Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

aiki yabaro yazo gareta,  to yazaiyi tunda tazama wani ɓangare na jikinsa...

Da matuƙar farinciki Husnah ta rungume Zahrah tana mejin daɗin ziyarar bazata da Zahrah'n takawo mata, saboda bata faɗa mata zata zoba.  Bayan Zahrah ta gaisa da Momyn Husnah ne, suka rankaya zuwa ɗakin Husna'n,,, ba ɓata lokaci Husnah ta cikawa Zahrah gabanta da kayan ciye ciye dasu drinks.

"Naji daɗin zuwanki sosai ƙawata, kamar  kuwa kinsan ina kewarki, jiyafa har mafarkin ki nayi, da safe naƙira wayarki kuma najita switch off, ina fata dai kina lafiya?"

Hijabin dake jikinta ta cire haɗe da cewa "Lafiya amma  ba sosai ba"

Da sauri Husnah ta dawo da kallonta ga Zahrah

"Meyafaru dear?" Husnah tatambaya cike da kulawa.

Kallon Husnah Zahrah tayi na tsawon minti guda....

"Babuƙatar tuna abun da yafaru Husnah, saboda kinsan inada raunin zuciya, tuna abun zai iya sake jefani cikin wani hali"

Damuwane ya bayyana ƙarara akan fuskar Husnah haƙiƙa tamkar ƴar uwa ta jini take kallon Zahrah saboda haka duk wata damuwa ta Zahrah damuwar tace itama.

"Zaki iya ɓoyewa kowa damuwarki amma bandani Zahrah, sai de kuma babu amfanin takuraki akan cewa lallai sai kin sanar dani, saboda bansan wani hali zaki samu kanki aciki ba bayan kin faɗamin"

Dafa kaɗan Husnah Zahrah tayi haɗi da daure zuciyarta...

"Nasake haɗuwa da.... da....wanda ya yimin fya......." kasa ƙarasawa tayi saikawai tafashe da kuka.

Ko bata ƙarasaba Husnah tafahimci me Zahrah take nufi.

Cike da tashin hankali Husnah tasoma salati... 

Sake jawo Zahrah jikinta tayi haɗi  da rungumeta...."Ki daina kuka, yanzu ba lokacin kuka bane Zahrah, kinmaci abinci kuwa ?" Husnah ta tambayi Zahrah cikin kulawa...

"Banajin yunwa Husnah!" Zahrah tafaɗi haka cikin shaƙewar murya, wani yunwa zataji ita da take cikin bala'in sake ganin Zaid...

"Kinsan de ba kyau zama da yunwa ko, kinga yau ni namayi abincin dakaina, bana zuba mana muci tare, kuma dan Allah kada kicemin a'a"

Babu yanda Zahrah ta'iya dole tabiyewa Husnah taci abinci,  gaba ɗaya Husnah se zuba take tamkar kurna,  takasa yin shiru koda na minti biyu ne, tayi hakanne kuma saboda ta gusarwa da Zahrah da muwarta, daga ƙarshe de har game, Husnah ta jona musu a tv suka buga, sosai kuma hakan ya ɗebewa Zahrah kewa....
Tare sukayi sallan la'asar daga nan kuma Husnah ta ɗebi Zahrah, suka tafi shoprite, dangin su ice cream da chocolate suka jida, daga nan sukayo gida.

Kamar yanda yafaɗa ƙarfe biyar da minti ɗaya dai dai ya ƙaraso ƙofar gidansu Husnah.. Ƙiran Zahrah yayi a waya ya tabbatar mata cewa yana ƙofar gidan su Husnah....

Zahrah na ajiye wayarta Husnah ta kalleta haɗe da kashe mata ido ɗaya.

"Ƙawata tazama ƴar soyayya, sosai yanayin soyayyarku da Man ɗin nan yake kasheni, kinfasan gayen naki ya haɗu over, da badan ke bace  danayi snatching ɗin sa!" cike da zolaya Husnah ta faɗi maganar...
Dariya suka sanya su dukansu, haɗe da rungume juna.

