Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wani abun dayayi saura aciki banda tsananin soyayyar Zahrah.....

Da wani irin mahaukacin gudu Zaid yafigi motarsa yafice daga cikin gidan saura kaɗan yabitakan me gadi daya wangale masa gate, Allah ne ya ta ƙaita Me gadin yayi saurin matsawa gefe, domin kuwa ko gama buɗe gate ɗin baiyi ba Zaid yayi yo kansa....

Tuƙi yakeyi amma kuma kwalbar giya ne riƙe a ɗayan hanunsa yana sha,  jinkansa yake gaba ɗaya yana juyawa, yayinda zuciyarsa keyi masa zafi,   idanuwansa Zahrah kawai suke  hango masa,   batare da Zaid yakulaba motarsa tayi karo da wata babbar mota, take motar tasa ta ɗagu sama haɗe da faɗowa ƙasa  sannan kuma tashiga gungurawa kan titi, batare da Zaid dake cikin motar ya tsira ba.....

*(Dan Allah ku daina min kutse acikin labarin nan, kudaina saurin yanke hukunci, haryau ban ce ga wanda zai auri Zahrah a tsakanin Zaid ko Dr.Sadeeq ba,  kubarni ni kaina nasan abunda ya dace, zaifi kyau ku sanyamin idanu kukuma ci gaba da bina harzuwa ƙarshen labarin nan, amma abun da wasunku sukemin banajin daɗinsa,  suna nunawa kamar ina shirin yin abun da bai dace ba, suna nunawa kamar bansan me nakeyiba,  dan Allah kuyi haƙuri zancigaba da rubuta labarin nanne kamar yanda yazomin acikin kai dakuma zuciyata, idan kukayi haƙuri komai zaizo cikin sauƙi kuma ina da tabbacin  cewa ƙarshen labarin zai muku daɗi, nasan dama dole zan fuskanci ƙalubale a wajen wasunku, amma banyi tunanin abun zaiyi tsanani har haka ba,, amma bakomai namuku uzuri my lovely fans nasan ƙaunace tajawo hakan😅... kuyi haƙuri nayau baida yawa wlhy gaba ɗaya banganewa kaina bane shiasa inafatan zakumin uzuri)*

       

            *Fatymasardauna*

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

          *SHU'UMIN NAMIJI !!*

     *Written By*
Phatymasardauna

*Dedicated To My Brother KHABIER*

*🌈Kainuwa Writers Association*

_{United we stand and succeed; our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}_

*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*

            *WATTPAD*
        fatymasardauna

*Editing is not allowed📵*


*(Wannan page ɗin baki ɗayansa kyautane agareki Masoyiyar asali MY SHALELE (marubuciyar RAGGON MIJI) kiji daɗinki Shalelena iya wuya munatare inakuma yi miki son so)*


        *CHAPTER 84 to 85*

Kyakkyawan murmushinsa ne ɗauke akan fuskarsa still hannayensa a ware suke, alamar ta taho zuwa garesa.

Ahankali tashiga takawa tana nufar inda yake, ganin haka yasanya Zaid sakin ajiyar zuciya me ƙarfi, haɗe da sake sakin murmushi alokaci na ba adadi,, koda tazo gareshi yana shirin yaji ta rungumesa amma kuma  sai yaji saɓanin haka, domin kuwa tana zuwa kusa dashi,  sai gani yayi ta raɓa ta gefensa ta wuce batare dako kallonsa tayi ba.      Cikin hanzari yasha gabanta haɗe da kamo hanunta. Cak ta tsaya daga tafiyan da takeyi haɗi da rumtse idanunta,,  a hankali ya zame guiwowinsa ƙasa, ya durƙusa mata,  duka hannayenta ya kama ya riƙe acikin nasa hanun....

