Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

masa, gaskiya wannan girkin nasa kam yacancanci abugasa a jarida kamar yanda ya faɗa, onion and egg soup ya ƙone dankali kuma bai soyuba.

Haka suka haƙura da dankalin suka sha tea tare da snacks  kawai. Bayan sungama cin abincin ya jawota jikinsa, haɗe da ɗaura kansa akan wuyanta, lumshe idanunsa yayi yana me sauƙe numfashi a hankali, wani abu yakeso daga gareta wanda yasan idan ya nema balallai yasamuba, kuma ma koda yasamu to ba a son ranta ta basa ba, shiyasani matuƙar zasu kasance waje ɗaya da'ita tofa har abada acikin sha'awarta zai kasance.. Jin yanda yake sauƙe mata numfashi akan wuyanta ne yasanya jikinta yin sanyi, ahankali kasala tasoma dirar mata, itama lumshe nata idanunta tayi, tana me yin wani tunani acikin zuciyarta.. Tsawon mintuna 15 suka ɗauka a haka babu wanda yace da ɗan uwansa ƙala, shi dai Dr.Sadeeq tsundum yake acikin kogin sha'awa, yayinda itakuwa take tsundum acikin kogin tunanin wani abu wanda bashida amfani a wajenta, wani abu wanda tunaninsa yazame mata jiki da jini, sai dai kuma tasan abun baidace da itaba, baidace da rayuwarta ba, ƙaddara ce kawai ta haɗasu, sannan kuma zuwa yanzu yakamata ace ta manta da babinsa, takuma daina tunasa, sai dai kuma duk yanda taso hakan yakasance abun yaci tura, dole zata haɗa da addu'a,  saboda addu'a  yafi gaban komai, duk da cewa dama tanayi amma dole zata ƙara akan wanda takeyi...

A hankali yajanyeta daga jikinsa haɗe da miƙewa yanufi ɗaki, da kallo kawai tabisa harya shige cikin ɗakin,  "Meke damunsa?" tatambayi kanta a bayyane.
Ganin batada maibata amsa, baikuma dace ta zauna batare da taji damuwarsa ba yasanya ta bisa zuwa cikin ɗakin..

Kwance ta iske sa akan gado yayi ruf da ciki yayinda yasanya hanunsa ɗaya akan mararsa, sam bata fahimci wani abu game da hakan ba, ahankali taƙarasa wajen da yake, cikin murya meɗan sanyi tace "Bakada lafiya ne?"

"Lafiyana ƙalau, kawai dai bacci nakeji ne" yafaɗi haka ataƙaice, baison yayi magana me tsawo ta harbo jirginsa, tsakani da Allah bayason yasake takurata, jiyama da yayi, yauda safe da kuka ta tashi masa, saboda haka yanzu baison ya ɓallo liƙi gwamma yabari ko zuwa dare ne ma, amma kuma idan yatuno irin daɗin dayaji jiya, sai yaji kamar bazai iya haƙura ba..  Haurawa tayi kan gadon haɗe da kwanciya a bayansa,   ƙurawa kwantaccen gashin kansa ido tayi, abubuwa da yawa nasa suna matuƙar burgeta, babu ma kamar idanunsa, idan yana kallonta harwani mutuwa jikinta yakeyi, babu ta inda Dr.Sadeeq ya gaza, komai nasa yayi 100%.

"Ɓacci bai isheki bane?" yayi mata tambayar batare daya juyo zuwa garetaba.

"A'a kawai dai ina hutawa ne" tafaɗi haka a taƙaice don talura kamar bayason damuwa.

Ƙarar wayartane ta karaɗe cikin ɗakin, da sauri ta ɗauko wayar dake aje kan ɗan ƙaramin drawer'n gefen gado.. Ganin Husnah ce me ƙiran yasanya ta ɗaga wayar da sauri, tana ƙoƙarin yin magana taji muryar Husnah tace "Gani a falo"

da sauri tatashi daga kan gadon haɗe da ficewa daga cikin ɗakin, ko bayani bata tsaya yiwa Doctor ba. Shikuwa da kallo kawai yabita harta fice daga cikin ɗakin, lumshe idanunsa yayi haɗi da sauƙe ajiyar zuciya.

