Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mata su uku ta gani, tsaye ko wacce ta kafa makeken glass akan idonta, yayinda suke taunar cingam cike da iyawa haɗi da salo......

(Manage please👏 rasuwa akai mana shiyasa banyi posting da wuri ba)

*21/December/2019*

*Follow me on Whatsapp and Wattpad*

*Wattpad user name fatymasardauna*

10:4 pm
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

            *SHU'UMIN NAMIJI !!*

  
      *Written By*
*Phatymasardauna*
_(shalelen kainuwa)_

*Dedicated To My Brother KHABIER*

             *WATTPAD*
       @fatymasardauna

*(Wannan page ɗin gaba ɗayansa kyautane a gareku Members na BENEFICIAL WRITERS ASSOCIATION haƙiƙa kuɗin na daban ne, sannan kuma kuna da ƙoƙari sosai da sosai wajen sanbaɗomana comment, muna godia Allah yabar ƙauna)*

*Editing is not allowed📵*

      *CHAPTER 64 to 65*

Baki da hanci Zahrah ta sake tana kallon waƴan nan ƴan matan  da suke tsaye suna me yimawa cikin gidannasu kallon wulaƙanci haɗe da ƙyama..

Cire glass ɗin dake idanunta Salima tayi, haɗe da watsamawa Zahrah wani irin kallo mai ɗauke da mugun tsana,    cike da ƙyama ta furzar da yawu, haɗe da kallon Laura  "Itace wan nan?" Salima ta tambaya tana me nuna Zahrah da hanunta cike da taƙama.

"Eh itace ƴar matsiyata" Laura ta faɗa tana yanatsina fuska.

"Lafiya kuwa bayin Allah? su waye ku? Zahrah ko kinsan sune?" Inna da fitowarta a ɗaki kenan ta tambaya, Tana me mamakin ganinsu haɗi da aljabi.

"Ba alkhairi bane ya kawomu, saboda baku kai matsayin da zamuzo muku da alkhairi ba,  sunana Salima, nazone domin najawa wannan matsiyaciya kuma karuwar ƴar taku kunne, koda wasa Doctor Sadeeq basa'an  aurenta bane, saboda yawuce ajin macen da taraba mutuncinta a titi"   takawa taci gaba da yi  cikin isa harta ƙarasa gaban Zahrah, da ta kasa ko motsi... "Banzo danna cutar dake ba, amma tabbas idan kika sake nakuma dawowa cikin gidan nan  to zanyi miki babban illa,  rabuwa dashi zai fi miki, idan kuma kika ƙi, hmmmm zakisan cewa bakin rijiya bawajen wasan makaho bane,  bake kaɗaiba, hatta tsohon da yake riƙe dake sai ya ɗanɗana"  Salima tana kai ƙarshen zancen nata tamaida glass ɗin ta dake riƙe a hanunta, haɗe da kallon su Laura "Muje" tace dasu, babu musu kuwa suka rufa mata baya, suna tafiya suna kareraya...

Tamkar statue haka Zahrah tayi ƙasaƙe tana kallonsu, harsuka fice daga cikin gidan.

Sallallami Inna tashiga yi haɗe da tafa hannuwanta duka biyu,  "Lallai kuwa wa ƴan nan ƴan iska masu jajayen fuskar suncika marassa ta'ido, rashin kunya har cikin gida" Inna tafaɗi haka cike da mamaki.

Kai kawai Zahrah ta girgiza, haɗe da jawo kwanon abincinta ta ci gaba da ci,  batare da ta tankawa Inna da take ta ɓaɓatu ba,,  sai dai kuma sosai maganganun Salima suka daki zuciyarta,  har wani ɗaci takeji a cikin maƙoshinta.. Tura abincin takeyi amma jinsa take tamkar maɗacin dayafi kowanne ɗaci,  har wani zafi takeji a ƙirjinta. Tana gama cin abincin, ta kora da ruwa, haɗe da tashi kai tsaye tanufi ɗakinta.