Cikin murya me ɗauke da matuƙar rauni yace da'ita...... "Koda kalamaina baza suyi tasiri acikin zuciyarki  ba, dan Allah  inaso ki tsaya ki saurareni, ki dubi halin danake ciki Zahrah, banda wani sauran farinciki a duniyar nan idan har babuke a tare dani,  haƙiƙa nayi nadama nakumayi dana sanin abun dana aikata a gareki, amma dan Allah Zahrah kiyi haƙuri kiji tausayina ki yarda muyi aure, wallahi namiki alƙawari zandaina duk wani abu danakeyi, zan baki farinciki me ɗorewa, zan mantar dake duk wani damuwa, me yasa bazaki cigaba da sona ba Zahrah? meyasa bazakiji tausayina ki yarda da tuban danayi ba,  inasonki Zahrah so irin wanda bantaɓa yiwa kowa irinsa ba acikin wannan duniyar, zan iya fansar da komai nawa idan har zaki amince ki aureni, zan iya rayuwa babu komai babu kuma kowa, amma bazan iya rayuwa babu keba, zan iya sadaukar da duka dukiyata, dakuma duk wani abu nawa dana mallaka, matuƙar zansameki amatsayin matata, dan Allah Zahrah ki yarda dani mana, ninefa Zaid, nine mutumin da kika fara so acikin rayuwarki, shin mai yasa bazaki tausayamin ba, kikalli cikin idanuwa na Zahrah  hakan kaɗai ya'isa bayyana miki irin tsananin ƙaunar danakeyi miki, inasonki, wallahi inasonki Zahrah!!.." gaba ɗaya zuciyarsa ta karye, sosai rauninsa ya bayyana...  A kan fuskar Zahrah kuwa hawayene ke zuba tamkar anbuɗe famfo sannan  kuma haryanzu idanunta akulle suke, yayinda  harkawo yanzu hannayenta ke cikin nasa hanun.   Bazatace yaushene ko kuma tayayane  itama ta tsinci kanta  da zamewa ƙasa ba, ta dai tsinci kanta  da kafa guiwowinta a ƙasa.  kukane  yaci ƙarfinta  bazata kuma iya cewa ga abu ɗaya dake damunta ba...    Hanunta tashiga ƙoƙarin cirewa daga cikin nasa hanun, amma kwata kwata Zaid yaƙi bata daman hakan saima ƙara matsowa kusa da'ita da yakeyi... 

"Zahrah!"  yaƙira sunanta cikin wata irin murya da bata fita sosai...

Manyan manyan idanunta da suka cika da ruwan hawaye ta ɗago haɗe da  waresu akansa,  batare da tace dashi komai ba,, wani irin kallo yakeyi mata wanda yake ɗauke da tarin ma'anoni masu yawan gaske..  Hanunta dake cikin nasa hanun  ya shiga murzawa  haɗe da langwaɓar da  kansa gefe yana me cigaba da kallon fuskarta.   Hawayene yaziraro daga cikin idanun ta zuwa kan ƙuncinta,  sam bata taɓayin zato ko tsammani ba, saijin sauƙar bakinsa tayi akan ƙuncinta, yayinda yasanya harshensa yana me lashe ruwan hawayen  dake gudu akan ƙuncin nata.  wani irin bugawa zuciyar Zahrah tashigayi da sauri, yayinda numfashinta keshirin ƙwace mata batare da tashiryawa hakan ba,,  cikin ɗan kuzarin daya rage mata tayi saurin tureshi gefe  haɗi  da miƙewa tsaye, ƙoƙarin kama hanunta  yakuma yi amma saidai baisamu daman hakan ba domin kuwa tuni harta fara tafiya.     "Zahrah"   yakuma ƙiran sunanta amma sai dai ko waiwayosa batayiba balle yasaran zata amsa masa..    Jefa ƙafarta kawai take batare dako da ganin gabanta tanayiba, gaba ɗaya ƙwalla suncika mata idanu,  yayinda ƙirjinta ke mata luguden duka kanta kuwa tamkar anɗaura mata gungumen ice haka takeji yamata nauyi...

