Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

domin kuwa kurzanta Zaid keyi tamkar anbasa brush ya wanke tayan machine,, ganin ihunta zai damesa yasanya hanunsa ya toshe mata baki,, saida Zaid yasamu gamsuwa kusan na uku kafun ya tashi daga kan Ramla, wanda a yanzu numfashin azaba kawai take fitarwa,, shikansa yasan cewa baiyi mata da wasa ba, domin dama da gayya yayi mata, haka al'adarsa take, idan har ransa ya ɓaci to fa baya samun relief harsai yasamu mace yayi ma ta cin kaca, sannan zaiji nutsuwa a zuciyarsa,, ko ajikinsa haka yashiga bathroom yayi wanka,, ko da yafito yashirya kansa, ɗan makullin motarsa yaɗauka, yafice daga cikin ɗakin ba tare da yace da Ramla ƙala ba..

Da ƙyar Ramla ta'iya yin wanka, harkukan azaba saida takumayi, tabbas yau Zaid yayimata cin da bai taɓa yi mata irin shiba, harwani zut zut wajen nata keyi, amma to yazatayi son kuɗinta ya ja wo mata, kwanciya tayi shame shame, akan gado, haɗe da ɗage ƙafafu sama, acewarta yau dolene HQ yasha iska saboda zafi yake tamkar anbaɗa masa barkono....🤣🤣


Zaid kuwa yanabarin Maitama kai tsaye *TRANSCOP HILTON* yanufa, domin yana da appointment da wani abokin business ɗinsa......


Kuka sosai Zahrah tayi a wannan daren harsai da ciwon kai ya sauƙa mata, wata irin zazzafar soyayyar Zaid ne ke huda jini da jijiyarta, batasan tana mawa Zaid tsananin so ba sai a yau ɗin, haka nan taji wani irin tsanan Jabeer ya ɗarsu acikin zuciyarta, a cewarta duk shine silan faruwar hakan,, haka tayi ta kuka babu mai rarrashinta........


Zaid kuwa bashine yadawo Maitama ba sai wajen ɗaya da rabi na dare (1:30 αм) koda ya dawo ya iske Ramla tana ta sheƙa baccinta tayi ɗaɗɗaya akan gado,, murmushinsa na mugunta yayi,haɗi da shigewa cikin bathroom yayi wanka... Babu tausayi ko lallama acikin sha'anin Zaid, haka yatashi Ramla daga baccin da takeyi, batare kuma da ya tsaya wani romance ɗinta ba, ya sake afka ma ta,, wannan karon kam Ramla hadda cizo ta haɗa masa amma kamar wacce ta ciji ƙarfe, ko gizau baiyi ba,,, iya wahaltuwa Ramla tayi a wajen Zaid, yanzu kam ko ɗaga kanta batayi, saboda tsabar wahala,, haka yaƙaraci sukuwarsa ya sauƙa akanta,, bayan yayi wanka, ya bata wasu ƙwayoyi na kashe zogi tasha, mintuna ƙalilan bacci yayi gaba da'ita,, shikuwa saida yakuma shan wata giyar kafun bacci yaɗaukesa.......


Washe gari....Haka Zahrah tatashi gaba ɗaya jikinta ba ƙarfi, domin jiya kwana tayi da zazzaɓi a jikinta,, a daddafe tayi shirin makaranta ta tafi.....
Haka ta wuni cikin makarantar sukuku batajin daɗin komai, Husnah ce ma mai ƙoƙarin kwantar ma ta da hankali.....

Abu kamar wasa yau Kwana huɗu kenan Zahrah bata sanya Zaid a'idanunta ba,, gaba ɗaya tashiga cikin damuwa bata wani walwalan kirki, ta kunna wayar daya bata ma wai ko ƙiransa zai shigo amma shiru ko saƙo babu balle ƙira,, takan kulle kanta a ɗaki tayi kuka sosai, domin gani take shikenan itakam ta rasa Zaid......

