Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mata da maganan auren Zaid, daɗine yakusa kasheta ganin irin damar da Allah yabata, ashe bata saniba gidan mutuwa takawo kanta, ita da har jinkanta tasomayi, har ɗagawa takeyiwa ƙawayenta, ita adole ta auri namijin duniya, batasan cewa wahala zata ruska ba, ta ɗauka cewa holewa zatayi,  harta fara tunanin ƙasashen da zata sasa yakaita, sai gashi haɗuwarsu ta farko ma da lafiyayyen mari ya tarbeta...

Zaid kuwa yana shiga cikin ɗakinsa yafaɗa kan gado haɗe da lumshe idanunsa, kansa ne yake matuƙar sara mae, tun jiya yakejin ciwon kan, amma yau abun ya tsananta sosai,     wata tsuka yaja me sauti, haɗe da sake gyara kwanciyarsa, shi wannan auren ma da aka laƙaba masa kaɗai ya isa ƙara masa ciwon kai, shiba yaro ba, shiba bagidaje ba amma ankama anyi masa auren dole...
******

Tsaye take agaban dinning area, ta kafesa da manya manyan idanunta, yayinda shikuwa baimasan tana kallonsa ba, hankalinsa gaba ɗaya yana ga agogon dayake ƙoƙarin ɗaurawa a tsintsiyar hanunsa..   Bakomai yasa take kallonsa ba, face kyawun da taga yayi mata,  shadda ne milk colour ajikinsa ɗinkin riga da wando, rigar ta tsaya iyaka guiwarsa, yayi kyau sosai yasha hularsa light brown wanda taƙarawa kwalliyartasa kyau..  Yana ɗago kansa suka haɗa idanu, da sauri ta kawar da idanunta daga kansa, haɗe da sunkuyar da kanta ƙasa.

Murmushi yayi haɗe da takowa yaƙaraso inda take, hanu yasanya ya rungumota ta baya.

"Namiki kyau ne haka kiketa kallo na?" yatambayeta yana me shaƙan daddɗan ƙamshin jikinta.

Ɓata fuska tayi haɗe da cewa

"Namiji kuma dama yana kyau ne idan yayi kwalliya?"

Dariya maganar ta ta ta basa, juyo da ita yayi yazamana suna fuskantar juna.   

"Eh mana bakisan maza sun mafi mata kyau ba?"  ya faɗi haka yana me ƙarewa fuskarta kallo.

Idanunta ta waro haɗe da  cewa "Maza sunfi mata kyau? cab aikuwa nidai baka fini kyau ba"

Dariya yayi haɗe da ɗan jan hancinta.
"Nafiki kyau sosai ma, nifa banasa jan baki, bana shafa powder, bana sa kwalli, bana kumayin jagira, haka kuma bana wani shafa mai wanda zai sa fatata tayi kyau, komai nawa daga Allah ne, ku kuma mata kullum cikin shafawa da gogawa kuke, kinga kenan dagaske munfiku kyau" yafaɗi maganar yana me ɗan ƙara fito da idnunsa waje.

Duk da tana cikin fushi, amma sai da tayi dariya.  

"Kafaɗi komai ma, amma nidai bazan yarda cewa  wai kafini kyau ba"
tafaɗi haka tana me ƙoƙarin zame jikinta daga cikin nasa. 

Sake riƙeta yayi gam haɗe da cewa

"Dagaske namiki kyau? naga har wani kishi na kike"

Ɗan ƙaramin bakinta taturo gaba haɗe da shagwaɓe fuskarta.

"Idan nayi kyau kaima baka barina nafita, to me yasa kai kakeson yin kyau ako da yaushe? kana tunanin bazanji haushi bane idan wata ta kalleka!" kafun taƙare maganar ma tuni idanunta sun soma kawo ruwa.

"Eh kumafa hakane, harma kintunamin, akwai wata kuwa a asibitin mu, kullum saitace namata kyau, sannan kuma saitace wai ina matuƙar burgeta, gaskiya nima kuma tana burgeni dan a ƴan kwanakin nan harma na fara tunaninta, to mezakice akanta?" yaƙare maganar yana me ɗaga mata giransa ɗaya.

