Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sai dai kuma bakamar wanda yakeji  yanzu ba, jiya bakaɗan ba ya'iya daure zuciyarsa, amma daba haka ba tabbas da baisan wani irin aika aika zaiyi mata ba,   a hankali yaji idanunsa sun soma rufewa da'alama dai shima bacci bai ishesa ba, ae dole ma jiya sunsha gajiya sosai,, cikin mintuna ƙalilan bacci ya ɗauki ma'auratan biyu,  yayinda kowanne daga cikinsu da irin samfurin tunanin dake cikin zuciyarsa.... 
***

10:00 am dai-dai ta buɗe idanunta, haɗe da waresu akan haɗaɗɗen zanen POP'n da ya cika  saman ɗakin,   kallonta ta mayar ga inda take tsammanin ganinsa, amma sai dai taga wajen wayam babu shi babu alamarsa.  Da sauri ta tashi zaune haɗe da maida kallonta  ga wani ɗan madaidaicin agogon bangon dake saƙale jikin ginin ɗakin.

"ƙarfe 10 nakai ina bacci?"

ta tambayi kanta cikin yanayi naɗan mamaki..  A hankali tazuro ƙafafunta ƙasa, haɗe da miƙewa tsaye, ɗakalallen cikinta daya soma mata kukan yunwa ta shafa, haɗi da ɗan yamutsa fuskarta, direct  ƙofar bathromm ta nufa, ɗan tsayawa tayi ta kasa kunnenta ajikin ƙofar, koda zataji ƙaran ruwa, amma saitaji shiru da'alama dai bakowa acikin bathroom ɗin, murɗa handle ɗin ƙofar tayi tashige ciki,, ruwan wanka ta haɗa yayinda ta cika turaren ƙamshi acikin ruwan,    wankanta tayi cike da nutsuwa...  Sanye da wani  ɗan madaidaicin towel pink colour ajikinta tafito daga cikin bathroom ɗin, hatta gashin kanta ajiƙe yaƙe, still ƙaramin towel ne kuma riƙe ahanunta tana goge gashin kanta dayake ajiƙe,,  daidai lokacin Dr.Sadeeq yaturo ƙofar ahankali yashigo, suman tsaye yayi ajikin ƙofar yana me ƙare mata kallo daga sama har ƙasanta, yayinda ita kuwa batasan ma da zuwansa ba, kanta kawai take aikin gogewa, saboda bataji motsin buɗewar ƙofar ba, shikuwa dama yabuɗe ƙofar ne ahankali gudun kada ya tasheta a baccin daya barta tanayi,,   wani yawu ya haɗiye, haɗe da jan ƙafansa a hankali yafice daga cikin ɗakin batare daya bari ta ganshi ba,, yana fita yajingina bayansa da ƙofar haɗe da sauƙe wani irin ƙaton ajiyar zuciya,, lumshe idanunsa yayi haɗe da sanya hanunsa acikin tulin sumar kansa yashiga shafawa a hankali,, ashe haɗuwar Zahrah yawuce yanda yake zato yake kuma tunani, wannan wace irin haɗaɗɗiyar surace Zahrah'n sa ta mallaka,, lallai Zahrah mace ce cikakkiya tagaban kwatance,, da ƙyar ya'iya jan ƙafansa ya koma cikin falo, kwanciya yayi akan kujera haɗe da lumshe idanunsa da suka sauya launi lokaci guda...

