Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ƙasa ƙasa batare daya gani ba, a zuciyarta kuwa cewa tayi "Inbanda Allah yaɗigamin soyayyarka a cikin zuciyata, da mai zai sanyani tsayawa, har ka wulaƙantani "

Ɗago da kansa yayi ya kalleta, cikin muryan dakewa  yace "Ni zan wuce "  

"Haba Yaya Sadeeq maiyasa kakemin hakane wai ? ko minti 30 fa bakayi da zuwa ba, amma kuma kace zaka tafi " taƙare maganar tana kwaɓe fuska tamkar wata ƙaramar yarinya, ko kaɗan kuma hakan baimata kyau ba, domin kuwa shekarunta ya wucewa abun da take ƙoƙarin yi, (wannan saimu nida bestyna jikar Hajiya sweet 19,lol)

Hanu yasanya a cikin aljihunsa yaciro kuɗi, aje mata yayi akan table ɗin dake gabansu, haɗe da tashi tsaye yasoma tafiya,, ganin haka yasa Zabba'u daɗa ɓata fuska, cike da ƙuncin zuciya, tarufa masa baya.

Mai gadi na  buɗe masa gate yafice da motarsa, Zabba'u naganin fitansa, tasaki tsuka cike da takaici, wai ace kamar ita babbar yarinyar da maza suke mararin samunta, amma wai  ita wani ke wulaƙantawa, kwashe kuɗin da ya aje mata akan table tayi haɗe da sakai tayi shigewarta gida...

Zahrah kuwa ba'ita tafarka daga wannan baccin da takeyiba, sai ƙarfe 6 na yamma, lokacin anata ƙiraye ƙirayen sallan magriba, har zuwa lokacin kuma Khausar tananan bata tafi ba,,

Koda ta tashi a baccin, ji tayi gaba ɗaya tayi sakayau da'ita, a cikin kaso ɗari na ƙunci da damuwarta, babu kaso talatin,  Allahu Akbar haƙiƙa karatun Al'Qur'ani warakace ga duk wani damuwar zuciya, harma da ta rayuwa.

Matsowa kusa da'ita Husnah tasakeyi, cike da tausasawa takama duka hannayenta biyu,

"Bazan gajiya da faɗa miki ba Zahrah, yin imani da ƙaddara mai kyau ko marar kyau, shi'ake so ga ko wani musulmin ƙwarai,  kuma Allah baya ɗaurawa bawa abun da bazai iyaba, idan kika ƙara haƙuri ki kaɗau ƙaddaranki, to ina mai tabbatarmiki da zaki samu kyakkyawan sakamako awajen ALLAH, haƙiƙa nasan Zayd ya cutar da rayuwarki, amma Allah bazai barshi ba, da sannu Allah zai saka miki,kimin alƙawari bazaki na yawan kukaba, sannan bazakina yawan damuwa ba, duk da nasan hakan abune mawuyaci, amma idan kika daure zaki iya,  sannan kuma kuka baya maganin damuwa, karatun Al'Qur'ani kaɗai zaki riƙa, insha Allahu damuwarki zata gushe, sannan kuma, kinyi kuskure Zahrah kinbari tarin damuwar da kika shiga, ya hanaki kai kukanki ga Allah, kin manta shine maikowa mai komai, dan Allah Zahrah kimin alƙawarin cewa zaki rage sanya kanki a damuwa, duk sanda wani tunani yake shirin zuwa miki, to ki gaggauta ɗaukan littafi mai tsarki, ki karanta hakan zai sanyamiki nutsuwa !!"  Husnah tayi maganganunta cikin lumana dakuma son sawa ƴar uwarta ƙwarin guiwa,,

"Bansan mai zance miki ba Husnah, amma haƙiƙa kinwuce ƙawa ke ƴar uwace, kuma koda a cikin ƴan uwanma keɗin ta da bance,  namiki alƙawari cewa zan maid komai nawa ga Allah, haƙiƙa rayuwata tana cikin ƙunci da kuma baƙin ciki, amma nasan babu a bunda yagagari Allah, kuma da sannu rayuwata zatayi haske, duk da banda tabbacin hakan !" Hawayene kawai ke tsiyaya daga idanun Zahrah, domin sosai takejin ciwon abun da Zayd yayi mata,  yanzu tayarda cewa dama haka Allah yatsara mata, kuma zata rungumi Ƙaddaranta, har Allah yakawo ma ta mutuwarta,, amma dudduniya bata taɓa jin matsanancin tsana ga kowa ba bayan Zayd,,

Sosai Husnah tabawa Zahrah shawara masu amfani, wanda zasu taimaka wajen cireta a damuwa,, saida akayi sallan Isha kafun driver'n gidan su Husnah yazo ya ɗauketa...

