Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wasu kayan nanan zuwa.

Kulawa Zahrah take samu a wajen Hajiya sosai, idan kaganta ma kamar ba itace ta haihu ba, sosai jikinta ya murje, tasakeyin fresh, hasken fatarta ma sosai ya ƙaru, komai nata ya cika, taƙara kyau akan nada, shikansa Dr.Sadeeq idan yaganta, ko son ɗauke idanunsa  akanta bayayi, saboda yanzu tasake zama wata mace ta musamman,  duk inda ta zauna kuwa ƙamshi take rabawa.

Ranar suna yaro yaci sunan baban Zahrah wato Adam, za'ana ƙiransa da (Asad) lokacin da labarin sunan  da aka sawa yaro yazo kunnen Zahrah sosai taji daɗi, wani irin farinciki taji acikin ranta, girman Doctor kuwa ya ƙaru acikin idanunta, ta tabbatar cewa shiɗin mai so da ƙaunarta ne.
Da sassafe meyi mata meckup tazo ta tsantsara mata ado, sosai fuskarta tasha kwalliya,  wani haɗaɗɗen lace orange and milk colour tasanya ajikinta, wanda yaji ɗinkin riga da sket irin 12 piecess ɗin nan, sosai kayan sukayi mata kyau, domin sunja kuɗi wajen sayansu da ɗinkasu, kowa yaga Zahrah da babynta saiyace masha Allah. Saboda  sunsha kyau sosai. Hidima sosai akayi tundaga kan abinci da abun sha, har izuwa abubuwan da za'a rabawa baƙi,  akwati guda biyu Hajiya tayiwa Zahrah da ɗanta, haka Baffa ma akwati yayi mata Inna ma zagewa tayi tayiwa Zahrah akwati shaƙe da kaya, Auntie Raliya ma akwati ta mata,  sosai Zahrah tasha kaya, har rasa inda zata sa kayan tayi,  ana cikin haka saiga kayan Dr.Sadeeq sun iso, akwatuna huɗu, biyu natane shaƙe da kaya,  sauran biyun kuwa  na yarontane,  bata gama mamakin irin dukiyar da Dr.Sadeeq yakashe mata ba, saiga Aunty Raliya tana rangaɗa guɗa, hanunta riƙe da key, danƙawa Zahrah key ɗin tayi ahanunta, haɗe da cewa "Ungo amsa kyautace ta musamman daga mijinki, ya baki kyautar gidansa dake cikin asokoro" mamakine ya kusan kashe Zahrah

"Gida kuma Aunty?" ta tambayi aunty Raliya don tayi tunanin ko kunnuwanta ne basu jiye mata da kyau ba.

"Ƙwarai kuwa gida, saima kinga gidan, don gidane me tsananin kyawun gaske, yafa kashe kuɗi sosai wajen ƙawata gidan"  Inji cewar Aunty Raliya.

"A'a Aunty gaskiya nikam banaso, wani irin kyautane haka? hidimar da Doctor yakeyi dani tayi yawa, daga haihuwata zuwa yau yakashe kuɗi yafi 3 million fa Auntie, yanzu kuma yace yabani kyautar gida suku tum, inajin tausayinsa Aunti banason nazama rauni acikin arzikinsa" Zahrah tafaɗi haka da iyaka gaskiyarta.

Murmushi Auntie Raliya tayi haɗe da sanya hanu ta dafa duka kafaɗun Zahrah.

"Kada ki damu Zahrah, shi ɗinfa mijinki ne, kuma kome zaimiki aduniyarnan bazai biyaki ba, kamar yanda kema bazaki iya biyansa duk abun daya miki ba, saboda haka babu wani abun damuwa don yamiki wannan kyautar, kin cancanci hakanne agareshi, don haka amshi makullin gidanki, ke dai kawai kiyi masa godiya, irin wacce ta dace" Aunty Raliya ta faɗi haka tana me damƙawa Zahrah makullin gidan ahanunta.

Kuka Zahrah ta fashe dashi tana jin ƙarin ƙaunar mijinnata na huda mata zuciya, lallai yazama dole agareta taƙara ƙaimi wajen kyautata masa. 

