Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

banga laifinka ba, sai dai kuma, akwai ƙalubale a gabanka!" Mahmud yaƙare maganar yana mai waina pen ɗin dake riƙe a hanunsa.

"Wani irin ƙalubale kenan Mahmud?" Dr Sadeeq yatambaya cike da zaƙuwa, saboda shi mafita kawai yake nema.

"Nasara ko kuma akasinta, sune babban ƙalubalen da zaka fuskanta, amma ina mai maka fatan nasara, duk dacewa banganta ba, amma nasan tahaɗu sosai, saboda nasan abokina ya'iya zaɓe!" Mahmud yafaɗi hakan cike da barkwanci, wanda hakan kuma halinsa ne.

"Bazaka taɓa canjawa ba Mahmud, kai ko da yaushe idan ana magana mai amfani saikayi yanda kayi ka sako wasa a ciki." Dr Sadeeq yafaɗi hakan yana mai shafa suman kansa.

Ƴar ƙaramar dariya Mahmud yayi haɗe  da ɗaukan cup ɗin juice ɗin dake gabansa yakai zuwa bakinsa.

"Babu amfanin ƙara tada zancen a gareta Sadeeq,  tunda ta nuna maka bata sonka, inaganin kabata lokaci, ko ba komai zatayi tunani mai kyau, amma fa hakan danace bawai yana nufin kada kasake zuwa gareta bane, zaka iya zuwa gareta ako da yaushe, amma kada ka sake ɗago mata da zancen inaga haka zaifi!" Mahmud yafaɗi hakan cike da son ƙarfafamawa abokinsa guiwa.

Ƙaƙƙarfan ajiyar zuciya Dr Sadeeq ya sauƙe, haɗe da haɗiyar yawu, sai yanzu yasomajin sanyi a cikin zuciyarsa,  domin kuwa da gaba ɗaya kansa ne ya kulle.
"Zanyi yanda kace Mahmud, sai dai kuma inajiyewa kaina tsoro, kada a gaba taƙi amsata,  sannan kuma yanzu bansan da wani ido zan kalle ta ba!" Dr Sadeeq ya faɗi haka cikin ɗar ɗar.

Dariya Mahmud yakuma kwashewa dashi a karo na biyu, lallai yayarda cewa so mugun abune, domin kuwa shi kaɗai ke sa jarumi kuma gwarzon namiji acikin tsoro dakuma ɗar ɗar.

"Yanaga jikinka gaba ɗaya yaɗau rawa, kada dai kabani kunya, tsoronta kakeji tun yanzu, idan kuma akayi auren yaya kenan?" Mahmud yatambaya cike da shaƙiyanci.

Tsuka kawai Dr Sadeeq yakuma ja,  haɗe da miƙewa tsaye, domin idan yabiye ta Mahmud to baƙin ciki sai ya cika masa zuciya, domin kuwa halin Mahmud ne tsokana da yawan barkwanci.

"Gwamma nayi tafiyata zaifi min, kayi dariyanka ka ƙoshi, ai nine nakawo kaina office ɗinka, kana da right ɗin da zaka iyamin komai" Dr Sadeeq yakare maganar yana mai gyara zaman suit ɗin dake jikinsa.

Ko sake sauraran Mahmud dake ta faman dariya baiyi ba, yayi ficewarsa daga office ɗin Mahmud ɗin.

Cikin ɗan kuzarin da yasamu yake tuƙa motar tasa, yanzu kam yagama aminta da shawaran da zuciyarsa ta basa. Kai tsaye gida ya koma, wanka yayi haɗe da shirya kansa cikin wani haɗaɗɗen riga da wando na jeans  masu kyaun gaske, sosai kayan sukai masa kyau a jiki, suka kuma fito da asalin kyawu da kwarjininsa, babu abun dake tashi ajikinsa sai daddaɗan ƙamshin turare. Makullin motarsa ya ɗauka haɗe dasakai yafice daga cikin ɗakin.