"Karuwa" sunan da Salima taƙirata dashi yafiye mata komai ciwo, tunda take a duniya ba'a taɓa ƙiranta da sunan karuwa ba, sai a yau ɗin, wasu irin zafafan hawayene taji sunshiga gangarowa daga cikin idanunta,  durƙushewa tayi a ƙasa  haɗe da soma rusa kuka,  filla filla kalaman da Salima ta faɗa mata suke dawowa cikin kanta, koda wasa bata taɓa tunanin za'afaɗi kalma na ɓatanci masu muni irin haka akan ta ba.

"Kacuceni Zaid, Kacuceni, me yasa ka aikata haka agareni, shin koda sau ɗaya ne bakayi tunanin yanda rayuwata zata kasance ba,   bazan taɓa yafe maka ba Zaid har kuwa nakoma ga mahaliccina" cikin kuka ta ƙare maganar, domin kuwa sai yau tasake tabbatar da cewa Zaid ya cuceta,  takuma ƙara jin matsanancin zafi dakuma  ciwo akan fyaɗen da Zaid yayi mata.. Abu kamar wasa haka Zahrah tayita kuka tamkar ranta zai fita, sai gashi cikin mintuna ƙalilan ciwon kai yakawomata ziyara, wanda har sai da yakaita ga kwanciya..  Ƙiran Dr.Sadeeq ne yashigo cikin wayarta amma tanaji tana gani takasa picking call ɗin har wayan ta tsinke, taƙi ɗaga wayan ne kuma don bataso yafahimci cewa tana cikin damuwa.   Wani ƙiran nasa ne kuma yasake shigowa, still dai har wayan ta katse, Zahrah bata ɗauka ba, domin har yanzu bata dawo cikin nutsuwarta ba..   Ƙira na uku ne yakuma shigowa cikin wayarta ta,  ƙoƙari tayi wajen ɓoye damuwarta haɗe da ɗaukan wayar ta kara akan kunnenta..

Ajiyar zuciya Dr.Sadeeq yasauƙe sakamakon ji dayayi ta ɗaga wayan.

"Wani irin laifi me girma na'aikata haka da aka ƙi amasa wayata?" Dr.Sadeeq yatambaya.

Cikin sanyin murya Zahrah tace dashi "Bana kusa ne shiyasa"

Wata ajiyar zuciya yakuma sauƙewa  cike da kulawa yace "Naji muryarki ta sauya ina fata dai kina halin lafiya?" cikin kulawa ya ƙare maganar.

"Lafiya ƙalau" tabasa amasa a taƙaice.

"Yakamata nazo muyi magana domin inaso nasan irin shirye shiryen da zakiyi, idan lokacin auren mu ya gabato, kinsan yakamata ace anfarayin komai akan lokaci, yanzu ina tuƙi ne idan na tsaya zanƙiraki"

"To" kawai ta'iya cewa dashi, har ya katse ƙiran.

Tanacire wayar akan kunnenta saƙo yashigo cikin wayar.

"Nakan ji wani iri a jikina idan har kina cikin wani irin yanayi, ki daina sa kanki a damuwa, saboda zaki iya cutar da zuciyarki, nikuma bazan so haka ba, saboda kece muradina"  abun da saƙon yaƙunsa kenan..

Tsuka Zahrah tayi bayan tagama karanta saƙon, haɗe da kashe wayarta ta baki ɗaya,  jira take kawai Allah yakaita gobe taga wayane yake raina mata hankali haka, daga goben kuma zata takamawa komaye birki, domin kuwa ko ma wayene bazai taɓa burgeta ba, zuwa yanzu babu wani ɗa Namiji da zaiyi tasiri acikin zuciyarta.

Zaid ne kwance akan makeken gadonsa wanda yasha bedsheet na alfarma,    kwanciyar nan yayi irin wanda ba kyau, wato rufda ciki,    wata doguwar takarda ne riƙe a hanunsa, wanda take ƙunshe da duk wani abu daya ƙunshi Dr.Sadeeq daga kan sunansa aikinsa har zuwa mazauninsa, dakuma a halinsa, kyakkyawan bincike Zaid yasa a kayi masa akan Doctor ɗin,  saboda a cewarsa babu wanda ya'isa ya shiga huruminsa, saboda Zahrah tasace shi kaɗai, saboda haka dole ne zaitakawa Dr.Sadeeq  birki..