Da gudu Zahrah taje ta faɗa jikin Husnah, rungume juna sukayi ƙam cike da kewar juna.

"Nayi kewarki sosai ƙawata" Husnah tafaɗi haka tana me ƙara rungume Zahrah.

Tureta Zahrah tayi haɗe da ɗan turo baki gaba.   "Bawani nan ni ae nayi fushi, tunda ranan nan kin yaudareni kin gudu"

Dariya Husnah tayi haɗe da cewa "Yi haƙuri amaryar likita"

Dariya suka sanya su dukansu,   saida Zahrah ta cikawa Husnah gabanta da su drinks kafun tazo ta zauna akusa da ita..

"Gaskiya dole ne nima acikin wannan shekaran nayi aure, kiduba kiga 2 days kacal amma gaba ɗaya sai wani shining kike" Husnah tafaɗi haka tana me ƙarewa Zahrah kallo.

Harara Zahrah ta wurgawa Husnah "Kinganki ko wallahi banason tsokana, ae ko a engine aka sani baici ace zuwa yanzu nafara walwali ba"

"Hahhh kedai faɗi gaskiya don da alama  doctor  madara  na musamman yake shayar dake kullum" 

Dariyane yakama Zahrah "wai madara" hmmm itasam bata fahimci inda kalaman Husnah suka dosa ba..

"Ke dai baki rabo da tsokana, wace madarace zatasa acikin 2 days kacal na sauya" Zahrah tafaɗi haka tana me duban skin ɗinta..

"Hahhhh madara mana irin taku ta masu aure, ae  babe kawai ki manta, nasan kinbasa yasha kuma kema yabaki kinsha"

Sai yanzu Zahrah ta gano me Husnah ke nufi, duka ta ɗaka mata abaya haɗe da yin dariya. Husnah ma dariyan tayi, kana taɗauki drinks tasoma sha..
****

Hira sosai Husnah da Zahrah sukayi, duk da Husnah tace bajimawa zatayi ba.  Bata jima ba kuwa tayi tafiyarta bayan tabawa Zahrah wasu ingantattun magunguna wanda Hajiya Shuwa ta bata tace takawo mata, har bakin gate Zahrah ta raka Husnah, cike da kewar juna sukayi sallama...
***

Kallon Dad ɗinsa yayi arikice gaba ɗaya idanunsa sun rufe, miƙewa yayi tsaye yasoma takawa ahankali, ganin zaifita daga cikin ɗakinne yasanya, Dad yayi saurin riƙosa,  "Bazaka iya kulawa da kanka ba Zaid, badai Nigeria kakeso mu koma ba?" cike da kulawa Dad ya tambayeshi..

Kansa ya kaɗa kamar wani ƙaramin yaro, ajiyar zuciya Dad ya sauƙe haɗe da ƙara riƙe hanun Zaid ɗin.

"Shikenan ka kwantar da hankalinka gobe zamu koma Nigeria"

Wani irin sanyi Zaid yaji acikin zuciyarsa, badon komai ba saidon zaije yaga Zahrah'n sa, babu ruwansa da wani tayi aure, shi so yarufe masa ido, hargidan nata zaije...  (🙆‍♀🙆‍♀ Anya Zaid bai samu matsala a ƙwaƙwalwarsa ba kuwa? )

Dad kuwa yayanke wannan hukuncinne saboda suna zuwa Nigeria zai ɗaurawa Zaid ɗin aure da ƴar abokinsa, wannan shi kaɗaine zaisanya Zaid ya nutsu yakuma dawo cikin hankalinsa....



