Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yaji daɗin aminta dashi da Baffa yayi.

"Nagode da wannan dama da kabani Baffa, Allah yajiƙan magabata" Dr Sadeeq yafaɗa cike da girmamawa.

"Mune da godiya Likita, ai mu ba'abun da zamuce maka saidai fatan alkhairi" Baffa yafaɗa shima cikin jin daɗi, domin yasan Zahrah na auren Dr.Sadeeq wahalanta yaƙare da yardan Allah,saboda yana da tabbacin cewa Dr.Sadeeq zai bata kyakkyawan kulawa, duk da kuwa cewa Dr.Sadeeq ɗin yasanar dashi cewa ba Zahrah ita kaɗai zai auraba, yasanar dashi komai, kuma Baffa yayi na'am da hakan, saboda shi baimaga wani aibu acikin hakan ba, ai namiji mijin mace huɗu ne.
(Nima nace wannan gaskia ne, sbd haka duk me mace ɗaya ya ƙara😜😂)

Cike da farinciki Baffa da Likita sukayi sallama, yayinda Baffa yakoma cikin gida, ya kumace da Dr.Sadeeq zai turo masa Zahrah suyi sallama.

Tanajin Muryan Baffa a tsakar gida, tayi saurin share hawayenta, haɗe  da miƙewa tsaye, domin har Baffa yafara ƙwaɗa mata ƙira.

Fuska cike da fari'a Baffa yace "Likita ke yake jira, zai tafi"

Sumi sumi haka Zahrah ta fice yayinda tabar Baffa yana gayamawa Inna abun da ya wakana tsakaninsa da Likita.

Tun fitowarta yake ta zabga murmushi, kallo ɗaya zakai mawa fuskarsa ka gane cewa yanacikin farinciki.

"Kitayani murna My Princess saura ƴan kwanaki ƙalilan na mallake ki!" Dr Sadeeq yafaɗi haka cike da shauƙi.

Kunyane yakama Zahrah, don haka ta sanya duka hannayenta biyu ta rufe fuskarta, bayan ta ƙaƙalo murmushi ta aza akan fuskar ta..

"Baffa yabani daman naturo magabatana don asa mana ranan aure, kuma insha Allah, gobe magabatana zasu zo, za'asa ranan aurenmu nan bada jimawa ba,  so sai ki shirya domin kin kusa zama amaryata!" yanayin yanda ya ƙare maganar kaɗai ya isa taɓa zuciya..

Kunyane yasake kama Zahrah, har batasan sanda murmushi mai sauti ya kufce mata ba,  gaba ɗaya ta lura Dr.Sadeeq ya ƙosa da ayi aurensu bata kumasan dalilinsa nayin hakan ba..

"Kinyi shiru kodai bakya farinciki ne my princess?" yatambaya.

Ɗan satan kallonsa tayi haɗe da sakarmasa murmushi mai tsayawa a zuciya.

Ƙaran wayarsane ta katsesa daga kallonta da kuma zancen zucin da yakeyi.  Ajiyar zuciya ya sauƙe ganin wacce take ƙiran nasa,  maida wayar tasa cikin aljihu yayi batare daya ɗaga ƙiran ba.

"Dare yayi Zahrah kishiga gida, zamuyi waya, kikulamin da kanki "   yafaɗi hakan yana me ƙoƙarin shiga cikin motarsa.

Murmushin dole Zahrah tayi haɗe da yi masa saida safe, tajuya ta nufi cikin gida, hakanan taji wani iri a zuciyarta duk da batasan me yasa baiɗaga ƙiran da ake mai ba, amma tana da yaƙinin cewa matar da zai aura tare da itane ta ƙirasa. Saurin kawar da tunanin tayi aranta, domin tuna hakan ma bashida amfani a gareta.

Washe Gari....

Kamar yanda Dr.Sadeeq yafaɗa hakanne ya kasance da  da dare bayan sallan magriba Baffa Amadu shida amininsa suka zo gidansu Zahrah don tambayan aurenta, balaifi Baffa yayi musu tarba mai kyau, sunkuma ji daɗin hakan, duk da sun lura cewa suɗin  basuda wani  ƙarfi, ma'ana arziki...