Murmushine ya bayyana akan fuskarsa bayan yasanya duka hanunsa biyu ya shafi sajen dake kwance akan fuskarsa,, shi kansa yaƙosa gobe tayi yaga Zahrah'n sa, duk da kuwa cewa yana biye da duk wani shiga da ficenta, amma  kwata kwata baya gajiyawa da ganinta, sam baisan meke damunsa ba,  zuwa yanzu yafara kokonto dakuma tunani anya ba wannan abun da yakeji shi ake ƙira soyayya ba kuwa? Idan kuwa harda gaske abun nan da yakeji a game da Zahrah shi ake ƙira soyayya, to tabbas yakamu da so matsananci, sai dai kuma bayida ikon tabbatarwa kansa cewa so yake, hakanne ma ya hanasa gane wanni hali yake ciki,  ko da wasa bai taɓa tunanin cewa Zahrah zata ƙisa ba, saboda haka ako da yaushe cikin ƙarawa kansa ƙwarin guiwa yake....

FRIDAY

Rana bata ƙarya,  ranan yau ta kasance Friday kuma yaune Ɓoyayyen mutumin ta yayi mata alƙawarin baiyana kansa gareta,  sai dai kuma baƙon al'amarin da ta wayi gari dashi yasoma tsinkar mata da zuciya, haɗe da sanyayewar jiki, domin kuwa yau ta tashi tana me jin faɗuwar gaba, haɗe da bugawan zuciya da akai akai, hakan kuwa baƙaramin tsoro yajefata ciki ba, saboda bata taɓa mantawa irin wannan faɗuwar gaban ta dinga ji a ranan da mummunar ƙaddaranta zata rusketa,, sai dai kuma babu abun da yagagari Allah, don haka ta shiga yin addu'o'i acikin zuciyarta, saboda ta samu salama..

Ƙarfe Uku na yammaci de de suka fito a lecture'n ƙarshe da suke dashi na wannan ranan,  gaba ɗaya sukuku haka ta wuni a cikin school ɗin,  Husnah tayi tambayan har ta gaji, akan ta faɗa mata meke damunta amma tace ba komai, to me zatace mata? ita kanta batasan meyake damunta ba.

Su Husnah ne suka kawota har ƙofar gida, saboda yanzu Dr.Sadeeq aiki yamasa yawa sosai, ga aikin office ga kuma hidiman hada hadan biki, gaba ɗaya baya samun isashshen lokaci, hakan yasa idan sun tashi a school take shiga motar da ake zuwa ɗaukar Husnah su sauƙeta a gida...

Tun azaure take ta kwaɗa sallama harta shigo cikin gidan nasu, amma babu wanda ya amsa mata, hakan yasa ta tabbatar cewa bakowa acikin gidan,  har ɗaki ta leƙa amma babu Inna babu alamarta, saboda haka kai tsaye ta wuce ɗakinta.   Zama tayi jigum tamkar wacce aka mawa mutuwa, fargaban haɗuwa da ɓoyayyen mutumin nan take, hakanan takeji dama bata nemi ganinsa ba,  saboda gaba ɗaya jikinta yagaya mata babu alkhairi a haɗuwarsu, sai dai kuma babu yanda ta'iya tunda ya tabbatar mata da cewa yau ɗin zaizo, ganin da tayi tunani na shirin damunta,  yasa ta ɗauko alƙur'ani mai girma tasoma karantawa,  saboda hakan yana sauƙar da salama sosai acikin zuciyar wanda yake cikin ƙunci da fargaba....

Tana kai sujjadar ƙarshe ta sallan isha tafashe da wani irin kuka me tsuma zuciya, hakan yafarune kuma saboda ta kasa control ɗin kanta, sosai faɗuwar gaban da takeji yake tsanan ta aduk bayan wasu mintuna.. Cikin kuka tasamu ta sallame sallan isha ɗin,  bayan ta gama faɗawa ALLAH buƙatunta, tana me kuma neman sauƙi a garesa, idanunta da suke cike da hawaye ta ɗaga haɗe da  maida kallon ta ga yagalgalellen agogon bangon dake ɗakin nata, ƙarfe bakwai da arba'in, saura mintunan da basufi Ashirin ba yaƙaraso kenan, domin ƙarfe takwas yace mata zai zo...