Zaune take akan ƴar katifarta, daga ita sai wata riga marar nauyi, jakan kayan shafanta ne aje a gabanta, da'alama daga wanka tafito, domin kuwa wani sashi na jikinta ɗauke yake da danshin ruwa.    Kallo ɗaya zakai mata kafuskanci irin ramar da tayi lokaci guda, gaba ɗaya ta zabge ta faɗa, hips da breast ɗin tane kawai suke a cike a jikinta.  A hankali take shafa Vaseline ɗin dake  riƙe a hanunta, Yanayin yanda take shafa vaseline ɗin idan ka gani, kace dole akai mata.    tana gama shafa mai ɗin, ta murza powder kaɗan akan fuskarta, haɗe da shafa kwalli a cikin idanunta,  take fuskarta ta tasakeyin fayau,  yayinda idanunta, suka sake bayyana girmansu a fili,kasancewar kwallin yana taimakawa wajen bayyana girman ido.

Kallonta tamayar kan ɗan ƙaramin agogon bangon dake ɗakin nata, ƙarfe 5 na yamma kenan, kuma dai dai lokacin sukayi da Husnah cewa zataje ta sameta a gida. Cikin rashin kuzari, ta miƙe haɗe da ɗaukan kayanta riga da sket na atamfa tashiga sanyawa, duk da cewa  atamfar mai sauƙin kuɗi ne, amma hakan baihana ta yi mata kyau a jikinta ba.  Wani irin zazzaɓi takeji yana sanɗan jikin ta, idan ba don tariga da tamawa Husnah alƙawarin cewa zata zo yau ɗin ba, to tabbas da ta ɗage zuwa gidansu Husna'n  saboda bata wani jin daɗin jikinta, takumasan cewa damuwace kurum tayi mata yawa.     

Inna ce tashigo cikin ɗakin, adai dai sanda Zahrah ta gama sanya hijab ɗinta.

"Au ashema kinsan da zuwansa kenan?" Inna tatambaya tana mai ƙarewa Zahrah kallo.

"Banganeba Inna, zuwan waye kuma?" Zahrah taje fawa Inna tambaya cikin rashin fahimtan inda kalaman Inna'n suka dosa.

"Naga kinshirya tsab kamar kinsan da zuwansa, to koma dai menene kije yanajiranki a waje!" Inna tafaɗi hakan tana mai ƙoƙarin barin ɗakin.

"Waye Inna? kuma ni shirin nan da kika ga nayi, gidansu Husnah zani, amma waye ke nemana ?" Zahrah takuma tambaya cike da son ƙarin bayani.

"Waye kuwa zaizo neman ki a yanda kike ɗinnan, ai sai dai shiɗin da har ya yarda zaiyi JIHADI ya  aure ki a haka, amma wai saboda son zuciya da butulci irin naki, kike neman watsa masa ƙasa a idanu!" Inna taƙare maganar dai dai sanda tayificewarta daga cikin ɗakin.

Wasu irin siraran hawayene suka samu nasaran gangarowa daga cikin idanun Zahrah, tabbas gaskia Inna ta faɗa, babu wani mai nemanta sai shi ɗin shi kaɗai, kuma tabbas tayadda shima JIHADI yayi kamar yadda Inna tafaɗa, ashe dagaske ne itakam ƙaddaranta tayi mata mummunan zane a goshinta,    saurin share hawayenta tayi haɗe da sakai tafice daga cikin ɗakin.

Tsaye yake a jikin motarsa yayinda kansa ke duƙe a ƙasa, ɗan makullin motarsa ce riƙe a hanunsa yana kaɗawa, wannan karon kam sosai yake yaƙi da zuciyarsa don bayaso tasake  sanya masa tsoro kokuma ɗarɗar.

A hankali take taku cike da nutsuwa har ta ƙaraso garesa, ɗan nesa dashi ta tsaya haɗe da yimasa sallama cikin sassanyar muryarta wadda bata fita sosai.

Lumshe idanunsa yayi haɗi da buɗesu a lokaci guda, badon komai ba sai don yanda sassanyar muryarta ta daki jiki da zuciyarsa.

"ZAHRAH!" yaƙira sunanta cikin murya marar fidda ƙaƙƙarfan sauti.

"Um!" Zahrah ta amasa masa batare da ta'iya motsa bakinta ba, haka kuma kanta a duƙe yake tunda tazo bata'iya ɗaga kai ta kallesa ba.

Kallonta yashiga yi tundaga ƙasanta har sama, tabbas duk da cewa a cikin hijab take, amma hakan bai hanasa hango rahamar da tayi ba,  take yaji zuciyarsa tayi sanyi, tausayinta yasake kamasa.

