Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kyautawa."

Bude baki nayi zanyi magana sai kuma kuka ya kufce min nasa hannu na gumtse bakina hawaye na shatata! jikinsa na wani irin rawa janyo ni jikinsa sosai ya rik'e ni yana kokarin goge min hawayen fuskata...Gwaggo tace."Khalid sakar mata jiki kada kasa mu shiga fushin ubangiji kayi maza!maza ka sakar mata jiki."
Da karfi take maganar tana kokarin mikewa tsaye!
Kasa'ke yayi yana kallonta hakan ya bani damar mi'kewa daga kusa dashi naje na samu wani gurin na zauna ina goge fuskata.

Yace."Gwaggo wace irin magana ce wannan."?

Girgiza kanta ta shiga yi tace."Khalid da naso ka zauna kaci abinci ka samu nutsuwa in yaso sai na zaunar da kai na fada maka abinda yake faruwa amma yanzu tunda hakan be samu ba dole na fada maka halin da ake ciki.....A yanzu dai Sa'ida tana da aure kuma ba kowa take aure ba face Alhaji Nura wannan dalilin yasa kaga hankalina ya tashi a lokacin daka ri'keta a jikinka."


Wani irin jiri ya dinga yi a zaune kansa ya dinga juyawa gabadaya ya nemi yawu ya rasa a bakinsa auntynsa tana da aure amma ta yaudare shi a waya tace ya dawo gida zata aureshi shin meye manufarta nayin wasa da hankalinsa.

Mi'kewa tsaye yayi jikinsa na wani irin rawa ya dumfari inda take zaune!.....tsorata nayi da ganin yanda ya tunkaro ni na mi'ke da saurin gaske Gwaggo na kokarin tare masa hanya da sauri ya kauce mata wuyana ya sha'ko ya had'a ni da bango (garu) ya matse ni sosai! ido jajawur! yace."Ni zaki yaudara ko."? Gwaggo hankalinta a tashe tazo tana kokarin janyeshi tana fadin."Haba Jarumi ka sassautawa zuciyarka mana." hannu ya daga mata a fusace! yace."Gwaggo ki 'kyaleni na kashe wannan mara imanin gwara na aika da ita barzahu tun kafin ta aika dani." Yana gama maganarsa ya sake matse wuya na da jikin bangon."

Gwaggo ta fashe da kuka hankali a tashe! ta fita daga dakin............Khalid dai da gaske so yake ya kasheni dan yanda ya matse min wuya gabadaya ya hana ni fitar da numfashi, sai kawai na rintse idanuwana zafafan hawaye suka shiga kwaranyo wa a saman fuskata.

*49&50*
Hawayen dake sharara a saman fuskata bai sanya shi ya sassauta matsar da yayi wa wuyana ba, yana wani irin huci da zufa! yace."Ni zaki yi wa haka ko? me yasa kin san an daura miki aure da wani zaki yaudare ni! kin mayar dani shakatafe sabida kina ganin ina sonki ko to wallahi ki rubuta ki ajiye sai na hana ki jin dadin rayuwa yanda kika hautsina min lissafi kema sai na hautsina naki sai na hana ki zaman aure da kowane mahaluki." Yana maganar yana matse ni a jikin bango had'e da bubbuga kaina yanda jikinsa yake rawa sai ka dauka tsumin 'yan bori yasha hannu nasa akan nasa ina k'okarin cire hannunsa ya sake shaqe ni da kyar nace."Kashe ni kake so kayi ko."?

Ido jawur! yace."Meye amfanin mayaudariya kashe ki zanyi dan baki da wani amfani." ya 'karasa maganar yana sake ma'kure ni a jikin bango(Garu) Gwaggo da Ummatu suka shigo dakin hankalinsu a tashe.

Ganin yanda nayi wujiga-wujiga a hannunsa ya tsorata su Ummatu tazo tana janyeshi had'e da bashi baki ya sake ni! kansa ya sunkuyar k'asa tare da sassauta matsar da yayi min amma bai sake ni gabadaya ba.


