Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wallahi ni marainiya ce, da Allah kaɗai na dogara " tuni hawaye sun wanke kan fuskarta, wata irin dariya Zaid yayi mai cike da mugunta, hannayensa yasanya duka biyu ya juyo da'ita gabansa, yazamana suna faced ɗin juna, wayarsa ya dannan take hasken tocila (torch light) yabayyana, rufe idanunsa yayi haɗe da kai hasken tocilan kan fuskarsa, cikin mayaudariyar murya yace " fatan baki manta da wannan fuskar ba" sai a lokacin Zahrah taɗago idanunta ta sauƙesu akan kyakkyawar fuskar Zaid, wata irin ƙaƙƙarfan ajiyar zuciya ta sauƙe, haɗe da yin hamdala acikin zuciyarta,, wani irin ƙawataccen murmushi Zaid yayi mata, haɗe da kashe mata idonsa ɗaya, " matsoraciya " yafaɗa cikin murya mai sanyi,, hararan wasa Zahrah tayi masa haɗe da cewa "ko wama matsoraci ne idan har yaga mutuwa " murmushi Zaid yayi haɗe dayi mata wani irin kallo, mai ɗauke da ma'anoni dayawa, wani irin yawu ya haɗiye alokacin da idanunsa suka sauƙa kan cikakkun breast ɗinta... "Muje mota" yayi maganar yana mai nufar inda motarsa ke fake,, bamusu itama ta biyo bayansa,, kan kujeran mai zaman banza ta zauna, haɗe da takure jikinta waje ɗaya, sam itakam sa gyale bawai yawani damunta bane, tafiso koda yaushe tazamana cikin hijabi, domin yana kare mata tsiraicinta, gashi yanzu duk ta takura kowani motsi tayi sai surarta ya bayyana,, "Yauma bazaki gaisheni bako ?" Zaid yafaɗa daidai sanda yajefa wani sweet cikin bakinsa,, sunkuyar da kanta ƙasa tayi cike da kunya, itakam balaifinta bane, i dan ta gansa ne komai ke kuncemata,, kallonta yayi ta gefen idanunsa haɗe da cewa " kinsan maiya kawoni unguwarku yau ?" "A'a" tabasa amsa a taƙaice,, "SOYAYYA !!" yafaɗa cikin wata irin murya mai ɗauke da shauƙi,, "Soyayya kuma ?" Zahrah tatambaya domin sam bata fahimci inda kalamannasa suka dosa ba,, "INASONKI ZAHRAH !!" Zaid yafaɗi maganar yana mai kafeta da idanunsa, cikin tsananin mamaki Zahrah ke kallon Zaid, ko da wasa bata taɓa zaton zaiyi mata maganar soyayya anan kusaba, "Kinyi shiru sanar dani idan kinasona " Zaid yafaɗa yana mai kama hannayenta yashiga murzawa a hankali,, wasu irin ƙwallane suka shiga gangarowa daga cikin idanunta zuwa kan fuskarta, " kada ka yaudareni, ni macece mai rauni da kuma naƙasu, kaduba gidanmu, kaduba irin shigar dake jikina, ka dubi kanka kasan cewa nidakai ba ɗaya bane, akwai tazara mai tarin yawa a tsakaninmu, ban taɓa soyayya ba, bakuma naso nafara soyayya a'inda zuciyata zata wahalta, don Allah kajanye maganar soyayyata a gareka, domin nida kai bamu daceba " tuni hawaye sungama wanke fuskarta,, murmushi Zaid yayi haɗe da cewa "Ba labari nake baki ba, saboda haka ki farka daga baccin dakike, nabaki nan da 3 days ki koyamawa zuciyarki soyayyata, zan aureki idan har kin amince da hakan, bana buƙatar da cewar mu ko rashin sa,, ungo wannan idan kin koma ki kunnata saboda zan iya nemanki koda yaushe " yaƙare maganar yana miƙomata wata leda dake hanunsa,, kai tagirgiza alamar bazata karɓa ba, take yaɓata ransa, wanda hakan yasa taji ba daɗi, haka dolenta ta karɓa,, saida safe tayi masa, kana ta shige cikin gida,, tana shigewa shima ya ta da motarsa yayi gaba...

