Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

domin typing ɗin ba ya yawa, ina busy ne sosai, dan Allah kada kuyi ƙorafi, insha Allah next page zanmuku da yawa)

*27/November/2019*

*Voted, Comment, and Share please...follow me on wattpad @fatymasardauna
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

                *SHU'UMIN NAMIJI !!*

    *Written By*
Phatymasardauna

*Dedicated To My Lovely Brother Khabier*

*🌈Kainuwa Writers Association*

*{United we stand & succeed; our ambition is to entertain and motivate the mind of readers}*

*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*

            *WATTPAD*
     @fatymasardauna

*Editing is not allowed📵*

*Chapter 42 to 43*

Suna fita kuwa ta iske Baffa yayi ɗare ɗare agaban motar Dr Sadeeq sai washe haƙora yake kai kace anmasa kyautar ƴan kuɗaɗe ne.

Dakansa ya buɗe mata murfin motar ɓangaren gidan baya, cikin sanyin jiki ta shiga cikin motar, kaitsaye yashige ɓangaren driver haɗe da mawa motar key...

Tunda suka ɗau hanyar makarantar tasu Baffa ke faman zuba kamar wani kurna, yayinda Doctor Sadeeq ke amsa masa jefi jefi, domin hankalinsa gaba ɗaya yana ga Zahrah, wacce ke zaune tayi jigum a gidan baya,  akai akai yake satan kallonta tacikin madubi.. 
A haka dai harsuka iso cikin makarantar tasu,  dai dai bakin ƙofar hall ɗin da zasu gudanar da lecture yau, ya yi parking motar tasa, domin dama already ansanar dashi cewa yau a wannan hall ɗin zasu gudanar da lecture.

A hankali ta buɗe murfin motar ta fito kafaɗarta ɗauke da jakar makarantar ta,  cikin takunta mai ɗauke da nutsuwa ta nufi cikin hall ɗin kai tsaye, ko wai gensu batayi ba,  tanashiga hall ɗin kallo yadawo kanta, take taji wani irin muguwar faɗuwar gaba haɗe da karyewar zuciya, gani take tamkar kowa yana ganin abun da yafaru da ita rubuce akan goshinta.

Karab idanunta suka sauƙa akan Husnah wacce take faman aikin haɗa wasu takardu dake gabanta. wani irin sanyi taji zuciyarta tayi sakamakon ganin husnah, domin kaf makarantar bata mu'amala da kowa bayan husnah,  da matuƙar farinciki Husnah ta rungume Zahrah, domin koda wasa batayi tunanin ganinta ba.   

"Kamar mafarki nakeyi gaskia naji daɗi sosai ƙawata!" Husnah tafaɗa cike da tarin farinciki.

Zama sukayi a tare dai dai lokacin  Sir Bature yashigo cikin hall ɗin, tsit haka ajin ya ɗauka ana ta sauraran lecture ɗin dayake yi musu, a zahirin gaskia tanajin abun da yake cewa, amma kwata kwata bata fahimtarsa,  awa biyu suka ɗauka chur suna lecture, kafun daga bisani yafita daga ajin,    gyara zama Husnah tayi haɗe da mai da kallonta ga  Zahrah cike da kulawa tace " Yanzu ina likitan yake ?" 

Ajiyar zuciya Zahrah ta sauƙe haɗe da cewa " Ba maganar Doctor bace damuwata Husnah, babban damuwata shine gani nake tamkar abun da Zaid yamin yana rubuce a gaban goshina, Husnah gani nake tamkar kowa yasan abun dake damuna !" Zahrah taƙare maganar cikin raunin zuciya.  