"Inaso kimini iso cikin gida, inaga maganar mu acan zaifi, domin ina buƙatar zama!"  yafaɗa cike da ƙosawa da tsayuwan da yakeyi.

Sumi sumi haka ta juya ta nufi cikin gida, harta shige cikin gidan bai ɗauke idanunsa daga kanta ba,  "Wallahi Zahrah ta haɗu, komai nata mai kyau ne!" yafaɗi hakan a fili, cike kuma da shauƙin soyayya.

Jim kaɗan Zahrah tafito, tana mai wasa da yatsun hanunta,  "Kashigo!" kawai ta'iya furtawa cikin murya mai sanyi. Tana gaba yana biye da'ita haka suka doshi cikin gidan.

Katuwar tabarma tabaje musu a hanyar zaure, yayinda ta je ta zauna a can ƙarshen tabarman ta takure waje ɗaya, tamkar amaryar da aka kaita ɗakin miji yau yau, lol.

Murmushi Dr Sadeeq yayi bayan yayimawa kansa mazauni,   dole dai shi zai ci gaba da zama jarumi ako da yaushe.

" Miye haka? ai ko da yanka naman jikin mutane nake, ya kamata ace kin matso kusa dani, balle ma kuma ni ba'abun da nakeyi, ko na taɓa miki wani abune ?" Dr yafaɗi hakan cike da kulawa.

Saurin ɗago da kanta tayi ta kallesa, domin yadawo mata asalin Likitan da tasani, kuma gaba ɗaya ya sauya wasu ɗabi'un nasa.

Giransa ɗaya yaɗage sama, haɗe da cewa "Yadai, ko nayi wani sabon laifi ne akan wancan banda labari?"

Girgiza kanta tashiga yi ita kaɗai tamkar ƙadan garuwa, domin ita tama rasa maizata ce dashi domin kuwa da wani salon yadawo.

"Matso kusa dani mana!" yafaɗa cikin sanyin murya, mai ɗauke da lallashi.

Cikin rashin kuzari, ta koma tsakiyar ta barman ta zauna, bayan ta haɗa jikinta duka ta takure waje ɗaya.

Ajiyar zuciya Dr Sadeeq ya sauƙe haɗe da sanya hanunsa yashafi ƙasumbar dake kwance akan fuskarsa.

"Maiyasa zakisa kanki a damuwa Zahrah? yawan kuka dakuma yawan tunani marassa amfani, basa haifar da komai sai gajiyar da ƙwaƙwalwa, please banso kina wahalar da ƙwaƙwalwarki, nasan cewa abaya banine sila ba, amma yanzu nine sila.!" ɗanjim yayi kana yaci gaba da cewa..." Kiyi haƙuri Zahrah, nasan bankyauta ba, amma inaso kimanta komai, inaso ki fuskanci karatunki, ki maida hankali sosai kinji ƙanwata, bawanda zaimiki dole, ke mutumce kuma kowani ɗan adam yana da ƴanci, kema kina da ƴanci, saboda haka ki daina kuka kinji ƙanwar Likita!"  Yanayin yanda yaƙare maganar kaɗai ya'isa yasanya zuciya hucewa daga cikin fushi.

Kuka kawai Zahrah ta fashe dashi mai sauti, domin kuwa sai yanzu nadaman abun da ta'aikata a garesa yadawo mata sabo fil. A hankali ta ɗago idanunta da suke ɗigan hawaye tamaida kallonta garesa,   wannan fuskar ta mara? ta tambayi kanta, tabbas batayiwa kanta adalci ba, Dr Sadeeq baicancan ci mari daga gareta ba. kukane yakuma ƙwace mata, don batasan tayanda zata soma basa haƙuri akan abun da tayi masa ba.

Cike da damuwa ya dawo kusa da'ita, har suna iya juyo ƙamshin turaren juna.

"Subahanallah Zahrah kuka kuma? kinfasan banaso, kidaina kuka kinji, ki faɗamin idan ganina ne bakiso, yanzu zantafi Zahrah, nazo ne dama nabaki haƙuri akan abun da yafaru tsakanina dake, kiyi haƙuri Zahrah haka bazata...." Kasa ƙarasa maganar yayi sakamakon Zahrah da ta sanya duka hannayenta biyu ta toshe masa baki.