Yamma nayi aka haɗa walima me rai da lafiya, bayan malama tazo tagabatar da wa'azine akayi ciye ciye, aka kuma sha drinks, duk wanda yazo sunan kuwa babu wanda baisamu kyaututtuka ba, abun sai dai ace Alhamdulillah, kafun magriba tuni mutane sun watse, gida ya saura daga Hajiya sai Zahrah da kuma Aunty Raliya.

Wanka tasakeyi ta tsantsara ado cikin wani irin meterial me kyau da tsada, wanda yana cikin kayan da Doctor ya ɗinka mata don fitan suna, doguwar riga akayi mata wanda ya matuƙar kama jikinta sosai,  dogon gashinta dayasha saloon ta kanannaɗe atsakiyar kanta, ba abun dake fita ajikinta sai ƙamshin humra dana body spray.
Zama tayi akan gado haɗe da ɗaukan wayarta tashiga kan whatsapp, yaronta kuwa tuni dama yana wajen su Hajiya dake zaune a falo suna hira,   Sadiya me aikin Hajiya ce tashigo cikin ɗakin haɗe da sanarwa Zahrah cewa wai tayi baƙo yana falo.
Jitayi gabanta yaɗan faɗi, amma saita dake tace da Sadiyan tace da baƙon tana zuwa.
Mayafi ta ɗauka ta yafa ajikinta, kana ta zura flat shoe ɗinta, tafice daga cikin ɗakin.

Su Hajiya tasamu zaune afalon, sai kuma wani, wanda bata ma taɓa ganin fuskarsa ba.  Kafun takai ga gaishesa, shiya ɗago mata gaisuwa, amsawa tayi tana ɗan murmushi,    gyara tsayuwansa yayi haɗe da cewa..

"Saƙone dama akabani nakawo miki, yana waje, idan ba damuwa muje saiki gani"

Kallon tsoro tashiga yi masa, saboda batasansa ba balle tasan wanene ya aikosa.

"Badamuwa, Raliya rakata sai kuje kuga saƙon ko"
Hajiya tafaɗi haka, don ta lura da tarin tsoron daya bayyana akan fuskar Zahrah'n.

Hakan kuwa akayi tare suka fita da Aunty Raliya.

A compound ɗin gidan suka tsaya gaban wata haɗaɗɗiyar mota ƙirar mercedes maroon colour,  mutuminne ya bubbuɗe ƙofofin motar, take kayan dake shaƙe acikin motar suka bayyana, ɗan makulli ya miƙowa Zahrah haɗe da cewa
"Ranki ya daɗe gashi ni nacika umarnin da aka bani, wannan kyautace daga megida na, yace na ce miki Allah ya raya" 

Mamaki haɗe da al'ajabi ne suka kama Zahrah da Aunty Raliya. 

"Kyauta daga me gidanka kuma? wayeshi to?" Zahrah tayi masa duka waƴannan tambayoyin cike da son jin amsa, haɗi da kuma mamaki, gani take kamar mutumin baida cikakken hankali.

Murmushi kawai ɗan aiken yayi haɗe da sake miƙo mata makullin motar  yace
"Kiyi haƙuri bai bani damar sanar miki dashi ɗin kowaye ba, amma yace dan Allah ki karɓa"

Ta buɗe baki zatayi magana kenan motar Dr.Sadeeq ta kutso kai cikin gidan.
Kasa cewa komai tayi har Dr.Sadeeq yafito daga cikin motarsa, ya ƙaraso garesu,  kallonsa Zahrah tayi shima kallonta yakeyi. 

"Hajiya ga makullin ni zan wuce" wannan mutumin yafaɗi haka, yana sake miƙa mata ɗan makulli.

"Ko ma waye ya aikoka, kace masa banaso, don bana buƙata" tafaɗi haka tare da juyawa daniyar komawa inda ta fito.

"Zahrah!"

Sunanta da Dr.Sadeeq yaƙirane yasanyata tsayawa cak haɗe da juyowa tana kallonsa.

"Zoki amsa, ki kuma yi masa godiya" Dr.Sadeeq yafaɗi haka, yana me karantar yanayinta.

Cike da mamaki tace "Amma..."  