Cikin Hanzari Zaid yarufa mata baya, yana me ƙiran sunanta amma kuma bata amsa masaba, haka kuma bata tsayaba, dai  dai lokacin wani me taxi yazo wucewa da sauri Zahrah taɗaga masa hanu, aikuwa take yatsaya,, ganin haka yasanya Zaid yaƙara sauri don yaga alamar tafiya zatayi batare da ta tsaya ta sauraresa ba,, amma ina yamakaro domin mai taxi ɗin yana tsayawa Zahrah    ta buɗe murfin motar tashige haɗe da cewa mai taxi ɗin yatada motar sutafi..    Zaid na ƙarasowa wajen, me taxi ɗin kuma na figar motar ya cillata kan titi.. Wani irin iska me zafi Zaid ya fesar daga cikin bakinsa, sam baiso haka ba, yaso ace yaji koda kalma ɗayane daga bakinta, amma kuma duk da haka yamatuƙar jin daɗin ganinta, gashi kuma har kusa da'ita yasamu yazo, babban abun farincikin kuma shine har numfashinta ya shaƙa. Take yaji zuciyarsa tayi masa wani irin sanyi, yayinda daɗi da kuma nutsuwa suka cika masa ruhinsa.. Cike da farinciki haka yakoma  inda yabar motarsa.....

Zahrah kuwa ko acikin taxi hawayenta kasa tsagaitawa sukayi, saima kara tuttulowa da suke tamkar ana hankaɗosu...   Ahaka har mai taxi ɗin yakawota ƙofar gidansu. Kuɗinsa tabasa ko canji bata tsaya karɓa ba ta wuce cikin gida.. A zauren gidan nasu ta tsaya haɗe da sanya hanu ta share hawayenta, sam bataso kowa yasan halin da take ciki, ta barwa Allah dakuma zuciyarta...

Tana shiga cikin gida Inna tayo wajenta da sauri 

"A'ina kika tsayane Zahrah? gaba ɗaya duk kinsa hankalinmu yatashi, munsan bakya kaiwa iwar haka baki dawo ba"  Inna tafaɗi haka tana me ƙaremawa yanayin Zahrah'n kallo.

"Bansamu abun hawa bane Inna, yau Samad yana da wani uzuri shi yasa baisamu daman ɗaukoni ba" Zahrah tafaɗi haka tana me ƙwaƙulo murmushi ta aza akan fuskarta..

Da kallon tuhuma  Inna tabi ta harta shige cikin ɗakinta, tana shiga cikin ɗakin ta dannawa ƙofarta sakata, a hankali tazame  ƙasa  haɗe da jingina bayanta da ƙofar, kana ta cusa kanta cikin cinyoyinta, wani irin kuka tashiga rerawa me tsananin bantausayi,   Yazatayi da rayuwarta ne itakam, da badon kada tayi saɓo ba da sai tace  wannan ƙaddaran nata yayi mata girma dayawa, amma sai dai kuma ba'aja da ikon Allah, haƙiƙa tayi imani cewa komai zaizo yawuce, domin kuwa komai yayi farko yana da ƙarshe, amma kuma sai dai tana da yaƙinin cewa kafun  nan wataƙila zuciyarta tayi  bindiga ta tarwatse,,   "yazatayi da abun da takeji acikin zuciyarta?" tambayar da kullum saitayi mawa kanta kenan, amma kuma zancen ɗayane shine bata da amsar da zata bawa kanta..  Tana cikin kukan taji wayarta na ƙara, amma ko ɗago kanta batayiba haka wayar  taƙaraci tsuwanta har ƙiran ya katse, wani ƙiran ne yakuma shigowa  still har wayar ta katse batako  ɗaga ido ta duba taga waye yake ƙiranta ba..  Kuka tayi sosai kafun tatashi daga durƙushen da take takoma kan katifarta,,,, kwanciya tayi luf tana me sauƙe ajiyar zuciya akai akai, yayinda tsikar jikinta ke yawanta tashi, idan tatuno kusancin da suka samu ɗazu ita da Zaid,  bakomai ke dagula mata lissafi da kuma hautsina mata ƙwaƙwalwa ba kamar idan tatuna da yanda yasanya harshensa akan kumatunta yanashan hawayenta, yana me kuma yi mata wani irin kallo wanda yakasa ɓacewa daga cikin idanunta,,,  batasan me Zaid yakeso a tattare da'ita ba,  wataƙila rayuwarta yakeso, wataƙila kuma hauka yakeso yaga tayi, baisan yatakeji idan ta gansa ba, baisan metakeji agame dashi  aduk sanda taɗaura idanuwanta akansa ba, sake gyara kwanciyarta tayi, tabbas tana da buƙatar samun wani wanda zata faɗawa gaba ɗaya damuwarta, tana da buƙatar wanda zai kwantar mata da hankali yakuma samamata nutsuwa, tana kuma buƙatar wanda zai fayyace mata abun dake cikin zuciyarta, koda hakan zaisanya tasamu sauƙi da salama,, haka dai Zahrah tayi bacci zuciyarta cike da tarin tambayoyi.....

