Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Inna da Baffa ke kallon busheshshen jinin dake manne a ƙafofinta,  "Nashiga uku Malam mai yasameta ne? kagafa taƙi buɗe idonta !" Inna tafaɗa cikin ruɗewa, " Ina zansani  Salame ba dake muka tsintota a ƙofar gida ba,  yanzu dai bana kawo ruwa ki zuba mata kozata farfaɗo "

Ruwa Baffa yakawo Inna tashiga zubawa Zahrah akan fuskarta, amma ina aiko alaman motsi Zahrah batayi ba,, " Mun shiga uku malam, kagafa haryanzu taƙi motsawa !" Inna takuma faɗa, cikin tsoro,    "Banaje nataro mai taxi sai muje asibiti !!" Baffa yafaɗa cikin gaggawa domin yatsorita da al'amarin Zahrah'n....

Mintuna ƙalilan Baffa yadawo damai taxi,  wata baƙar riga Inna tasanyama Zahrah, haka suka ɗebeta, aka sanyata acikin taxi kaitsaye suka wuce asibitin cikin gari.....

Mai taxi na fakawa Baffa ya arta a guje, yayi cikin asibitin, yanashiga yataradda wasu nurses suna zaune, bawani ɓata lokaci Baffa yasoma kora musu bayani akan cewa yazo da marar lafiya ne,,  taɓe baki ɗaya daga cikin nurses ɗin tayi, haɗe da yi mawa Baffa kallon rainin hankali, cike da gadara tace " Bama karɓan marar lafiya sai anyanki kati " jiki na rawa Baffa yace " Kiyi haƙuri bansani bane, nawa ake yankan katin? kuma a ina ake yanka ?"   bakinta takuma taɓewa haɗe da cewa " 1k ne sannan kuma acan wajen ake yanka " taƙare maganar tana maiyi masa nuni da wani waje,,

"menene kuma 1k yarnan ?" Baffa yatambaya,,  cike da shaƙiyanci duka Nurses ɗin suka sanya masa dariya,     "Hmm lallaima tsohonnan wato kai bakasan komai ba, amma kaɗauko marar lafiyanka kukazo asibitinnan, Hmm talaka baijira kansa ba, to abun da ake nufi da 1k shine dubu ɗaya " again nurse ɗin taƙara magana tana yatsine fuska... "To to to shikenan banaje na yanka " Baffa yafaɗa, cikin hanzari yanufi inda wannan nurse ɗin ta gwada masa,  sosai Baffa yajima kafun yasamu ya yanki katin, saboda zalunci ma mai yanka katin dubu ɗaya da ɗari biyar takarɓa a wajensa, babu kuma yanda ya'iya haka yabayar,   yana kawo katin yamiƙamawa nurse ɗin, yatsina fuska ta sakeyi haɗe da cewa aje katin a can, zuwa anjima maduba,,,  

"Dan girman Allah ƴarnan kitaimakeni, wallahi ɗiyatace nakawo ko numfashi batayi, bansaniba ma ko tamutu kotana da rai !!" Baffa yafaɗa cike da tashin hankali, ganin suna neman aje katin daya basu,

"What ! bata numfashifa kace ? " su duka Nurses ɗin suka faɗa cikin ruɗewa, "ƙwarai kuwa " Baffa yabasu amsa... Ai da hanzari nurses ɗinnan sukayi waje, yayinda wasu sukatafi ɗauko  wannan ɗan gadon da ake ɗaura mutanen da aka kawosu emergency akai,,     akan wannan gadon aka ɗaura Zahrah da hanzari suke turata,don kaita abata taimakon gaggawa.... duk yanda suka so ceto rayuwarta abun yafi ƙarfinsu,   ɗaya daga cikin Nurses ɗinne ta sharce gumin dake kan goshinta,  ɗan nisawa tayi haɗe da kallon ƴan uwanta, cike da gajiya tace " gaskia inaga bazamu iya aikin nan ba, domin kuwa case ɗin fyaɗe ne, ba kuma hurumin mu bane, dole sai mundangana ga Doctor S.S domin wannan aikin sane "    "Cab gaskia inajin tsoro mar'uda yanzufa time ɗin shin sane, kinaga yadace mukai masa wannan case ɗin ?, kuma ma idan yasan abun da muka aikata tun farko, wallahi bazamu share ba.."  wacce ke tsaye gefen Mar'uda ta faɗa,, " gaskia saidai yayi haƙuri Aisha domin kuwa tabbas shiɗinne kaɗai zai iya kamo bakin zaren, banaje naƙirasa " Mar'uda nakaiwa nan a zancenta tafice daga cikin emergency room ɗin.....

