Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta'iya cewa   "Bansan maganar Zaid bace takawoka wajena ba,  da bantsaya ɓata lokacina wajen saurararka ba, don bazan ɓata lokacina abanza ba, dan Allah kufita a rayuwata, kacewa Zaid ya ƙyaleni  na huta, domin kuwa  ko maza sun ƙare a duniya bazan taɓa auren Zaid ba!" Zahrah tafaɗi haka cikin dakiya dakuma ɓacin rai...

"Ba gaskiya bane Zahrah, wannan maganar da kika faɗa ba daga cikin zuciyarki tafito ba daga bakinki tafito, kobaki furta ba raunin kalamanki sunnuna cewa kinason Zaid har yanzu, me yasa bazaki yafe masa ba? Allah ma muna masa laifi ya yafe mana, dan Allah Zahrah ki taimaka ki auri Zaid, haƙiƙa nida Zaid muna biyewa zuciyarmu muna aikata abunda baidace ba, amma kuma ina me tabbatar miki da Zaid ɗin dakika sani a yanzu bashine wanda kika sani ada ba, soyayyarki ta sanjawa Zaid tunani, soyayyarki ta juyamasa ƙwaƙwalwa, wallahi ke kaɗaice muradinsa acikin duniyar nan, Zaid baisan damuwa ba sai akanki Zahrah, yayi nadama me tsanani akan abun daya aikata miki,  akan ki Zaid yafara sanin menene ƙunci, akanki yafara sanin menene  ɗacin soyayya dakuma zaƙinta, haka akanki Zaid ya kasa fuskantar gabansa dakuma bayansa, akan kine kuma dalilinkine Zaid yakamu da ciwon zuciya me tsanani, ahalin yanzu Zaid yana acikin wani hali, Zahrah ke kaɗaice zaki iya sanjasa ki kuma ceto rayuwarsa please koba don nida Zaid ba kodan ceton rayuwarsa ki taimaka ki auresa!" Abid yaƙare maganar cike da raunin murya sosai yake matuƙar tausayin Zaid musamman ma dayaje yagansa yau, gaba ɗaya yafita hayyacinsa...

Murmushi me tsananin ciwo Zahrah tayi haɗe da sanya haƙoranta tacije lips ɗinta, kallon Abid tayi kana ta girgiza kanta

"Meyasa ku kazamanto mutane masu tsananin son kansu? Zaid rayuwarsa kawai zai rasa, amma ni gani da raina ta sanadiyarsa ne kuma narasa farinciki na, rayuwata tazamo marar amfani a gareni, ya katsemin farinciki dajin daɗi na, yakawo kansa gareni alokacin dayaga dama, yakuma sanyamin soyayyarsa alokacin dayaga dama, sannan yakuma ketamin haddina alokacin da yaga dama,  yayimini duk wani abu da ransa keso alokacin dayaga dama,  nima kuma yanzu nadawo mutum zankumayi duk wani abun daya dace alokacin dana ga dama, idan shi ne ya aikoka da waƴannan yaudararrun kalaman to kaje kasanar masa cewa kalaman naku basuyi aiki akai na ba, zaifi kyau kubarni nayi rayuwar aurena cikin farinciki da salama,  domin kuwa gobe iwarhaka najima da zama matar wani insha Allah,  inaso kuma kasani cewa najima da barin Zaid da Allah, haƙiƙa ya cutar dani, amma kuma dama hakan yakasance rubutaccen ƙaddarata ne wanda Allah ya rubuta, kaje kawai Abid bana tunanin sake burin haɗa rayuwata da ta Zaid!"  hanu tasanya ta sharce hawayen da suka silalo daga cikin idanunta haɗe da juyawa tasoma tafiya...

