Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sanya wani haɗaɗɗen net me matuƙar kyaun gaske, sosai net ɗin da aka sanya abayan rigan yakuma ƙawata ɗinkin,   lace ɗin yakasance light pink colour yayinda kayan ƙyale ƙyale najikinsa yakasance golding ash colour,  sosai kayan yayiwa Zahrah kyau,,, haɗaɗɗen ɗaurin ɗan kwali aka tsantsara mata akanta, take tasake yin kyau,,,,   yau dai kwalliya da kuma kyawun da Zahrah tayi haryafi  wanda tayi a ranan kamu, komai nata yau na musamman ne tasha kyau sosai, ga doguwar riganta me ɗaukar hankali, daddaɗan ƙamshi kawai take fitarwa ajikinta me sanya nutsuwa,,  duk da irin wannan kyawun da tayi sai dai fuskarta babu wani wadataccen walwala domin kuwa idanunta sunyi luhu luhu dasu,  cikinta kuwa banda kukan yunwa babu abun dayake yi mata, amma kuma saboda masifar taurin kai irin nata taƙi sanyawa cikin nata komai na abinci..  Husnah ma yau zama tayi akayi mata meckup nagani na faɗa, sosai itama tayi kyau, tasha adonta cikin wata doguwar riga  na golding white lace,  idan ka kalleta dole ka ƙara domin itama tayi kyau sosai dama kuma itaɗin ma ko babu meckup tana da kyau masha Allah....

Yauma dai ango tare da amaryarsa zasu wajen dinner kowa yariga daya tafi harsu Auntie Raliya kuwa....

Husnah ce riƙe da hanun Zahrah suka fito compound ɗin gidan inda motar ango ke jiransu.  

Shikam gaba ɗaya kwana biyunnan salon kyawun  na Zahrah namatuƙar tafiya da imaninsa babu ma kamar yau, gaba ɗaya komai na surar jikinta ya bayyana bama kamar hips ɗinta yafito raɗau acikin rigan..          

Husnah ce ta buɗe murfin motar dayake zaune aciki, sai da ta tattaro ƙasan rigan Zahrah'n  kafun Zahrah ta'iya shiga cikin motar ta zauna,, lumshe idanunsa yayi haɗe da shaƙan daddaɗan ƙamshin daya kawowa hancinsa ziyara, wani irin ajiyar zuciya me ƙarfi ya sauƙe,, kallonsa yakuma dawowa dashi kan tauraruwar da haskenta yacika idanunsa,,,  murmushi yasakar mata me ƙayatarwa, yayinda ita kuwa kanta ke duƙe aƙasa tama kasa ɗago idanu ta kalleshi,,  hanunsa ya sanya ya ɗago haɓarta, sai alokacin ta iya jefa idanunta cikin nasa idon, wani irin abu yaji acikin jikinsa, ita ɗinma hakane, da sauri ta rumtse idanunta,,  abun daba ta tsammata ba, sai jitayi ya jawota jikinsa,   haɓanta yakuma ɗagowa da hanunsa na dama, haɗe da sanya ɗayan hanunsa yashafi gefen kumatunta  

"My Princess!"
yaƙira sunanta cikin wata muryarsa me sanyi. a hankali ta ware idanunta acikin nasa idanun,  ƙasa ƙasa yayi da idanunsa haɗe da maida kallonsa ga ɗan ƙaramin bakinta dayasha lipstick,  murmushi yakuma sakarmata haɗe da sake jawota ya ɗaurata akan cinyarsa.
 
