Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da ɗan kunnayenta babu wani mai sauƙin kuɗi acikinsu gwala gwalanta har guda uku,, san nan kuma ɓanagaren jaka da  takalma ma yayi ƙoƙari sosai, domin kuwa  kusan kowani kaya yanada jaka da takalmi hadda mayafinsa,, wajen kayan shafa ma yayi ƙoƙari sosai  wajen fidda naira yasai kayan shafa ƴan yayi masu kyau duk da kuwa yasan cewa ita ba gwanar kwalliyan fuska bace...

"Gaskiya kaya yayi kyau yarinya tayi goshi,  ai wan nan kayan ko ɗiyar babban attijiri sai haka" Maman Badi'a tafaɗi haka bayan taƙarewa wani haɗaɗɗen leshi dake riƙe a hanunta kallo wanda a ƙalla kuɗinsa zai kai 50k,,,

"Ƙwarai kuwa yarinya tayi goshi Maman Badi'a ai dama tuntuni nasan fiye da haka ma sai yafaru, ga kaya kan nan harda nasadakarwa!" Inna tafaɗi haka cikin murna...

Wata dake zaune kusa da Inna tace "wan nan haka yake muma dai Allah yabawa namu ƴaƴan mazajen aure masu ƙashin arziki" 

Duka matan suka haɗa baki wajen cewa Ameen domin kuwa babu wacce  zataƙi ace ƴarta ce tasamu wan nan kayan more rayuwan....

Sai kusan magriba matan dasuka karɓi lefen Zahrah suka  soma tafiya, bayan Inna ta yaga musu wani abu daga cikin dubu hamsin ɗin daya rage,, haka suka tafi suna mata godiya suna kuma zuba santin kayan domin kuwa koda maƙiyin Zahrah ne yaga wan nan uban kaya da Dr.Sadeeq yayi mata tabbas dole sai ya jinjina abun.....

Lokacin da Zahrah taga irin yawan kayan lefen da Dr yayi mata kasacewa komai tayi,  sosai abun yabata mamaki domin kuwa bata taɓa zaton zai ɓarnata dukiya mai yawa harhaka wajen yi mata lefe ba, bayan kuma yasan cewa ita ba cikakkiyar budurwa bace,,, sai de taƙudura aranta cewa zata faɗa masa   kayan sunyi yawa......

Gidansu Doctor...

"Gaskiya da sake Hajiya, yakamata a dakatar da wan nan batun auren na Sadeeq da yarinyar nan,  kinkuwa ga gidansu Hajiya? wlhy ko suminti babu a tsakar gidansu zallan turbuɗin yashine, kallo ɗaya zakai musu kafuskanci cewa suɗin faƙara'une basu da komai, kwata kwata ma Sadeeq baisan inda zaije ya nemo aure ba domin a wan nan gidan bana tunanin akwai wata halitta da zata burge wani ɗa namiji acikinsa, kawai dai ni inaga ma asiri sukayi masa wlhy, amma bacin haka banjin dakansa zaije neman aure wan nan gidan!" Auntie Raliya ce ke faɗan haka cikin ɓacin rai.....

Ajiyar zuciya Hajiya tayi cikin ɗacin rai tace  "Hmmm Raliya kenan aeni ban isa hana wan nan auren ba ko kinmanta cewa har ƙarana wajen Baffan ku Sadeeq yakai akan naƙi amincewa da aurensa,  ni yanzu baruwana acikin lamarin aurensa ko mai ya jajiɓowa kansa shiya sani"

Ƙwafa Auntie Raliya tayi haɗe da sakai tafice daga cikin ɗakin Hajiyar, harga Allah ita sam batason wan nan auren da Sadeeq zaiyi, yarasa ma wacce zai kwaso musu sai wacce wani ya haiƙewa a waje san nan kuma ƴar talakawa futuk...

Auntie Raliya tana fita falo ƙawayenta da ta gaiyato suka kai lefe  tare, sukayi caaa akanta kowacce tana ingizata akan cewa tasa afasa auren domin kuwa sam ajin  Sadeeq  yagirmewa neman aure a wan nan gidan matsiyatan,,, take kuwa Auntie Raliya tahau kan zancen tazauna dabas, takuma ƙuduri aniyar lalata zancen auren abune me sauƙi kuma dakanta zataje ta kwaso kayan lefen ƙanin nata........