Har bakin motar Dr.Sadeeq Husnah ta raka Zahrah, bayan Momyn Husnah ta cikawa Zahrah leda da dangin su turare dakuma kayan shafa hadda kyautar wani haɗaɗɗen leshi, sosai Zahrah tayi godia, hakan kuma yana ɗaya daga cikin abubuwan daya sanya bata son zuwa gidansu Husnah, saboda idan dai tazo tofa sai mahaifiyar Husnah tayi ɗawainiya da'ita wajen bata kyautan kayayyaki masu kyau da tsada...

Harsaida Husnah taga tashin motar su Zahrah kafun takoma cikin gida...

"Kinsamo abun daɗi shine kokimin tayi ko?" Dr.Sadeeq yafaɗi haka ga Zahrah wacce ta ɗaura ledan sayayyar da sukayi a shoprite ita da Husnah akan cinyarta...

"Murmushi me sauti tayi haɗe da cewa "Ba'abun daɗi bane, kayan shafa ne"

"Um um ni banyarda ba, kitaimaka kiban ko chocolate ɗaya ne, naci yunwa nakeji, yau duk banci abinci ba" yaƙare maganar yana me  shagwaɓe fuska, sai kace wani ƙaramin yaro...

Dariya Zahrah tayi haɗe da satar kallonsa "wai ma ya'akayi yasan cewa acikin ledar hanunta akwai chocolate?" ta tambayi kanta.

"Kina mamakin ya'akayi nasan cewa a ledarki akwai chocolate ko?, ai ba abun mamaki bane, tunda nasan shiɗin favorite ɗin ki ne" yafaɗi haka cikin yanayin shauƙi, amma still idanunsa naga titi..

Buɗe ledar tayi taciro wani chocolate mai kyau da daɗi kusan yafi kowanne ma daɗi acikin sauran chocolate ɗin da ta saya, ta miƙa masa  haɗi da cewa "Ga wan nan amma bazan iya baka kyautarsa duka ba, saboda haka kaci rabi kabarmin rabi"

Saurin kallonta yayi fuskar sa ɗauke da murmushi... " Naƙi wayon, idan har kinaso na karɓa saide kibani kyautansa duka"

Turo ɗan ƙaramin bakinta tayi gaba, haɗe da noƙe kai alamar hakan bazai yiwuba, kallon bakin nata yayi, harsai da yaji tsikar jikinsa ƴa zuba,  hmmm lallai idan ya auri Zahrah, zai tsotse wan nan ɗan ƙaramin bakin nata ne yanda ya kamata🙈...

"Kici chocolate ɗinki ke kaɗai nikam na gode" yafaɗi haka a  taƙaice domin dama wasa yake mata baci zaiyi ba, shi da yake fama da ciwon ciki idan yaci chocolate kuma yake nan?

Lokacin da suka iso gida biyar da rabi har ta gota...  kallon Zahrah Dr.Sadeeq yayi haɗe da ɗan nisawa.

"Nagama haɗa miki kayan lefe da kuma sauran abun da suka dace,  wace rana kikeso a kawo?" 

Saurin ɗaga idanu tayi ta kallesa jin abun da yace.
Idanunsa ɗaya ya kashe mata, wanda yasanya taji gabanta yafaɗi, saboda a wajen mutum ɗaya ta saba ganin irin wan nan kashe idon, kuma shi hakan yazame masa al'adarsa ne, bakowa bane kuma face ZAID.

"Zamuyi waya" Zahrah tafaɗi haka don son kawar da tambayar tasa, saboda a yanzu bata da amsar da zata basa..

Ajiyar zuciya ya sauƙe haɗe da dafa steering motar da duka hannayensa biyu. "Shikenan idan kin nutsu zan ƙiraki" yafaɗi haka cikin sanyin murya..

Murmushi tayi masa irin me tsayawa a rai  ɗin nan, kana tabuɗe murfin motar tayi ficewarta, sai de batare da yasani ba, ta aje masa wan nan chocolate ɗin...

Bayan kamar 2 minute da shiganta cikin gida yaja motarsa shima yayi tafiyarsa...

*ZAID*

Tunda yasha wan nan ƙwayoyin baisan inda kansa yake ba harsai ƙarfe uku na yammaci,,  ko da ya buɗe idanunsa ji yayi duniyar na juya masa, amma haka adaddafe ya shiga bathroom yayi wanka haɗe da ɗauro alwala, sai yanzu zaiyi sallan Azahar don tsabar asara, gashi har la'asar ma takawo kai....