"Banaso kice komai ki amsa kawai nace" yakatseta daga maganar da take ƙoƙarin yi.

Jiki asanyaye ta karɓi makullin motar.
Ciki ciki tace "Kace nagode"

   "To" kawai ɗan aiken yace kana ya juya yafice daga cikin gidan.

"Wai meke faruwa ne, waye ya aikosa?" Aunty Raliya ta tambayi doctor, don ta lura kamar yana da masaniya akan wanda ya aiko motar da cikinta ke shaƙe da kaya.

Murmushi Doctor yayi haɗe da cewa "wani aminina ne dake zaune a Dubai, shine dana gaya masa ta haihu yayi mata wannan kyautar"

Dafe ƙirji Aunty Raliya tayi tare da cewa
"Lallai wannan koma wayeshi yanaji da naira,  wannan motarfa zatakai 4million inma bata fi ba, ga kuma kayan dake cikinta, wanda suma kaɗai sun haura 1m, me kenan yake nufi?"

"Babu wani abun da yake nufi Aunty, haka dama shi yake kyautarsa, muje ciki ko" yaƙare maganar yana kallon Zahrah wacce ta daskare a wajen. 

Cike da mamakin kyautar abokin Doctor ɗin Aunty Raliya taja ƙafanta takoma falon Hajiya,  Zahrah ma jikinta a sanyaye tabi bayanta, shima falon yanufa, yanda yaga tana tafiya asanyaye ne yasanyasa yin murmushi kawai.
Bata tsaya a falon ba direct ɗakin dayake masauƙinta ta wuce, tsayawa tayi a gaban mirror zuciyarta cike da tarin tambayoyi  kala kala, sam bataji zuciyarta ta aminta da kyautar nan da'akayi mata ba, kwata kwata  batama yarda cewa wai abokin Doctor bane ya bata.  Tana acikin tunanin, yaturo ƙofar ɗakin yashigo bakinsa ɗauke da sallama.

Amsa masa sallaman nasa tayi haɗe da zuba masa idanunta, dagani kai kasan tambayoyine cike a bakinta.

takowa yayi ya ƙaraso daf da ita, hanunsa yasanya ya jawota jikinsa, saida yashaƙi daddaɗan ƙamshin dake fita ajikinta, ya sauƙe ajiyar zuciya, kana yace.

"Kinyi kyau sosai"

Murmushi ta ƙaƙalo haɗe da cewa.   "Nagode"

Cikinsa yashafa  tare da cewa. "Yunwa nakeji sosai, nayi missing sweet cook ɗinki, please ko zaki kawomin abinci?"

"Meyasa kake barin kanka da yunwa? kasan banaso, yanzu me zakaci na kawo ma?" tatambayeshi cike da kulawa.

"Koma me idan kika kawomin ni mai iya ci ne" yafaɗi haka yana me zama a bakin gado.

Harta kusa fita daga cikin ɗakin sai kuma  ta tsaya cak,  haɗe da juyowa, idanunsu yafaɗa cikin na juna, domin dama shima kallonta yake.

"Waye ne yaturomin da mota? Nasan kasan ko waye, domin zuciyata tafaɗamin cewa,  ba abokinka bane ya turo, kamar yanda kafaɗa a baya" tambayar da tayi masa kenan, cike da burin samun amsa agareshi.

"Baki yarda da abun dana faɗa ba kenan?"   ya tambayeta yana me ƙara tsareta da manyan idanunsa.

Murya a sanyaye tace "Kayi haƙuri, bawai ina nufin kamin ƙarya bane, kawai dai naji zuciyata ce bata gamsu da amsar da ka bayar ga Aunty Raliya ba"

Murmushi yayi haɗe da cewa "Zuciyarki tafaɗa miki gaskiya, domin kuwa ba abokina bane yaturo kamar yanda na faɗa a baya"

Waro idanunta tayi, duk da zuciyarta ta raya mata cewa ba abokinnasa bane, amma kuma duk da haka bata tsammaci jin haka daga bakinsa ba.

"Waye?" tatambaya murya na rawa.

"ZAID" yabata amsa ataƙaice...