Zaune yake akan tankamemiyar ƙujeran dake cikin haɗaɗɗen office ɗinsa,  kyakkyawan matashin saurayine wanda aƙalla bazai wuce 30 years ba, sanye yake da riga da wando baƙaƙe, yayinda yaɗaura farin suit akai mai matuƙar kyaun gaske,,  riƙe yake da wani file ahanunsa, yana dubawa yayinda yake shan coffee  ahankali, da'alama abu mai mahimmanci yakeyi,     farine shi amma basosai ba, sannan yana da ƙawataccen saje akan fuskarsa, yana da manyan idanu dakuma dogon hanci, wanda suka taimaka wajen bayyana kyawunsa, masha Allah shima dai kyakkyawane na nunawa sa'a....

Knocking ƙofar office ɗinnasa akashi ga yi,   ajiye kofin coffee ɗin nasa yayi, haɗe da yamutsa fuska, cikin wata irin murya yace "yes, come in "  Mar'uda ce taturo ƙofar tashigo, cike da girmamawa tace " sorry for disturbing you sir, we have an emergency patient"

" but i have closed for today, inama ƙoƙarin tafiya gidane " Doctor S.S yafaɗa cikin gajiyawa..

"Sir, the patient has been raped and she is unconscious !!"

" Suban Allah, fyaɗe fa kikace Mar'uda !!"  Doctor S.S ya faɗa cikin kaɗuwa,, kai Mar'uda ta ƙaɗa alamar eh,   miƙewa yayi cikin gaggawa yace  " Muje "... Doctor S.S na gaba Mar'uda, nabiye dashi haka suka nufi emergency room ɗin,,   yana shiga cikin Emergency room ɗin yaji ƙirjinsa ya buga,   da sauri yaƙarisa kan Zahrah dake kwance tamkar gawa,   take sauran Nurses ɗin nan suka shiga cikin taitayinsu, domin sun san Doctor S.S baya wasa, musamman ma idan akan irin wannan case ɗinne na fyaɗe...  Taimakon gaggawa Doctor S.S yashiga bawa Zahrah,  bayan yasanya Nurses sun haɗa masa kayan aiki,   bakaɗan ba Doctor S.S ya tsorita, ganin irin taɓargazan da akayi mawa Zahrah a ƙasanta, domin sosai wanda yayi mata fyaɗen, ya ɓarkata,, "Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un !!" kawai Doctor S.S kefaɗa acikin zuciyarsa, domin kuwa duk wanda yayi mata wannan abun yacika marar imani kuma marar tausayi,   Doctor S.S nayi mata ɗinki amma zuciyarsa ƙuna da tafarfasa takeyi, "Haryaushene za'a ɗauki mataki akan banzayen mazajen da sukeyi mawa yara mata ƙanana fyaɗe ?, har yaushe za'adaina yi mawa mata fyaɗe ?, haryaushene  wasu mazan zasu daina cin mutumcin mata tahanyar yi musu fyaɗe ?,  ako da yaushe yana matuƙar jin ciwo acikin zuciyarsa, aduk sanda yaji cewa anyi mawa mace fyaɗe, tabbas da ace yana da wani babban iko, to da ya ɗauki tsattsauran mataki ga duk wani namiji da yayi mawa mace fƴaɗe" haka dai Doctor S.S yaɗinke Zahrah tsaf, bayan yagama ɗinketa ne, yayi mata treatment ɗin goshinta wanda yake a fashe, aƙalla dai Doctor S.S yakai kusan 1 hour yanayi mawa Zahrah teatment,   allurai yayi mata kala biyu,  saida yakammala yi mata komai kafun yafice daga cikin ɗakin bayan yabawa Nurses umarnin kaita ɗakin hutu, duk dacewa bata farfaɗo ba...   "Suwaye suka kawota ?" Doctor S.S yatambayi Mar'uda fuskarsa babu alamar wasa,,  inda su Baffa da Inna ke zaune Mar'uda tayi masa nuni,,  cike da ɓacin rai Doctor S.S yanufi inda suke...