Magana ta fahimta akayi tsakanin Baffa da kuma Baffa Amadu,  a taƙaice dai Baffa yabasu auren Zahrah, yayinda sukuma suka ɗau alƙawarin cewa a cikin satin za'akawo kayan tambaya dakuma na lefe, daga nan sai asa ranan aure, amma basason auren ya ɗau lokaci, saboda rana ɗaya suke so ayi dana Salima.. Da to kawai Baffa ya amsa musu domin shi baida wani abun cewa banda hakan, sai dai a ƙasan zuciyarsa tunani yake taya zai samu kuɗin da zaiyi mawa Zahrah kayan ɗaki, domin dai bayanda za'ayi ace anyi aure ba kayan ɗaki... Haka dai sukayi sallama cike da mutun ta juna...

Baffa ne Zaune akan tabarma ya yi jigum bakomai ke damunsa ba, kamar sha'anin auren Zahrah, Allah yasani ko abincin da za'aci abikin bai tanada ba, balle wata uwa uba kayan ɗakin da za akaita dashi..

"Wai tunanin mekakeyine haka tun ɗazu?" Inna dake zaune gefensa ta jefo masa tambaya.

"Ba dole nayi tunani ba Salame, kinga dai yau iyayen yaron nan Sadeeq suka zo, kuma da duk kan alama basa so aja auren nan yakai wani lokaci, kin kuma san halin dai da muke ciki na rashin kuɗi"

"Yo dama akan wannan kake ɗaga hankalinka? hmm Malam kenan to ai ni banga abun ɗaga hankali anan ba, ca nake shi Sadeeq ɗin yasan duk halin da muke ciki, kuma shi yakawo kansa yace ya na so, bawai mu makai masa dole ba,  saboda haka malam ka kwantar da hankalinka, Zahrah ya nema kuma Zahrah'n  zamu bashi" Inna tafaɗi haka da'iyaka gaskiyarta...

Kallon Inna kawai Baffa yayi haɗe da girgiza kansa,  yasan ma koda yayi ƙoƙarin fahimtar da'ita to fa bazata fahimta ba.

***
"What? Mom cewa fa kikayi wai bani kaɗai Sadeeq zai aura ba, anya kuwa Mom kinji abun da Hajiya Habiba tafaɗamiki da kyau?" Salima tatambayi mahaifiyarta Hajiya Furaira cike da mamakin jin abun da mahaifiyarta tace da'ita..

"Abun da na faɗa miki shi naji daga bakin Hajiya Habiba, Salima kicire Sadeeq a ranki, domin kuwa aurenki dashi bazai taɓa yiyuwa ba, da raina dakuma hankalina bazan taɓa bari ƴata taje kan kishiya ba!" Hajiya Furaira tafaɗi haka cikin ɓacin rai..

Kuka ne ya ƙwacemawa Salima cikin muryan kuka ta soma cewa "Wani irin cin amana ne wannan mom, sai da maganar aurena dashi ta kankama sannan wata banzar magana zata ɓullo,  wallahi bazan haƙura da shi ba, bakuma zan taɓa zama da wata a matsayin kishiyata ba, dole ne Sadeeq ya aureni ni ɗaya batare da wata ba, bazan iya jure rashin saba Mom, dan Allah kiyi wani abu" Salima ta ƙare maganar cikin shaɓe shaɓe da hawaye. 

"Mekikeso nayi Salima? so kike naje na basu haƙuri akan su sa Sadeeq ya aureki ke kaɗai? ko ko sokike na zubar miki da ƙima daƙuma ƴancinki?  Hajiya Habiba ƴar uwatace kuma ƙawata, bantaɓa tunanin haka daga gareta ba, amma bakomai, zanyi maganin abun, kuma ni banzauna da kishiya ba, ƴa tama bazata zuana da kishiya ba, wannan alƙawarine na ɗaukar mawa kaina" still cikin ɓacin rai Hajiya Furaira take maganan...

Cikin matsanancin ɓacin rai Salima ta juya ta koma ɗakinta, ji takeyi zuciyarta na tafarfasa, kamar ita ace ta haɗa miji da wata, sam bazai yi wuba, lallai ko da mahaifiyarta bazatayi wani abu ba yakamata ace ita tayi, wayarta da mayafinta ta ɗauka, a fusace ta fice daga ɗakin nata, tana son Sadeeq tun ba yau ba, zata kuma iyayin komai akan sa.