"Komai yana hanunki Zahrah idan har kikace afasa aurenki da wanda zaki aura aɗaura da Zaid nasan iyayenki zasu amince,  shin maiyasa bazaki cika muku burinku ba? kinasonsa shima kuma yana sonki,  ki amince ki aure sa, wallahi namiki alƙawari ko nawa kikeso aduniyar nan zan mallakamiki shi koda kuwa duka dukiyata kika buƙata nabaki zan baki,  amma bazan tilastaki ba sai dai inaso kisani idan Zaid ya rasa rayuwarsa a yanzu kece SANADI"  Abid yana kaiwa nan azancensa  yabuɗe murfin motarsa, wata ƴar madaidai ciyar jaka ya ɗauko,  takawa yashigayi harsai da yazo kusa da'ita kafun ya tsaya... "Ki amshi wannan jakan idan kika buɗe laptop ɗin dake ciki zakiga yanda Zaid ya koma A SANADI'N SONKI"  Abid yafaɗi haka yana me miƙa mata jakar..   Tsintar kanta tayi da kasa ƙin karɓan jakar, yana bata jakar ya juya yayi tafiyarsa,,, har motar Abid ta ɓule Zahrah na tsaye sororo hanunta riƙe da jaka,,,   saurin share hawayenta tayi, haɗe da nufar cikin gidan su,,, sumi sumi haka ta shige cikin ɗakinta, abun yayi mata daɗi sosai   data iske Husnah hartayi bacci,, mayafinta ta cire haɗe da neman waje ta zauna, kanta ta kifa akan guiwowinta, damuwane cike azuciyarta, takasa sanin wani hali take ciki,   kanta ta ɗago takalli jakar da tashigo dashi, da sauri tajawo jakar haɗe da buɗeta,  a hankali ta zaro laptop ɗin dake cikin jakar, saida ta ƙarewa laptop ɗin kallo kafun ta buɗeta,    tana danna wani madanni laptop ɗin takawo haske take kyakkyawan hoton fuskarta ya bayyana akan screen na laptop ɗin, mamakine yakamata ganin hotonta wanda batasan ma dashi aduniya ba, balle tasan yaushe ko wace ranace aka ɗauketa hoton ba, ƙurawa hoton nata idanu tayi tamakasa yin komai,  bata ɗauke idanunta akan hoton ba har saida hasken screen ɗin laptop ɗin ya gaji dan kansa ya ɗauke..  Ajiyar zuciya me ƙarfi ta sauƙe haɗe da sake kunna laptop ɗin, batasan inazata shiga ba, bata kuma san mezata fara dubawa ba, hakanan ta ji zuciyarta ta ingizata da tashiga ɓangaren hotuna,, tana kutsawa ɓangaren hotuna,  hotunantane suka farayi mata wellcome, mamakine yasake kasheta ganin hotunanta kaca kaca babu adadi acikin laptop ɗin, wanda ita a iya tsawon tarihin rayuwarta ma bata kasance mace meyawan sonyin hoto ba, yanzu haka ko hotonta ƙwaya ɗaya bata dashi acikin wayarta,,,,  bata da me amsamata tarin tambayoyin dake ranta dan haka kawai saita shiga wuce hotunan nata,  hotunan Zaid takuma cin karo dasu wanda saida gabanta yayi wani irin faɗuwa yayinda ƙirjinta yashiga dokawa da sauri..  da ƙyar ta'iya view ɗaya daga cikin tarin hotunan nasa,   sanye yake da wandon jeans baƙi dakuma wata farar riga saikuma hular sanyi daya sanya akanshi yayinda kunnensa ke sanye da farin earpiece, yayi kyau matuƙa a hoton domin kuwa fuskarsa ɗauke take da wannan ƙawataccen murmushin nasa wanda yake ƙara masa kyau ako da yaushe...   Ƙura mawa hoton nasa idanu tayi, saitaga tamkar shiɗinne da kansa agabanta,  batasan sanda wasu hawaye suka silalo daga cikin idanunta zuwa kan ƙuncinta ba,,  tajima tana kallon hoton nasa, haka kuma hawaye na tsiyaya daga cikin idanunta,  ɓangaren vedios takuma kutsawa, sai dai vedion farko da ta gani shine wanda yakusa tarwatsa mata zuciya, yakuma ɗaga mata hankali,,  Zaid tagani kwance akan gadon asibiti ansanya masa oxygen, yayinda aka dasa masa wasu ƙarafan na'urori akan ƙirjinsa dai dai saitin zuciyarsa, da badon ɗan abu kamar computer'n dake gefensa wanda shike nuna alama yana da rai ba, to tabbas da saidai ace dashi gawa,,, wani irin sarawa taji kanta yayi, yayinda wani irin kuka yazo mata alokaci guda, saurin sanya hanu tayi ta toshe bakinta haɗe da  rumtse idanunta, a hankali ta jingina bayanta da bango,,, hawayene suka shiga gudu wani na koran wani akan fuskarta,, duk yanda taso daurewa kasawa tayi saikawai tafashe da wani irin kuka me sauti, kuka take sosai yayinda ta rungume wannan laptop ɗin akan ƙirjinta,,,, kamar amafarki Husnah kejin gunjin kuka natashi acikin ɗakin, dayake ita ba me nauyin bacci bace yasanyata buɗe idanunta ahankali, aikuwa dagaske ba amafarki bane, kukan Zahrah taji raɗau acikin kunnenta, da sauri ta tashi zaune haɗe da dawo da kallonta inda sautin kukan ke fitowa,, sake waro idanunta tayi ganin da tayiwa Zahrah na kuka tsakaninta da Allah.   "Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un! Zahrah meyafaru kike irin wannan kukan?" Husnah ta tambaya cikin ruɗewa...   Jin muryar Husnah acikin kunnenta yasanya, tataso daga inda take da sauri ta faɗa jikin Husnah ae kuma saita ƙara volume ɗin kukan nata,, kai Husnah ta dafe cike da tashin hankali, "Allah yasa dai bawani gagarumin abubane yafaru" Husnah tafaɗi haka acikin zuciyarta.

