Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

santala santalan cinyoyinta da suke bayyane a fili yashiga yi, wani iri yaji acikin jikinsa, da sauri ya ɗauke kansa..

Ganin da tayi cewa baya kallonta ne yasanya tayi saurin zura dogon wando na pencil jeans haɗe da wata farar top shirt me kyaun gaske ajikinta,  yaune karo na farko da ta fara sanya irin waƴannan kayan ajikinta, ita kanta saitaga ta burge kanta domin kuwa hips ɗinta sunfito acikin wandon sunyi ɗas dasu kamar wanda aka zana.. Kasa daurewa yayi saida ya kafa mata idanunsa,  sosai tayi masa kyau baitaɓa ganinta acikin irin wannan shigar ba, ta ɗau hankalinsa ƙwarai lallai Zahrah macece har mace komai nata me kyau ne...     Tana tsaka da shafa turare ajikinta taji yaƙira sunanta.   Tsayawa tayi cak daga abun da takeyi haɗe da juyowa  sai dai bata kallesa ba ta amsa ƙiran dayayi mata.

"Zonan!" yace da ita ata ƙaice.. Ahankali tashiga takawa harzuwa inda yake, tana ƙarasawa garesa ta durƙusa a ƙasa haɗe da sunkuyar da kanta tana me wasa da yatsun hanunta.. Hanunta yakamo haɗe da jawota jikinsa ya zaunar da ita akusa dashi,    cike da kulawa haɗi da lallami  yashafa kumatunta yace "Kinyi kyau"

Tsintar kanta tayi dayi masa murmushi kawai... 

"Meke damunki? Sannan menene dalilin dayasa naga wayarki a fashe gaba ɗaya kuma tatarwatse?" 

Kanta tashiga girgizawa alaman babu

"Kinsan banason ƙarya, menene dalilin da yasa zaki ɓoyemin damuwarki? kada ki manta yanzu bake kaɗai kike iko da kanki ba, nima nan inada iko dake, saboda haka na cancanci ki sanardani damuwarki, ni mijin kine bazan taɓa son naganki acikin damuwa ba!" cike da lallashi ya ƙare maganar.

Mezata faɗa masa? tace masa Zaid ne yaƙirata a waya ko me? ko kuma tace masa hawayen da takeyi duk akan Zaid ne? 

"Dagaske nake bakomai, na ɗaga wayar hanuna da kumfa shine ta suɓuce ahanuna tafaɗi"  tsintar kanta tayi da basa wannan amsar, duk da cewa ƙarya ba ɗabi'arta bane amma yazama dole yau tayi, saboda sanar dashi gaskiyan lamarin daya faru bashida wani alkhairi saidai ma ransa ya sosu.

Ajiyar zuciya yasauƙe haɗe da jinjina kansa "Naji amma meyasaki kuka?"

Jitayi gabanta ya faɗi amma saita dake tace "Kuka nake saboda na fasa wayata"

Ɗan guntun murmushi yayi sam bai gamsu da maganganunta ba, amma kuma yazaiyi tunda ta ɓoyemasa gaskiya bazai tursasata ba..    

"Saboda wayarki ta fashe kawai shine kike kuka? har yanzu dai ke yarinyace ƙarama Zahrah, amma mene abun kuka, idan kikace na saya miki wata kina ganin bazan saya miki bane?"

Kanta ta jinjina alamar "A'a"

"To indai hakane miye na kukan tunda kinsan zansaya miki wata wadda ta fita,  kitaimaki zuciyata ki daina sa kanki acikin damuwa please, inasonki banason naga wani abu ya ɓata ranki!"

Raunannun idanunta ta ɗago ta kalleshi, wannan maganar daga cikin ƙahon zuciyarsa yake fituwa, tabbas ita kanta ta gamsu da ƙaunar da doctor yakeyi mata ɗari bisa ɗari,   ya cancanci tasakamai da farinciki ne bawai akasin haka ba..

"Ki kwantar da hankalinki, gobe Insha Allah namiki alƙawari zamuje dake ki zaɓi irin wayar da kike so,  shikenan?"