Zaid ne kwance akan  wata haɗɗɗiyar kujera mai kama da gado, wanda take aje cikin wani irin katafaren falo wanda aka ƙawatasa da kayan ƙyale ƙyale dakuma more rayuwa.    Murmushine ɗauke akan fuskarsa, yayinda kyawawan idanunsa suke a lumshe, wani irin shauƙi me tsanani yakeji a tattare dashi,  a iya ganinta da yayi jiyake tamkar anyaye masa gaba ɗaya damuwarsa ne,   idanunsa yasake lumshewa haɗe da  sake shaƙan daddaɗan ƙamshin da yakeyi masa yawo acikin hanci,  ƙamshin da tun ɗazu yakasa barin  hancinsa, "wani irin daddaɗan ƙamshine haka Zahrah'nsa keyi?"  ya tambayi kansa,,  tabbas zai so ace  iyanzu Zahrah na kusa dashi,  dakuwa kwana zaiyi manne da'ita yana shaƙan wannan daddaɗan ƙamshin nata,  sannu ahankali wani irin muguwar kasala ke dirar masa, yayinda wani irin sha'awarta me tsanani ya kawo masa ziyara,,   a hankali yasanya harshensa ya lashi laɓɓansa haɗe da sanya hanu yashafi  ƙwantaccen beard ɗin sa wanda koda yaushe yake ƙara ƙawata masa fuskarsa,,    a hanakali ya ware manyan idanunsa wanda suka soma sauya launi daga farare zuwa kalan bacci, wanda idan ka kallesu dole zasu sauƙar maka da kasala...  Laptop ɗin dake kusa dashi ya ɗauka, haɗe da buɗewa, take hoton kyakkyawar fuskarta ya bayyana akan screen na laptop ɗin,, murmushi yayi haɗi da sanya hanu yashafi kan screen ɗin laptop ɗin..

"Inasonki Zahrah!" 

ya faɗi haka cikin wata irin murya me ɗauke da matsanancin shauƙi.  Take yaji yana matuƙar sha'awan kallon vedion dayayi mata ɗazu batare da tasani ba, lokacin fitowarta daga gidan Hajiya Shuwa.   Wayarsa da vedion ke ciki ya ɗauka haɗe da kunnawa,  kallon vedion yakeyi yana murmushi, amma  kuma kwata kwata saƙonnin da suke shigowa ta Email ɗinsa sun hanasa sakat..   Kai tsaye fita daga ɓangaren vedion yayi ya kutsa cikin Email ɗin nasa,  saƙonnin abokanan business ɗinsa ne, sama sama yakaranta saƙonnin, haryana shirin fita daga cikin Email ɗin sai kuma idanunsa suka sauƙa akan    saƙon  Jasheer wanda yaturo masa,, hakanan yaji gabansa yaɗan faɗi saboda  yasan duk saƙon da zaizo daga Jasheer to akan Zahrah ne,,   buɗe saƙon yayi haɗe da ƙurawa hoton da Jasheer yaturo masa idanu..  Wani irin abu ne yaji ya taso yatokare masa maƙoshi, yayinda idanunsa suka kaɗa sukai jajur dasu, take gashin jikinsa suka mimmiƙe,   wani irin juyawa yaji kansa nayi masa,, shin dagaske katin ɗaurin auren Zahrah idanuwansa suke gane masa ko kuwa? sake waro manya manyan idanuwan nasa yayi aikuwa ba ƙarya idanun nasa keyi masa ba, sunan Zahrah ne rantaɓe ajikin katin dakuma sunan Dr.Sadeeq,, wani irin ƙara Zaid yayi haɗe da yin cilli da  wayartasa, take ta bugi bango  takuma faɗowa ƙasa lokaci ɗaya ta tarwatse.. Cikin matsanancin ɓacin rai jikin Zaid yasoma rawa take yaji wani irin matsancin  zafi a dai dai saitin zuciyarsa, lokaci ɗaya wani irin tari  ya tasomai,  take yasoma tari babu ƙaƙƙautawa, sai ga jini na fita ta bakinsa abun mamaki, abun da bai taɓa gani ba arayuwarsa,,  da ƙyar yasamu tarin ya tsagaita, amma kuma duk da haka ƙirjinsa bai daina yi masa ƙuna ba, yayinda zuciyarsa keyi masa zafi har cikin cikinsa kuwa yakejin zafin,, a hankali ya jingina bayansa da jikin bango, haɗe da rumtse jajayen idanunsa,    numfashi yashiga fitarwa a hankali, daga ni kai kasan yana matuƙar jin ciwo,, cikin yanayi na wahaltuwa  haka ya daddafa zuwa cikin ɗakinsa,  ƙaramin drower'n dake gefen gadonsa ya jawo haɗe da ciro magungunansa,  tsabar ɗacin da yakeji a maƙoshin sa da ƙyar ma ya iya haɗiye magungunan... Kwanciya yayi  akan gado haɗi da rumtse idanunsa, baisan ina zai tsoma rayuwarsa ba,  baisan tayaya zai fara jure rashin Zahrah akusa dashi ba... Kamar dai yanda Zaid yaga rana haka yaga dare, koda kuwa na minti guda ne baiji wani salama ko sanyi acikin zuciyarsa ba, haka ya share awanni masu yawa cikin ciwo,, sai da yayi sallan Asuba ƙafun wani irin bacci me nauyi ya sace sa batare daya shiryawa hakan ba......