Ɓangaren Dr Sadeeq kuwa tuni yasoma haɗa mawa Zahrah kayan lefe, sosai yake iya ƙoƙarin sa wajen ganin yasanya duk wani abu da yasan zai burge Zahrah.
Ɓangaren Hajiyarsa da Aunty Raliya kuwa, sam basu wani damu da auren ba, hakanne ma yasa suka tura masa aniyarsa, su dai sunfi bada ƙarfi wajen ganin Salima tasamu abun da take so, yayinda Hajiya Furaira ta kafe kan cewa ƴarta bazata auri Sadeeq ba matuƙar ba'a fasa aurensa da Zahrah ba, ranta bai ƙara ɓaci ba ma, sai da taji labarin cewa Zahrah ƴar talakawa ne, sannan kuma bata da wani galihu, ai take ranta yaƙara ɓaci, tace sam bata amince ba, yayinda Salima kuwa ta kafe akan cewa lallai sai ta ruguza auren da Dr.Sadeeq yake nema bayan nata.

Gaba ɗaya Zahrah ta ruɗe, zuwa yanzu wanda yake turo mata saƙo ya uzurawa rayuwarta, a yanda ta fahimta shine duk inda tayi yana biye da'ita, wani babban tashin hankali daya kunnu mata shine, sabbin saƙonnin da yafara turo mata a cikin wayarta, tagama iya hasashenta ko zata gano a ina yasamu number'n ta amma takasa samun daman sanin inda yasamu number'nta,  gaba ɗaya yanzu salon saƙonnin nasa sun sauya salo, domin kuwa yanzu saƙon kalamai yaƙe turo mata masu daɗi, wanda kuma duk rabin saƙon yaba kyawunta yake,   babban abun daya ƙara ruɗata shine irin maƙudan kuɗaɗen dayake turomata ta waya.  sannan kuma idan ta gwada ƙiran number'n da yake turo mata saƙo dashi, bata samu domin da zaran taƙira wayan za'ace mata a kashe wayar take, hakan yasa tafara tunanin cewa kodai  gamo tayi...

Ɗan ƙara wayarta tayi alamar shigowar saƙo, take taji gabanta yafaɗi, zuwa yanzu har tsoro take taji wayarta tayi ƙara, domin kuwa tasan idan har wayanta tayi ƙara to ko ƙiran Dr.Sadeeq ko kuma saƙon mutumin da batasan shiba...

Number'n nan ce dai, da aka saba turo mata saƙo dashi, yauma saƙonne aka kuma turowa..

_Tunaninki ya hanani sukuni My Zahrah, ina fatan dai kina lafiya, ina kuma fatan zuwa yanzu kindaina tsoro da kuma mummunan tunanin da kikeyi akaina, kina da kyau My Zahrah, komai naki me kyau da burgewa ne._

Abun da saƙon ya ƙunsa kenan.
Zahrah ta karanta saƙon nan yafi sau biyar, kwata kwata ta kasa fahimtar abun da saƙon yake nufi.

Saurin yin Deleting saƙon tayi haɗe dayin switch off ɗin wayar tata, bazata taɓa yarda wan nan mai saƙon ya haukata mata tunanin ta ba,  yazama dole a gareta ta sanja layi.. Kwanciya tayi lamo tana mai addu'an Allah yasa bacci ya ɗauketa. domin bacci ne kaɗai zai kawo mata sauƙi a zuciyarta.

Zaune suke dukansu a ɗan madai dai cin tsakar gidan nasu,  domin dama idan dare yayi sukan zauna a tsakar gida su ɗan taɓa hira, haka al'adarsu take..

Wani yarone yashigo cikin gidan bakinsa ɗauke da sallama, haɗa baki sukayi wajen amsa masa sallaman.

"Wai ana sallama da mai gidan nan" yaron  yafaɗa.

"To kace inazuwa" Baffa yafaɗi haka yana ƙoƙarin miƙewa tsaye.

Kusan tare suka fita shida yaron sai da Baffa yaji wani irin faɗuwar gaba sakamakon wasu irin danƙara danƙaran motoci guda biyu da yagani fake a ƙofar gidansa.