Kanta ta ɗaga tana ɗan murmushi, kamar da gaske maganar wayarce a cikin ranta.. Miƙewa yayi yafaɗa toilet, tanajin sauƙar ruwa aƙasa ta sauƙe nannauyar ajiyar zuciya,  bataso doctor yasan cewa Zaid yafara bibiyar rayuwarta. Sumu sumu haka ta fice falo. 

Tana zaune tayi jigum ya fito daga cikin ɗakin, sanye yake da blue ɗin wando kalan nata, sai dai nasa na maza ne babu ado kamar nata, saikuma farar polo shirt,  murmushi tayi domin kuwa yayi mata kyau sosai, shima murmushin yayi mata haɗe da kashe mata idanunsa ɗaya...

Ita da kanta ta zuba musu abinci, yanaci yanata zuba mata santi, har batasan lokacin da tarin damuwar dake cikin ranta suka kau tasoma ƙyalƙyalewa da dariya ba ...

****

Zaid ne zaune agaban Dad ɗinsa ya sunkuyar da kansa ƙasa, magana Dad ɗin keyi masa amma kuma kwata kwata bayajinsa, hankalinsa da tunaninsa sunyi nisa sosai wajen tunanin Zahrah, muryarta dayaji ɗazu shiya kara rikita masa tunani,  baisauraran Dad dake yimasa bayani amma duk da haka yaji abun da Dad ɗin yafaɗa na ƙarshe, cike da ƙuncin rai haɗe da tsananin mamaki yake kallon Dad ɗinnasa cikin wata murya me ɗaci yace

"Aure fa kace Dad? ni ɗin, kuma da wata ba Zahrah ba?"

Cikin takaici Dad yake kallon Zaid ɗin, wato tunkan ayi nisa ma yafara nuna masa cewa hakan bazai yiwuba kenan.

"Natabbatar kajini, kuma aure babu fashi!" Dad yafaɗi haka a ƙufule, domin kuwa shima yafara gajiyawa da halayyan Zaid na rashin hankali, taya zaka je kana yiwa matar wani soyayya me tsanani irin haka.

Wani murmushi Zaid yayi me matuƙar ciwo haɗe da sanya haƙoransa ya ciji laɓɓansa.

"Bazan iyaba Dad, kaima kafi kowa sanin hakan, aduniyar nan mace ɗaya kawai nakejin zan iya rayuwar aure da ita, bakowa bace kuma Zahrah ce, saboda haka please Dad maganar wani aure na da wata kabarshi don banaso, idan kuma ka matsa shikenan, amma idan kuka tsinci gawanta nayi mata mugun illa kada ku zargeni kufara zargin kanku"  yana kaiwa nan azancensa ya tashi tsaye yafice daga falon mahaifinnasa.. Baki a wangale haka Dad yabi Zaid da kallo har yaɓacewa ganinsa..

"Lallaima kuwa Zaid ya ɗauko babban al'amari, amma kuma wannan karon sam bazai lamunta masa ba aure dole sai yayi masa, acikin satin nan ma kuwa" Dad yafaɗi haka acikin zuciyarsa...

Zaid kuwa yana fita a ɗakin Dad direct motarsa yashiga, dagudun gaske ya ja motar yafice daga cikin gidan,    tafiya yake akan titi amma zuciyarsa ƙuna takeyi masa, har wani ɗaci yakeji a maƙoshinsa, wayarsa ce tayi wani ɗan gajeren ƙara alamar shigowar saƙo (Message), da sauri ya ɗauki wayar ya duba, domin kuwa tun ɗazu dama saƙon yake jira, adireshi ne na gidan da Zahrah take aka turo masa.. Wani mugun murmushi naga yayi haɗe da ɗan dukan kan steering motar, lallai dole zai cimma burinsa ne kota halin yaya kuwa...