  
(Nagaji kuyi manage, idan nasha ruwa zan ɗora daga inda na tsaya)

      *29/February/2020/*

 
*✔️OTE ME ON WATTPAD*
          @fatymasardauna

#Love
#Romance

#One Love My Wattpadians
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

    *SHU'UMIN NAMIJI !!*

    *Written By*
Phatymasardauna

*Dedicated To My Brother KHABIER*

*🌈Kainuwa Writers Association*

         *WATTPAD*
  @fatymasardauna

     *Chapter 116*


"ZAID!" ta maimaita sunan abakinta cike da tsananin mamaki.

Yanda yaga jikinta na ɓari shine abun daya basa mamaki, zallan tsoro ya hango kwance akan fuskarta, yayinda cikin idanunta kuwa, suka bayyana soyayyar dake kwance acikinsu, wato soyayyar ZAID, shi yasani ba tun yauba, bakuma zai yaudari kansa ba, yasani ƙwarai Zahrah na son Zaid, so ba irin na wasaba, so matsananci, amma kuma babu yanda zaiyi, dayana da iko to daya cire mata son Zaid acikin zuciyarta, amma wannan banasa bane, na Allah Ne, yasan Zahrah tana sonsa, amma soyayyar da takewa Zaid ta dabance,  da ace zai iya, to daya danne zuciyarsa, ya miƙata ga Zaid, yasan hakan zai samarmusu da farinciki, ita da Zaid, amma kuma yasan koda yayi hakan to ba mafita bane, domin ayanzu yasan dole idan baya tare da Zahrah tayi kewarsa, yana sane da cewa yakafa mata tutar son sa, wanda bazata ankara da hakan ba, har sai randa yazama baya tare da'ita, baya fatan wata ƙaddara ta rabasu, amma yasani ko mai daren daɗewa sai sun rabu, saboda akwai mutuwa, koshi ko ita, watarana ɗaya dole zai bar ɗaya, yau idan baya raye, baya fata Zahrah ta auri wani namiji idan ba Zaid ba,  tunaninsa yayi nisa, baisan da cewa ta ƙaraso inda yake ba, saida yaga ta zube a gabansa, tana kuka, cikin muryar kukan takecewa.

"Kada kamin haka doctor, wallahi ni banason duk wata kyauta da zatafito daga garesa,  namantasa acikin rayuwata, banaso kuma nasake tunasa, kamayar masa da kyautarsa, bana buƙata farincikin da kake bani kaɗai ya isheni"

Tunda tafara maganan yake kallonta,  ajiyar zuciya yayi, haɗe da kamo hannayenta, cikin murya me sanyi yace.  "Kinsani bakyau maida hanun kyauta baya, meyasa to zakiyi haka? mekike tunani akan Zaid?" ɗan dakatawa da maganar yayi, tare dayin wani murmushi, kana ya miƙe tsaye, daga zaunen da yake.
 
"Kyautace kawai ya miki, ai atunanina hakan ba wai yana nufin wani abubane,  bazan tilasta miki ba, amma nasan abundake cikin zuciyarki, don gashi har a idanunki sun nuna, so ba ƙarya bane Zahrah,  haka kuma ba laifi bane, don zuciya na dakon so, wannan ma wata ƙaddarace, wanda babu wani wanda ya isa ya kauce mata"  yanakai ƙarshen zancen nasa yanufi hanyar fita daga ɗakin.

Da sauri taje ta faɗa jikinsa, kuka take sosai, durƙusawa tayi haɗe  da zube  guiwowinta a ƙasa, kana ta riƙe rigarsa, kanta tashiga girgizawa, tana kuka tace.    "A da na sosa fiye da yanda naso kaina, amma ayanzu baya acikin zuciyata kamar yanda kake tunani,  Inasonka da duka zuciyata, bana fatan wata ƙaddara tazo wacce zata rabani dakai, kabani farinciki, kajiyar dani daɗi, kashayar dani zuman soyayyarka, bazan iya watsa maka ƙasa idanunka ba, kai mijinane wanda bayan kai bani da wani tamkarka,   nasan kai ɗin me sonane, amma meyasa kayi haka? mai yasa kai da kanka, zaka amince da na karɓi kyautar wanda yazama silar rugujewar rayuwata?"

