Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

haɗe da miƙewa tsaye "Mace zaki haifa insha Allahu, wannan bayin kaina ko yin wani bane, yin Allah ne, shiya hanani, yanzu kuma shiya bani, saboda haka bazan gajiya dayi masa godiya ba" yana kaiwa nan azancensa yawuce ɗakinsa.   Haryanzu dai ita bata fahimci ina kalamansa suka dosa ba, kwanciya tayi akan kujera, minti kaɗan bacci ɓarawo yayi gaba da ita.

Shikuwa yana shiga cikin ɗakinsa, ɗan ƙaramin drawer ɗinsa ya buɗe wanda ciki yake aje diary'nsa, ɗauko diary,n yayi yasoma rubutu, yana kammalawa ya buɗe shafin farko na diary'n nasa, take wani hoto wanda ke ɗauke da kyakkyawar fuskarta ya bayyana, tayi kyau ƙwarai acikin hoton, gaɗan ƙaramin bakinta nan yasha lipstick, murmushi yayi alokacin daya kai hanu yashafi kan kumatunta,   ahankali yace "Nasani dama zaki dawo gareni, kobata hanyar zama tawa ba, amma tabbas zaki dawo gareni, gashi kuma kindawo ta hanyar dayafi dacewa,  nan bada jimawa ba zakizo amatsayin tawa ta har abada, duk wuya duk tsanani ke ɗin zaki kasance tawace, nine wanda bakida kamarshi acikin duniya, nine mutum guda ɗaya wanda zai kasance me matuƙar mahimmanci a wajenki, nine wanda bazaki taɓa samun irina ba har abada, ni ɗayane nake da wannan matsayin agareki, bayanni babu wani"   wasu irin hawayene masu zafi suka gangaro daga cikin idanunsa, da sauri yarufe diary'n kana ya shiga toilet donyin wanka, jinsa yake acikin matsanancin farinciki, lallai Allah yamasa kyauta, wacce zata kasance mafi soyuwa agareshi.
(Wayaga Zaid da ƴa ko ɗa😜)

***
Wani irin kulawa na sadidan Zaid ke bawa Afrah, kome takeso adunia shiyake yi mata,  zuwa yanzu harmamakinsa takeyi, irin yanda yake nunamata tsananin ƙauna,  wani lokaci har kuka takeyi, itama tana matuƙar son cikin sosai, amma yanda Zaid ke ƙaunar cikin ba'a magana, tasani badon komai yake nuna mata wannan ƙaunarba saidon cikin dake jikinta,   haka take rainon cikinta cike da ƙaunar abun dake cikinsa, wani lokaci tana mamakin yanda Zaid keta faɗan wasu irin maganganu wanda suke matuƙar ɗaure mata kai, daga zaran yataɓa cikin sai yafara cewa "Babyna kina lafiya ko, na ƙosa kidawo gareni, inakewarki sosai, kizo muyi rayuwarmu wacce bamuyita ba da, muyi rayuwa cikin farinciki, inasonki sosai babyna!" abun dayake faɗa kenan, hakan kuwa mamaki yake bata sosai, duk kuwa yanda taso fassara kalaman nasa, bata iyawa, hakanan take haƙura kawai ta share. Cikin nada wata huɗu Zaid ya ware wani ɗaki dake cikin bedroom ɗinsa, saida yacika ɗakin tam da kayan wasan yara, babu abun da babu nawasan yara acikin ɗakin,   acewarsa ɗakin babynsa ne, itadai Afrah idanu kawai tazuba masa, saboda taga soyayyar dayakeyiwa abun dake cikinta naneman zautar dashi.

*** *** ***
Nigeria.

Masha Allah cikin Zahrah ya ƙara girma sosai domin kuwa yanzu yana wata na bakwai ne, sosai cikin yayi turtsetse dashi,  zuwa yanzu batasanya wani kaya sai dogin ruguna, irin masu faɗin nan.
Tana zaune atsakiyar falon, yayinda ta tusa wani tray wanda ke ɗauke da kayan fruit agaba, gefe kuwa plate ɗin dambun nama ne wanda yaji albasa, sai kuma ɗan wake wanda yaji cabbage da cocumber ga tomatoes, yasha mai da yaji, wai duk wannan tulin kayan ciye ciyen Zahrah so take taci kowanne acikinsu.  