Zaid kuwa fushi yake da'ita amma bawai hakan nanufin yasauya ƙudirinsa akan taba ne,, yana nan akan bakansa kuma alƙawari ya ɗauka sai ya cika sa insha Allahu,, yau kwanansa biyar rabonsa daya sanyata acikin idanunsa, haka nan yaji yauɗin yanason ganinta.....tsab yashirya kansa cikin wani haɗaɗɗan milk colour yard mai kyau da tsadar gaske, sosai kayan ya amshi jikinsa, domin Zaid ba baya bane wajen iya gaye,, daddaɗan ƙamshi ne kawai ke tashi ajikinsa,, motarsa ƙiran Range Rover brown colour yashiga,, kaitsaye Unguwar su Zahrah yanufa, bayan yabiya ta *JABI LAKE* yayi mata siyayya.....

"Ke Zahrah wai mekikeyi ne da haryanzu bazaki tashi kije aikan da nayi miki ba ?" Inna dake tsaye abakin ƙofar ɗakin Zahrah ta tambaya... Cikin sanyin muryarta tace "Gani nan zuwa Inna yanzun zanje"
Hijab ɗinta ta sanya haɗe da zura flat shue ɗinta mai sauƙin kuɗi,,, kuɗi takarɓa a wajen Inna tayi ficewarta... tafe take akan layinnasu amma kanta duƙe yake a ƙasa kamar koda yaushe, kallo ɗaya zakai mata kafuskanci cewa tanacikin damuwa,, tazo shiga kwana kenan shikuma ya danno hancin motarsa,, sam bata lura da shiba kasancewar kanta duƙe yake a ƙasa,, cak ya tsaida motar tashi, yana mai kafeta da mayun idanunsa,, ci gaba da tafiya Zahrah tayi domin bata lura da shiba,, a hankali yabuɗe murfin motar haɗe da fitowa, cikin takunsa na ƙasaita yasoma bin bayanta,, kasancewar a hankali take tafiya yasanyashi saurin cimma ta,, "Ina zakije ?" muryarsa ta doki dodon kunnenta,, da sauri tajuyo gareshi, aikuwa tabbas shiɗinne, take taji wani irin shouck a jikinta, sakamakon karabkiya da idanunsu sukayi da juna, idanunta ne sukayi rau rau dasu, yayinda ƙwalla tacikasu tab,, kallon juna suka shiga yi har na tsawon wasu mintuna, batare da kowannensu ya ɗauke idonsa daga kan na ɗan uwansa ba,, "Ina zakije ?" yasake mai maita tambayar tasa gareta...Ƙasa tayi da kanta yayinda ƙwallan dake cikin idanunta suka gangaro,, cikin murya mai sanyi tace "Aika" kansa ya gyaɗa haɗe da miƙo mata hanunsa yace "Zo mu koma gida" ba musu ta miƙa masa hanunta yakama, wani irin abune yaratsa jiki da zuciyarsu, su duka biyun,, hanunta dake cikin nasa yashiga murzawa duk da cewa tafiya suke,,, ƙofar gefen mai zaman banza ya buɗe mata ta zauna, shikuma ya koma gefen driver yayi mawa motar key,, mintu 2 yakawosu ƙofar gidansu Zahrah'n.... kafeta yayi da idanunsa masu riki tata, yayinda yake sauƙe numfashi a hankali.......


