Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba,  miskilancin nasa ne ya motsa, banaje dakaina nasa mesa nikam ae be isa yanunamin halin ƙyaliya ba" Mom tafaɗi haka tana me miƙewa tsaye daga zaunen da take..

Itama ɗin de knocking tayi masa haɗe da ƙiran sunansa amma shiru bai amsata ba, hakan yasa ta murɗa handle ɗin ƙofar ta kutsa kanta ciki bakinta ɗauke da sallama..

Tsuka Mom taja sakamakon ganinsa da tayi kwance akan gado yayi ruf da ciki, lallai ma wato iskancine ya hanasa amsa mata, da fari hartayi zaton ko baya gidan ne..

"Zaid!" taƙira sunansa cikin kakkausar murya... Ko motsawa baiyi ba balle tasaran ze amsa mata..

Kafeshi da idanu tayi tana me nazartarsa, a iya saninta da Zaid baya bacci a irin wan nan lokacin, impact ma shiba mutum bane ma'abocin yawan bacci ba'a bisa ƙa'ida ba, idan kuwa harda gaske baccin yake to baya rasa ɗayan biyu kodai baida lafiya ko kuma yayi halin nasa nashan ƙwayoyi,  "Sai yaushene Zaid ze san ya girma? sai yau shene zai dena nuna rashin damuwa da lafiyarsa?" tajeromawa kanta waƴan nan tambayoyin,  "Haƙiƙa Zaid ɗanta ne amma ita kanta har yau batasan wani irin haline da shi ba, shi mutum ne me nuƙu nuƙu bakoda wani lokaci ne kake sanin gaba da bayansa ba, haka nan yake bakomai ne zaka masa ƙa burgesa ba yanada wani shegen shu'umin hali saide kawai Allah yashirya mata shi"...

A hankali tashiga takawa zuwa gaban gadon nasa..

Idanu Mom tasake warowa waje, tabbas idan de idanunta de de suka gane mata to kuwa Zaid baya numfashi, domin  babu wata alamar  da take nuna akwai nunfashi a tattare dashi saboda ko cikin sa baya motsawa, alama ta baya shaƙan numfashi kenan..
Hanunta takai setin hancinsa ko da zataji ɗumin numfashin sa.

Salati Mom tasa haɗe da dafe ƙirjinta, sakamakon wani irin bugawa da taji zuciyarta tayi.

"Zaid!Zaid!" Mom tashiga ƙiran sunansa cikin tashin hankali haɗe da soma jijjigasa.
Hawayene suka shiga bin ƙuncin Mom bashiri ta fita daga ɗakin, direct ɓangaren Alhaji Ma'aruf ta nufa saboda yana gida baikai ga fita office ba..

"Alhaji! Alhaji! katemaka wlhy Zaid baya numfashi zo muje ka gani, katemakeni kada na rasa ɗana mafi soyuwa a gareni!!" gaba ɗaya cikin tashin hankali Mom keyimawa Dad bayani..

Mamaki haɗi da al'ajabi ne yakama Alhaji Ma'aruf amma de yanzu balokacin tambaya bane gwamma yabita yaga meke faruwa da Zaid ɗin....

Shima sosai ya tsorita kuma hankalinsa yatashi daganin Zaid yashe a gado baya numfashi sai kace gawa...

Da ƙyar Abba ya'iya sungumarsa yasanyasa a mota, abunka da ƙaƙƙarfa kuma ma'abocin yin gym shiasa jikinsa yake ko ina a murɗe, san nan kuma me ƙaramin ƙarfi bazai iya ɗaga sa ba, Dad ɗin ma saida temakon Mom ya iya ɗagasa... Daga Mom har Labisat hankalinsu amatuƙar tashe yake haka suka shiga mota suka rankaya zuwa asibiti...

Direct Emergency  aka kai Zaid cikin gaggawa likitoti suka shiga basa temakon gaggawa...

Jigum jigum haka Abba da Mom sukayi a wani ɗan corridor dake kusa da ɗakin da aka kai Zaid, iya ƙololuwar tashin hankali sun shigesa, kuka kawai Mom da Labisat keyi, kasa koda rarrashinsu Alhaji Ma'aruf yayi domin shima da akwai hali da kukan ze sanya ko da zaiji sassauci a cikin zuciyarsa...