" Kada kice haka Zahrah, babu wanda yasan abun da yafaru dake, kada ki ɗaga hankalinki ƙawata kinfasan kowa da irin tasa ƙaddaran, kuma zuwa yanzu na tabbatar kin mai da al'amuranki ga Allah, shima Zaid nasan kinbarsa da Allah "

Murmushi mai ciwo Zahrah tayi haɗe da kallon ƙawarta ta, cike da ƙuna tace " Banda wata hanya wanda tawuce barinsa ga Allah, nasan nan bada jimawa ba Allah zai bimikin haƙƙina " taƙare maganar cikin raunin zuciya,

Hannayenta Husnah ta kama suka fice daga cikin ajin, kai tsaye cafeteria suka nufa don cin abinci. Balaifi sosai tasamu nutsuwa a yau ɗin domin kuwa Husnah bata barta tayi kaɗaici ba. Ƙarfe  5 dai dai suka fito daga  cikin lecture ɗin ƙarshe na ranan yau ɗin, kasan cewar ta kwana biyu bata zo makarantar ba, sai take jinta gaba ɗaya duk ta gaji,   cikin nutsuwa take takunta yayinda kanta ke duƙe a ƙasa, ba abun da zuciyarta keyi banda bugawa, gaba ɗaya tsoron fita daga cikin school ɗin takeyi, gani take tamkar tana fita za'a kamata, da ƙyar take iya ɗaga ƙafafunta, dagani kasan bason tafiyar take ba. a hankali ta matsa gefe, haɗe da waigowa don ganin waye wannan ya matsa mata da horn ɗin motarsa, karab idanunta suka sauƙa akan sa, kasancewar  gilasan motar tasa gaba ɗaya a sauƙe suke, sam batayi tsammanin ganinshi ba,  murmushi yasakar mata haɗe da cewa " Da baki matsaba ai dana take ki !" yafaɗi maganar cikin yanayin tsokana, ɗan guntun murmushi itama tayi haɗe da taɓe baki, "ai idan haka ta kasance zanfikowa jin daɗi " Zahrah tafaɗi hakan da iya gaskiyarta.

"Shigo mutafi!" yafaɗa cikin tsare gida.

Saurin kallonsa tayi bakinta ɗauke da tarin tambayoyi, amma kuma takasa koda motsa bakinta ne balle ta furta wata kalman.

"Kintsaya kina kallona, ba dole idan bazaki bini ba, saina yi tafiyata!" yaƙare maganar yana mai niyar tada motar tasa.

Da sauri ta zagaya haɗe da buɗe murfin motar, gefen mai zaman banza ta shiga haɗe da tamke fuskarta tamau tamkar wanda yagayamata magana marar daɗi.

Da ƙyar ya iya ɓoye dariyan dake cinsa, domin kuwa tsoro ya hango ƙarara akan fuskar Zahrah,     "Naɗauka ai zakijamin ajine, da sai na tafi na barki ba ruwana!" yafaɗi hakan cike da shauƙi.

Harara ta watsa masa haɗe da sake turo baki gaba, cike da shagwaɓa wacce batasan tayi ba tace "Nifa idan surutu zakamin ka sauƙeni nayi tafiyata"

Yanzu kam kasa ɓoye dariyarsa yayi saida ya dara kafun ya ce " Bazan sauƙe kiba ai bani na ɗauko ki na saki ba, zaki iya fita da kanki ma, ai nasan ke jaruma ce zaki iya kare kanki ako da yaushe, har ma zaki iya shiga cikin ko wani abun hawa da ƙwarin guiwarki !"

Saurin kallonsa tayi domin kuwa sarai ta fahinci inda maganganunsa suka dosa, wato dai shima ya hango zallan tsoron dake kwance akan fuskarta.

"Shikenan tunda haka kace" tafaɗi maganar tana mai ƙoƙarin buɗe murfin motar ta fita.

"Haba ƴar ƙanwata, nifa wasa nake miki, kiyi haƙuri ki bari na kaiki gida kinji ko!" Doctor yafaɗi maganar cikin  lallashi, domin yafahimci cewa saurin fushi ne da'ita.

A cikin zuciyarta tayi hamdala, sakamakon hanata fita daga motar da yayi, domin dama burga ce kawai tsoron dake cikin zuciyarta bazai barta  ta iya tafiya ba, duk runtsi tafiso shiɗin ya kaita domin tafi yarda dashi fiye da kowa a yanzun..