Bugawan da agogo yayi 8:00 pm, yayi dai dai da bugawar zuciyar Zahrah, har saida taji cikinta yabada wani sauti. Kallon agogo takumayi akaro na barkatai,  bazata iya tantance me takeji ajikinta ba, tsoro ne kokuma ruɗewa ne, takasa banbancewa.

Idanun Zahrah nakan agogo har ƙarfe takwas da minti biyar, ko ƙyafta idanun ta batayi ba, azahiri agogon take kallo, amma a baɗini ba da idanunta take kallo ba, da ƙwaƙwalwarta take gani,  kallon agogon kawai take amma bata fahimta saboda tunaninta ba a kansa yake ba.

Saƙone yashigo cikin wayarta, wanda yayi dai dai da kusan ɗaukewar numfashinta.

"Inaƙofar gidan ku" bakinta na rawa haka takaranta saƙon saikace wanda aka turomata saƙon ranar mutuwarta.

Takai kusan minti huɗu tana sake maimaita karanta saƙon, sai kace wanda aka yo saƙon da wani harshe bana hausa ba, idan kaga yanda take karanta saƙon zakai tunanin bata iya hausa bane, kokuma bata  gane abun da saƙon yake nufi ba,  bakomai yasa hakan ba kuma face tsoro da taji ya daki zuciyar ta, yayinda gabanta yatsananta faɗuwa, tabbas wannan faɗuwar gaban bana haka kawai bane, lallai dole akwai abun da zai faru da ita,  amma kuma yazama dole taje taga wanda yake turomata saƙonni, hanunta na rawa haka ta ɗau hijib ɗinta ta sanya,  da ƙyar take iya jan ƙafanta ta fita daga ɗakin...
Inna ta iske zaune a tsakar gida, tana jin radio,    "Inada baƙo a waje Inna" Zahrah tafaɗa cikin wata irin murya me rauni. Yanayin yanda Inna taji muryan Zahrah yasanya ta ɗago da kanta ta kalle ta,     "Lafiyanki kuwa, meke damunki?" Inna tatambaya cike da mamakin yanda taga jikin Zahrah  a sanyaye.

"Babu komai Inna" Zahrah tafaɗi haka tana me nufar hanyar ƙofar fita daga gidan..

Kasancewar akwai wadataccen haske a ƙofar gidan nasu na ƙoyayen wuta wanda maƙotansu suka kukkuna hakan yasa wajen baida duhu, zaka iya hango duk wanda ke tsaye dakuma wanda ke tsugunne, kai harma wanda ke kwance zaka iya ganinsa. 

Bugun zuciyarta ne yaƙaru yayinda ƙafofinta suka soma yi mata nauyi, wani mutumi tagani tsaye ajikin wata mota da ta amsa sunanta mota, sai dai kuma yajuya baya, saboda haka bayansa kawai take iya hangowa, sanye yake da wandon jeans black dakuma black ɗin riga sannan kuma akwai hula irin fosin kaf ɗin nan akansa.  A hankali take taka ƙafafunta dasuka mata nauyi tanufi inda yake tsaye,  yayinda ta sanya hanunta ta cikin hijab ɗinta ta dafe ƙirjinta da takejinsa kamar zai daka tsalle yafito waje..

Abu na farko daya fara hargitsa mata ƙwakwalwa bayan ta isa gareshi shine fitinannen ƙamshin turarensa wanda har gaban abada bazata taɓa manta wan nan ƙamshin ba,   wani irin killer smile Zaid yayi bayan yatabbatar da cewa ta karaso gab dashi,  fuskarsa ɗauke da murmushi ya juyo zuwa gareta, haɗe da sanya hanunsa ya cire hular dake kansa, take kyakkyawar fuskarsa ta bayyana, wacce take ɗauke da murmushi.