Ɓata fuska Zahrah tayi haɗe da tunzuro ɗan ƙaramin bakinta gaba  cike da shagwaɓa tace "Dagaske nake faɗa maka kayan lefen nan sunyi yawa, ko ɗazu dawowan Baffa daya gani shima haka yace, kuma kafasan ba kyau yin wasa da dukiya" taƙare maganar tana me langwaɓar da kanta gefe.

Murmushi Dr.Sadeeq yayi haɗe da kwantar da bayansa ajikin kujeran motar dayake zaune akai kana ya lumshe gajiyayyun idanunsa, sautin muryarta nayi masa daɗi sosai...

Shirune yashiga tsakaninsu har na tsawon minti ɗaya.

"Duk abun da mayi miki kin can can ci haka daga gareni ne Zahrah, dan Allah kibar maganar yawan lefen nan, ni banga wani yawa da sukayi ba, naso ma nayi miki wanda yafi wan nan to abubuwane sukai min yawa, amma kin wuce haka a wajena, kuma kinsan ku biyu ne" yafaɗi haka yana me kafeta da idanunsa..

Murmushi kawai Zahrah tayi haɗe da kawar da kanta gefe, sam bataso idan yana kallonta itama ta kalleshi saboda takanjin nauyinsa awasu lokutan,, amma kuma hakanan taji kalmar dayace su biyu ne yaɗan sosa mata rai,  wato idan ma ta manta to yatuna mata...

Wani murmushin Dr.Sadeeq yakumayi sakamakon ganin yanda fuskarta ya ɗan sauya lokaci ɗaya yakuma san maganarsa ce batai mata daɗi ba, dama kuma yafaɗi hakanne don yagane cewa tana kishinsa ne ko a'a....

"Bansan wani irin daɗi da kuma farinciki zan tsinci kaina ciki ba aduk sanda wannan ranar  taruskeni, amma kuma da zanfi kowa jin daɗi idan har Allah ya gwadamin wannan rana!" yafaɗi haka cikin shauƙi, dason kawar da wancen zancen nasu..

Cike da mamaki Zahrah taɗan saci kallonsa haɗi da cewa "Wace rana ce wan nan?"

"Ranar da zaki zamo mallakina, ranarda za'akawomin ke ɗakina amatsayin matata ta sunna, ranar da zan kwana ina kallon wannan kyakkyawar fuskar taki babuko ƙyafta ido"

Kunyane yakama Zahrah wanda haryakaita ga cusa kanta  tsakankanun cinyoyinta, sautari Dr.Sadeeq yakan faɗi abubuwan da suke sanyawa takejin kunyarsa sosai...

Murmushi Dr.Sadeeq yayi haɗe da sake kwantar da jikinsa akan kujeran motar,,,, yana matuƙar son komai na Zahrah ciki kuwa hadda wan nan kunyar nata, tun asalinsa yanason mace me kunya, sai gashi kuma yanzu Allah yabasa, sai de kuma yasan nan gaba kaɗan zaisha fama da'ita saboda idan sunyi aure yasan wan nan halin nata na kunya zatai ta gwadamasa.

Kallon agogon dake ɗaure a hanunsa na dama yayi.

"8:30pm" yafaɗa a bayyane  kana yadawo da kallonsa ga Zahrah wacce har yanzu bata ɗago kanta ba.

"Shikenan to tunda dai kunyana kikeji ni zantafi naga dare yasoma yi" yafaɗi haka adai dai lokacin da yake ƙoƙarin  ɗaura sit belt ajikinsa..

Sai alokacin taɗago kanta amma bata yadda ta kallesa ba,, "Sai da safe" tafaɗi haka tana me ƙoƙarin fita daga cikin motar domin dama taƙosa yace mata zaitafi saboda tagaji da zaman motan gashi tana da assigment kuma gobe zasuyi submit ɗinshi, san nan kuma tana buƙatar kasancewa ita kaɗai domin tattaunawa da zuciyarta a game da sabon al'amarin dayake shirin kunnu mata kai....