Durƙusawa yayi agabanta, haɗe da sanya hanunsa ya share mata hawayen dake gudu akan fuskarta, cike da kulawa yace.   "Banason kukanki Zahrah, keɗin wata babban jigo kuma mahaɗi ne acikin rayuwata,  nasan Zaid ya cutar da rayuwarki, amma kuma hakan bazai hana ki amshi kyautarsa ba, ayanzu kowa yasan cewa ke matatace, saboda haka Zaid bazaiyi miki kyauta da wata manufa ba, kuma kafun ya miki kyautar saida ya tambayi amincewata tukunna, nakuma amince masa,  nayarda da Zaid Zahrah, nasan idan duka mutanen duniya zasu taru su cutar dake, to Zaid bazaiyi hakan ba, haka kuma idan ni zan iya cutar dake, to ina tabbatar miki idan Zaid yasan da hakan, to  bazai bari na cutar dake ba, Zaid ɗin da kikasani ada bashine wanda yake a yanzu ba, kada kiyi tunanin wai ko zanji haushi akan kyautar da Zaid yayi miki, niba jahili bane Zahrah, haka kuma halina ya banbanta da na wasu mazan, ni mutum ne me saurin fahimta, sannan kuma abune mawuyaci nayiwa wani na mummunan zato,  agurin wasu mazan, hakan zai iya zama matsala, amma a wajena hakan ba komai bane, tunda nasan cewa keɗin tawace ni kaɗai, bakuma wai don bana kishinki bane yasa hakan tafaru ba a'a, ni kalan nawa kishin ba irin na wasu bane,  inakishinki sosai, sai dai kuma kome acikin nutsuwa nakeyinsa, ke kinsan inasonki ina kuma kishinki " yaƙare maganar yana me lakace mata dogon hancinta.

Kukane yakuma ƙwace mata sai kawai tafaɗa jikinsa, ta rungumesa ƙam, shima rungumeta yayi yana shafa bayanta ahankali, haɗe da hura mata iskan bakinsa, acikin kunnenta.
Saida tayi kukanta sosai, kafun ta soma sauƙe ajiyar zuciya,  cikin murya me sanyi tace.
"Kai na da banne Mijina, irinka basu da yawa acikin duniya, haƙiƙa nafi kowacce mace sa'a dana sameka,  dakai kaɗai zan rayu har izuwa mutuwa ta, kaima ka rayu dani ni kaɗai kaji, bazan iya jure ganinka da wata mace ba bayanni, Ina maka son da bansan iyakarsa ba!"

Murmushinsa dake ƙara masa kyau yayi, haɗe da sanya iskan bakinsa ya hura mata fuska.

"Dake kaɗai Zan rayu Zahrah na, ni nakine ke kaɗai,  amma idan kina kukan nan fa, dole zan ɗan yi ƙasa da idanuna, na hango wata, saina kawota ko wanke wanke ne tanayi mana ko, idan dare yayi kuma sai ina raba muku kwana ko..."

Bata bari yakai ƙarshen zancen nasa ba, ta muntsine sa aciki, saida yasaki wata ƴar ƙaramar ƙara,   cike da shagwaɓa tace "Wallahi nidai babu ruwana dakai, idan dai har kace zakamin kishiya!"

Dariya yayi sosai haɗe da cusa kansa acikin ƙirjinta.  "Ni na isa ma nayiwa ƴar sakalalliyar matata kishiya,  amma bandai saniba wataƙila idan naga kin tsofe na miki!" yanzuma cikin zolaya yayi maganar.

Hannayenta tasanya acikin gashin kansa, tashiga ya mutsawa, hadda kai masa cizo a wuyansa.   Sai da tayi masa buji buji da kayan jikinsa kafun ta ƙyalesa, gashin kansa ma gaba ɗaya ta hargitsa masa shi.  Koda ta kawo masa abinci tare sukaci, yana kwance ajikinta itakuma tana bashi abincin abaki,  ahaka har ya ƙoshi.

Kallonta yayi da idanunsa, dake tsumata kana yace "Namatsu abani ke Baby na, wallahi ina kewar ɗumin ki sosai, amma Hajiya gaba ɗaya ta kanenaye min ke, waidole saikinyi arba'in, Babyna kice tabarmu mu koma gidanmu kinji!" cikin yanayi na shagawaɓa ya faɗi haka.