Kwantar da bayanta tayi akan kujeran motar haɗe da lumshe idanuwanta, gaba ɗaya jinta take a gajiye, ga wani irin ciwon kai dake damunta,  a hankali  take buɗe  idanunta, a zabure tatashi zaune sakamakon ganin da tayi Doctor ya nufi wata hanyar da ita saɓanin hanyar gida.

"Inazaka kaini !" Tafaɗa a razane, kuma cikin yanayin tsoro,

"Saidake zanyi!" Yayi maganar babu alamar wasa akan fuskarsa.

"Dan Allah kayi haƙuri ka sauƙeni, ka barni naji da duhun dake cikin rayuwata, kada ka ƙaramin wani bala'in dan Allah!!" tuni hawaye sungama wanke fuskarta.

Wani irin kallo Doctor yayi mata haɗe da sakin murmushi bai kuma sake ce da ita komai ba, saima maida hankalinsa da yayi ga tuƙin da yake,

Yanzukam kuka mai sauti ta sanya haɗe da soma cewa " Dan Allah kada ka sake cutar da rayuwata, zan iya amincema ka kasheni amma bazan iya jure wa ba, idan kaci mutumcina, wlh na yarda ka wurgani kan titinnan mota ta taka ni, amma dan Allah kada kamin komai!!" taƙare maganar cikin matsanancin kuka mai taɓa zuciya.  Daidai lokacin suka iso gaban wani makeken mall wanda yagaji da ƙawatuwa, 
yana parking motar baiko kalletaba yayi saurin ficewa daga cikin motar haɗe da dannawa gabaki ɗaya ƙofofin fita a motar luck, domin yasan dole zatayi ƙoƙarin fita daga cikin motar,

Kuka sosai Zahrah keyi haɗe da sanya ƙarfinta tashiga dukan glass ɗin motar, tana mai ihun neman taimako amma babu kowa a wajen balle tasaran za a temaketa, domin kuwa wajen parking space ne.

"Ashe duniya cike take da azzaluman maza, ashe itakam rayuwarta a haka zata ƙare? wayyo Allah itakam ƙaddaranta kenan" abun da take faɗa kenan acikin zuciyarta tana kuka mai tsuma zuciya,domin a zaton ta hotel ya kawota zai kuma lalata mata rayuwa.

Daidai lokacin Doctor Sadeeq ya dawo hanunsa ɗauke da manyan manyan ledodi guda biyu, yana shiga cikin motar yakuma danna mata luck haɗe da mawa motar key da gudun gaske ya hau titi.

Zahrah kam muryanta har ya dashe kukanma harya daina fita domin gaba ɗaya ta gama sadaukar da cewa yau ce ranar mutuwarta,   kukantane yasoma tsagaitawa ganin sun nufi hanyar unguwarsu,   a hankali hawayenta suka daina zuba, yayinda tashiga sauƙe ajiyar zuciya akai akai, bakomai yasa hakanba face ganinsu da tayi sun shigo cikin unguwarsu tsulum,  a bakin ƙofar gidan nasu yayi parking cike da kulawa yajuyo da kallonsa ga Zahrah wacce take ta sauƙe nannauyar ajiyar zuciya, alamar taci kuka ta ƙoshi.

"Banga laifin kiba Zahrah, domin dole zakiji matuƙar tsoro, a iya tsawon rayuwata bantaɓa cutar da wata mace ba, kuma bazan fara akan ki ba,  bazan taɓa iya cutar dake ba Zahrah, inaso ki yarda dani, ban kuma yi haka don na cutar dake ba, nabiya dake ta mall ɗinne don inaso muje kiyi sayayyan abubuwan dakikeso da kanki, amma sai naga gaba ɗaya kinfirgita, kiyi haƙuri na tsorataki ko ƙanwata !!" Doctor Sadeeq yafaɗi maganar cikin tsananin tausayawa da kuma lallashi ga Zahrah'n..

Kuka kawai Zahrah takuma fashewa dashi haɗe da cusa kanta cikin cinyoyinta,  a hankali ya kama hanunta haɗe da matsewa a cikin nasa hanun,  "Banason kuka Zahrah, bana ce kiyi haƙuri ba!"  Dr yafaɗa cikin damuwa.