Tana shiga cikin gida Inna tayi yo kanta tana washe baki, sakamakon ganin leda da tayi ahanun Zahrah, wafcar ledan Inna tayi haɗe da cewa "ɗan albarka yaukuma mai yakawo mana ?" kwalin danƙareriyar iphone 11 pro max Inna tafara cirowa, a je kwalin tayi a gefe haɗe da zazzage ledan a ƙasa, kayan snacks dasu choculate ne suka zubo, saikuma mai gayya mai aiki wato farare bugun Abuja, dariya Inna tayi haɗe da buga shewa, itakam Allah yakashe ya bata, lokacin yin arzikinta yayi,, jin shewan Inna yasa Baffa dake cikin ɗaki fitowa, "lafiya kuwa.... " kasa ƙare maganar Baffa yayi sakamakon tozali da kuɗaɗen da ke gaban Inna da yayi........


(Readers maikuke tunanin zai wakana tsakanin Zaid da Zahrah ? Zahrah zata amince da soyayyar Zaid kuwa ? kokuwa zata ɗauki Jabeer ne tabar Zaid ? kuci gaba da bibiyata don sanin mai zai faru anan gaba...)




*19/October/2019*


*MRS SARDAUNA*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*SHU'UMIN NAMIJI !!*


*Written by*
phatymasardauna
*🎈Mrs Sardauna🎈*


*Dedicated To My Lovely Brother Khabeer*


*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*

*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*

*WATTPAD*
@fatymasardauna


*Editing is not allowed 📵*

*Chapter 12*

*( INA MAI BAKU HAƘURI DOMIN KUWA KWANA BIYU, ZAKUJINI SHIRU BA NEW UPDATE, WATA ƘILA NAYI 1 WEEK BANYI TYPING BA, WATAƘILA KUMA BAZAN KAI HAKANBA, HAKAN YAFARU NE SABODA WANI DALILI NAWA, INSHA ALLAH AMMA ZAKUCI GABA DA JINA IDAN KOMAI YA DAI DAI TA, NAGODE....)*