"Kunkuwa san mekukeyi ? taya zakubanzatar da ɗiyarku, har aimata mummunan fƴaɗe irin wannnan ?, ko kunsan wani irin haɗari ƴarku tashiga, a sanadiyar wannan fyaɗen da akayi mata ?, maiyasa iyaye kuke sakaci da rayuwar ƴaƴayenku mata ne?, shin bakusan cewa ranan gobe, Allah zai tambayeku game da amanarsu daya baku ba ? ".. Doctor S.S yajero musu tambayoyi cikin matsanancin ɓacin rai,, jikin Baffa da Inna ne yayi laƙwas, domin su sam basuma san cewa fƴaɗe akayimawa Zahrah'n ba sai yanzu, take Inna tasoma share ƙwalla hadda shashsheƙar majina,, wani irin kallon tsantsar takaici Doctor S.S  yayi mawa su Baffa haɗe da cewa "Kubiyoni Office " yanakaiwa nan a zancensa yanufi hanyar office ɗinsa,, haka su Baffa suka rufa masa baya jiki ba ƙwari, domin kuwa dukansu sun kaɗu dajin cewa wai fyaɗe akayimawa Zahrah, to waye ? suka tambayi kansu...  Zama yayi akan kujera gaba ɗaya jin zuciyarsa yake ba daɗi, wani irin masifaffen haushin iyayen yarinyar ma yakeji, da ƙyar ya iya daure zuciyarsa,  yace "Ya akayi abun yafaru ?"   gyara zama Baffa yayi haɗe da cewa "Wallahi likita bansani ba, nidai natafi wajen sana'ata, dana dawo kuma sai bantarar da Zahrah a gida ba,  shine kuma daga baya nataradda ita yashe a ƙofar gida !" Baffa yaƙare maganar yana matsan ƙwalla,    laɓɓansa ya cije cike da takaici,  domin gaba ɗaya abun ma yalura rashin kula ne yajawo, amma tun da shi ba ɗan sanda bane bai dace yatsare su da tambayoyi ba,   "  Yanzu dai maganar gaskia ƴarku tana cikin hatsari, tana matuƙar buƙatar taimako, wanda yayi mata fyaɗe yayi mata rauni sosai a gabanta, wanda yaja dole akayi mata ɗinki, amma ba'anan matsalar take ba, ba lallai ƴarku, ta farfaɗo  yau ba, zata iyakaiwa gobe koma fiye da haka, sannan baizama lallai ta dawo cikin hayyacinta ba kodama ta farfaɗo ɗin, saboda ana yawan samun irin waƴannan matsalolin, dayawan mata idan aka musu fyaɗe yakan taɓa musu ƙwaƙwalwa, sai dai ako dayaushe fatanmu shine komai yazo da sauƙi ".... Bakaɗan ba hankalin su Baffa yatashi jin abun da Doctor ke cewa, ya ilahi wani irin iftila'i ne ya faɗo cikin rayuwarsu haka ????......

((Kuyi haƙuri jiya kunjini shiru abubuwane sukaimin yawa, Zee black nagode da kulawa...))

    *10/November/2019*

     *MRS SARDAUNA*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

         *SHU'UMIN NAMIJI !!*

     *Written By*
phatymasardauna
       *🎈Mrs Sardauna🎈*

*Dedicated To My Brother Khabier....*

*🌈Kainuwa Writers Association*

*((United we stand ans succeed our ambition is to entertain & motivate the mind of readers))*

*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*

            *WATTPAD*
      @fatymasardauna

   *Chapter 25 to 26*

"Yanzu likita ya za ayi kenan ?" Baffa yatambaya fuskarsa ɗauke da damuwa,  ajiyar zuciya Doctor S.S yasauƙe haɗe da cewa " asamu wanda zai kwana da'ita, kafun gobe Idan Allah yakaimu " yanaƙare zancen, yasoma tattare files ɗin dake baje kan table ɗin dake gabansa..