Murmushi Zahrah tayi, haɗe da sanya hanu ta shafi kumatun sa, cike da ƙaunarsa tace "Kayi haƙuri Hubby, nima ina kewar sucking ɗinka,  kuma ai bawai bazan dawo bane zan dawo fa" tafaɗi hakane don kawai  ta kwantar masa da hankali.

Ya buɗe baki zaiyi magana kenan muryar Hajiya ta karaɗe kunnuwansu, inda take cewa. 
"To iyayen rashin kunya, saika tashi katafi dare na ƙarayi, ke kuma miji daɗi, ga yaronki nan, abincinsa yakeso ki basa."   kunyar Hajiya ne yakama Zahrah, haka ta amshi yaron kanta a ƙasa. 
Doctor kuwa turawa Hajiya baki yayi, haɗe da cewa "Hajiya zantafi, amma kiɗanyi haƙuri ba yanzu ba mana"

Baki Hajiya ta sake tana kallonsa. "Sannu marar ta ido, wallahi saika tafi yanzu kuwa" Hajiya tafaɗi haka tana me kama hanunsa, haka yanaji yana gani ta fitar dashi daga ɗakin, Zahrah kam dariya taketa yi masa.   Bayan ta shayar da yaron natane, tashiga toilet tayi wanka, doguwar rigan bacci tasanya, kana ta ɗauko diary'nta, rubutu tayi aciki, ta mayar dashi ma'ajinsa. Kwanciya tayi luf akan gado, cike da tunani kala kala bacci ya ɗauketa.... 

*** *** ***

Yau kwanansu 50 cif cif agidan Hajiya, sunƙara kwanaki 10 akan kwanakin gama wankansu,  idan kaga Zahrah bazakace ita bace, sosai taƙara cika da kyau, fatarta ta ƙara haske, komai nata yasake cika, gwanin sha'awa,  yau ne zata koma gidanta, tuni Dr.Sadeeq ya sanja mata kayan furnitures ɗinta, komai yasanya mata sabo,  Hajiya kuwa tun tuni taketa ɗirka mata magunguna, haka Aunty Raliya ma ta dage sai bata wasu magunguna masu ƙarfi take, ita kuwa sha take abunta, wanda taji yanada bauri ne kawai take ajiyewa bata sha.

Wanka ta tsantsara cikin wata jar atamfa Super Exclusive, wacce taji ɗinkin riga da sket, sosai kayan ya amshi jikinta,   zama tayi da kanta, ta tsantsarawa fuskarta kwalliya, sai gashi kuwa kyawunta ya ƙara bayyana,  dogon gashinta dayasha gyara ta tubke da ribbon haɗe da kafa ɗaurin ɗan kwalinta me kyau,  wani red ɗin takalmi tasanya aƙafanta me tsinin gaske, ɗan ƙaramin mayafi ja ta ɗauka ta rufe jikinta dashi, babu abun dake fita ajikinta, sai daddaɗan ƙamshi.

Yana tsaye ajikin motarsa dake fake a  compound ɗin gidan,  yaga fitowarta, kusan suman tsaye yayi.  "Tabbas Zahrah me kyauce, tahaɗu tako ina, kullum ƙara kyau da cika take, lallai kuwa da yayi saken barin Zahrah, tabbas da yazama soko, marar rabo, samun mace kamar Zahrah, babban sa'ane daya samu a rayuwarsa" yafaɗi haka acikin zuciyarsa, yana hangame da baki wajen kallonta, baisan ma taƙaraso garesa ba, saida yaji ni'imtaccen ƙamshinta na ratsa cikin hancinsa.

Murmushinta me kyau tayi masa haɗe da kashe masa idanunta ɗaya.    "Ya dai kwalliyar tayi maka ne" tafaɗi haka tana me juya masa bayanta. Alaman yaganta da kyau.

Yawu ya haɗiye, alokacin da idanunsa suka sauƙa akan hips ɗinta,   baigama dawowa hayyacinsa ba, yakuma jefa idanunsa akan ƙirjinta, jikinsa na rawa ya jawota ya rungumeta.