Gwaggo tazo ta rike hannunsa a sanyaye tace."Haba Jarumi ka zama mai hakuri da yarda da kaddara mana me yasa zaka aikata haka ka duba kaga yanda duk ka galabaitar da ita kayi hakuri ka saketa komai kaga yana faruwa to dama can haka Allah ya shirya."


Ya kalleta da jajayen idanunsa yace."Gwaggo wato har dake za'a hada baki a yaudare ni ko? me yasa kin san tayi aure baki fada min ba bayan kullum muna waya dake."


Kallona tayi tana so tayi magana sai ta kasa nace."Me yasa zakiyi shuru Gwaggo ki fada masa cewa nice na tsara haka in yaso sai ya dauko wuka ya soka min a ma'koshi."
Raina a 'bace nake magana.

Matse wuya na ya sakeyi ya tsira min rikitattun idanunsa, da 'kyar nace."Khalid ka kashe ni mana mai ka tsaya jira ne." Shuru yayi bai ce komai ba ya dai zuba min idanunsa da nake hango ruwan hawaye a cikinsu.

Ummatu tazo ta cire hannunsa daga wuyana ai banyi wata-wata ba na fitar da hannu a zafafe zan kai masa mari!

Hannun ya rike ya murd'e da mugun karfi na saki ihu! ya yarfar min da hannuna yana huci! ya matsa daga gurin.

Tsugunawa nayi a gurin hawaye masu zafi na zubo min hannuna kawai nake dubawa kamar wacce tayi targade sabida zafi.

Gabad'ayansu kansa suka rufu suna bashi baki babu wacce tabi ta kaina. raina ya 'baci sosai na kalli gefe na kwalbar cocar colar da Gwaggo kesa maganin sauro a kai na dauka a fusace na kai masa jifa da ita. cikin zafin nama ya kauce yana kallona.

Murya na rawa nace."Wallahi sai kasan wanda kayi wa wannan iskanci Khalid sai na fad'awa Kawu yayi min tsakani da kai shashasha mara hankali kawai."

Gwaggo a fusace! tace."Wato ba zaki daina zaginsa ba ko.''

Nima a fusace! Nace." Gwaggo abinda yafi zagi zanyi masa mutukar bai fita daga dakin nan ba."

Tace." ba zai fita ba din sai dai ke ki fita dama ai rashin hakurin ki ne yasa mijin naki ya koro ki gida.""

Cikin takaici da mugun bakin ciki nace."Haka zaki ce ko."? Da sauri tace."Eh mana ai gaskiya ce ya za'ayi ki yaudari yaro bayan kin san ba auransa za kiyi ba shiyasa lokacin da kika zo da maganar hankalina bai kwanta da ita ba saboda nasan halin Khalid da zafin zuciya.

Nace."A lokacin da nazo da maganar gabad'ayan ku kuna neman hanyar da zaku bi kuga ya dawo gida kun rasa me yasa dana kawo shawarar hakan kuka amince sai yanzu kuma ki goya masa baya to bari kaji da kai da Gwaggo a yanzu koda aurena zai mutu ba zan aureka ba kaje can ka nemi daidai da kai." na 'karashe maganar idona a tsaye a kansa.

Gwaggo tace."To dama me zaiyi dake kuma ai shi sabuwar budurwa zai aura mai jini ajika.

Kallonta nayi zuciyata na ingiza ni akan na tashi na hada kayana na bar gidan wata zuciyar tace ki zauna dai har Kawu ya dawo ya yanke hukunci.

Ummatu tace."Ke Sa'ida magana ta mutu dan kyautawa baki kyauta ba kai kuma Khalid ka shiga hankalinka ka gane samu da rashi duk na Allah ne.

Yace."Ummatu wallahi hakkina ba zai bar wannan mayaudariyar ba ta cuce ni."

Nace."Kai har kana da bakin wata magana akaina ko.''? Gwaggo da sauri tace."Magana dai a barta ni bana son wani tashin tashina."

Girgixa kaina nayi cikin tsantsar takaici na kalleshi nace."Hakki ko."?

Kallona yake babu kiftawa nace."To ina rokon Allah ya gaggauta bi maka hakkinka a kaina idan kuma ni nake da hakki Allah ya gaggauta bi min akanka.''