*Happy New Month 🍝🥂*

*1/November/2019*


*MRS SARDAUNA*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*SHU'UMIN NAMIJI !!*



*WRITTEN by*
phatymasardauna
*🎈Mrs Sardauna🎈*


*Dedicated to my lovely brother Khabier*


*🌈Kainuwa Writers Association*


*WATTPAD*
@fatymasardauna

*Editing is not allowed 📵*

```{{In ƙaramuku yawan typing, kullum batun kenan🤦🏼‍♀waiku don Allah bakwa tunanin nima ina da abubuwanyi da yawa ne ?, bafa typing bane kaɗai aikina, ina da miji, ina zuwa school, kuma komai yana buƙatar lokaci, saboda haka kuyi haƙuri, hakan ma ina ƙoƙari ni aganina...}}```


*Chapter 17 to18*


Tsawon lokaci Zaid yaɗauka yana kallon Zahrah batare da yace da'ita ƙalaba, ɗan nisawa yayi haɗe da sauƙe ajiyar zuciya, "maiya sameki kike kuka ?" yayi mata tambayar cikin taushin murya,, ɗan ƙaramin bakinta taturo gaba haɗe da cewa "to bakai bane katafi kabar..... !" saurin toshe bakinta tayi jin ɓarakar da take shirin yi,,, murmushin gefen baki Zaid yayi, haɗe da yi mata wani irin kallo, "umm ƙarisa mana inajinki" yafaɗa da sassanyar murya...Sunne kanta ƙasa tayi domin kuwa ba shakka suɓutar baki na nema yakaita gajin kunya,, gyara
zamansa yayi haɗe da cewa "Waye shi ?"...ɗan satar kallonsa tayi cikin siririyar muryarta tace " Shi wa ?"... "ba'a dawomin da tambaya, amsa kawai nake nema, don haka faɗamin wanene shi...?" sai yanzu tagano abun dayake nufi,, jitayi gaba ɗaya jikinta yayi sanyi.. "Wanine !!" tabasa amsa cikin ɗarɗar... Kansa kawai ya kaɗa haɗe da taɓe baki, satan kallonta yayi ta gefen ido " kinasonsa kenan ?" ya jefo mata tambayar da ba ta shirya amsar sa ba... Satan kallonsa takumayi akaro na biyu, haɗe da girgiza kanta alamar a'a,, yaga abun datayi amma saiya share yayi kamar baigani ba, domin so yake tabuɗi baki tayi magana.... Tambayar yakuma maimaita mata,, cikin sanyi tace "A'a" numfasawa yayi haɗe da cewa " to wakike so ?"... Dum haka ƙirjinta ya buga, domin bata da iko ko zarran da zata fuskancesa gaba da gaba tace shi takeso, ko ma ba haka ba ita macece mai alkunya da kuma ƙima, furtawa namiji kalmar so, awajenta ba dai dai bane,, bata taɓayi ba bakuma zatayi azarɓaɓi ba.... "kinyi shiru" yafaɗa dai dai sanda ya ɗau gorar ruwan swan yakai bakinsa, idan tace dashi babu ƙwarai ta cuci kanta da zuciyarta ne, idan kuma tace dashi akwai to hakan nanufin yankewar alaƙarta dashine, saboda zaiga kamar bashi ta ke so ba....

Murmushi yayi haɗe da aje goran ruwan dake hanunsa, "MY ZAHRAH !!" yaƙira sunanta da muryarsa mai kashe mata jiki,, "Na'am !" ta amsa masa itama cikin sassanyar murya.... Ahankali ya lumshe kyawawan idanunsa haɗe da jingina bayansa ajikin kujeran motar,, kallonta ta maida kansa, tunda idanunsa a rufe suke yanzu zata samu chance ɗin kallonsa da kyau,, tabbas Zaid kyakkyawane na gani a nuna, yana da abubuwan ɗaukar hankali a tattare dashi, tanason Zaid sosai, ko don kyawunsa ma ya cancanta aso shi,... A