Tiryan tiryan Baffa ya ɗebi ƙafa, har ofishin Alhaji Umar, gaba ɗaya abun da yafaru da Zahrah, Baffa ya kwashe ya faɗa masa, bakaɗan ba hankalin Alhaji Umar ya tashi, domin kuwa shi Zahrah tamkar ƴa yaɗauketa, saboda mahaifinta yayi masa taimako sosai,  cikin faɗa da hargowa Alhaji Umar kecewa zai kai case ɗin koto,  saurin dakatar dashi Baffa yayi, haɗe da yagyara zama,    ban baki  Baffa yashiga yi wa Alhaji Umar, akan cewa kada yakai case ɗin kotu, domin kuwa yaron yafi ƙarfinsu, sannan kuma idan har aka kai case ɗin kotu, tofa sunan Zahrah ne zai sake ɓaci, wanda basusan an ma ta fyaɗe bama zasu sani, sannan kuma zata rasa mijin aure, domin wasu zasuce ba fyaɗe aka mata ba, ita takai kanta, kuma dole su zasukwan a ciki, domin basu da kuɗi, a yanzu yanda rayuwar duniyar nan  take,  mai kuɗi shine sarki,  kuma mai kuɗi shi kaɗaine mutum, haka wasu suka ɗauka, ko shari'a ake mai kuɗi shiyake nasara,,   sosai jikin Alhaji Umar yayi sanyi, domin kuwa tabbas maganganun da Baffa yafaɗa haka yake, kuma yasan duk kuɗinsa bai isa yaja da wanda suka fisa ba, domin shi ɗan ƙaramin mai arziki ne akan wasu...

((Sau dayawa akan cutar damu ƴaƴan talakawa,   amma bamu isa mu kai ƙara ba,  mune da gaskia, amma mu'ake bawa rashin gaskia, maiyasa ? saboda mu bamu da kuɗi, wanda bashi da kuɗi kuma ba mutum bane a wajenku ko?  anacin zarafin ƙananan yara dakuma ƴan mata,  amma ba a iya ɗauka musu mataki, saboda kawai wanda suka aikata abun masu hanu da shuni ne, mukuma an maidamu ko'oho, Allah sarki Allah ka'iyar mana, kabimana haƙƙinmu gaduk wani wanda yazaluncemu Ameen.))

    
        *20/November/2019*

    
       *Voted, comment, and share please... Wattpad @Fatymasardauna*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

       
           *SHU'UMIN NAMIJI !!*

      *Written By*
Phatymerhsardauna

*Dedicated To My Lovely Brother Khabier*

*🌈Kainuwa Writers Association*

{United we stand and succeed; our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}

*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*

            *WATTPAD*
      @fatymasardauna

*( Masha Allah! ina matuƙar tayaki murnan kammala daddaɗan book ɗinki my sweetheart (Ladingo Ummu Fareesa) Allah ya baki ladan dake ciki, yakuma yafe miki kurakuran dakikayi aciki, haƙiƙa kinyi ƙoƙari sosai Sweetheart, kuma littafin HATSABIBIYA RAMLAT ya nishaɗantar, yakuma faɗakar, fatan mu Allah yaƙara miki basira da hazaƙa Ameen, ina miki fatan alkhairi My Sweetheart.)

*Chapter 36 to 37*

  A hankali yake tafiya da motarsa har yakawo ƙofar gidan,  dai dai tsayawur motar tasa, Baffa ya fito daga cikin gida.    

cikin hanzari ya ƙaraso inda motar Dr Sadeeq ɗin ke fake, "A'a likita kaine da yammacin nan haka ?" Baffa yafaɗa fuska cike da annuri,

"Eh wlh nine Baffa, tun safe naso zuwa, to aikine yayimin yawa "  Dr Sadeeq yafaɗa yana mai ƙoƙarin fitowa daga cikin motar tasa.