      *24/January/2020*



      *Fatymasardauna*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

       *SHU'UMIN NAMIJI !!*


   *Written By*
Phatymasardauna


*Dedicated To My Brother KHABIER*

*🌈Kainuwa Writers Association*

_{United we stand and succeed; our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}_

*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*


           *WATTPAD*
     @fatymasardauna

*Editing is not allowed📵*


       *CHAPTER 98 to 99*


Tana idar da sallan isha, ta ɗauki wata doguwar riga marar nauyi ta zura ajikinta, rigace irin shara shara ɗin nan, gashi kuma yaɗan kamata ta ƙasa, yayinda saman rigan kuwa ya buɗe,  zura rigar kawai tayi  batare da koda  ta kalli kanta a madubi ba tafice zuwa falo.  Sauri take batason Bollywood sufara haska film ɗin Bajrangi Bhaijaan bata kusa, ƙarfe takwas kuma dai dai zasu saka film ɗin, gashi yanzu bakwai ne hadda wasu mintuna, direct kitchine ta wuce taɗauko wani ɗan ƙaramin cup, fridge ta buɗe ta ta ɗauko babban cup ɗin milk shake dake cikin fridge'n ta tsiyaya, ahankali take tafiya tana ɗan zuƙan milk shake  ɗin a bakinta,  yajima yana jingine jikin ƙofa, kan ƙirjinta kawai yaketa kallo tun fitowarta daga cikin ɗakin, daga kan fatar cikinta har brezia'n dake sanye a jikinta, duk sun bayyana kansu a fili kasancewar rigar bata wani ɓoye sirri, sam bata lura dashi ba, hankalinta yana ga tv, hanu yasanya ya jawota jikinsa, saura kaɗan cup ɗin hanunta ya suɓuce ya faɗi ƙasa.  Da sauri ta kalleshi haɗe da ɗan turo ɗan ƙaramin bakinta gaba.

Ta baya ya rungumeta, haɗe da ɗaura kansa akan wuyanta,  cikin wata murya me sanyi yace "Ɗaukar alhaki ne, ko kuma kawai anyi danni ne?"

Cikin rashin fahimtan inda kalamansa suka dosa tace

"Bangane ba"

"Ummmm nima so nake nagane saina baki amsa"   yafaɗi haka yana me ƙoƙarin zame wuyar rigar daga kan kafaɗunta.

Dasauri ta nemi matsawa daga jikinsa, amma saidai bata samu daman hakan ba, domin kuwa ya riƙeta gam..    Baidamu da yanda takeyi ba yasanya hanunsa yazame wuyar rigan, dake rigan dama tana da faɗin wuya sai gashi yakawo wuyan har kusan ƙasa da kafaɗunta,   bakinsa ya ɗaura adai dai saitin wuyanta ta baya, wani irin lafiyayyen kiss yabata wanda saida yasanya tsikar jikinta suka tashi, da sauri ta juyo tana fuskantarsa, idanunsa da suka koma kamar na mejin bacci, ya ɗago ya watsa mata su,  wani dokawa taji ƙirjinta yayi, yanayin da taga ƙwayan idanunsa shiyafi komai sanya mata faɗuwar gaba, har abada bazata taɓa manta mutumin data fara ganin irin wannan yanayin acikin idanunsa ba, kusan nasakamma har yafi na Doctor tsanani, domin kuwa bata taɓa mantawa da yanda idanun suka riƙiɗe suka zama jajaye suke kuma lumshewa alokaci guda ba, Zaid shine mutum na farko da ya fara kallonta da irin wannan yanayin, "mekenan hakan yake nufi? me yasa idanun suka sauya launi alokaci ɗaya?" tayi mawa kanta duka waƴannan tambayoyin da bata da me amsa mata su..