hankali ya buɗe idanunsa da suka soma sauya launi daga farare zuwa ja, wani irin zubawa tsikar jikinta sukayi, sakamakon haɗuwar idanunsu waje ɗaya, wayyo Allah Zaid yana da mayun idanu masu matuƙar kyau da ɗaukar hankali, haƙiƙa kallon idanun Zaid sai wanda ya daure, domin suna da saurin kashe jiki da sauƙar da kasala... " Banagajiya da kallonki, amma ke kina gajiya da kallona bakima so ki kalleni, maiyasa ?" ya tambayeta dai dai lokacin daya ware idanunsa akan cikakkun breast, ɗin ta, da tudunsu suka bayyano ta wajen hijabin dake jikinta, sunkuyar da kanta ƙasa tayi tana mai wasa da yatsun hanunta, batare da tabashi amsaba...

"Oh Allah wannan yarinyar zata kasheni, lallai randa na kamaki bazan miki da sauƙi ba !!" Zaid yafaɗa a cikin zuciyarsa, shi bakomaine ma yake basa takaici da'ita ba kamar rashin magana da batayi, daga eh sai a'a kawai take cewa shi wallahi haushima take basa...

Ita kuwa Zahrah batasan wainar da Zaid ke toyawa ba, saboda kanta na ƙasa, shikuwa gogan tudun breast ɗin ta kawai yakafe da ido, harwani haɗiye yawu yake, tamkar (bestyna Jikar Hajiya tasamu zazzafan balangu,lol)... Daddaɗan sauti ne yasamo tashi daga cikin wayarsa, da alama ƙira ne yashigo wayar tasa "Baby" shine sunan dake yawo akan screen ɗin wayar ɓaro ɓaro, wani irin dokawa zuciyar Zahrah tayi, domin kuwa taga sunan dake yawo akan screen ɗin wayar tasa... A hankali yaɗauki wayar haɗe da karawa akan kunnensa, tunda ya ɗauki wayar baice ƙalaba saidai murmushi kawai da ya yawaita akan fuskarsa, hakan kuwa ba ƙaramin ƙona zuciyar Zahrah yayi ba, wato dai dama yana da budurwa,, har ya cire wayar akan kunnensa banji yace ƙala ba, "Ina wayar dana baki ?" yayi maganar cikin halin ko inkula, "Tana nan" tabasa amsa a taƙaice domin wani haushi ne ya tokare ma ta maƙoshi,, "Maiyasa bakya amafani da'ita ?" "Babu amfanin hakan " takuma basa amsa ataƙaice, kallonta yayi haɗe da fashewa da dariya harsai da fararen haƙoransa suka bayyana,, tamkar wani tv haka Zahrah tayi ƙasaƙe tana kallonsa bakaɗan ba yayi kyau da yana dariyan, lalle Zaid ƙarshene wajen kyau,, saida yayi dariya sosai kafun ya tsagaita haɗe da kallonta "Kishi ko Ƴan mata ?" turo ɗan ƙaramin bakinta gaba tayi haɗe da yi masa hararan wasa, lumshe idanunsa yayi gami da buɗewa alokaci guda, "Soyayyata tayi miki mummunan kamu amma zurfin ciki ya hanaki faɗa, shikenan to ni zantafi sai kificemin a mota ko" yaƙarasa maganar yana mai tamke fuska tamkar bashine ya gama dariya yanzu ba....Hmm Zahrah uwar kuka, take idanunta sukayi rau rau dasu, cikin muryar ta mai sanyin amo tace "Kayi haƙuri !!" kallonta ya kuma yi alokaci na barkatai "Hakan nanufin kin amince kina so na kenan??" A hankali tashiga kaɗa kanta alamar "eh" Kyakkyawan murmushinsa mai sauti yayi haɗe da kashe mata idonsa ɗaya, da sauri tayi ƙasa da kanta, tana ɗan murmushi, tana mai kuma jin wani irin farinciki na ratsa zuciyarta, ko ba komai