Zahrah kuwa tana gama goge gashin nata tayi amfani da  hand dryer  wajen busar dashi mintuna kaɗan gashin yabushe tashafa masa mai,,,  wani lotion me ƙamshi ta shafa ajikinta haɗe da murzawa fuskarta hoda da kuma kwalli, light pink lipstick tagoga akan leɓenta, take fuskarta ta tasake yin kyau,,  gaban  makeken drower'n dake kafe ajikin bangon ɗakin taƙarasa haɗe da buɗewa, kayane jere reras acikin drower'n kala kala sai wanda ranka yaso zaka saka, wata jar atamfa taciro wacce taji ɗinkin pencil gown,, tana sanya doguwar rigan yayi mata kyau haɗe dayi mata ɗas ajikinta,  daga kan guiwanta harzuwa ƙafarta atsage yake ta bayan rigan,   tanason atamfar sosai saboda tana ɗaya daga cikin kayan da  Maman Husnah ta bata, Husnah ce kuma takai akayi mata irin wannan ɗinkin duk da kuwa irin tsadar da atamfar take dashi, kallon kanta tayi acikin madubi, murmushi tasakarwa kanta saboda ita kanta ta yaba da yanda rigan tayi mata kyau ajiki,  wani ɗan madaidaicin vail me kalan ja ta ɗauka haɗe da rufe jikinta, duk da kuwa cewa kayan yana da ɗan kwali, sai dai bazata iya tafiya daga ita sai wannan rigan agaban Doctor ba saboda sosai hips ɗinta suka bayyana, ga shi breast ɗinta sun bayyana kansu ta saman rigar kasancewar wuyan rigan yana da ɗan faɗi. Da turaruka masu daɗi ta feshe jikinta... A hankali ta buɗe murfin ƙofar ɗakin tafito,  ɗan tsayawa tayi tana kallonsa,, kwance yake akan kujera yayinda idanunsa ke a lumshe,  yasha adonsa cikin wata bugaggiyar shadda blue colour.  Murmushi tayi domin kuwa yayi mata kyau, sosai kuma hasken fatarsa yasake bayyana acikin blue ɗin kayan. A hankali tashiga takawa har zuwa tsakiyar falon,  ƙarewa falon kallo tashiga yi, ita dai  haryanzu bata gamsu da cewa wai nan ɗin falon ta bane,  koda wasa ma bata taɓa tunanin zata shiga cikin daula irin wannan ba,, bata ankara ba saiji tayi anriƙe mata hanu, da dauri ta juyo don batayi zaton idonsa biyu ba,, Murmushi yasakar mata haɗe da cewa,

"yaushe kika tashi?" yayi tambayar kamar bashi yaganta ɗazu ba..

Zama tayi akan kujera haɗe da cewa " banjima da tashi ba"

Tashi yayi daga kan kujeran haɗe da kama hanunta, kaitsaye haɗaɗɗen darny area'n dake cikin falon yanufa da'ita,  jawo kujera ɗaya yayi daga cikin kujeru huɗu dasuka ke waye wani babban table,   zaunar da'ita yayi haɗe da buɗe wani babban food flask, plate ya ɗauka yazu ba mata soyayyen dankalin turawa'n dake cikin kulan (Chips)   wata food flask ɗin yasake jawowa pepper chicken ne dayasha albasa, shima zuba mata yayi haɗe da haɗa tea acikin wani  cup, turo mata duka plates ɗin dakuma cup ɗin tea ɗin yayi gabanta,, saurin ɗago kanta tayi ta kallesa,  kansa ya jinjina mata alamar koma me take tunani hakane,   take ta shagwaɓe fuska haɗe da cewa "Bazan iya cinye duka wannan abincin ba yamin yawa"

"Bakomai kici sosai, nasan kinajin yunwa" yafaɗi haka yana me ƙoƙarin barin wajen.

"Kai kuma fa?" batare da ta shiryawa fitowar tambayarba, saikuma bakinta yayi saurinfurtawa,,  tsayawa yayi da tafiyar haɗe da juyowa, murmushi yayi mata haɗe da cewa "Ni bayanzu zanci ba"   harya fice daga cikin falon bata ɗauke idanunta  daga kansa ba,,  ajiyar zuciya ta sauƙe haɗe da ɗaukan fork tasoma cakan chips ɗin tana kaiwa bakinta,  dama yunwa takeji sosai,,    sosai taci chips ɗin saidai tea ɗin sama sama tasha shi, naman kuwa ko taɓa shi batayi ba, domin ita gaba ɗaya naman kaza baiwani dameta ba, tafison gasashshen naman sa, fiye da na kaza, sai da taji cikinta yayi haniƙan kafun ta kimtsa wajen haɗe da miƙewa takoma cikin falon,,  haryanzu dai idanunta basu ƙoshi da ƙarewa falon kallo ba, rayuwa kenan wai yau ita Zahrah ce zaune acikin wannan katafaren gida dasunan gidan aurenta, ita da ko gado bata dashi akan zallan  ƴar katifa take kwana sai gata yau ta kwana akan haɗaɗɗen gado harda lallausan bargo da ta rufa dashi,,   a hankali ya turo ƙofar falon yashigo, wayarsace riƙe a hanunsa yana latsawa,,  gaf da'ita ya zauna har kafaɗunsu suna gogan na juna,  hanunsa ya sanya ya shafi ɗa kalallen cikinta,  "Wannan ɗan ƙaramin cikin baiƙoshi ba"