Faka motan yayi yana me ƙaremawa gaban gidan kallo, gidane me kyau da kuma aji, dagani kasan ankashe kuɗi wajen tsara gidan, amma Zaid dake kishi yacika masa zuciya sam baiga wani kyawun gidan ba, saima ji da yayi ya tsani gidan..  Idanunsa ya tsaida akan tankamemen gate ɗin gidan tamkar wanda yake karantan wani abu, a hankali ya buɗe murfin motar tasa yafito waje, cikin takunsa na isa yashiga takawa harzuwa wajen gate ɗin....... (🤔Anya zaishiga kuwa?hmmm inaga dai yau Zaid aƙasam kanta zai kwana😂)


*(Kuyi haƙuri dan Allah kwana biyu kunjini shiru wallahi neighbour ɗitace tarasu ranan friday da dare shiyasa kuka jini shiru, naji mutuwar ajikina wallahi sosai shiyasa nakasa koda yin typing ɗinne ma, please kusata a addu'anku Allah ubangiji yayi mata rahama, yasa aljanna tazamo makoma a gareta Ameen thumma Ameen. Ina me ƙara neman afuwarku sosai 🙏🙏🙏)*


     *Tuesday 28/January/2020*



           *Fatymasardauna*



🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

      *SHU'UMIN NAMIJI !!*

     *Written By*
Phatymasardauna

*Dedicated  To My Brother KHABIER*

*🌈Kainuwa Writers Association*

_{United we stand and succeed; our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}_

*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*

            *WATTPAD*
      @fatymasardauna

*Editing is not allowed📵*

        *CHAPTER 100 to 101*

Tsayawa yayi  yana me ƙarewa gate ɗin kallo, idan da zaibi son zuciyarsa ne, to tabbas da shiga cikin gidan zaiyi, amma kuma saidai wata zuciyar tana gargaɗinsa da kar ya shiga cikin gidan, bawai kuma don yanajin tsoro ba, kawai  dai yana me tausayawa kansa ne, yasan idan yaga Zahrah dole sai ciwonsa yasake motsawa, duk da yanzun ma bawai ciwon nasa ya kwanta bane,   komawa yayi cikin motarsa yazauna, haɗe da Kifa kansa akan steering motar, lumshe idanunsa yayi sai kawai ga hawaye suna fitowa daga cikin idanun nasa, wai yau shi Zaid ke kuka akan mace, lallai rayuwa juyawa take, gashi shikam tajuyo masa da saɓanin tunaninsa...  Ƙarar motar dayaji shi yasanya sa ɗago kansa yakai kallonsa wajen gate ɗin gidan, ko ba a faɗa masa ba yasan motar RIVAL ce (wai  Dr.Sadeeq ne rival ɗin nasa) balle ma kuma yagansa acikin motar, wani irin abune yazo ya tokarewa Zaid maƙoshinsa, baƙinciki, haushi, takaici, da kuma tsanar doctor ne duk suka haɗe masa waje guda. Ji yake kamar yafita acikin motar yaje ya shaƙo sa kozaiji salama acikin ransa.. Har motar doctor tashige cikin gidan  bai ɗauke idanunsa akan gate ɗin ba,   da sauri ya rumtse idanunsa lokacin da motar tagama shigewa cikin gidan aka kullo gate ɗin gidan, da ƙarfi ya danne lips ɗinsa haɗe da buga steering motar,   yanaji yana gani wani  zai yi masa rayuwa da Zahrah'nsa.     "Yanzu Allah ne kaɗai yasan shigarsa mezaiyi mata, wata ƙilama rungumeta zaiyi, wataƙila kuma har kiss zaice zaiyi mata"    wata zuciyar tafaɗa masa haka.  Da ƙarfi ya shiga dukan steering motar,  yana me jijjiga kansa,  ƙwaƙwalwarsa bazata iya ɗaukar masa wannan tashin hankalin ba, jiyake komai na duniyan nan najuya masa,   Allah yasa abun da zuciyarsa ta faɗa masa bahakanne zai kasance ba,  bazai taɓa iya jurewa ba,  hanunsa ya ɗaura adaidai saitin zuciyarsa haɗe da sake rumtse idanunsa, zafi yakeji haɗe da zogi acikin ƙirjinsa,  da ƙyar ya'iya tada motar  ya cillata kan titi a zafafe, gudu sosai yakeyi akan titi babu ruwansa da waƴanda suke gabansa ko suke bayansa, idanunsa sun rufe sosai.. Ikon Allah ne kawai yakawoshi gida, amaimakon yawuce ɓangarensa sai ya wuce ɓangaren mom ɗinsa..