Auntie Raliya ce tafito daga kitchine hanunta ɗauke da  wani cup wanda cikinsa ke ɗauke da wani zuma, me magani aciki.

"Manya anata fama kenan" Inji cewar Auntie Raliya.

"Wallahi Auntie ni duk na rasa ma da wanne zan fara, inaga ɗanwakena kawai zanci sauran kuma nabari saina koma gida" Zahrah tafaɗi haka ga Auntie Raliya tana me jawo plate ɗin ɗanwaken ta.

Dariya Auntie Raliya tayi haɗe da zama kusa da Zahrah'n  "Gaskia Bro bai iya ajiyaba, wannan wani irin ɗa ne haka yasa miki acikin cikinki, yaro ne zance ko yarinya, sai shegen ci"

Dariya Zahrah tayi sosai haɗe da kallon Auntie Raliya cikin dariya tace "Wallahi kuwa Auntie, dubeni fa yanda nayi ƙatuwa, nayi muni, shikuma duk kwanan duniya ƙara kyau yake, gaskia ni bazan yarda ba, auntie wayo kawai yamin"
Dariya Auntie Raliya tayi haɗe da miƙowa Zahrah kofin dake riƙe a hanunta.   "Ungo amsa kishanye duka"
Zaro idanu Zahrah tayi, haɗe da kallon Auntie Raliya'n "Auntie kamar tsumi ne fa, acikin cup ɗin?"
"Ba kama bane, tsumine me kyau na mata, wanda yake matuƙar wujijjiga oga, amsa kisha banason gardama" Auntie Raliya tace tana ƙoƙarin kai kofin bakin Zahrah.

Kwaɓe fuska Zahrah tayi, haɗe da ɗan marerece ido. "Wallahi Auntie tsoro nake insha wani tsumi, a yanzun, kinsan kuwa yanda nake fama, doctor fa shiɗewa yake, nasha wannan kuma ae shikenan sumar dashi kikeso nayi"

Dariya sosai Auntie Raliya tayi, haɗe da ɗaukan tsuminta ta shanye  "Shikenan to idan kin haihu na miki haɗi na musamman, matar doctor, ashe ba abanza ba, gaba ɗaya ƙanina ya sukurkuce akanki, wato kinsan me kikeyi masa" cewar Auntie Raliya.
Dariya Zahrah tayi haɗe da cigaba da cin ɗanwakenta, sai kaɗa kai take wai ɗan waken yayi daɗi, itakuwa Auntie Raliya saiyi mata hira take,  sosai suka seta ita da ƴan uwan mijinta,  ƙauna sadidan take samu daga wajen Hajiya,  yayinda Auntie Raliya ma ke nuna mata so, sun saba sosai da Auntie Raliyan, harjinta take kamar ƴar uwarta tajini, don babu abun da take ɓoyewa Auntie Raliyan, dayake Auntie Raliyan ma irin wayayyun matan nanne, basu da nuƙu nuƙu, baruwanta dawani abu waishi surukanta, ta ɗauki Zahrah'nne kamar ƴar ƙaramar ƙanwarta, don har sirrin yanda ake kama me gida a hanu take faɗa mata..
Sunsha hira sosai da Auntie Raliya, sai bayan sallan Isha doctor Sadeeq yazo ya ɗauketa suka koma gida.  Washe gari kuwa, tun 7 am tatafi gidansu amarya Husnah, don yau za'ayi kamunta, kuma itace best friend, don ma ciki yayi mata cikas. 
Anyi kamu cikin kwanciyar hankali, yayinda kamun ya ƙawatar sosai, anyi ɓarin naira sosai baga gidansu ango ba baga gidan su amarya ba, naira tayi kuka don ankasheta a wannan ranan, kayan da amarya tasanya ma kaɗai kuɗinsu baƙaramin yawane dasu ba. Zahrah bata bar gidansu Amarya ba sai bayan magrib kusan 9 pm,  haka ta koma gida agajiye. Washe gari kuma,  aka rangaɗa walima, shima sosai yaƙayatar don anyi musu wa'azi me ratsa jiki,  ranan friday kuma aka ɗaura auren Husnah da angonta,  sosai dai akasha shagalin bikin Husnah, inda Zahrah tataka rawar gani sosai, wajen ganin tabawa ƙawartata kyauta, wacce zata burgeta. Ranan da aka kai Husnah ɗakin mijinta sosai Zahrah tayita mata tsiya, ita kuwa Husnah ko ajikinta, cewa ma tayi "Mijinta baifi ƙarfinta ba, bata wani jin tsoro, tsaf zata iya ɗauke buƙatarsa".....
***
Yana zaune akan kujera ita kuma tana zaune aƙasa, wani irin ciwo takejin cikinta nayi mata, tun ɗazu yake ankare da ita, amma dai baice da ita komaiba, ganin dayayi tana murƙususu waje ɗaya ne yasanya sa cewa "Baby yadai, akwai damuwa ne?"  murmushin dole ta ƙaƙalo haɗe da dubansa ta mererece fuska. "Samad marata kemin ciwo da cikina" tafaɗi haka tana me cije laɓɓanta.