Ja Baffa yayi ya tsaya turus yana me mamakin ganin waƴan nan rantsatstsun motocin a ƙofar gidansa, "Allah yasa da alkhairi suka zo" Baffa yafaɗi haka a cikin zuciyarsa.

Buɗe murfin motar Alhaji Ma'aruf yayi haɗe da sako ƙafarsa waje.

Sake waro idanu Baffa yayi haɗe da kafe Alhaji Ma'aruf dake ƙoƙarin fitowa daga cikin mota da ido.

Fuska cike da annuri Alhaji Ma'aruf ya ƙaraso wajen Baffa, haɗe da miƙa masa hanu alamar su gaisa.

Cikin ɗari ɗari Baffa ya ɗago hanunsa haɗe da miƙamawa Alhaji Ma'aruf suka gaisa.

"Inafatan kaine ma mallakin wannan gida, kuma Baffa ga Zahrah?" Alhaji Ma'aruf ya tambaya.

Saida Baffa yaji zuciyarsa tayi tsalle sakamakon jin an ambaci Zahrah, Allah yasa ba wani abun Zahrah tajawo musu ba.

"Eh nine ranka ya daɗe, Allah yasa lafiya?" cikin dar ɗar Baffa yafaɗi hakan.

Murmushi irin  nasu na manya Alhaji Ma'aruf yayi haɗe da kallon Baffa..."Nazo da magana mai mahimmanci, inaga zaifi kyautuwa kabiyoni cikin mota mu tattauna, don maganar bata tsaye bace"

Kallon Alhaji Ma'aruf Baffa yashiga yi, haɗe  da excort ɗin da suke bayan Alhaji'n, tabbas Alhaji Ma'aruf baiyi masa kama da irin mugayen mutanen nan ba, domin daga ka gansa zaka fahimci cewa dattijon arziki ne, hakanne yasa Baffa bai musa masa ba, yabisa zuwa mota..

Acikin mota kuwa bayan sun sake gaisawa,  Alhaji Ma'aruf yayi gyaran murya haɗe da cewa...

"Sunana Alhaji Ma'aruf,  kasancewar dare ne yasanya ka kasa shaida fuskata, domin ni ba ɓoyayyen mutum bane. Nazo gare ka ne domin nemawa ɗana Auren Ƴar Wajenka Zahrah, ina fatan bazaka watsa mini ƙasa a ido ba".......

(Kowani amsa Baffa Zai bawa Alhaji Ma'aruf🤔)

*19/December/2019*

*Follow me on Whatsapp and Wattpad*
*Wattpad user name fatymasardauna*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

            *SHU'UMIN NAMIJI !!*

    
       *Written By*
*Phatymasardauna*
_(shalelen kainuwa)_

*Dedicated To MY Brother KHABIER*

*🌈Kainuwa Writers Association*

{United we stand and succeed; our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}

*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*

           *WATTPAD*
     @fatymasardauna

*(Wannan page ɗin gaba ɗayansa ƙyautane a gareku Maman Teemah, and Ummu Fateema, inaƙaunarku  Momy's ɗina)*

*Editing is not allowed📵*

  *CHAPTER 63 to 64*

Shirune yashiga tsakanin Baffa dakuma Alhaji Ma'aruf,  bakomai ne kuma yasa hakan ba face nazari da Baffa yashigayi, lallai wannan abu da mamaki yake, neman aure mace ɗaya duk alokaci guda.

"Naji kayi shiru, Allah yasa dai ba wata matsala bace ta faru" Alhaji Ma'aruf  ya faɗa, domin ko kaɗan baya fatan wani abun da zai zo ya gifta har ya katsewa  Zaid cikar burinsa..

Gyara zama Baffa yayi haɗe da sauƙe ajiyar zuciya..