"Kiyi shiru dan Allah Zahrah, kinga dai yanzu dare ne sokike kowa saiyaji gunjin kukan ki? kiyi shiru kisanar dani meke faruwa" Husnah tafaɗi haka ga Zahrah cike da damuwa...   Yau Zahrah tsintar kanta tayi da kasa daina kuka, ji ma take tamkar Husnah ingizata take da ta ƙara volume,,    sororo haka Husnah tayi ganin Zahrah taƙi daina kukan,  zame ta tayi daga jikinta haɗe da nufar inda  aka aje musu ledan ruwa na pure water,  guda ɗaya ta zaro acikin ledan haɗe da fasawa ta tsiyaya acikin cup,, dawowa tayi ta zauna haɗi dakai kofin ruwan bakin Zahrah,  babu musu Zahrah ta amshi kofin takai bakinta, gaba ɗaya ruwan dake cikin kofin tashanye tas haɗe da aje kofin agefe, ajiyar zuciya tasoma sauƙewa akai akai amma na kuka,,,  kwanciya tayi luf haɗe da sanya hanu ta dafe kanta dake matuƙar sara mata,,, idanu kawai Husnah ta zuba mata tana me mamakinta, gaba ɗaya aƴan kwanakinnan talura Zahrah ta maida kuka abinci da kuma ruwan shanta,  ita yanzu hartama fara tunanin ko aljanune suka shiga jikin Zahrah'n,,   bayan kamar minti goma Husnah taƙira sunan Zahrah,, amma kuma saitaji shiru Zahrah bata amasa mata ba, hakan ne yasanya tayi tunanin cewa Zahrah'n tayi bacci,  raɓawa gefen Zahrah'n itama tayi ta kwanta, mintuna kaɗan bacci yakuma surarta, Zahrah na jin sauƙar numfashin Husnah nafita a hankali ta tabbatar da cewa Husna'n tayi bacci,  ahankali ta ware idanunta dasuka cika tab da ƙwalla,  sarai tanaji sanda Husnah taƙira sunanta, taƙi amsawa ne gudun kada ta tonawa kanta asiri, saboda batason wannan sirrin yafita daga cikin zuciyarta, har abada tafiso ta bunneshi ita kaɗai batare dakowa yaji koya gani ba, ada tana ganin cewa ita mahaukaciya ce datakeson wanda ya zalunceta, sai ayanzu ta sake tabbatarwa kanta cewa shi so babu ruwansa, idan zai shiga jikinka baya duba wani cancanta ko matsayi haka nan yake faɗa ma, ashe da fari tayi ƙarya da tace zatayi yaƙi da soyayyar Zaid a zuciyarta, ashe ba'a iya yaƙi da soyayyar da take acikin jini da tsoka,,  ada tana tunanin cewa zuciyarta bata kyauta mata ba, ashe itace bata kyautawa kanta ba, yanzu ta gamsu cewa so ne ya lalata mata rayuwa ba wai Zaid ba, ashe so shine ya yaudareta, ashe so shine yaci amanarta, ashe Zaid bai aikata mata wani babban laifi ba So ne ya aikata mata laifi me girma, inama da ana ganin so, to da tayi masa roƙo takuma yi masa magiya akan cutarwar da yayi mata daya barta haka,,   itakuma SO shine ƙaddaranta, ada ta ɗauka idan tafaɗawa mutane cewa tanason mutumin dayayi sanadiyar rugujewar rayuwarta, kowa zai ɗauketa mahaukaciya wacce batasan me takeyi ba, amma kuma ayanzu tagane cewa wanda duk ya mata kallon mahaukaciya akan soyayyar da takeyia Zaid, to ko kaɗan baisan menene SO ba, SO shine wanda ke sauyawa mutum tunani alokaci ƙanƙani batare daya shiryawa hakan ba, SO shine wanda ke makantar da idanun mutum yazamanto bayaji baya gani, haka kuma tasanadiyar SO wasu ke salwantar da rayuwarsu, SO shike sawa kabi wanda baidace dakai ba, SO shike sawa amaka wulaƙanci amma kuma gobe ka koma inda aka wulaƙanta ka, SO shike sawa mutum yazalunceka amma kuma bazakaga laifinsa ba,kuma koda ma kagani bazaka iya juya masa bayaba, SO yana da matuƙar haɗari sannan yafi kowani abu saurin ɗaiɗaita tunanin meyinsa, SO shikaɗaine abun da zafinsa ke narkar da zuciya,,,,SO shine babban jagoran zuciya haka kuma shine raunin ta,,  hanu ta sanya takuma dafe kanta wanda takeji kamar zai zazzago ƙasa,, hmmm kamar dai yanda Zahrah taga rana haka taga dare bacci sam yaƙauracemawa idanunta.....