"To muje nayi maka iso zuwa cikin gidan ko, aikuwa mutumiyar taka tanacan ta kulle kanta a ɗaki, tana karatu "

"Karatu kuma Baffa? badai ta dawo normal ba ?" Dr Sadeeq ya tambayi Baffa cikin sakin fuska, domin har yaɗanji sanyi a cikin zuciyarsa daga jin maganan Baffan,

"Ƙwarai kuwa likita, ai yanzu duk wannan hargowan kukan ta dainashi!" Baffa yafaɗa dai dai sanda suka kawo cikin gidan,

Da fari'a Inna ta tarbi Dr Sadeeq,  haɗe da baje masa tabarma a ɗan madaidaicin tsakar gidan nasu,   shima cike da mutum tawa ya gaida ta.

Bayan sun gama gaisawanne yake tambayar ko Zahrah tana shan magungunanta ?

Take Inna tace yabiyota tayi masa iso zuwa ɗakin Zahrah'n,
Ba musu yabi bayan Inna duk da cewa yasan hakan baidace ba, amma bayida wani zaɓi sai hakan, domin kuwa shima yanason ganinta.

Zaune take akan katifa, yayinda hanunta ke ɗauke da wani ɗan ƙaramin Al'Qur'ani, tana karantawa ƙasa ƙasa,  a hankali taɗago kanta jin muryar Inna abakin ƙofar shigowa ɗakin nata,  

"Shigo mana likita " Inna tafaɗa tana mai wangale ɗan yalolon labulen ɗakin,

Yanashiga cikin ɗakin,  Zahrah tamiƙe zumbur daga zaunen da take, take jikinta yasoma rawa,

Ganin yanda yanayinta ya sauya alokaci ɗaya, yasa Dr Sadeeq tsayawa cak a inda yake, yana mai ƙare ma ta kallo,  kallo ɗaya yayimawa idanunta, yafahimci cewa tayi kuka, take yaji ba daɗi a zuciyarsa.

"Zahrah!" yaƙira sunanta cikin muryar nutsuwa,

Kasa amsa masa tayi saima kau da kanta gefe da tayi tana mai rumtse idanuwanta, domin kuwa sosai Likitan yake mata yanayi da Zaid.

Cikin muryar nutsuwa ya kuma  cewa "Kifito waje inason magana dake"

Yanakai ƙarshen zance'nnasa,  yajuya yafice daga cikin ɗakin.

Tunyanasa ran fitowar Zahrah hardai yacire rai domin kuwa babu alaman zata fito ɗin.

Daga ƙarshe dai kayan marmari da kuma sauran magungunanta da ya taho mata dashi, sai Baffa ya bawa yace a bata, don yafahimci batason damuwa, kuma yafuskanci cewa tana matuƙar tsoronsa, baikuma san dalilin hakanba.

Tanajin ƙaran tafiyar motarsa ta sauƙe nannauyar ajiyar zuciya, hakanan duk sanda ta kallesa takejin faɗuwar gaba, shigowar Inna cikin ɗakin shiyayi sanadiyar katsuwar tunaninta,,

Ƙatuwar ledan da Dr Sadeeq  yakawo, wanda yake cike da kayan marmari Inna ta aje mata haɗe da watsamata harara gami dayin tsuka tafice daga cikin ɗakin, domin yanzu gaba ɗaya tsananin haushin Zahrah'n takeji.

Ko kallon ledan Zahrah batayiba ballantana ta duba miye a ciki, domin itakam yanzu anshata kuma haryanzu bata warke ba, don haka babu wani ɗa Namiji daya isa yasake yaudaranta, babu kuma wani Namiji da zata sake amincewa dashi a iya tsawon rayuwarta, tasan cewa ingancin rayuwarta yariga dayagama ƙarewa, domin kuwa tasan cewa babu wani namiji dazai aureta, bayan yasan cewa Zaid yariga da ya gama keta mata rigan mutumcinta.