Yana idar da sallan azahar ya miƙe daga kan sallaya haɗe da zura slipper ɗinsa yafice daga ɗakin... Kai tsaye masallacin jikin gidansu yanufa don gudanar da sallan la'asar wanda ake ƙira yanzu.. Ko a cikin masallacin mutane sai mamakin ganinsa suke saboda abune mawuyaci ka gansa a masallacin da wan nan time ɗin, yafi yawan zuwa sallan isha ko asuba, amma banda azahar da la'asar saboda a wan nan lokacin ma kwata kwata baya gida, sai de yayi sallah a wani wajen.  Baidamu da kallon da mutane suke masa ba, yana idar da sallan sa yatashi yayi shigewarsa cikin gida...

Tsab yagama shirya kansa cikin ƙananan kaya, riga da wando na blue jeans wanda suka matuƙar amsar jikinsa.  Ba abun da yake sai tashin ƙamshi.

Zama yayi abakin gadonsa haɗe da sanya hanunsa duka biyu ya dafe kansa dake yi masa ciwo kaɗan kaɗan,, wani irin sabon al'amari yakeji a cikin zuciyarsa, baisan da wani suna ze ƙira abun ba, amma tabbas jiyake zuciyarsa na azalzalarsa akan Zahrah, san nan yanajin cewa itace muradinsa, saurin buɗe idanunsa da ke lumshe yayi sakamakon hasko masa marukan da Zahrah ta sharara masa akan fuskarsa da sukayi, hanunsa yakai kan ƙuncinsa ya shafa haɗe da sakin murmushi, tunda yake a a rayuwarsa wata mace banda mahaifiyarsa bata taɓa kai hanunta jikinsa da sunan duka ba ballan tana har akai ga mari, sai gashi yau, Zahrah ta shararamasa lafiyayyun maruka harguda biyu akan fuskarsa, takuma haɗa masa hadda duka, amma ko kaɗan baiji zafin abun ba,  anya kuwa shine? kodai an musanyashine bai sani ba? meke damun ƙwaƙwalwa da zuciyarsa ne? shine Zaid kuwa? Yajerowa kansa waƴan nan tambayoyin....

*(Team Zaid saiku basa amsa, shi ɗin ne koba shiɗin bane?)*

*27/December/2019*

*Follow me on Whatsapp and Wattpad*

*Wattpad user name fatymasardauna*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

           *SHU'UMIN NAMIJI !!*

  
     *Written By*
*Phatymasardauna*

*Dedicated To My Brother KHABIER*

*🌈 Kainuwa Writers Association*

_{United we stand and succeed; our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}_

*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*

         *WATTPAD*
   @fatymasardauna

*Editing is not allowed📵*

    
       *CHAPTER 70 to 71*

Yajima zaune a kan gadon nasa, gaba ɗaya kansa ya kulle yarasa meke damunsa,  wai shin da gaske SO yake ko kuwa? anya kuwa yanaga zaman sa haka zai yi wu? zaifi masa kyau yanemi Abid domin shi ne kaɗai zai iya fayyace masa halin da yake ciki,  tabbas shi koda son Zahrah Abid ɗin yace masa yanayi yanzu bazai musa masaba, idan kuwa har haka so yake to yana mawa Zahrah so me tsanani,  saurin laluɓar wayarsa ƙirar  Samsung dake kusa dashi yayi. Numbern Abid ya dannawa ƙira, bugu biyu Abid ya ɗaga ƙiran cikin muryan kasala yace "Mutumin ya akayi ne, ka katseni ina cikin holewata"

"mcheeww aikin ka kenan cin ƴaƴan mutane, kana ina yanzu inaso muyi serious magana da kai" Zaid yafaɗi haka cike da zaƙuwa.

Miƙa Abid dake kwance shame shame a gado yayi haɗe da sakin daria, wai yau shi Zaid ke cewa baida wani aiki se cin ƴaƴan mutane, hmm ai duk iskancinsa shikansa yasan a ƙarƙashin Zaid yake, domin kuwa Iskancin Zaid me lasisi ne.