Kansa yajinjina haɗe da cewa "Dama so kike natafi ko?"

Murmushi tayi masa kana taɗan  girgiza kan ta alamar a'a, cikin murya me sanyi tace "Bahaka bane kawai de nafara jin bacci ne"

Kansa yakuma jinjinawa cike da gamsuwa  haɗe da juyawa baya yaɗauƙo wata farar leda dake aje kan kujeran gidan baya na motar.

"Idan Allah yakaimu da safe zanƙiraki ina fata zakiyi bacci me daɗi" yafaɗi maganar yana me miƙomata ledan dake riƙe a hanunsa...

Shagwaɓe fuska Zahrah tayi haɗe da marairaice manya manyan idanunta da suke sauƙar masa da kasala aduk sanda ya kallesu,,   "Gaskiya ni dai a'a nagaji da wayon da kakemin, kuma tun ba yauba na faɗa ma hidiman dakakemin yana yawa!"

Lumshe idanunsa yayi  haɗi da buɗesu alokaci guda, idan yanaganin irin wan nan shagwaɓan nata to tabbas zata iya zautar dashi lokaci ɗaya, yafice a hayyacinsa, domin shi shagwaɓan mace nasanyawa yaji feeling ajikinsa sosai,, cikin murya me sanyi yace "Kiyi haƙuri  ki ƙarɓa kinji princess ɗina, kinga ba kyu maida hanun kyauta baya!"

Sake turo baki tayi haɗe da kwaɓe fuska,    abun mamaki sai taga shima ya marairaice mata fuska kamar wani ƙaramin yaro,,  "Please!" yafaɗa cikin muryarsa da tayi ƙasa sosai..

Dole babu yanda ta'iya haka tasanya hanu takarɓi ledan haɗe dayi masa saida safe tafice daga cikin motar,,,  yanaganin shigewarta cikin gida yasaki murmushi haɗe da sanya hanu yashafi sajen dake kwance akan ƙuncinsa,  key yayi mawa motar haɗe dayin reverse yabar unguwar tasu.    Yana tuƙi amma shikaɗai yaketa zuba murmushi, aduk sanda yake tare da Zahrah yakansamun kansa cikin farinciki da nishaɗi, tabbas yanayimawa Zahrah so me tsanani.....

Zahrah kuwa tana shiga cikin gida direct wajen da Inna ke zaune tanufa,  ƙoƙarin zama tasomayi haɗi dayimawa Inna sannu da gida.

Washe da baki Inna ta amsa mata bayan ta kafe Zahrah da'ido, Allah Allah take taga menene acikin ledan da  Zahrah ta shigo dashi..

Dariyane ya ƙwace mawa Zahrah sakamakon ganin yanda Inna ta tsareta da'idanu tamkar wata mayya.

"Dariyan uban me kike? banson shashanci wallahi" Inna tafaɗi haka ga Zahrah a hasale, ganin bata da shirin buɗe ledan...

Hannayenta tasanya ta toshe bakinta haɗe dasoma ƙoƙarin shanye dariyar ta.

Ledan da tashigo dashi ta buɗe tasoma dubawa gasassun kajine manya guda biyu sai kuma sauran kayan ciye ciye kamar su snacks dakuma chocolate,,
Ledan da kajin ke ciki ta ciro ta miƙamawa Inna ae kuwa hanun Inna har rawa yake lokacin da tazo karɓan ledan tsabar kwaɗayi.

Fari'ar Inna ne yasake yawaita sakamakon ganin kaji da tayi, babu wani ɓata lokaci ta yago cinyar kaza ɗaya takai bakinta,, tsabar daɗin kazar saiga Inna tana lumshe idanu haɗi da jijjiga kai.

Murmushi kawai Zahrah tayi haɗe da ɗaukan sauran kayan tawuce ɗakinta yayinda tabar Inna tayi pieces  tana cin kaza hadda rausayar da kai gefe alamar daɗinta takeji....