Ina k'are magana ta na fita tsakar gida na zauna dandaryar 'kasa tunanin mafita kawai nake.


Gwaggo da Ummatu da 'kyar suka rarrasheshi ya tsakuri abinci kadan yace ya koshi! mikewa yayi ya fita ya barsu a dakin suna tattaunawa.


Bayansa nabi da kallo a lokacin da yake kokarin fita daga gidan, daidai bakin kofa ya yanke jiki ya fadi.

Gabana yayi wani irin fad'uwa! "Gwaggo." da karfi na kwala mata kira."

Tare suka fito ita da Ummatu na nuna musu inda yake kwance tamkar mara rai.

Gwaggo salati ta rafka hankali a tashe ta kamfato ruwa ta kuza masa a jikinsa, tsayuwa sukayi kansa suna kuka Gwaggo fadi take "Sa'ida kinga masifar da kika janyo mana ko zaki kasheshi ki huta ai.

Daki na shiga na dauko waya ta hannuna sai rawa yake na marasa wanda zan kira a wayar.

Ummatu ta tsuguna kusa dashi tana masa firfita hade da kiran sunansa.

Idonsa ya bude a jigace yake kokarin tashi zaune kansa na wani irin sarawa hakika al'amarin yayi masifar firgitashi da sashi cikin tashin hankali .

Gwaggo hannunsa ta rike sai sannu take masa tana yi masa firfita da mahuci.

Kawu ne ya shigo gidan hannunsa rike da ledoji ganinsu sun masa rumfa da mafici a hannu yasa ya tsaya yana tambayar abinda ke faruwa.

Gwaggo hawaye ta share tace."Faduwa yayi ya suma bayan ya samu labarin auran Sa'ida yanzu yanzu ya farfado.

Kawu bece komai ba ya tsallakesu ya shige ciki

Kallona yayi cikin kulawa nace."Kawu Sannu da zuwa." yana sake nazari na yace."Sa'ida kiyi hakuri da rayuwa kinji ko." hawaye suka zubo min hannu nasa na goge nace."To Kawu insha Allah. Har yayi nufin wuce wa gurinsu sai ya tsaya da fad'in "Har yanzu dai Alhaji Nura beyi magana ba ni kuma bana so na tunkareshi da maganar sabida kada yaga kamar wani abu dole dai zamu cigaba da sauraransa daga nan zuwa gobe idan beyi magana ba to zan samu Alhaji Shamsu da maganar muji hukuncin da zai yanke.

A raunane nace." To shikkenan Kawu."

Gurinsu ya shige ba tare daya waiwayi su Gwaggo ba haushin Khalid din ya shafe su ya lura wani lokacin mahaifiyar tasa ce take d'aurewa yaron gindi yake iskancin da yake so.



Nima mi'kewa nayi na shiga daki na bar su a gurfane a gabansa suna rarrashinsa mussaman Gwaggo da duk ta fita daga hayyacinta, shima abinda ya gani kenan yasa ya sassautawa zuciyarsa ya daure ya mike tsaye, Gwaggo tace ka shiga dakinka ka kwanta ka huta kaji ko Khalid dan Allah dan Annabi ka cire Sa'ida daga cikin ranka idan ka mutu mune mukayi asara ba wani ba.

Kansa kawai ya daga mata ya bar gurin kallo suka bishi dashi suna jimanta abinda ya faru.


To sai da na bari Kawu ya ci abinci ya nutsu tukkuna na shiga gurin na same shi a kashingid'e akan dadduma yana hutawa.


Gaishe shi na sakeyi ya amsa cike da kulawa da fadin "Sa'ida akwai magana a tare dake ko."?

Nace." Eh Kawu nazo ne akan inaso kayi min tsakani da Khalid ya fita daga harkata tunda dai ni ba sa'arsa bace Kawu wai kamar ni Khalid zai shaqewa ma'kogwaro kuma su Gwaggo suna gani sun kasa daukar mataki."


Kawu Iro ya mike zaune ransa a bace yace."Wato Khalid din daga zuwan sa da abinda ya fara kenan me kikayi masa da zaiyi yun'kurin kasheki.