Cike da ƙuluwa Zaid yace " Nifa bana ƙira ka kamin iskanci bane, da zaka tsaya kanamin dariya"

"Yi haƙuri mana nawan, maganartaka ce tabani dariya, zuwa anjima mu haɗu a Millinion Park ina fata de bawata matsala bace ta afku?"

Ɗan yamutsa fuska Zaid yayi haɗe da duban agogon Rolex ɗin dake ɗaure a tsintsiyar hanunsa.  "Shikenan to muhaɗu ƙarfe 5 na yamma banakumason kamin african time, 5 nacika idan bakazoba, bazan tsaya ɓata time ɗina wajen jiranka ba" yayi maganar cikin yanayi da yake nuna cewa ba wasa yake ba..

"Okay" kawai Abid yace haɗe da aje wayartasa yajawo babe ɗin dake kusa dashi, suka ci gaba da watsewarsu ko kunyar Allah dayake ganinsu basayi, Allah karabamu da ƙeƙashewar zuciya Ameen.

Zaid yana aje wayartasa yasanya hanu yashafi cikinsa, sai alokacin yake tuna rabonsa da yasanya abinci acikin cikinsa tun jiya da yammaci,  amma saboda tsabar yashiga tension ko yunwarma bayaji,  murmushi yayi tunowa da yayi da yanda yaji muryan Abid, dagajin yanda yaji yanayin muryartasa yatabbatar masa cewa holewa da mace Abid ɗin keyi, "hmmm Abid ba dama wajen iya latsa mace" yafaɗi haka a fili, shikamma rabonsa daya kusanci wata mace harya manta,  shi yanzu ko mace ma yagani bata wani burgesa, yanzu idan zaiyi sex to badakowacce mace yakeso yayi ba, face Zahrah ita kaɗai yakejin cewa zai iya sauƙewa damuwarsa yanzu, itakuma kaɗaice zata iya basa gamsuwa ɗari bisa ɗari.  Miƙewa yayi yanufi wajen fridge ɗin dake ɗakin nasa, fresh milk ya ɗauka haɗe da tsiyayawa a cikin glass cup, zama yayi yasoma sipping fresh milk ɗin a hankali,  gaba ɗaya hankali da tunaninsa sunaga Zahrah, ko yanzu wani hali take ciki? Allah masani...

***

Sake narke masa murya tayi cikin shagwaɓa tace "Nide bance bana sonka ba, aikaima kasan inasonka, kawai de nakasa sakewa da kai ne har yau!" taƙare maganar tana me rausayar dakanta gefe tamkar yana ganinta..

Dr.Sadeeq dake zaune cikin luntsumemiyar kujeransa na office ya lumshe idanunsa haɗe da gyara zaman wayar akan kunnensa,  sosai shagwaɓan Zahrah ke sauƙar mai da kasala acikin jikinsa, yayinda idan yaji muryarta yake samun nutsuwa a cikin zuciya da ruhinsa...

"To meyasa bakya iya sakewa dani ne My Princess, kinkuwa san irin sonda nake miki?  inasonki Zahrah fiye da tunaninki,  amma bazaki gane hakan ba, sai idan nasameki a matsayin matata, na tabbata nan da 3 weeks kinzamo mallakina daganan kuma zaki gaskata soyayyata a gareki!" yafaɗi maganar tasa cikin  yanayi na shauƙi..

Saurin kulle idanunta  tayi haɗe da sanya hanu tarufe fuskarta, saikace wanda take aga banshi,  sosai maganarsa yasa taji kunya,, ta lura haka Dr.Sadeeq ɗin yake watarana baruwansa kansa tsaye yake faɗar maganar da zaisanya taji kunya.

"My Princess kinyi shiru" Dr.Sadeeq  yafaɗi haka a kasalance.

Numfashi Zahrah ta fesar haɗe da sake yin ƙasa da muryarta cikin shagwaɓan daya zamemata sabo tace "Munyi magana da Baffa, yace ku kawo kayan lefen duk sanda kuka shirya kawai"

Daɗi ne yakama Dr.Sadeeq harsaida yakasa ɓoye murnarsa idan kuwa hakane to tabbas acikin satin nan zai sanar da ƴan uwansa saisu shirya rananda zasu kawo kayan, shida zasuce yauma to tabbas da zaiso hakan.