Hajiya Safara'u ce tsaye agaban dinning table tana shirya abinci,  batare da sanin shigowarsa ba saiji tayi anrungumeta ta baya,  ƙamshinsa kaɗai taji tagane cewa tilon ɗanta ne,    mamakine tsantsa ya bayyana akan fuskarta yaushe rabon Zaid yazo ya rungumeta haka?     kansa ya ɗaura akan wuyanta haɗe da sauƙe ajiyar zuciya,  wani abu me ɗumi da taji yana sauƙa akan wuyanta ne yasanya tayi saurin juyowa garesa,     batayi mamakin ganinsa ahaka ba amma ƙwarai tayi mamakin ganin yanda hawaye ke zuba daga cikin idanunsa. 

  "Zaid!!"

taƙira sunansa cike da tsananin mamaki haɗe da tashin hankali.

Jajayen idanunsa ya ɗago ya kalleta haɗe da sake rungumeta.

"Mom nakasa jurewa, bazan iyaba, please ki ciremin soyayyarta acikin zuciyata, koda zan samu nutsuwa na minti ɗaya acikin ruhi na!"  cikin matsanancin rauni yake maganar gaba ɗaya yazama abun tausayi yadawo saikace yaro ƙarami..

Ahankali Mom take shafa bayansa haɗe da jinjina kanta, tabbas da ace akwai yanda zatayi da ta cirewa Zaid soyayyar Zahrah acikin zuciyarsa, bazata iya jure ganin hawaye da kuma damuwar ɗanta ba.  

Kamasa tayi suka zauna akan kujera, kansa yaɗaura akan cinyarta yayinda ita kuma take shafa  tarin sumar dake kansa .

"Nakanji ciwo acikin zuciyata idan naganka kana kuka Zaid, bansan wani irin soyayya kakeyiwa Zahrah ba, amma kuma bamu da yanda zamuyi  Zahrah matar wani ce yanzu" Mom tafaɗi haka cike da lallashi.

"Mom  ki taimakeni, zafi nakeji acikin zuciyata, yanzu kenan bazan sameta ba?   shikenan har abada saidai naƙare rayuwata a haka babu ita?   bazai yiwuba Mom, dana sani tun farko daban yaudareta ba, dana sani tun farko dana aureta, duk nine najawa kaina ni da kaina na haramtawa kaina ita, nasan dabanyi mata fyaɗe ba dayanzu na sameta, nine fa nayi mata fyaɗe mom, meyasa nayi haka mom? kaicona yau nayi danasanin yi mata fyaɗe da nayi fiye da  ko yaushe!"  yafaɗi haka yana me sake fashewa da kuka kamar yaro..
Mamaki haɗi  da ruɗani dakuma tsantsar kaɗuwa su suka bayyana akan fuskar Mom, kallonsa kawai takeyi zuciyarta na tafarfasa.

"Kana da hankali kuwa Zaid? Fyaɗe fa kace, anya kuwa ƙwaƙwalwarka bata fara taɓuwa ba?"

Sai yanzu yatashi daga kan cinyarta, bayi da wani zaɓi wanda ya wuce yafaɗawa Mom ɗinsa gaskiya...  

"Ban haukace ba Mom, dagaske ne nine nayi mata fƴaɗe, nine nan na tozarta rayuwarta, nine nan na fara gurɓata mata rayuwa, na rabata da farincikinta da duk wani jin daɗinta, narufe idanuna naketa mata haddinta alokacin da take tsananin buƙatar taimakona,  nayi mata fyaɗe  mom nabiye son zuciyata nasan ban kyauta mata ba amma kuma babu yanda zanyi ne yazama dole......"

Tassssss      haka mom ta ɗaukesa da wani irin lafiyayyen mari,  marin daya matuƙar firgitasa ya ɗaiɗaita tunaninsa, tundayake yataso yayi wayo mahaifiyarsa bata taɓa sanya hanu ta mareshi ba sai yau, kai koda tsawa me ƙarfi bata taɓa yi masa ba,  bakinsa ya hangame haɗe da sanya hanunsa akan ƙuncinsa inda ta maresa yana kallonta.