(Kada kuga laifin Zahrah dan ta ci gaba da son Zaid, haƙiƙa Zaid ya cancanci Zahrah taƙisa mugun ƙi mawa kuwa, amma kuma SO bazai taɓa barin haka yafaru ba, wallahi Soyayya tawuce gaban kwatance, so babu ruwanshi da wai ancutar dakai ko ba a cutar dakai ba, shi so kaitsaye yake abunsa batare da yatambayeka shawara ba,  nikam bana ganin laifin Zahrah dan taso Zaid domin shi so baya fita acikin sauƙi, sannan kuma zafinsa yanada matuƙar illa, ba'akanta aka fara ba, sau da dama zakuga namiji yana zagi dakuma dukan matarsa amma kuma duk da haka tanazaune dashi saboda tana sonsa, haka kuma saudadama zakuga Saurayi yayi amfani da soyayyar da budurwarsa takeyi masa ya yaudareta sun aikata zina, daga baya kuma idan ciki yashiga jikinta sai kuga yagujeta, saboda yasamu abun dayakeso daga wajenta, amma kuma idan harson gaskiya takeyi masa saikuga bata daina sonsaba duk dakuwa irin girman abun dayayi mata,, wallahi soyayyar gaskiya bata taɓa gushewa koda kuwa girman laifin da mutum ya aikata maka bazai misaltu ba, haƙiƙa idan banda sharrin SO babu wata mace da namiji zaiyi mata fyaɗe kuma ta dawo tacigaba da sonsa, wannan sharrin SO ne kawai wanda bashida magani😭 nidai nace ko guba baikai so hatsari ba, wallahi so mugune, inkun ganshi kukamaminshi kumai duka😰)