Baki kawai tasake tana kallonsa yayinda wani malolon baƙin ciki ya tokare mata zuciya. Da ƙarfi ta soma turesa tanason ƙwace jikinta daga nasa.   

Ganin haka yasanya yasake riƙeta  da kyau haɗe da cewa

"Mekikeyi haka?"

"Kafi kowa sanin abunda nakeyi,  inatunanin tsayuwan da kakeyi anan kana ɓata lokacin kane, domin wacce kake muradi tanacan tana jiranka, koba don itane kayi kwalliyar ba? ai bana tunanin ni inada wani amfani a wajenka, ka sakeni kaje tayaba kwalliyar taka banaso na ɓata bata gani ba."

Dagajin yanda take maganar kasan kishine tsantsa kecinta, domin kuwa har hawaye sun gangaro daga cikin idanunta..

Dariya sosai yashiga yi batare daya sake ta ba.

"Kasakeni nace, ai nasan baka buƙata ta!" tafaɗi haka tana me yunƙurin ƙwace hanunta dake cikin nasa.

Da ƙyar ya iya tsagaita dariyan   nasa, yashiga dubanta da kyau, yasani dama da sannu zuciyar Zahrah zata nutsa acikin ƙaunarsa sosai, gashi kuma yafara ganin alama tunda har kishinsa ya bayyana acikin idanunta..

Fuskarta yatallafo da tafukan hanunsa haɗe da sanya bakinsa yashiga lashe hawayen dake fitowa daga cikin idanunta.

"Bazan iya jure ganin matata tana kuka ba, ki kwantar da hankalinki kinji me daɗi na, babu wata mace da ta isa ƙwace miki doctor ɗinki,  ketawace ni ma kuma naki ne,  babu wata kuma danake tunani bayanke kiyarda dani!!" yafaɗi maganar cikin lallausan murya yana me ƙara riƙe fuskarta acikin tafukan hanunsa. 
Ajiyar zuciya ta sauƙe wanda harsaida ya bayyana afili, har cikin ranta taji daɗin maganganunsa, amma kuma afili bata nuna  hakan ba, ƙoƙarin ƙwace kanta daga jikinsa tacigaba dayi.

"Nine bakyaso ko? shikenan tunda bakyaso nariƙeki" yafaɗi haka yana me sake ta yanufi hanyar fita daga cikin falon.  Da sauri ta je ta rungumesa ta baya, wani murmushi yayi haɗe da juyowa  gareta yazamana suna fuskantar juna.

"Dan Allah kada ka ƙaramin irin wannan wasan, gashi duk kasa ma naji natsani komai!" tafaɗi haka a shagwaɓe.

Murmushi yayi mata haɗe da sanya hanunsa yaɗanja kumatunta. 

"Bazan sakeba, kiyi haƙuri kinji me daɗi na!"

Da sauri ta cusa kanta   acikin ƙirjinsa haɗe da sanya hanunta ta  mintsineshi acikinsa.  Da ɗan ƙarfi yace "Ahhhshhhh!"

Dariya tayi masa haɗe da yi masa gwalo ta wuce zuwa dinning domin dama abinci take haɗawa.
Biyota yayi kan dinning table ɗin suka shirya abincin atare,  acikin plate ɗaya sukaci abinci, gaba ɗaya yanzu doctor yagama shagwaɓata abinci ma shiyake bata abaki, har sai ta ƙoshi,   tana ajiye cup ɗin ruwan dake hanunta, ta ɗan saci kallonsa, ta lura tun ɗazu yaketa kallonta.

"Kaima nayi maka kyaun ne, kaketa kallona haka?" ta tambayeshi.

Murmushi yayi mata haɗe da cewa
"Ae ni dama kullum kinamin kyau,  ke mai kyauce ai ako da yaushe, amma kuma..." baiƙarisa maganar dake cikin bakin nasa ba yayi shiru.

"Amma kuma me?" ta tambayeshi da sauri domin atunaninta ta zaci zaice amma bata masa kyau sosai ne.