New York City

Gudu sosai motar tasa keyi akan  titi tamkar zai tashi sama, yayinda jami'an tsaron dake tsaron titi suke tayi masa magana amma bayako sauraransu,   kai tsaye katafaren gidansa dake cikin New York ɗin ya nufa, tundaga fitowarsa acikin motar zaka gane cewa a matuƙar buge yake  domin kuwa sai haɗa hanya yake gakuma zungureriyar kwalbar giya dake  riƙe a hanunsa,  yana shiga cikin katafaren falonnasa, yafaɗa kan kujera, haɗe da lumshe  idanunsa,
"MY ZAHRAH!!"   yaƙira sunanta cikin wani sweetness voice ɗinsa, sannan kuma cikin yanayi mai nuni da cewa mutum yana cikin shauƙi,, da ƙyar ya iya miƙewa yakai kansa zuwa ɗaki, yanashiga cikin bedroom, kaitsaye ya wuce bathroom saida ya amayar da gaba ɗaya giyan da yasha, kafun yasamu nutsuwa, amma duk da haka mayen giyan bai sake sa ba.

Buɗe drowern sa yayi, haɗe da fiddo wani irin ƙaton hoto wanda gaba ɗayansa aka rufesa da glass ma'ana akayi masa gidan glass, ba hoton kowa bane face hoton kyakkyawar fuskar Zahrah tana murmushinta mai burgewa.

Murmushi yayi haɗe da mannawa hoton kiss, cikin unique voice ɗinsa yace "Inakewarki My Zumata, haƙiƙa keɗin ta da bance, verysoon inanan dawowa gareki, har yanzu sha'awarki bata sakeni ba, banƙoshi dake ba babyna, kikulamin da kanki kinji Sweet Zahrah na!!" yaƙare maganar cike da tsananin shauƙi, domin kuwa wani irin feelings yakeji a ga me da Zahrah'n, yarasa maiyake damunsa akan Zahrah, aƙa'idansa idan yayi sex da mace sau ɗaya, to baya sake waiwayanta harsai idan ita tawaiwayesa, nan ma saiyaga dama ya amsa tayinta, amma yau gashi yana mugun kewar Zahrah saboda yasha zumanta mai daɗin ɗanɗano, haryanzu baisan menene so ba, sha'awa kawai yasani akan haka kuma ya dogara.

Haka Bacci yaɗauki Zaid yanata sambatu irin na mashaya yayinda yake rungume da hoton Zahrah akan ƙirjinsa, yana ji  tamkar Zahrah'nce dakanta ya runguma a ƙirjinsa.

Washe gari bashine yatashiba sai ƙarfe 9 na safe, salati yasoma yi cike da ƙuncin rai,  sam baisan maiyasa yake makara  sallan asuba a kwana biyunnan ba,  ( Nace Saboda Zina bata haɗuwa da ibada )  daƙyar ya'iya tashi yashiga bathroom domin gaba ɗaya jiyake jikinsa na masa ciwo,gashi kuma baida time ɗin da zaiyi gym,   wanka yayi cikin mintuna ƙalilan, fitowa yayi sanye da rigan wanka ajikinsa, agurguje yamurza lotion ajikinsa haɗe da sanya hand dryer ya busar da gashin kansa,   wata baƙar jallabiya yasanya haɗe da nufar inda darduma ke shumfuɗe, yatada kabbaran sallah, ko kunya bayaji.

(Tir da hali irinnaka Zaid, sallah da rana faɗe faɗe Allah yashirya)

Yana idar da sallah, ya buɗe ma'adanan clothes ɗinsa haɗe da zaro wasu riga da wando masu matuƙar kyaun gaske,   koda yasanya kayan sosai suka amshi jikinsa kasancewarsu masu kalar  fari, daga takalmi, belt harzuwa agogon dake ɗaure a hanunsa kalar maroon garesu, haɗaɗɗiyar rigar suit maroon colour yaɗaura akan kayannasa, take yafito a asalin Zaid ɗinsa, wato  Abundance, Increase, Increment, Superabundance, Addition, Excess, Surplus, haƙiƙa Zaid kyakkyawane kuma cikakken namiji da ya isa ɗaukar hankali ko wacce irin mace ce afaɗin duniyar nan, haƙiƙa Zaid yana da kyakkyawar sura irinta cikakkun maza, haka kuma yanada matuƙar burgewa abubuwan da Zaid kedasu  naburgewa suna da tarin yawa, tamkar yanda ma'anar sunansa ke da tarin yawa,  shikansa yasan yayi kyau sosai, babu kuma abunda ke tashi a jikinsa sai tashin ƙamshi mai sanya nutsuwa da kuma sanya shauƙi,