Jigum tayi haɗe da sake takurewa  waje ɗaya akan ƴar katifartata,,,  tabbas Dr.Sadeeq yacancanci ta sadaukar masa da duka soyayyarta ko dan saboda halaccin da yayi mata a rayuwa, bazatace batasan menene so ba, itacema zata ba da labari akan so, domin ta ɗanɗana zafinsa me matuƙar ɗaci da dafi,,   idan tace Dr.Sadeeq baya burgeta tayi ƙarya, haka kuma idan tace Dr.Sadeeq baida abubuwan burgewa ajikinsa da zasu sa mace tasosa nan ma tayi ƙarya? tabbas Dr.Sadeeq baida wani makusa daga halayya ɗabi'a harma da surarsa yacika cikakken namiji, amma babban abun dake damunta shine batajin tsananin soyayyarsa acikin zuciyarta, bawai tana ƙinsa bane, kawai de zafin soyayyar tasa ne bataji a jiki da zuciyarta, ba kamar yanda taji na Zaid ba,, ada batajin soyayyar Dr.Sadeeq acikin zuciyarta amma ayanzu tayi ƙoƙari wajen ganin takoyawa zuciyarta sonsa,  takuma yarda cewa zata iya zaman aure dashi domin baida wani makusa  atattare dashi wanda zaisa a ƙisa, murmushine yasuɓuce mata sakamakon tunowa da tayi da irin kallon dayakeyi mata ɗazu, tabbas ya iya nuna soyayyarsa a fili, abu ɗaya ne ajikinsa wanda yake ɗaukar hankalinta,  shine ƙwayar idanunsa, duk da cewa shi ɗin namiji ne amma yanada idanu masu kyau wanda zasu sanya maka nutsuwa aduk sanda ka kallesu, hakan yasa ako da yaushe takeson kallon cikin idanunsa amma bata iyawa saboda kunya..... Tunanin Zaid ne yakutso kansa cikin zuciyarta harsai da taji faɗuwar gaba,,    "Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un!" shine abun da tashiga nanatawa acikin zuciyarta,, wannan wani irin bala'i ne? tunda Zaid yashigo cikin rayuwarta shikenan kuma komai nata ya ruguje, lallai itakam taɗaukeshi amatsayin annoba wanda gani da jinsa babu alkhairi .....

Yau Kwanansa ɗaya da wuni ɗaya cur baisanya ko wani irin abinci abakinsa ba, sai ruwan giya dayake ta kwankwaɗa ba dare ba rana,, damuwa ce tayi masa mugun yawa abubuwa gaba ɗaya sun caɓemasa,    kallo ɗaya zakai masa kafuskanci cewa yanacikin halin damuwa, domin kuwa lokaci ɗaya ya zabge rama ta bayyana kanta ajikinsa, yayinda manya manyan idanunsa suka sake fitowa waje,,    wani irin zafi zuciyarsa keyi masa, baisan da yaushene kuma ta yaya yakamu da soyayyar Zahrah me tsanani haka ba,     tunjiya yarasa nutsuwarsa a sakamon labari dayaji daga bakin wanda yasanya  yana kulamasa da shiga da ficen   Zahrah,  inda yasanar masa cewa ankawowa Zahrah kayan lefe, iya ƙololuwar tashin hankali Zaid yashiga dajin wannan magana, sam be shirya wa rasa Zahrah ba saboda rasata dai dai yake da rasa rayuwarsa gaba ɗaya, akuma yanda yakejin matsanancin sonta a cikin zuciyarsa zai iya sadaukar da komai nasa gareta, ko da kuwa ransa ne...

Yanzuma zaune yake yatusa wani ƙaton hoton zanen fuskarta daya zana a daren jiya a gaba yana kallo, saboda tsabar kyawun da zanen yayi idan kagani bazamakace zane bane...