Jikinta ne yaɗauki rawa yayinda idanunta suka ƙara buɗewa take numfashinta yasoma ƙoƙarin ƙwacewa, zuciyarta tashiga duka, ƙafafunta suka ƙage waje ɗaya, yayinda hawaye suka dinga fitowa daga idanunta tamkar anyi ambaliyan su.
Kallon yanda jikinta yake rawa Zaid yayi haɗe da dawo da kallonsa kan fuskarta jefa idanunsa  yayi cikin nata.    "ZAHRAH!" yaƙira sunanta da wata irin murya me sanyi,  sakamakon ganin da yayi  kamar cewa bata cikin hayyacinta...

"ZAHRAH" yasake ƙiran sunanta, de de lokacin ne kuma numfashin ta yashiga gudu yana neman ƙwace mata, aikuwa kasa fusgo numfashin nata tayi, lokaci ɗaya numfashinta yayi nasaran fita daga jikinta,  take ta yanki jiki tafaɗi warwas a ƙasa, cikin mugun tashin hankali Zaid yayi kanta, haɗe da sanya hannayensa duka biyu ya ɗagota zuwa jikinsa,   sunanta yashiga ƙira cikin tashin hankali dakuma ruɗewa,  a matuƙar firgice ya sanyata acikin motarsa haɗe da shiga cikin motar da wani irin gudun gaske Zaid yafigi motar ya cillata kan titi...  Gaba ɗaya ya ruɗe wani irin gudu yake shararawa baburuwansa da wanda ke gabansa ko bayansa, gaba ɗaya ya ruɗe sunan Zahrah kawai yake ambata,  Allah yasa ba zuciyarta ta haɗiya ba..

Matsanancin gudun da Zaid yakeyi har ya wuce hankali,  da wani irin gudu yashigo cikin asibitin yayin da ya ɗauko Zahrah caɗak a hanunsa tamkar wata ƴar tsana, haka yashigo da'ita cikin asibitin, ganin haka yasa Doctors sukayo kansa da sauri,  hankalinsa a matuƙar tashe ya miƙa ta ga doctors sukayi emergency da'ita kai tsaye.. Taimakon gaggawa likitoci suka shiga bawa Zahrah domin kuwa bako maine ya haifar mata da ɗaukewar numfashin ba, face razana dakuma tsananin firgita haɗi da tsoro da suka rusketa alokaci guda, sannan yanayin yanda zuciyarta ke bugawa, yawuce mizani, idan har zuciyar tata tacigaba da bugawa da sauri sauri haka, tofa lalllai rayuwar Zahrah tana cikin haɗari...

(Niko nace idan Zaid yakashe mana Zahrah zamuci .... ko  fans😂)

Iya ruɗewa Zaid ya ruɗe yakasa koda zamane, damuwarsa ɗaya shine Doctors ɗin da suke kan Zahrah, su sanar dashi meke faruwa, lallai idan har Zahrah tasamu wani matsala, to bazai taɓa yafewa kansa ba, sannan kuma babu uban da ya'isa yazauna lafiya, matuƙar likitocin nan suka kasa shawo kan matsalan Zahrah..

Kusan minti talatin likitocin nan sukayi suna ƙoƙarin shawo kan numfashin Zahrah, cikin ikon Allah kuwa sun samu komai yayi dai dai sai dai dole tana buƙatar hutu kodan zuciyarta ta samu salama...

Suna fitowa Zaid yayi kansu, gaba ɗaya idanunsa sun kaɗa sunyi jajur dasu.

Kallonsa ɗaya daga cikin manyan  likitocin dasuke kan Zahrah yayi haɗe da dafa kafaɗunsa,  "Ka kwantar da hankalinka, komai yayi dai dai, yanzu biyoni office ɗina"

Ba musu balle girman kai Zaid ya bi bayan liikitan.

Kasa zama akan kujeran da Dr ɗin yabasa yayi,  babban damuwarsa shine yasan wani hali Zahrah take ciki.

"Nace ka kwantar da hankalinka, kazauna saimuyi magana ko" likitan yafaɗa yana me nuna masa kujera..

"Kaga Doctor bazamane yadameni ba, babban damuwana  shine nasan wani hali take ciki" Zaid yafaɗi haka cikin damuwa..