Wani irin ajiyar zuciya suka sauƙe atare. 
  "I really Miss you Babyy!!"  yafaɗi haka akasalance.

"Miss you too dear!"  itama ta mayar masa da amsa cikin muryar raɗa.

Hajiya dake kallonsu ta window tasaki murmushi haɗe da komawa cikin falonta ta zauna, aranta tanayi musu fatan shiriya.

Saida suka biya ta JABI lAKE sukayi sayayya tukun kafun daga nan suka wuce gida.

Wanka ta sakeyi ta shirya kanta cikin wata irin fitinanniyar sleeping gown, wacce ta bayyana komai na surarta bata ɓoye komai ba,  rigar doguwace har kusan ƙafa, amma kuma duk da haka itaɗin kamar babu take, kasancewarta shara shara.   dogon gashinta ta sake a bayanta, haɗe da shafe jikinta da shu'umar Humra,     wani sweet Lip Gloss tashafa akan leɓenta.

Yana zaune a falo yana danna laptop ɗinsa,  ƙamshinta ne yafara kawo masa ziyara, lokacin daya sauƙe idanunsa, akanta sai da yaji wani irin shock ajikinsa,  da sauri ya miƙe ya ƙarasa gareta.   buɗe hannayensa yayi daniyar rungumeta, da sauri ta matsa gefe, tanayi masa dariya, haɗe da yin wata irin tsayuwa,  wacce takusa zautar dashi.

Lumshe idanunsa yayi tare da sanya hanunsa ya jawota jikinsa. Ƙam ya rungumeta, sai gashi yana sauƙe ajiyar zuciya akai akai.   Kallon juna suka shiga yi idanun ko wannensu ɗauke da tsananin sha'awar ɗan uwansa. Jikinsa na rawa ya kama lip ɗinta na ƙasa, yana tsotsa ahankali, jiyake kamar yanashan honey.    da kanta ta zame rigar dake jikinta, ta faɗi ƙasa, take surarta ya bayyana,  hmmm ba yau yafara ganinta ba, amma kuma ya zautu ƙwarai daganin surar jikinta, jiyake kamar ma baitaɓa kusantarta ba, sosai yayi missing ɗinta.    Jikinsa na rawa ya ɗauketa suka wuce bedroom,  tuni dama Asad yayi bacci, dama shi haka yake sam baida ƙiriniya,  daya ƙoshi sai bacci, bakuma zai tashiba sai dai idan yanajin yunwa.  

A yau ɗin ne suka sake tabbatar da cewa sunyi kewar juna,  musamman ma  Doctor Sadeeq da kusan cinyeta ne kawai baiyi ba, gaba ɗaya ya zauce, ya susuce, wasu maganganu yake wanda ita kanta batasan me yake cewa ba, saboda sun lula wata duniya ta musamman, wacce  sukayi nisa  acikinta basaji basa gani, kansu kawai suka sani. Aranan nan wata zuma suka shayar da junansu, wanda bazasu taɓa mantawa ba. Wannan ranan takasance rana ta biyu masu muhimmanci a garesu.

*** *** ***

Bayan wata 6........

America

Zufa ne keta ketowa ta goshinsa, gaba ɗaya baya cikin nutsuwarsa, kai komo yaketayi agaban labour room ɗin sama da 1 hour kenan yana abu ɗaya, jiyake kamar yasanya hanu akansa yaita ƙwala ihu.  Ɗaya daga cikin  Nurse ɗin dake kanta na fitowa  ya nufi wajenta, da sauri idanunsa sunkaɗa sunyi jajur dasu.  Murmushi Nurse ɗin tayi masa haɗe  da cewa "Ina tayaka murna, matarka ta haihu, kasamu baby girl"   wani irin sanyin daɗi yaji acikin ƙirjinsa, baisan lokacin dayayi sujja don nuna godiyarsa ga Allah ba. 