"Kinyi kyau fiye da kullum my princess!" yafaɗi haka still yana me shafa gefen kumatunta da hanunsa,    wani irin kunyarsane yakamata tunda take dashi baitaɓa yi mata irin kallon dayakeyi mata a yanzu ba, haka kuma baitaɓa jawota yaɗaurata akan cinyarsaba sai yau. Marairaice fuskarta tayi haɗe da sunkuyar da kanta ƙasa,,   sweet ɗin dake cikin bakinsa ya cire, haɗe da ɗago fuskarta ya sanya mata acikin bakinta,   kallonsa tayi da ɗara ɗara idanunta, kansa ya jinjina mata yana ɗan murmushi, ahankali tashiga juya sweet ɗin acikin bakinta, dama kuma tunsafe babu wani abu daya shiga bakinta inbanda ruwa, sai wannan sweet ɗin daya bata yanzu,,  hanunta yakama yashiga murzawa ahankali haɗe da kafeta da idanunsa wanda lokaci ɗaya suka wani marairaice....   Sauƙeta yayi daga kan cinyarsa haɗe da kama hanunta ya buɗe murfin motar riƙe da hanunta haka suka fito daga cikin motar,, kamar wata jela haka take binsa still hanunta na riƙe acikin nasa, direct wani dogon gini dake cikin gidan nasu suka nufa.   Ita dai kawai binsa take cikin takunta me ɗauke da nutsuwa yayinda rigar jikinta kuwa ke share wajen, don ma wajen babu datti,     wani haɗaɗɗen falo ta tsinci kanta a ciki, suna shiga cikin falon Doctor yatsaya daga tafiyan da yakeyi haɗe da juyowa gareta,  murza hanunta dake cikin nasa yayi haɗe da zaunar da'ita akan kujera,  kaitsaye wajen wani fridge dake aje cikin falon ya nufa,  buɗe murfin fridge ɗin yayi haɗe da ɗauko kwalin fresh milk wanda bashida sanyi sosai,   glass cup ya ɗauka ya tsiyaya fresh milk ɗin aciki, saida yakusa cika kofin kafun yamaida sauran cikin fridge ɗin ya aje..  Inda Zahrah ke zaune ta sunne kai ƙasa ya nufo, aje kofin fresh milk ɗin yayi akan ɗan ƙaramin table ɗin dake kusa da kujeran daya zauna,  jawo Zahrah yayi jikinsa haɗe da sake ɗaurata akan cinyarsa, kofin da fresh milk ɗin ke ciki ya kawo dai dai saitin bakinta, cikin muryar lallami yace
"Anfaɗamin bakici komai ba tun safe, banaso kina zama da yunwa fa, banso tayi miki illa, kisha ko kaɗanne kinji baby na!"

Tsintar kanta tayi da kasa musa masa, saidai amma kuma gaba ɗaya a tsarge take, bata taɓa zama akan cinyar wani haka ba, hakan yasa gaba ɗaya ta takura,,   a hankali take ɗan shan fresh milk ɗin wanda harkusa da bakinta Dr.Sadeeq yake kawo mata kofin, shan fresh milk ɗin take cike da nutsuwa yayinda shi kuma gaba ɗaya idanunsa ke kanta, bakinta kawai yake kallo, karo na farko kenan arayuwarsa dayaji wani irin muguwar sha'awarta na fusgarsa,,, kafun shida ita su ankara tuni  hartasha  fiye da rabin kofin,, ɗan ya mutsa fuskanta tayi  haɗe da sanya hanu ta shafi ɗakalallen cikinta

"Naƙoshi fa!" tafaɗi haka tana me langwaɓar da kanta gefe. 

"Um'um ban yarda ba nasan kinajin yunwa sosai, ki ɗan ƙarasha ko kaɗan ne kinji _MY WIFE_!"  

Kalmar nan ta_MY WIFE_ daya ƙirata dashi  shiyasanya taji gaba ɗaya jikinta yayi mata wani iri,,, bakinta ta turo gaba haɗe da cewa
"dagaske ni na ƙoshi, gashi kuma duk kasa janbakina ya goge!" taƙare maganar akasalance.