*Kuɗanyi manage da wannan 👇🏼*


Kasa ƙare maganar Baffa yayi sakamakon tozali da kuɗaɗen dake gaban Inna da yayi, cike da tuhuma yake kallon Inna yamakasa ce da'ita komai, ganin haka yasa Inna ta washe baki, haɗe da soma tattare maƙudan kuɗaɗen, cikin hanzari Baffa yasanya hannayensa duka biyu ya wawashi kuɗin, haɗe da cusawa cikin aljihunsa, da sauri Inna tayo kansa tana muzurai, haɗe da cewa "Haba Malam yazakayi haka, aidai katsaya nayi maka bayani kafun ka kwasa rabonka ko" harara Baffa ya watsamawa Inna haɗe da taɓe baki yace " ba abun da bansani ba, nasan duk wani abu dakike shiryawa, kuma wallahi daga yau idan aka sake kawo kuɗi cikin gidannan ba ki jira dawowata munraba ba, ninasan matakin da zan ɗauka, yarinyace dai ƴar wa na ne, don haka babu wanda ya'isa ya gwadamin iko da'ita, kuma shima saurayin zaizo yasameni haka ake zuwa hira babu wani tambayar izini ba komai" Baffa yaƙare maganar yana mai nufar ƙofar fita daga gidan, yana fita Inna ta buga tsuka haɗe da cewa " shikenan kuma ae tunda yagano abun danake shiryawa, bazai taɓa barina naci arziki ni ɗaya ba, mcheeew !" taƙare maganar tana mai tattare ƴan ragowan kuɗaɗen da Baffa ya bar mata, raba snacks ɗin biyu tayi taɗauki rabi, yayinda tabarmawa Zahrah rabi, waya kuwa danƙamawa Zahrah abunta tayi, domin ita keypad ma bawani iyata tayi ba, balle kuma shafa shafa (touching screen)... Jigum haka Zahrah tayi zuciyarta cunkushe take da tarin tunani kala kala, da zaran ta kulle idanunta, mood ɗinsu na ɗazu ne ke faɗo mata, wanda hakan yasanya takejin gaba ɗaya jikinta yayi sanyi, batasan dame zata ƙira wannan yanayinba, saboda batasan ma da akwaishi acikin duniyar nan ba, duk dacewa bawani abune yashiga tsakaninsu ba, amma kusancin da sukayi da juna duk ya dagula mata lissafi, ga fitinannen ƙamshin turarensa daya kama jikinta, tamkar wacce tayi wanka da turaren,daga wani ɓangare na zuci yarta kuwa kaico takeyi da mummunan hali irin na Inna da Baffa, wato su baruwansu da koma waye zaizo wajenta, sudai kawai abasu kuɗi suka sani, koda ma iskanci takeyi su baidame su ba kuɗi kawai suke so, haƙiƙa rashin iyaye babban matsalane arayuwar ƴa mace musamman ma idan batayi dace da iyayen riƙo nagari ba, sai kuga rayuwarta nashirin lalacewa, akan abun da bai kai yakawo ba, Allah ka zama gatan mu aduk inda muke Ameen,,, a hanakali taciro wayar daga cikin kwalinta, subahanAllah shine abun da tafurta lokacin da'idanunta suka sauƙa akan haɗaɗɗiyar wayar, jikin wayar ma kaɗai abun kalloce balle kuma kakai ga shafata, tabbas idan baza ta mantaba, wannan wayar itace wacce taji ƴan school ɗinsu na magana sabuwar fitowa ce, kuma burin kowanni ɗan gata da ƴar gata, shine su mallaki wayar, domin kuwa aƙalla kuɗinta zaikai dubu ɗari biyar da tamanin,, wani irin faɗuwar gaba taji ya shiga zuciyarta a lokaci guda, take kuma mugun zargin Zaid ya ɗarsu acikin ranta, tabbas akwai abun daya ɓoye acikin zuciyarsa, amma idan ba haka ba babu yanda za'ayi yasiya mata wayan dubu ɗaruruwa, batare da suna da wani kyakkyawan alaƙa atsakaninsu ba, a maimakon ta kunna wayar kamar yadda ya umarce ta, batayi hakan ba saima mai da wayar tayi cikin kwalinta haɗe da cusata cikin kayanta, taƙudura acikin ranta cewa idan yasake da wowa zata mayar masa da wayarsa, domin ita bata kai martaba da ƙimar da zata riƙe wannan zuƙeƙiyar wayarba,, sam bacci ya ƙaurace mawa idanun Zahrah kalaman Zaid ne ketayi mata yawo acikin kunnu wanta, bama kamar kalmar *INASONKI ZAHRAH* daya faɗa, gaba ɗaya zuciyar Zahrah kasa sukuni tayi a wannan dare, da ƙyar bacci ɓarawo ya ɗauketa......


Zaid kuwa yana barin unguwar su Zahrah guest house ɗinsa ya nufa, sai dai yau ba ya tare da kowacce karuwa, yana shiga cikin bedroom ɗinsa yasoma rage kayan jikinsa, saida yacire duk wani kaya dake jikinsa, kafun ya ɗaura towel a ƙugunsa kaitsaye ya shige bathroom,, a ƙalla ya kwashi kusan 1 hour a cikin bathroom ɗin kafun yafito, sanye da rigar wanka a jikinsa, gaban mirror ɗinsa yaje ya ɗanyi shafa, combat jeans black ya sanya haɗe da black t-shirt, sosai kyawun Zaid ya bayyana acikin wannan kayan, wayarsa kawai ya ɗauka yafice daga cikin ɗakin, makeken friedge glass ɗin dake cikin katafaren falon nasa yanufa, zuƙeƙiyar kwalbar wine mai tsadar gaske yaɗauko a cikin friedge ɗin haɗe da glass cup zama yayi akan ɗaya daga cikin kujerun falon, yayinda ya buɗe kwalbar wine ɗin ya tsiyaya a cup, kana yakai bakinsa, a hankali yake shan wine ɗin, yayinda idanunsa ke alumshe, bakomai yake hasa sowa ba sai kyakkyawar surar Zahrah wacce ke tafiya da imaninsa ako da yaushe, haƙiƙa ya kamu da tsananin sha'awar Zahrah, kuma alƙawari yaɗaukar mawa kansa idan dai har yacika *SHU'UMIN NAMIJI* kamar yadda abokansa ke ƙiransa, to sai ya keta mawa Zahrah rigar mutumcinta kota wani hali kuwa,, wayarsa yaɗauka haɗe da laluɓo numbern sim ɗin dake cikin wayar Zahrah, yana dialing aka sanar dashi cewa wayar a kashe take, wani irin munafukin murmushi Zaid yayi haɗe da sanya hanu ya shafi sajen dake kwance akan fuskarsa, kashe idanunsa ɗaya yayi haɗe da cewa "My Sugar Baby bakijin magana ko ?" yayi maganar tamkar wanda yake gabanta,, sosai Zaid ya sha wine a wannan dare, da ƙƴar ma yasamu bacci ya ɗaukesa bayan yagama kwarara aman giyan da yasha .......