A hankali yake ƙara matseta haɗe da kusanto da fuskarsa daf da tata, burinsa kawai shine yaji bakinta acikin nasa. Kawar da kanta gefe tayi tana me sauƙe numfashi ahankali, gaba ɗaya tunowa da tayi da Zaid ya sanja mata yanayinta,  Zaid ba mutum ne da zata manta dashi ba, lallai dole harta mutu yana cikin rai da zuciyarta, kodan abun da ya aikata a gareta. 
Hanu yasa ya juyo da fuskarta, yazama suna fuskantar juna,  baijirayi komaiba ya ɗaura bakinsa akan wuyanta, kissing ɗin wuyanta yake sosai, wanda hakan ya haifarmata da mutuwar jiki,  cikin nutsuwa ya dawo da bakinsa kan nata bakin, ahankali yake sucking lips ɗinta, lumshe idanunta tayi tana me karɓan saƙon sa, karo na farko a rayuwarta da taji hakan dayakeyi mata yayi mata daɗi, batasan lokacin da ta gama sakar masa jikinta ba haɗe da sake buɗe masa bakinta,  shikuwa dama abun da yake jira kenan, ba ɓata lokaci ya kamo tongue ɗinta yashiga tsotsa a hankali.. Wani irin numfashi kawai yake fitarwa,  ko a iya haka  idan ya tsaya yasan zaisamu gamsuwa, har  abada shikam yanaji ajikinsa bazai taɓa gajiyawa da tsotsan baki da kuma harshenta ba, wani ɗanɗano na musamman yakeji acikin bakinsa idan yana tsotsan harshenta,  yakan rasa duk wata nutsuwarsa idan laɓɓansu suka haɗe waje guda,yakan tsinci kansa cikin matsanancin shauƙi dakuma wani irin yanayi me daɗin gaske.
 
Ƙafafunta ne suka soma saƙewa, gaba ɗaya tsayuwar ta gagareta, yayinda shikuwa yaketa jifanta da salonsa iri iri, idan zasu shekara a haka sai dai ƙafafunsa su gaji suƙi ɗaukarsa, amma bawai shi ya gajiya da shan tausassun laɓɓanta ba,  ƙoƙarin zamewa ƙasa takeyi da sauri ya riƙota haɗe da ɗagata caɗak kamar wata ƴar ƙaramar yarinya...        Direct ɗaki yanufa da ita, bai direta ako inaba sai akan gado,  ɗan ƙaramin  ƙara tasanya haɗe da cewa  "Wayyo nauyi!"

Dariya yayi haɗe da jan hancinta cikin muryarsa da ta soma sarƙewa yace
"Waye ne me nauyin?"

"Kai mana!" tafaɗa a shagwaɓance.     Gaba ɗaya rigan jikin nata ya zame ƙasa, haɗe da soma bin ko wani ɓangare na jikinta da hot kiss, shiru tayi tanajin yanda yake tsotseta kamar wani maye, amma kuma fa saƙon nasa  na yau yana shiga inda ya kamata domin kuwa tun ɗazu jikinta yagama mutuwa. 

Kissing ɗin bakinta yaci gaba dayi, batasan lokacin da itama ta soma tayasa ba,  baitaɓa tunanin zata taya saba, shiyasa sanda takama harshensa tana tsotsa a hankali, yaji gaba ɗaya ya ruɗe haɗe da zaucewa, jiyake kamar awata duniyar aka tsoma shi..  Yanayin yanda yake romancing ɗinta ne yasa har kuka sai da tayi masa wanda batasan na menene ba,  jitakeyi kamar kan nipples ɗinta zasu cire, tsabar anbasu kyakkyawan sucking.
"wallahi doctor ma mugu ne" tafaɗi haka acikin zuciyarta..... Yau dai ba iya Dr.Sadeeq bane kaɗai yaji daɗin kasancewarsu tare  ba, hadda ita kanta me daɗi'n nasa,  sai dai kuma gaba ɗaya zautar dashi takeyi, yauma da ƙyar yasamu ya iya dawowa cikin duniyarmu, bawai don yasoba saidon gudun wahalar da ita... A hankali yasa hanu yashafa gashin kanta, haɗe da manna mata kiss akan goshinta, Zahrah dake kwance luf acikin ƙirjinsa ta lumshe idanunta haɗe da sake cusa kanta acikin ƙirjin nasa..

"I'am sorry me daɗi na na gajiyar dake ko? ba laifi na bane, inata so nayi controlling ɗin kaina amma nakasa, ke ɗince kin cika da...."     saurin toshe masa baki tayi haɗe da sake ɓoye kanta acikin ƙirjinsa,  kunya takeji tsantsa idan yaƙirata da sunan me daɗi'n nan, sai taji gaba ɗa tazama wata iri da ita..  Tsotsan hanunta dake kan bakinsa yasoma yi, da sauri tacire hanun nata haɗe da tashi zaune, bargo ta rufa ajikinta tayi toilet da sauri gudun kar ya tsaidata,  jingina tayi da jikin ƙofar toilet ɗin tana sauƙe numfashi ahankali,   gaba ɗaya abun daya wakana a tsakaninsu ne yashiga dawowa cikin kanta, tanaso ƙwarai taga tana farantawa mijinta rai, zatayi iyaka ƙoƙarinta wajen ganin tayi yaƙi da zuciyarta, wajen ganin ta basa farinciki me ɗorewa yanda ya kamata.    Wanka tayi haɗe da zura rigan wanka tafito...