"Amma bakyason bani abun daɗi na, please yau ki tausayamin kinji, bazan iya bacci bafa yau idan baki bani ba!" yafaɗi haka cikin sigar shagwaɓa haɗe da ɗanyin ƙasa ƙasa da muryarsa.

Maganganunsa kunya suka bata da sauri ta sanya hanunta ta rufe fuskarta,   jawota jikinsa yayi haɗe da sanya bakinsa adai dai saitin kunnenta cikin muryar raɗa yace
"Bazan iya jurewa ba Zahrah, inaso akullum kina bani kanki sau ba adadi, inason kasancewa tare dake ako wani lokaci" bakinta yashafo da hanunsa haɗe da lumshe idanunsa.   "Nayi missing waƴannan lips ɗin amma yau zanyi musu sucking na musamman har ma...." bata jirayi jin ƙarshen zancen nasa ba ta ruga da gudu zuwa cikin ɗaki, bazata iya cigaba da sauraran waƴannan manya manyan kalaman nasa ba. Murmushi kawai yayi haɗe da miƙewa yafice daga cikin falon, dama sabiti zaije.

Tanajin fitar motarsa acikin gidan ta sauƙe ajiyar zuciya haɗe da lumshe idanunta, kwanciyarta ta gyara, tana me tuno kalamansa,    itakanta tana tsananin son taji ta ajikinsa, musamman idan fatarsu ta haɗe waje guda hakan na haifarmata da wani irin yanayi me daɗin gaske,  kallonta ta mayar ga agogon bangon dake kafe acikin ɗakin.   Ƙarfe 11 na rana yau take da lecture saboda haka tana da ɗan sauran lokaci, domin yanzu ƙarfe 10 ma batayi ba, wani English Novel  mesuna  ( Just A Friend)   tajawo haɗe da buɗe chapter'n da take ta soma karantawa, agurin wata ƴar class ɗinsu ta karɓo  shi.
****

Ƙarfe 4 na yamma dai dai suka fito daga cikin lecture ɗinsu wanda shine na  ƙarshe a  wannan ranan, direct library ta nufa saboda akwai wani littafi da takeson dubawa, kasancewar akwai assigment ɗin da aka basu, idan ta samu littafin kuma sosai zai taimaka mata wajen yin assigment ɗin cikin sauƙi.     Gaba ɗaya hankalinta naga littafin da take dubawa, sam bata damu da mutanen dake wajenba kasancewar kowa karatu kawai yakeyi.   Tana zaro littafin daga ma'ajinsa ta saki murmushi,  juyawa tayi daniyar tafiya idanunta suka sauƙa akan shi, waro manyan idanunta waje tayi haɗe da sakin littafin yafaɗi ƙasa.   Jikinta ne yaɗauki rawa da sauri ta tsugunna ta ɗauki littafin haɗe da nufar hanyar waje, tsabar sauri har ƙafafunta harɗewa suke,  batayi auneba saiji tayi ta buge mutum, da sauri taɗago don ganin waye ta buge, shiɗinne dai tsaye a gabanta yana me kallonta da jajayen idanunsa, da sauri taja baya, haryanzu jikinta rawa yake kamar wacce taga mutuwarta.

"ZAHRAH!"

yaƙira sunanta cikin wata irin murya me matuƙar rauni.

Kusan mintuna uku takasa amsa masa da ƙyar ta iya motsa bakinta,

"I..na..da au..re" 
shine kalaman da suka fito daga cikin bakinta awawware batare kuma da ta shiryawa fitowar kalmomin ba.

Rumtse idanunsa yayi haɗe da dunƙule hanunsa. Cikin murya me ɗaci haɗe da bushewar maƙoshi yace 

"Nasani!"

Bazata iya jurewa ganinsa ba da sauri ta bi ta wata hanyar ta wuce da gudu, ko takan littafinta daya kuma faɗuwa batayi ba.

Bayanta yabi da kallo haɗe da tsugunnawa yaɗauki littafin, juyawa shima yayi yafice daga cikin library ɗin. Sai dai ko daya fito,  ko ƙyallinta bai gani ba.