Likitotin nan sunci baƙar wahala kafun da taimakon Allah suka samu suka daidai ta numfashin Zaid. Haka suka fito suna sharce gumi....   Kallon Alhaji Ma'aruf ɗaya daga cikin Doctors ɗin yayi haɗe da cewa "Ranka ya daɗe muje office"    ƙoƙarin binsu Mom tasomayi Alhaji Ma'aruf yaɗaga mata hanu alamar tajirasu....

Handkerchief likitan nan yaɗauka ya ƙare share gumin dake tsatstsafawo akan goshin sa..
Ganin haka yasa Abba cike da tashin hankali yace "Yade Dr.Bilal meke faruwa ne, dan Allah kada kafaɗamin wani mummunan labari!"

Jinjina kai Dr.Bilal yayi haɗe da kallon Dad.  "Kwakwantar da hankalinka Alhaji zuwa yanzu komai ya daidaita munshawo kan matsalan"

Nannauyar ajiyar zuciya Dad yasauƙe haɗe dayin hamdala acikin ransa...

Sake gyara zama Dr.Bilal yayi haɗi da cewa "Sai de kuma agaskia bazan ɓoye maka ba Alhaji ɗan ka yana cikin matsala wanda yake gab da rasa rayuwarsa matuƙar baikiyayewa kansa shan ƙwayoyi masu mugun haɗari ba, baya ga haka kuma idan har ya cigaba dashan giya  nan da ƴan kwanaki tofa sai de kuma abun da Allah yayi!"

Yanzukam Dad ne yashare gumi ba Dr.Bilal ba, domin kuwa a iya tsawon rayuwarsa baitaɓa sanin Zaid nashan wasu ƙwayoyi masu bugarwa ba,  yade san da ya nashan giya amma kuma atunaninsa yajima da dena shan giyan.

"Bangama fahimtarka ba likita, naji kace ƙwayoyi na bugarwa, kana nufin shiɗin ne yakeshan ƙwayoyin bugarwa?" Dad yatambayi Dr.Bilal cike da son sanin ƙarin haske akan batun..

"Wato a iya bincikenmu mungano cewa akwai wata ƙwaya me haɗarin gaske da yakesha lokaci zuwa lokaci, wanda kuma haɗarin ƙwayar yana da matuƙar yawa,  bazanyi mamakin a ina yasamu ƙwayan ba, saboda nasan shiɗin isashshene, saboda ƙwayar ba ako ina ake samunta ba, a ƙa'ida ma anhana shigo da ƙwayar nan gida Nigeria, kawai de rayuwar yanzune  da ta zama sai a hankali, zai iya yuwuwa kuma ba anan yake sayan ƙwayan ba daga can waje yake shigowa da abarsa, sai de kuma wan nan duk bashine damuwar ba, idan har ya cigaba da shan wan nan ƙwaya to ina me tabbatar maka da cewa zai iya rasa ransa ako da yaushe, duk da kuwa dama munsan mutuwa tana kan kowa yanzu ko anjima, amma tabbas kiyayewan shine yafi, san nan kuma giya tayi masa mummunan illa saboda tasamu mafaka acikin cikinsa, wataƙila yamai da ita ruwan shansa ne, amma kuma duk hakan ba wani babban matsala bane idan har ze kiyaye to da taimakon Allah komai zezo masa cikin sauƙi!"

Salati Alhaji Ma'aruf yayi a bayyane haɗe da sanya hanu yazame hular dake kansa,  ashe bayan giya hadda wata tsinanniyar ƙwaya me haɗari Zaid yake sha? anya kuwa Zaid yanada cikakken hankali? shin wani irin haline haka da Zaid? amma babban abun tambayar shine laifin waye acikinsu, laifinsune su iyayensa kokuwa laifinsa ne shi kansa Zaid ɗin?