Wannan shagwaɓan da takeyi masa shiyake sanyawa yaji gaba ɗaya jikinsa ya mutu,  har wani rufewa idanunsa keyi,, yabuɗe baki zaiyi magana kenan wayarsa tasoma ƙara, kobai ɗaga ba yasan dalilin ƙiran, yanzu haka yasan anacan antaru a wajen dinner su kawai ake jira, miƙar da'ita yayi tsaye bayan ya aje cup ɗin dake hanunsa,, amaimakon ya riƙe mata hanu su tafi kamar yanda suka zo sai gani tayi ya ɗagata caɗak yayi hanyar waje da'ita,, a tsorace tanemi sauƙa daga jikin nasa amma kuma kyakkyawan  riƙon dayayi mata yakasa bata daman hakan....
Bai direta ako ina ba sai acikin mota, yanashiga driver yaja motar suka fice daga cikin gidan... Kwanciya tayi luf ajikin kujeran motar haɗe da lumshe idanunta gaba ɗaya sanyin AC'n da motar ke busawa ne ke damunta, sam batason sanyi yacika yawa a waje.  daga wani ɓangare kuwa amatuƙar takure take, saboda yanayin yanda yake murza hanunta dake  cikin nasa. sosai hakan kesawa taji wani iri acikin jikinta,  gani tayi gaba ɗaya yau ɗin ya sanja mata, yanayi mata wasu irin abubuwa da baitaɓa ƙoƙarin kwatanta yi mata shiba acan baya,  ada sam baya taɓa yunƙurin kama hanunta sai dai idan yazama dole,kuma koda ma ya kama hanunta bawani jimawa zai sake, sannan kuma sam baya yawan jawota jikinsa kamar yanda yakeyi mata ayau, gashi gaba ɗaya taga yanayinsa ya sauya, idanunsa sunyi wasu kala tamkar wanda yakejin bacci...  Zuciyarta nayi mata lugude haka suka iso wajen dinner inda mutane suka cika maƙil zuwansu kawai ake jira... Suna isowa waje yaɗauki sowa yayinda mc yasake musu daddaɗan kiɗa me daɗi ta romantic...  kamar dai yanda kamu ya ƙayatar haka dinner ma yaƙayatar sosai Dr.Sadeeq yayiwa Zahrah ɓarin kuɗi lokacin da aka ƙirasu tsakiyan fili,  sunsha liƙin kuɗi kam sosai, su Auntie Raliya ma sunzo sun liƙa musu,   amma duk yanda akaso amarya tayi rawa kasawa tayi, saboda bata iyaba, bakuma al'adarta bane yin rawa agaban mutane, kunya ma bazai taɓa iya barinta ba,, saida Dr.Sadeeq yariƙe hanunta yashiga juyawa da'ita afilin rawan, take aka hau musu tafi yayinda wasu daga cikin abokansa  suka ci gaba da yi musu ɓarin kuɗi,,  suna komawa kan kujeransu mc yasanya musu daddaɗan waƙar Ed sheeran,  shiru Zahrah tayi tana sauraran waƙar sosai dama takeson waƙar domin kuwa duk waƙan Ed sheeran yanayi mata daɗi...  Koda aka yanka haɗaɗɗen cake  ɗin da aka ƙawatashi da sunan ango da amarya, da ƙyar Zahrah ta'iya bawa Dr.Sadeeq cake ɗin abaki, gaba ɗaya nauyi da kunya sun isheta gawani zazzaɓin daya sake kawo mata ziyara lokaci ɗaya,,, lokacin da aka tashi a dinner tuni amarya Zahrah tayi laushi, hartakai bata iya dogon tsayuwa da ƙafafunta,  ƙarfe 10 na dare aka tashi a dinner Aunty Ladi da kuma Husnah su suka sanyata a wata mota, direct aka wuce da'ita asalin gidan da zata zauna wato gidan aurenta....    Gidane me matuƙar kyaun gaske wanda aka kashe kuɗi sosai wajen ƙawatasa,      baginin gidan sama bane amma kuma yanayin yanda akayi ginin yayi kyau sosai,       wata haɗaɗɗiyar ƙofa suka nufa, suna buɗeta kuwa suka tsinci kansu cikin wani ƙawataccen falo me kyaun gaske.   haɗaɗɗen falone  wanda yasha kujeru light orange and milk colour,  yayinda aka ƙawata jikin ƙofa da window'n da wasu irin haɗaɗɗun labulaye masu kyau,  tsakiyar falon kuwa  mamaye yake da  wani haɗaɗɗen carpet  Orange colour,, ga wani irin ƙaton tv plasma dake aje kan wani haɗaɗɗen glass,, falon dai ba'acika masa kayan ado ba amma kuma yaƙawatu sosai komai na falon me tsada ne,, direct wani ɗaki dake cikin falon aka wuce da Zahrah,,  ɗakine me kyau wanda yaji royal furnitures milk colour, yayinda aka lailaye kan makeken gadon  da wani irin zanin gado pink me kyawun gaske...   Akan gado sukayimawa Zahrah masauƙi,   Husnah dakanta ta haɗawa Zahrah ruwan wanka,  koda tafito a bathroom ɗin hannayen Zahrah dake zaune kan gado ta kamo, haɗe da janta har zuwa cikin bathroom inda ta haɗa mata ruwan wanka...