yanzu ya fahimci cewa akwai soyayyarsa acikin zuciyarta.... Ledan dake bag sit ɗin motar ya ɗauko haɗe da miƙo mata cikin murya mai sanya nutsuwa dakuma nuna tsantsar soyayya yace "wannan kyautane a gareni, sauran kuma special gift na amsar soyayyata da kikayi very soon yana nan zuwa, amma bana fara baki wata kyauta..." ya ƙare maganar yana murmushi. Wani ɗan ƙaramin box ya ɗauko daga cikin wani keɓaɓɓen waje dake cikin motar, box ne mai kyaun gaske wanda aka ƙawata jikinsa da wasu irin furanni masu kyawu da ɗaukar hankali, koda ya buɗe box ɗin wani kyakkyawan zube ne ya bayyana, wanda akayisa da zallan gold, murmushi Zahrah tayi domin kuwa sosai zoben yayi mata kyau, hanunsa yamiƙa mata, alamar ta bashi nata hanun, cike da kunya tamiƙa masa lallausan hanunta, saida Zaid ya sauƙe ajiyar zuciya, lokacin da taushin fatar Zahrah da tasa suka haɗe waje guda,, kama hanunnata yayi da kyau haɗi da ciro zoben yasanya mata cikin yatsarta ta uku, ɗas zobennan yazauna acikin yatsar Zahrah, tamkar angwada hanunnata kafun ayishi, batasan sanda tayi murmushi ba harsaida haƙwaranta suka bayyana, bakomai yasa hakanba, face kyaun da taga zoben yayi mata a hanunta, dama ita mutumce mai tsananin son kayan ado, rashi ne yasanya ta dangana komai nata ga Allah.... "Cire zobennan daga yatsarki dai dai yake da cire sona azuciyarki, please ki tausayamin kada kicire domin ina tsananin sonki My Zahrah ta, ke ɗin ta dabance a wajena, kimin alƙawari bazaki taɓa cire zobennan ahanunki ba, har abada !!" Yanda yayi maganar idan ka kallesa zaka rantse da Allah cewa bashi bane, domin kuwa sam baiyi kama da irin mutanennan da zasuna baran soyayya ba, Wani irin farinciki haɗe da tsananin daɗi, su suka shiga huda zuciyar Zahrah, "Haƙiƙa Allah yayi mata babban zaɓi, har abada bazata taɓa daina mamakin soyayyarsu da Zaid ba, domin kuwa duk da kyawunta wallahi Zaid yakerewa ajinta, tayi imani da cewa Zaid ba'irin mazajennan bane, da ake samunsu saka ka acikin gari, irinsu Zaid sai wacce take da rabo da kuma tsananin sa'a ke samunsu, tabbas itakam tana da sa'a, tana kuma daɗa godemawa Allah ako dayaushe.." "My Zahrah !!" yakatsemata tunaninta tahanyar ƙiran sunanta,, "Nayi maka alƙawari bazan taɓa cire zobennan ahanuna ba, har gaban abada,harsai munhaifi ƴaƴa da jikoki, da shima zan mutu" Zahrah tafaɗa cike da kunya. .. Baki kawai Zaid ya hangame yana kallon Zahrah, bakaɗan ba kyawunta yaƙaru da ta ke magana, ashe haka shugar baby'ntasa take kyau intana magana baisani ba?.. Ɗan numfasawa yayi haɗe da gyara zamansa cike da salon yaudara, yace "Zantafi Dad ɗina yana ƙirana, amma gobe zandawo saboda nasake ganin wannan kyakkyawar Baby'n tawa !!".... Saurin cusa kanta cikin cinyoyinta tayi tana murmushi, (Allah sarki basaban ba su Zahrah anji kalaman love,lol)... "Inasonki My Zahrah !!" yafaɗa cikin shauƙin ƙauna,, yanzu kam ɗago da kanta tayi haɗe da watsa masa kyawawan idanunta, wani