"Subahanallah to kodai naƙira Bro nafaɗa masa ne?" yatambayeta cike da damuwa.

Da sauri ta girgiza masa kae haɗe da cewa "A'a  dan Allah Samad karka ƙirasa, banaso yatashi hankalinsa"

Murmushi kawai Samad yayi haɗe da cewa "Babe ƴar daɗi miji"

Harara ta aika masa haɗe da murguɗa masa baki tace "Eh ɗin"
Murmushi yakumayi yaci gaba da cin abincinsa, itakuwa sake matsewa tayi tana mejin ciwon naƙara ƙaruwa.   (Kodai Babe haihuwa zatayine ? Chaiii wayaga Zahrah a Labour room🏃‍♀🏃‍♀)

(Bansan me na rubuta a chapter 66 kuma 112 ba😂 nasan nayi muku shirme lokacin wallahi ina yanayi ne😂 komai bibbiyu nake gani🤣 amma yanzu nadawo normal💃🏼  My Wattpadians ina ƙaunarku har acikin jinina, inamugun ganin mutumcinku, wallahi na rantse muku saboda ku kaɗai nake typing, inaji daku irin sosai ɗinanan fa, kucigaba da bani vote nikuma zan kawo muku wani labari me sugar, sai yafi Zaid daɗi💃🏼😂)


      *26/February/2020*


   *✅OTE ME ON WATTPAD*
          @fatymasardauna


#Love
#Romance
#SON SO @ my only wattpad fans
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

      *SHU'UMIN NAMIJI!!*

    *Written By*
Phatymasardauna

*Dedicated To My Brother KHABIER*

*🌈Kainuwa Writers Association*

           *WATTPAD*
     @fatymasardauna

  
      *Chapter 114*

Har ya ƙare cin abincin tana nan zaune sai rumtse ido da cije baki take,  ƙirjinta ne yasoma bugawa akai akai, sakamakon tunawa da tayi cewa akwai aiki  babba agabanta.  Miƙewa tayi daga zaunen da take, ahankali take taka ƙafanta data ɗan kumbura, harta shige cikin ɗakinta.  Da kallo yabita har ta ɓacewa ganinsa, murmushi kawai yayi shima kana ya ɗauki wayarsa yafice daga cikin falon.
Tana shiga cikin ɗaki direct ta wuce bathroom wanka tayi da ruwan zafi, kana ta zo ta ɗauki magungunanta tasha.    wata ƴar ƙaramar riga tasanya ajikinta, kana tabi lafiyar gado ta kwanta, minti shida tsakani bacci ya ɗauketa.