Wani Turare ta bata tace inji  Hajiya Shuwa,  sannan kuma tayi mata bayanin yanda zatayi amfani  dashi...  

Zahrah tana fitowa a wanka Husnah ta shafa mata powder haɗe da lipstick, wani riga da sket na material marar nauyi Husnah ta bata tasanya, take tafito ɗas da'ita,  a tsakiyar gado Husnah ta zaunar da Zahrah haɗe da rufe mata kanta da wani irin haɗaɗɗen mayafi  me sheƙi da walwali, wasu turaruka masu ƙamshi Husnah takuma feshi jikin Zahrah dasu, take ɗakin yakuma ɗumamewa da ƙamshi,,   sake matsowa kusa da Zahrah Husnah tayi cikin murya ƙasa ƙasa tace

"Dan Allah Zahrah karkice zaki ci gaba da wannan kukan naki, ki ɗan daure zuciyarki kinji ƙawata, kuma sannan kada ki hana Doctor haƙƙinsa, nasan zakiji tsoro amma please ki daure kinji ƙawata, banaje  falo na amsa waya " Husnah taƙare maganar tana me miƙewa tsaye, idanu tayiwa Auntie Ladi suka fice a tare....

Tun Zahrah na jiran dawowan su Husnah hartasoma jin tsoro, domin kuwa gaba ɗaya gidan yaɗau shiru babu alaman akwai motsin wani mutum bayan ita,,, abun da Zahrah bata sani ba shine  su Husnah wayo sukayi mata suka tafi suka barta, sunyi hakanne kuma saboda taƙaitamata wahalan kuka, domin sun san sunace mata zasu tafi zata ƙara fawan kukanta.....

Gyangyaɗine yasoma ɗaukarta, dan haka saita jingina bayanta ajikin saman gadon  haɗe da lumshe idanunta da suketa tsiyayar hawaye...

A hankali yaturo ƙofar ɗakin bakinsa ɗauke da sallama,  yasake shiga cikin wata farar shadda sabuwa ƙal sai sheƙi takeyi,  ƙamshi ne kawai ke fita ajikinsa, daganinsa kasan yana cikin matsanancin farinciki,, ledan dake hanunsa ya aje, haɗe da takowa zuwa wajen datake zaune ta jingina bayanta da saman gado,,     zama yayi akusa da'ita haɗe da ƙiran sunanta,, cikin murya me sanyi da kuma alamar bacci ta amasa masa,,    ahankali yasanya hanunsa ya  ɗan jaye mayafin dake kanta, hawaye yagani kwance akan fuskarta,  hanunta yakamo haɗe da jawota jikinsa,  hanu yasanya yashiga share mata hawayen dake kan fuskarta.

"Ki daina kuka kinji my wife, bacci zakiyi ne?" yatambayeta yana me ƙaremawa fuskarta kallo,, fuska ta kuma kwaɓewa, haɗe da  kaɗa kanta, cike da shagwaɓa tace

"Ina  Husnah?"

Ajiyar zuciya yasauƙe haɗe da sanya hanu yashafi lallausan gashinta dayasha gyara

"Husnah kuma Zahrah?" yatambayeta cike da mamaki..

"Eh tacemin zata amasa waya tana zuwa kuma haryanzu bata dawo ba!" yanzuma dai asangarce tayi maganar,,  murmushi yayi mata haɗe da cewa
"Kada kidamu Husnah zata dawo gobe, taso muje kiyi alwala idan munyi salla saikici abinci ko"  

Jitayi gabanta yayi wani irin faɗuwa amma kuma yazatayi da rayuwarta babu yanda ta'iya haka tabisa kamar jela harcikin bathroom,, saida yayi nasa alwalan kafun yabata waje itama ta ɗauro alwala,,  tana fitowa daga cikin bathroom ɗin ya miƙo mata  wata lufaya,  a ɗaɗare tasanya lufayan  daya bata, hanunta yakama suka hau kan sallaya, shi yajasu salla raka'a biyu,   suna idarwa yayi musu addu'o'i haɗe da  kama kanta itama yayi mata addu'a... A tsorace ta zauna  akan gado haɗe da sake takure jikinta waje ɗaya...