"Haƙiƙa dukansu suna da laifi, amatsayinsu na iyaye basu wani tsaya sunbawa Zaid kyakkyawar kulawa ba, kuɗi kawai suka sake masa haɗe da turasa makaranta har wata uwa duniya, amma duk da haka bekamata ace yakasance haka ba, idan su basa lura da al'amuransa shi ɗin mahaukaci ne da be san dede ba?   tabbas yasan shiyake da alhakin kulawa da tarbiyan Zaid tunda shine yaɗaukosa daga wajen Mahaifiyarsa yadawo dashi  America kusa dashi,  tunda suke America bai taɓa tsayawa da kyau yakula da wani irin rayuwa Zaid ɗin keyi ba, shide kawai yabuɗe masa bakin aljihu yana ganin hakan shine gata,  ƙwarai mafiyawancin iyaye ayanzu sunfi bada kulawarsune ga Ƴaƴa mata, yayinda ƴaƴansu maza kuwa ko oho, duk wata kyakkyawar tarbiya Ƴaƴa mata ake ƙoƙarin koyawa, yayinda Ƴaƴa maza kuwa suka zama hoto, aganin iyaye komiye ɗa namiji yayi adone bakamar ƴa mace ba, tabbas hakane duk abun da ɗa namiji yayi adone bakamar mace ba, amma hakan bawai yananufin shi ɗa namiji abarsa sakaka haka bane batare da annuna masa kulawa ba,  shi namiji a koda yaushe ana ganin zai iya kula da kansa, amma yana da kyau ana nuna masa kulawa ana kuma jansa ajiki kodan yasamu inda zena faɗan damuwarsa, kowafa yanason yasamu tarbiya me kyau daga Namiji har mace, saboda haka yazama lalle iyaye su tashi tsaye wajen kulawa da ƴaƴansu maza saboda ba mata ne kaɗai suke buƙatan kulawa ba harsuma maza suna buƙata......

Dr.Bilal ne yakatse Dad daga tunanin da yafaɗa me zurfi tahanyar cewa da yayi dashi.    "Zaid yana buƙatar hutu saboda haka sai nan da 4 hours kafun su samu ganinsa"

Jiki ba ƙwari haka Dad yafito daga office ɗin  yanufo inda su Mom ke tsaye suna sharce hawaye..

"Yaya de Alhaji me likitan yacema?" Mom tatambaya cike da damuwar son sanin wani hali ɗanta yake ciki..

"Kada kidamu, ku kwantar da hankalinku jikinsa da sauƙi zuwa anjima kuma insha Allah zamu samu ganinsa yanzu likita yace yana buƙatar hutu ne, to dole zamu barsa yaɗan huta" Dad yaƙare maganar yana me kamo duka hannayen mom alamun rarrashi..
Hamdala Mom tayi haɗe da sauƙe ajiyar zuciya

Sake kallon Dad tayi cikin yanayi na tuhuma tace "Meyasanya naga fuskarka ɗauke da tashin hankali me tsanani Alhaji?"

Murmushin dole Dad yanemo ya ara akan fuskarsa bayason faɗa mata wan nan maganar yanzu yafiso saisun samu nutsuwa sunkoma gida tukunna, sai de kuma abun da shi besani ba shine tafikowa sanin cewa Zaid yanashan giya, saboda tasha kamasa acikin maye yayi mankas, san nan kuma tajima da sanin cewa yanashan ƙwayoyi, sede abun da bata sani ba shine haɗarin da ƙwayoyin suke ɗauke dashi....

********

Haka Zahrah tawayi gari yau da zazzaɓi sede duk da haka bata nunawa kowa cewa bata da lafiya ba, sede kuma idanunta sun kunbura sakamakon kukan da taci ta ƙoshi a daren jiya..
Haka de tashirya kanta tsab don zuwa makaranta amma kowa yaganta yasan bata da wani isashshen kuzari a tattare da'ita,, ko abun kari bata tsaya taci ba haka ta fice a gidan nasu....

********

"Kuka bazai taɓa yimiki maganin komai ba Zahrah, tabbas nasan kinajin raɗaɗi a cikin zuciyarki amma zuwa yanzu yakamata ace kimanta da baya kifuskanci gaba,   aure zakiyi  yanzu babu amfani kicigaba da sanya kanki cikin ƙunci!" Husnah tafaɗi haka ga Zahrah cikin yanayi na tausasawa, kasancewar duk wunin yau ɗin da sukayi amakaranta bata gane kan ƙawarta ta ba...