Ƙarfe 2 na dare ciwon Zaid yatashi sosai, abun gwanin ban tausayi, zuwa yanzu kam ciwon nasa yasoma fin ƙarfin tunanin Doctor's domin kuwa sai anyi tunanin cuta tayi sauƙi saikuma tadawo, yanzu haka bincikensu yanuna musu cewa zuciyarsa ce takumbura, gaba ɗaya hankalin Alhj Ma'aruf yakai ƙololuwa wajen tashi, Mum kuwa yanzu bata da aiki saina kuka dare da rana, hakanne ma yasanya Alhj Ma'aruf yanke hukuncin tattara Zaid ɗin sutafi Jermany, saboda ya ga abun yana nema yafi ƙarfin likitotinmu na nan, saboda koda yaushe Zaid  cikin aman jini yake, lokaci ɗaya ya lalace yayi wani irin rama, kamar ma ba
Zaid ba.....

Washe Gari (Asabar)

*ƊAURIN AURE*

Tun ƙarfe 8 na safe  gidansu Zahrah yake acike yayinda ƴan uwansu na nesa suka soma hallara don ɗaurin aure,, hayaniya ne ke tashi kota ina acikin gidan...

Ɗakin Zahrah na garzaya don inga awani hali take ciki...

Kwance take akan katifarta yayinda duka jikinta ke rufe da bargo, amma duk da haka bargon bai ɓoye rawan da jikin nata keyi ba, karkarwa kawai takeyi acikin bargon yayinda jikinta yaɗauki zafin zazzaɓi zau..

"Kitashi kisha maganin nan dan Allah Zahrah, kinga fa babu amfanin zama da ciwo batare da kinsha magani ba" Husnah tafaɗi haka ga Zahrah cike da lallami..

Kai kawai Zahrah ta'iya kaɗawa alamar "A'a bazata sha ba" komagana ma yanzu bata iyayi saidai kawai ta kaɗa kai, hakan yafarune kuma saboda ciwon kai me tsanani da ta tashi dashi a safiyar yau ɗin,, duk yanda Husnah takaɗa ta buga akan Zahrah tatashi tasha magani ƙiyawa tayi, sai ruwan hawaye dake ta fita daga cikin idanunta, dole haka Husnah ta ƙyaleta..

10:30 tuni ƙofar gidansu Zahrah yasake cika da jama'a  bamasaka tsinke, hayaniya ne kawai ke tashi tako ta ina, yayinda tsala tsalan motocin ango suka ƙaraso,, hmmm Dr.Sadeeq yasha kyau sosai cikin wata  haɗaɗɗiyar gezina milk colour me matuƙar kyau da tsadar gaske, ɗinkin rigane da wando saikuma gare, amma kuma sunyi masa kyau sosai, yayinda ya ɗaura tsadadden agogo a hanunsa na dama,  takalmin ƙafarsa kuwa ƙirar kamfanin GUCCI ne me matuƙar kyau,, ango fa yasha kyau iya kyau, sai yau nima nasake tabbatarda cewa shiɗin ma wani Handsome guy ne mezaman kansa, domin kuwa duk ƙwaƙwan mutum babu ta'inda zai kushesa, yahaɗu iya haɗuwa sonkowa ƙin wacce ta rasa😜,  bakin ango fa yaƙi rufuwa sai murmushi kawai yake, yayinda abokansa keta tsokanansa,, shidai kawai murmushi yaketa zubawa, bazai taɓa iya misalta irin tarin farincikin dayake ciki ba, haƙiƙa yau yana cikin nishaɗi dakuma jin daɗi, yau takasance babban rana agareshi ranar da duk wani gauro da gauruwa suke jira, ranar da duk wani mai hankali da nutsuwa yake biɗar zuwanta wato RANAR AURE, shikam sai dai yace Alhmdlh yagodewa Allah mai kowa me komai daya nuna masa wanann rana... Baffa na hango shima yau cikin farinciki yake, yasha adonsa cikin farar shaddansa riga da wando dakuma gare, su uban amarya manya,,,     11:00 am   dai dai dandazon jama'a suka shaida ɗaurin auren SADEEQ KHABEER SARDAUNA (Dr.Sadeeq) da amaryarsa FATIMA ADAM (Zahrah) akan sadaki naira dubu ɗari,,  masha Allah ana kammala ɗaurin aure aka soma taya ango murna da Allah yasanya alkhairi, ae kuwa fuska asake haɗe da tarin annuri Dr.Sadeeq ke amsawa, hamdala kawai yakeyi acikin zuciyarsa shikenan Zahrah ta zama tasa mallakinsa halaliyarsa... Bayan angama musabahane kuma aka ɗunguma zuwa wani babban hotel wanda anan za'a gudanar da receiption....