Wani ɗan madaidaicin carpet Dr.Sadeeq  yashimfuɗa haɗe da cika tsakiyar carpet ɗin da kayan ciye ciye, hanu ya miƙawa Zahrah alamar tataho garesa, cikin ɗari ɗari haka ta shiga takowa zuwa inda yake, hanunta yakamo yazaunar da'ita acikin jikinsa,  hijabin dake jikinta yasoma ƙoƙarin cire mata, da sauri tasake ƙanƙame jikinta, ganin haka yasanya shi yin murmushi, ya fasa cire  mata hijab ɗin,,  juice ya zuba acikin kofi haɗe da kai kofin bakinta, babu musu tabuɗe bakinta ta kurɓi kaɗan,   aje kofin yayi,  haɗe da yago gasasshen nama yakai bakinta,, kanta tashiga girgizawa alaman bazataci ba.

"Kiyi haƙuri kici kinji Baby na, kaɗan zakici bamai yawa ba!" yafaɗi haka cike da lallami,,,  shida kansa yake bata kazan, bata wani ci me yawa ba tace masa ta ƙoshi,  dakansa yatattara wajen yakai kitchine,, yana dawowa ɗakin yasameta tsaye ajikin mirror tayi jigum,, fargabane yacika mata zuciya, wani irin tsoro ne taji ya ɗarsu acikin zuciyarta wanda bazata iya misaltashi ba,,

Kaitsaye drower ɗin dake cikin ɗakin ya nufa,  wata doguwar rigan bacci sleeping dress  yaciro haɗe da ƙarasowa gareta,, "Kije kiyi brush, wannan kayan kuma kisanya kizo kiyi bacci"  hanunta na rawa haka ta amshi kayan sumi sumi ta wuce cikin bathroom, tana kammala brush tasoma cire kayan jikinta,  warware rigan da Dr. yabata tayi  tashiga ƙaremawa rigan kallo, doguwar rigace na bacci me net, amma kuma tana da faɗin wuya  sannan kuma rigan irin me nuna jiki ɗinnan ne,,  badon tasoba haka ta sanya rigan ajikinta,  hmmm sam bazata iya fita da wannan rigan gaban Dr. Sadeeq ba, saboda  gaba ɗaya rigan ta bayyana breast ɗinta, yayinda komai nata yafito  fili,  hijabin da tayi salla dashi ta ɗauka ta sanya,, a ɗaɗare  ta fito daga cikin bathroom ɗin,, zaune tagansa akan gado tuni yasanja kaya zuwa farar jallabiya,    murmushi kawai Dr.Sadeeq kejifanta dashi,   cikin zolaya yace "Meye narufe jikin da hijabi?"

Ƙasa takumayi da kanta, yanzu kam ko ɗan shagwaɓan ma takasayi masa...