"Dan Allah kada ka ƙasƙantar da kanka awajen wacce bata dace ba, bata kuma cancanta ba, bakaine yakamata kabani haƙuri ba, nice yakamata na baka haƙuri, bai kyautu ace na mareka ba, nayi nadama Doctor, dan Allah kayi haƙuri, bansan yanda zanyi ba ne banda zaɓi, kayafemin!" Zahrah ta ƙare maganar cikin kuka, haɗe da karyewar zuciya.

Take yaji tausayinta yasake ninkuwa acikin zuciyarsa.

A hankali ya sanya hanu yazame hannayenta dake kan bakinsa, domin kuwa hakan da tayi masa har ya sanya tsikar jikinsa sun soma motsawa.

"Kinaso nayi haƙuri?" Dr yatambayeta.

Kaitashiga kaɗawa cikin kuka alamar "Eh"

"To kidaina kuka, domin kuwa daina kukanki shikaɗaine zaisanya nayi haƙuri nakuma manta da komai, kuma ko dama ni Zahrah batayi mini laifi ba, ƙanwata bata laifi a wajena, saboda haka share hawayenki kinji!"  yaƙare maganar yana me miƙomata wani farin handkerchief wanda yafito dashi daga cikin aljihun wandonsa.

Karɓan handkerchief ɗin Zahrah tayi, cike da shagwaɓa tashiga share hawayen dake gudana akan fuskarta,    ajiyar zuciya kawai take sauƙewa akai akai domin kuwa ko ba komai tarage wani nauyi dake maƙare a  gefen zuciyarta.

"Yauwa ƙanwata, kinga kinfi kyau idan kina murmushi dakuma dariya, inaso akoda yaushe kikasance cikin farinciki!" Dr yafaɗa cikin nishaɗi, domin kuwa sosai yaji daɗin yanda Zahrah ta sauƙo daga fushin da takeyi dashi.

Tana gama share hawayen nata ta miƙamasa handkerchief ɗinnasa. 

Kai yagirgiza alamar a'a haɗe da gyara zamansa "Nabaki kyauta, ki ajiye a wajenki, ko saboda gaba, domin naga ke kuka baya baki wahala, kinga duk lokacin da kika soma koke koken ki saiki share hawayenki da shi!"

Hararan wasa ta jefesa dashi, haɗe da murguɗa masa ɗan ƙaramin bakinta.

Dariya yayi domin sarai yana lure da'ita kuma yaga abun da tayi masa.

"Inazakije kikaci uban kwalliya haka? gashi kuma kinzo kinɓata shi da kuka." Yafaɗi maganar alokacin dayake ciro wayarsa daga cikin aljihunsa.

Turo bakinta tayi gaba, cike da ƙunƙuni tasoma motsa bakinta, da'alama wani abu takeson faɗa,  "wai a hakanne nayi kwalliya, kawai dai yace banyi  masa kyau ba" Zahrah tafaɗi hakan a cikin zuciyarta.

"Wayace miki hakane a zuciyata? ni na'isa nace kyakkyawar ƙanwata batayi kyau ba, to ma duk cikin garin Abuja wayakai ki kyau ne? babu fa!"

Dariya tasanya, wanda tajima batayi shiba, cab aikuwa ko da acikin makarantarsu akwai waƴanda suka fita kyau dayawa, balle kuma duka garin Abujan baki ɗaya.

Tsayawa yayi yana kallon yanda take dariyan, komai tayi ƙara kyau take.

Hanunsa ya sanya acikin aljihun wandonsa haɗe da ciro wani haɗaɗɗen choculate,   ɓare ledan choculate ɗin yayi haɗe da miƙo ma ta.  Kyawawan idanunta ta ɗago haɗe da watsa masa su, girgiza kanta tayi, alamar bata buƙata.

Kwaɓe fuska Dr Sadeeq yayi haɗe da marairaice idanunsa, take taji tsikar jikinta ya zuba, yayinda gabanta yayi wani irin mummunan faɗuwa,   domin kuwa hakan da yayi yasanya fuskarsa ta koma yanayi da fuskar Zaid,    saurin ɗauke kanta tayi daga garesa, haɗe da sauƙe idanunta ƙasa, yabuɗe baki zaiyi magana kenan wayarsa tasoma ƙara, alamar shigowar ƙira,   cike da girmamawa yaɗauki ƙiran ganin cewa ƙiran daga  Hajiyarsa ce.