Tuƙi yakeyi amma gaba ɗaya jinsa yake wani iri, duk wata ƴar walwala da kuzarinsa sun ƙaura daga garesa, sosai fyaɗen da akamawa yarinyar yataɓa ransa, hakanan yakejin matsanancin tausayin yarinyar na ratsa zuciyarsa,gaskia wasu mazan basu da imani, ka suma ƴar ƙaramar yarinya kamar wannan, ka danneta kakuma yi mata fyaɗe da ƙarfin tsiya, idan kai akamawa taka kuma bazakaji daɗi ba, ya  Allah kasakama bayinka,...  Horn biyu yayi kacal maigadi ya wangale masa tankamemen gate ɗin gidannasu, a parking space yayi parking motar tasa, haɗe da fitowa, kai tsaye ɓangarensa yanufa, domin yana da yaƙinin zuwa yanzu su Hajiyarsa sunshiga, ko yaje ɓangarensu bazai tadda suba,

"SADDIQ!!" wata ƴar dattijuwar mata dake tsaye a bayansa taƙira sunansa,,  ƙaƙƙarfan ajiyar zuciya Doctor S.S yayi haɗe da juyowa, ƙoƙarin ƙaƙalo murmushi yayi ya aza akan fuskarsa,   "Hajiya barka da dare" yafaɗa cike da girmamawa, "Yauwa barka dai, sai yanzu kake dawowa ?"  sunkuyar dakansa ƙasa yayi haɗe da sanya hanunsa abayan kansa yashiga shafa ƙeyarsa,   "Hmm da kyau, duk nasan mai yajawo hakan, rashin iyali ne, kuma wallahi komai yakusa zuwa ƙarshe, a wannan karon ko kana so ko baka so,yazama dole kafitar da mata ko kuwa, in zaɓa maka cikin ƴaƴan ƙannena, bazanci gaba da sanya maka idanu ƙato dakai ace baka da mata ba !!" Hajiya tafaɗa cikin faɗa,  "Kiyi haƙuri Hajiya Insha Allah nan ba da jimawa ba komai zai dai dai ta"

"Koda yaushe haka kake cewa, inanan inasa ido, idan naji shiru kuma kasan sauran " Hajiya tafaɗa,  juyawa tayi kaitsaye tanufi ɓangarenta, shima nasa ɓangaren yanufa, jinsa yake amatuƙar gajiye,  wanka yayi haɗe da bin lafiyar gado ya kwanta, abu na farko daya fara ziyartan idanunsa bayan yarufesu, shine hoton fuskar Zahrah, sosai hoton fuskarta keyi masa gizo,acikin idanunsa, da sauri yabuɗe idanun na sa, a zuciyarsa yana mai mamakin faruwar hakan,  dayaga abun bana ƙare bane, kawai saiya dangana hakan, dacewa tsananin tausayinta ne yajawo hakan......

ZAID kuwa yana barin Zahrah kai tsaye TRANSCORP  HILTON yanufa, domin dai yauma yana da meeting a can...  Bayan sunkammala meeting ɗinne, kai tsaye yawuce ɗakinsa dake ɓangaren V.I.P,,   yanashiga yasoma rage kayan dake jikinsa, direct bathroom yashige yasakarmawa kansa shower,, wani irin sanyi da nishaɗi yakeji a cikin zuciyarsa, tun bayan abun daya shiga tsakaninsa da Zahrah, yakejin ransa yayi fari, nishaɗi kawai yakeji acikin zuciyarsa, gaskia yau yasha zallan madarar daɗi, domin kuwa sosai ɗanɗanon Zahrah yayi masa hundred percent, yanason mace mai ɗanɗano sosai...   Yana fitowa daga wanka, wayarsa dake aje kan gado, tasoma ƙara haɗe da kawo haske, alamar shigowar ƙira,  saida wayar tasa takusa katsewa kafun yaɗauki wayar haɗe da karawa akan kunnensa, "Shigo ciki" Zaid yafaɗa a taƙaice haɗe da cilla  wayartasa kan gado,,    Abid ne yaturo ƙofar ɗakin yashigo,, rungumar juna sukayi, kamar yanda suka saba koda yaushe idan sun haɗu,,