Sarai ya fuskanci halin da take ciki,     "Zoki kwanta" yafaɗi haka yana meyi mata nuni da kan gadon dayake zaune,,  kamar wacce ƙwai yafashewa haka Zahrah ta zo ta kwanta akan gadon, gaba ɗaya ta takure kanta waje ɗaya,,,   miƙewa yayi daga zaunen dayake haɗe da  kashe  wutan ɗakin ya kunna na bacci, Zahrah najin takusan alamar yakusa zuwa kan gadon taji bugun zuciyarta ya tsananta, yayinda ƙirjinta yashiga wani irin luguden duka,,  kwanciyarsa akan gadon yayi dai dai da kusan ɗaukewar numfashinta,,,,   da ƙyar ta'iya ƙwato numfashinta, haɗi sa soma  sauƙe ajiyar zuciya  a ɓoye, kusan minti goma da hawansa kan gadon amma kuma taji baiyi mata wani abu ba, hakan yasa taɗanji zuciyarta tayi sanyi.    Shiru tayi tana me jin sauƙar numfashinsa ahankali, wani irin mugun tausayinsa ne taji yaɗarsu acikin zuciyarta amma kuma ita bata da yanda zatayi, tunaninta ne ya katse alokacin da taji sauƙar hanunsa  a bayanta,,   ahankali ya juyota tadawo tana fuskantarsa,, kallon fuskarta yashigayi batare dayace da ita komai ba, kusan mintuna 4 yayi yana kallonta, cikin wata irin murya wanda batasanshi da ita ba yace
"kicire hijabin nan saboda kiji daɗin baccinki ko"   
babu musu ta cire hijabin daga jikinta sai dai kuma bahaka ranta yaso ba, bargo yaja ya rufa musu  hanunta yakamo ta cikin bargon yariƙe acikin nasa,  "Ki kwantar da hankalinki, nasan kingaji, kiyi addu'a, kiyi bacci me daɗi" yafaɗi haka cikin muryar raɗa,  hanunta yasake damƙewa acikin nasa hanun haɗe da lumshe idanunsa,  zai bartane kawai saboda tausayinta dayake ji, amma bawai don baya sha'awarta ba, hasalima baita ɓa jin matsanancin sha'awarta irin nayau ba,  hakan yafarune kuma saboda baitaɓa samun kusanci me tsanani da ita irin na yau ɗin ba, da wannan tunanin bacci ya ɗaukesa,,,,   Zahrah ma dai baccin ne yaɗauketa batare data shiryawa hakan ba,,    ƙarfe ɗaya na dare wani irin zazzafan zazzaɓi yarufe jikin Zahrah take tasoma karkarwa haƙwaranta har haɗewa suke, suna ba da wani sauti, hakan yafaru ne kuma sakamakon  sanyin AC wanda yayi mata yawa,   acikin baccinsa yakejin hucin numfashinta nafita da sauri,  a hankali ya buɗe idanunsa ya sauƙesu akanta, da sauri yatashi ya zauna haɗe da kamo kafaɗunta,,  "Zahrah!" yaƙira sunanta a hankali,,   tanajinsa amma bazata iya amsa masa ba domin kuwa ba iya zazzaɓi ba hatta kanta jinsa take tamkar anɗaura mata gungumen ice, yamata nauyi   Da sauri ya sauƙa akan gadon, AC'n yafara kashewa, kana ya buɗe wata ƴar drower  maganin ciwon kai da zazzaɓi ya ɗauko haɗe da goran ruwa,, yana zuwa ya ta data zaune, ɓalle maganin yayi yasa mata abaki haɗi da kafa mata goran ruwa, babu musu ta haɗiye maganin, ajiye goran yayi  haɗe da hawa kan gadon, hanunsa yasanya akan wuyanta, zafi yaji zau kamar wuta,  ajiyar zuciya ya sauƙe, haɗe da cire rigan dake jikinsa, cikin  bargon yakoma, haɗe da jawota kusa dashi,  ahankali yasanya hanunsa a bayanta yayi ƙasa da zip ɗin  doguwar rigan dake jikinta,,  cike da nutsuwa ya cire mata rigan,, Zahrah tana jinsa amma kuma ayanzu babu wani abu da zata iyayi wanda zata kare kanta,, bashi kaɗaiba har ita kanta saida ta sauƙe wani irin ajiyar zuciya me ƙarfi alokacin da  zallan fatar jikinsu suka samu haɗewa waje guda.    lokaci ɗaya yaji tunaninsa yasoma sauyawa, nutsuwarsa tafara gushewa, haka kuma idanunsa sun soma rufewa,,  haɗewar jikin Zahrah danasa jikin baƙaramin feeling me girman gaske ya sauƙar masa ba, tunda yake aduniyarsa yau shine karo na farko, da ya fara haɗa jikinsa dana mace haka, yasan yataɓa rungumar   Zahrah amma ba runguma irin wannan ba,,,,  Zahrah  kuwa baƙaramin jin daɗin jikin nasa tayi ba, jitayi gaba ɗaya nutsuwa yasoma sauƙar mata, sake maƙalewa ajikinsa tayi haɗe da cusa kanta acikin faffaɗan ƙirjinsa har yazamana laɓɓan ta suna gogan  fatar wuyansa,, jin yanda take ƙara shigewa jikinsa shiya ƙara taimakawa wajen ƙara masa wutar sha'awarta, hannayensa duka yasanya a bayanta yasake riƙeta gam,  numfashi kawai yake fitarwa akai akai shi kaɗai yasan meyakeji acikin jikinsa,,  yana cikin wannan irin yanayin yaji sauƙar numfashin Zahrah ahankali yana fita da'alama baccine yakuma ɗaukarta,,,   haka yarungumeta ƙam acikin jikinsa yayinda yacusa kansa acikin gashin kanta yana shaƙan daddaɗan ƙamshinta dake ƙara rikitasa,, bakaɗan ba ya yi jarumta wajen ganin ya ƙyaleta baiyi mata komai ba,  haƙiƙa bakowani irin namiji bane zai haɗa jiki da mace ace ya iya daure zuciyarsa baiyi mata komai ba, balle ma mace irin Zahrah wanda irinsu basu da yawa acikin mata,,  da ƙyar bacci ya'iya ɗaukarsa.......