*****

Zahrah kuwa yau  da wani irin irin matsanancin ciwon kai ta tashi,  gaba ɗaya  idanunta sunyi luhu luhu dasu,  da gani kai kasan cewa kuka tasha ta ƙoshi. 
Yau ya kasance  aurenta da Dr.Sadeeq saura kwanaki shida kenan tana ƙirgawa kuma acikin kwanakin nan ne zasu fara gudanar da shirye shiryen da suka tsara,, gaba ɗaya ji takeyi bata marmarin auren, sannan kuma ji takeyi komai yafice mata arai, bawai kuma don batason Dr.Sadeeq ɗin ba, tun shekaran jiya Dr.Sadeeq yakawo mata ɗinkunanta da kuma kayan da zata sanya a kamu da wajen diner, amma kuma ko duba kayan batayi ba balle taga ma ko sunyi mata ko basuyi mata ba, batasan meyake damunta ba, amma tabbas tasan akwai wani baƙon al'amari dayake ta kusanto rayuwarta aduk kwanan duniya.     Yau hakanan tatashi taji ko gyaran jikin ma batason zuwa, amma kuma dazaran tace bazata jeba  tasan Inna zata sanyata agaba da yawan tambayoyi, don haka ma gwamma kawai ta je ɗin zaifiye mata...    Sauri sauri haka ta shirya tafito, saboda  tasan cewa yanzu haka Samad na ƙofar gida yana jiranta... ai kuwa tana fitowa taga motar Dr.Sadeeq fake a ƙofar gidan nasu, murmushi kawai tayi haɗe da ƙarasawa wajen motar...  "Allah sarki Samad yana da haƙurin jira, da Dr.Sadeeq ne da yanzun ya ƙirata a waya" tafaɗi haka a zuciyarta dai dai sanda taƙaraso gaf da motar, buɗe murfin motar tayi tashiga bakinta ɗauke da sallama,  "Kayi haƙuri Samad nabarka kana ta jira"  tafaɗi haka tana me ƙoƙarin rufe murfin motar, batare da takalli Inda Samad ɗin ke zaune ba.
Tana rufe murfin motar   tadawo da kallonta wajen zaman driver  fuskarta ɗauke da murmushi,,   a maimakon taga Samad saitaga Dr.Sadeeq, mamakine ya bayyana akan fuskarta alokaci guda, sake ware idanu tayi tana kallonsa, da'alama dai ganinsa yabata mamaki sosai...