Tsaye tagansa daga shi sai 3 guater jeans ajikinsa, kallo ɗaya tayi masa tayi saurin ɗauke kanta, har yanzu bata taɓa amincewa yaga tsiraicinta cikin haske ba, sannan haka itama bata taɓa tsayawa takalli jikinsa acikin haske ba komai sunayinsa ne acikin rashin wadataccen haske,    "Jikinsa yanada kyau" tafaɗi haka acikin zuciyarta haɗe da ɗan satan kallon 6 packs ɗin dake kwance akan cikinsa.

Raɓawa yayi ta gefenta yashige cikin bathroom ɗin fuskarsa ɗauke da wani irin murmushi.

Wata ƴar ƙaramar riga wacce ta tsaya iyaka guiwarta kawai ta sanya haɗe da sanya igiyoyin dake gaban rigar ta ɗaure cikinta, haurawa tayi kan bed ɗin ta kwanta.. Yana fitowa yakuma sanya wani 3 guater jeans ɗin haɗe da feshe jikinsa da turare..  Wutan ɗakin yakashe yakunna musu na bacci, hawa kan gadon yayi haɗe da jawota jikinsa,  kwanciya ajikinsa yanayi mata matuƙar daɗi shiyasa aduk sanda yajawota jikinsa bata bijirewa.      "Kinyi addu'a?" yatambayeta.

Kai kawai ta ɗaga masa alamar "Eh"   addu'a yayi shima ya shafa kana ya lumshe idanunsa, ahankali yake shafa bayanta, cikin mintuna ƙalilan bacci ya ɗauke ta, sannu sannu shima bacci me nauyi ya ɗaukesa....

*****

Washe Gari.

Ƙarfe 5 dai dai jirginsu ya sauƙa acikin Nnamdi Azikwe International airport.

A hankali yake taka matattakalan sauƙowa daga cikin jirgin, sanye yake da riga da wando irin na sanyi navy blue colour,  hatta takalman  dake sanye a ƙafafunsa navy blue colour ne, yayi kyau sosai yaƙara haske, sai dai kuma sosai rama ta bayyana kanta ajikinsa.  Yana gama saƙƙowa daga kan matattakalan yanufi wajen da motocin da sukazo ɗaukarsu ke fake,  4matic yabuɗe yashiga haɗe da hakincewa agidan baya, bayasan damuwa shiyasa bayason shiga mota ɗaya dasu  Dad ɗinsa..    Harsuka isa gida tunani yakeyi, maiya kamata yayi? sai kuma yanzu daya dawo yakeji gaba ɗaya Nigeria'n tayi masa ƙunci haɗe dayi masa duhu,daya kulle idanunsa Zahrah kawai yake gani...    Yana fita daga cikin motar direct ɓangarensa dake cikin gidannasu ya nufa.     Falo'n sa tsab-tsab yake tamkar wanda wani yake rayuwa aciki, bedroom ɗinsa ya wuce, yana shiga yaƙarasa gaban wani tangamemen hotonta da yasa aka masa  kalanda (Calender)  dashi yakafa ajikin bangon ɗakin,  rungume ƙaton kalandan yayi haɗe da lumshe idanunsa.