Al'adarsa ce kullum kafun yafita saiya bawa hotonta kyakkyawan sumba (kiss), to yauma hakance takasance domin wannan hoton nata yaɗauko, ya manna mawa kiss, haɗe da maidashi ya aje, kaitsaye yafice daga cikin ɗakin, ko sauraran kayan breakfast ɗin da aka aje masa akan derny table baiyi ba yasakai yafice daga cikin Aljannar duniyar falon nasa,, yana fita yashiga cikin motarsa, kai tsaye yawuce babban hotel ɗin dazasu gudanar da meeting, domin yau sunada gagarumin meeting, zuwa yanzu gaba ɗaya duk an hallara a wajen shikaɗai kawai ake jira, domin shida ma'aikatansa ne zasuyi meeting ɗin.

Nigeria

Yau kimanin sati guda kenan tunda Dr Sadeeq yazo baisake zuwaba, ɓangaren Zahrah kuwa sosai takesamun sauƙi acikin zuciyarta, sakamakon karatun Al'Qur'ani da tariƙe babu dare ba rana, zuwa yanzu ta dangana komai nata ga Allah, tasan ko ba daɗe ko ba jima zai bi mata haƙƙinta.

Zaune take a tsakar gidannasu tazuba uban tagumi, amma a zuciyarta karatu takeyi,  Inna ce kishingiɗe a gefenta, tana koran sauron dasuka addabeta kasancewar dare yasoma rufawa domin kuwa har an idar da sallan magriba,,

Baffane yashigo cikin gidan fuskarsa ɗauke da fari'a, Inna ce kawai ta amsa masa sallaman da yayi, kallon Zahrah yayi haɗe da cewa "tashi ki ɗauko hijabinki likita na jiranki a waje"

Wani irin mummunan faɗuwa gabanta yayi, domin dudduniya a yanzu babu abun da zai ɗaga mata hankali kamar ace wai wani naƙiranta a waje,  sam itakam tagama cire ƙauna da sake zuwa ƙiran wani,  bata ƙaunarma koda sake fita waje ne,

"Wai ba magana nakeyimiki bane Zahrah kin shareni kuma bayan kinajina!" Baffa yafaɗa cikin faɗa faɗa,

Kuka Zahrah tafashe dashi haɗe da ɗago idanunta, ta kalli Baffa cikin muryan kuka tace "Baffa kataimakeni dan Allah, wallahi banso wani abu yasake faruwa da rayuwata !! "

"Ikon Allah, Malam kajita ko zata sake ɓarar mana da daman da muka samu na biyu, saikace akanta aka fara yin fyaɗe!" Inna tafaɗa cikin ɗaga  murya,,

Da gudu Zahrah tajuya ta shige cikin ɗakinta haɗe da faɗawa kan gado tashiga rera kuka mai sauti, itakam batasan yanda zatayi da rayuwarta ba, batasan wasu irin iyaye bane Baffa da Inna, son zuciyarsu tayi yawa, kansu kawai suka sani, anya kuwa zasu rabauta da rahamar Allah ? cutar da maraya abune wanda ba kyau, kuma sunsani amma suke take saninsu, "Ya Allah kataimakeni !" tafaɗa cikin muryar kuka,

"Banni da'ita Salame nida itane, ai inbazata fita ba shi zaishigo cikin gidan " Baffa yaƙare maganar yana mai nufar ƙofar  fita daga gidan.

Dr Sadeeq ne tsaye a jikin motarsa yasha sky blue ɗin shadda sai tashin ƙamshi yake,

Baffa yafito fuska a sake kai tsaye yanufeshi,  "Yauwa likita ka'iso saikuyi maganar acikin gida ko, kasan mutumiyar taka sai a hankali"  Baffa yafaɗa still  washe da baki,  like  namesake ɗina (fatiwasha lol), ba musu Dr Sadeeq yarufa masa baya suka shiga cikin gidan.

