Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zaiƙi ci da kowa amma zaici da ita, kujera Afrah taja ta zauna itama, haɗe da soma yin serving ɗin kanta, don ta lura babu wani wanda yake ta ita, daga Zaid ɗin har Zahrah, su dama kansu kawai suka sani. 

Shida kansa yaciyar da ƴartasa, itama haka ta dinga basa abincin abaki har ya ƙoshi,   sama sama suke hira da Afrah, nan ma itace take jansu da hira, amma daba haka ba bazasu kulata ba, ita har mamakinsu ma take, Zahrah sam bata damu da ita ba, kamar ba itace ta haifeta ba, zancenta baya wuce mahaifinta dakuma Momyn Friend ɗinta, wanda suke makaranta ɗaya dashi.

Tana gama goge bakinta da tissue ta kalli Papa Luv ɗinnata ashagwaɓe tace.    "Please Papa luv yau muje shan ice cream mana!"

"My Soul yau inada aiki, mubari sai gobe mana, kinga fa next week zamu koma U.S.A, akwai abubuwan danakeso nayi kuma kafun mu koma" yafaɗi haka bayan ya aje kofin tea ɗin dake riƙe ahanunsa.

Sake shagwaɓewa tare da narke fuskarta tayi, ɗan ƙaramin bakinta taturo gaba haɗe da cewa
"Ae Dan Allah Nace Papa Luv, inaso naje ne!"

"Shikenan zo muje na shiryaki" yafaɗi haka yana mai miƙo mata hanunsa.

Tsalle ta doka haɗe da faɗawa jikinsa ta rungumesa, cike da farinciki ta kai masa sunbata akan ƙuncinsa. 

"Thank You Papa Luv"

Ɗagata yayi caɗak akan kafaɗunsa haɗe da sanya hanu ya kwashe wayoyinsa dake kan table, direct suka wuce ɓangarensa. 

Kai kawai Afrah ta girgiza haɗe da cigaba da cin abincinta, sam abunsu baya damunta, tasaba da hakan, koda yaushe haka suke, kamar tip da taya basa rabuwa.

Shida kansa yayi mata wanka yashiryata cikin wasu riga da wando na jeans masu matuƙar kyaun gaske, naɗe mata dogon gashinta yayi a tsakiyar kanta, da wani babban ribbon,  lokaci ɗaya kyawunta da tsananin kamaninta da Zahrah suka sake bayyana, shima wanka yayi kana ya shirya kansa, cikin wasu riga da wando masu kyaun gaske,  sosai yayi kyau sai tashin ƙamshi yake, Little Zahrah dakanta saida tayaba kyawun da Papa Luv ɗinta yayi.  

Yana riƙe da hanunta suka fito harzuwa falo, kallonsa ya maida ga Afrah wacce ta mato akan kallonsa.

"My Wife bazaki zo kirakamu bane?" ya tambaya.

Murmushi kawai tayi haɗe da lumshe idanunta, akasalance tace "Kuje kawai Dear nikam inanan, amma ku tahomin da nawa ice cream ɗin"

Hanu Zahrah ta ɗaga mata alaman bye bye kana suka fice daga cikin falon.  

Barinta yayi awajen sayan kayan maƙulashe irinsu chocolate da sauransu shikuma ya nufi wajen turaruka.    Tana tsaye ta ƙurawa wani babban ledan chocolate dake can sama idanu, so take ta ɗaukoshi ta sanya acikin kayanta amma kuma wane ita, ya ɗarawa tsayinta,  jitayi anrufe mata idanu a hankali,   a iya saninta mutum ɗayane keyi mata hakan,  saboda haka yanzuma tasan cewa shiɗinne, dariyan farinciki tasaka haɗe da cewa "ASAD!" 

Dariya yayi haɗe da sake mata fuska ta juyo zuwa garesa, kyakkyawan yarone wanda bazai wuce 7to8 year ba, yarone fari tas dashi tamkar ajinsin larabawa yafito,     tsallen murna Zahrah tasanya haɗe da rungumesa, shima rungumeta yayi cike da jin daɗin ganin ƙawartasa wacce rabonsa da ita yau tsawon sati uku kenan, tun da aka basu hutun makaranta rabonsa da ita..