"I really Miss you My Zahrah!"

ya faɗi haka cikin murya me sanyi da kuma tsananin rauni, hanu yasanya yashafa daidai saiti laɓɓanta dake jikin hoton calender'n.
"Bana tunanin zan daina kewarki Zahrah na,  tunaninki yazama abincin ruhina, inasonki sosai,  lokaci yayi daya kamata  ki dawo gareni, muyi rayuwar auren mu cike da tarin farinciki, nadaina komai Zahrah shan giya, zina, duk na daina please ke nake jira har yanzu, ina fata baki bawa wanina kanki ba?"  yanayin yanda yake magana da hoton idan ka gansa kaitsaye dasunan mahaukaci zaka ƙirasa, domin kuwa me cikakken hankali bazaiyi haka ba..       Wayarsa ya ɗauka yayi dialing number'n Abid, bugu uku Abid ya ɗauki wayar baijirayi abun da Zaid ɗin zaice ba yace
"Wow surprise kenan?"

Ƴar ƙaraman tsuka Zaid yayi cikin muryarsa me rauni yace "Inason ganinka Abid, yanzu agidan mu please!"  baijirayi me Abid ɗin zaice ba ya katse wayar haɗe da cilla wayartashi kan gado, yasan Abid bazaiƙi zuwaba shiasa baijirayi amsar saba yakashe ƙiran.  Zama yayi akan wata kujera dake cikin ɗakin,  kan ɗan madaidaicin fridge'n dake aje cikin ɗakin ya maida idanunsa, jiyake kamar yatashi yaje ya ɗau wine ɗinsa yasha, sai dai kuma wata zuciyar tana gargaɗinsa da cewa, Zahrah bataso, tun randa ta gayamasa wata baƙar magana akan shan wine da yake, bai ƙara shaba harkuwa rana me kamar ta yau, duk da kuwa irin azabtuwan da yakeyi idan baisha wine ɗin ba, saboda yariga daya saba.  Shiru kawai yayi haɗe da kama kansa ya rumtse idanunsa..    Abid ne yaturo ƙofar ɗakin yashigo bakinsa ɗauke da sallama, ciki ciki Zaid ya amsa masa sallaman haɗe da watsa masa idanunsa da sukayi jajur dasu.. Cike da mamaki haɗi da tsoro Abid ya matso kusa da Zaid da ɗan sauri.

"Zaid meke damunka haka? yaushe kuka dawo? yajikin naka?" duka waƴannan tambayoyin Abid yayiwa Zaid su a lokaci ɗaya kuma duk amsarsu yake nema idan zai samu..

"Abid nakasa mantawa da ita, itace nutsuwar tunani na, banajin zan iya kaiwa lokaci me tsawo batare da na sanyata acikin idanuna ba, Inasonta sosai kai kasani!"

Kallon Zaid kawai Abid keyi yamarasa me zaice masa..  Kallon ɗakin yashiga yi sai alokacin ya Lura da maka makan hutunanta dake manne ajikin bangon ɗakin Zaid ɗin,wasu zane ne wanda Zaid ɗin yayi wasu kuwa hotunanta ne.  Wani irin tausayin Zaid ɗinne ya tsirga masa me tsanani, shidai bazaice baitaɓa soyayya ba, amma kuma baita ɓayin kwatan kwacin irin wannan son me tsanani da Zaid keyi ba. Zama yayi akan kujeran dake fuskantar na Zaid, hanun Zaid ɗin yakamo haɗe da cewa "Kazama jarumi Zaid, kada kamanta fa yanzu Zahrah matar wani ce kuma...."

"Ya isheka haka Abid!!" Zaid ya katse Abid cikin tsawa sosai.

"Matar wani, Matar wani, abun da kuke ta faɗa kenan, meyasa ni bazaku duba halin danake ciki ba? shikenan don tana matar wani sai nadaina sonta? kafun wanda kuke ikirarin matarsace yasota nine nan nafara sonta,  kada kataɓa tunanin zan daina son Zahrah Abid, bakuma zan taɓa samun nutsuwa ba harsai Zahrah ta zamo mallakina, kataimakeni Abid kazo muje gidanta mu ɗaukota tazo nan mu rayu tare nasan itama tana sona!"  cikin murya me tsananin rauni yake faɗan maganar..