"Naji daɗin maganarki My princess saboda haka kincancanci nabaki kyauta ta musamman, idan banzo da dare ba gobe zanzo insha Allah"

Murmushi kawai Zahrah tayi haɗi da cewa "Nagode amma kariƙe kyautarka bayanzuba"

"Meyasa?" yatambayeta cikin yanayi na ɓata fuska.

"Saboda hidiman da kakeyi yayi yawa, dan Allah kabari haka kaji!" taƙare maganar cikin yanayin shagwaɓa. 

"Inde akan kine Zahrah bazan taɓa gajiyawa ba, zanyi wani aiki yanzu zanƙiraki anjima kinji princess ɗina!" yafaɗi haka cike da lallashi.....

Haka sukayi sallama cike da kulawa ga junansu, yanzu kam tagama aminta da Dr.Sadeeq insha Allah kuma idan ta auresa zata basa farinciki me ɗorewa, iyaka iyawarta.....

Sosai Zaid yashaƙa da irin yanda Abid yasanyasa agaba yaketa yi masa dariya,,   tsuka Zaid yaja me tsayi haɗe da kawar da kansa gefe jiyake tamkar ya tashi ya rufe Abid da duka, idan banda iskanci taya zai sanyasa gaba yayi ta masa dariya bayan yagama jin matsalarsa...

Wani mugun kallo Zaid yajefawa Abid me ɗauke da tarin ma'anoni da yawa, ganin haka yasanya Abid saurin gimtse dariyarsa haɗe da kama hanun Zaid ɗin...

"Yi haƙuri Abokina, maganar ce tabani dariya"

Tsuka Zaid yakuma ja batare da yace komai ba.....

"Nafuskanci inda matsalanka ta dosa Zaid amma kuma nasan abune me wahala ka yarda da abun dazan faɗa ma"

"Bazaka gane yanda nakeji agame da'ita ba ne Abid, dakasan yanda nakeji a zuciyata da ka tausaya kasanar dani maganin matsala ta, kodai shine so ɗin da kake cewa?" Zaid  yatambayi Abid cike da damuwa...

"Ƙwarai kuwa Zaid wan nan shine SO, sai de naka SO'n ya banbanta da sauran soyayya'n, kai naka soyayya'r me tsanani kakeyi, wanda tariga da tajima acikin jikin ka batare da ka sani ba, ina da yaƙinin cewa tun farko Son Zahrah kake bawai sha'awarta ba kamar yanda ka ɗauka!" Abid yafaɗi haka da iyaka gaskiyarsa...

Nannauyar ajiyar zuciya Zaid ya sauƙe haɗe da sanya duka hannayensa ya dafe kansa wanda yake ɗan sara masa a hankali..   Tabbas yanzu kam ko yaso ko yaƙi dolensa ya yarda da maganan da Abid yafaɗa masa, domin kuwa idan har ba soyayya ba menene ke damunsa dayake sawa yakejin zafi a zuciyarsa? idan ba soyayya ba menene yake sanya tunaninsa hargitsewa da zaran yatuno Zahrah? idan ba soyayya ba menene yake sanya sa rasa sukuni da nutsuwarsa aduk sanda yatunanota kokuma yaganta? lallai kuwa soyayya baimasa adalci ba da bai sanar dashi kansa ba tun sanda yafarasa batare da yasani ba..  

Idanunsa da sukayi jajur dasu ya ɗaga haɗe da maida kallonsa ga Abid  "Inasonta Abid inasonta sosai!"

Waro idanu Abid yayi yana me kallon Zaid  idan da ba Zaid ɗin ne da gaske a gabansa ba, to tabbas da sai yace badaga bakin Zaid wa ƴan nan kalaman suka fitoba, yau Zaid da kansa yake cewa yakamu da son wata? lallai kuwa rayuwa tana shirin juyawa abokin nasa baya.

Miƙewa Zaid yayi daga zaunen da yake haɗe da sanya hanu ya kwashe wayoyinsa dake kan ɗan ƙaramin table ɗin dake aje gabansu.

Kallonsa Abid yayi cike da mamakin ganin yanda lokaci ɗaya yanayin Zaid ɗin ya sauya.