Cike da ɗokin ganinsa Zahrah tace. "Laaa Asad dama zanganka anan? kaida waye kukazo? nidai nida Papa Luv ɗina mukazo, aibansan zamu sameka anan ba da munzo tunda wuri"

Hanu yasanya ya ɗan murɗe bakinta cikin halayyarsu ta yara yace "Baki gajiyawa da Surutu Soul ina Papan naki?"  yaƙare maganar yana me baza idanunsa.

"Asad me kakeyi anan, bacemin kayi chocolate zaka ɗauka kazo ba?"  

Daga Asad har Zahrah atare suka juya suna kallon mai maganar.     Kyakkyawar mace wacce ta amsa sunanta mace mai aji da kamala, sanye take da abaya gown black colour ta yane jikinta da mayafin abayar, komai nata na burgewa ne, kallo ɗaya zaka mata, kakuma son sakewa domin ba irin ƙananan matannan bane, duk da cewa bata da wani jiki, haka kuma bata wani sanja ba, har yanzu  tana nan da kyawunta mai fusgar hankali.

"Itace Mamanka?" little Zahrah tafaɗi haka ƙasa ƙasa tana kallon Asad.

Kai Asad ya kaɗa mata alamar "Eh" 

Da gudunta ta ƙarasa wajen Momyn Asad ta rungumeta,  cikin surutunta daya zame mata sabo tace.
"Oyoyo Mom Asad, dama inataso mu haɗu dake, amma bakya zuwa school ɗinmu, Dad ɗin Asad ne kawai yake zuwa,  ni da Asad abokaine sosai, kuma dan Allah kudawo U.S.A kunji, muma kunga can zamu koma" tunda little Zahrah tafara zuba bata tsagaitaba sai yanzu.

Hakanan Zahrah taji yarinyar ta burgeta, durƙusawa tayi agaban yarinyar haɗe da sanya hanu ta shafa fuskarta, hakanan taji bugun zuciyarta ya ƙaru, "Idanunta ne ke mata gizo kokuwa dagaske kamanninta take hangowa akan fuskar yarinyar?" tambayar da tayiwa kanta kenan, cike da son sanin amsa.

Murmushin da Little Zahrah tayiwa Mom Asad ne yayi sanadiyar kusan rugujewar zuciyarta.    "ZAID" tafurta sunan acikin maƙoshinta da kuma kan laɓɓanta, sai dai kuma amon sauti baifito ba.

"My Soul"

Taji wata murya dabazata taɓa mantawa da ita ba tafaɗa.

Dagudu Little Zahrah takamo hanun Papa Luv ɗinta dake tsaye.

"Yauwa Papa zokaga Momyn Friend ɗina Asad, wacce nafaɗamaka tana da kirki, tana bawa Asad abun daɗi, shikuma yana bani." 

Idanunsa ya sauƙe akan bayan wata mace dake durƙushe a ƙasa tabasa baya,   cigaba da jansa little Zahrah tayi harzuwa inda Mom Asad ke durƙushe amma bata ɗago fuskarta ba.

"Momyn Asad, ga Papa Luv ɗina nima, tare dashi mukazo" little Zahrah tafaɗa cike da kauɗi.

Ahankali ta ɗago manya manyan idanunta ta ta kalli mutumin da Zahrah ke cewa shine Papa Luv ɗinta.

Atare bugun zuciyarsu suka tsananta, take wani irin abu ya tsarga jiki da jijiyoyinsu.

Da ƙyar ta'iya daure zuciyarta ta ƙaƙalo murmushi.

Shima murmushin yayi haɗe da sunkuyar da kansa ƙasa.

Hanun Asad ta kama jiki asaɓule ta juya daniyar barin wajen.

"Asad" taji muryar Zaid yaƙira sunan yaron.

Tsayawa sukayi cak amma ita bata juyo garesa ba,  takowa yayi har inda suke ya durƙusa haɗe da kamo hanun Asad.

"My dear ya hutu?" yatambayi Asad.

"Lapiya" Asad yabashi amsa yana murmushi.

Kallonta yayi haɗe da cewa "Dama Asad ɗanki ne?"