Kai kawai Abid yake girgizawa azuciyarsa kuwa wutar tausayin Zaid ne ta kunno, So yamakantar da zuciyar Zaid yasanya harya kasa tuna cewa Zahrah a yanzu ta haramta a garesa, shi duk iskancinsa baya tunanin Zaiso matar da take da aure,  dukansu shida Zaid sunsani cewa shangiya da zina duk haramunne amma kuma saboda son zucia irin tasu suke aikatawa,  yanzu kuma ga wani sabon saɓon da Zaid yafito dashi, yana goya masa baya akan komai, amma a wannan karon kam baya tunnin zae goya masa baya yaci gaba da son matar aure, haƙiƙa Zahrah takai macen da kowani ɗa namiji zai sota, amma kuma tunda ayanzu tazama mallakin wani babu amfanin Zaid yata takura kansa akanta.   "Zaid!" Abid yaƙira sunansa araunace.  Kansa kawai ya ɗago ya kallesa batare dayace dashi komai ba.  

"Kada kaga laifina Zaid, mun hau wani mataki da yanzu dole ne  mufaɗawa kanmu gaskiya, menene ribar da zakasamu idan kacigaba da dakon soyayyarta acikin zuciyarka? tazarar dake tsakanin ka da Zahrah a yanzu yanada matuƙar yawa,  tana tare da mijinta kuma nasan zuwa yanzu tajima da zama shi kuma shima yazama ita, me yasa to kowannan bai isa yasanya kacireta acikin zuciyarka ba, akoda yaushe kada kana tunanin cewa wai Zahrah zata dawo gareka,  so ne yasa mijinta ya aureta, kaga kenan haka nan kawai bazai rabu da ita ba, kasa aranka ma idan ƙaddara ta rabasu babu yiwuwar Zahrah zata amince ta aureka,  kai da kanka kasan haka amma zuciyarka tana yaudaranka, haƙiƙa nima shaidane akan cewa har yanzu Zahrah tana sonka, amma hakan bawai yana nuni da cewa zata iya kashe aurenta ta aureka ba ne, kai koma da ace tafito agidan aurenta to bana tunanin Zahrah zata amince ta aureka,  kamanta da ita Zaid, kasawa zuciyarka salama, akwai mata da yawa acikin ƙasarnan dama sauran wasu ƙasashen kasamu wata kabawa ajiyar zuciyarka, na tabbatar watarana komai zai zamo labari!" Abid yaƙare maganar yana me dafa ka faɗan Zaid almar son ƙarfafa masa guiwa..

Wata tsuka me ƙarfi Zaid yaja haɗe da ture hanun Abid dake kan kafaɗansa...    har abada bazai daina yiwa wanda yace yarabu da Zahrah kallon mahaukaci ba,  wai Zahrah'nsa ake so yamanta ya daina sonta, sai yaushe mutane zasu gane cewa cire so bakamar cire takalmi bane? miƙewa yayi daga zaunen da yake   haɗe da shigewa cikin bathroom ko sake kallon inda Abid ke zaune baiyi ba.. Ajiyar zuciya Abid ya sauƙe  haɗe da gyara zamansa akan kujeran, yana nan yanajiran fitowarsa koda awa ɗaya zai share a banɗakin bazai tafiba saiyajirasa,  Zaid bayason gaskiya wani lokaci, kuma kozai mutu saiya faɗamai gaskiya, ae soyayya ba hauka bane, son matar aure mezai jawo maka inbanda wahala da ƙarin zunubai....


Zaid kuwa yajima tsaye ruwa na fitowa daga  shower yana dukan jikinsa....  Ɗaure da towel a ƙugunsa yafito daga cikin bathroom ɗin,  kallo ɗaya yayiwa Abid yaɗauke kansa,  Abid na kallonsa   har yagama shafa man lotion ajikinsa...

"Saboda nace kamanta da Zahrah shine kake fushi dani? kai kanka kasan abun da kakeyi ba daidai bane Zaid sannan....."

"Ya isa Abid!" Zaid ya katsesa aɗan kausashe. 

Murmushi kawai Abid yayi haɗe da sa kai yafice daga cikin ɗakin, yasan Zaid ya hau sama bazai taɓa sauraransa ba, wanda yayi nisa bayajin ƙira.