Ana kaita ɗakin hutu, wata nurse tace yashigo ya karɓi babynsa,    lokacin daya sanya hannayensa ya amshi babyn, wani irin kukane ya ƙwace  masa, alokacin da idanunsa suka sauƙa akan kyakkyawar fuskarta kuwa,  bugun zuciyarsa ne ya ƙaru, saboda  kokaɗan  yarinyar bata kama da mahaifiyarta,  durƙushewa yayi aƙasa, riƙe da yarinyar tasa yana kuka, hakan kuwa sosai yabawa likitotin mamaki.

Bakomaine yasa sa yake kuka haka ba,  face tsananin danasani na rayuwar da yayi abaya da yake.   yakasance mazinaci, mashayin giya.  "Yanzu idan ƴarsa mafi soyuwa agaresa, tataso taji labarin abun da ya aikata a baya,  wani irin kunya zaiji? mezaice da'ita idan ta tambayesa, meyasa yazamo haka?" tambayar da yayiwa kansa kenan, amma kuma baida amsa, baida kuma me amsa masa.

Rungumeta ya sakeyi tsam,  acikin ƙirjinsa, ahankali yace.

"Kindawo gareni Zahrah, Allah yadawomin dake, Inasonki Inasonki, inamiki so na musamman Allah ya albarkaceki ƴata!!!" kiss ya manna mata akan goshinta, kana yazuba mata idanu,  bazaiyi mamakin kamannin daya gani akan fuskar ƴartasa ba, saboda yasan ba aja da ikon Allah, kuma hakan ma wata rahamace da Allah yayi masa,  Allah ya hanasa Zahrah alokacin dayaso, yanzu yakuma basa Zahrah alokacin dayaso,   hancinta bakinta duka kalan nasa ne, amma kuma idanunta tamkar idanun Zahrah aka ciro aka sanya mata, kallon farko da yarinyar tayi masa, saida yaji tsikar jikinsa ya tashi, saboda gani yayi tamkar Zahrah ce dakanta agabansa.  yana rungume da yarinyar ya ƙarasa gaban Afrah dake kwance akan gado tana kallonsu,  ranƙwafowa yayi ya manna mata kiss akan goshinta, hanu yasa yashafi kumatunta, haɗe da cewa "Nagode ƙwarai Afrah, Allah ya miki albarka, bazan manta da wannan ƙoƙarin da kikamin ba, Inasonki"

Karo na farko kenan arayuwarta da taji kalmar nan tafito daga bakinsa akanta,  "Inasonki" ta maimaita kalmar abakinta cike da mamakinsa.
Kansa yajinjina mata haɗe da sakin murmushi. 

"Ki kwanta ki huta, nasan kinsha wahala sosai" yafaɗi haka yana shafa kanta.
Lumshe idanunta kawai tayi saiga hawaye nabin kan fuskarta. Hanu ta miƙa masa ya bata yarinyar,   ba iya mamaki ba hadda tsoro saida ya bayyana akan fuskar Afrah, sakamakon ganin fuskar yarinyar ɗago kanta tayi ta kalleshi da sauri.

Kamar yasan me take tunani,  murmushi yayi mata haɗe da ɗaura hanunsa akan kafaɗanta.   "Kada kidamu, Allah ne yayi ikonsa, Allah ne yadubeni yayimini rahama,  sannan kuma ko da ace kowa zaiyi mamakin kamannin yarinyar ni bazanyi ba, saboda wacce take kama da ita, jinin jikinane, sannan kuma Allah yana da ikon yin komai"

Ajiyar zuciya kawai Afrah ta sauƙe haɗe da kafe yarinyar nata da ido, tabbas da badan taji ƙauna irinta uwa da ƴa akan yarinyarba, to tabbas da tace ba itace ta haifi yarinyar ba, Zahrah ce, shine aka sanja mata, aka ɗauki nata aka kaita wani gun, itakuma aka kawo mata wannar, a matsayin ƴarta. Rungume ƴar tata tayi, tanajin ƙaunarta aranta.
***

Suna komawa gida Zaid yayiwa Afrah kyautar zuƙeƙiyar mota, tare da kuɗi Naira Million 3 duk na murnan ta haifa masa baby ne,  washe gari kuwa suka tarkato suka dawo Nigeria, abisa takurawan Mom ɗinsa. amma da anyi suna yace  zasu koma.  Aranan da aka haifa masa Zahrah aranan ya mallaka

Please Login or Register in order to submit comment