Murmushi tayi masa haɗe da waro idanunta   "Dan Allah kayi haƙuri wallahi na ƙoshi" tafaɗi haka tana me ɗauke hanunsa daga kan cikinta..    Kallonta yashigayi  yana me karantar yanayinta yayinda ita kuma tayi ƙasa da kanta, batason haɗa idanu dashi kwata kwata,   "taso muje" yafaɗi haka yana me miƙewa tsaye, babu musu ta miƙe, hanunta ya kama suka nufi wata ƙofa dake cikin falon, key ya sanya ajikin ƙofar ya murɗa,  tura ƙofar ɗakin yayi, still hanunta na riƙe acikin nasa hanun suka kutsa cikin falo'n, falone ma dai-dai ci wanda aka kewaye tsakiyansa, da wasu kujeru dark purple masu kyau, yayinda tsakiyar falon kuwa aka cike sa da wani ɗan madaidaicin chanies carpet dark and light purple colour,  wasu labulaye masu kyau kalan light purpule su suka ƙawata jikin ƙofa dakuma windown falon,  wani ɗan ƙaramin plasma ne  maƙale ajikin bangon falon, su kenan iya abun dake cikin falon amma kuma duk da haka falon yayi kyau, kasancewar kalan kujeru da labulayen kalane me ɗaukar hankali, ga kujerun sunsha pillow ƴan ma dai-dai ta gwanin ban sha'awa,   yana riƙe da hanunta suka kuma shiga cikin wani ɗaki dake cikin falon,,  gadone me kyau irin na zamani da drower'nsa me ɗauke da murafe shida, sai kuma su dressing mirror dakuma abun aje takalma da jaka,,  kayan furnitures ɗin bawasu masu tsada bane daga kujerun har gadon bazasu wuce dubu ɗari huɗu ba, amma kuma anyi kayan da kyau da kuma inganci,,  kallon  sa Zahrah tayi alamar tanason ƙarin bayani,, murmushi yasakar mata haɗe da sa hanu ya shafa kumatunta, yace da'ita
"Kayan ɗakin da  Baffa yayi miki ne"  

Daɗi da farinciki ne suka cika zuciyar Zahrah take tacigaba da wurga idanunta tana kallon kayan, Allah sarki Baffa ashe haka yayi mata ƙoƙari batasani ba, lallai Baffa yafaranta ranta sosai, bata taɓa tunanin zata samu kaya haka ba, ashe dai Baffa yanasonta yana kuma ƙaunar fitar da'ita kunya, lallai wannan kaya sunfiye mata komai, saboda koba komai zata tsallakewa gorin wasu mutanen,  wani irin tausayin Baffan nata ne taji ya sake ɗarsuwa aranta,, duk da cewa shiba mawadaci bane amma yayi ƙoƙari ya wadata ta da kayan ɗaki masu kyau dai dai da me rufin asiri,  babu abun da zatace da baffanta sai godiya,, kan gadon taje ta zauna tana murmushin jin daɗi, sai taji tafi ƙaunar ɗakin ma fiye da wanda aka kaita daga farko, duk daɗin kyauta dai baikai ace da kuɗinka kacire ka saya ba.

"Yanaga kin wani zauna madam? taso muje nunamiki kawai nayi, bawai nace anan zaki zauna ba" Dr.Sadeeq yafaɗi haka yana me miƙa mata hanunsa alamar takama sutafi,,

Shagwaɓe fuska Zahrah tayi haɗe da kwantar dakanta gefe

"Nidai nafison nan please kabarni anan!" taƙare maganar cike da zallan shagwaɓa..

Takowa yayi yazo gaf da'ita haɗe da sanya hanunsa ya ɗago kafaɗunta.