"Zan faɗama ko wani hali take ciki, amma dole sai ka zauna"

Badon Zaid yasoba haka yazauna akan kujera haɗe da sanya duka hanunsa ya dafe kansa.

"Bawani babban abubane yake damunta, akwai abun da yafirgita ta ne, kuma dama anasamun irin haka, sau da dama firgici da tsoro, yakansa mutum yasamu ɗaukewar numfashi naɗan wasu daƙiƙu, amma idan tadawo hayyacinta komai zaidawo dai dai, sai dai kuma tana buƙatar hutu sosai, saboda haka bayau zaku samu sallama ba, dole sai kunjira zuwa gobe da safe, saboda yanzu haka akwai alluran damuka mata kuma suna sa bacci sosai" 

Ajiyar zuciya me ƙarfi Zaid ya sauƙe, saboda jin bayanan Doctor da yayi, sun sauƙar masa da nutsuwa    "Amma dole sai anan zamu kwana? me zai hana kabani ita mutafi gida, idan yaso saitayi baccinta acan" Zaid yafaɗi haka fuskarsa ɗauke da damuwa.

Murmushi Doctor yayi haɗe da cewa "Hakan bazai samu ba, saboda zata iya farkawa da kowani lokaci, bamu kuma san a wani hali zata tsinci kanta ba, bayan ta farka, saboda haka zamanku anan ɗin zaifi amfani" Doctor yafaɗi haka cike dason gamsar da Zaid.

Kai kawai Zaid yajinjina haɗe da kallon Doctor  "Zan'iya ganinta kuwa? sannan kuma inaso akaita ɗaki na musamman konawane kuɗin ɗakin zan biya"

"Wannan ba'abun damuwa bane, zamu kaita ɗaki na musamman sannan kuma zaka iya ganinta,  bana ƙira nurse sai a sanja mata ɗaki daganan saikaje ka ganta ko" Dr yafaɗi haka bayan yakara waya akan kunnensa.  Cikin mintuna ƙalilan aka sanjawa Zahrah ɗaki inda aka kaita ɗaki na musamman. 

Zaid ne tsaye akanta yana me ƙare mata kallo, karo na farko kenan daya farajin wani irin matsanancin tausayin ta acikin zuciyarsa, haɗe da wani shauƙi mai fisgar zuciya.  A hankali yaƙaraso dab da gadon nataz haɗe da ranƙwafo da kansa dakuma ƙirjinsa zuwa gaf da'ita, lumshe idanunsa yayi haɗi da kai bakinsa gefen kumatunta ya yi mata kiss, haɗe da sa hanu yashafi gefen fuskarta,  "I'm sorry Zahrah!" yafaɗi haka acikin maƙoshinsa. Karo na farko kenan a rayuwarsa daya soma bawa wata mace haƙuri..  Zama yayi a  bakin gadon, haɗe da kama hanunta na dama yasanya acikin nasa hanun, a hankali yake murza hanunta haɗe da lumshe idanunsa.

Abu kamar wasa hankalin Inna ne yasoma tashi ganin Zahrah ta kwashe sama da awa ɗaya, a waje batare da ta shigo gida ba, gashi ta leƙa waje bataga ko da me kamannin Zahrah bane, kasa zama inna tayi gaba ɗaya hankalinta a tashe yake,  Baffa ne yashigo cikin gidan bakinsa ɗauke da sallama,  ko amsa sallaman nasa Inna batayi ba tayo kansa tana cewa "Yau wa Malam gwamma da ka dawo, ko ka haɗu da Zahrah a waje kuwa?"

"Zahrah kuma, ina Zahrah'n take?" Baffa yatambaya cike da mamaki.

Nan Inna tashaida masa cewa tunɗazu tafita bata dawo ba,bayan tasanar mata cewa wani ne yaƙira ta a waje.