irin zubawa tsikar jikin Zaid yayi domin kuwa wani irin kallo Zahrah keyi masa "Nima Inasonka !!" Zahrah tafaɗa tana mai shagwaɓe fuska, haɗe da karya wuyanta gefe,, har abada bazai taɓa gajiyawa da murmushi ba, domin yanzuma murmushin kawai yayi mata,, cike da nutsuwa ta buɗe murfin motar, bayan ta ɗauki ledan daya tursa sa ta kan saita ɗauka,, wani irin kallo sukamawa junansu, kafun tashige cikin gida,, Zaid yana ganin shigewarta ya saki wata irin mahaukaciyar dariya, hadda riƙe ciki, dariya sosai Zaid yakeyi tamkar wani mahaukaci, bakomai yasa hakanba, face tunowa da kalaman Zahrah dayayi, "Wai ita da shi zasu haifi ƴaƴa hadda jikoki " Lallai yariyarnan ta haukace... Yakuma fashewa da dariya, saida yayi dariya sosai, kafun ya tsagaita hanunsa yasanya yasoma shafa, kwantaccen sajen dake kan fuskarsa,, " Very soon zakiga Special gift ɗinki !!" yafaɗa ahankali, kansa yajinjina haɗe da fidda iska tacikin bakinsa, key yayi wa motarsa, haɗi da harbata kan titi, yau ƙal yakejin zuciyarsa domin kuwa yanzu yafara buga game ɗin yana da tabbacin cewa kuma bazaiyi game over ba.....


Zahrah kuwa tanashiga cikin gida da lale marhaban, Inna ta tarbeta, domin tuni a leƙe leƙenta da ta sabayi waje, ta leƙosu cikin mota,, amsar ledan Inna tayi, haɗe da bajewa kan taburma tashiga ciro abubuwan dake cikin ledan, still kayayyakine na kanti masu kyau da tsadar gaske, sai kuma mayukan shafa, dasu powder, hadda su tsadaddun turaruka, gefe kuwa ɗaurin kuɗine ƴan dubu dubu masu yawan gaske,, jiki na rawa Inna ta ɗauka haɗi da kaiwa kan hancinta tashiga shinshinasu, "Um kuɗi masu gidan rana, kuɗi maganin damuwar babba da yaro, kuɗi masu saiwa mutum ƴanci, kuɗi basu zuwa gareka saikana da rabo, ni dai Allah yakashe ya bani !" Inna tafaɗa cike da jindaɗi,, kai kawai Zahrah ta girgiza, har cikin zuciyarta batajin daɗin abun da Inna da Baffa keyi, domin hakan kamar zubar mata da mutumci ne, saboda iyayen ƙwarai basa haka,,, wasu ƴan tsiraru daga cikin kuɗin Inna ta kama hanun Zahrah ta damƙa mata, haɗe da cewa "Saura kifaɗamawa wancan ƙwarnafaffen Baffan naki cewa Zaidu yaron arziki yazo, ni dake ne, tattare kayayyakinnan maza kisasu a ɗakinki, domin ban buƙatarsu, kuɗi ne nawa kuma na samu, saura kwana kaɗan nima nafara sanya lasa lasai, hmmm nimafa saina zama wata babbar ƙwaruwa acikin garin Abuja'nnan, domin kuwa Allah yabani bazan tauyewa kaina haƙƙi ba ehe !!" Inna taƙare maganar tana mai turo ɗaurin ɗankwalin ta gaban goshi,, ita dai Zahrah batace da'ita ƙalaba, saima tattare kayan tayi tanufi ɗakinta...

Dariya sosai Abid keyi hadda tsugunnawa ƙasa, sosai labarin da abokinnasa yabasa yasanyashi nishaɗi... Ɗan tsagaitawa da dariyan yayi haɗe da maida kallonsa ga Zaid wanda hanunsa ke ɗauke da glass cup yana sipping alcohol, "Gaskia kai ɗin Shu'umi ne, amma miye next target ɗinka ??" Wani irin murmushi Zaid yayi wanda yafiyinta idan zai gudanar da mugunta, *"RAPING ɗinta zanyi (Fyaɗe)"* Zaid yafaɗa a taƙaice.....