Kwanciya yayi luf abayanta bayan yacire rigar dake jikinsa,  hanunsa yasanya ya ɓalle mata aninayen dake jere a gaban rigarta,  lumshe kyawawan idanunsa yayi haɗe da sanya hanu ya shafi breast ɗinta.  Saida ya sauƙe ajiyar zuciya me ƙarfi, kana ya sake rungumeta ajikinsa, kansa ya ɗaura akan wuyanta, haɗe da sanya harshensa, yashiga lasan fatar wuyanta, yayinda hanunsa ke kan breast ɗinta, yana murzawa a hankali. Kamar acikin mafarki takejin abun da yakeyi mata,ahankali ta buɗe idanunta, batakai ga kallonsa ba, daddaɗan ƙamshin turarensa, ya sanar da ita cewa shine, sake narke jikinta tayi acikin nasa,  jin alamun cewa tafarka ne, yasanyasa juyo da ita suka zama suna fuskantar juna.  Kallonsa tayi da idanunta, da suke cike da magagin bacci, murmushi tasakarmasa haɗe da sanya hanu ta shafi lallausan sajen fuskarsa.   Idanunsa da suke cike da  tarin sha'awarta ya watsa mata haɗe da matso da fuskarsa daf da tata, har numfashinsu na gauraya dana juna,  yanayin irin yanda yake kallonta ne, yasanya taji gaba ɗaya jikinta yayi sanyi, wani irin ƙaunarsa me sanyi taji tana shiga cikin jikinta.  Ranƙofowa yayi haɗe da yi mata rumfa da ƙirjinsa,  baikai gayin romancing ɗinta ba, amma gaba ɗaya kallon daya keyi mata, ya gama kashe mata jiki,  ahankali ta lumshe idanunta, sosai ƙamshinsa keyi mata daɗi.   Kansa ya cusa acikin ƙirjinta dake tashin ƙamshi, ahankali yake goga mata lallausan sajensa akan breast ɗinta.  Sake lumshe idanunta tayi, haɗe da sanya hanunta, a bayansa ahankali take shafawa, tana fidda wani irin numfashi.  Slowly yake kissing ɗinta, tundaga ƙirjinta har zuwa kan bakinta, da kaɗan kaɗan yake tsotson pink lips ɗinta, yana me lumshe idanunsa, da suka koma kalar ja,     baitaɓa mata irin wannan kissing ɗin me rikita tunani ba sai yau, sosai takejinta cikin wani irin yanayi na musamman,  ajiyar zuciya me ƙarfi ta sauƙe, haɗe da buɗe bakinta,  kamar zatace dashi wani abu, amma kuma babu wata kalma da zata iya fitowa daga bakinta, saboda gaba ɗaya ya shiɗar da ita. Ya ruɗata da salonsa,   harshensa ya tura acikin bakinta, haɗe da soma kaɗa mata shi acikin bakin nata.  Hanunsa yasanya ya zare ƴar rigan dake jikinta.  ƙasa yayi da kansa yana sucking ɗinta,  kamar kullum daya fara sucking ɗinta take saka masa kuka ta kuma shiɗe masa, yau ma hakance takasance, ganin numfashinta nashirin ƙwace mata ne, yasa ta janye kansa, haɗe da mirginawa gefe tana sauƙe wani irin numfashi,  ji take kanta na juya mata,  ga wani irin sha'awarsa dake fusgarta. Sake kwanciya yayi a bayanta, haɗe da cusa kansa cikin tulin gashin kanta.   Numfashi shima yake fitarwa akai akai, burinsa ɗaya shine yaji wannan ɗumin nata, me zautar masa da tunani.
Juyowa tayi gareshi haɗe da hayewa saman ƙirjinsa, hanu tasanya tana shafa gashin kansa, yayinda taɗaura bakinta akan ƙirjinsa, tana sakar masa wasu irin kiss dake tada masa da tsikar jiki,    lumshe idanunsa yayi yana me karɓan saƙonta, dama akunne yake matuƙa, gashi yanzu tana ƙara kunnasa.   Ganin da yayi cewa zata haukatasa da yawa ne, yasanya sa dawo da ita ƙasansa yazamana shine a samanta.   Kallon da yayi mata ne ya ƙara kashe mata jiki,  haɗe bakinsu yayi waje ɗaya,  lokacin da ɗumin jikinta ya ratsashi saida ya sauƙe wata ajiyar zuciya me ƙarfin gaske, take kuma ya fara manta awacce duniya yake, atare suke kissing ɗin juna, cike da wani irin so,   sun matuƙar zautuwa, kowannensu yatafi wata duniyar ta daban, amma duk da haka bakinsu yana cikin na juna..........