Take hankalin  Baffa yatashi, domin kuwa Zahrah bata taɓa irin haka ba,  har maƙota ya aika ko taje amma aka ce masa bata zoba, take Baffa da Inna suka zuba tagumi, sun marasa ta ina zasu fara,  Inna cema takawo shawara akan cewa aƙira Doctor Sadeeq koshine yazo ya ɗauketa, aikuwa Baffa yayi na'am take  yadannawa number'n Dr.Sadeeq ƙira, bugu biyu Dr.Sadeeq yaɗaga wayan,, shima bakaɗan ba hankalinsa yatashi jin dayayi cewa wai su Baffa basuga Zahrah ba, ae take yashiga motarsa yataho gidansu Zahrah'n duk da cewa dare yayi...

Kallon agogon hanunsa Zaid yayi a karo na barkatai, ƙarfe 10 na dare kenan,  ajiyar zuciya ya sauƙe akaro na uku, haɗe da furzar da iska a bakinsa,  kallonsa yakuma mayarwa ga Zahrah, wacce take ta sharan bacci,  hakanan yatsinci kansa da sakin murmushi mai sauti,  komai na Zahrah me kyaune, tafiyin kyau ma idan tana bacci.
Zama yayi akan wata kujera dake kusa da gadon haɗe da jingina bayansa da jikin bango, lumshe idanunsa yayi tare da cije laɓɓansa sai yanzu ƴake tunanin ya makomarsa zai kasance idan Zahrah tafarfaɗo, domin kuwa ya hango muguwar tsanarsa acikin idanunta.

*23/December/2019*

*Follow me on Whatsapp and Wattpad*

*Wattpad user name fatymasardauna*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

            *SHU'UMIN NAMIJI!!*

        *Written By*
  *Phatymasardauna*

*Dedicated To My Brother KHABIER*

*🌈Kainuwa Writers Association*

{United we stand and succeed; our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}

*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*

          *WATTPAD*
    @fatymasardauna

*Editing is not allowed📵*

   *CHAPTER 66 to 67*

Lokaci ɗaya hankalin Dr.Sadeeq yayi wani irin mummunan tashi, take ƙwaƙwalwar kansa tashiga charge, a iya tsawon sanin da ya yi mawa Zahrah, ita ba mace bace meson fitar dare, balle har tayi nisa da gida, sai dai kuma abun mamaki gashi yau annemeta an rasa, bayan ko ɗazu  suna tare a waya shida ita, baikuma ji wani sauyi a tattare da'ita ba, sai dai kawai muryarta da yaji cikin sanyi.  "To ina Zahrah taje?"
Yayi mawa kansa tambayar da bayi da amsa.. "Kodai Zahrah tayi hakane don batason aurena da'ita?" yakuma tambayar kansa, sai da zuciyarsa ta buga, shi kansa yatambayi kansa abun daya faɗar masa da gaba,  kai amma Zahrah bazatayi haka ba, saboda ita da kanta ta tabbatar masa cewa ta amince da auren sa, saboda haka bazata bar gida saboda batason auren sa ba..
Kallonsa yamaida ga Inna wacce tayi tsuru tsuru da ido tamkar wata munafuka..."Da tazo fita bakiga wani alaman damuwa ko tashin hankali akan fuskarta ba?" Dr yatambaya cike da kulawa.

"Ƙwarai kuwa da damuwa tafita, saboda kwana biyun nan gaba ɗaya   da damuwa take wuni sakamakon waƴansu tsinannun ƴan mata da suka zo, acewar ɗaya daga cikin su wai ita zaka aura Samira take ko Salma oho, haka nan suka zo hargida suka zagemu kaf, tamkar ma zasu mana luguden duka, to tundaga tafiyarsu dai take fama da ƙuncin rai har kawo yau, Allah dai yasa ma basune sukai mata wani abun ba" Inna tafaɗi haka cike da jimami..

Cike da mamaki Dr.Sadeeq yace "What Salima tazo har gidan nan taci muku mutunci?"