"Kana'ina?" Hajiya tatambaya a kausashe.

Baikai ga bata amsaba taci gaba da cewa  "Koma mekakeyi kabari, Inaso kaje gidansu Salima yanzu, umarni ne ba shawaraba!" ƙit takashe wayan batare da tajira taji mai zai ceba.
Ajiyar zuciya ya sauƙe haɗe da maida kallonsa ga Zahrah.

"Wani uzuri yatasomin, zantafi kikula da kanki!"  yafaɗi maganar yana me miƙewa tsaye.

Miƙewa itama Zahrah tayi batare da tace dashi komai ba tashiga naɗe tabarman da suka tashi akai.

Wani irin kallo haɗe da murmushi mai tsayawa a zuciya yayi mata, kana yasa kai yafice daga zauren gidan nasu, yana fita yafaɗa motarsa yayi mata key.

Tanajin ƙaran tashin motarsa ta sauƙe a jiyar zuciya haɗe da komawa cikin gida.

Kamar yanda mahaifiyarsa ta umarcesa hakan yayi domin kuwa yaje gidan su Salima sungana da'ita, yarinyar bata da wani aibu, amma kwata kwata jininsa danata baizo ɗaya ba, domin kuwa sam bata burgesa kasancewarta mace mai rawan kai da shegen girman kan tsiya, har gwamma masa Zabba'u akan Salima,  domin dai shikam Salima batayi masa ba. Haka dai suka gaisa sama sama,  ko minti 20 baiyiba yabaro gidan nasu..

Bayan Sati Ɗaya.

Kusan ko da yaushe sai Doctor Sadeeq yazo gidan su Zahrah, amma kuma tundaga wannan lokacin baisake koda ɗago wani zance makamancin wancan ba, sai dai yana'iya ƙoƙarinsa wajen bata kyakkyawan kulawa. Sannan  kuma dake ita ɗin me raunin zuciya ce take ta sake  bashi yardanta akaro na biyu.

Ɓangaren gidansu Dr Sadeeq kuwa harsun fara shirye shiryen bikinsa, domin kuwa Hajiyarsa wannan karon bada wasa take ba,  tace acikin 3 weeks takeso ayi bikin. Shi dai Dr Sadeeq idanu kawai ya zuba musu, domin kwata kwata baijin auren a jikinsa, da za'afasa auren to dazai fi kowa murna,  saboda Zahrah yakeso Zahrah ce muradinsa, amma kuma haryanzu yakasa samun wani gamsashshiyar amsa daga gareta.

Ƙarfe 3 dai dai jirginsu ya sauƙa a babban airport ɗin dake cikin garin Abuja, motoci ne iri da kala har guda shida suka zo tarbansa, ciki kuwa hadda Dad ɗinsa, a hankali yake sauƙowa daga cikin matakalar jirgin sanyen yake da kayan sanyi hadda hula, yayinda fuskarsa ke ɗauƙe da wani haɗaɗɗen baƙin glass na maza,   sosai yaƙara kyau da fari,  kallo ɗaya zakai masa katabbatar da cewa yakai cikekke kuma gwarzon namiji, a gaskia yana da kyau da kuma kwarjini, uwa uba kuɗaɗe sun samu mazauni a jikinsa. Bakowacce mace bace zatayi tozali da haɗaɗɗen  namiji kamar Zaid, kuma takau da idanunta ba, saboda Zaid yahaɗa duk wani abu da kowacce mace zata so awajen ɗa namiji, shidai matsalan sa ɗaya munanan  halaiyansa.    Yanda yake tafiya cike da izza shiyafi komai ɗaukar hankali, dakuma jan hankali zuwa garesa.    Cike da farinciki Alhaji Ma'aruf yarungume ɗa'nnasa, duk da cewa babu wani shaƙuwa me ƙarfi a tsakaninsu amma yana matuƙar son Zaid.   
Mota ɗaya suka shiga shida Dad ɗinsa, yayinda guard ɗinsu suka mara musu baya a cikin sauran motocin.      Kwanciya yayi lamo ajikin kujeran motar  haɗe da lumshe idanunsa, wani irin sanyi yakeji acikin zuciyarsa,  koda wasa baitaɓa tunanin haka zai kasance dashi ba, kamarshi Zaid ace tunanin mace yahanasa sukuni harsaida yabaro duka abun da yakeyi ya dawo zuwa gareta,  amma zaiyi maganin abun a yau bawai sai gobe ba yake da buƙatar ganin sugar baby'nsa, sai dai kuma wannan lokacin bada wasa yazo ba...