Zahrah kuwa tana fitowa daga cikin library ɗin direct wani ɗan corridor wanda mutane basu cika yawan bi ba tanufa, kaitsaye ta tsinci kanta awani fili wanda bakowa acikinsa sai shuke shuke,  zama tayi akan wani benci dake wajen, haɗe da fashewa da kuka,  tashiga ukunta itakam, wannan wace irin jaraba ne, meyasa Zaid bazai barta ta huta bane,  jitayi lokaci ɗaya ƙirjinta yayi mata nauyi kamar anɗaura mata gungumen dutse, wayarta dake ringing ta kalla,  Dr.Sadeeq ne ke ƙira amma bazata iya ɗagawa ba, ahalin da take ciki yanzu ma batasan me zata ce masaba idan ta ɗaga.  Da ƙyar ta'iya tashi tabi ta ƙofar baya tafice daga cikin makarantar gaba ɗaya, tana fita ta tare me taxi haɗe da gaya masa inda zai kaita, ko ciniki basuyi ba ta faɗa cikin motar haɗe da ce masa yaja suje.

Yana kawota ƙofar gida ta basa kuɗinsa haɗe da ficewa acikin motar ta kutsa kanta cikin gidanta.

Bata damu da duhun dake cikin ɗakin ba  haka ta faɗa kan gado ko mayafin dake jikinta bata cire ba..  Zazzaɓine me zafin gaske ya rufeta alokaci guda..

Zaid kuwa yana fita daga cikin library ɗin direct wajen da motarsa ke fake ya nufa, buɗe murfin motar yayi, ya shiga ya zauna, kifa kansa yayi akan steering motar yana mejin zafi da raɗaɗi na ratsawa har cikin ƙwaƙwalwarsa,   akaro nafarko daya yardarwa kansa cewa zai haƙura da Zahrah kenan, tabbas yazama dole ya yi haƙuri da ita koda kuwa hakan nanufin mutuwarsa ne,   yau Zahrah da bakinta ta faɗa masa cewa tana da aure, maganar dayajita tamkar anwatsa masa tafasheshshen ruwan zafi,   bayajin zai iya yin rayuwa idan babu Zahrah, amma kuma ayau yaɗaukarwa kansa alƙawarin cireta acikin zuciyarsa, duk da yasan hakan zai zamo kamar yaudaran kansa ne yakeyi, amma kuma dole zai jarraba....

****

Cikin matsanancin tashin hankali Dr.Sadeeq yadawo gida, yaje makarantar su Zahrah yanemeta sama da ƙasa bai ganta ba, gashi yaƙira wayarta bata ɗauka ba daya ƙara ƙiranta kuma yaji wayar akashe, hankalinsa atashe yake sosai, yana shigowa cikin ɗakin yadanna madannin ƙoyin wuta take haske ya gauraye gaba ɗaya ɗakin, wani irin ajiyar zuciyar dabai taɓa yin irinta ba ya sauƙe, haɗe da lumshe idanunsa, da sauri yaƙaraso gareta haɗe da sona ƙiran sunanta, jin shiru bata amsa saba yasanya yakai hanunsa jikinta, zafi zau yaji jikin nata, take tausayinta yakamasa, shidai yasan hakanan Zahrah bazata dawo gida bata jirasa yazo ya ɗauketa ba, sannan kuma haka nan bazata kashe wayarta ba.  Zama yayi akan gadon haɗe da ɗagota ya kwantar da'ita ajikinsa.  Mayafin dake jikinta ya zare haɗe  da sanya hanu yashiga shafa kumatunta.

 "Zahrah!" yakuma ƙiran sunanta cikin sassanyar murya.

"Na'am!" ta amsa masa cikin wata irin murya, dagaji kasan tanajin jiki.

Kanta yashiga shafawa ahankali, zuge mata zip ɗin rigar dake jikinta yayi, haɗe da cire  rigar gaba ɗaya daga jikinta, kwantar da ita yayi akan gado, kana ya  nufi wajen da ɗan ƙaramin drawer ɗinsa ke aje,  maganin da zai  sauƙar  mata da zazzaɓi cikin gaggawa yaɗauko.

Dakansa ya lallaɓata tasha maganin, abun gwajinsa ya ɗauko yashiga gwadata, cutar dayaga tana damunta shiyayi matuƙar ɗaga masa hankali, wani irin zufane yashiga keto masa.

"Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un!!"

kawai yake ambata acikin zuciyarsa,  duk sanyin A.C'n dake cikin ɗakin  amma Dr.Sadeeq gumine ke tsastsafowa daga jikinsa.

"Taya akayi Zahrah takamu da wannan ciwon?" tambayar dayake tayi mawa kansa kenan.....

(😲Wani ciwo mun banu🙆‍♀

Banyi editing ba idan kunga typing error kuyi haƙuri!)

     
   *Thursday 30/January/2020*

    

         *Fatymasardauna*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇


*SHU'UMIN NAMIJI !!*


*Written By*
Phatymasardauna


*Dedicated To My Brother KHABIER*


*🌈Kainuwa Writers Association*

_{United we stand and succeed; Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}_

*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*

*WATTPAD*
@fatymasardauna

*Editing is not allowed📵*


*CHAPTER 104*



Hanu yasanya akan goshinsa ya share zufan dake tsastsafo masa. Tashi yayi tsaye haɗe da tattara kayan aikin nasa ya ajiye a gefe. Direct bathroom ya shiga haɗe da sakar mawa kansa ruwa....

Tun shiga wankansa har kawo yanzu da ya fito yake shirya kansa tanajin sa,amma idanunta alumshe suke kamar meyin bacci.

Zama yayi akan gadon haɗe da ɗagota ya jawota zuwa jikinsa, kanta ya kwantar akan ƙirjinsa haɗe da soma shafa bayanta a hankali, still ɗaya hanunsa yasanya yana me shafa gashin kanta.
Cikin murya me ɗauke da nutsuwa ya soma cewa.

"Meyasa haka Zahrah? me yasa kika zaɓi ƙuntatawa kanki? tun bayauba nasha faɗa miki cewa ki daina yawan sanya kanki cikin damuwa, na faɗa miki kirage yawan tunani, har acikin zuciyata inamiki wani irin so wanda bansan iyakacinsa ba, bana so nagan ki cikin damuwa, ganin farincikin ki yafiyemin komai aduniyarnan, kinkuwa san meke damunki yanzu? damuwar da kike yawan sanya kanki aciki tahaifar miki da matsala wanda baikamata ace yarinya ƙarama kamarki tana ɗauke da wannan ciwonba, mekika nema kika rasa aduniyar nan? banaso ki ɓoyemin komai inaso kifaɗamin shin azamana dake ina cutar dake ne? ko kuwa inayi miki wani abu wanda ba kya so ne?"

Kanta tashiga girgizawa alamar "A'a" tuni hawaye sungama wanke mata fuska.

"To idan dai har hakane yakamata ki faɗamin damuwarki koda nima zanji sauƙi acikin zuciyata"
yafaɗi haka a gareta cikin tausasawa.

Kuka ta fashe dashi haɗe da sake rungumeshi cikin kukan tace.

"Nakasa daurewa ne, nakasa daure zuciyata, idan dai yana cikin wannan duniyar bazai taɓa barina ba, bazai barni ba harsai yakasheni sannan zai huta, naso namanta dashi amma nakasa, bansan meyasa ba kullum zuciya ta me rauni take kasancewa akansa, dan Allah kayi haƙuri banfaɗi haka agareka don na ɓata ranka ba, kawai dai nafaɗi abun dake zuciyata ne!" taƙare maganar tana sheshsheƙan kuka..

Rumtse idanunsa yayi haɗe da cije laɓɓansa, dama yasani duk duniya damuwarta bazata wuce akansa bane yajima da sanin wannan. Ɗagota yayi daga jikinsa yazamana suna fuskantar juna. Cikin wata irin murya yace..