"A gaskiya Alhaji bazan ɓoyemaka ba, yanzu haka na bada auren Zahrah ga wani,  wanda kuma tariga da ta aminta dashi, sai dai bazan yi saurin yanke hukunci ba, idan har Zahrah ta aminta dashi ɗan wajen naka, shikenan, saboda ni bazan mata dole ba, duk wanda takawo tace shitake so, to  shi zan aura mata, amma kuma a iya sanina babu wani wanda yake zuwa wajenta, bayan likita'n dana bashi aurenta, sai dai kuma bansan shi ɗan wajen naka a ina yaganta har yaji yanada burin aurenta ba"

Ɗan jim Alhaji Ma'aruf yayi haɗe da sauƙe ajiyar zuciya. Lallai yakamata yayi duk abun da zaiyi, domin shikansa yanaso Zaid  yayi aure, amma kuma yasan cewa nema cikin nema haramunne, tunda gashi har shi Baffan yarinyar ya ri ga daya shaida masa cewa yabada auren yarinyar ga wani, yazama dole suyi haƙuri kenan.

"Naji maganarka Malam Hayatu, nakuma gamsu, amma bayar da aurenta ga wani, ae  bashi yake nufin anɗaura aurenta ba, koda yaushe ra'ayin mutane yana iya sanjawa,  saboda haka zanbaka dama kayi tunani mai kyau" Alhaji Ma'aruf yafaɗi haka bayan yaciro wasu maƙudan kuɗi a cikin aljihun rigarsa ya ɗauramawa Baffa akan cinyarsa..

Ware idanu Baffa yayi sakamakon ganin  maƙudan kuɗin da Alhaji Ma'aruf yaɗaura masa akan cinyarsa, badai yana nufin duk nasa bane.

Murmushi irin na manya Alhaji Ma'aruf yayi haɗe da cewa "Kada kadamu bawai nabaka kuɗinnan bane,don ka bawa ɗana auren ƴarka ba, nabaka ne kawai saboda shi meyin alkhairi ako da yaushe baya rasawa"

Cikin sanyin jiki Baffa yayi masa godiya haɗe da buɗe murfin motar yafita, zuciyarsa cike da ɗunbin mamaki...

Baffa na fita daga motar Alhaji Ma'aruf yamawa driver'nsa umarni akan cewa su tafi, aikuwa ba ɓata lokaci drivern yatada mota..

Saida suka ɓacewa ganinsa kafun Baffa ya iya ɗauke idanunsa daga kansu,  kuɗin dake hanunsa yashiga juyawa,  "Lallai wannan mutumi yanada ihsani, amma kuma yazo da babbar magana, da ace yanada dama to da a yanzu yabawa ɗan Alhaji Ma'aruf ɗin auren Zahrah, to saidai kuma yanzu ya saduda, sakamakon wa'azi mai tsoratarwa dayaji akan cutar da maraya, da kuma irin azabar da za'amawa mai cutar da maraya,  tundaga wannan lokacin yaƙudurta aransa cewa bazai sake cutar da Zahrah ba, yanzu ma dolensa zai bata zaɓi, domin ita zatayi zaman auren ba shiba...

Yanashiga gida Inna da takasa zaune takasa tsaye, ta ƙaraso wajensa da sauri tana me cewa "Lafiya naga ka jima, har nafara jin tsoro naɗauka irin mutanen nan ne masu garkuwa da mutane suka kamaka, domin na leƙa naga wasu fankama fankaman motoci a waje"

Harara Baffa ya wurgamata, haɗe da jan tsuka "Bazaki taɓa sanja halinki ba ko Salame, wato ke dai koda yaushe kai da kuma idanunki sunaga ƙofar gida, kullum cikin leƙe kike, wato dai har dare ma yanzu leƙe kikeyi, Allah ya kyauta" yafaɗi haka yana mai nufar hanyar ɗakinsa...

Fuska Inna ta ɓata haɗe da kafe aljihunsa da idanu, domin kuwa tuni idanunta sun ƙyallaro mata tudun da aljihunnasa yayi, ƙwafa tayi haɗe da rufa masa baya, koma mene sai
taje taganema idanunta, idan ma abuncine aci da'ita..

Sake gwalo idanu Inna tayi, ganin kuɗin da Baffa ya'aje akan gadonsa,   "Malam kace farar fita kayi, a shema baƙin arziki ne, nayi musu mummunar fahimta, ae irinsu muke fatan suta zuwa" washe da baki ta ƙare maganar...