"Inakuma zaka?"   Abid yatambaya..

"Zanje gidansu Zahrah Abid, idanuna sun matsamin zuciyata har bugawa take Abid, ita kawai nakeson gani,  idan har zata amince inaso ayau base gobeba koda ƙarfe ɗaya ne  na dare  a ɗaura mana aure da'ita" yanakai wa nan a zancensa yayi tafiyarsa.. Hangame baki Abid yayi yana kallonsa harya ɓacewa ganin idanunsa.   Anyakuwa Zaid yana cikin hankalinsa? Kodai asiri yarinyar talakawan nan tayi masa ne?  Abid yajerowa kansa waƴan nan tambayoyin,  bayan yasan baida amsa bai kuma da me basa amasar...

Zahrah dake zaune tana gudanar da assigment ɗinta, wani yaro yashigo cikin gidan nasu haɗe da kwaɗa sallama..  Amsa masa Zahrah tayi batare da taɗago kanta takalli yaron ba..

"Wai ana ƙiran Zahrah a waje" yaron yafaɗa yana me kallon Zahrah domin kuwa yasan cewa itace wacce aka aikosa yayi ƙiranta..
Sai alokacin Zahrah taɗago kanta ta kalli yaron, haka nan taji gabanta yafaɗi, to waye kenan yake sallama da'ita? ta tambayi kanta, wayarta dake kusa da'ita ta ɗauka haɗe da dubawa, 1 missed call tagani na Dr.Sadeeq,  dayake wayartata a silent tasanyata shi yasa bataji ƙiran nasa ba, kenan shine yazo yaƙira wayarta bata ɗauka ba shiasa yaturo yaro.   "Jekace inazuwa" ta  bawa yaron amsa a taƙaice..

Miƙewa tayi haɗe da tattara takardunta tayi ɗaki.  Mayafi taɗauka   ta yafa akan kayan dake jikinta...

Tsaye yake ajikin motarsa yayinda yakifa kansa asaman  motar yana me kaɗa key ɗin motarsa dake riƙe a hanunsa..

Kanta a ƙasa tafito daga cikin gidan tana me duba wayar dake hanunta.  Tsayawa tayi cak bayan ta haɗe wani  miyau dayazo me ɗaci ya maƙale mata a maƙoshinta. 

Murmushi yasakarmata haɗe da soma takowa zuwa gareta..
Lokaci ɗaya idanun Zahrah suka sauya kala daga fari zuwa ja, juyawa tayi a fusace tanufi hanyar shiga gida, da sauri Zaid yasha gabanta haɗe da marairaice fuska cike da tashin hankali yasoma cewa....

"Dan Allah Zahrah kitsaya ki saurareni, dan Allah kada kimin haka Zahrah,  inaso ki saurare....." kasa ƙare maganar nasa yayi sakamakon kyakkyawan marin da Zahrah ta shimfiɗa masa akan  kyakkyawar fuskarsa...
Cikin ƙuna da kuma zafin zuciya     haɗi da raɗaɗi Zahrah ta haɗa yatsanta na tsakiya dakuma babbar yatsarta, ta kaɗa ade de fuskar Zaid duk da kuwa cewa yakerema tsayinta..

"Natsaneka tsana mafi muni, natsani jin kowani irin kalma ce da zata fito daga bakinka,  wlh wlh nayi rantsuwa sau biyu, idan har ka sake naƙara ganin fuskar  ka to zanyi maka abun da baka taɓa tunani ba!" cikin matsanancin ɓacin rai taƙare maganar tana me raɓan gefensa zata wuce,  Zaid da zuciyarsa tariga da ta karye baiyi ƙasa a guiwa ba yasake shan gabanta.

"Kimin duk abun da kikeso Zahrah, zanfi jin daɗima idan akace kece zakiyi silan mutuwa ta, dan Allah ki saurareni mana Zahrah!!" yaƙare maganar cikin rawan murya...

Kuka ne ya ƙwacewa Zahrah me tsanani cikin muryan kukan tasoma cewa.....