Hannayen Husnah duka Zahrah takama haɗe da kallonta.  Cikin murya me rauni tasoma cewa.....

"Ni kaina inaso naganni cikin farinciki Husnah, amma nasan hakan bazai samu ba matuƙar Zaid yana raye a doron ƙasa,  koda ma ace baya raye nasan bazanyi farinciki ba Husnah saboda yariga daya gama lalatamin rayuwa, bana tunanin cewa  akwai wani namiji da zaiyi ɗokina idan ya aureni?  Shifa budurci wani abune me matuƙar mahaimmanci a rayuwar ƴa mace Husnah, babu wani mutumci dakuma karamci wanda ya wuce mace takai budurcinta ɗakin mijinta,  mafi ganganci da kuskure da mace zata aikata kafun aurenta shine ta yarda ta bawa wani  kyautar budurcinta,   mata irina suna da yawa Husnah wa ƴanda aka mawa fyaɗe aka ƙwaci budurcinsu da ƙarfin tsiya, san nan kuma akwai waƴanda maza suke ruɗansu da kuɗi ko kuma da soyayya harsu yi nasaran rabasu da budurcinsu,  san nan akwai kuma wanda dan kansu suke bada kyautar nasu budurcin  ga wani daban,   rasa budurci abune me matuƙar ciwo Husnah musamman ma ga iri na wanda aka mawa fyaɗe, Yawancin maza suna fatan idan sunyi aure  su samu matansu  da cikekken mutumcinsu, inde kuwa har a matsayin budurwa suka aureta,  haƙiƙa akwai wata soyayya dakuma girmamawa dake shiga tsakanin mace da mijinta matuƙar takawomasa  budurcinta ɗakinsa, saɓanin haka kuwa shike hargitsa tunanin namiji, shike jagulawa mace zaman aure'nta, koda ace ya yarda ƙaddarane hakan amma tabbas wani lokaci abun zaina masa ciwo, duk da nasan cewa Dr.Sadeeq yasan komai daya faru dani, amma duk da haka tabbas nasan duk randa yakusanceni saiyaji ciwo acikin ransa, saikuma yaji wani abu saɓanin tunaninsa, shi a yanzu yana ganin cewa hakan bakomai bane, amma kuma hakan komai ne bakuma ze gane hakan ba sai randa ya aureni yakuma nemi dana basa haƙƙinsa na aure,,   wan nan ranan nake gujewa kaina  Husnah bansan ina zan tsoma kai da zuciyata ba amma nabarwa Allah komai!!" gaba ɗaya hawaye sungama wankewa Zahrah da Husnah fuska, lalle kuwa wan nan itace mummunar ƙaddara wand ba'a taɓa mantawa da'ita,,  rungume Zahrah Husnah tayi cike da tsananin tausayin ƙawarta ta,,, tabbas duk abun da Zahrah tafaɗa gaskiya ne kai budurci ɗakin miji yafi komai daɗi a rayuwa saboda ko ba komai zaiƙara muku danƙon soyayya dakuma mutunta juna, duk da cewa Zahrah ba'asonta tarasa budurcinta ba amma kuma tabbas kamar yanda Zahrah ta faɗa hakan yake dolene Dr.Sadeeq zaiji zafin abun sosai aduk ranarda kusantar farko tashiga tsakaninsu, amma kuma babu wanda ya isa ya tsallakewa ƙaddararsa.....

Hawayenta tasanya hanu tashare kafun tashiga sharewa Zahrah ma nata hawayen,,,,   

"Ki kwantar da hankalinki Zahrah komai zai zo cikin sauƙi insha Allah taso muje musamu ruwa muwanke fuskarmu ko"

Ba musu Zahrah ta tashi tsaye Husnah takama hanunta suka nufi wajen da sukasan zasu samu ruwa......

***********

Jigum haka su Dad  dake tsaye  agefen gadon Zaid sukayi, yanzu awa 5 kenan suna irgawa batare daya buɗe idanunsa ba, gashi kuma  4 hours likita yace musu zaiyi....