"Ba iya miji bane ni agareki, ni ɗan uwa ne wanda baki da kamarsa, najima da sanin cewa har yanzu Zaid yana cikin rayuwarki, nasan Inasonki so me tsanani, sai dai kuma duk irin soyayyar danakeyi miki Zaid yafini sonki, da ace zan iya to da najima da mallakawa Zaid ke amma bazan taɓa iyawa ba Zahrah nima masoyinki ne na haƙiƙa kamar yanda Zaid yakejin bazai iya rayuwa ba idan babuke, haka nima nakeji ajikina, batun yauba nasan Zaid yana nan kwance aƙasan zuciyarki, bana yaudaran kaina nakan faɗi abu ne aduk yanda natsaya na fahimceshi, koda kuwa abun dana faɗa bazasuyimin daɗin ji acikin kunnuwa naba, duk da kuwa nina faɗesu, bana ɓoye gaskiya saboda biyan buƙatar kaina"

Kafaɗunta yakama da duka hannayensa. Ci gaba yayi da cewa
"Yanzu zanyi miki magana ne a matsayina na mijinki kuma wanda yake sonki, har yanzu duk da na aureki kina aƙarƙashin ikona bazan taɓa takuramiki ba, inamatuƙar son farincikin ki, idan har kinaji ajikinki cewa bazaki iya rayuwa ba idan babu Zaid shikenan zan iya....." rumtse idanunsa yayi da ƙarfi ya kasa ƙarasa maganar, da sauri ya miƙe yafice daga cikin ɗakin.

Zahrah wanda tun fara maganarsa tayi saroro tana kallonsa, tana ganin ficewarsa ta fashe da kuka.

"Me doctor yake shirin cewa? badai zai haƙura da ita ba?" tambayar da tayiwa kanta kenan, sam haka bazai taɓa yiwuwa ba, wace irin banzace ita? taya ya zata iya jure rashin masoyi kamar doctor Sadeeq? kuka tashiga rerawa me tsuma zuciya, kaiconta tunda dai harta bari Dr.Sadeeq ya iya sanin sirrin dake cikin zuciyarta, yanzu da wani idanu zata kalleshi bayan yasan cewa akwai son wani maƙare acikin zuciyarta? lallai koda ace Zaid ubantane yakamata tayi ƙoƙarin mantawa dashi....

Dr.Sadeeq kuwa yana fita daga ɗakin falo yanufa, yanazuwa ya buɗe fridge haɗe da ɗaukan goran ruwa yakafa a bakinsa, saida yasha ruwan fiye da rabin gora kafun ya kai goran ƙasa, ajiyar zuciya kawai yake sauƙewa akai akai.

"Meyake shirin aikatawa ne haka?" yatambayi kansa. Girgiza kansa yayi haɗe da ware idanunsa, idan yace zai iya rabuwa da Zahrah to yayi ƙarya, amma kuma idan yazamana bashine zaɓin ranta ba, to fa tabbas yazama dole ne yarabu da ita, badon kowaba saidon samun ingantaccen farincikinta, yasani shima abune me wahala ya iya jure rashinta, amma kuma itama yakamata aduba zuciyarta, yakamata tasamu abun da takeso.
key ɗin motarsa dake aje kan ɗan ƙaramin stull dake falon ya ɗauka haɗe da sakai yafice gaba ɗaya daga cikin falon, motarsa yashiga ya fice daga cikin gidan, bayajin zai iya zama acikin gidan gaba ɗaya zuciyarsa a dagule take..

Zahrah kuwa tanajin alamar fitansa daga cikin gidan tasake fashewa da kuka, duk da kuwa zafin zazzaɓin dake damunta. Kuka tayi sosai amaimakon zazzaɓin nata ya ragu sai gashi ya ƙara hawa, to taƙi tabar zuciya da ƙwaƙwalwanta su huta...

****

Da ƙyar ya iya kai kansa gida, tsabar yana acikin wani irin yanayi har idanunsa soma rufewa sukayi, yazamana duhu duhu kawai yake gani, hanunsa dafe da saitin zuciyarsa yafito daga cikin motar, taku biyu yayi duhu ya mamaye duka idanunsa take wani irin juwa ta ɗebesa saigashi yashe a ƙasa bayako da numfashi, da gudu ma aikatan gidan sukayo kansa suna ƙiran sunansa
"Oga! Oga!!"
Oga baimasan sunayi ba, wani daga cikin masu bawa flowers ruwa ne ya ranta aguje yaje yasanarwa Mummy dama Dad na nan atare suka fito amatuƙar ruɗe.