*** *** ***
Bayan Wata Biyu.😜

Yanzu cikinta yana wata tara harda sati biyu, amma haihuwa shiru, zuwa yanzu ko tashi bata iyawa sai antaimaka mata, cikinta yayi wani irin girma, hakannema yasa Hajiya da kanta taje ta ɗaukota, ta dawo gidanta da zama, bahaka Dr.Sadeeq yasoba amma babu yanda ya iya, dolensa ya haƙura, kuma sosae yake kewar matartasa, wai donma yanasamu suna keɓewa, idan dare tayi, har hotel suke zuwa.

Kwance take akan doguwar kujeran dake falon Hajiya, green Apple ne riƙe a hanunta, ita bata ciba ita bata ajiye ba.  Tun daran jiya take fama da wani irin ciwon mara dana baya,  amma babu wanda ta faɗawa, gudun kada su tashi hankalinsu,  yanzu kam abun yasoma fin ƙarfinta, don ciwon kamar zai zautar da ita haka takeji, zamowa tayi ƙasa daga kan kujeran da take, haɗe da durƙushewa aƙasan tiles, hanu tasanya takama gefe da gefen cikinta, tare da sakin wani ƙaran azaba, lokaci guda taji wani irin ciwo yataso mata gadan gadan.  Fitowar Hajiya daga ɗaki, yayi daidai da shigowan Doctor Sadeeq cikin falon.  Dukansu da sauri sukayi kanta. 
"Innalillahi Hajiya, dama bata da lafiya ne?" Dr. Yatambayi Hajiya a matuƙar ruɗe.  Kafun Hajiya takai ga cewa wani abu Zahrah ta fashe da kuka haɗe da faɗawa jikin Doctor ta ƙanƙameshi ƙam,  gaba ɗaya ya ruɗe yarasa inda zai tsoma kansa, shima rungumeta yayi tuni idanunsa sun kawo ƙwalla.
Hajiya ce tafito daga ɗakin Zahrah'n hanunta ɗauke da Hijab, ita tasawa Zahrah'n hijab ɗin, kana tace doctor Sadeeq ɗin ya ɗauki Zahrah su wuce asibiti.  Jikinsa na rawa haka ya ɗaga ta ca ɗak yasata a mota, Hajiya tashiga motar ta riƙeta, shikuma yaja suka nufi asibiti, gudu yake dasu kamar zaitashi sama, kanaganinsa kaga wanda baya cikin hayyacinsa,  bayaso wani abu na wahala yasamu matarsa ko kaɗan, da ace zai yiwu to daya karɓa mata naƙudan, don baya ƙaunar ganinta cikin wahala da azaba har haka.

Suna shiga cikin asibitin direct aka wuce da Zahrah labour room.  Wasu likitoti ne guda uku mata akanta,  babu abun da take sai salati da cije baki, ita kaɗai tasan me takeji,  ganin bazai iya jurewa ba, yasanya sa faɗawa cikin labour room ɗin, dayake dama asibitinsu ya kawota, yanazuwa gaban gadon, ya kama hanunta,  buɗe wahalallun idanunta tayi ta kalleshi,  atare wasu hawaye masu zafi suka fito daga cikin idanunsu,  matsanancin tausayinta yakeji, fiye da tunanin me tunani,  Hanunsa dake saman nata, takama ta matse, haɗe da girgiza masa kanta, cikin wata irin murya me ɗauke da tsananin ciwo tace.
"Kayafemin idan na mutu dan Allah!"