****

Tun fitarsa ta shige cikin kitchine  yau bataso ya sayo musu abinci tafiso ta girka musu da kanta,  fried rice tayi wanda taji zallan tsokan kaza,   da kanta ta haɗa shaka ta sanya acikin fridge, takammala komai yanzu saura kawai tayi wanka.. Ƙaran wayarta take ta jiyowa, da sauri tanufi ɗaki inda wayartata take.  Wata number ce  special ke yawo akan screen ɗin wayar, ɗan tsayawa tayi tana ƙarewa number'n kallo, har ƙiran ya katse bata ɗauki wayarba, wani ƙiranne kuma sake shigowa.... A hankali ta ɗaga wayan ta kara akan kunnenta.   

"Zahrah!!!" taji wata murya wacce bazata taɓa mantawa da itaba ta ƙira sunanta, jikinta ne yasoma rawa yayinda bugun zuciyarta yaƙara tsananta shin dagaske ne kokuwa kunnuwanta ne basuji da kyauba,  kusan mintuna biyar ba asake cewa komai daga cikin wayarba haka kuma itama bata ce komaiba..

"Wa....y..e?"

tayi tambayar cikin wararrun kalmomi yayinda tsoro ke sake ɗarsuwa acikin zuciyarta.

"Zahrah na! me yasa zaki barni? kin barni cikin ƙunci da tarin damuwa, yazanyi da soyayyarki ne Zahrah, bazan iya rayuwa ba idan babu ke, please ki taimaki rayuwata dakuma zuciyar da ta jima da matowa akan ƙaunarki!!"

Jikinta ne gaba ɗaya yaɗauki rawa harbatasan sanda wayar ta zame daga hanunta ba, take ta faɗi ta tarwatse a ƙasa.  Itakanta batasan sanda ta zame ta durƙusa guiwowinta a ƙasa ba,  hawayene suka shiga fitowa daga cikin idanunta.   "Zaid" shine sunan da take ta nanatawa acikin zuciyarta, sai yaushene Zaid zai barta ta huta tayi rayuwar aurenta cikin nutsuwa? anya kuwa Zaid baisamu matsalan ƙwaƙwalwa ba? ta tambayi kanta, shiru tayi haɗe da lumshe idanunta ƙirjinta kuwa har yanzu bai daina bugawa da sauri ba.   

Cikin tsananin mamaki yake kallonta, da sauri ya ƙaraso inda take durƙushe haɗe da tsugunnawa yaɗaura hanunsa akan kafaɗunta
"Meke faruwa?" yatambayeta cike da kulawa.

Da sauri tabuɗe idanunta da suke a lumshe, batasan yaushe yashigo ba.
Kallonta yakeyi sosai da alama amsa yakeson ji daga bakinta.

Dasauri tashiga goge hawayenta haɗe da tashi tsaye,   kallonta yakeyi harta shige cikin toilet,  idanunsa yasauƙe akan wayarta wanda ta tarwatse akan tiles gaba ɗaya ma screen ɗin wayar ya fashe, mamaki  haɗi da ɗaurewar kaine matuƙa suka kamashi, "Meya faru? yaganta tana hawaye gakuma wayarta daya gani aƙasa a tarwatse"  yayi mawa kansa tambayar cike da son sanin amsa. Tattare wayar yayi haɗe da komawa kan gado ya zauna zuciyarsa cike fal da tarin tambayoyi..

Zahrah kuwa tana shiga cikin toilet ta soma sauƙe ajiyar zuciya akai-akai, meta aikata hakane, gashi yanzu yazo ya ganta acikin halin damuwa, tasan dole ne shima saiya sanya kansa a damuwa, yanzu idan ya tambayeta metasan zata ce masa, wasu hawayenne suka kuma zubowa daga cikin idanunta, da sauri ta sanya hanu ta share.. Haka tayi wanka duk tanajin zuciyarta babu daɗi, ɗan ƙaramin towel ta ɗaura ajikinta, wanda yatsaya a iyaka cinyarta. A hankali ta buɗe ƙofar bathroom ɗin tafito,  karaf idanunsu suka haɗe waje guda, da sauri ta kawar da kanta gefe, haɗe da nufar wajen drawer.. Kallon

Please Login or Register in order to submit comment