"Daga ina haka ?" Zaid ya tambayi  Abid, murmushi Abid yayi haɗe da zama akan hamshaƙiyar kujeran dake gefen gadon ɗakin,  " yau nasha sweet abokina, wata babe nasamu mai zafi, inagayamaka tashayar dani zuma !!" Abid yafaɗa cike da nishaɗi,,     Dariya sosai Zaid yayi hadda ƙyaƙyatawa,  shiru kawai Abid yayi yatsaya yana kallon Zaid, domin dai Zaid baya dariya abanza, abune mai wuya kaga dariyansa, sai dai idan ya ƙulla wani abun...     " Final !!" Zaid yafaɗa yanamai cije laɓɓansa,, zaro idanu Abid yayi cike da mamaki yace " what ! ? badai kanaso kacemin harka gama da Zahrah ba ??"   ƙayataccen murmushi Zaid yayi haɗe da cewa "Tuntuni harma anwuce wajen " dariya Abid yayi haɗe da cewa " Har yau bansan kai wani irin mutum bane Zaid, idan kaso abu, to ko ta wani hali sai ka sameshi, Allah sarki, Innocent girl, tanacan tana fama, nasan kabata kaya da yawa, may be ma haryanzu bata san awace duniya take ba " Abid yafaɗa... Still murmushi Zaid yayi haɗe da gyara zamansa, wayarsa yajawo yashiga latsawa, amma fuskarsa ɗauke take da murmushi... Ganin haka yasa Abid sha re maganar domin yafahimci me abokinnasa yake nufi,, Jefi jefi suke hira da Abid.....

Washe gari... Har 9:00 am Zahrah bata farfaɗo ba, Doctor S.S yazo yasake dubata, yakumayi mata duk wani abu daya kamata, amma still ko motsawa batayi ba... Abu kamar wasa tun anasa ran farfaɗowar Zahrah  har dai akasoma cire rai, domin kuwa yau kwananta biyu batasan inda take ba... Sosai Doctor Saddiq yake bawa Zahrah kulawa, kuma yau yake da yaƙinin farfaɗowarta insha Allah...

Ƙafantane yafara motsawa, sannu a hankali idanunta suka soma ɗan buɗewa,  ƙwaƙwalwarta ne tashiga tariyo mata duk wani abu daya faru da'ita, wani irin ƙara Zahrah tasanya wanda yayi matuƙar firgita su Baffa da Inna dake zaune gefe da gadon da take kwance,, "Subahanallahi !!" Baffa ya faɗa cike da tashin hankali,,, ihu kawai Zahrah ke yi haɗe da fisge fisge, tamkar dai mahaukaciya,, Dagudu Baffa yayi waje don ƙiran likita,, duk yanda Inna taso riƙe Zahrah abun yagagara domin kuwa duk ta fusge ƙarin ruwan da akayi mata,  cikin hanzari Doctor Saddiq yaƙaraso cikin ɗakin, cak yatsaya ganin yanda Zahrah ke ihu tana ta fusge fusge,  wani irin mugun tausayinta yaji ya daki zuciyarsa,, tattaro duk wani kuzarin sa yayi yaƙarasa gareta, wani irin fusga Zahrah tayi, ai kuwa saiga Inna dake riƙe da ita, tafaɗi ƙasa warwas,, da hanzari ya kama hannayenta duka biyu, yana mai ƙoƙarin nutsar da ita, wani ihun takumayi wanda sautinsa ya zagaye kowani kusurwa na ɗakin, fuskar Zaid kawai take hangowa akan ta Dr Saddiq,