"Bakaine zaka bani haƙuri ba likita, nice zanbaka haƙuri, nayi maka mummunar fahimta, dan Allah kayi haƙuri, wlh tsoro nakeji banso wani abu yasake faruwa dani...!" taƙare maganar tana kuka sosai.

"Idan kinaso nayi haƙuri to kidaina kuka kinji ƙanwata!" yafaɗi maganar yana mai ƙare matse hanunta a cikin nasa hanun.

A hankali tashiga share hawayen dake ambaliya akan fuskarta,  ji takeyi zuciyarta tayi mata sanyi.

"Bakya kyau idan kina kuka, kinfi kyau idan kina dariya, kije gida kiyi wanka ki huta, banso kisake zubar da hawayenki kinji Zahrah, ungo wannan ledan kishiga gida, akwai waya a ciki na samiki sim da komai,  akwai games dayawa a ciki,nasan zai ɗebe miki kewa,  banson ganinki cikin damuwa Zahrah, kije gobe zanzo na kaiki school dakaina, Allah yasa bazakimin gardamaba " yaƙare maganar yana ƴar dariya.

Murmushi itama Zahrah tayi haɗe da ƙarɓan ƙatuwar ledan dayake miƙo mata, batare da tayi masa gardama ba, cikin rashin kuzari ta buɗe murfin motar tayi ficewarta,  harsai da yaga shigewarta cikin gida kafun ya ta da motar tasa ya bar unguwar tasu..

Zahrah tanashiga cikin gida kai tsaye ɗakinta tawuce, jakarta da  ledan da Dr Sadeeq ya bata ta ajiye. Kayan jikinta tashiga cirewa, zani ta ɗaura a kirjinta haɗe da sanya hijabi tafice daga  cikin ɗakin,   zaune ta taradda Inna a tsakar gida, sannu da gida kawai Zahrah tayi mata, haɗe da shigewa cikin bayan gida,  tana fitowa a wanka ta bi lafiyar katifarta domin dama dai bata wani jin yunwa, ledan da Doctor yabata ta jawo haɗe da buɗewa, kyawawan dogin riguna ne suka bayyana acikin ledar saikuma dangin su snacks dasu choculate, kyakkyawar kwalin wayar da tagani acikin ledar taciro SAMSUNG GALAXY S10 shine sunan  da ke  rubuce ajikin kwalin wayar,   wani irin faɗuwa gabanta yayi take nunfashinta yashiga gudu akai akai, bazata taɓa mantawa ba shima da haka yafara, daga ƙarshe kuma ya dasa mata babban tabo acikin zuciya da rayuwarta mai wahalan gogewa,    saurin sake kwalin wayar tayi haɗe dayin watsi da kayan da suke zube a gabanta,   talauci bahauka bane, bazata sake bari haka yafaru da'ita ba,   hawaye ne suka shiga sauƙa akan ƙuncinta,   haƙika soyayya bata mata adalci ba, kwanciya tayi lamo akan katifa tana nai sauƙe a jiyar zuciya,  jin da tayi zuciyarta na shirin dawowa ɗanyea shakaf ne yasanyata tashi ta ɗauko littafi mai tsarki wato Al'Qur'ani tasoma karantawa domin rage damuwar dake damunta a zuciya....

"Salima kuma Hajiya?" Doctor Sadeeq yatambaya cikin muryar damuwa.

"Ƙwarai kuwa Sadeeq, ko ita Saleema'n tana da wani aibune? ƙwarai nayaba da hankalinta dakuma tarbiyanta, saboda haka nagama yanke shawarata, gobe zanfaɗamawa ƙanin mahaifinku yaje yatambayo maka aurenta, idan ma a so nane banso bikin yawuce nanda wata ɗaya " Hajiya tafaɗi maganar babu alamar wasa akan fuskarta.