Zahrah ne keta kai kawo a tsakiyar ɗakinta, tabbas tayarda da duk wani shawara da zuciyarta ta bata, zuwa yanzu yakamata ace tayi abunda ya dace. Wayarta ne yasoma ƙara alamar shigowar ƙira, tana ɗaga wayar Dr Sadeeq yace "Gani na'iso ina ƙofar gida!"

"To" tace haɗe da aje wayar, ajiyar zuciya ta sauƙe haɗi da cije lips ɗinta, dama ɗaya kawai take dashi kuma tabbas idan tarasa wannan daman to zaiyi mata wahala tasake samun wani daman.

Hijib ɗinta ta sanya, koda tafito tsakar gida bata taradda Inna ba tana kuma da tabbacin cewa bama ta gidan.

Zaune yake acikin motar tasa, dagani kasan cewa yana cikin damuwa, domin gaba ɗaya har rama tasoma bayyana a jikinsa. Murfin motar tabuɗe tashiga, bakinta ɗauke da sallama, amsa mata sallaman nata yayi haɗe da gyara zamansa yafuskance ta " Baki taɓa min irin wannan ƙiran ba, naƙosa naji wace maganace zaki faɗamin mai matuƙar mahimmanci haka" gaba ɗaya hankalinsa ya tattara zuwa gareta.

"Dagaske kake Zaka aure ni?" Zahrah tajefo masa tambayar
dabai taɓa zata ba balle tsammani.

Kansa yashiga kaɗawa muryarsa har rawa take yace "Dagaske nake Zahrah, wallahi auren ki nakeso nayi, samunki a matsayin mata shine babban burina a yanzu." yafaɗi hakan da iya gaskiya'rsa

"So na kakeyi kokuma tausayina?" Zahrah takuma jifansa da wata tambayar.

"Sonki nake Zahrah, inamiki so mai tsanani, wlh inasonki da duka zuciyata!" Dr Sadeeq yabata amsa, cike da kulawa.

"Nayarda na Amince Zan aureka, muyi zama na har abada!"  Abun da yafito daga bakin Zahrah kenan bayan tagamajin amsar da take buƙata daga garesa, cikin tsananin mamaki Dr Sadeeq yashiga kallonta, jin sauƙar maganarta yayi tamkar daga sama, kodai kunnuwan sa basu jiye masa dakyau bane?....

(To fa readers Ga Baba Zaidu yashigo Gari, ga kuma Zahrah ta amince da auren Dr Sadeeq, gashi kuma ɓangaren gidansu Dr anatashirye shiryen bikin Dr da Salima, koya zata kaya 🤷‍♀, please kusani a addu'anku wlh cikina ke ciwo sosai😥 idan kunga typing eror kuyi haƙuri gaba ɗaya banda wata isashshen nutsuwa ne 😭)

   *10/December/2019*

*Voted,Comment,and Share please.... Follow me on Wattpad @fatymasardauna*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

           *SHU'UMIN NAMIJI!!*

    
         *Written by*
  *Phatymasardauna*

*Dedicated To My Brother KHABIER*

*🌈Kainuwa Writers Association*

'''{United we stand and succeed; our ambition is to entertain & mitivate the mind of readers}'''

*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*

     
          *WATTPAD*
    @fatymasardauna

*Editing is not allowed📵*

*(This  page is Dedicated  to you  HAROUN UMAR (H Umar) admin of 📖✍️BENEFICIAL WRITERS ASSOCIATION, inajinjinamawa ƙoƙarinka ako da yaushe haroun, kuma inagodia a gareka marar iyaka.)*

    *CHAPTER 53 to 54*

Kasa motsa koda laɓɓansa yayi balle har yakai ga furta wata kalman, "dagaske ne abun da kunnuwansa suka jiye masa kokuwa mafarki yake?" yafaɗi hakan a  cikin zuciyarsa.