"Wayyo Allah na, Baffa kataimakeni zai kasheni, zai kasheni, wayyo !!!" abun da Zahrah take ta faɗa kenan cikin hargowa da son ƙwace kanta daga wajen Doctor Saddiq,,   duk yanda Dr Saddiq yaso tayi shiru abun yacitura, domin da alama bata cikin hayyacinta,,  wani irin cizo Zahrah ta gantsara masa ahannu, sosai yaji zafin cizon amma yasan tabbas yana saketa, guduwa  zatayi, ko kuma ma tayimawa kanta rauni,,  wani irin ƙara ta callara tana mai shirin turesa ta gudu, yayi saurin rungumeta ƙam acikin ƙirjinsa,   wasu lafiyayyun cizo Zahrah tashiga gantsara masa akan ƙirjinsa, sake rungumeta yayi ƙaƙam acikin jikinsa, haɗe da rumtse idanunsa, yakuma datse lips ɗinsa da haƙoransa,, sosai yakejin zafi har cikin ƙwaƙwalwarsa, domin kuwa da iya ƙarfinta take cizon sa,,   ganin cizo bazai wadatar ba yasanyata sanya hannayenta, duka biyu ta shiga dukansa tako ina,,   tabbas duk wanda yaga abun da Zahrah takeyi yasan cewa bata cikin hayyacinta,,  da ƙyar Dr Saddiq ya'iya danneta yayi mata wata allura wacce take kashe jiki, ta kuma gusar da ƙarfin jikin ɗan adam,,  take tayi laƙwas haɗe da sulalewa daga jikinsa tafaɗa kan gado,  kallonta yashiga yi gaba ɗaya tayi buji buji da tulin gashin kanta, gashi duk taɓalle maɓallan gaban rigarta, wanda hakan yabayyana kyakkyawar surar ƙirjinta,, saurin ɗauke idanunsa yayi daga kan ƙirjin nata, haɗe da sauƙe ajiyar zuciya, juyo da kallonsa yayi zuwaga kan su Baffa da suke tsaye cirko cirko, gaba ɗaya sunyi wani tsuru tsuru dasu, tamkar ace musu as su antaya a guje, bama kamar Inna,,

Kansa kawai ya jijjiga batare da yacemusu komai ba, yayi ficewarsa daga cikin ɗakin,, direct office ɗinsa ya nufa,   da kansa ya haɗa tea mai kauri, kaitsaye  ɗaki na musamman ɗin daya sa aka kai Zahrah yanufa, riƙe da kofin tea ɗin a hanunsa,   baitaradda su Baffa a cikin ɗakin ba, don haka kansa tsaye yanufi gaban gadon nata,, kwance take flat daganinta kasan babu wani wadataccen ƙarfi ajikinta, saidai hawayene kawai ke ambaliya yana gangarowa ta gefen idanunta,,, "Zahrah" yaƙira sunanta, duk da yasancewa bazata taɓa amsa masa ba, saboda batacikin nutsuwarta...

Aje ƙofin tea ɗin dake hanunnasa yayi, haɗe da ɗaukar pillow yasanya a bayanta, da ƙyar yasamu ya iya jinginar da ita ajikin pillow'n,  a hankali yake ɗiban tea ɗin cikin tea spoon yanakaiwa bakinta, duk yanda yaso ta buɗe baki tasha tea ɗin hakan yagagara, domin daya sanya mata ruwan tea ɗin acikin bakinta,  zaidawo waje,,   aje kofin yayi haɗe da harɗe duka hannuwansa akan ƙirjinsa, kallon fuskarta yashiga yi natsawon wasu mintuna, ajiyar zuciya ya sauƙe alokaci guda, haɗe da ɗaukar kofin tea ɗin yafice daga cikin ɗakin,,  umarni yabawa wata nurses da tayi mawa Zahrah alluran bacci, domin duk yafahimci irin situation ɗin da take ciki a yanzun...

Gaba ɗaya ihun Zahrah ya karaɗe ɗakin, hankalinsu Inna gaba ɗaya atashe yake,  kamar yanda tayi ɗazun, yanzuma haka takeyi, domin ihu da fusge fusge kawai take saidai yanzu, cewa take "Kutaimakeni, zai kasheni, wayyo Allah na, kutaimakeni !!!" abun da Zahrah take faɗa kenan cikin hargowa,  da wani irin hanzari ta diro daga kan gadon, da take kwance,    kaitsaye bakin ƙofa tanufa da gudun gaske, da sauri Baffa yasha gabanta, wani irin ƙara ta sanya, domin kuwa Zaid tagani tsaye a gabanta, amaimakon Baffa, wani irin ƙarfine yazomata aikuwa  kyakkyawan hankaɗa tayimawa Baffa, saigashi jagwaf a ƙasa, dama bawani kuzari gareshi ba,,  gaba ɗaya tayi buji buji da jikinta, ta tarwatsa gashin kanta, gudu kawai Zahrah take tsakaninta da Allah,  daga zangar ta haɗu da mutane sai tasanya ihu, domin kowaye zatayi tozali dashi to fuskar Zaid take gani, akan tasa,     hartakai bakin ƙofar fita daga cikin asibitin, cikin zafin nama ya cafko hanunta, wani irin ihu Zahrah tashiga kurmawa, tamkar wacce ake yankan naman jikinta, tun fitowarta mutane ke kallonta, atunaninsu mahaukaciya ce,, bai damu da ihun da takeyi ba, duka hannayen ta yahaɗe waje ɗaya, caɗak ya ɗagata haɗe da saɓata kan kafaɗarsa, yayi cikin asibitin da'ita,,  wani irin ƙara tayi, take kuma jikinta ya sake numfashinta gaba ɗaya ya ɗauke,
Duk inda suka wuce sai ankallesu, wasu suna matuƙar tausayinta, da ƙuruciyarta amma hauka ta risketa, anasu zaton mahaukaciya ce..