Cike da sanyin jiki Doctor Sadeeq yace " Shikenan Hajiya, Allah yasa hakan shine mafi alkhairi, amma dakin ƙara haƙuri, nan bada jimawa ba zan kawo wacce nakeso"

"Hmmm ai aikin gama yariga daya gama Sadeeq, nagaji dajin wannan zancennaka, koda yaushe haka kake cewa, to yanzu dai nagaji da ƙaululan dakakemin saboda haka natsaida magana,zaka iya tafiya"

Gaba ɗaya hukuncin da Hajiyar tasa ta yanke masa baiyi masa daɗi ba, amatsayinsa na Namiji bai dace ace anyimasa dole akan aure ba,  shi sam Saleema ma bata ɗaya daga cikin irin tsarin matan dayakeso, amma yazaiyi tunda dai Hajiya ta kafe, yasanta da wuyar sha'ani, idan tace eh zaiyi wuya kuma tace a'a,  jiki a mace haka yafice daga falonnata, kaitsaye  ɓangaren sa yanufa, yanashiga cikin falonnasa direct friedge yanufa, goran ruwa mai sanyi ya ɗauko, haɗe da zama akan kujera, saida yasha ruwan fiye da rabin gora, kafun yashiga sauƙe ajiyar zuciya,  wayarsa yaciro acikin aljihun rigarsa, kai tsaye lambar sim ɗin dake cikin wayar daya bata, ya danna wa ƙira, saidai yaji saɓanin tunaninsa, domin kuwa cemasa akayi wayar a kashe take, nannauyar ajiyar zuciya ya sauƙe, haɗe da aje wayartasa a gefe,    "Maiyasa nadamu da'ita sosai ne?" yatambayi kansa, bayan kuma yasan baida amsa, 

"Inatausayinta sosai,amma kuma bayan tausayi inajin wani  abu na daban a ga me da'ita, menene wannan abun ? yazama dole nasan menene amma tabbas ina da burin inganta rayuwarta " Ƙaran wayarsane ya katse sa daga zancen zucin da yakeyi,  ganin da sabon number ake ƙiran nasa yasa bai ɗauki ƙiranba, saima tashi dayayi yawuce cikin bedroom ɗinsa...

Washe gari.

Yau tunda safe takammala shirinta,  tayi kyau cikin shigar ta ta atamfa riga da sket, yayinda  lufayant dake jikinta ya kasance hot pink colour,  sama sama tasha ruwan shayin da Inna ta dafa,  tana kammala shan ruwan shayin ta ɗauki jakarta haɗe da nufar hanyar waje. domin batamaso likita yazo yasameta, tafiso tayi tafiyarta, sam bataso yanashiga cikin rayuwarta,  takuma yanke shawaran gaya masa yafita acikin rayuwarta, domin sam baikamata tasake bawa wani namiji dama ba.

Turus haka taja ta tsaya, domin kuwa tsaye tagansa ajikin motarsa, yasha ado cikin wata blue ɗin shadda, sam batai tsammanin ganinsa a daidai wannan lokacinba.

Murmushi yayi mata haɗe da soma takowa harzuwa inda take tsaye.

"Baki tsammaci ganina a dai dai wannan lokacin ba ko?" yatambayeta kansa tsaye yana mai kafeta da idanu.

Ɗan ƙaramin bakinta taturo gaba haɗe da cewa "Ina kwana"

"Lafiya ƙalau, yakika tashi?"

"Lafiya" tabasa amsa a taƙaice, haɗe da sunne kanta ƙasa, domin hakanan taji yamata wani irin kwarjini.

"Muje kada kiyi latti ko" Doctor yafaɗa yana mai yi mata nuni akan cewa tashige gaba.

Bazata iya musa masa ba, domin kuwa yayi mata kwarjini sosai, don haka cikin sanyin jiki tanufi wajen motar tasa, shikuma yarufa mata baya, gaba ɗaya jitayi jikinta yayi sanyi, alƙawarin da ta ɗaukawa kanta nacewa zata faɗa masa yafita a rayuwarta gaba ɗaya ya ruguje, domin kuwa tanaganinsa taji bakinta yamutu murus, tana shiga cikin motar ta lumshe idanu, domin kuwa wani irin daddaɗan ƙamshi cikin motar keyi, cike da nutsuwa yake tuƙin nasa, yayinda jefi jefi yake satan kallon Zahrah, wanda gaba ɗaya hankalinta yana ga ababen hawan da suketa hada hada akan titin.