*21/October/2019*


*MRS SARDAUNA*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*SHU'UMIN NAMIJI !!*




*WRITTEN by*
phatymasardauna
*🎈Mrs Sardauna🎈*


*Dedicated to my lovely brother Khabier*


*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*

*WATTPAD*
@fatymasardauna


*Editing is not allowed 📵*


```{{ Dan Allah kuyi haƙuri, kubarni na cigaba dayin littafina a yanda natsara, banson ƙorafi kokuma cece kuce, haka labarin Zaid da Zahrah yake, bakuma zan sauya ba, baikamata ace tun bakuji mai zai wakana gaba ba, kunsoma yanke hukunci, inyi kaza kar inyi kaza, kada Zaid yayi kaza, 🤦🏼‍♀ Please kudaina haka ba daɗi, inaso kusani a yanda na tsarashi ahaka zanci gaba da tafiya dashi, babu wani kwana kwana, kuma abu na farko da nakeso ku fara sani shine, kowa a duniya da irin tasa Ƙaddarar, so komai kuka gani sai ku ɗaukeshi a matsayin ƙaddara....}}```

*Chapter 13....*


Yaune kwanaki ukun da Zaid ya ɗibar mawa Zahrah suka cika cif cif, don haka yau da wani irin matsanancin faɗuwar gaba ta wayi gari, haƙiƙa bazata yaudari kanta ba, tasani cewa ƙwarai zuciyarta ta aminta da Zaid to amma babban abun dubawa shine, shin Zaid ɗin yadace da rayuwarta kuwa? ko kaɗan bata hango dacewarsu da Zaid ba, duk da tasan cewa tana da kyawun da kowani ɗa na miji zaizo da ƙoƙon soyayyarsa gareta, amma bata tunanin haɗuwarsu da Zaid zaiyi dai dai, kallo ɗaya zakaima Zaid kafahimci cewa shiɗin mai tarin arziki ne, haka ma iyayensa, itakuwa bakomai bace face *TALAKA* ƴar *TALAKAWA* wacce talauci yabayyana tambarinsa ajikinta, sam bata mawa kanta adalci ba matsawar ta ɗauki kanta takai zuwa matsayin da bana taba, wasu irin hawayene suka shiga gangarowa daga cikin idanun Zahrah, yayinda zuciyarta keyi mata zafi, batasan menene so ba, domin bata taɓa yi ba, amma a yanda takejin Zaid acikin zuciyarta, yasa tafara kokonton cewa takamu da tsananin soyayyarsa, gaba ɗaya wunin yau a susuce tayi sa, damuwarta ɗaya idan Zaid yazo maizatace dashi ? idan ta furta masa kalmar ƙi to fa har abada bazata taɓa yafemawa kanta ba, domin ta cutar da zuciyarta, idan kuwa ta furta masa kalmar so, tofa ba makawa tajefa kanta acikin ɗauri ne mai wuyar suncewa.... Wunin ranar dai haka Zahrah tayi shi sukuku babu daɗi, fargaba ne fal cike a zuciyarta....koda tayi Sallan la'asar banɗaki tashiga tayi wanka , zama tayi akan katifarta, haɗe da ɗauko wata hand bag ɗinta, wanda ciki take ajiyar kayan kwalliyanta, duk da cewa dai itaɗin ba mace bace ma'abociyar yawan kwalliya,, hakanan ta tsinci kanta da son yin kwalliya a yau ɗin, hoda (powder) ta murza akan fuskarta, haɗe da shafa janbaki (lipstick) dark maroon colour, akan laɓɓanta, black eye pencil, tasanya acikin idanunta, haɗe da shafa mascara akan zara zaran gashin idanunta, take fuskar Zahrah tasakeyin kyau, duk da dama cewa itaɗin mai kyauce,, wata Arebian gown maroon colour tasanya ajikinta, sosai da sosai rigar ta amshi jikin Zahrah, tayi mata ɗas, duk acikin kayanta Zahrah tana matuƙar son rigan, domin kuwa maman khausar ce takawo musu, ita da khausar ɗin, daga