Yauma dai a tsakar gidan yazauna duk da cewa babu yawancin haske a tsakar gidan amma akwai hasken farin wata.

"Wai Zahrah bazaki tashi kije bane, nacemiki gashi yashigo har  cikin gida, dan Allah Zahrah kada ki watsamana ƙasa a ido,  kidubi girman mutumcin dayayi miki sanda kike ciwon hauka kitashi kije " Inna tafaɗa cikin lallami.

"Ciwon Hauka kuma Inna?" Zahrah ta tambaya cike da mamaki domin dai ita a saninta batayi wani ciwon hauka ba,

"Ƙwarai kuwa kedai tashi kije kawai" Inna ta faɗa still cikin lallami,  bawai don tasoba haka tasanya hijab haɗe da ficewa daga cikin ɗakin.

Tun fitowarta a cikin ɗakinnata ya kafeta da idanunsa, har taƙaraso  can gefe dashi ta zauna, haɗe da takurewa waje ɗaya tana matsan ƙwalla,

"Saiyaushe zaki daina kuka ne?" Dr Sadeeq yatambaya cikin tattausar murya, 

Shiru tayi bata amsa masa ba domin jin kalamansa take tamkar zuban narkakken dalma acikin kunnuwanta,

"Matsowa yayi gaf da ita, har tana iya jiyo ƙamshin turarensa, babu wani tsoro kokuma ɗar ya sanya hannayensa akan kumatunta yashiga share ma ta hawaye,  sosai jikinta yaɗauki rawa domin tayi matuƙar tsorata da hakan,   

"Banason kukanki Zahrah, nasani dole kina buƙatar ayi miki uzuri, kinajin ciwo da damuwa a cikin ranki, kuma kinada buƙatar kyakkyawan kulawa,  kidaina min kallon wani bare kokuma na daban, kiyi mini kallon ɗan uwanki, wanda zaki iya gayawa damuwarki,  inaso kifaɗamin duka damuwarki kinji ƙanwata, nasan zakiji sanyi idan kika faɗi ko kaɗanne daga cikin damuwarki !!" Dr Sadeeq yayi maganar cikin lallashi dakuma tausasawa,

Kuka takuma sanyawa mai sauti, domin kuwa tabbas abun daya faɗa ɗin hakanne, tana buƙatar mai kulawa da'ita, tana buƙatar ɗan uwa mai ɗaukar damuwarta,  saurin ɗago da kanta tayi ta kallesa, sakamakon jin hannayensa da tayi akan nata, 
Kai ya jinjina mata batare da yace da ita komaiba,   yana kallonta tayi kuka harta ƙoshi, a hankali take sauƙe ajiyar zuciya,  kofin ruwan dake gefensa ya ɗauka, haɗe da kawai bakinta, babu musu taɓuɗe baki ta soma sha, domin kuwa yanda zuciyarta ta bushe tana buƙatar ruwan,, saida tasha fiye da rabi kafun ta tsagaita da shan ruwan, sosai taji zuciyarta tasoma dawowa daidai nutsuwarta kuma yasoma sauƙa,,

"Yaushe zaki koma makaranta ?" Yajefomata tambayar kansa tsaye,  kallon mamaki tabisa dashi, domin kuwa ko a wasan mafarki bata sake kawo sake zuwa makaranta acikin zuciyarta ba, itakam ai duk wani farinciki yawuce mata,

"Kada ki yarda da abun da zuciyarki takecewa,  ba'akanki aka faraba, haƙiƙa abune mai ciwo amma idan kika daure zuciyarki, zaki iyayin rayuwar farinciki kamar kowa" Dr Sadeeq yafaɗa cike da son ƙarafafa mata guiwa, 

"Kada kayi ƙoƙarin yaudarana domin kuwa sam banda wani sauran farinciki, yaruguzamin duk wani burina,  to yanzu inaso kasanar dani shin menene amfanin karatuna bayan zuciyata cike take da ƙunci? kuma miye amfanin farincikina bayan rayuwata ke waye take da duhu ?, zanfaɗama damuwata domin nayarda dakai, inajin ciwo mai zafi a zuciyata bankuma san ranan warkewarsa ba,  shin maiyasa zaka ce nayi farinciki bayan kasan cewa bazantaɓa samuba ?" 