((😳😳😳 Readers...... 🙆🏻🙆🏻))



*3/November/2019*


*MRS SARDAUNA......*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

        *SHU'UMIN NAMIJI !!*

      *Written by*
Phatymasardauna
     *🎈Mrs Sardauna🎈*

*Dedicated to My Brother Khabier*

*🌈Kainuwa Writers Association*

      *WATTPAD* *@fatymasardauna*

*Editing is not allowed📵*

   
*Chapter 19 to 20*

Jinjina kai Abid yayi haɗe da kallon Zaid, "maiyasa bazakayi amfani da soyayyar da take yi maka ba wajen biyan buƙatan ka, dole sai kayi raping ɗinta??" Abid ya tambaya, Murmushi Zaid yayi haɗe da sanya haƙoransa ya cije kyawawan lips ɗinsa, batare dayace da Abid ƙalaba, yaci gaba da shan wine ɗinsa,, sarai Abid yafahimci abunda Zaid ɗin ke nufi don haka shima baisake ɗago zancen ba, saima ɗaukar wayarsa da yayi yasoma latsa ta....
Kwance take akan ƴar yaloluwar katifarta, gaba ɗaya hankalinta da tunaninta sunaga tunanin masoyinta Zaid, wayar da Zaid yabata ne tasoma kara alamar shigowar ƙira, hanunta har rawa yake wajen son ɗaukar ƙiran, domin tana da yaƙinin cewa Zaid ɗin tane... "My Zahrah na !!" Muryar Zaid yadoki cikin dodon kunnenta, lumshe idanunta tayi alokaci guda haɗe da buɗesu, sosai taji nishaɗi na ratsa zuciyarta,, "Na'am !!" ta amsa masa in a low voice ɗinta, Zaid dake kwance kan makeken gadon sa,gyara kwanciya yayi haɗe da ɗaura hanunsa kan joy stick ɗinsa, haƙiƙanin gaskia ko muryan Zahrah yaji to fa sai sandar girmansa ta motsa, wani irin muguwar sha'awar Zahrah yakeji, ba dare ba rana, "Bakiyi bacci ba ??" yayi mata tambayar yana mai ƙasa da muryarsa,, saida ta ɗan ja numfashi kafun tace dashi " Eh" kansa ya jinjina kamar dai tana ganinsa, sake lafewa akan gadon yayi, haɗe da ƙasa da muryarsa sosai yanda yatabbatar da cewa zataji a jikinta, " Soyayyata ce tahanaki bacci ko !! ?" ya ƙare maganar yana mai rumtse idanunsa,, gaba ɗaya ji tayi tsikar jikinta ya shiga zubawa, take kuma kasala ta lulluɓe mata jiki, shiru tay na ɗan wani lokaci, domin takasa amsa masa tambayarsa, a zuciyarta kuwa mamaki take ga me da yanda Zaid ke sanin duk irin halin da take ciki,,...."My Zahrah !!" yasake ƙiran sunanta,, yanzu kam gaba ɗaya rasa control ɗinta tayi, domin yanda yake ƙiran sunan nata da salo acikinsa,, "Umm" tafaɗa cikin muryar shagwaɓa wacce batasan ma tayi taba,, "Ya Allah !!" Zaid yafaɗa acikin zuciyarsa, domin bakaɗan ba salon shagawaɓan nata yatafi dashi, yana matuƙar son mace shagwaɓaɓɓiya, lallai Zahrah tacika mace hundred percent,, "Naga kamar kinajin bacci, zan barki sai da safe ko Dear ?" yayi hakanne don gano wani irin yanayi take ciki,, " Ni banjin bacci fa !!" Zahrah tafaɗa still a shagwaɓe, (Like Jikar Hajiya, da Sugar dady'nta,lol 🙈)