Idanunsa dake kan idanunta na cikin zanen ne suka kaɗa sukai jajur dasu.  Saiyanzu yakejin tsanar kansa dakuma tsanar wannan banzan halin nasa, sai yanzu yake tsananin danasanin abun daya aikatawa Zahrah, haƙiƙa yasan cewa ya zalunci Zahrah ya cutar da'ita ya lalata mata rayuwa, kuma hakan da yayi mata shiya nisan ta masa ita, wani irin tsana ne Zahrah tayi masa haka? shin tasan irin zafi dakuma raɗaɗin dayakeji akanta kuwa? yadaina cin abinci tasanadiyar ta, wannan yasa  ulcer tayi masa mummunan kamu, gakuma soyayyarta da ta sanya masa ciwo a zuciya,, ta wani ɓangare kuma yana fama da wani  matsanancin ciwon kai wanda dashi yake kwana yake kuma tashi, cikinsa kuwa tamkar anhura masa wuta haka yakeji aciki,, hanu yasanya yashafi zanen fuskartata, tabbas idan baisamu Zahrah ba bazai taɓa iya cigaba da rayuwa ba,,, abun da Zaid baisani ba shine tuni  ruwan hawaye sun cika idanunsa gangarowa kan fuskarsane kawai da basuyi ba,  zumbur haka yamiƙe tsaye haɗe da zura silifas ɗinsa ko wayoyinsa bai tsaya ɗauka ba, haka yafice daga cikin ɗakin nasa....

Yana fita compound ɗin gidan nasu driver'n sa yaƙaraso garesa da sauri,,,, "Oga fita zamuyi ne?" driver'n yatambaya cike da girmamawa,,  kai kawai Zaid ya ɗaga masa alamar "eh"    jikin driver'n na rawa yace "Oga da wacce motar zamu fita?"

Cike da ƙosawa Zaid yace "Kowacce"

Driver yayi mamaki sosai dajin maganar Zaid domin yasan idan dai har fita Zaid ɗin zaiyi to sai yazaɓi motar dayakeso amma kuma sai gashi yau yace kowacce..   Wata haɗaɗɗiyar baƙar benz driver'n yatuƙo daga cikin parking space zuwa inda Zaid ke tsaye ya harɗe hannayensa acikin  aljihun wandon track suit ɗin dake jikinsa..

Zaid nashiga cikin motar driver yabawa motar wuta yayinda me gadi ya wangale musu gate suka fice daga cikin gidan.....

Baffa ne zaune akan dakalin ƙofar gidan yana me latsa ƴar ƙaramar wayarsa, zaman da yayi Zahrah yake jira ta dawo daga aiken da yayi mata,, daf dashi motar tayi parking, hakan yasa Baffa  ya kafe motar da'ido don ganin wanene zai fito daga ciki...

A hankali Zaid yabuɗe murfin motar yafito, kallonsa Baffa yashigayi daga sama har ƙasa saboda sarai yagane shine  ɗan iskan me kuɗin da yamawa Zahrah fyaɗe,  saida Baffa yagama ƙaremasa kallo kafun yakawar da kansa gefe...

Da sallama Zaid yaƙarasa wajen Baffa,, ciki ciki Baffa ya amsa masa sallaman,    durƙusawa Zaid yayi haɗe dayin ƙasa da kansa cikin murya me sanyi yace "Kagafarceni Baffa, nasan ban kyautaba amma dan Allah kada ka hanani auren Zahrah, wallahi a yanda nakeji idan bansamu Zahrah ba mutuwa zanyi!"

Baki Baffa yasake yana kallon Zaid,  namiji har namiji amma wai yana cewa idan bai auri Zahrah ba mutuwa zaiyi kuji iskanci fa,,
Sake ɗago kansa Zaid yayi haɗe da watsawa Baffa jajayen idanunsa,   "Wlh Baffa yanzu da gaske nake aurenta zanyi, kada kace zaka hanani ita dan Allah, wallahi Zahrah tana da matuƙar mahimmanci acikin rayuwata!"

Yanzukam kallon tsab Baffa yashiga yi masa saida yaɗauki kusan minti biyu yana kallon Zaid ɗin kafun yaɗan nisa haɗe da cewa "Bantaɓa tunanin kana da idanun da zaka dawo ka kallemuba, amma sai gashi kadawo kana kallona har kuma kana roƙona dana baka auren Zahrah, idan da kanasonta tunfarko mai yasa baka aureta ba kalalata mata rayuwa? ni bazance maka komai ba saide ince munbarka da Allah saboda bamu da yanda zamuyi dakai, amma kuma kasani bazan baka auren Zahrah ba harsai da amincewarta, idan har tace ta amince zata aureka shikenan nime iya baka aurenta ne" Baffa yana kaiwa nan a zancensa yatashi yayi shigewarsa cikin gida.. Da ƙyar Zaid ya'iya tashi ya  zauna akan dakalin da Baffa yatashi hannayensa duka biyu yasanya ya dafe kansa dake yi masa nauyi kamar ze faɗo ƙasa.....