"Nan ɗakin hutawan kine, can kuma ɗakin aurenki ne ɗakin dana zaɓa mana ni dake domin muyi rayuwar auren mu, kodai baki yaba da zaɓin nawa bane? kokuma baki amshi kyautar danayi miki bane?" 

Ɗara ɗaran idanunta ta ɗago ta sauƙesu akan nasa idanun,  kanta ta girgiza cikin sanyin murya tace " Ba haka nake nufi ba, kuma nayarda da duk inda kazaɓamin zanyi rayuwa aciki, kayi haƙuri idan maganata ta ɓata maka rai ban....."

"Shiiiiii" ya katseta ta hanyar ɗaura  hanunsa akan laɓɓanta,  jawota jikinsa yayi , haɗe da sanya yatsarsa yashiga zagaye ɗan ƙaramin bakinta,,  ƙasa tayi da'idanunta domin kuwa bazata iya jure kallon cikin idanunsa ba,  sake matso da fuskarsa yayi daf da tata har numfashinsu na'iya gauraya waje guda, yayinda dogon hancinsa ke gogan nata hancin,  atare suka lumshe idanunsu,   ahankali laɓɓansa suka sauƙa akan nata laɓɓan, baikai ga soma yin kissing ɗinta ba ƙaran wayarsa ta karaɗe cikin kunnuwansu, da sauri ya sake ta,haɗe da sanya hanu acikin aljihunsa ya ciro wayarsa dake ta faman ƙara, katse ƙiran yayi haɗe da kashe wayar baki ɗayanta ya kuma maidata cikin aljihun rigansa.

Hannayenta dake cikin nasa hanun ya murza haɗe da ɗanyin ƙasa da murya   "Kibani aron 1 hour inaso in ɗan fita"

Batasan lokacin da ta ɗago kanta ta kallesa ba,  mamaki ya bata wai ta basa aron 1 hour shida ƙafarsa ae bazata ɗaure saba, 

Baijirayi abun da zatace ba yakama hanunta suka fice daga cikin ɗakin, direct asalin falonsu suka dawo,  matsawa kusa da'ita yayi ya manna mata kiss akan goshinta, haɗe da cewa "Sainadawo" adawo lapia tayi masa cike da kunyar sunbatar da yayi mata agoshinta,, tanajin tashin motarsa ta sauƙe ajiyar zuciya haɗe da zama akan kujera tamaida hankalinta ga tv, a zuciyarta kuwa hamdala take da Allah yasa bai sumbaceta ɗazu ba,  itakam matuƙar kunyarsa takeji, sosai yakeyi mata kwarjini acikin idanunta.....
***

*GERMANY*

Tunda suka iso cikin ƙasar suka kuma sauƙa ababban asibitin dake cikin birnin Germany ɗin Zaid bai buɗe idanunsa ba, duk da kuwa irin kulawan da ƙwararrun likitotin asibiti'n suka basa,   bawai baya cikin hayyacinsa bane,  sarai yana a cikin hayyacinsa, ƙunci da kuma tarin damuwa me tsanani ne suka hanasa buɗe idanunsa,  baison ya buɗe idanunsa kunnuwansa su jiye masa labarin cewa anɗaura auren Zahrah, baya buƙatar yin tozali da fuskar kowa acikin duniyar nan idan ba fuskar Zahrah ba,, yagama yarda da hukuncin da zuciyarsa ta yanke masa, lallai kwanciyarsa haka baida wani amfani, yakamata ne yatashi yayi yaƙi don samo soyayyar Zahrah,  idan har bai manta da date ɗin daya gani ajikin katin auren ba, to jiya ne ɗaurin aurenta,  wasu irin hawaye masu zafin gaske ne suka silalo daga cikin idanunsa haɗe da gangarowa tagefen kumatunsa,, a hankali ya ware idanunsa da suka jima da rikiɗewa suka zama jajur dasu,  baya tunanin zaisake samun farinciki acikin rayuwarsa matuƙar yarasa abar ƙaunarsa Zahrah,  tashi yayi zaune haɗe da rumtse idanunsa, ƙuna yakeji acikin ƙirjinsa sai dai kuma zafin wannan ƙunan baikai zafin ƙunan da soyayyar Zahrah keyi masa azuciyarsa ba,,,  Alhaji Ma'aruf dake tsaye a wajen ɗakin da Zaid ɗin ke kwance, ta cikin makeken    glass ɗin daya zamewa ɗakin window ya hango  Zaid ya tashi zaune, da sauri yaje ya ƙira Doctor domin kuwa tunda suka zo Zaid ɗin bai motsaba sai yanzu,,  ƙa'idansu ne idan zasu duba marar lafiya babu wani me shiga kansu harsai   sun ga babu wani matsala sannan zasu bar ƴan uwansa suje kansa,,  hakan yasa dole Alhaji Ma'aruf ya dakata daga waje likitan shi kaɗai ya shiga..    Bayan kamar wasu mintuna likitan yafito yabawa Alhaji Ma'aruf daman ganin Zaid ɗin, ae ba'iya Alhaji Ma'aruf kaɗai ba hadda Mum suka rankaya zuwa cikin ɗakin,,  har gabansa dukansu suka ƙarasa, hanu Alhaji Ma'aruf ya ɗaura akan kafaɗan Zaid haɗe da cewa "Ya ƙarfin jikin naka?"