Ɗan gajeren murmushi yayi haɗe da matse hannayenta gam acikin nasa, "Saboda inada yaƙinin baki farinciki mai ɗorewa, amma saikin daina sakanki a damuwa "

Wani irin kallo tawatsa masa wanda yake nuni da cewa tana buƙatar ƙarin haske akan maganganun nasa.

"Zahrah ke yarinyace mai ɗauke da tarin ƙuruciya, kinaga yadace kibar rayuwarki tatafi a haka ?"

Dr Sadeeq yatambaya yana mai kafeta da idanu.

"Haka Allah yatsaramin, BAZAN BUTULCE BA, yadda da ƙaddara yana da kyau, NAYARDA DA ƘADDARA TA, saidai kuma bazan mantaba har abada,  babu mai aurena, babu kuma mai tallafawa rayuwata, zanƙare rayuwata acikin ƙunci, idan har kaɗaukeni ƴar uwa kamar yadda kafaɗa, to inaso ka yi tunani shin wacce ta tsinci kanta acikin mummunar ƙaddara irin tawa akwai sauran farinciki da yarage mata?,  ni yarinyace haryanzu bangama sanin rayuwaba, amma tabbas nasan mai kyau dakuma marar kyau, saboda haka rayuwata a gurɓace take, yariga daya ruguzata, bakuma zata taɓa kafuwa ta tsaya da ƙafafunta ba har abada,  BANI DA ZAƁI likita amma akwai Allah ya isarmin komai!!" gaba ɗaya hawaye yagama wanke mata fuska, wannan karan ba iya zuciyarta bace tayi rauni hadda tashi zuciyar, lallai ƙaddaran Zahrah mummuna ce, amma kuma yazama dole yatsaya yakawar mata da duk wani duhu dake rayuwarta shi mai iya dawo mata da farincikin tane idan harzata amince, amma yasani Zahrah ta yanke ƙauna gaduk wani ɗa namiji,

"Likita ga abinci ko" Inna takatsemusu tunanin da sukeyi su dukansu.

Inna tana aje abincin tajuya tashige cikin ɗaki,  kallonsa yamaida kan ɗan ƙaramin bakinta dake bushe, sannan yakuma maida kallonsa kan idanunta, a matsayinsa na mutum mai karantar yanayin ɗan adam, take yakaranci halin da take ciki, bayajin yunwa ko kaɗan domin saida yaci abinci kafun yafito, amma saboda dalili ɗaya yasa yajawo kwanon abincin gabansa, shinkaface ƴar gida jalof, ko mai batajiba ballantana albasa, amma haka ya share, yakai loman abincin cikin bakinsa, taunawar farko yaci karo da dutse amma haka dolensa ya basar (readers likitafa yagamu da girkin manya Inna, lol🤣).

"Zo muci" yafaɗa a taƙaice,

Saurin kallonsa tayi haɗe da girgiza kanta, domin ita yanzu abinci baya gabanta, damuwarta ma abincine a wajenta,,

Babu alamar wasa akan fuskarsa kaitsaye yanufi bakinta da hanunsa wanda yake ɗauke da ƙwayoyin shinkafa domin da hanu yakecin abincin,, 

Saƙare haka tayi tanakallonsa domin wannan shine karo na farko a rayuwarta da wani ɗa Namiji ba muharraminta ba ya taɓa yunƙurin bata abinci a baki,

Kai tagirgiza masa alamar bataso haɗe da kawar da kanta gefe,

"Kinaso muyi faɗa kenan, kuma hakan nanufin baki ɗaukeni ɗan uwaba, nasan wunin yau bakisa komai a cikin kiba, sbd haka banason gardama, idan kuwa kikace bahaka ba, to akwai alluran da na taho da'ita, yanzu sainasa Baffa da Inna su riƙemin ke na yi miki har guda uku!! "  yaƙare maganar in a serious tone,   aikuwa ya faɗar mata da gaba domin kuwa tsoron alluran da takeyi haryazarce tunanin mutane,    "Haaaa" Dr Sadeeq yafaɗa still yana kusanta hanunsa ga bakinta, tamkar dai za abawa ƙaramin yaro abinci.