Saudiya,, rigace mai kyau da tsadar gaske, uwa uba idan ta sanya rigar ita kanta tasan tanai mata kyau,, kan katifarta ta koma ta zauna, bayan tagama kimtsa kanta, jigum tayi tana tunanin waishin maiyasan yata yin kwalliya batare da wani dalili ba? "saboda Zaid zai zo, zuciyarta ta bata amsa, "idan kuma baizo bafa ?" tatambayi kanta, take wani irin faɗuwar gaba ya ɗarsu acikin zuciyarta, wanda batasan dalilin faruwan hakan ba,, abu kamar wasa, har yammaci ta rufa babu Zaid babu alamarsa, tuni jikin Zahrah yayi sanyi laƙwas,, hardai akayi sallan Isha, ba'azo daga waje ance anaƙiran Zahrah ba,, tuni ta wanke ɗan kwalliyan da tayi a fuskar tata ma, domin zuwa yanzu tacire rai da zuwan Zaid... Zaune take a tsakar gida, gabanta ɗauke da kwanon shinkafa da wake, a hankali take tsakuran shinkafan tana kaiwa bakinta, kallo ɗaya zakai mata kahango tarin damuwa acikin zuciyarta,, kamar daga sama wani yaro yashigo, yace wai anaƙiran Zahrah a waje,, wani irin farincikine ya lulluɓe zuciyar Zahrah, domin kuwa tana kyautata zaton cewa Zaid ne,, koda tashiga ɗaki don ɗauko mayafinta saida tasake murza powder a kan fuskarta haɗe da sanya kwalli a idanunta, Zahrah dai bata tsayananba hadda shafa jambaki,, wani rover hijab tasanya ajikinta, kalar maroon, wato kalar doguwar rigan dake jikinta, gaba ɗaya lufayar iyaka cinya ta tsaya mata, hakan kuma yayi nasarar bayyana surar jikinta, kasancewar lufayan mai rover ce, tayi kyau kuma balaifi, tamkar dai balarabiya, abunka da farar fata,, turarenta mai sauƙin kuɗi (TONY MONTANA) tafeshe jikinta dashi, take ta ɗau ƙamshi,, a hankali take taku harta fice daga cikin gidan nasu,, koda tafito daga gidan cikin nutsuwa take takunta, yayinda kanta ke duƙe a ƙasa, zuciyarta kuwa bugawa tashiga yi akai akai,, kaitsaye tanufi wajen da taga motarsa na fake,, tun da tafito daga cikin gidan, ya kafeta da mayun idanunsa, masu rikita mata, sosai yau ɗin tayi masa kyau, hakanan yaji sha'awarta ta ninku akan nada,, tana ƙarasowa wajen motar ta sa, taja ta tsaya, still kuma kanta na kallon ƙasa tana wasa da yatsun hanunta, a. hankali yabuɗe murfin motar tasa haɗe da ziro ƙafafunsa waje, take wani irin fitinannen ƙamshin turarensa yacika ko'ina na wajen, a hankali ta lumshe idanunta, domin kuwa bakaɗan ba ƙamshin turaren nasa ya tafi da'ita,, kallonta ya shiga yi tundaga ƙasanta harzuwa samanta, kafun ya saki shu'umin murmushinsa, "MY ZAHRAH !!" yaƙira sunanta da wani irin murya mai sauƙar da kasala, kasa amsa masa Zahrah tayi saima sake sadda kanta ƙasa tayi tana mai wasa da yatsun hanunta,, murmushi yakumayi a karo na biyu, "yau kuma tsayuwa kikeji da shi ?" yayi tambayar cikin nuna halin ko inkula,, jin haka yasanya ta gane mai yake nufi, jiki a sanyaye ta nufi ɓangaren mai zaman banza tabuɗe murfin motar haɗe da shiga ta zauna,, a hankali Zaid ya yi ƙasa da kujerar dayake zaune, ɗan zamewa yayi ya jingina bayansa da jikin kujeran haɗe da lumshe kyawawan idanunsa, a hankali Zahrah ta ɗan saci kallonsa haɗe da cewa "Ina wuni !" jin muryarta da yayi ta ratsa kunnuwansa yasa sa