatu ki kwantar da hankali yanzu zan shigo na sheda miki dukkanin abinda yake faruwa." Tana kuka tace."Aa ai zuwanka bashi da amfani tunda ban isa na baka umarni ka dauka ba kana so ka tozarta ni ko to shikkenan kaje duniya ce." Kafin yace wani abu ta kashe wayarta. Shuru yayi da wayar a hannunsa nace."Me tayi maka da zaka kore ta a gidanka." ? Hannu ya daga min da fadin." Ba abinda ya shafe ki bane." Nace."Ya shafe ni tunda ya shafe ka." Tsaki yaja ya mike ya nufi wardrobe kayansa ya dauko yasa yana d'acin rai Nace."Don Allah duk abinda tayi maka kayi hakuri ka dawo da ita dakinta ina amfanin hakan idan laifi tayi maka bata wannan sigar zaka hukuntata ba tunda kaga 'yar uwarka ce.'' Uffan bece min ba ya kwashi wayoyinsa da key na mota ya bude kofa ya fita ya barni da mamaki...........Baito har kofar Gwaggo ta shiga ta dinga zazzaga masifa Gwaggo tace."Baito ni dik abinda yake faruwa bani da labari amma kuyi hakuri dukkaninmu mu jira zuwansa domin muji laifin da tayi masa. Baito tace."Bayan daukar kwanan da yake yana kaiwa Jikarki duk hakan be isheshi ba sai da ya koreta to wallahi daku da malamin dake muku aiki sai munyi maganinku." Gwaggo tace."Baito kece kika yarda da shirka da surkulle ni Allah kadai na gazgata saboda haka dik abinda zakuyi kuje kuyi." Baito na numfarfashi ta fita daga gurin...Ita kuwa Gwaggo hawaye kawai take sharewa tana jin bakin ciki da takaicin abinda yaron yayi.........Kwata-kwata Ummatu kin sauraran uzirinsa tayi ta rufe shi da fad'a Baito tana taya ta Jamila tazo ta fada musu karya da Gaskiya sun yarda da maganarta sosai al'amarin yayi masa ciwo ya kuma kudiri aniyar sakin yarinyar tunda ta zame masa annoba....Koda ya shiga gurin Gwaggo ma rufe shi tayi da fada tace."Wannan ai shashanci ne saboda kawai kun samu sa'bani da yarinya sai ka koreta wannan ba hukunci bane." Yace."Gwaggo yarinyar

Please Login or Register in order to submit comment