"Miye laifina Zaid? Menene aibuna? shin wani abu na aikata maka da ka zaɓi cutar da rayuwata? ashe de ganganci ne don na ɗau soyayyata na baka? me yasa ka yaudareni Zaid? meyasa dole saini kazaɓi ka tozarta? Kacutar da rayuwata ka dasamin ƙunci a cikin zuciyata, wlh natsaneka Zaid,  Idan har yaudara zata zamemaka abun ado mezaka amfana dashi acikin rayuwarka? Miye ribar aikata zina da fasiƙanci? Natsaneka Zaid! Natsaneka!! Bana fata Allah yaƙara haɗa fuskata da taka fuskar har gaban abada! Dan Allah kafita a rayuwata Zaid!!!" cikin matsanancin kuka taƙare maganar tana me durƙushewa ƙasa domin kuwa zuwa yanzu tsayuwa ya gagarewa ƙafafunta...

Idanun Zaid ne suka kaɗa suka zama jajur dasu tamkar wanda aka zuba musu jan barkono.   gaba ɗaya jikinsane yasoma ɓari, shi ɗin ma durƙusawa yayi agabanta cikin murya me tsananin rauni yaƙira sunanta,, saurin ɗaga masa hanu Zahrah tayi alaman batason jin komai daga garesa..

"Banason nasake koda jin muryarkane Zaid, kafita a rayuwata, wai mekake nema dani ne? ko kana tunanin zan sake aminta da kai ne? hmmm kayi babban kuskure Zaid idan kuwa har haka kake tunani,  zaifi maka kyau, kamanta dani kakuma manta da wacece ni, ni na barwa Allah cutarwan da kayi agareni, kuma insha Allah nasan zai ɗaukarmin fansa,, sai de inaso kasani cewa har abada bazan taɓa yafe maka ba, inaso kuma kada kamanta da cewar natsaneka !"  a fusace ta faɗa cikin gida haɗe da banko ƙofar gidan nasu. 

Tashi yayi daga durƙuson da yake haɗe da bin bayanta da kallo, gaba ɗaya zuciyarsa tagama karaya, wani irin abu yakeji ajikinsa yayinda kansa yayi masa wani irin masifaffen nauyi,  zafi yakeji azuciyarsa irin sosai ɗin nan.

Zahrah kuwa zamewa tayi jikin ƙofar gidan nasu tasaki wani irin kuka me tsuma zuciya. Se yaushene zata warke daga raɗaɗi dakuma ciwon abun da Zaid yayi mata?   ganinsa yasake tasomata da mikin daya ƙi warkewa tsawon lokaci acikin zuciyarta,  maiyasa Zaid yazame mata bala'i acikin rayuwarta? kuka tashiga yi sosai da sosai...

Zaid kuwa daƙyar ya iya jan ƙafafunsa yanufi motarsa,  kasa tuƙa motar tasa yayi, gaba ɗaya idanunsa duhu suke gane masa, tabbas bazai taɓa iya tuƙa mota yana a irin wan nan halin ba,, da ƙyar ya'iya laluɓa wayarsa yaƙira driver'nsa... Mintuna kaɗan drivern Zaid yazo ya wuce dashi....

Saida tayi kukanta son ranta har sai da taji kanta yasoma ciwo kafun ta tsagaita, haɗe da miƙewa daga jikin ƙofar tashige cikin gida, direct ɗakinta ta wuce ta kwanta numfarfashi kawai take sauƙewa, lokaci ɗaya zazzaɓi yarufeta, harsaida tajawo mayafi ta lulluɓi jikinta....

Sanda yashiga falonsa ko gani bayayi sosai,  wani irin ciwo kansa ke masa me tsanani wanda yasanya idanunsa sukayi nauyi,  da ƙyar ya'iya jan ƙafansa yashiga ɗaki,  kalaman Zahrah ne sukeyi masa yawo acikin kansa,, yatsani jin kalmar tatsaneshi da take yawan faɗa ɗin nan,  wlhy a gurinshi da ta faɗi wan nan kalman gwamma ta sharara masa maruka koda kuwa guda biyarne akan ƙuncinsa..     Ya yanke shawara da de yakasance a irin wan nan yanayin ya gwammace yafita daga cikin hayyacinsa idan yaso bayan wasu tsawon lokaci yadawo cikin hayyacin nasa,,  wasu ƙwayoyin magani yaɗauko harkala biyu, wanda suke gusarwa mutum da hankalinsa, maganin suna da hatsari sosai hakan nema yasanya ba'a sai dasu a bayyane sai de a ɓoye, kuma suna mugun sa bacci sosai...   Saida ya ɓalli guda uku uku daga jikin kowani sachet, kafun ya watsa maganin cikin bakinsa, wan nan karon ko ruwa baisha ba haka ya haɗiye magungunan,  yanda kalaman Zahrah ke dawowa cikin kunnensa yafi komai ɗaga masa hankali,  kwanciya yayi lamo akan gado yayinda yake ƙwato numfashinsa dake ƙoƙarin ƙwace masa da ƙyar.  wani irin fusga numfashinsa yayi lokaci ɗaya kuma komai najikinsa ya sake...