Lokacin da labari ɗaurin auren ya'isa ga kunnen Amarya wani irin faɗuwar gaba wanda bata taɓa jin irinsa ba taji ya rusketa, shikenan yanzu tazama matar Doctor,  zuciyar tane tashiga bugawa da sauri sauri yayinda har ƙirjinta yasoma amsawa, take taji wani abu maikama da tsananin tsoro ya lulluɓe mata jiki,ae kuwa sai neman ɗan kuzarinta tayi ta rasa,jitayi gaba ɗaya gaɓoɓinta sun mutu laƙwas kamar ansassare mata su,, sake duƙunƙunewa tayi acikin bargo tashiga rera kuka marar sauti,  ita bata tsani Dr.Sadeeq ba ko kaɗan, amma kuma tarasa meke damun ƙwaƙwalwa da zuciyarta....

(Kuyi haƙuri Team Zaid wallahi nima Allah jikina gaba ɗaya yayi sanyi sai dai kuma kunsan ita ƙaddara bata taɓa sanjawa dole saitazo a yanda Allah ya aikota😭 yanzu haka jinake kamar ruwan jikina ya ƙare😥)

Ƙarfe 2 dai dai jirginsu Zaid yatashi daga cikin garin Lagos Nigeria zuwa Jermany saidai shi Zaid sam baisan wainar da ake toyawa ba saboda baya cikin hayyacinsa kwata kwata, tunda suka baro Abuja har suka iso Lagos baisan inda kansa yake ba....

Ɓangaren ango kuwa reception aka gudanar gangariya, anci kaji ansha fruits juice kowa cikin sa yayi haniƙan sai dai godiyar Allah da sanya albarka...

Amarya kuwa koda ruwane takasa sanyawa acikin cikinta, rashin lafiya sosai ya tsananta a gareta, zuwa yanzu kam hawayen ma sun kafe sundaina fitowa, sai numfashin wahala da take fitarwa ta bakinta kawai,, kasancewar anata hidima yasa babu wanda yadamu da cinta kokuma shanta, Husnah ce kaɗai ke tsaye akanta tana bata kulawa. 

"Dan Allah Zahrah ba danniba kitashi inrakaki toilet kiyi wanka kizo kisamu koɗan sabon kayane kisanya kingafa zuwa anjima za'a zo ɗaukarki!" Husnah tafaɗi haka tana me ƙoƙarin tada Zahrah dake kwance zaune.

Da taimakon Husnah Zahrah taje banɗaki tayi wanka, koda tafito wata haɗaɗɗiyar doguwar rigar atamfa Husnah ta bata tace ta sanya, babu musu tasanya saigashi kuwa rigan tayi matuƙar yi mata kyau ajiki, da ƙyar Husnah ta lallaɓata tashafa mata powder haɗe  da man leɓe, sai kace wata ƙaraman yarinya,,,   komawa gefe Zahrah tayi ta takure bayan Husnah tagama shiryata, still Husnah maganar abinci tayi mata amma Zahrah tasake bushe idanunta tace ita sam bazataci abinci ba batajin yunwa  (Ninaga jarfa saikace wanda aka mawa auren dole 😏)...

Ƙarfe 5 tsala tsalan motocin ɗaukar amarya suka shiga fakawa a ƙofar gidansu Zahrah motocine reras masu kyau har guda 15 suka zo don ɗaukar amarya yayinda motar da amarya zata shiga ta banbanta da duka sauran motocin don tafi duka sauran kyau..