"Maiyasa ki kaƙi kunna wayar dana baki?"

Sunkuyar da kanta ƙasa tayi haɗe da soma wasa da yatsun hanunta,  "Babu" tafaɗi hakan cikin sanyi murya.

"Ko kuma dai bakyason kyauta daga gareni ba "

Saurin kallonsa tayi, jin abun da yace, ai kuwa karab idanunsu suka haɗe a waje ɗaya, saurin sadda kanta ƙasa tayi, domin batason haɗa idanu dashi kokaɗan,    "Bahaka bane, kawai dai  banson rayuwata tasake cutuwa ne" tafaɗi hakan da iya gaskiyarta.

Kansa ya jinjina haɗe da cizon lips ɗinsa,  "Eh ta wani wajenma kina da gaskia, amma ai bada wata manufa na baki ba, amma idan kinaga zaki takura to shikenan saikiyi abun da yadace"  shima yayi maganar da iya gaskiarsa.

Daga haka dukansu basu sake ce da junansu komaiba, har suka iso cikin makarantar, yauma har gaban lecture hall ɗin su ya kaita, sai da kuma yaga shiganta cikin hall ɗin kafun yayi tafiyarsa.

Koda aka tashi yauma shiya zo da kansa ya ɗauketa,  sai dai tunda suka kama hanya harsuka isa gida babu wanda yace da ɗan uwansa wani abu.

A daidai ƙofar gidan su ya tsaida motar, haɗe da juyo da kallonsa gareta ƙoƙarin fita tasomayi daga cikin motar, cikin wata irin murya mai sanyi yace "Inason magana dake"

Kallo ɗaya tayi masa ta kau da kanta gefe,  "Wace irin maganace ?"

"Maganace mai matuƙar mahimmanci , amma kuma tana buƙatar ishashshen lokaci " Doctor yaƙare maganar yana mai duban agogon dake ɗaure a tsintsiyar hanunsa.

"Inajinka" Zahrah tafaɗa a taƙaice,

"Bakina jina zaki ce ba,  hankali da tunaninki nakeso kibani "

Gyara zamanta tayi haɗe da ɗan satar kallonsa, batare da tace komaiba.

Kwantaccen sajen dake kan kumatunsa ya shafa, haɗe da cewa " No kada kiyi zaton wani abu zance, dama  alluranki ne banƙara sa miki ba, kuma akwai matsala idan banyimiki su ayau ba!"

Gaba ɗaya idanunta ta ƙwalalo su waje, yayinda tsoro yacika zuciyarta, "Dan Allah kayi haƙuri wallahi na warke, yanzu banajin komai ajikina!" taƙare maganar lokacin da muryarta ke rawa, alamun zatayi kuka.

"A'a ni gaskia banyarda da cewa kin warke ba, saboda naga kina yawan sanya kanki a damuwa kuma jiya ma dana riƙe hanunki naji zazzaɓi a jikinki, don haka kawai zan ƙarasa miki yanzu" yaƙare maganar yana mai shirin buɗe wani ɗan ƙaramin drower dake cikin motar, take allurai suka bayyana, ai a ɗari Zahrah ta buɗe murfin motar haɗe da rugawa zuwa cikin gida,  ko tsayawa ɗaukar jakarta batayi ba.
Dariya sosai Doctor Sadeeq yasanya, hadda riƙe ciki, shi dama burinsa yaga yanayin tsoronta, domin idan tana cikin wannan yanayin tsoron sosai take burgesa,  ɗaukar jakar nata yayi haɗe da fita acikin motar kai tsaye yanufi cikin gidan. Yana sallama Inna ta tarbesa da fari'a, haɗe da cewa "Ai dama nasan tare kuke domin daganin yanda tashigo a guje nasan cewa ba ita kaɗai bace"  ɗan guntun murmushi yayi haɗe da cewa " waifa dan nace zanmata allurane, shine duk tabi ta ruɗe, kuma yau bazan bar gidannan ba harsai na mata alluran nan, ko yakikace Inna?"