Kai ya girgiza mata da sauri haɗe da cewa. "Bazaki mutu ba Zahrah, zamu rayudake acikin duniyarnan insha Allah, zaki raini abun da zaki haifa ɗa hanunki, insha Allah!!" cike da tsananin rauni ya faɗi haka, sosai zuciyarsa ta karye,  bata sake ce dashi komaiba, kawai ta ɗauke idanunta akansa, cigaba tayi da nishi haɗe da karanto addu'a, Doctor na riƙe da hanunta, yana tofa mata addu'a, haɗe da shafa kanta, ƙwalla ne kawai suke fita daga idanunsa. Wani irin yunƙuri haɗe da nishi tayi sai ga kukan jariri ya cika ɗakin.  Laƙwas haka tayi akan gadon, lokaci guda komai nata ya tsaya, motsi da numfashinta, duk suka ɗauke, kumatunta yasoma bubbugawa yana ƙiran sunanta, hawaye kuwa akan fuskarsa wani na koran wani kamar an buɗe famfo.
Wata daga cikin likitoti matanne ta ɗauki yaron, takaishi wajen da ake aje jariri, kallon Dr.Sadeeq da yake hawaye tayi, tace
"Haba Sir, wannan fa ba wani abun damuwa bane kasani, yanzu zata farfaɗo insha Allah"
Hankalinsa ma baya wajenta balle yaji me take cewa, shigaba ɗaya ma basirarsa toshewa tayi, amaimakon yabata taimakon dayasan zai dawo da ita hayyacinta, saiya tsaya yana ƙiran sunanta, yana kuma jijjigata.   Likitance tashiga bata taimako,  wani ƙaƙƙarfan ajiyar zuciya Zahrah ta sauƙe,  alaman ta farfaɗo, bayan kamar mintuna uku ta shiga buɗe idanunta a hankali,  dashi tafara tozali ya tusata a gaba, sai kuka yake, hanunta ta miƙa masa, da sauri yataho yakama hanun,  kissing ɗinta yayi akan goshinta, haɗe da  rungumeta, atare suka shiga sauƙe ajiyar zuciya akai akai, sun kusan 8 minute ahaka, kafun taɗan janye jikinta daga nasa, murya a sanyaye tace "Ina Hajiya?"  "Tana waje" yabata amasa a taƙaice, yana me binta da kallo me ɗauke da tsananin ƙauna, haɗe da tausayi me ruguza zuciya.  

Wata daga cikin likitotinne tace "Sir yakamata a kimtsata, sai mukaita ɗakin hutu"
Juyowa yayi ya kalli likitan haɗe da cewa. "Babu buƙatar ɗaya daga cikinku sai ta kimtsata, nida kaina zan kimtsa abata"

"Sir tana buƙatar ɗinkifa, saboda ta ƙaru" likitan takuma faɗan haka.

Da sauri ya kalli Zahrah, take hawayen dake cike acikin idanunsa, suka gangaro kan ƙuncinsa, wani sabon tausayinta ne yasake kamasa, "Ina sam bazai iya mata ɗinki ba, bazai taɓa koda kwatantawa bane ma, dakansa da hanunsa ya huda Zahrah'nsa? wannan abun bamai yiwuwa bane" yafaɗi haka acikin ransa. Baice da likitotin komai ba, sai matsawa dayayi kusa da Zahrah, yasake sumbatarta akaro na biyu, wata allura ya ɗauko yayi mata a hanunta, tayanda yasan bazataji zafiba,   kallonta yayi still hawaye yake, daƙyar ya iya jan ƙafansa yafice daga cikin ɗakin, abun mamaki kota kan jaririn baibiba, tun dama yafaɗo dunia bai kulasaba, yanata rabin ransa Zahrah. 

Likitotinnan ne suka ɗinke ta tsab, saidai bata wani ji zafi sosai ba, domin alluran da Doctor yayi mata, allurace me ƙarfi dake hana jin zafi, suna gama ɗinketa, wata acikin likitotin takamata suka wuce bathroom,  likitance ta haɗa mata ruwa tayi wanka, tana fitowa likitan tabata wata riga wacce takarɓo awajen Hajiya tasanya, miƙo mata jaririn likitan tayi, hanunta na rawa haka ta karɓi jaririn ɗan nata, tana karɓansa taji wani irin sanyi ya ratsa zuciyarta, fuskar Dr.Sadeeq ta kalla sak akan fuskar yaron nata, lokaci ɗaya taji wani irin so da ƙaunarsa sun cika mata zuciya, tana fitowa acikin labour room ɗin, Hajiya da Dr.Sadeeq sukayo kanta, daga ita har jaririn Hajiya ta haɗasu ta rungume, sai ga ƙwallan farinciki na zuba daga idon Hajiya, amsar yaron tayi daga hanun Zahrah haɗe da sanya sa acikin ƙirjinsa ta rungumesa, sosai takejin ƙaunar jikan nata, musamman dataga yana kama da ubansa, sai dai duk da haka akwai kamannin Zahrah a tattare dashi. Dr.Sadeeq kuwa ko kunyan Hajiya dake tsaye baiyiba yaje ya rungume matarsa, kyakkyawan kiss ya sauƙe mata akan ƙuncinta, haɗe da ɗaura kansa akan kafaɗanta.