Hawaye na share nace."Sabida kawai anyi masa dubara akan idan ya dawo gida za'a daura mana aure shi ne daya samu labarin aurena da Alhaji Nura ya yanke min wannan hukuncin."


Kawu na kokarin yayi magana ya fito daga dakinsa, a kaina ya tsaya kamar zai mangare ni yace."Ni yaro ne da zakiyi mun dubara mai yasa baki fada min gaskiya ba kika yaudare ni shin kin san halin da nake ciki a yanzu."?


Kawu ya buga masa tsawa da fad'in "Yanzu daka tsaya a kanta dukan ta za kayi kome."?

Sunkuyar da kansa yayi ya nemi gefe ya tsuguna yana watsa min harara! al'amarin ya dinga bani mamaki da tsoro yanzu gabad'aya tsoronsa nake ji sabida dazu nayi masifar galabaita a hannunsa.


Kawu ya kalleshi rai a 'bace murya a kausashe yace." Khalid wallahi ka fita daga idona na rufe kabar ganin duk abinda kayi Gwaggo tana daure maka gindi wallahi ka guji fushi na wato har ka manta laifinka ko ka dawo zaka yi rashin mutunci da rashin arziki ko? Yanzu Sa'ida sa'arka ce da zaka dinga dukan ta."?


Yace."Kawu ka gafarce ni dan Allah ni wallahi 'karya take min ban doke taba."

Kallonsa nayi ina mamakin maganarsa wai yau yaron dana sharewa majina shine yake 'karyata ni."


Kawu ya cigaba da cewa." Kayi yun'kurin kasheta ta hanyar matse mata ma'kogwaro kana nufin idan ka kasheta za'a saurara maka."? shuru yayi Kawun ya cigaba da cewa''Yarinya tace bata sonka bata sonka amma saboda naci ka nace sai ta aureka waye ya fada maka a nai wa so dole ne."?

Khalid ya dinga jin wani maqaqin bakin ciki a cikin ranshi! Kawu Iro ya cigaba da watsa masa 'bakar magana iya yanda ransa yake so tas yayi masa wankin babban bargo dama haushinsa yake ji! Khalid ya rasa inda zai sanya kasa sabida bakin ciki da takaici babu shakka da yasan wannan bakin cikin zai zo ya tarar to da yayi zamansa a inda yake.


Kawu Iro ya cigaba da cewa"To wannan ce maganata da kai ta 'karshe Khalid nayi maka tsakani da Sa'ida babu kai babu ita babu kuma maganar so Sa'ida ta girme maka a yanzu tunda tanada aure sabida haka kada na 'kara jin ka furta mata kalmar so gaisuwar mutunci ce a tsakaninku.
Kaji ko ba kaji ba.?
Cikin Jin mugun ciwon kai yace." Naji Kawu." Ya kalleni da fad'in "Ki tashi kije ki kwanta ki huta insha Allah itama Gwaggon gobe zan zauna da ita akan wannan matsalar.'' Cikin jin dadin abinda yayi wa Khalid din nayi masa sallama na tafi zuciyata fes nasan tunda mahaifinsa yaja masa kunne dole ya fita daga harkata.

.🥰🤝🏻💜_*
*51&52*
Ko dana koma d'akin Gwaggo 'kin sakar mata fuska nayi duk wani abu dana san zanyi a dakin nayi na fito nayi shimfida a tsakar gida nayi kwanciyata itama uffan ba tace dani ba, tsakanin ni da ita ban san waye yafi jin haushin wani ba.

Ummatu kuwa itama da bakin ciki ta kwana dan bayan fita ta daga gurin Kawu Iro kiranta yayi itama ya 'kare mata tanadi yace kuma ta jawa Khalid kunne ya shiga hankalinsa idan kuma yasan neman fitina ne ya dawo dashi to sawun sa a likkafa ya koma inda ya fito baya bukatarsa a cikin gidansa....Ummatu taci kukanta ta koshi ba tare da tace masa komai ba ta bar gurin tare da kudirin wani abu ranta.