Zahrah na zaune wata Aunty Ladi ƴar uwar mahaifiyarta wacce tazo daga Niger tashigo cikin ɗakin babban mayafi  me kyau ta ɗauka haɗe da rufe Zahrah dashi, miƙar da'ita tsaye tayi cikin farinciki tace
"Allah yayi yauzaki tafi ɗakinki amarya muje ɗakin Inna'n taki aimiki nasiha"
aitun kan aƙarasa ɗakin Inna Zahrah ta ɓarke da kuka wiwi,  (Wayyo Allah, wallahi duk rashin daɗin gidanku randa zaka barshi saikaji ciwo acikin ranka harna tuna da nawa ranan 😭🙈)

Nasiha Inna da sauran matan dake ɗakin suka shiga yi mawa Zahrah akan tabi mijinta sauda ƙafa inayi bari na bari, komin ƙanƙantan ɓacin ransa ta gujesa, duk kuma wani abu datasan bayaso kada ta aikata, sannan kuma taji taƙi ji tagani taƙi gani,  takuma riƙi haƙuri don shine tubali kuma gini haka ƙinshiƙin zaman aure, bawai idan anyi aure kullum soyayya ake ci ba, a'a watarana dole sai kunɓatawa juna, dole sai kunyi haƙuri kundanni zuciyarku tukun zamanku zaiyi daɗi, sannan kuma idan tasan tayi masa laifi kada tayi girman kai, tasameshi har ƙasa ta duƙa tabasa haƙuri, domin kuwa har kullum shine sama da'ita, yanzu amatsayin uba yake agareta bata da wani wanda yafishi,, wayyo Allah Zahrah tayi kuka sosai harda shiɗewa, Allah sarki sabo turken wawa duk da cewa Inna watarana tana hantararta amma yau duk saitaji babu daɗi tafiyan Zahrah'n saiga Inna tana hawaye tana jan majina, shikenan Inna kuma fa cin kaza ya yanke mata lol 😂.

Su Inna suna gama nasu nasihar aka garzaya da'ita wajen Baffa,, wayyo Allah Zahrah tana ganin Baffanta ta faɗa jikinsa haɗe da sake ƙara volume ɗin kukanta, Allah sarki take Baffa shima yasoma hawaye,  daƙyar ya'iya daure zuciyarsa yayi mata nasiha, duk dai maganar ɗayace shine tabi mijinta sau da ƙafa takumayi masa biyayya akan duk abun dayace, sannan kuma tazamo me haƙuri akan dukkan komai, sannan kuma yaroƙi yafiyarta akan abun dayayi mata baya, tana kuka tace tajima da yafe masa kuma ita baimata komai ba, itama tanemi yafiyarsa yakumace ya yafe mata😭

Haka Aunty Ladi da Husnah suka fita da Zahrah  tana kuka Husnah kanta kuka take, yanzu itama haka watarana za'a zo a ɗauketa daga gaban Momynta akaita can cikin wasu dangin😭...

Anasa amarya acikin mota sauran ƙawaye da ƴan uwa ma kowa yashiga motar da ransa keso, bayan komai yakammalane  motocinnan suka gangara kantiti, atare suke tafiya wani abayan wani, sannan kuma komai anitse akeyinsa babu wani hargowa...

Direct gidansu Dr.Sadeeq aka wuce da amarya, domin kuwa 8:00 pm nayi za a wuce wajen diner...

Abun mamaki tarba me kyau Hajiya tamawa amarya dakuma danginta, ko kaɗan bata nuna musu ɓacin rai kokuma tsana ba, sai dai su Aunty Raliya dasuketa binsu da wani irin kallo dake nuni da cewa baƙaunarsu sukeyi ba, ɗaki guda aka warewa amarya, balaifi ɗakin yayi kyau sosai, akan gado Aunty Ladi ta zaunar da Zahrah,  mintuna kaɗan da shigowansu ɗakin wasu ƴan mata suka cika musu gabansu da kayan ciye ciye dakuma na sha abun gwanin burgewa, gaskiya sun samu tarba na mutumci daga Hajiyar Doctor......

Wayar Husnah ce tafara ruri ganin wanda ke ƙiran nata yasanya ta ɗaga wayar bawani ɓata lokaci 

"Bestie'n mu how far?"  abunda wanda yaƙirata acikin wayar yafaɗa kenan..