ɗagowa, yazauna haɗe da kafeta da'idanunsa, yakai kusan 3 minute yana kallonta "kinyi kyau !!" yafaɗa in a unigue voice ɗinsa, wani iri Zahrah taji a cikin jikinta, wannan shine karo na farko a duniya da wani ɗa namiji ya fara faɗa mata cewa tayi kyau,, cikin salonta na kunya, ta ɗago idanunta takalleshi karab idanunta suka sauƙa acikin nasa idanun, wani irin shock taji ajikinta, da sauri tayi ƙasa da kanta, cikin salonsa ya ce " Idan kinajin kunyana ta ya ya zaki iya nunamin zallar soyayyar danake buƙata a wajenki ? inasonki da duka zuciyata My Zahrah ina fata kema zaki soni kamar haka ko fiye da haka ? " a yanda yayi maganar idan kakallesa zaka iya rantsewa cewa bashine yayi ba,, jitayi jikinta gaba ɗaya yayi laƙwas, wani irin zazzafar ƙaunarsa takeji yana huda kowani irin saƙo na jikinta, a hanakali ta ɗago manya manyan idanunta da suka cika da ƙwalla, ta sauƙe su akan kyakkyawar fuskarsa, cikin murya mai rauni tasoma cewa "bantaɓa soyayyaba, bankumasan ya akeyinta ba, ni marainiyace bayan Allah sai Baffana nakedasu acikin wannan duniyar, nasan kafi ƙarfin ajina, dan Allah kada kayaudareni da soyayyarka " taƙare maganar lokacin da hawaye suka shiga sauƙowa a kan fuskarta,, kafeta da idanunsa yayi harnatsawon wasu mintuna, shikaɗai yasan abun da yake saƙawa acikin zuciyarsa,, "Idan kin yarda dani to kibani soyayya da amincewarki, nikuma bazanci amanarki ba" yayi maganar cikin muryarsa mai sanyawa zuciyarta nutsuwa,, ƙaƙƙarfan ajiyar zuciya Zahrah ta sauƙe haɗe da yimawa Allah godiya daya kawomata ma'agaji adai dai lokacin da ta ke buƙata, shirune yashiga tsakaninsu na ɗan wani lokaci, bayan Zaid yagama saƙa abun da zai saƙa acikin zuciyarsa, yasaki wani irin killer smile haɗe da mai da kallonsa ga Zahrah, "ya kamata ki kaini nagaidasu Baffa ko " ya yi maganar yana mai kashe ma ta idanunsa ɗaya,, murmushi kawai zahrah tayi haɗi da cewa "banaje na sanar dasu to " buɗe murfin motar tayi ta fice haɗe da shigewa cikin gida, bayanta kawai Zaid ya ƙura ma wa ido bakaɗan ba ya kwaɗaitu da yarinyar kuma insha Allah saiya cimma burinshi a kanta,, bawani jimawa Zahrah tafito daga cikin gidannasu, kamar dai ko da yaushe kanta duƙe yake a ƙasa harta ƙaraso garesa,, iso tayi masa zuwa cikin gidannasu, gaba ɗaya a takure take domin kuwa itace a gaba shikuma yana biye da'ita a baya, ahaka suka shiga cikin gidan,, cike da ƙyanƙyami Zaid yazauna akan tabarmar da Inna ta shimfuɗa ma sa a tsakar gidannasu, tunda yake a duniya yaune karo na farko a rayuwarsa da yafara zama cikin gidan talakawa, lallai idan yakama Zahrah ba zai mata da sauƙiba, da ƙyar ya'iya kai zuciyarsa nesa yagaisa dasu Baffa da suka ƙura masa ido, tamkar sunga baƙon halitta,, har rige rigen amsa gaisuwar tasa Inna da Baffa sukeyi, daganinsu kaga mayun ku ɗaɗe,lol, shirune yabiyo baya bayan sungama gaisawa, domin dai harga Allah Zaid bayi da abun cewa, saboda shi bai ma taba irin hakan ba, bayan iyayensa babu wasu wanda yataba gaisarwa da ladabi haka, sai gashi yau akan wata tatsitsiyar yarinya yazo yana kaskantar da kansa gaban