Khalid yana kwance a d'aki! yaji duk irin cin mutuncin da Kawun kewa mahaifiyarsa ransa ya sake 'baci ya sake 'kullatar Auntyn nasa yana tunanin irin hukuncin da zai yanke mata.

Da zazzafan zazza'bi da ciwon kai ya kwana dan haka yana dawowa daga sallah ya shiga dakinsa ya kulle k'ofa ya kwanta ba tare da yayi tunanin zuwa ya duba Gwaggo mutuniyar tasa ba.

Cikin baccin daya soma fizgarsa ya dinga jin bugu ana kiran sunansa.

Mikewa yayi yaje ya bude kofar dakin, Ummatu ce ya bata hanya ta shiga dakin ta mayar da kofar ta rufe.

Gefan katifarsa ya zauna yana gaisheta ta amsa tana kokarin ajiye fulas din shayin dake hannunta.

Tace."Khalid ina fata jiya duk kaji irin cin mutumcin da mahaifinka yayi min ko."?

A sanyaye yace."Eh Umma naji kiyi hakuri dan Allah kin san halin baba be iya 'bacin rai ba."

Girgixa kanta tayi cikin takaici tace." Ba haka bane Khalid dama haka halin mahaifinka yake wani lokacin idan yayi ra'ayi haka zai zauna yaci mutuncina iya yanda ransa yake so akan wannan yarinyar Sa'ida babu abinda ba zai iya aikatawa ba."


Yace."Ummatu kiyi hakuri ki saba da halinsa idan kuma nine nake janyo muku sa'bani insha Allahu zan koma inda na fito kamar yanda naji yana fada jiya.

Tace."Khalid idan kai ka cika dan halak ne to dan Allah ka rabu da Sa'ida bafa ita kadai ce 'ya mace a duniya ba shin wai me ka hango a tattare da ita kake kulafunci.


Kansa ya sunkuyar kasa ta cigaba da cewa" A matsayina na mahaifiyarka nake umartarka a karo na biyu ka fita daga sabgar Sa'ida idan kana so kayi albarka a rayuwarka."


Ajiyar zuciya ya sauke ya kalleta a raunane yace."Umma ki taya ni addua akan abinda ke damuna a zuciyata insha Allahu zanyi kokarin ganin na cire aunt Sa'ida daga rayuwata."


Tace."To shikkenan Khalid zan cigaba dayi maka addua sannan inaso ka auri Jamila 'yar 'kanina Garba."

Ya kalleta cikin wani irin yanayi yace."Ummatu ki ajiye maganar Jamila a gefe guda ni bana ra'ayinta.

Tace."Khalid tuntuni fa na fahimci cewa baka kaunar dangi na kafi kaunar dangin mahaifinka yanzu meye aibun Jamila kasan dai tafi Sa'ida kyau ko gata yarinya daidai da kai."


Yace."Umma kin san shi so babu ruwan sa da wani kyau ko muni duk kyawun Jamila bata burge ni ba kuma bana jin sonta ko kadan a cikin raina.


Tace."Ni dai umarni nake baka ba za'bi ba saboda haka idan kana so kayi albarka to kabi umarnina."


Ya jima kansa a kasa kafin yace."Shikkenan Umma zanyi miki biyayya akan abinda kike so." murmushin jin dadi tayi tace."Insha Allahu kuwa zakayi alfahari da auran Jamila.

Shuru yayi bai ce mata komai ba tace."Ga ruwan shayi nan a fulas bari na kawo maka awara da sauran kayan shayin."

Yace."Nagode Ummana." fita tayi daga dakin ranta fari sol babu shakka za tayi farin ciki idan al'amarin nan ya tabbata.
3qutar ne a jikinsa sai kawai ya sanya k'aramar
T-shirt a jikinsa ya fito daga dakin nasa a daidai lokacin da Kawu ya fito daga nasa d'akin da shirin tafiya kasuwa.

'Dan risinawa yayi yace.''Kawu barka da asubah." Ba tare da ya kalleshi ba ya amsa da "Barka dai." ya d'aga labulan d'akin Ummatu yana mata magana. ganin haka yasa da sauri ya fita daga gurun.