Bai amsa musu ba saima kallonsu daya shiga yi kamar wani wawa... 

  "Ina Zahrah?"  shine abun daya iya fitowa daga cikin bakinsa kawai, saboda shine abun dake cikin zuciyarsa..

Kallon Kallo Alhaji Ma'aruf da Mum suka shiga yiwa juna, sukam dai basuda wani amsa da za su bashi domin kuwa sarai labarin Auren Zahrah ya isa ga kunnensu,  yanzu haka itaɗin matar wani ce, babu amfanin  ɗago zancenta...

Alhaji Ma'aruf ne yayi ta maza haɗe da sauƙe ajiyar zuciya  cike da lallashi  yakuma dafa kafaɗun ɗan nasa        " Yanzu ba lokacin damuwa bane Zaid, bakuma lokacin daza ka sa kanka acikin ƙunci bane,  kabar maganan Zahrah, yanzu samun lafiyarka yafi komai a wajen mu, idan kasamu lafiya sai ayi abun daya dace amma maganar Zahrah abarshi" Alhaji Ma'aruf yaƙare maganar cikin kwantar da murya.  

Laɓɓansa ya cije haɗe da girgiza kansa
" Bazan taɓa samun nutsuwa da salama ba  Dad har sai Zahrah tazamo tawa,  Inasonta Dad,  so ba irin na wasa ba,  samunta ayanzu yafiyemin komai, taɓa kaji Dad, zuciyata takusa bugawa akan soyayyarta, ba irin bugawan da kasani ba Dad, Bugawa zatayi tayanda bazata sake aiki ba har abada kuwa!" Zaid yaƙare maganar yana me ɗaura hanun Dad ɗinsa akan ƙirjinsa dai dai saitin da zuciyarsa take....

"Baka da hankaline Zaid? ka kosan mekake cewa? wani irin mahaukaciyar soyayya ce wannan? anya kuwa Zaid baka zautu akan wannan banzar soyayyarba?" Mum ta tambayesa cikin yanayi na ɓacin rai, sosai abun nasa yanzu yake sosa mata rai..

"Mutuwa zanyi Mum akan Zahrah zan iyayin komai wallahi dagaske ni mahaukacine akan soyayyarta inason...."

"Kanasonta ko, shikenan tunda baka gujewa saɓon Allah saikaci gaba da sonta idan zaka sameta, domin kuwa yanzu ta riga da tayi maka nisa, saboda matar wani ce!" Mum tafaɗi haka ta hanyar katsesa daga maganar dayake...

Tamkar sauƙar guduma aka haka yaji sauƙan maganganun mahaifiyartasa acikin kunnuwansa,, kallonsa yamayar ga Dad ɗinsa,,  kai Alhaji Ma'aruf  ya jinjina masa alamar kalaman mahaifiyarsa gaskiya ne..