"Ƙwarai kuwa ashe dagaske kasanta, tabbas haka tace sunanta wai Salima, ita da waƴansu masu ƙoƙaƙƙun fuska, kamar an gasa nama"

Hanu Dr.Sadeeq yasanya yadafe kansa, lallai idan de har Salima bata ji kunyar zuwa ta zagar masa abar sonsa ba, to tabbas shima bazaiji kunyar zuwa har gidansu  yaci mata mutumci ba,  Uwa mahaifiyarsa kaɗai ze iya ɗagawa ƙafa akan Zahrah, amma duk wacce tace zata ci mutumcin Zahrah tofa shima zaici nata mutuncin, lallai yakamata ne yafara nemo inda Zahrah take  kafun yasan matakin da zai ɗauka akan Salima. Sake dialing number'n Zahrah yayi amma still ce masa  ake wai wayar akashe take, tun ɗazu yake ƙiran wayar anacemasa akashe wayarta ta take.. Tunanin ƙiran abokinsa inspector Adam ne ya faɗo masa, saboda yalura lamarin dole sai anshigo da hukuma ciki, tunkan suyi sake lokaci ya ƙure musu. Nan yashiga dialing Number'n inspector Adam amma har wayar ta katse bai ɗauka ba, sake ƙira yayi amma still bai ɗauki wayar ba, tsuka Dr.Sadeeq yayi haɗe da maida wayarsa cikin aljihunsa....

Asibiti

Sai yanzu tunanin halin da iyayen Zahrah zasu shiga yafaɗo masa arai,  tabbas yakamata ne yasanar dasu halin da ake ciki,  wayarsa yaɗauka haɗe da soma rubuta saƙo, domin bayason wayar da zaiyi yatashi Zahrah a baccin da takeyi, saboda haka gwamma yatura saƙo,a ganinsa hakan zaifi... wata number yaturawa saƙon, batare da yajira amsar da wanda yaturawa saƙon zai basa ba, ya maida wayarsa cikin  aljihu.....

Dr.Sadeq ne yadubi Baffa dake a halin damuwa. "Banaje nasanarmawa ƴan sanda, akwai abokina inspector, inaga kawai gwamma naje gidansa na sanar dashi abunda ke faruwa, ina ga zaifi akan tsayuwan damuke" yafaɗi maganar yana me duba  agogon dake ɗaure a tsintsiyar hanunsa, ƙarfe sha ɗaya na dare kenan agogon sa yanuna masa..

Sallaman da sukaji ana kwaɗawa a ƙofar gidan ne yaɗauki hankalinsu, ae ba shiri Baffa da Dr. Sadeeq suka ɗunguma zuwa ƙofar gidan, Inna ma ba'a barta a baya ba ta rufa musu baya.

Wani mutumi me shigar cute baƙaƙe suka gani tsaye a bakin ƙofar gidan, yayinda yarufe idanunsa da tabarau, da ganinsa dai zaka gane irin body guard ɗin nan ne.

"Waye kai?" Dr.Sadeeq yatambaya yana me ƙaremasa kallo.

"Saƙo aka bani  nasanar daku cewa Zahrah bata da lafiya, yanzu haka tana asibiti.." baikai ga idar da zancen nasa ba, Dr.Sadeeq yace "Meyasameta sannan kuma a wani asibiti take?" duka tambayar yayisune alokaci ɗaya, kuma
cikin ruɗewa..

"Zaku iya biyoni muje" Body guard ɗin nan yafaɗa yana me nufar wajen da motar da yazo da ita ke fake.
Kallon su Baffa Dr.Sadeeq yayi haɗe da cewa su shigo motarsa subi bayan body guard ɗin, hakan kuwa akayi  motar Dr.suka shiga yayinda Dr.yashiga bin bayan motar body guard ɗin. Gaba ɗaya ba acikin nutsuwarsa yake driving ɗin ba. Fargabane cike a zuciyarsa, bayi da wani buri da yawuce yaga Zahrah, yakuma ji meke damunta, har aka kawota asibiti batare da sanin su Baffa ba..
Suna shiga cikin asbitin wannan body guard ɗin  ya kalli  Dr.Sadeeq haɗe da cewa ya biyosa ciki, su Inna kuwa su jirasa,  da su Inna sunso ƙi, amma sai Dr. Sadeeq yace su yarda su jirasu anan ɗin, badon su Inna sun so ba, suka tsaya daga waje... Suna shiga cikin wani corridor  guard ɗin yaciro wayarsa, haɗe da karawa akan kunnensa.

"Oga

Please Login or Register in order to submit comment