Itakanta mamakin marin datayi masa take, sai dai kuma ranta amatuƙar ɓace yake..

"Kayi mata Fyaɗe? kacuceni Zaid, bantaɓa tunanin zaka iya aikata wannan rashin imanin ga wata ƴa  mace ba arayuwa, meyasa? meyasa? idan aure kakeso meyasa bakayiba?  kahalakar da rayuwar ƴar mutane, kaicon wannan gurɓataccen halin naka,   tabbas yanzu na yarda alhaki ne kawai ke bibiyarka, idan kuwa hakane to wallahi baka ga komai ba arayuwarka,  niba azzaluma bace kuma bana zama inuwa ɗaya da mutum meyin zalunci,  bansan zuciyarka tayi tauri harhaka ba, dahar kake tunanin aurenta, nayi danasanin tura mahaifinka nemamaka aurenta, ashe kai macucine agareta azzalumi, taya kake tunanin zata amince dakai?" kanta tashiga girgizawa haɗe da juyawa ta nufi matattakalan dake cikin falon ranta amatuƙar ɓace, sam batasan abun da Zaid ya aikata ga Zahrah ba sai yanzu, lallai da ita da kanta zata ɗaukawa Zahrah mataki.

Zaid kuwa har Mom tagama haura step ɗin dake cikin falon, bai ɗauke idanunsa akanta ba, mamakine ya lulluɓesa matuƙa, sake shafa kumatunsa yayi inda mom ɗin ta zabga masa mari, baitaɓa ganin ɓacin ran mahaifiyarsa irin nayau ba tun dayake.  Miƙewa yayi yawuce ɓangarensa shi dai idan za amaresa sau million a basa Zahrah to bazai taɓa damuwa ba..

Mom kuwa tana shiga ɗaki wayar Dad taƙira tasanar masa komai,  ɓacin ran da  Mom tashiga  kaɗanne akan  wanda Dad ya tsinci kansa aciki, lallai Zaid yamaidashi mutumin banza, dayasan haka tafaru tsakaninsa da Zahrah da baije ne ma masa aurenta wajen Baffanta ba, wannan ma ai rashin ta ido ne,  amma zaiyi maganinsa ne, jibi jibin nan zai ɗaura masa aure kuma dolensa ne yazauna da matar, hukuncin da Dad ya yankewa Zaid kenan.

*****

Tun jiya suka koma makaranta amma bata samu daman zuwa ba, doctor da kansa yace ta bari sai yau...   Buɗe ƙofar ɗakin tayi ta fito, dagani sauri take,  ta shirya tsab cikin riga da zani na atamfa ta rufa jikinta da wani ƙaton mayafi me ɗan kauri..
Kallonta yakeyi sosai, take yaji wani irin kishinta ya lulluɓemai zuciya,  duk da ba wani kwalliya tayi sosai ba, amma shikam baijin zai barta tafita ahaka,  kishi yake wani ya ganemai fuskar mata, ganin yanda yake kallonta ne yasanya taɗan shagwaɓe fuska haɗe da karyar da wuyanta gefe, don daganin yanda yake kallonta tasan akwai magana abakinsa.

"Banjin zan barki kifita a haka, maza je ki ɗauko hijab kisanya" yafaɗi haka cikin dakiya da'alama babu wasa a lamarin nasa.     Bata musa masa ba ta koma ɗaki, hijab ta ɗauka ta sanya wanda ya tsaya iyaka guiwarta,  tana fitowa yasake kafeta da idanu, har yanzun ma dai baijin zai iya barinta tafita ahaka, gaba ɗaya ma shi kullum gani yake tana ƙara yi masa kyau, nana gaba kaɗan zai hanata fita ne ma kwata kwata.

"Dan Allah yanzu kam kabarni natafi kaga fa zanyi latti!" tafaɗi haka cikin shagwaɓa.

Marairaice fuska yayi haɗe da sanya hanu yashafi sajen dake kwance akan ƙuncinsa, ba tare dayace komai ba yamiƙe tsaye yanufi hanyar fita daga cikin falon, ganin haka yasa itama ta rufa masa baya da sauri...