"Zahrah zata dawo gareka idan har Allah ya rubuta cewa itaɗin matarkace, amma yanzu kacireta acikin zuciyarka, saboda ahalin yanzu Zahrah tajima da zama mallakin wani,  kasani kuma tunata da kuma cigaba da sonta zai iya jefaka cikin halaka"  Dad yafaɗi haka ga ɗannasa cikin tsananin tausayawa...

Dafe ƙirjinsa yayi da sauri haɗe da cije laɓɓansa,  da ƙyar ya'iya motsa laɓɓansa  aniyarsa yafurta wata kalma, sai kuma labari yasha banban, tarine ya sarƙesa, take jini yasoma fitowa daga cikin bakinsa,  ƙoƙarin riƙesa Dad yasomayi amma kuma kafun yakai ga riƙesa tuni yafaɗo daga kan gadon, Mum kuwa tuni tafice aɗakin taje taƙira Doctor's,,  kafun Doctors ɗinma suzo tuni Zaid yayi mugun fita acikin hayyacinsa, gaba ɗaya jini ya ɓata gaban rigar dake jikinsa, idanunsa ne suka juye   wani irin numfashi yaja me sauti, saikuma komai  na jikinsa yasake alokaci guda, daidai lokacin Likitoti suka ƙaraso cikin ɗakin ....  Taimakon gaggawa suka shiga bashi don ceto rayuwarsa cikin ikon Allah kuwa suka samu numfashinsa ya dai-dai ta, allurai suka narka masa wanda zasu sanyasa bacci...

Babban likitan dake kula da al'amuran Zaid ɗinne, ya rufe Dad da faɗa akan wai saboda me yasa aka faɗawa Zaid ɗin maganar da zata tada masa da hankali, haƙuri Dad yashiga bawa Doctor ɗin,   sharuɗa masu tsauri Doctor ya shumfuɗa musu, akan cewa lallai dole babu wanda zai sake ganawa da Zaid ɗin harsai bayan kwana uku, sannan kuma koda sunkoma gida yazama dole akiyaye shiga damuwa dakuma ɓacin ransa, saboda yanzu zuciyarsa tazama kamar wani ɗanyen ƙwai sai anayi ana lallaɓata, zuwa yanzu abu kaɗan ne zai sanya ta buga, wanda hakan kuwa dai dai yake da rasa rayuwar Zaid ɗin baki ɗaya
***
Bayan awanni 4

Shikaɗai yasan irin raɗaɗi dakuma ciwon dake kwance acikin zuciyarsa,  hawayene suke ta fita daga cikin idanunsa suna gangara akan ƙuncinsa,,   "Da gaskene Zahrah'n sa tayi aure? me yasa Zahrah zatayi masa haka? Bazai taɓa iya jurwa ba, lallai koda Zahrah tayi aure bazai taɓa daina sonta ba, kuma koda duka mutanen duniya zasu taru akansa bazai sanja ƙudurin dake zuciyarsa na auren Zahrah ba, zaiyi duk wani abu wanda yasan Zahrah zata dawo garesa koda kuwa hakan zaijawo sanadiyar rasa rayuka ne, ZAHRAH kawai yasani kuma itace cikar burinsa"..... (😳 karya kasheni nima🏃‍♀🏃‍♀)

*(Gobe Birthday na💃💃 zan baku updated insha Allah💃💃gobe akwai show agidan Doctor 🙊 )*

        *21/January/2020*


         *Fatymasardauna*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇  

      *SHU'UMIN NAMIJI !!*

     *Written By*
Phatymasardauna

*Dedicated To My Brother KHABIER*

*🌈Kainuwa Writers Association*

_{United we stand and succeed; our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}_

*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*

              *WATTPAD*
        @fatymasardauna

*Editing is not allowed📵*

        *CHAPTER 94 to 95*

*NIGERIA*

Tunda Doctor yafita baisake dawowa cikin gidanba harkuwa Zahrah ta ƙaraci zamanta acikin falon ta koma uwar ɗaka, sai dai kuma yayi mata waya yasanar mata cewa yana gidan Hajiyarsa wani uzuri ne ya riƙesa...
***