Ganin da suka mawa Zaid yashe a ƙasa yafi komai ɗaga musu hankali, da taimakon ma'aikatan wajen Dad yasanyasa amota direct suka wuce asibiti Mom sai kuka take.

Emergency aka karɓesa, Lallashin duniya Dad yayimawa Mom akan tayi shiru ta daina kuka amma taƙi, duk da cewa tana fushi dashi amma bata ƙaunar taga ko taji wani abu yasameshi, yanzu idan akace ya mutu yazatayi da rayuwarta?

Sama da 1 hour likitoti suka kwashe akansa suna bashi taimakon gaggawa. Ɗaya daga cikin likitotin ne ya kalli Dr.Bilal haɗe da ɗaga masa kai alamar wai Zaid ɗin babu rai ajikinsa. girgiza kai Dr.Bilal yayi alamar bai yarda cewa babu rai ajikin Zaid ɗin ba..

Hmmm likitotin nan sunsha matuƙar wahala kafun suka samu numfashin Zaid ya dawo dai-dai. Dukansu haka suka fito suna gumi domin kuwa da fari harsun cire rai dashi, sun ɗauka dagaske ya mutu.

Da gudu gudu sauri sauri Dad yataho wajen Doctor Bilal, hanun Dad Dr.Bilal yakama suka wuce office ɗinsa.....

"Yajikin nasa doctor? dan Allah kafaɗamin wani hali yake ciki a yanzun?" Dad yatambayi Dr.Bilal cikin yanayi na matuƙar ruɗewa.

"Ka kwantar da hankalinka Alhaji, yau Zaid ya hau matakin ƙarshe wanda da taimakon Allah muka samu da ƙyar muka shawo kan matsalan, amma bazan taɓa ɓoye maka ba idan har yasake shiga cikin yanayi irin wannan to fa tabbas wata ƙila saidai haƙuri, ba'aja da ikon Allah amma kuma fa da matuƙar wahala idan zai sakeyin numfashi, dama wannan shine matakin ƙarshe kuma gashi yakawosa idan irin haka tasake faruwa kuma to saidai dukanmu muyi haƙuri, haka Allah dama yake abunsa, duk wani me rai mamaci ne, koda ciwo ko babu ciwo, watarana dole mutum saiya mutu idan lokacinsa yazo, haka kuma gaba ɗaya zamu zama tarihi, saidai aba da labarin mu kamar yanda aka bamu na waƴanda suka shuɗe kafun zuwanmu iyaye da kakanninmu kenan!" Dr.Bilal yafaɗi haka yana me tattara nutsuwarsa ga Dad.

Gumi kawai Alhaji Ma'aruf ke sharewa sai ambatan
"Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un!" yakeyi gaba ɗaya ji yayi duniyar tayi masa nauyi.

"Doctor menene mafita?" Dad yatambayi Dr.Bilal cikin sanyayewar guiwa.

"A yanzu kam dai bamu da mafita Alhaji Ma'aruf, sai dai mujira muga me Allah zaiyi, wataƙila Zaid zai iyakaiwa kwana uku batare daya farka ba, wataƙila kuma ko nanda kwana biyu ya farka, amma yazama dole ku kula dashi, yanzu bakamar da bane, yanzu abu kaɗan na ɓata masa rai zuciyarsa zata hau zafi, sannan kuma idan ya yawaita yin tunani to fa akwai babbar matsala, yazama dole ku tsaya akansa ku lura, akwai magungunan dazan rubuta muku, idan yatsaya akansu insha Allah zasu taimaka masa sosai."

Sai alokacin Alhaji Ma'aruf ya ɗanji sanyi acikin ransa.

"Nagode ƙwarai Dr.Bilal kuma Insha ALLAH zamu kiyaye sosai!" Dad yafaɗi haka yana me miƙewa tsaye. Musabaha sukayi da Dr.Bilal kafun ya fice acikin office ɗin.