Tafiya suke amma yaƙi cewa da ita komai, kallon yanda ya haɗe fuska tayi, sai kawai tasaki dariya, wai ahakan shi fushi yakeyi da ita, sam yanayin fushi bayayi masa kyau akan fuskarsa.

"Meyasa bazaka kulani bane wai? idan makarantar ne bakaso sai ka maidani gida, amma kadaina fushi bakayin kyau kwata kwata idan kana fushi"  tafaɗi haka tanaɗan dariya.

Sai alokacin ya juyo da kansa ya kalleta.     "Ni ba fushi nake ba"  yafaɗi haka cikin cushewar murya. 

Murmushi kawai tayi batare da ta sake ce dashi komai ba, saima kwantar da kanta da tayi ajikin kujeran motar tana kallon yanda mutane suke ta hada hadan su.      
A dai dai inda yake ajiyeta lokutan baya yauma anan yayi parking motar tasa, buɗe murfin motar tayi zata fita, da sauri ya riƙo hanunta,  juyowa garesa tayi tana ɗan murmushi,  shima murmushin yayi mata haɗe da matsowa daf da ita, kiss ya manna mata akan kumatunta haɗe da cewa
"Ki kulamin da kanki" 

Tsadadden murmushinta tayi masa haɗe da jinjina kanta alamar zata yi yanda yace. Sai da yaga shiganta cikin hall ɗin da zasuyi lecture kafun ya ja motarsa yabar haraban makaranta baki ɗaya..

Tana shiga cikin hall ɗin suka ɗinke ita da Husnah sukaita hira, kafun lecturer yashigo....

Ƙarfe biyar na yamma suka kammala duk wani lecture  ɗin da suke dashi,  har bakin motar doctor ɗin Husnah ta rako ta..

Ƙoƙarin janta da hira yake amma tayi masa shiru, saboda gaba ɗaya agajiye take, dolensa shima ya ƙyaleta  harsuka isa gida.

Da ruwan ɗumi tayi wanka, tana fitowa ta zura wata riga doguwa marar nauyi ajikinta, haɗe da faɗawa kan gado,  numfashi kawai take sauƙewa na gajiya, mintuna kaɗan bacci ɓarawo ya saceta,  koda Dr.Sadeeq ya shigo yasamu tana bacci baiyi yunƙurin tashinta, falo yakoma yayi zamansa....

*****

Bayan kwana uku.

Yau kusan kwanansa uku kenan a guest house ɗinsa yake kwana, gaba ɗaya abubuwan duniyane suka haɗu sukayi masa yawa,  bayacin abinci a iya tsawon kwanakin nan, gashi ciwonsa ya dawo sosai, daga zaran yayi tari sai jini, magungunan nasa ma yadaina sha, addu'a yake Allah yasa wannan ciwon nasa yazamo ajalinsa ko zai samu sauƙin raɗaɗin dayakeji acikin zuciyarsa... 

Horn ɗin motarsa yake dannawa a ƙofar gidannasu  kamar zai tashi sama, da sauri me gadi ya wangale masa gate ɗin gidan ya tura hancin motarsa ciki,    ko kyakkyawan parking baiyi ba, haka yafito daga cikin motar yanufi ɓangarensa,   yana shiga falonsa yasoma ƙoƙarin cire rigar jikinsa,  dai dai lokacin wata ƴar mata shiyar budurwa ta buɗe ƙofar ɗakin dake kusa da bedroom ɗinsa ta fito,  tsananin mamakine yakashe Zaid, kallon tuhuma kawai yake aika mata dashi.

Yanda ta gansa sai da taji gabanta ya faɗi amma dayake  dama tayi masa farin sani yasanya taɗan wayance haɗe da sakar masa murmushi..

Kallonta yakeyi daga samanta har ƙasanta,  "wace ƴar iska ce haka da har tasamu daman shigo masa ɓangarensa har da kuma kutsawa cikin ɗaki?" tambayar da yayiwa kansa kenan.