Idar da sallan isha ɗinta kenan ta miƙe haɗe da ƙarasawa gaban dressing mirror,  lotion ɗinta me ƙamshi ta shafa ajikinta,  powder kawai ta shafa akan fuskarta sai kuma man leɓe...   Wata rubber pencil gown maroon colour ta sanya ajikinta, rigace irin marar nauyi ɗinnan sannan kuma an cika gabanta da fararen duwatsu wato (stones)   wani maroon ɗin mayafi me ɗan kauri ta ɗauka haɗe da kafa ɗaurin ɗan kwalin nan na turban akanta,   sosai tayi kyau saikace wata balarabiya,  zama tayi akan gado haɗe da jawo wayarta, ajiyar zuciya ta sauƙe, har cikin ranta tana mamaki ƙwarai na rashin dawowan Dr.Sadeeq, tun safe daya fita haryanzu baidawo ba,,  tashi tayi ta rage gudun ac'n dake cikin ɗakin, haɗe da ɗaukar wayarta tafice zuwa falo,  hankalinta gaba ɗaya ta maida kan  tashan MBC Bollywood da suke haska film ɗin nan me suna SANAM TERI KASAM bata taɓa kallon film ɗin ba amma kuma tana da waƙoƙin film ɗin acikin wayarta saboda sosai waƙoƙin sukeyi mata daɗi,, ta shagala a kallon film ɗin har idanunta sunfara kawo ƙwalla saboda tausayi,  jitayi ansanya hanu anrufe idanunta , a razane ta ƙwalla ƙara domin kuwa sam bataji motsin shigowan  mutum cikin falon ba, da sauri tature wanda yarufe mata idanun gefe haɗe da tashi tsaye,,  ganin cewa shine yasanya tashiga sauƙe ajiyar zuciya akai akai,, murmushi yasakamar mata haɗe da cewa

"Matsoraciya" 

Zama yayi akan kujera,, itama zama tayi tana me da numfashi sosai yatsorata ta donkuwa bata tsammata cewa shi bane sam ta manta ma da cewa babu mayafi ajikinta... Kafeta da'idanunsa yayi yana me ƙarewa kwalliyartata kallo,, sai alokacin ta ankara da irin kallon dayake jifanta dashi.

  "Sannu da dawowa!" tafaɗi haka cikin sassanyar murya.

"Yauwa, kimin afuwa najima da yawa" yafaɗi haka yana me sanya hanunsa ya kama kunnensa alamar yana neman afuwa,   murmushi kawai tayi masa haɗe dayin ƙasa dakanta...

Miƙewa tsaye yayi haɗe da cewa "Bari naje nayi wanka, akwai kayan fruit acikin fridge please kiɗan yanka min kafun na fito"

"To" kawai tace dashi haɗe da tashi tanufi wajen fridge ɗin shikuma direct ya wuce ɗaki donyin wanka...

Tana kammala yanka fruit ɗin ta ɗauko wani plate me kyau tarufe yankakken fruit ɗin,  kan kujera ta koma ta zauna haɗe da sake maida hankalinta ga tv.. Sanye da tree guater jeans ajikinsa haɗi da wata farar t-shirt ya fito, ƙamshi kawai yake fitarwa, satan kallonsa Zahrah tayi haɗe da ɗan sakin murmushi, bata taɓa ganinsa acikin irin wannan shigar ba amma kuma yayi mata kyau sosai..   Akan lallausan carpet ɗin dake malale tsakiyar falon ya zauna haɗe da tanƙwashe ƙafafunsa,    alama yayi mata da hanunsa cewa ta miƙo masa fruit ɗin, ɗaukan plate ɗin tayi taƙarasa gabansa, durƙusawa tayi har ƙasa kana ta aje plate ɗin,, "Miƙomin wancan ledan"  yafaɗi haka yana meyi mata nuni da leda wanda shiya shigo dashi sam ita batama lura ba,,  cike da nutsuwa taɗauko ledan kamar yanda ya umarceta ɗan duƙawa tayi  haɗe da miƙa masa ledan,,  amaimakon yakarɓi ledan sai taga ya jawota jikinsa,  zaunar da ita yayi acikin jikinsa  haɗe da sanya hanu ya zame ɗaurin turban ɗin dake kanta, take lallausan gashinta ya zubo harzuwa kan bayanta,   kansa ya cusa acikin gashin nata yana me shaƙan daddaɗan ƙamshin dake tashi ajikin gashin nata,,   "Kiyi mini afuwa my princess,  banƙi dawowa haka kawai ba!" yafaɗi haka yana me ƙara matseta acikin jikinsa.