talakawan unguwa, lallai yaci amanar jinkai dakuma ajinsa, amma yazaiyi tunda shiyake nema dole yayi biyayya,, ganin yayi shirune yasa Inna gyara zama hade da cewa, " munagodiya sosai bawan Allah ga me da taimakon mu da kakeyi, Allah ubangiji yasaka da alkhairi, " murmushi kawai Zaid yayi hade da mikewa tsaye, bandir din kuɗaɗe yaciro daga cikin aljihunsa, hade da ajewa akan tabarmar daya tashi,, tsadaddun takalmansa yasanya hade dayi musu sai anjima yafice daga cikin gidan, "bawan Allah harda dawainiya haka to to masha Allah, Allah yasaka da alkhairi " Inna tafada tana mai washe baki,, Zaid yana ficewa daga cikin gidan, Inna da Baffa suka dakamawa kudin wawa, Zahrah dake tsaye a gefe kuwa idanunta ne suka ciko da kwalla, sam batajin dadin abun da Baffa da Inna sukeyi, suna nuna zalamarsu afili,, "Miye kika yi wani ƙasaƙe kina kallonmu bazaki bisa ba " Baffa yafaɗa yana hararan Zahrah, jiki a sanyaye Zahrah tarufa mawa Zaid baya,,,, Zaid kuwa yana fita kaitsaye motarsa ya wuce, sosai yaji daɗin yanda ya hango zallan son kuɗi irin na Baffa da Inna, tabbas yanzu yasake samun ƙwarin guiwa akan burinsa, yanzu yasan cewa bazai wahala wajen samun galaba akan Zahrah ba,,, tana fitowa ya sakar mata kyakkyawan murmushinsa, wanda yake ƙara mawa kyakkyawar fuskarsa kyau aduk sanda yayi sa......



*Kuyi hakuri wallahi kwata kwata banjin yin typing dinne, abubuwa sunmin yawa, nasoma ace 2 weeks nayi, amma sai wasunku suka nuna rashin jin dadin hakan, so please kunamin uzuri duk dama nasan wasunku bazasu so hakan ba, a gaskia bako da yaushe zanna typing ba, saboda kowani ɗan adam yana buƙatar hutu a rayuwarsa, kuyi haƙuri duk bayan kwana ɗaya zandingayin new update....*



*27/October/2019*


*MRS SARDAUNA*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*SHU'UMIN NA MIJI !!*



*WRITTEN by*
phatymasardauna
*🎈Mrs Sardauna🎈*


*Dedicated to my lovely brother Khabier*


*🌈Kainuwa Writers Association*


*WATTPAD*
@fatymasardauna


*Editing is not allowed 📵*


*Chapter 14*

Wani irin kallo mai ta da tsikar jiki Zaid yayi mawa Zahrah, still fuskarsa ɗauke da wannan sheɗanin murmushinnasa, sadda kanta ƙasa tayi haɗi da soma wasa da yatsun hanunta,, Sunanta yaƙira da wata irin murya mai kwantar da zuciya, bata iya amsa masa ba saima ɗago kanta da tayi ta kallesa, wani irin baƙon yanayi ta tsinci kanta aciki mai wuyar fassaruwa, a hankali ya lumshe kyawawan idanunsa masu kalar bacci haɗe da buɗesu a lokaci guda,, "Zantafi !!" yafaɗa daidai lokacin dayake ɗaura sit belt a jikinsa, kasa ce dashi komai tayi saima wani iri taji dayace zaitafi ita a sonta bataƙi su tabbata a haka ba, domin ganinsa kaɗai yakansa taji wani irin nishaɗi a cikin zuciyarta,, wata ƙatuwar leda mai ɗauke da tambarin wani makeken mall yamiƙo mata, sadda kanta ƙasa tayi haɗe da girgiza kanta, alaman bazata karɓa ba,, ɗan ɓata fuska Zaid yayi haɗe da cewa " idan baki karɓa ba bazanji daɗi ba, kuma kinsan cewa bakyau maida hanun kyauta baya " wani irin sanyi taji a cikin ranta tabbas

Please Login or Register in order to submit comment