Babban yatsar ƙafansane tasoma motsawa kafun idanunsa da sukayi nauyi suka soma buɗewa a hankali,, da sauri Dad ɗinsa yaƙaraso jikin gadon yanayi masa sannu...

Ƙoƙarin tashi zaune yasomayi da sauri Dad ɗinsa yamaidasa ya kwanta "Ba sai ka tashi ba Zaid yakamata kabari kaɗan wastsake tukunna kafun kasoma yunƙurin tashi"

Ɗan yamutsa fuska Zaid yayi haɗe dabin ledar ruwan da aka ɗaura masa da kallo.
Dai de lokacin Labisat suka shigo ita da Dr.Bilal domin dama Mom naganin Zaid ɗin yabuɗe ido tace da Labisat tayi mata ƙiran Doctor...

Ƴan gwaje gwaje Dr.Bilal yayi masa haɗe dayi masa wasu ƴan tambayoyi, ko motsawa bakin Zaid beyiba balle Dr.Bilal yasa ran samun amsa, ganin haka yasa Dr.Bilal yin murmushi batun yauba yasan Zaid ɗin saboda haka shirun da Zaid ɗin   yayi masa bawani abu bane daya kamata ace yadamu ba,,  kallon Dad Dr.Bilal yayi haɗe da cewa

"Ko yanzu idan kuna buƙatar sallama se a baku saboda babu wata damuwa, se daifa a kiyaye kamar yanda na faɗa"

Kai Dad yajinjina haɗe da cewa "Shikenan Doctor insha Allah za'a kiyaye, muje sai nakarɓi takardan sallaman ko"    Dad da Dr.Bilal suna fita Zaid yatattaro duka wani kuzarinsa dayayi masa saura yamiƙe tsaye, kafaɗun Labisat dake tsaye kusa dashi ya kamo haɗe da ɗaura hanunsa akan kafaɗan nata suka nufi hanyar fita daga ɗakin, domin kuwa koda Dr.Bilal be basu sallama ba tabbas bazai ƙara 1 hour a cikin asibitin ba...

Yana riƙe da kafaɗan Labisat harzuwa cikin mota, shida Labisat  mota ɗaya suka shiga, yayinda su Dad da Mom suka shiga wata motar wanda duk su sukazo da ita... Direct  gida suka nufa

Idanunsa gaba ɗaya suna a lumshe yayinda yajingina bayansa a jikin kujeran motar wanda yake zaune akai.

Ɗan satan kallonsa Labisat tayi hakanan taji wani irin mugun tausayin ɗan uwan nata ya kamata, tabbas basuyi wani shaƙuwa da yayan nata ba amma tafuskanci cewa yanacikin damuwa, takuma tabbatar da cewa sanadin damuwarne ma har ya kaisa ga kwanciya a asibiti, to wan nan wace irin damuwace yayanta yake ciki haka? tabbas zataso sanin damuwar dake damunsa  saboda tana matuƙar son ɗan uwan nata bandashi batada wani ɗan uwa dasuke uwa ɗaya uba ɗaya shikaɗaine yayanta kuma garkuwanta......

Koda suka isa gidama Labisat ce tarakasa har ɓangarensa,,  zama yayi akan kujera haɗe da jawo wani ɗan ƙaramin table ɗin dake tsakiyar falon yaɗaura ƙafafunsa akai..

"Yaya mezan kawo maka, yakamata kasa wani abu acikin ka!"  cike da ɗar ɗar Labisar tafaɗi maganar saboda tasansa sarai ba'a iyarmasa yanzu saiya saceka..

"Friedrice" yafaɗa a taƙaice batare kuma daya buɗe kyawawan idanunsa dasuke a lumshe ba..

Jiki na mazari haka Labisat ta tafi kawo masa friedrice ɗin dayace, domin kuwa dama agidan nasu ba a rasa friedrice..

Mintuna kaɗan tadawo hanunta ɗauke da ƙaton tire hadda plate ɗin  yankakkun kayan marmari akan tire ɗin,, adede gabansa ta ajiye tire ɗin haɗe da ɗaukan plate ta buɗe kulan da friedrice ɗin ke ciki ta zuba masa.