 Murmushinsa me kyau yayi mata haɗe da kafeta da idanunsa wanda suke sauƙar mata da wani irin yanayi na kasala ajikinta..      Itama murmushin tayi masa haɗe da shagwaɓe fuska....
"Ni dai nayi fushi!"  tafaɗi haka a shagwaɓe...     

"Tuba nake"

Dr.Sadeeq yafaɗi haka yana me kama kunnuwansa da duka hannayensa..   alaman ban haƙuri.

  "Ni dai naƙi wayon"  tafaɗi haka  tana me kaɗa idanunta..     Murmushi yayimata haɗe da kamo duka hannayenta yasanya acikin nasa hanun,  lumshe idanunsa yayi alokaci guda haɗe da buɗewa

"Nayi kewarki sosai Zahrah na!" yafaɗi haka cikin wata murya me sanyi. 
Ɗan guntun murmushi tayi haɗe da soma ƙoƙarin janye hanunta  daga cikin nasa  hanun, amma kuma  bata samu daman hakan ba.    "Meyasa jiya kika ƙi ɗaga wayana?"  yatambayeta cike da kulawa bayan yagama karantar yanayin da take ciki.     Sai alokacin ne ma Zahrah ta tuno da cewa jiya taga  missed calls ɗinsa, sanann kuma bata bi bayaba,, ƙaƙalo murmushi tayi haɗe da cewa " Kayi haƙuri nayi bacci ne alokacin" 

Kansa ya jinjina badon wai ya gamsu da abun da ta faɗa ba,, ta da motar yayi suka hau kan titi.    Saida sukayi nisa a tafiyar kafun yadawo da kallonsa gareta, sosai tayimasa kyau komai nata ya canja, sai dai kuma kallo ɗaya yayimawa fuskarta yafuskanci cewa tayi kuka,  dafari yaso tambayarta meke damunta, amma kuma sai kawai ya share,,, sama sama yake janta da hira harsuka iso gidan Hajiya Shuwa... Yana ganin shigewarta cikin gidan ya sauƙe ajiyar zuciya ƴaɗe da kifa kansa akan steering motar,    "meke damun Zahrah ne?"   ya yiwa kansa tambayar a bayyane, amma sai dai kuma bayida amsar da zai bawa kansa....    A jiyar zuciya yakuma sauƙewa akaro na barkatai, zuciyarsa cike da tunani kala kala yaja motarsa yabar ƙofar gidan....... Ɓangaren Zahrah kuwa kwana biyun nan wasu irin magunguna masu ƙarfin gaske Hajiya Shuwa take bata tanasha, hakan kuwa shike taimakawa wajen hautsina mata tunaninta, wani irin abu takeji acikin jikinta  wanda kai tsaye za'a iya ƙiransa da suna sha'awa,  ko da yaushe yanzu Zahrah cikin jin feelings take, hattakai ta kawo yanzu alwala  ma baya daɗewa ajikinta yake karyewa  saboda sosai sperm ke fita ajikinta, duk kuma ɗaya daga cikin aikin magungunan ƙarin ni'iman da Hajiya Shuwa ke bata ne, lallai ita kanta tasan cewa Hajiya Shuwa tayi mata babban haɗi me matuƙar kyau...... (su Doctor za'asha nice😜🙈)


Tunda bacci ya ɗaukeshi da asuba bashi yafarka ba sai ƙarfe 9:30 am, da wani irin zazzafan zazzaɓi yatashi, wanda ya zamana ko ɗaga kansa ba ya'iyawa  hatta numfashima da ƙyar yake iya fitarwa. Yana a wannan halin  ne yaji anturo ƙofar ɗakin nasa, bai iya ɗago kansa ya dubi ko waye ba amma kuma duk da haka ya gane waye ne yashigo cikin ɗakin...   Dasauri Alhj Ma'aruf   yaƙaraso garesa...