A kan gado ya shimfuɗeta, haɗe da rufamata bargo, wasu allurai yayi mata, bayan yasanya mata drip ɗin dazai taimaka wajen bawa jikinta kuzari, koda bataci abinci ba....

"Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un, ya Allah kataimaketa, haƙiƙa tanacikin mawuyacin hali, ya Allah kasa kada abun danake zargi yatabbata, Allah katsaremata ƙwaƙwalwarta, da kariyarka !!" Dr Saddiq yafaɗa cikin karyewar zuciya, haɗe da tsananin tausayin Zahrah,,  sau da dama akanyi mawa yara ƙanana fyaɗe, firgici da tsoron da  suke samun kansu ciki, yakan taɓa musu ƙwaƙwalwa, sai aga kamar sun zare,  hakan yasa basa da wowa hayyacinsu cikin sauƙi,,  a wannan rana dai Dr Saddiq da ƙyar ya iya barin asibitin, gaba ɗaya lamarin Zahrah ƴatsaya masa arai, tausayinta yakeji sosai....

Tsaf yagama shirya kansa cikin wasu mayun riga da wando, masu kyau da tsadar gaske, bakaɗan ba yayi kyau sai tashin daddaɗan ƙamshi jikinsa yake, SHU'UMIN NAMIJI kenan ganinka babu alkhari acikinsa,  ƴar ƙaramar trolly bag ɗinsa ya shiga ja, bayan yaɗauki wayoyinsa da kuma duk wani abu dayasan zai buƙata,, wannan karan ko ɓangaren mahaifiyarsa bai jeba, motarsa  ƙirar BUGATI yashige, yayin da driver yabamawa motar wuta, kaitsaye airport suka nufa, domin dai alƙawari Zaid yaɗauka yau bazai kwana acikin Nigeria ba,  yawon shaƙatawa zai tafi  New York City (America)..  Yana  shiga cikin jirgin baiwani jimaba, jirginnasu yaɗaga zuwa sararin samaniya.....

  *((kuyi haƙuri page ɗin  yau baida yawa...))*

       *12/November/2019*
      _________________________

      *MRS SARDAUNA*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
      
             *SHU'UMIN NAMIJI !!*
                
   *Written By*
phatymasardauna

*Dedicated To My Loveƙy Brother Khabier...*

*🌈Kainuwa Writers Association*

'''{United we stand and succeed our ambition is to intertain & motivate the mind of readers}'''
*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*

             *WATTPAD*
        @fatymasardauna

*Editing is not allowed📵*

*Wannan Page ɗin gabaki ɗayansa kyautane a gareku.*
    
     *UMMIEE-ZARIA.*
     *MRS MAI LAWAL.*
     *MAMAN TEEMAH.*
     *ZEE BLACK.*
     *AYSHA HUMAIRA.*
    *SA'ADAH GALADIMA.*
    *MY ADIZATOU (Ummu Adnan.)*
    *MARIYA...❤.*

*Chapter 27 to 28*

Tunda Zahrah tasume, bata sake sanin inda kanta yake ba, sai ƙarfe shida na yamma, alokacin anata ƙiraye ƙirayen sallan magriba,  wannan karon sam  batayi wannan iface ifacen  da kuma  fusge fusgen da tasaba yi ba, sai dai idanunta da ta tsayar waje ɗaya,wato kan  ceiling ɗin dake saman ɗakin, hawayene kawai kefitowa daga cikin idanun ta, yana mai sauƙa a gefen fuskarta,   "Zahrah !" Inna dake gefe taƙira sunan Zahrah.