Gwaggo na kokarin fitowa daga d'akin ya shiga tace."Ai dama yanzu nake maganarka ina cewa ko da kaina zan shiga gurin naku na dubaka naga baka shigo mun gaisa ba."

D'akin ya shiga babu walwala a tare dashi yace." Na d'an yi bacci ne."

Tace."Koda naji nima nace ko bacci kakeyi to zauna ga guri mu gaisa a nutse." gefanta take karkad'e masa tana marmatsar da abubuwa sai kace barasake ne zai zauna a gurun.

Hankalinsa akanta tana bacci a gadon ba tare da tasan ya shigo dakin ba....Gwaggo ta lura da irin kallon 'kurrular da yake mata sai duk jikinta yayi sanyi itakam wannan jaraba ta isheta wai shin wane irin so yaron nan yake wa Sa'ida.


Labari take bashi wai dan duk ta dauke masa hankali jinta kawai yake amma gabadaya hankalinsa da tunaninsa baya kanta yana can tunani akan Sa'ida duk da yasan ya ga mai mata illah amma yana bala'in kishin Alhaji Nura akanta shi kad'ai yake so ya cigaba da dabdala a wannan ramin amma wani katon banza ya shigar masa gona.


Gwaggo haushi ya bata ganin ya'ki barin abinda yake tace.''Ni kam banta'ba ganin mara zuciya irinka ba."

Sumar kansa ya shafa babu sukuni yace."Me nayi miki kuma."? Tsaki taja tace."Tunda ka shigo kake kallon Sa'ida alhalin bacci take yi ko gaisawa ba muyi ba hankalinka gabadaya yana kanta to ka dai kiyaye kada ka jefa kanta a matsala domin naga idanuwanka sunyi ja."

Murmushi yayi yana kallonta yace."Waye yace miki ita nake kallo."? Tace."Ai makauniya ce ni." Dariya yasa yana sosa kansa tace."Ka karya kummalo."?

Girgiza kansa yayi tace."To bari na zuba maka abinci." Yace."Gwaggo ba zanci abinci da safe ba ki bani ruwan shayi." Tace."Aa Ni yau kunu nasha ruwan shayi ka tambayi mahaifiyarka."

Yace." Okey na manta ma da akwai a fulas a dakina idan nasha zanzo naci abincin." Tace."To shikkenan.

D'akin ne yayi shuru na minti biyu ya cigaba da satar kallon Sa'ida ta 'kasan ido Gwaggon ta kalleshi tana girgiza kanta Hankali tace."Kasan abinda yake faruwa ko.''?

Girgiza kansa yayi yana d'an ya mutsa fuskarsa yace."Sai kin fad'a."


Juyawa tayi ta d'an kalli inda take kwance ta dawo da hankalinta kansa 'kasa-'kasa tace."Ai *GA IRINTA NAN!* ta guje ka ta auri wanda take so gashinan tana fuskantar matsala a gurinsa da matarsa ya hanata komawa gurin aiki kuma baya biya mata bukatarta.''

Jim yayi yana kallonta kafin yace."Gwaggo ban gane baya biya mata bukata ba."?

Waiwaya wa tayi ta sake kallon inda take kwance tayi 'kasa da murya tace."Bukatarta ta gurin auratayya mana wai baya son haihuwa shine yake inzali a waje ma'ana yana zubar da 'kwayoyin haihuwarsa."

Cike da mamaki yake kallonta! tana so ta 'kara tabbatar masa da maganar na tashi zaune duk sai suka diririce mussaman Gwaggo da gabadaya yanayin ta ya nuna na marasa gaskiya.

Yi nayi tamkar ban fahimci abinda suke ba na mike na fita, brush nayi na dawo d'akin na tarar dasu suna wata hirar.


Ta kalleni da fad'in '"Ga kayan karin kummalo nan." Ba tare da nace mata komai ba na hau bud'e kwanukan...........dakin yayi shuru na minti biyu kafin naji sautin muryarsa da fadin" Kin tashi lafiya."?