*(Kuyi Haƙuri idan kunga typing error ina busy ne)*
   
        

*18/January/2020*

          *Fatymasardauna*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

       *SHU'UMIN NAMIJI !!*

    *Written By*
Phatymasardauna

*Dedicated To My Brother KHABIER*

*🌈Kainuwa Writers Association*

_{United we stand and succeed; our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}_

*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*

            *WATTPAD*
     @fatymasardauna

*Editing is not allowed📵*

       *CHAPTER 92 to 93*

Ƙiran sallan asuban fari akan kunnensa,, a hankali ya ware idanunsa akanta, baccinta takeyi cikin kwanciyar hankali da'alama zazzaɓi da ciwon kan dake damunta sun jima da kama gabansu,,  baisan lokacin da murmushi ya ƙwace masa ba, komai na Zahrah me kyau ne, har idan tana bacci kyawunta baya ɓuya, kallon zara zaran eye lashes ɗinta daya kwanto aɗan ƙasan idanunta yayi,,  ahankali ya zare jikinsa daga nata jikin, cikin sanɗa yatura ƙofar bathroom yashige, gudun kada motsinsa ya tashe ta daga daddaɗan baccin da take,,  saida yafarayin wanka kafun ya ɗauro alwala,,  tsayawa yayi yana kallon yanda taketa fidda numfashi a hankali,  badon sallah yazama dole akanta ba, to tabbas da babu abun da zai sanya ya tasheta a dai-dai wannan lokacin, zai bartane tasha baccinta ta ƙoshi,, ahankali yashiga girgiza ƙafanta haɗe da ɗan ƙiran sunanta, cikin murya ƙasa ƙasa... Da yake bata da nauyin bacci, ƙira biyu yayi mata ta buɗe idanunta,, da sauri ta sake jawo bargo ta rufe jikinta, kana tasoma raba idanu,   murmushi yakumayi mata haɗe da sanya hanu ya shafi gefen kumatunta.

"Kitashi kiyi sallah, ni na wuce masallaci"

Bata iya amsa masa ba haryafice daga cikin ɗakin,,    kallon kanta tashiga yi gaba ɗaya gashinta ya watse yayi buji buji dashi, da'alama dai tasha juyi acikin bacci,,,    tana shiga bathroom ta haɗawa kanta ruwa me ɗan ɗumi, wanka tayi itama kana ta ɗauro alwala (🤔Yadai dukanku wanka sai kace 🙊)....