Idanu Zahrah tasake gwalowa jin abun da yake cewa,  gaskia ita daya mata allura gwamma yabata magani amma sam batason allura, kuma ita taji sauƙi, amma su sundage akan cewa wai bataji sauƙi ba,  kafun ta gama zancen zucin da takeyi taji muryarsa a bakin ƙofar ɗakin yanacewa Inna ta ɗauko masa ita....

(Kuyi haƙuri jiya kunjini shiru,  muna biki ne, yauma a daddafe nayi muku typing bacci nakeji)

         *30/November/2019*

*Voted, Comment & Share please....Follow me on wattpad @fatymasardauna


🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

                   *SHU'UMIN NAMIJI !!*

      *Written By*
Phatymasardauna

  
*Dedicated To My Lovely Brother Khabier*

*🌈Kainuwa Writers Association*

{United we stand and succeed;our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}

*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*

           *WATTPAD*
      @fatymasardauna

*Editing is not allowed📵*

*(Ina mai baku haƙurin rashin jina kwana biyu da kukayi, insha Allah hakan bazai sake faruwa ba)*

*Chapter 44 to 45*
 

Sake matse jikinta tayi ajikin bango, haɗe da turo ɗan ƙaramin bakinta gaba.   

"ZAHRAH!" taji muryarsa yana ƙiran sunanta,  cikin tsoro da ɗar ɗar, ta   buɗe ƙofar ɗakin nata, kallo ɗaya yayi mawa cikin idanunta yakau da kansa gefe, domin kuwa wani irin zubawa yaji tsikar jikinsa tayi, gaskia Zahrah tana da abubuwan ɗaukar hankalin ɗa namiji da yawa a tattare da'ita.

Batare da yakuma kallonta ba, ya miƙomata jaƙarta dake riƙe a hanunsa, da sauri ta fusge jakar haɗe da komawa cikin ɗakin ta,ta kuma  datse ƙofar,  murmushi kawai Doctor Sadeeq yayi haɗe da girgiza kansa, kallonsa yakomar ga Inna, cikin girmamawa yayi mata sallama, bayan ya cika mata hanunta da alkhairi,  cike da farinciki Inna tayi sallama dashi, don tsabar daɗi ma har kusan ƙofa ta rakasa, tana mai zabga masa godiya.

Tafiya yake amma shi kaɗai yake murmushi, sosai Zahrah take burgesa, yanason komai na yarinyar, fushinta, dariyanta, tafiyarta, nutsuwarta, dama duk wani abu nata, tabbas Zahrah tana ɗaya daga cikin irin matar da yake fatan mallaka a matsayin matarsa ta sunna,  ko dai zai jarrabane ?" ya tambayi kansa, saurin dukan seterin motar tasa yayi haɗe da cije laɓɓansa,  "Ka dawo cikin hankalinka Sadeeq, maikake shirin aikatawa ne haka?" yatambayi kansa a fili.

"No baikamata nayi haka ba, dole zanyi haƙuri !" yafaɗi hakan cikin karyewar zuciya, dai dai lokacin kuma ya iso gaban makeken gate ɗin gidansu, mai gadi yana gama wangale masa gate ɗin ya cusa motar tasa zuwa cikin gidan.

Saida tagama ƙaremawa wayar kallo kafun ta danna madannin da zai sanya  wayar ta kawo haske,    nannauyar ajiyar zuciya ta sauƙe, haɗe da jingina bayanta da jikin bango,  "Yazama dole kikawo sauyi acikin rayuwarki   Zahrah,  kada ki bari abunda Zaid yayi miki, yazama sanadiyar lalacewar duk wani farinciki dake cikin rayuwarki"  zuciyarta ta faɗa mata hakan cike da ƙarfafa mata guiwa, "Amma tayaya hakan zai kasance, bayan banda wani ginshiƙi dazai taimakamin ?" Zahrah tatambayi kanta,  sake gyara zamanta tayi haɗe da ɗaukar wayarta, kai tsaye tashiga wajen dazai sadata da apps ɗin wayar,  Word Charm shine game ɗin daya ɗauki hankalinta, duk cikin apps ɗin dake wayar, dama tanason game ɗin, don haka kaitsaye tashiga tasomayi, take taji kewa da kaɗaicin da take ji sun soma ragewa, a wannan rana dai  Zahrah batayi wani dogon tunani  da takura kanta ba, dazaran taji ta takura zata ɗauki wayarta tasoma buga game,  idan ta gaji  da buga game ɗin kuwa, sai ta shiga Instagram shima sosai yake rage mata kewa (nima haka, lol)..