"Wacece ke? Uban waya baki daman shigomin ɗaki?" ya tambayeta murya a kausashe.
Sai da taji tsoro amma kuma hakan bai hanata bayyana murmushi akan fuskarta ba.   Wani ƙululun takaici da baƙincikine suka cika zuciyar sa, badon komai ba sai don murmushin dayaga tanayi masa.

"Dan ubanki bamagana nake miki ba!" ya kuma faɗa cikin tunzura. 

Yanzu kam ta tsorata dashi sosai da sauri ta juya zata koma cikin ɗakin,  taku ɗaya yayi ya fincikota, yana juyo da ita ya bata kyakkyawan mari akan fuskarta wanda ya sanyata fasa wata uwar ƙara, sosai  zafin marin ya ratsata..

"Bazaki faɗamin mikikeyi a cikin ɗakin nan bako dan ubanki, inaga sainaci uwarki tukun zakimin bayani, banza me kama da fara!!" yafaɗi haka yana me ƙoƙarin zare belt ɗin dake jikin wandonsa, da'alama dai so yake ya jibgeta.

"Kada ka kuskura ka taɓa ta inagaya maka idan bahaka ba ranka zaiyi mummunan ɓaci!"

Muryar Dad da shigowarsa kenan yakaraɗe gaba ɗaya falon, aƙufule Zaid yajuyo yana kallon mahaifinnasa.

"Dole ne zan daketa matuƙar bata ficemin acikin ɗaki ba, taya ma zakubar wata kucaka tashigomin ɓangarena, dubeta fa ƙazama da ita, wata ballagazar mata,  kunfi kowa sanin bana buƙatar ƴar aiki, me yasa to zaku ɗaukarmin? kurasa ma wacce zaku kawomin amatsayin ƴar aiki sai wannan baƙar yarinyar!" Zaid yafaɗi haka yana me nuna ta cike da  ƙyama.

"Ba ƴar aiki bace matarkace, kuma wallahi kada kasake kace zaka saketa nafaɗa ma!" Dad ɗinsa yafaɗi haka  cikin ɓacin rai, baijirayi me Zaid ɗin zaice ba yasakai yafice daga cikin falon..

Tsananin tashin hankali ne ya bayyana akan fuskar Zaid, kalaman Dad ɗinsa sunyi matuƙar sanyasa cikin mamaki.

 "Matata?"

tambayar da ya yiwa kansa kenan, sake kallonta yayi, tana nan tsaye sai raba idanu take kamar mayya, dagani a matuƙar tsorace take..

"Da gaskene abun da Dad ɗina ya faɗa?" yayi mata tambayar babu alaman wasa akan fuskarsa.

Kanta ta jinjina masa alamar "Eh"

Wannan wani irin cin fuskane Dad ɗinsa yayi masa? aure batare da saninsa ba auren dole fa kenan?  ae kuwa yau zataci ubanta ne,  matsowa yashiga yi daf da ita hanunsa yasanya ya damƙi gashin dokin da akayi mata kitso dashi, yawun dake cikin bakinsa ya tofa mata akan fuskarta, cike da tsananin takaici ya tureta gefe, take ta ƙwalla ƙara domin kuwa kan table na glass tafaɗa daya tureta,   baiko saurareta ba ya shige cikin bedroom ɗinsa,    yanashiga cikin bedroom ɗin ya buɗe cikin fridge ɗinsa ya ɗauƙo kwalbar alcohol me matuƙar sanyi,  da ƙarfi ya ɓalle murfin alcohol ɗin yakafa kwalban abakinsa, saida yasha fiye da rabi kafun yayi wurgi da kwalban gefe, wani irin haushin kansane yakamasa, baisan da yaushe yaɗau kwalbar giyan yakai bakinsa ba,  yanaso yadaina aikata duk wani abu dayasan Zahrah bataso amma kuma yau baida wata mafita wacce ta wuce nashan alcohol ɗin,  takaicine yasake cika masa zuciya,   duk waccar shegiyar yarinyarce tasa sa shan alcohol ɗin don haka dole itama sai ya horata, yanzu idan Zahrah tasan yasha alcohol bazata taɓa jin daɗi ba.. Ɗaukar sauran alcohol ɗin yayi yafice zuwa falo, tananan ƙudundune ajikin kujera sai maƙyarƙyata takeyi, matuƙar tsoron Zaid takeyi, ko yanzu dataga fitowarsa saida gabanta yafaɗi..