"Yaya gashinan na kawo" tafaɗa tana me tura masa plate ɗin friedrice ɗin gabansa.

Ganin da tayi bece da ita komai ba yasanyata miƙewa sumu sumu tafice daga falon nasa...

Jawo plate ɗin yayi gabansa yasoma tsakuran abincin yanaci kaɗan kaɗan duk da kuwa bawai buƙatar abincin yakeyi ba adole kawai yakeci...   Lomansa huɗu ya aje spoon ɗin dake hanunsa haɗe da jawo plate ɗin yankakkun kayan marmarin dake gabansa yasoma sha,  sai alokacin yasoma jin daɗin bakinsa, amma da kwata kwata bayajin ɗanɗanon komai,, fruits ɗinma baiwani sha me yawaba haka yature yakuma maidakansa yajingina da kujera,, idan akwai abun dayake ƙauna dakuma muradin gani yanzu arayuwarsa baiwuce Zahrah ba, dole yaje gidansu ayau ɗin koda kuwa idan yaje zata ɗauki wuƙa ne taluma masa a cikinsa.....

Yauma de kamar kullum Zaune take a tsakar gidan nasu,  kwanon abincine aje agabanta tana tsakura da kaɗan kaɗan tana kaiwa bakinta domin kuwa haryanzu bata wani jin daɗin jikinta..

Inna ce zaune daga gefenta tana ta ƙoƙari wajen ganin ta seta tashan radion ta..

Wani yarone yayi sallama yace wai ana ƙiran Zahrah,,   "Jekace tanazuwa" Inna tahanzarta faɗa, har yaron yakama hanyar fita daga gidan, Zahrah ta tsaidasa haɗe da cewa "Kace bazata zo ba"

Hangame baki Inna tayi tana kallon Zahrah "Bazakijeba fa kikace?"

"Eh Inna dan Allah kuma kada kitambayeni dalili" tayi maganar tana me langwaɓar da kanta gefe.
Harara Inna ta watsa mata haɗe dayin tsuka baƙin ciki kawai Zahrah'n takeyi mata wayasani ma ko wanda ke ƙiran nata da alkhairi yazo...

"Wai Bazata zoba" yaron nan yafaɗawa wanda ya aikosa.

Waro idanu Zaid yayi maganar ma shi dariya taso basa, amma a irin wan nan yanayin dayake ciki bayatunanin zai iyayin dariya...

"Wayene yacema bazata zo ba?" Zaid yatambayi yaron.

"Ita da kanta" yaron yabasa amsa domin kuwa shiɗin ɗan maƙotansu ne saboda haka yasan Zahrah'n.

Kai Zaid yajinjina haɗe da cije laɓɓansa,,  Allah sarki rayuwa babu yanda bata juyawa mutum, amma in banda haka wai yau shine a wata ƙasƙantacciyar unguwa kuma ƙofar gidan su mace yakuma aika tace bazata zo ba, shine fa Zaid ɗin da har gobe ƴan mata suke rushing akan sa, to amma meyasa haka takasance dashi?"   ganin da yayi yaron nashirin tafiya ne yasanya yace "Kaje kace injini nace tayi haƙuri tafito"   bamusu yaron yakoma yakuma faɗi saƙon da akabasa umarnin yafaɗa..

Tsuka Zahrah taja haɗe da tashi tsaye  "Kaje kace wai inji Zahrah kozai mutu a tsaye baza ta zoba" tanakaiwa nan azancenta tayi wucewarta ɗaki..

Abunda Zahrah tafaɗa shi yaron nan yazo ya sanarwa Zaid,   kuɗi Zaid yaciro a aljihunsa 1k yabawa yaron  dafari yaron yatsorita yaƙi amsa, amma Zaid yatilasta masa saida ya amsa, haka yaron yatafi yana murna...

Motarsa yabuɗe yashiga yayinda yakifa kansa a steering motar meyasa soyayya zata masa haka, idanunsa Zahrah kawai suke son gane masa tabbas yau bazai taɓa iya runtsawaba matuƙar baiga Zahrah ba,  yana mawa Zahrah wani irin mugun so me tsananin zafi..      Jan motarsa yayi yakoma ƙarƙashin wata bishiya tayanda bakowa zai lura da cewa yana wajen ba, yaƙudurta aransa cewa koda zai kwana a wajen ne bazai gusa ba harsai idanunsa sun mai tozali da Zahrah....