"Kada kayi kokonto kokuma shakka, dagaske nake, na amince da aurenka, amma ina mai roƙon wata alfarma a gareka"...."Dan Allah kada ka wulaƙantani aduk yanda kasameni, kada kuma ka tozartani, nasan cewa tausayina yafi yawa acikin zuciyarka fiye da soyayya ta, saboda haka ina da tabbacin cewa ko gaba zaka iya sake samun wata mace,wacce itace zata kasance zaɓinka, kada haka yasa ka wulaƙantani dan Allah, kada kuma kacutar da rayuwata!" cikin sanyin murya ta ƙare maganarta ta, yayinda hawaye suka shiga fitowa daga cikin idanunta,suna sauƙa akan ƙuncinta.

Jiyayi gaba ɗaya wani irin matsanancin farinciki ya lulluɓesa, gani yake tamkar wasa Zahrah take masa, amma kuma ba'abun mamaki bane, saboda babu abun da yagagari Allah.

"Bansan ta'ina kokuma tayaya zan fara godemiki ba Zahrah,  kin gusarmin da duk wata damuwa dake damuna, kinbani farinciki cikin ƴan mintuna ƙalilan,  kiyarda dani Zahrah, inamiki Soyayyace ta gaskiya bawai, irin soyayyarnan tako oho ba, zan'iya sadaukar da duk wani abu nawa akanki Zahrah,   soyayyar da nake miki, yasanya bana ganin laifi ko kuma aibun duk wani abun da kikamin,   burina da fatana shine murayu tare dani dake amatsayin miji da mata, kuma aƙarƙashin inuwa ɗaya,  Inasonki Zahrah, kuma namiki alƙawari komai wuya komai tsanani bazan taɓa gujemiki ba, ZANRAYU DAKE Zahrah!!" Dr Sadeeq yafaɗa cike da matsanancin farinciki, jiyake tamkar yajawo Zahrah jikinsa yabata kyakkyawan runguma.

Kuka Zahrah ta fashe dashi, wanda batasan dalilin yinsaba, ita ta amincewa kanta cewa zata auri Dr Sadeeq amma saitakeji tamkar dole tayimawa kanta.

Batayi zato ba saiji tayi Dr Sadeeq yajawota jikinsa haɗe da sanya hannayensa duka biyu ya rungumeta.  "Inasonki Zahrah, kuma nayi maki alƙawarin bazantaɓa wulaƙanta ki ba har'abada, kidaina kuka kinji princess ɗina!" yaƙare maganar tasa cikin sigar lallashi.

Daddaɗan ƙamshinsa shiyaso birkita mata tunani don haka tayi saurin janyewa daga jikinsa, tana mai yin ƙasa da kanta.

Sam shikam ma yamanta da cewa hakan da yayi ba'abu bane mai kyau, gaba ɗaya murna yacika masa zuciya.  

"Uh sorry baby, gaba ɗaya kece kikamantar dani komai!!"  Dr Sadeeq yafaɗi hakan yana mai dafe goshinsa.

Ƙasa ƙasa Zahrah tayi murmushi haɗe da kawar da kanta gefe, hakanan taji wani irin nauyin Dr Sadeeq ɗin yaƙaru acikin zuciyarta, haka kuma yaƙara girma acikin idanunta.

Wani irin kallo Dr Sadeeq yashiga yimawa Zahrah duk dacewa takau da kanta gefe,   sai yanzu nema yake ƙara ganin haɗuwarta fiye da  da, tabbas da Zahrah bata amince dashi ba to da ya tabka babban rashi, domin kuwa Zahrah tahaɗu, macece ita da kowanni Namiji zaiyi fatan mallaka.

Sam batayi tunanin kallonta yake ba, don haka taɗan juyo dan itama ta saci kallonsa,  aikuwa karab idanunsu suka sauƙa akan najuna, da sauri Zahrah tayi ƙasa da kanta haɗe da cusa fuskarta tsakan kanun  cinyoyinta.

Dariya Dr Sadeeq yayi cike da shauƙi haɗe da shafa sajen dake kwance akan fuskarsa. "Yaushe kika farajin kunyana? lallai zamu ɓata idan harkinajin kunyana!" ya faɗi hakan cike da zolaya.

Ɗan ƙaramin bakinta taturo gaba, haɗe da marairaice fuska cike da shagwaɓa tace "To bakaine kaketa kallo na ba, saikace baka sanni ba!"