"Lafiya Zaid meke damunka?" Alhaji Ma'aruf yafaɗi haka yana me kai hanunsa jikin Zaid, da sauri yajanye hanunsa daga jikin Zaid ɗin domin kuwa jiyayi jikin Zaid ɗin yaɗau zafi rau kamar wuta.   "Subahanallah, bana ƙira Doctor yanzu" Dad yafaɗi haka yana me ƙoƙarin ciro wayarsa daga cikin aljihu,,   bugu biyu Dr.Bilal yaɗauki wayar, cike da damuwa Dad yace yanason ganinsa jikin Zaid ne yatashi. take Dr.Bilal yace gashinan zuwa.. 
Zama Dad yayi jigum agefen gadon Zaid ɗin,  gaba ɗaya yarasa mekeyi masa daɗi, sosai matuƙa cutar Zaid ke damunsa, yana matuƙar ƙaunar Zaid sam bayaso wani abu ya samesa, musamman ma yanzu da Dr.Bilal yashaida masa cewa Zaid ɗin yana ɗauke da ciwon zuciya me tsanani... Mintuna kaɗan Dr.Bilal yaƙaraso gidan, babu wani ɓata lokaci kuwa yashiga yiwa Zaid wasu ƴan gwaje gwaje,  drip  yaɗaura masa bayan yayi masa wasu allurai guda biyu wanda zasu taimaka wajen kawar da zazzaɓi da kuma ciwon da kansa keyi masa uwa uba kuma su sanyasa bacci,  saboda idan yana a cikin hayyacinsa bazai taɓa barin zuciyarsa ta huta ba, yin hakan kuma shike ƙara sawa ciwon yayi tsanani...    Bayan sun fito compound ɗin gidan ne Dr.Bilal yagyara tsayuwarsa haɗe da  duban Alhaji ma'aruf,, bayani  yashiga yimawa Alhaji Ma'aruf ɗin sosai agame da ciwon Zaid ɗin.   Bayan sun kammala maganan ne Alhj Ma'aruf yakoma wajen Zaid da tuni wani baccin wahala yasake ɗaukansa......

*****

Rana bata ƙarya, ranar yau takasance laraba kuma yautake kamun Amarya, tun da safe gidan su Zahrah yake acike ƴan uwan Inna sun tattaro ƙwansu da ƙwarƙwatansu sun garzayo, don haka tuni gida yaɗauki hargowa da hayaniyan mutane yayinda amarya kuwa tunsafe take ƙunshe a ɗaki acewarta cikinta ne keyi mata ciwo,, Husnah da Suhaima ne suka taimaka wajen ɗebe mata kewa ta hanyar zama da'ita.....

Ƙarfe uku na yammaci kenan amma tuni gidansu Zahrah ya ɗinke da mutane, ciki kuwa hadda ƴan matan school ɗinsu  wanda Husnah ce ta gayyacesu, domin ita dai Zahrah bata da wasu ƙawaye Husnah ce kaɗai ƙawarta...  Kowacce ka kalla acikin ƴan matan nan  tasha kyau cikin kayan anko ɗinta.    Husnah ce tsaye akan Zahrah tana ta faman ɓaɓatu akan cewa Zahrah'n ta tashi su tafi shagon meckup domin tuni Dr.Sadeeq yaturo freinds ɗinsa waƴanda zasu kaisu shagon yin meckup ɗin suna ma jiransu aƙofar gida,,  ita dai Zahrah yau jitayi gaba ɗaya bakinta ya mutu sambatajin wani kuzari ajikinta.  Kayan da zata sanya da duk wani abun da zatayi amfani dashi, Husnah ta ɗaukar mata haɗe da kama hanunta suka fice daga cikin gidan.  Wasu haɗaɗɗun motoci suka shiga  kai tsaye aka wuce dasu wani shahararren shagon meckup....    