"Basaikabani ba zan iya ci!" Zahrah tafaɗa cikin raunanniyar muryarta, 

"To ci ingani" Shima yafaɗa yana mai turo mata kwanon abincin gabanta,  ahankali ta sa hanu ta tsakuri abincin, tamkar wacce akace ta tsakuro garwashin wuta da hanunta,  daƙyar ta iya buɗe baki ta kai loman abincin bakinta,  murmushi yayi haɗe da sanya hanunsa acikin kwanon abincin yasoma ci, duk da cewa ba daɗin abincin yakejiba, adole Zahrah take kai loman abincin bakinta bayanda ta'iyane kawai,,

Lomanta huɗu ta soma kwarara amai a wajen tamkar zata amayar da ƴaƴan hanjinta,  miƙewa tayi daga tsugunen da take domin tasoma ɓata jikinta da amai, aikuwa wani irin jiri ne ya ɗe beta take ta faɗa kan Dr Sadeeq dashima yake yunƙurin tashi tsaye,, gaba ɗaya yatarota tafaɗa cikin ƙirjinsa, yayinda aman dake jikinta ya gogu ajikin kayansa,,

Da sauri su Inna da Baffa suka ƙaraso wajen domin tundaga ɗaki sukejin ƙaran amannata, "Lafiya likita maiyasameta kuma ?" duka suka tambaya cikin ƙosawa, da'alama dai sungaji da lamuranta.

" Bakomai inaga olsa (ulcer) ce kawai ke damunta " Dr Sadeeq yafaɗa yana mai ƙoƙarin shimfiɗeta a akan tabarman da suke zaune,

Saidai gaba ɗaya ba ƙarfi a jikinta, saboda haka duk ta narkemasa a cikin jiki, yayinda shikuwa zuciyarsa ke tsananta bugawa, addu'a yake a zuciyarsa Allah yasa ba abun da yake zargi bane ke damun Zahrah idan kuwa abun da yake zargine tabbas babban tashin hankali na gaba...

(Wani tashin hankali munbanu readers 😲, Allah yasadai bacikine da ita ba, da Zaidu ya yi aiki mai tsada 🤣 )

*Breakfast na baku kuji daɗinku*

   
       *23/November/2019*

*Voted, Comment, and Share please....follow me on  Wattpad @fatymasardauna
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

          *SHU'UMIN NAMIJI !!*

      *Written By*
  Phatymasardauna

*Dedicated To My Lovely Brother Khabier*

*🌈Kainuwa Writers Association*

{United we stand & succeed; our ambition is to entertain and motivate the mind of readers}

*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*

          *WATTPAD*
   @fatymasardauna

*Editing is not allowed📵*

*Chapter 38 to 39*

A hankali Doctor ya kwantar da ita, cikin sanyin jiki yanufi motarsa don ɗauko jakarsa ta aiki, domin dama daga office yake yabiyo tagidannasu,, Allah yasa ba abun dayake hasashe bane yake shirin faruwa, lallaiko idan har ya zamana Zahrah ciki ne da ita, to fa shikansama yashiga tashin hankali, bawai ita kawai ba, domin yasan ɗan guntun tsarin daya shirya rugujewa zaiyi, to ina kuma ga Zahrah wacce bata gama warkewa daga ciwon dake jikinta ba, kuma ace taƙara faɗawa cikin azabar  wani ciwon, tabbas yasan tashin hankalin da zata shiga sai ya take wanda tashiga a baya,, jiki a saluɓe haka Dortor Sadeeq yadawo cikin gidan, zuwa lokacin har Inna ta ɗauketa takaita cikin ɗaki.

Tana kwance akan ƴar katifarta, sai faman sauƙe numfashi take a hankali, dagani kasan aman da tayi ya galabaitar da'ita sosai,  zama yayi gaf da'ita, haɗe da kama hanunta, lokaci guda yaji jikinta yaɗau zafi sosai, kayan aikinsa dake cikin jakarsa ya ciro ya fara yi mata ƴan gwaje gwaje,  

Wata irin ƙaƙƙarfan ajiyar zuciya Dr Sadeeq ya sauƙe sakamakon gano abun dake damun Zahrah da yayi, duk da cewa baiyi mata gwajin ciki ba, amma a iya ɗan bincikensa

Please Login or Register in order to submit comment