Tana fitowa daga bathroom ɗin ta zura wata jan doguwar riga marar nauyi, haɗe da zura hijab ajikinta,  kan sallaya tahau  haɗe da dai-dai ta tsayuwarta......      Koda ta'idar da sallan saida tayi azkar kafun ta miƙe daga kan sallayan,,   harta zauna akan gado, maganganun Hajiya Shuwa suka faɗo mata arai inda take ce mata  _"Kada ta sake ƙamshi yabar jikinta, sannan kuma idan tayi sallan asuba kullum tana shafa turare aduk wani lungu da saƙo na jikinta"_ batasan mene manufar hakan ba, amma dai ta ɗau maganar kuma zatayi aiki dashi.   Gaban mirror tanufa haɗe da ɗaukan ƴar ƙaramar hand bag ɗinta dake aje kan mirror'n  wani ɗan kwalban body spray ta ciro daga cikin jakar, haɗe da fesawa ajikinta, daga kan wuyanta har zuwa bayan kunnenta, sosai turaren yake da ƙamshi, take ɗakin ya gauraye da ƙamshin turaren,, tana shirin maida turaren cikin jakarta, Dr.Sadeeq yaturo ƙofar yashigo bakinsa ɗauke da sallama,, cikin murya me sanyi ta amsa masa sallaman nasa,,    direct inda take tsaye ya nufo, batayi tsammani ba saiji tayi ya buɗe hannuwansa ya rungumeta ta baya haɗe da ɗaura kansa akan wuyanta,,,, idanunsa ya lumshe haɗe da buɗe hanci ya shaƙi daddaɗan ƙamshin dake fita ajikinta cikin wata irin murya yace
"Good morning madam!"

Kunyan sane yakamata,  saikawai tayi ƙasa da kanta haɗe da cewa

"Ina kwana"

"Lafiya ƙalau, yajikinki?" ya amsa mata yana me cusa kansa acikin wuyanta..

"Da sauƙi"

Ta mayarmai da amsa cikin ƙasa da murya...

"Ƙamshinki yamin daɗi sosai, kinyi sallah ne?"

Kanta ta ƙaɗa masa alamar "Eh" hanunta yakama yajata zuwa kan gado... Zama yayi kana ya jawota jikinsa,,    ɗago fuskarta yayi haɗe da jefa idanunsa cikin nata.     Sunanta yaƙira cikin wata irin murya me ɗauke da nutsuwa..

Kanta ta ɗago ta kallesa, ganin idanunsa tsaye cak akanta yasanya tayi saurin meda kanta ƙasa..    

"Meyasa kikejin kunya na sosai ne?"

Yayi mata tambayar da bata tsammata ba,, jijjiga kanta tayi alaman 
"babu"

Sake matseta acikin jikinsa yayi haɗe da kwantar da kansa akan kafaɗanta.

"Mallakarki danayi wata babban nasara ce dana samu acikin rayuwata Zahrah, inasonki ne da duka zuciyata,  dakuma iya gaskiyata, banda niyar cutar dake acikin rayuwar zaman aurenmu,   abu ɗaya nakeso kiyi mini shine, ki rage yawan tunani da kuma kukan nan dakikeyi, inajin tsoro kada su haifarmiki da wata cuta, yanzu nasan kina da buƙatar hutu ko, ki kwanta ki huta, kafun anjima sai kiyi break fast"   

Miƙewa tayi daga jikinsa haɗe da hayewa  kan gadon ta kwanta, amma kuma bata ɗauke idanunta akansa ba,    bayan kamar mintuna biyar da kwanciyarta shima yatashi daga zaunen da yake, kan gadon ya hau, har Zahrah taji bugun zuciyarta yasoma ƙaruwa, sai kuma taga ya lulluɓe mata duka jikinta da blanket, agefe da ita ya kwanta haɗe da juya mata baya... Shiru ɗakin ya ɗauka babu abun dake tashi sai sautin fitar numfashinsu,,,  bayansa ta kafe da idanu, yayinda a cikin zuciyarta take wani tunani na daban, haƙiƙa duk duniya babu wani namiji daya dace yazamo miji agareta sama da Dr.Sadeeq, ya cancanta ƙwarai, shi mutum ne  wanda zaiyi wahala asamu kamarsa, Dr.Sadeeq kuwa lumshe idanunsa yayi bawai don bacci ya ɗauke sa ba,,  shima wani tunanin yakeyi daban,   baisan meyasa aduk sanda idanunsa zasuyi masa tozali da Zahrah yakejin matsanancin sha'awarta ba, wanda ada kuma ba haka abun yake ba, bazaice da bayajin sha'awarta ba, yanaji

Please Login or Register in order to submit comment