Direct wajen da take zaune ya nufa,  gashinta yakuma damƙowa haɗe da jawota zuwa tsakiyar falon,  bakinta yakamo da hanunsa ya matse haɗe da tura mata kwalbar giyan acikin bakin nata,  kuka take tana girgiza kanta amma yaƙi sakinta, adole wai saitasha alcohol ɗin, cikin rashin imani irin na Zaid haka ya danne yarinyar mutane ya ɗura mata giya acikinta da ƙarfin tsiya,  sai da yatabbatar ragowan giyan dake cikin kwalbar yajuyemata shi acikinta kafun ya hankaɗata gefe,  ganin yanda take kuka kamar ranta zaifitane,  yasanyasa fashewa da dariyan mugunta,  lokaci guda kuma ya tsume haɗe da kawar da kansa gefe,  miƙewa yayi yafice daga cikin ɗakin, azuciyarsa yace "anjima kaɗan wanka zanmiki da ruwan ƙanƙara dan ubanki....."

(🙆‍♀🙆‍♀🙆‍♀🙆‍♀ Allah yajiƙanki yarinya kinshigo hanun mugu)


  *Wednesday/29/January/2020*


          *Fatymasardauna*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

      
     *SHU'UMIN NAMIJI !!*

  
     *Written By*
Phatymasardauna


*Dedicated To My Brother KHABIER*


*🌈Kainuwa Writers Association*

_{United we stand and succeed; our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}_

*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*

            
            *WATTPAD*
      @fatymasardauna


*Editing is not allowed📵*


      *CHAPTER 102 to 103*


Kuka sosai  Afra keyi, wani irin miji ne haka iyayenta suka aura mata? duk da cewa da amincewa da kuma yardanta akayi mata auren, amma sam bata tsammaci mugunta da shuɗewar hankalin Zaid har yakai haka ba, tun da take arayuwarta bata taɓa kwatanta koda shan codine bane ballantana uwa uba giya,   iskancinta baije can ba, duk da cewa itama tana da  nata wayewar.     Wani irin amai tashiga kwarawa atsakiyar falon,  lokaci ɗaya ta harar da duk wani abu dake cikinta, jingina bayanta tayi da jikin kujera tana me da numfashin wahala..

Zaid da shigowarsa falon kenan, yayi saurin toshe hancinsa haɗe da kawar da kansa gefe cike da bala'i yace
"Ke dan ubanki duk girman gidannan kirasa inda zakiyi amai sai a cikin falon nan?  ki share wajennan yanzu kafun infito kokuwa idan nafito nasamu baki shareba nasa ki lasheshi yakoma inda yafito, ƙazama kawai, wai ahakane zanyi rayuwa dake mcheeww!" cikin ɓacin rai yaƙare maganar haɗe da shigewa cikin ɗakinsa..
Jikin Afra na rawa ta ɗauko moper tashigayin mopping ɗin wajen, ƙaramin aikinsa ne idan har yadawo yasamu bata gyara wajen ba yasata ta lashe aman, tabbas tasan zai iya, yau kaɗai tafuskanci cewa shiɗin tsananin mugu ne, wanda babu kamarsa, tana gama gyara wajen ta gudu cikin ɗakin da aka sauƙeta, ɗakin dake kusa da nasa, tanashiga ɗakin ta murza key, haɗe da faɗawa kan gado, tasaki wani irin kuka,  danasani kawai takeyi acikin ranta,  itafa tayarda ta auri Zaid ne saboda dama tuncan yana matuƙar kasheta aduk sanda tagansa sai taji inama dazai zamo nata, sannan kuma gayen akwai kuɗi uwa uba aji, duk da cewa ita ɗinma babanta me kuɗi ne amma baikai na baban Zaid  dashi kansa Zaid ɗin ba,   lokacin da babanta yazo

Please Login or Register in order to submit comment