Kaina a kasa na amsa da lafiya lau." Gwaggo tace."Kina bacci dazu da safe aka kira wayarki kin san ni ban iya dauka ba shiyasa na barta ta katse."

Hannu na mika na dauki wayar ina dubawa Alhaji Nura ne sai naji wani sanyi a cikin raina text d'inshi na gani da sauri na shiga ina dubawa......Hakuri yake bani akan abinda ya faru wai nayi hakuri insha Allahu hakan ba zata sake faruwa ba kuma idan anjima zai zo ya daukeni.

Zuciyata tayi sanyi kad'an amma dai duk da haka idan na koma sai na nuna masa 'bacin raina.


A nutse nace."Gwaggo Alhaji Nura ne yake baku hakuri akan abinda ya faru yace insha Allahu hakan ba zata sake faruwa ba kuma anjima da daddare zai zo mu tafi."

Ta'be bakinta tayi tace."Ai sai ki zuba ruwa a 'kasa kisha saboda murna."


Kallonta nayi ta gyda min kai da fad'in "Eh mana ai kinga kuka da damuwa ya 'kare zaki koma d'akin ki tunda anan akan qaya kike."

Takaici ya hanani ce mata komai kawai na d'auki kofin kunu na fara kur'ba ina duba wayata.


Katsaham! naji maganarsa a kunnena" Aunty Sa'ida idan kin koma gidan mutumin nan waye zai dauke miki bukatunki na yau da kullum.

Babu walwala a tare dani nake kallonsa, shima ya 'bata rai da fad'in ''Kin kawo 'kararsa akan baya biya miki bukatarki ta aure sannan baya so ya haihu dake amma sabida rashin sanin ciwon kai zaki koma gidanshi meye amfanin zama dashi a haka kodai kwad'ayin kud'insa kike."?


Na dinga jin wani irin gumi mai zafi na tsatstsafo min a jikina shin ko dama maganar da sukeyi kenan a lokacin da na tashi na ga sun nuna alamun rashin gaskiya! "Yanzu Gwaggo meye amfanin yin wannan maganar da Khalid? me ya shafe shi a ciki da har zaki zauna kina fada masa halin da nake ciki a gidan aurena."


Shuru tayi bata tanka min ba, naji wasu hawaye masu zafi suna kokarin zubo min na kalleshi raina a 'bace nace."Wato dai ba kaji gargadin da mahaifinka yayi maka ba ko."

Cikin rashin tsoro yace."Ai magana ta wuce aunty Sa'ida na rabu dake kije kiyi rayuwar auranki wannan magana kuma da ki kaga nayi miki ba wai da wata manufa nayi miki ba ina jin tausayin halin da zaki shiga anan gaba."

Nace."To ina ruwan ka da dukkanin halin da zan shiga a gidan aurena bana so ka nasa bakin ka akan al'amuran da suka shafe ni ka tsaya a matsayin ka."

ta'be bakinsa yayi yace." To shikkenan aunty Babbah na daina saka bakina akan abinda ya shafe ki tunda bakya bukata."

Nace."Hakan shi zai fi maka alkairi." Shuru dakin yayi kowa yana sabgar gabansa.....Yace."Gwaggo kin san wata yarinya Jamila 'yar Kawu Garba 'kanin Ummatu."

Da sauri tace."Eh kwarai kuwa nasan yarinyar ko ba wata 'yar fara siririya ba."

Yace."Eh ita ce Ummatu take fada wai na nemi auranta."

Gwaggo ta rangwad'a buda tana washe baki da fad'in "Kai Alhamdulillahi amma naji dadin wannan al'amari tabbas wani hanin ga Allah baiwa ne Khalid nima na goyi da bayan ka auri Jamila domin ta cancanta.

Murmushi yayi yace." To shikkenan Gwaggo ku cigaba dayi min addua akan Allah ya tabbatar mana da alkairi.'' ta amsa da ameeeen ya rabbi.
Gabad'aya ji nayi na kasa nutsuwa a gurin jikina yayi bala'in sanyi jin maganar da sukeyi fita nayi na bar musu dakin na zauna baki soro ina dube-dube a wayata gabadaya na rasa

Please Login or Register in order to submit comment