"Akwai matsala Salame, amma jeki ƙiramin Zahrah" Baffa yafaɗa bayan yayimawa kansa mazauni, a bakin gadonsa.

"Yanzu kuwa" Inna tafaɗa tana me fita daga ɗakin..

Zahrah ce zaune akan gadonta, game take bugawa a cikin wayarta, da'alama dai game ɗin yayi mata daɗi, domin kuwa ita kaɗai sai murmushi take.

Inna ce tashigo cikin ɗakin haɗe sa shaida mata ƙiran da Baffa keyi mata,  haka nan taji gabanta yafaɗi. Tare suka fito da Inna, dukansu suka ɗunguma zuwa ɗakin Baffa'n...

Gyara zama Baffa yayi haɗe da maida kallonsa ga Zahrah, wacce ta duƙar da kanta ƙasa.

"Bayan Likita akwai wani wanda kikasan yanasonki, ko kuma kika basa dama ya turo magabatansa wajena?"  Baffa yatambayeta cike da kulawa.

"A'A Baffa bana mu'amala da kowa sai likita, bankuma bawa kowa izinin zuwa wajenka ba" tafaɗi haka cike da girmamawa, duk da kuwa cewa kanta ya ɗaure da jin tambayar da Baffa'n yayi mata...

Kai Baffa yajinjina haɗe da cewa "Ƙiran da akai min ɗazu wani ne yazo nemawa ɗansa aurenki, shine nayi tunanin ko kinsan da zuwansa"

Wani irin bugawa Zahrah taji ƙirjinta yayi, har batasan sanda ta ɗago da idanunta ta kalli Baffa ba.

Baffane yacigaba da cewa "Bansan ko su ɗin suwaye bane, amma ban ɓoyemusu komai ba, nasanar dasu cewa nabada aurenki ga wani, amma mahaifin yaron yace yabani lokaci nayi tunani,  saboda hakane ma naƙiraki domin ni bazan miki dole ba,  zanbaki dama ne ki zaɓi wanda kikeso"

Take idanun Zahrah suka kawo ƙwalla, sakamakon jin wani baƙon al'amari dayake shirin kunno kansa cikin rayuwarta.

"Kinyi shiru, ki kwantar da hankalinki bazan miki dole ba Zahrah, kema kina da ƴan ci, zan kuma baki ƴancin ki, sai dai abun da nakeson sani  shine wanene yaron nasa, saboda bai yiwuwa a haɗaki aure  da wanda  bamusani ba, amma idan ke kinsan sa shikenan ba damuwa"

"Bansan saba Baffa, kuma ma koda nasansa bazan aminta dashi ba, saboda idan nayi haka ban yi mawa Dr.Sadeeq adalci ba" Zahrah tafaɗi haka cikin sanyayewar murya...

"Adalci, kaji shirmen banza don Allah Malam, wani adalcine yarage miki, wanda yawuce ki kai kanki cikin arziki kicisa yanda yakamata,  saidai ko inkuma baƙin ciki kike mana"
Inna ta tsomo bakinta cikin maganar batare da angayyaceta ba...

"Tashi kije Zahrah, idan suka sake zuwa zan sanar dasu cewa hakan da sukeso bazai yi wuba" Baffa yafaɗa, yana mai wurgamawa Inna harara..

Cikin rashin ƙwarin jiki haɗe da ɗaurewar kai Zahrah tabar ɗakin..  Haushin Zahrah da Baffa ne yacika zuciyar Inna, amma ganin yanda Baffa yahaɗe fuska bai bata damar yin ƙorafi ba yasanya itama tafice daga ɗakin tana me ƙananan maganganunta wanda ita kaɗai tasan metake cewa..

Zama Zahrah tayi jigum haɗe da zurfafa tunanin ta,  ba'abun dake bata mamaki da ɗaure mata kai, kamar neman aurenta da Baffa yace anzo anyi,  "To waye zai zo neman aurenta batare da saninta ba? batare da ta kuma sanshiba, lallai koma waye baisan meyafaru da'ita ba, domin tasan daya sani, da baiyi gigin turo magabatansa nema masa aurenta ba" Haka dai tayita saƙawa da kuncewa har bacci ya ɗauketa......