*****

A daddafe ta tashi tayi sallan isha. Tana kan sallayan bata tashiba yashigo cikin ɗakin, idanunta ta zuba masa, bada kayan da yafita ya dawo ba, yanzu rigane da wando na jeans ajikinsa, kallonsa takeyi kamar wani wanda bata taɓa ganinsa ba, shima kallonta yayi haɗe da yi mata murmushi, ya wuce cikin bathroom, mintuna kaɗan yafito daga cikin bathroom ɗin.

"Kizo kici abinci" yana faɗa mata haka yafice daga cikin ɗakin.

Wani irin kunyan sa ne yaka mata, amma kuma babu yanda zatayi, abundake cikin zuciyarta ta faɗa.

Miƙewa tayi sumi sumi ko hijab ɗin dake jikinta bata cire ba ta fita zuwa falo.

Zama tayi akan sofa kusa da inda yake zaune, haɗe da takure jikinta waje ɗaya, shawarma ne da gasashshen kifi (roasted fish) ya sayo musu, tura mata plate ɗin yayi gabanta.

"Kici sai kisha magani" yafaɗi haka fuskarsa ɗauke da ɗan murmushi, kallonsa tayi kamar zatace dashi wani abu kuma saita fasa tasoma cin abincin da kaɗan kaɗan. Shikuwa sannu a hankali yake sipping country yoghurt ɗinsa yana me kuma latsa wayarsa.

Haka suka zauna shiru babu me cewa da ɗan uwansa ƙala.

Tana kammala cin abincin ya bata wasu magunguna daya shigo dasu, babu musu ta amsa tasha. Ganin yatashi yabar falonne yasanya itama ta tashi ta koma ɗaki, wanka tayi kana ta fito ta sanya wata sleeping gown wacce ta tsaya iyaka cinyarta, ko guiwa bata ƙarasa ba, sosai rigar tayi mata kyau ta kuma fito da farar fatarta fili, dogon gashinta ta kama ta tubke a tsakiyar kanta haɗe da ɗaureshi da ribbon, turarenta me daɗin ƙamshi ta shafa, tana nan tsaye a cikin ɗakin yaturo ƙofar ɗakin yashigo.

Wani irin yawu ya haɗiye a maƙoshinsa, sanda idanunsa sukayi masa tozali da ita, sosai tayi kyau acikin rigar, ga fararen cinyoyinta sun bayyana kansu a fili, da ƙyar ya iya daure zuciyarsa, murmushi kawai yayi mata haɗe da kawar da kansa gefe, shi kaɗai yasan me yakeji acikin zuciyarsa, yana tsananin kishin matarsa, kamar yanda yake tsananin sonta.

Kan gado ta koma ta kwanta, agogon hanunsa yacire haɗe da cire rigarsa, 3 guater jeans yasanya..

Zama yayi a gefen gadon haɗe da jawo laptop ɗinsa yasamo dannawa, dama yanada ayyukan da suka masa yawa yanaso ya ɗan ragesu, bayaso ya kwanta shiru tunani ya damesa.

Hanu tasa ta share hawayen dake fitowa daga cikin idanunta.

"fushi Dr.Sadeeq yakeyi da ita kenan?" tambayar da take ta yiwa kanta tun ɗazu kenan, bazata iya jure fushinsa akanta ba, duk da baifito ya nuna mata hakan afili ba, amma duk wasu alamu sun nuna hakan, bayason yi mata magana me tsawo sannan kuma baya sake mata kamar yanda ya saba, idan tabarsa haka batayi masa adalci ba, ayanzu bata da wani wanda ya wuce mata shi, shi ɗinne dai komai nata, bazata iya ɗaukar fushinsa akanta ba.

Aikinsa yake cikin nutsuwa amma kuma gaba ɗaya tunaninsa akanta yake, ba abun dayafi damunsa kamar cutar hawanjini dake da munta, yasani sarai cutar hawan jini bata da kyau tana cutarwa sosai, musamman ma ga yarinya kamarta hakan yasa yake tsananin tausayinta.

Baizataba saiji yayi ta rungumeshi ta baya, haɗe da ɗaura kanta akan wuyanshi, me makon tace wani abu sai kawai ta fashe masa da kukan shagawaɓa.

Lumshe idanunsa yayi har a cikin zuciyarsa bayason kukanta idan tana

Please Login or Register in order to submit comment