Tayi kyau sosai cikin blue rover gown ɗin dake jikinta,  wata baƙar lufaya ta sanya a jikinta wanda yataimaka wajen ƙarawa shigar tata kyau da armashi,  batayi wani kwalliya akan fuskarta ba, ta dai shafa man leɓe dakuma kwalli, amma duk da haka tayi kyau, dama mai kyau ko baiyi kwalliya ba kyawunsa baya ɓuya.

Kasancewar yau baza su jima a makaranta ba, yasanya bata ɗauki jakaba, sai wasu ƴan littatafai da ta ɗauka a hanunta, sai kuma wayarta,      koda ta fito tsakar gidan zaune a bakin  murhu ta iske Inna tana tuyan ƙosai, wanda Baffa yace ayi na karyawa.

"Inna ni zanwuce makaranta" Zahrah ta faɗa tana mai ƙoƙarin gyara zaman lufayan dake jikinta.

"Bazaki tsaya ki karyaba Zahrah"
Baffa dake fitowa daga cikin ɗakinsa ya faɗa.

Ɗan guntun murmushi Zahrah tayi haɗe da shafa cikinta "Banajin yunwa sosai Baffa, kuma ina tsoro kada na makara!"

"Eh kina da gaskiya, kinga kuwa tun ɗazu likita, yazo yana jiranki, bayanda banyi da shi ba akan yashigo, amma sam yaƙiya, don haka gwamma ki hanzarta, a dawo lafiya "  Baffa yaƙare maganar yana mai yunƙurin komawa cikin ɗakinsa.

"Ameen Baffa nagode!" Zahrah tafaɗa cike da farinciki, domin kuwa karo na farko kenan a rayuwarta da taga tsananin kulawan Baffa a kanta.

Tana fitowa yasakar mata kyakkyawan murmushinsa,  ga mamakinsa sai yaga itama ta sakar masa murmushi, wanda yayi matuƙar taɓa masa zuciya, domin kuwa bakaɗan ba tayi kyau, da tana murmushin.

"Saiyanzu ki ka ga daman fitowa? kinshanyani kamar kin aje dutse" Doctor yafaɗi maganar yana mai turo baki gaba, tamkar ƙaramin yaro.

Dariya sosai Zahrah ta shiga yi, domin yanayin yanda yayi maganar yazama dole wanda ya gani ya dara,   hangame baki Dr yayi yana kallon yanda take dariyan, abun da bai taɓa gani ba kenan, tun haɗuwar su da'ita, bai taɓa ganinta tana dariya ba sai yau, ashe ma duk kyawunta da yake gani, bai ga komai ba, domin da tana dariyan tafi  masa kyau.

Hanunta tasanya ta toshe bakinta, haɗe da tsagaita dariyan da takeyi, kallonsa tayi haɗe da cewa "Bakaga yanda kazama yaro ba dakana maganan nan, tamkar ɗan shekara takwas!"

Murmushi yayi haɗe da jefamata hararan wasa, cikin yanayin da yayi magana ɗazu yakuma cewa "Shine kikemin dariya ko? sai na faɗaki da mamana!"  ai kamar yaƙara mata fower'n da riyan nata ne,  nan take taci gaba da dariyanta, hadda ɗan guntun ƙwalla a idanunta,  wani irin sanyi da nishaɗi yaji yana huda zuciyarsa, tabbas bashida wani buri da yawuce yaga Zahrah tana cikin farinciki Alhmdlh, yau gashi ta sanadiyarsa tana dariya dakuma nishaɗi,

"Kayi haƙuri, bazan

Please Login or Register in order to submit comment