Da ɗan sauri take tafiya tana latsa wayanta burinta kawai shine taganta acikin gida, duk sanyin da akeyi yau yagama ratsata, saboda haka take Allah Allah ta'isa gida.. sam bata lura da akwai mutum a ƙofar gidan nasu ba dan hankalinta gaba ɗaya nakan wayartata...

"Zahrah!" taji anƙira sunanta da murya wacce bazata taɓa mantawa da'ita ba a iya tsawon rayuwarta...
Ja tayi  ta tsaya haɗe da maida kallonta inda taji sautin muryar tafito,, tabbas kuwa  ba gizo kunenta keyi mata ba shiɗinne dai, kallonta yashigayi da idanunsa wanda suka zama jajaye, itama tsayawa tayi tana kallonsa, a wannan karon kam babu alamar wasa kokuma tsoronsa akan fuskarta,, kallonsa takeyi ido cikin ido...

"Dan Allah Zahrah ki saurareni, wallahi inasonki inamiki so me tsanani, inamiki soyayyar da babu wani wanda zaiyi miki shi a duniyar nan, meyasa bazakisoni ba Zahrah? Inasonki, Inasonki, Inasonki da duka zuciyata, dan Allah kiyarda muyi aure Zahrah!" cikin rauni yaƙare maganartasa saikace ba jarumin namiji ba...

Kallonsa Zahrah tashigayi tundaga ƙasan sa harzuwa samansa, wani irin murmushi tayi masa wanda ita kaɗai tasan ma'anarsa,,,      "Bantaɓa tunanin zaka iyayin wannan jarumtar ba,  ƙwarai kayi ƙoƙari dahar ka iya tunkarana da wannan maganar, sai de kuma tun awancan lokacin na faɗamaka kafita a rayuwata, idan duka mazan duniya zasu ƙare na gwammace na mutu babu aure dana aureka,  ka kalleni da kyau bancancanci zama matar mazinaci kuma ɗangiya ba,  niba irin matan nan bane da yacancan ci fasiƙai irinka su samuba,  natsaneka Zaid tsana me tsanani, wlhy danaga ranar da zan zamo matarka gwamma acemin naga ranar mutuwa ta,  katafi kawai Zaid kaje nabarka da Allah, kuma inaso kasani cewa yau ɗin nan za'a tsaidamin ranar aurena da wanda zuciyata ta aminta dashi, wanda yake kamili me tsoron Allah,  shi ba kamar kai bane ɗan giya!" tanakaiwa nan azancenta tajuya daniyar shigewa cikin gida...
Dasauri Zaid ya kamo hanunta haɗe da jawota  da ƙarfi tafaɗa cikin jikinsa, dai dau lokacin ne kuma motar Dr.Sadeeq taƙaraso wajen....


*Happy New Year 💃*

    *2/january/2020*
__________________________

*Follow me on Whatsapp and Wattpad*

*Fatymasardauna*

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*SHU'UMIN NAMIJI !!*

*Written By*
*Phatymasardauna*

*Dedicated To My Brother KHABIER*

*🌈Kainuwa Writers Association*

_{United we stand and succeed; our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}_

*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*

*WATTPAD*
@fatymasardauna

*Editing is not allowed📵*

*CHAPTER 76 to 77*

Saurin turesa tayi haɗe da hankaɗasa gefe da iya ƙarfinta ta ƙwace jikinta daga nasa, wani irin mugun kallo tashiga yimasa haɗe da tofar da yawu aƙasa, da ace wulaƙanta ɗan adam abune me kyau to tabbas da akan fuskarsa zata tofa wan nan yawun ko hakan zai sanya ya gamsu da irin tsantsar tsanar da takeyi masa.
"Banafatan na sake haɗa jikina da wan nan ƙazamemmen jikin naka mai ɗauke da tarin najasa!" cike da tsananin ƙyamata Zahrah ta faɗi haka ga Zaid haɗe da juyawa tanufi hanyar shiga gida..