Cike da tsananin mamaki Zaid yake kallon mahaifinsa, sakamakon ji da yayi mahaifin nasa nacewa "Wai anbada auren Zahrah'nsa ga wani"  " Anya kuwa gidan su Zahrah Dad ɗinsa yaje? kodai yayi mistake ne yaje wani gidan amadadin nasu Zahrah?" duk wannan tambayar kansa ya mawa.

"Inaga zaifi kyautuwa kanemi wata My Son, domin kafasan nema cikin nema haramunne"  Alhaji Ma'aruf ya faɗa yana me kallon ɗan nasa.

"Inaga ba gidansu kaje ba Dad,
domin ni nasan Zahrah tawace, baza'a bawa wani ita ba bayanni" Zaid yafaɗi haka bayan yayi sipping holandia milk ɗin dake aje cikin  glass cup ɗin dake gabansa.

Kallon mamaki Alhaji Ma'aruf, yashiga yi mawa Zaid, sakamakon jin abun daya faɗa.
Baisan me yake shirin faruwa da ɗansa ba, amma tabbas ya hango wata irin soyayya acikin idanun Zaid ɗin me matuƙar zafi, wanda Zaid shikansa baisan da'ita ba...

"Akwai matan aure dayawa Zaid, zaifi kyau ka zaɓi wata, koda a cikin ƴan uwankane" Alhaji Ma'aruf yafaɗi haka cikin lallashi. 

Murmushi kawai Zaid yayi haɗe da kallon mahaifin nasa...

"Kai mahaifinane saboda haka bana iya ɓoye maka komai,  a gaskiya banjin zan iya zama da wata daban, idan ba Zahrah ba, zanyi komai da kaina kawai" yafaɗi haka yana me miƙewa tsaye...  Da kallo kawai Alhaji Ma'aruf yabi sa dashi har ya fice daga cikin  falon nasa. Ajiyar zuciya yayi haɗe da cewa "wataƙila idan kuɗi na magani, to zasu maya Zaid, ta hanyar samo masa auren Zahrah"
(hmm bakomai ake nema a samu ba, bakuma komai kuɗi yake iya saya ba)

Kai kawo Zaid yashigayi a tsakiyar tankamemen aljannar duniyar falonsa, gaba ɗaƴa yarasa me yake masa daɗi, shin maganar da Dad ɗinsa ya faɗa masa cewa anbada Zahrah, gaskiya ne kokuwa Dad ɗinnasa ne yayi mistake wajen gano gidan su Zahrah,  dudduniya babu wani mahaluƙi daya isa yimasa shamaki da muradinsa,   lallai lokaci yayi daya kamata ya bayyana kansa gareta,  baidamu da yanda zata ɗaukesa ba, shidai burinsa kawai shine ya mallaketa amatsayin matarsa,    lallai yanzune zai gudanar da babban takunsa, sannan kuma yazama dole yagano bayanshi wayake bibiyan Zahrah, har ake yunƙurin aura masa ita, dole yagano wannan, domin yayi imani cewa Zahrah tasa ce...

***

Fitowarsu daga lecture kenan, wayarta tayi ƙara alamar shigowar saƙo,, ko kaɗan batayi mamaki ba, domin zuwa yanzu tasaba da saƙonnin da'ake turo mata batakuma san waye yake mata hakan ba. 

Ajiyar zuciya ta sauƙe bayan ta gama karanta saƙon, yau madai kalamaine masu tsayawa a zuciya, ɓoyayyen mutumin nata ƴarubuta mata, sai dai kuma duk sanda ya turo mata da saƙo, idan takaranta kalaman sukan tsaya mata arai suna kuma yawan yi mata yawo a ƙwaƙwalwarta,   koda sau ɗaya ne bata taɓa tunanin mayar masa da amsa ba, amma hakanan taji yau tanason tambayarsa ko shiɗin waye.

"Waye kai?" Abun da tarubuta tatura masa kenan.

Zaid dake kwance cikin wata luntsumemiyar kujera yana  sipping wine yaji wayarsa tayi ƙara alamar shigowar saƙo,   ɗaga wayartasa yayi yaduba, murmushinsa me kyau yayi bayan yagama karanta tambayar nata..

"Kinason ganina?"  shima yamayar mata da tambaya, tahanyar tura mata saƙo.