Zahrah kuwa zazzaɓine ya dirarmata me zafin gaske, wanda yasanya lokaci ɗaya jikinta yasoma ɓari ta fara rawan ɗari, har zuwa yanzu hawayenta bai tsaya ba. Zaid ya cuceta itakam duk irin ƙuncin daya jefata a baya bai ishe saba saida yakuma da wowa gareta, sai yaushene hawayenta zasu tsaya? sai yaushene zata samu farinciki ingantacce wanda babu algus acikinsa? tunda ta haɗu da Zaid ƙuncin rayuwarta yasoma, wani irin annoba Zaid yazame mata ne?.....

*(Kuyi haƙuri kuyi manage da wan nan, headache ke damuna, nida Zaid duk cutarmu ɗaya😜 banyi posting da wuri ba wlh network ɗin sim ɗi nane gaba ɗaya ya ɗauke😥)*

   *29/December/2019*

*Follow me on Whatsapp and Wattpad*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

       *SHU'UMIN NAMIJI !!*

 
      *Written By*
*Phatymasardauna*

*Dedicated To My Brother KHABIER*

*🌈Kainuwa  Writers Association*

_{United we stand and succeed; our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}_

*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*

         *WATTPAD*
   @fatymasardauna

*(💗Wannan page ɗin baki ɗayansa kyautane agareku my wattpadi'ans  inagodiya sosai a gareku💗)*

*Editing is not allowed📵*

   
     *CHAPTER 72 to 73*

Baki Labisat dake tsaye taturo gaba haɗe da ɓata fuskarta duk wai akan don  Mom ɗinsu tace taƙira mata Zaid a ɓangarensa ne yasa take wan nan abun...

"Tsayuwan uban me kike bacewa nayi ki ƙiramin yayanki ba!" Mom tafaɗi haka cike da faɗa, ganin Labisat ɗin bata da niyar zuwa aiken datayi mata.

"Mom wlhy tsoro nakeji kada naje ya masifance ni!" Labisat tafaɗi haka cikin shagwaɓa. 

Harara Mom tawurga mata bashiri Labisat takama hanyar fita daga cikin falon...
Aranta kuwa roƙon Allah take yasa idan taje kada ya masifanceta saboda shi abun faɗa baya masa kaɗan ko kaɗan,  jiya jiya dawowanta daga boarding school amma Mom zata haɗata da masifan Yaya Zaid (Su yaya manya😂)

Kusan sau huɗu Labisat tana knocking ƙofar daze kaita cikin falonsa, amma shiru ba amsa, hakan yasanya tatura ƙofar tashiga,,   bakowa acikin falon sai daddaɗan ƙamshinsa dake tashi.. Direct ƙofar bedroom ɗinsa tanufa haɗe da soma knocking ƙofar,, jin shiru ne yasanya tashiga ƙiran sunan sa...

"Brother! Brother!"  ko gyaran murya bataji yayiba balle tasa ran zai amsa mata, batama tabbatar yana cikin ɗakin ko baya ciki ba..
Gajiya tayi da knocking ƙofar ta juya tayi tafiyarta...

"Mom inaga fa kamar Bro bayanan domin nayita knocking door ɗinsa amma bai amsa ba"

"Tabbas yana cikin gidan nan Labisat domin kuwa tunjiya daya shigo baifita ba, har me gadi na tambaya naji ko yaga fitarsa amma yacemin tunjiya daya shigo bai fita

Please Login or Register in order to submit comment