Saurin tureshi tayi daga jikinta, ta haye gado ta kwanta, tana sauƙe numfashi, kawar da kanta gefe tayi, wasu irin siraran hawayene suka gangaro daga cikin idanunta, ita kaɗai tasan menene yasata wannan hawayen. Mintuna kaɗan bacci ɓarawo ya ɗauketa, dagani kuma kasan tanajin daɗin baccin.

Alokacin da Doctor yakarɓi jaririn ahanun Hajiya, kafesa yayi da manyan idanunsa, wani irin ƙaunar ɗan nasa ne ke fusgarsa, sosai yaron ke kama dashi, rungume ɗan yayi acikin ƙirjinsa, sai kawai ga hawaye nafita daga cikin idanunsa, kallonsa ya maida ga Zahrah wacce take bacci, wutar sonta ne ke ƙara ruruwa acikin zuciyarsa, lallai Zahrah tana da babban matsayi agareshi, ta basa farinciki me ɗorewa, tahaifa masa ɗa, tayi masa komai a duniyarnan, baisan damene zai saka mata ba.

Hajiya dakanta ta ƙira Inna tasanar mata maganan haihuwan, dama tuni Aunty Raliya kam ta tsofe a asibitin, koda su Inna sukaji cewa Zahrah ta haihu, ba ƙaramin farinciki sukayi ba, sunji daɗi sunyi murna sosai, ita da Baffa duka suka rankayo zuwa asibitin.

Ba ita tafarkaba sai bayan azahar, bathroom ɗin ɗakin da take ciki ta shiga, haɗe da sake tsabtace jikinta, tana fitowa kuwa tasamu Doctor ya karɓo musu takardan sallama. Gaba ɗaya likitotin asibitin babu wanda baitaya Dr.Sadeeq murnan samun ƙaruwan da yayi ba, har ɗaki suke zuwa su duba Zahrah, sukuma tayasu murna.

Hanyar da Hajiya taga ya miƙa ne yasanyata cewa.
"Wai ina zaka damu ne Sadeeq?"

Da compidence ɗinsa ya juyo gareta haɗe da cewa. "Gidana mana Hajiya"

"Gidanka? to ba gidanka zamuba, gidana zamuyi, hauka kake na ɗauki yarinya da ɗanyen jiki, na baka? wama zai tsaya ya kula da ita? maza juya akalar motarnan" Hajiya tafaɗi haka babu alamar wasa akan fuskarta.

Sam bahaka yasoba, amma babu yanda zaiyi, shikenan shi baza abarsa yaji ɗumin matarsa dana ɗansaba, haka yata ƙunƙuni acikin ransa shi kaɗai, har suka isa gidan Hajiya.


Abinci mai rai da lafiya Hajiya ta kawowa Zahrah, ga kuma gasashshen nama, bayan taci abincin Hajiya dakanta, tasakeyi mata wanka.
Zama tayi agaban mirror tashafe jikinta da manta me daɗin ƙamshi, powder tashafa afuskarta, bata tsaya nanba harda janbaki tashafawa laɓɓanta, ga kuma kwalli da ta sanyawa cikin idanunta, mascara ta ɗauko ta zizira akan eye lashes ɗinta, take fuskarta taƙarayin kyau. Wani riga da sket na material me tsada tasanya ajikinta, take takoma ƴar baby kamar yanda take da, dogon gashinta ta kanannaɗe a bayanta, haɗe da hayewa gado, zataci gaba da bacci, miƙo mata yaron Inna tayi haɗe da cewa "Wani kwanciya kuma zakiyi bayan baki bawa yaron nono ba?"