Zahrah na karanta saƙon tasoma typing kamar haka...."Mezai hana idan zaka bayyana kanka"  tana gama rubutawa tayi sending..

"Kishirya ranan friday 8:00 pm zankawomiki ziyara, ina fatan zakiji daɗin ganina, sannan zan taho miki da kyakkyawan surprise"  yana tabbatar da cewa saƙon ya isa zuwa wayarta, yayi switch off na wayarsa,   sake gyara  kwanciyansa  yayi ajikin kujeran, haɗe da lumshe idanunsa,  jiyake mararsa tana yi masa ciwo, kusan kwana uku kenan da yake fama da wannan ciwon maran,  hakan kuma yasamo asali ne da wata irin sha'awa da ta damesa, sai alokacinne ma yake tuna cewa yajima baiyi sex ba, lallai akwai abun da yake damunsa, Zaid ɗin da baya iya kwana ɗaya baiyi sex da mace ba, wai shine yanzu yake iya kwanaki batare da yayi sex ba,  shida mace ɗayama bata isan sa, amma sai gashi, yau ɗayan ma, yakasa nutsuwa yakusanceta, lallai yanzu kam yayarda da cewa akwai abun dake damun jiki da zuciyarsa....

Ɗan jim Zahrah tayi bayan tagama karanta saƙon nasa,  idan bata mantaba yau Tuesday kenan saura kwana biyu jumma'a tayi, lallai tanaso taga wanene wannan wanda yaɗau lokaci yan ɓata tunaninta,  ta wani ɓangare na zuciyarta kuwa, ji takeyi tamkar akwai wani gagarumin abu dazai faru da'ita, yayinda idan ta tuna aurenta da Dr.Sadeeq  saitaji ta zama wani iri da'ita, bakuma aurenta da Dr. ɗinne bataso ba, a'a kawai dai tanaji ajikinta kamar basu dace da juna ba ita dashi...

Dariya sosai Salima tashiga yi, sakamakon labarin da ƙawarta kuma aminiyarta Laura tabata yanzun.     Wani irin daɗi taji haɗe da sanyi acikin zuciyarta,  gaba ɗaya labarin Zahrah Laura ta kwashe ta sanar da Salima, wanda Laura ta samo asalin labarin Zahrah ne daga bakin wata Asma da take unguwarsu Zahrah'n kuma har school ɗinsu ɗayama da Zahrah..

"Dama akan sauran wani Doctor yake wulaƙantani hadda jamin aji, hmm lallai kuwa bazanyi kishi da mai aji bama ballentana marar aji" Salima ta faɗi haka cike da kunfar baki...

"Ae magana taƙare Salima, kamar yanda na faɗamiki, tashi kawai zamuyi muje hargidansu, muci mata mutunci mukuma gargaɗeta da tafita hanyar Doctor Sadeeq" Laura tafaɗi haka cike da son zuga Salima.

"Gaskiya ne nima ina bayan maganarki Laura" wata wacce take zaune gefen Laura ta faɗi haka, tana me taɓe baki..

Kallonta Salima tayi haɗe da cewa "Shiyasa nake sonki ƙawata, bakida wasa, wajen sawa ayi rashin mutumci, idan kinshirya muje gidan nasu yanzu, domin akan Doctor sai inda ƙarfina ya ƙare" Salima tafaɗi haka tana maitashi daga zaunen da take.
Motar Salima suka shiga su duka ukun yayinda Laura ke tuƙasu, domin itace jagoran tafiyan kasancewa har gidansu Zahrah ta sani, saboda tasa Asma ta nuna mata....

Zahrah ce zaune a tsakar gida bisa kan tabarma, kwanon abincine aje a gabanta, gaba ɗaya ta kasa tsayawa taci abincin yanda yakamata domin kuwa yau Thursday gobe ne kuma haɗuwarsu da mutumin dayake ɓoye mata kansa, duka nutsuwarta baya gareta, hakanan takejin babu alkhairi a haɗuwarta da mutumin...

Wani irin bangaja da aka mawa ƙofar gidansu shiyasanyata ɗago kanta takai kallonta zuwaga ƙofar gidan nasu..

Wasu tsalan tsalan ƴan

Please Login or Register in order to submit comment