Dariyane yakamata amma saita taƙaita dariyan haɗe da cewa "I'am fine sai dai gaskiya na gaji"

Murmushi shima yayi haɗe da cewa "Ina Amaryata Allah yasa tana lafiya, nayi kewarta sosai rabona da'ita fa tun ranan alhamis" Dr.Sadeeq yafaɗi haka yana me gyara kwanciyar dayayi akan gadonsa...

"Kamar kuwa kasan kainaketa so kaƙira, wallahi yau tun safe Zahrah taƙicin komai kuka kawai takeyi, gashi bata da lafiya temperature ɗinta ya hau sosai"  Husnah tafaɗi haka ga Dr.Sadeeq.

"Subahannallah, keda su waye aɗakin?" Dr. yatambayi Husnah cike da zaƙuwa..

Kallon waƴanda ke cikin ɗakin Husnah tashiga yi kafun tace

"Gaskiya munada ɗan yawa"

"Oh my God to shikenan, please anjima kikawomin ita ina cikin boys guaters kinji"

"To shikenan zan kawota insha Allah"

Daga haka suka kashe wayar murmushi kawai Husnah tayi bayan ta'ajiye wayar tata gaskiya azamaninnan idan mace tasamu wanda ke sonta kamar irin sonda Dr keyiwa Zahrah yakamata ta riƙeshi da kyau hanu tara tara domin samun irinsu wahalane dashi, saboda yanzu zuciyoyin yawancin mutane duk taɓaci da yaudara.........

*Inasonku masoyana na Wattpad irin sosai ɗinnan, ina yaba ƙoƙarin ku wajen min comment, Allah yabar ƙauna*

*Kuɗin ma ae nadabanne masoyana na Whatsapp inajin daɗinku sosai iya wuya muna jone Insha Allah*




*Comment*
*Share*
*and Voted please*

         

          *Fatymasardauna*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

       *SHU'UMIN NAMIJI !!*

    *Written By*
Phatymasardauna

*Dedicated To My Brother KHABIER*

*🌈Kainuwa Writers Association*

_{United we stand and succeed; our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}_

*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*

             *WATTPAD*
       @fatymasardauna

*Editing is not allowed📵*

       *CHAPTER 90 to 91*

Saida kusan gabaki ɗaya mutanen da suka kawo Zahrah suka soma watsewa zuwa wajen dinner, kafun Husnah ta matso kusa da amarya Zahrah wacce take aikin kuka.   Hannayenta takamo haɗe  da zama gaf da'ita.

"Please Zahrah kidaina wannan kukan, yanzu haka Doctor yace inkai masa ke yana boys guaters, kuma kinga babu amfanin kije wajensa kina kuka" Husnah tafaɗi haka ga cikin lallashi.

Zahrah dai bata kumace da'ita komai ba bata kuma daina kukan ba,,  wayar Husnah ce tayi ƙara alamar shigowar ƙira, sunan Dr.Sadeeq ne keyawo akan screen ɗin wayar,,  tana kara wayar akan kunnenta yace

"Yadai Husnah, najiku shiru"

Sake kallon mutanen da sukayi ragowa acikin ɗakin Husnah tayi.  
"Gaskiya babu dama Doctor, saboda dazaran anga zamu fita za'ace ina zankaita" Husnah tafaɗi haka cikin ƙasa ƙasa da muryarta....

Ajiyar zuciya Dr.Sadeeq yayi haɗe da cewa
"Okay to bakomai zan san yanda za'ayi, ku shirya me meckup tana nan zuwa"

Cikin matsanancin ciwon kan dake ɗawainiya da'ita tashiga toilet ta ɗauro alwala, kan ƙaton darduman dake shimfuɗe a tsakiyar ɗakin ta hau ta kabbara sallah'n magriba,, tana idar da sallan meyi mata meckup ta ƙaraso, haka tanaji tana gani ta bada fuskarta aka zizara mata meckup wanda yaɗauki fuskarta sosai..  Yauma dai meyin meckup ɗinne ta shiryata tsab cikin wata haɗaɗɗiyar doguwar riga (wedding gown) na wani tsadadden leshi me matuƙar kyaun gaske, riga ce doguwa har tana sharan ƙasa yayinda bayan rigar aka

Please Login or Register in order to submit comment