Wani irin munafukin murmushi Zaid yayi domin kuwa yasamu abun da yakeso,, Zahrah kuwa takurewa tayi kan lasheshshiyar katifarta, babu abun da take fitarwa sai numfashi a hankali hankali, hakanan ta tsinci kanta cikin wani irin yanayi, mai wuyar fassaruwa,, lumshe idanunsa Yayi yana mai sauraran sauƙar numfashinta acikin kunnensa, sosai hakan ke yimasa daɗi, sai da suka kwashe kusan mintuna takwas, a haka kafun Zaid ya sauƙe ajiyar zuciya haɗe da da cewa "Tunanin mekikeyi ?" murmushi mai sauti Zahrah tayi, haɗe da cewa " nima bansani ba amma dai haddakai a cikin tunanin" ƙasa ƙasa Zaid yayi dariya, batare da taji saba....Sosai ya daure zuciyarsa sukayi hira, kalaman soyayya kawai yayita zuba mata, tun Zahrah na noƙewa har tasaki jiki, saida dare yayi sosai kafun sukayi sallama da juna, bayan ya tursasa ta faɗamasa cewa tana sonsa... Zaid yana aje wayar yasanya hannayensa duka biyu yakama kansa, wani irin baƙon al'amari yakeji a tattare dashi, haushin kansa ma yakeji, ba ɗabi'arsa bane yawan magana, amma sai gashi dolensa ya koya saboda Zahrah,, ƙwayoyin paracetamol ya haɗiya haɗe da ƙorawa da ruwa, domin ɗan maganan dayayi harkansa yafara ciwo.... Zahrah ma dai haka aka kwana a najin feelings, ƴan mata anshiga baƙon yanayi........


Bayan Sati Biyu....

Wata irin gagarumar shaƙuwa haɗi da soyayya ne, suka shiga tsakanin Zaid da Zahrah, wani irin sabo sukayi naban mamaki, sosai soyayyar Zaid ta faɗa ɗa a cikin zuciyar Zahrah, Zaid yayi matuƙar jajircewa wajen inganta soyayyarsa ga Zahrah, yayi mata babban ɗauri da soyayyarsa, kulawa sosai yake bata, koda yaushe suna cikin waya ba dare ba rana,, kuɗi kuwa sosai yasake mawa su Baffa da Inna, domin shi kuɗi ba matsalar sa bane,, Zahrah kuwa harta gaji da amsar kyaututtukansa, gaba ɗaya yanzu kayan da take sanyawa masu tsadar gaske ne, duk kuma aikin Zaid ne, lokaci ɗaya Zahrah ta sanja, mayuka masu tsada take amfani dasu, jikinta yayi fresh, yayinda a kullum surarta ke ƙara haukatar da Zaid cikin kogin sha'awarta,, zuwa yanzu Zahrah tayi sabon da taɗauki duk wani yarda da amincewarta tabaiwa Zaid, yanzu Zaid shine komai nata, son da take masa na da banne,,

Ƙarfe tara na daren yau, Zaid yaƙira ta a waya,, cike da shagwaɓa kamar yadda tasabar masa taɗauki wayar, "Baby nayi fushi, wanin yau duk baka ƙira ni ba sai yanzu !!" Zahrah tafaɗa tunkan Zaid yayi magana, tana mai tura ɗan ƙaramin bakinta gaba, murmushi Zaid yayi haɗi da sauƙe ajiyar zuciya, cikin muryan kasala, yace "My Zahrah, yau nagaji da yawa, saboda wuni nayi a office, amma kinsan ako da yaushe kini raina, domin bayanda za'ayi mutum yamanta da rayuwarsa !!" murmushin jin daɗi Zahrah tayi haɗe dayin fari da idanunta, tamkar yana ganinta, "naji daɗi dana zama rayuwarka, amma kasan nafi sonka ko ?" murmushin gefen baki Zaid yayi haɗe da cewa "Gobe dukanmu zamu tabbatar da wa yafi son wani tsakaninmu, domin kuwa gobe zanbaki special gift ɗinki, na tabbatar bazaki manta da wannan ranan ba, har gaban abada !!" murmushi Zahrah tayi haɗe da cewa

Please Login or Register in order to submit comment