Kwalliya sosai shahararriyar meyin meckup ɗinnan ta tsantsarawa Zahrah akan fuskarta lokaci ɗaya saiga Zahrah ta sauya kamanni asalin kyawunta yasake bayyana tamkar wata balarabiya ita kanta Zahrah saida tayi mamakin ganin kanta, tabbas dabadan tasan ita ɗin ceba, to da sai tace sanja mata fuska akayi,    kowa yaga kwalliyanta saiyayi santi saboda tasha kyau iya kyau..    Wani doguwar rigan leshi me kyau da tsada ta sanya ajikinta, take  kyakkyawar surar jikinta ya bayyana kansa acikin kayan,  sosai ɗinkin yayi kyau yakuma amshi jikinta,  zama tayi aka tsantsara mata  haɗaɗɗen ɗaurin ɗankwali akanta, yayinda  aka nannaɗe mata dogon gashinta atsakiyar kanta, ita dai tsayawa tayi kamar wata statue tana mamakin irin baiwar kyawun da Allah yayi mata,   daga riganta har zuwa kan takalminta dakuma ɗan karamin fos ɗin dake rike ahanunta kalarsu yakasance light peach ne, yayinda stones ɗin kayanta suka kasance farare,   lokacin da su Husnah sukayi tozali da Zahrah ihu dakuma shewa suka sanya haɗe da tsantsar mamakin irin kyawun da Zahrah tayi, kowa dai yasan Zahrah kyakkyawace amma kuma basuyi tunanin kyawunnata har ya kai hakaba, lallai duk namijin daya samu Zahrah amatsayin mata yayi babban gamdakatar. Take su Husnah suka shiga ɗaukarta hotuna da kuma vedios suna watsawa a instagram dakuma whatsapp, suna cikin buga selfie abokan ango suka ƙaraso don ɗaukar ƙawayen amarya,, duka ƴan matan kowacce da motar da tashiga, yayinda aka bar Zahrah da Husnah sukaɗai saboda Ango yace shi dakansa  zaizo yaɗauki amaryarsa...   Ƙawaye basu jima da tafiya ba wayar Husnah tasoma ƙara,, murmushi tayi haɗe da kallon Zahrah adai dai lokacin da taɗaga wayar takara akan kunenta,    "To ranka shi daɗe gamunan fitowa" abun da Husnah tafaɗa kenan haɗe da miƙewa tsaye hannuwan Zahrah takamo haɗe da miƙar da'ita tsaye..
"Angonki yaƙaraso yace nafito masa dake"  murmushi kawai Zahrah tasakar mawa Husnah kana ta sunkuyar da kanta ƙasa.. A hankali Zahrah ke takawa yayinda rigar jikinta kejan ƙasa, babu abun dake tashi ajikinta sai daddaɗan ƙamshin turare,,  gaskiya Zahrah tayi kyau sosai ayau ɗin..

Ware idanu Dr.Sadeeq dake zaune acikin motarsa yayi yana me kallon Zahrah, shima yasha ado cikin wata farar gezina me matuƙar kyau da tsada yayi kyau sosai da sosai, kwarjininsa yasake fitowa fili..... Har Husnah ta buɗe murfin motar ta tura Zahrah ciki bai rufe bakinsa ba haka kuma bai ɗauke idanunsa daga kallon da yakeyi wa Zahrah ba, lallai ne godiya ta tabbata ga ALLAH (S.W.A) daya tsara wannan kyakkyawar halitta,  kullum kuma koda yaushe yana kallon kyawun Zahrah amma kuma yau saiyake ganin kyawun nata yafi na koyaushe ƙawatuwa..   A hankali ya sauƙe wata irin ajiyar zuciya haɗe da lumshe idanunsa,,,  Zahrah kuwa tunda tashiga cikin motar ta sunkuyar da kanta ƙasa tana me wasa da yatsun hanunta,,    Motar Habeeb dake bayan ta su Zahrah Husnah tashiga,,, atare motocin suka tashi tafiya sukeyi ahanakali akan titin... 

"Zahrah!" Dr.Sadeeq yaƙira sunanta cikin wata irin murya me sanyi dakuma sauƙar da nutsuwa.    Kasa amsa masa Zahrah tayi, hakanan taji wani irin nauyinsa ya lulluɓeta.  
   
"Kinyi matuƙar kyau sosai, sai yanzu nasakejin cewa nayi babban sa'a dana sameki, inasonki sosai Zahrah na, ina fata watarana nima kisoni tamkar yanda nake sonki!"

Sai alokacin Zahrah ta ɗago kanta, haɗe da sakar masa ƙawataccen murmushi,  jiyayi gaba ɗaya ta kashesa  da salon murmushin nata, a hankali ya matso daf da'ita haɗe da kamo hannayenta duka biyu ya riƙesu gam acikin nasa,  wani irin soyayyartane yaji yana ƙara shiga jikinsa, jiyakeyi tamkar ya jawota jikinsa

Please Login or Register in order to submit comment