Bayan awa ɗaya

Zahrah ce tafito daga cikin gidan nasu sanye da wani siririn mayafi wayarta ce riƙe a hanunta se kuma wani littafi.     Zaid dake zaune cikin motarsa yana ganinta ya sake waro idanu haɗe da sauƙe ajiyar zuciya me ƙarfi,   jiyakeyi tamkar yaje ya ɗauƙota can caɗak yatafi da ita... Yana kallonta tayi shigewarta wani gida dake kusa da nasu gidan.. Bayan kamar mintuna 8 da shiganta gidan yaga takuma fitowa  da sauri yabuɗe murfin motarsa daniyar ƙarasawa gareta sai de kuma ko taku biyu baiyiba tashige cikin gida ko ganinsa ma ita batayi ba,  haushine yasanyashi buga tayar motarsa da ƙafarsa,      haka yakoma yayiwa motarsa key haɗe dayin reverse yabar unguwar tasu cike da ƙuncin rashin samun daman yi mata magana da be yiba, amma de yaji sanyi sosai a zuciyarsa daya ganta...

*********

Yau tunsafe Zahrah tashiga busy hidama kawai sukeyi ita da Husnah domin kuwa yaune ranar da Dr.Sadeeq yace mata za'a kawo lefenta,,   yanzuma daga shopping suke sunje sun sayo kayan drinks da kuma su snacks wanda za'abawa baƙi.  Zama sukayi akan tabarma suna me da numfashi saboda sungaji sosai,,,   kallon Zahrah Husnah tayi haɗe da sakin murmushi.

"Ƙawata nifa yau daɗi nakeji jinake tamkar ma nice za'a kawowa lefen"   dariya Zahrah tayi haɗe dacewa "To aike kince bayanzu zakiyi aure ba saikin gama school gashi Nuruddeen yana tsananin son kuyi aure amma ke kinƙi"

"Hmm ai zan masa maganane yaturo kawai domin ni mafa yanzu dagaske auren nakeso nagaji da rungumar pillow idan nazo bacci" Dariya suka sanya su dukansu hadda tafawa,   "Allah yashiryeki Husnah" Zahrah tafaɗa tana dariya..  Haka de sukaci gaba da ƴan hirarrakinsu irin na ƙawaye..........

Ƙarfe biyar dai dai wasu rantsa rantsan motoci suka soma tsayuwa a ƙofar gidan su Zahrah duk macen da tafito acikin motar sai kaga tana yatsuna fuska haɗe da soma ƙarewa wajen gidansu Zahrah kallo,   motocine kusan guda goma sha biyu suka kawo kayan lefen ahankali aka shiga fito da akwatuna ana shiga dashi cikin gidan su Zahrah..  Fuska babu yabo ba fallasa haka matan nan suka soma shiga cikin gidansu Zahrah,,,,, da fari'a Inna da tawagarta suka tarɓi mutanen haɗe da basu wajen zama, haka suka zauna wasu daga cikinsu suna yatsuna fuska kamar wanda akace su zauna akan kashi...

"Sannunku da zuwa lale marhaba" Wata mata maƙociyar su Zahrah tafaɗa ga matan da suka kawo lefen.  Amma kuma daƙyar aka samu biyu daga cikinsu suka amsa mata..