Shagwaɓe fuska Zahrah tayi haɗe da turo ɗan ƙaramin bakinta gaba, da ƙyar ta iya ciro nonon nata ta kai bakin yaron, yana kamawa ta runtse idanunta da ƙarfi, saboda wani zafi da taji, haka dai ta ɗan daure, shikuwa yaron sai zuƙeta yake, gajiya tayi dajin zafin ta cire nonon abakinsa, kwantar dashi tayi, itama kana ta kwanta agefensa, baccin gajiya ne ya kuma ɗaukarta...


Idan dai hartaji sauƙan numfashinsa akan wuyanta, to yazame mata dole ne farkawa daga baccin da take, yanzu ma sauƙan numfashin nasa taji adai dai saitin kunnenta, a hankali take ware idanunta harta sauƙesu akansa. Murmushi yasakar mata haɗe da ɗaura kansa akan ƙirjinta.

"INA SONKI!!!" yafaɗa murya a sanyaye....


*(Insha Allah gobe zanmuku update, yau naso nayi da yawa, to wallahi tsoron editing nake, amma Insha Allah gobe kujira sabon posting, maybe ma yanzu kullum zanna baku update saboda mugama book ɗin da wuri)*


*28/February/2020*


*✅OTE ME ON WATTPAD*
@fatymasardauna


#Love
#Romance
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

      *SHU'UMIN NAMIJI !!*

    *Written By*
Phatymasardauna

*Dedicated To My Brother KHABIER*

*🌈Kainuwa Writers Association*

         
*WATTPAD*
@fatymasrdauna


     *CHAPTER 115*


"NIMA INASONKA!"

Tafaɗa tana me lumshe idanunta. Iskan bakinsa ya hura mata akan fuskarta, haɗe da sake rungumeta,  ɗayan hanunsa yasanya ya shafi kan jaririn nasa, dake ta bacci.   Murmushi Zahrah tayi ganin yanda Dr.Sadeeq ya kafe yaron nasa da ido.    Hajiya da Inna ne suka shigo cikin ɗakin atare, da sauri Zahrah ta janye jikinta daga na doctor, shima a kunyace ya sauƙa daga kan gadon yana sosa kai.

"Hmmm Allah yashirya, Inna kina gani ko, wai da ahakan yakeso na basa ita" inji cewar Hajiya.

Murmushi kawai Inna tayi batace komai ba.  ( Su Inna anzama nitsaljin🤣)   Kallon Doctor Hajiya tayi haɗe da cewa "Zo muje inason magana dakai"  babu musu yabi bayanta suka fice daga cikin ɗakin.

Zama tayi akan kujera haɗe da maida hankalinta garesa.
"Me dame kake shiryawa sunan nanne?  sannan kuma da wani suna kayiwa yaron huɗu ba?"

Murmushi ya ɗanyi haɗe da cewa  "Ai nagama shirina tuntuni Hajiya, dama lokaci kawai muke jira,  sannan kuma dama tuntuni sunan babanta nake son sawa yaron, dashi kuma nayi masa huɗu ba"

Hajiya tace "Masha Allah, To Allah Ubangiji ya rayasa, hakan da kayi kuma ka kyauta, tashi kaje dama maganan da zamuyi kenan" 

Miƙewa yayi haɗe da yi mata sallama yafice daga cikin falon.

Lokacin da Husnah tazo ganin Baby kusan haukacewa tayi, sai santin yaron take wai yayi mata kyau sosai, komai nasa irin na babansa, ga idanunsa kyawawa, itadai Zahrah dariyanta kawai take, saboda itama Husnan tana ɗauke da ɗan ƙaramin ciki.

Akwatuna guda biyu Dr.Sadeeq ya  kawo wa Zahrah, ɗaya nata ɗaya na baby'nsa  wai kayan barka,  kayane masu kyau da tsadar gaske sosai ya kashe kuɗi, wai ahakanma

Please Login or Register in order to submit comment