"Ni bakayi mini laifi ba sam sam,  nasan ae bazaka ƙi dawowa haka kawai ba" tafaɗi haka cikin zazzaƙan muryarta..

"Yauwa my wife nasanki dama kina da haƙuri, natsaya a wajen ƴar uwarki Salima ne, ina fatan banyi laifi ba?"

Da sauri tajuyo da kanta tana kallonsa,  "Salima kuma? bakace tafasa aurenka ba" tatambayeshi fuskarta ɗauke da tsananin mamakin jin abundayace..

Dariya yayi ganin yanda tawani zaro idanu kishi ya bayyana akan fuskarta ƙarara daga ambatan sunan Salima.   

"Wasa fa nake miki Madam, miye na wani tsorita haka"  yafaɗi  haka yana me ƙarewa kyakkyawar fuskarta kallo..

Ƙaƙƙarfan ajiyar zuciya ta sauƙe haɗe da  ɓata fuska, ta juya da kanta batace dashi komai ba,, sarai ya lura taji haushi,,,  yankakken apple ya ɗauka haɗe da kaiwa kusa da bakinta..  ƙin buɗe bakinta tayi saima daɗa kauda kanta da takeyi jefa apple ɗin yayi cikin bakinsa, haɗe da sanya hanu ya juyo da kanta yazama tana fuskantarsa...

"Fushi kike da mijinki? kiyi haƙuri banfaɗi haka don ranki ya ɓaci ba, wasa nake miki kiyi mini murmushi kinji Zahrah na!"

Hakanan taji zuciyarta tayi sanyi harbatasan sanda tasaki murmushi ba..   Yankakken apple yakuma ɗaukowa  yakai bakinta babu musu ta buɗe bakinta yasanya mata... Tana zaune acikin jikinsa haka yaciyar da'ita domin kuwa atare sukasha fruit ɗin haɗe da ɗaura fresh milk akai.. Yana nan azaune ta tattare wajen takai kitchine haɗe da dawowa, miƙewa tsaye yayi haɗe da ƙarasawa gaban tv wanda yaketa ɓaɓatu shikaɗai ya kashe,  kallonta yayi kamar zaiyi magana saikuma ya fasa, wutan falon ya kashe kana yakama hanunta suka nufi ɗaki,  hmmm tun ɗazu bata ji tsoro ba sai yanzu da ta gansu sun hallara acikin bedroom, janta yayi har cikin bathroom sukayi brush... Da kansa yaciro  wani ƴar fingilar rigan bacci wanda take shara shara kamar rariyan tata sai dai kuma tana da ado ata wajen wuyan..  Ganin yanufota kai tsaye ne yasanya tayi saurin saddakanta ƙasa, zuciyarta kuwa luguden duka tashiga yi mata, kamar anka mata tana sata, harga Allah ita tsoronshi take Allah yasa yauma karyayi mata komai.. Tunaninta ne ya katse sakamakon sauƙar hanunsa da taji abayanta,  matsowa yayi gaf da'ita harsuna iya jiyo hucin numfashin junansu,,  ahankali yayi ƙasa da zip ɗin rigar nata, lokaci guda yasanya hanu ya soma zame rigar daga kafaɗunta, rumtse idanunta tayi ƙam, haɗe da takure jikinta waje ɗaya,  bazata iya hanasa ba, amma kuma dazai barta yace ta cire rigan da kanta da hakan yafiye mata komai daɗi, saboda ko bakomai zatayi iyaka ƙoƙari wajen ganin ta kare ƙirjinta,  lokacin daya kawo ƙirjinta kasa jurewa tayi, dasauri ta duƙa ƙasa haɗe da cewa "Dan Allah kabarni naje toilet na cire da kaina"

Bai tanka mata ba saima ɗagota daya sakeyi tsaye,  rungumeta yayi ta baya haɗe da ɗaura kansa akan wuyanta, hancinsa yasanya yashiga shaƙan daddaɗan ƙamshin da fatarta

Please Login or Register in order to submit comment