Akwatuna ne harguda shabiyu aka jibge akan wata tabarma dake shimfuɗe,,  su Inna ne suka fara ɗagawa matan da suka kawo lefen gaisuwa ciki ciki suka amsa musu cike da isa,,,,,  Aunty Raliya ce ma tayi ƙarfin halin cewa  "Ga kayanan munkawo Allah yasa ayi bikin a sa'a,  Allah kuma yasa asamu kyakkyawar zuri'a"  dagajin yanda tayi maganar kaɗai ya isa ya tabbatarmaka cewa kalaman ba anyi su bane cikin daɗin rai,,,  da Ameen kawai su Inna suka amsa musu,,,  kuɗi Aunty Raliya taciro acikin jakarta bandir ɗin ƴan dubu dubu har na dubu ɗari ta ɗaura akan wani akwati haɗe da kallon ƴan uwanta tace  "Muje ko"   dukansu miƙewa sukayi suka nufi hanyar waje,,, yayinda Inna tasa yaran maƙotansu suka kwashi kayan tarban baƙin da suka musu aka kai musu cikin mota, maman Badi'a ɗaya daga cikin maƙotan su Zahrah ita tazari dubu hamsin daga cikin kuɗin da suka aje tabawa ƴarta Badi'a tace takaiwa matan dasuka kawo lefen,,,  dawowa da kuɗin Badi'a tayi tace ae sun riga da sun tafi koda tafita ƙurar motarsu kawai tagani,,, "To suko wasu irin mutanene haka ae ba haka akeyi ba, ko fa kayan basu tsaya sun nuna mana ba saikace wanda suke akan ƙaya" Maman Badi'a tafaɗi haka cike da mamakin hali irin na matan da suka kawo lefen,,,    washe da baki wata mata daga cikin gayyar Inna tace "Kai amma kuwa Zahrah tayi goshi kuga kayafa kamar wanda za a buɗe kanti" ae kuwa basusan cewa Zahrah tayi goshi ba saida suka soma buɗe akwatunan,, kowanni akwati shaƙe yake da kaya nagani na faɗa,, take Inna tasoma rangaɗa guɗa hadda rawan murna.......

(Team Dr.Sadeeq da Zahrah saiku wanke ƙafa don zuwa gano  kayan  lefen Zahrah🤗)

  *31/December/2019*

*Follow me on Whatsapp and Wattpad*

*Wattpad user name fatymasardauna*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

           *SHU'UMIN NAMIJI !!*

  
       *Written By*
*Phatymasardauna*

*Dedicated To My Brother KHABIER*

*🌈Kainuwa Writers Association*

_{United we stand and succeed: our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}_

*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*

       
         *WATTPAD*
     @fatymasardauna

*Editing is not allowed📵*

(Kutayani jaje wlh sau biyu kenan typing ɗina yana gogewa😨😨 yanzu saida nayi 2000 words wlh ya kuma gogewa maganan danake wlh yanzu haka ina rubutun nan ina kuka😭😭 wlh abun da ciwo sosai😭😭)

       *CHAPTER 74 to 75*

Hayaniya haɗi da guɗan da su Inna keyi  shiyayi sanadiyar janyo hankalin Zahrah dakuma Husnah da suke zaune a ɗakin Zahrah sunyi muƙus,,,,

"Ke nifa tashi zanyi naje nabawa idanuna abinci, dan wlh bazan iya zama aɗaki kamar wata sabuwar amarya ba, ke dai da zaman yazamemiki dole saiki ta fama" Husnah tafaɗi haka tana me miƙewa tsaye daga zaunen da take,,,  murmushi kawai Zahrah tayi mata haɗe da binta da kallo hartafice daga cikin ɗakin...

Hamdala Husnah tayi haɗe da nunatsantsar farincikinta alokacin da idanunta sukai mata tozali da kayan lefen ƙawartata,,,, lallai Dr.Sadeeq yayi ƙoƙari domin kuwa naira tayi kuka, koda kyawun akwatunan aka barka sun isa sanyaya maka rai, balle kuma aje ga kayan ciki masu kyau da tsadar gaske, wan nan shiyasake tabbatar mata da cewa Zahrah bazatayi kuka ba idan ta auri Dr.Sadeeq, saboda me sonkane kaɗai zai iyayin komai dayasan zai faranta maka rai....

Duk yawan atamfofin dake cikin akwatunan nan saida su Inna suka irgesu kaf, turame hamsin banda su laces haɗi da shaddodi dakuma  dangin su materials,,     ɓangaren dogin riguna ma akwati guda aka cika dasu, sosai kuma yasaki bakin aljihunsa wajen zaɓo masu kyau da tsada,,  haka ɓangaren sarƙokima komai yaji domin kuwa kaf cikin sarƙoƙi

Please Login or Register in order to submit comment