Lumshe idanunsa yayi haɗe da buɗesu a lokaci guda, irin wannan salon shagwaɓan ai saita sashi bacci batare da yashiryawa hakan ba,lol.

"Ki faɗamin laifi ne don nakalli abar sona? saidai kiyi haƙuri amma kallonki yanzuma na fara, tunda kinamin kyau, kina kuma burgeni!" yanayin yanda yayi maganar abun burgewa ne, ga macen da tasan daɗin soyayya.

"Nidai kada ka wani ce inada kyau, daɗin bakine kawai nasan kakemin!" still da yanayin shagwaɓa tayi maganan.

Lumshe idanunsa yayi haɗe da fitar da iskan numfashi daga bakinsa,  yanayin shagwaɓan  Zahrah yafi komai burgesa a tattare da'ita, haka kuma sosai yake sauƙar masa da kasala.    "Princess!!" yaƙira sunanta dawani irin murya mai taɓa zuciya.

A hankali ta ɗago idanunta ta kallesa, batare da ta amsa masa ba,    ganin idanunsa a rufe, yasanya taɗan tsaya ƙaremawa fuskarsa kallo.     "Duk kallona  ɗaya da zaki yi bazai tafi a banza ba, sai kin biya kuɗi, gwamma ma kisani!" Dr Sadeeq yafaɗi haka batare da ya buɗe idanunsa ba.
Saurin ɗauke kanta tayi daga kallonsa haɗe da cewa "Niba kallonka nake ba"   

"Zaki iya rantsewa cewa bani kike kallo ba?" yaje fo mata tambayar da batayi zato ba.

kanta tashiga girgizawa haɗe da cewa "Ai bankalleka sosai ba, kaɗan nakalleka!"

Dariya Dr Sadeeq yasanya wanda harsaida dimple ɗinsa suka bayyana,  yanzu yayarda cewa Zahrah yarinyace ƙarama, kuma zakayi saurin kamata idan tamaka laifi.

Ƙoƙarin buɗe murfin motar Zahrah tasomayi, cikin mamaki Dr yace "ina zaki?"

"Zankoma gida ne, dama magana zan faɗa ma, shiyasa  na ƙiraka, kuma nafaɗa ma, inada karatu, gobe muna da test a makaranta" Zahrah tafaɗi hakan dai dai lokacin da ta gama sanya ƙafafunta waje.

"Shikenan to My Princess kikulamin da kanki kinji, inasonki sosai!" Dr Sadeeq yafaɗa cike da kulawa.

Wani irin muguwar kunyarsace takama Zahrah, bashiri ta wuce cikin gida tana mai rufe fuskanta da tafukan hanunta.

Shima Dr ɗin murmushi yayi cike da jindaɗi,  lallai idan ya auri Zahrah yakasance mutum mai sa'a,   acikin satinnan insha Allah, zai sanarda ƙanin mahaifinsa azo a nemamasa auren Zahrah, a wajen Baffa.

"Aurenka da Salima fa?" Wata zuciyar ta jefo masa wannan tambayar, wani irin bugawa yaji ƙirjinsa yayi,  gaba ɗaya amincewa dashi da Zahrah tayi yasanyashi manta halin da yake ciki na batun auren sa da Salima. Jiyayi gaba ɗaya jikinsa yayi sanyi, tabbas akwai ƙalubale a gabansa, domin kuwa yanada tabbacin cewa Hajiyarsa bazata taɓa sanja maganarta ba, gashi har ansoma shirye shiryen bikinsa da Salima, kuma shi a tsarinsa bai sha'awar auren mata biyu, Zahrah ita kaɗai ta'ishesa rayuwa, amma kuma tabbas yasan zai fuskanci matsaloli da yawa daga ƴan uwansa, matuƙar ya jajirce akan cewa Zahrah yakeso ba Salima ba, to amma dole zai jarraba sa'ansa, domin a gaskiya baijin cewa zai'iya haƙura da Zahrah.
Cike da sanyin jiki yayimawa motar tasa key, haɗe da nausawa kan titi.

Suna isa katafaren gidannasu, adai dai parking space motar tasu ta tsaya.

Bawani jinkiri Zaid yabuɗe murfin motar yafito,    batare da

Please Login or Register in order to submit comment