"Koda kuwa na daina aikata zina nakuma daina shan giya?" Zaid yafaɗi haka cikin dakakkiyar muryarsa...

Cak ta tsayawa daga tafiyan dakeyi, sosai maganar tasa ta daki zuciyarta..

A hankali yashiga takowa zuwa inda take saida yazo gaf da'ita kafun ya tsaya....... " I promise to leave all my bad habit if you wish to marry me, I love you Zahrah, trust me for the sake of God, i will not hurt you!" gaba ɗaya muryarsa tayi rauni dagajin muryartasa kasan cewa yana cikin matsanancin damuwa...

Idanunta da suka kawo ruwa ta ɗago ta watsa masa su,,,,, Shi ɗin ma kallon ta yakeyi da idanunsa wanda suka zama tamkar an watsa musu garin barkono,, sun ɗauki tsawon mintuna biyu suna kallon juna kafun da ga bisani Zahrah tajuya ta shige cikin gida, ko sake waiwayosa batayi ba yayinda yashiga ƙiran sunanta amma bata amsa masa ba harta shige cikin gida, because tagaji da wannan ɗan iskan yaudaran nasa, yanzukam bazata iya ɗauka ba....

Iskan dake cikin bakinsa ya fesar haɗe da meda duka hannayensa cikin aljihun wandonsa, cikin sanyin jiki haka yakoma cikin motarsa driver yayimawa motar key suka ɗauki hanyar fita unguwar batare da sun kula da Dr.Sadeeq dake zaune cikin motarsa ba...

Haƙoransa ya sanya ya danne laɓɓansa na ƙasa komai daya faru akan idanunsa ya wakana sai de baijiyo magan ganun da suka shiga tsakaninsu ba,, wani irin ɗaci yaji maƙoshinsa nayi, iya matuƙa ɓacin rai yashigesa, bakomaine yafi komai ƙona masa ransa ba kamar yanda yaga Zaid yajawo Zahrah jikinsa, hakanan yaji wani irin mugun kishi ya turnuƙe masa zuciya,, babban abun dayafi ɗaga masa hankali shine yanayin daya hango fuskar Zahrah, tabbas yafuskanci wani ɓoyayyen abu daga gareta,,, key yayi mawa motarsa cikin ƙunan rai yayi reverse haɗe da barin ƙofar gidan nasu batare da ya aika ayi masa ƙiranta ba..

Zahrah na shiga cikin ɗakinta ta durƙusa a ƙasa haɗe da fashewa da wani irin kuka me tsuma zuciya kaicon zuciyarta da ta so mata namiji irin Zaid, ashe da gaske shiɗin mazinaci ne tunda gashi da bakinsa yafaɗa, kuka tashiga yi tamkar wacce aka sanarmawa da ranar mutuwarta, yayinda wani abu yataso ya tokare mata ƙirji wanda batasan komenene shi ba kamar yanda batasan kukan me takeyi ba...

Driver yana parking motar Zaid yace yafita ya bashi waje, aikuwa babu musu driver'n yafita daga cikin motar..... Kansa ya kafa ajikin kujera haɗe da fidda wani irin zazzafan numfashi ta bakinsa, zuwa yanzu kam bazai iya jurewa ba, sam bazai iya jure raɗaɗi dakuma azaban soyayyar Zahrah dake damunsa ba, tabbas da ace zai iya to da yayi iya ka ƙoƙarinsa wajen ganin ya yakice soyayyarta acikin zuciyarsa amma hakan bazai yiwuba domin kuwa duk kowani kwanan duniya soyayyarta ƙara ninkuwa takeyi acikin zuciyarsa, zuwa yanzu soyayyar Zahrah babu inda bata ratsa acikin jikinsa ba,,,, a ƙalla yakai kusan 30 minute acikin motar yana saƙawa da kuncewa, da ƙyar ya'iya fitowa daga cikin motar kai tsaye yanufi babban parlour'nsa dake cikin guest house ɗin nasa, domin kuwa daga gidan su Zahrah guest house ɗinsa suka yiyo....