Ko gizau Zahrah ba tayi ba, balle Inna tasaran zata amsa mata,  gyra tsayuwa Inna tayi haɗe da jinjina kanta, tabbas tasan koma meyafaru da Zahrah sune sanadi, domin kuwa basu riƙe amanar da iyayenta suka basu kafun su rasu ba.
Dr Saddiq ne yaturo ƙofar ɗakin yashigo, bakinsa ɗauke da sallama, yayinda Baffa ke biye da shi a baya,    "Yauwa likita kazo ko? ta farka amma kwata-kwata bata magana!" Inna tafaɗa cike da damuwa.
Ɗan guntun murmushi kawai Dr Saddiq yayi,haɗe da nufar inda Zahrah'n ke kwance, kallonta yayi na ɗan wasu mintuna, kana yajuyo da kallonsa wajen su Baffa...   "Inaso Za'ayi mata gwajin ƙwaƙwalwa, domin sake tabbatar da lafiyarta, saboda haka zanturo Nurses su ɗauketa "  Dr Saddiq yafaɗa.

Sosa kai Baffa yashiga yi, cike da damuwa yace "To kamar nawa ake buƙata likita?  kuma naga tunda mukazo ka ke bata kulawa, amma banji anyi min maganar nakawo ko sisi ba, fatana Allah yasa gwajin ƙwaƙwalwar bashi da tsada !" Baffa yafaɗa cikin karyewar zuciya, domin kuwa idan gwajin yana da tsada tofa sai dai ahaƙura, saboda bashi da kuɗi.

Kallonsa kawai Dr S.S yayi batare da yace dashi ƙalaba, ya sa kai yayi ficewarsa daga cikin ɗakin.

Mintuna kaɗan da fitarsa, wasu nurses su biyu suka shigo, ɗaukan Zahrah sukayi, suka ɗaurata kan wani gado mai ƙafafun taya,  suka fice da'ita,  ba don idanunta da suke buɗeba, tabbas da idan ka ganta zakayi zaton gawace, domin kuwa babu abun dake, motsi a jikinta, sai hawaye kawai dake ambaliya a cikin idanunta...

Alhmdlh anyi mawa Zahrah gwadin ƙwaƙwalwa lafiya,  saura kawai  ajira fitowar result.
Babu abun dayake ɗaga mawa Dr S.S hankali a yanzu, kamar yanda take yawan firgita, gashi hawaye sun kasa daina zubowa daga cikin idanunta, babban abun damuwar kuma shine bata um balle um um, ko motsawa bakinta bayayi, sannan kuma waje ɗaya idanunta suke kallo, wato sama.

Result ɗin gwadin da'akayi mata yafito, kuma masha Allah, ƙwaƙwalwarta tana nan lafiya, babu abun daya sameta, kawai dai tashiga halin firgici ne, kuma dama ana yawan samun irin haka...

"Likita ya sakamakon, Allah yasa bata samu wani matsala a ƙwaƙwalwarta ta ba ? " Baffa dake zaune cikin office ɗin Dr S.S ya tambaya.

"ku kwantar da hankalinku, sakamako yayi kyau, domin kuwa brain ɗinta nanan lafiya"

"Alhamdulillah, Allah mungodema !" Baffa yafaɗa cike da jin daɗi,

"Kaine Babanta mahaifi ?" Dr S.S yatambaya sanda yake ƙoƙarin cike wani file dake gabansa.

"A'a bani na haifeta ba, ƴar ɗan uwana ne da ya rasu, amanarta yabarmin, gashi yanzu bansan wani tsinannen bane ya aikata ma ta wannan abun ba !" Baffa yaƙare maganar yana matsan ƙwalla.

Kallon sa Dr S.S yayi na tsawon wasu mintuna, kafun ya kau da kansa gefe,  "Dawa take mu'amala, saurayi ko aboki ?"  Dr S.S ya kuma tambaya.

"Bata mu'amala da kowa sai wani yaron arziki, shine ma yace yana sonta, kuma hargida yataɓa zuwa ya gaisheni, a zahirin

Please Login or Register in order to submit comment