Yana shiga cikin falon ya faɗa kan doguwar kujera haɗe da lumshe kyawawan idanunsa, kansa ne ke saramasa yayinda juwa ke ɗibansa, lallai yazame masa dole yasamawa kansa mafita, yazama dole yafarka daga wannan mafarkin daya keyi tabbas al'amuransa a yanzu suna masa kama da al'amara,, tabbas yana buƙatar samun relief daga damuwar dayake ciki, amma sai dai babu amfanin shangiya a yanzu domin kuwa koda yashama bata basa wani relief ɗin da ya kamata, miƙewa yayi yashiga cikin ɗakinsa, kai tsaye wani ɗan drower yanufa haɗe da buɗewa, hanu yasanya ya ɗauko wata wayarsa ƙirar techno phantom 9 wanda dama yana ajewane saboda rana irin haka, kasancewar baifito da wayoyinsa ba duk yabarsu a gida,, yana kunna wayar ya laluɓo wata lamba haɗe da turawa lambar text message, yana ganin alamar saƙon ya isa inda yakeson yaje yayi switch off ɗin wayar haɗe da maidata inda ya ɗaukota kwanciya yayi akan makeken gadonsa wanda yasha shumfuɗa ta alfarma, cusa kansa yayi cikin pillow haɗe da soma fitar da numfarfashi akai akai....

A hankali taturo ƙofar ɗakin wanda kafun ma tashigo tuni ƙamshinta yarigata shigowa, sanye take da jan wando pencil wanda yayi matuƙar bayyana kyakkyawar surar jikinta yayinda rigarta yakasance baƙa me kyau, rigan irin masu faɗin wuyan nan ne hakan ne yasanya manya manyan breast ɗinta bayyana kansu tasaman rigar,, takalmine me uban tsini a ƙafarta yayinda ta tufke dogon gashin kanta da jan ribbon kalan wandonta,, kallo ɗaya zakayi mata kafahimci cewa wayayyar macece ƴar duma, shigarta kaɗai ya isa yabayyana maka ainihin ko wacece ita, saboda bashigane da mata masu mutumci sukeyi su fita ba kamar yanda ita tayi, domin kuwa ko ɗan kwali babu akanta, wani irin murmushine kwance akan fuskarta dake nuna alamar cewa tana cikin farinciki,, lumshe idanunta tayi haɗe da buɗesu alokaci guda, kallon surarsa kaɗai ya isa sanya mata nutsuwa, tajima tana tsumayi da kuma fatan Allah ya sake ɗaurata akansa, harta cire rai saikuma gashi yau shi da kansa ya gayyatota, lallai zata iya cewa a rana irin ta yau tafi kowa sa'a..

Duk da yaji ƙamshin turarenta acikin hancinsa hakan baisanya yaɗago kansa ba,,
Cikin taku irin na matan da suka goge wajen iya ɗaukar hankalin ɗa namiji tashiga takowa har zuwa inda yake kwance ya yinda juyawa ƙofa baya...

Hanunta tasanya a bayan wuyansa haɗe da soma shafawa a hankali,, cikin wata murya me sanyi dajan hankali tace "Man!"
Shiru yayi bai amsa mata ba, duk da kuwa cewa yanajinta,,, ganin bai amsa taba yasanya tayi murmushi haɗe da cire takalman dake ƙafarta ta hawo kan gadon,, bakinta ta sanya adai dai saitin tsakiyar bayansa tashiga tsotsa haɗe da shafa bayan wuyansa a hankali,,,, wani irin zubawa Zaid yaji tsikar jikinsa tayi, adai dai sanda take ƙoƙarin nuna masa wani sabon salo.... "Meenal!" yaƙira sunanta da wata irin murya wacce ta riga da ta cushe..

Murmushi Meenal tayi haɗe da mirginowa ta dawo gabansa suna fuskantar juna, lumshe idanunta tayi alokacin da tayi arba da kyakkyawar fuskarsa, wallahi tana

Please Login or Register in order to submit comment