Kanta kawai ta jinjina masa alamar "Eh" gaba ɗaya ta ƙosa subar wajen shikuma yakama Asad ya riƙe ƙam.

Murmushin dake ƙarawa fuskarsa kyau yayi haɗe da cewa "Fine boy, natayaki murnan samun wannan kyakkyawan yaron,  amma kuma saidai inajin tsoron abunda zai faru anan gaba,  Asad abokin Zahrah na ne, idan nan gaba yasan nayiwa mahaifiyarsa laifi mai girma yakike tunanin zai ɗauki abun?" 

Kanta ta girgiza masa haɗe da ɗanyin murmushi.  "Kada kace haka Zaid, abu idan ya wuce yana da kyau amantasa, afuskanci gaba, banafatan Asad yasan abun da ka aikata agareni" ɗan numfasawa tayi tare da kama hanun Asad.     "Sauri nake zanwuce gida" kallonta ta mayar ga Little Zahrah da ta ƙura mata idanu tun ɗazu, murmushi Zahrah tayi mata, haɗe da shafa kanta, sosai taji son yarinyar acikin ranta.

"Allah ya albarkaci rayuwarki Rabin raina"    Tana faɗan haka taja hanun Asad suka bar wajen.

Saida ta ɓacewa ganinsa kafun yasaki wani murmushi haɗe da cusa duka hannayensa acikin aljihun wandon jeans ɗin dake jikinsa.   Little Zahrah ce tataho zuwa garesa haɗe da maƙalewa acikin jikinsa, murya asanyaye tace "Papa dama kasan Mommyn Friend ne?"

Murmushi yakumayi akaro na sau babu adadi,  hanunta yakama suma suka bar wajen, batare daya bata amsar tambayar da tayi masa ba.

Tunda suka shiga mota batace da yaronnata ƙalaba,  shima baitanka mata ba, domin dama shi hakanan yake ba mutum ne mai son yawan magana ba, yana da miskilanci wani lokaci.  Ganin da yayi cewa kamar Momyn nasa na cikin damuwa ne yasanyashi gyara zama haɗe da cewa.
"Momy wani laifi ne Papan Friend yayi miki? naji kamar yace wai bayaso muji ko mu sanine oho"

Harara ta watsa masa, hakan yasashi yin gum da bakinsa, shidama gulmace ke cinsa, da yasani ma da baitambaya ba.

Tana isa gida tasamu Husnah da Areefa matar Asad, sunzo suna jiranta, sam basu sanar da ita zuwansu ba,  batayi mamakin ganinsuba kamar yanda tayi mamakin  ganin yanda aka sauya mata tsarin falonta, aka mamaye gaba ɗaya falon da decorations masu kyaun gaske,  tsayawa tayi tana ƙarewa falon nata kallo.

"Happy Birth Day to you my dear Wife!!!" 
muryar Dr.Sadeeq ta karaɗe ilahirin kunnuwanta, kallonta ta maida inda taji muryartasa na fitowa.

Fitowarsa daga ɗaki kenan yasha ado cikin riga da wando na jeans masu matuƙar kyau.  Murmushi tasakar masa,  gaba ɗaya ita tamanta da cewa yaune birth day ɗinta.

Hanunta yakama suka nufi wani ɗan keɓeɓɓen waje dake cikin falon, sosai aka ƙawata wajen da decoration's mai kyau,  kusan suman tsaye tayi alokacin dataga irin hidiman da mijinnata ya shirya mata, manya manyan cake masu kyau da tsada yasa akayi mata har guda uku, ga kayan ciye ciye dana shaye shaye, tsananin farinciki da ƙaunarsa ne suka mamaye zuciyarta, juyawa garesa tayi ta rungumesa, haɗe da cusa kanta acikin ƙirjinsa tana shaƙan daddaɗan ƙamshin jikinsa.  

"Thank you so much my lovely husband!!!" tafaɗa cikin sanyi yayinda ƙaunarsa ke ƙara ratsa zuciyarta.

"Babu godiya atsakaninmu My Wife kina da babban matsayi a wajena, keta musamnan ce, inasonki da duka zuciyata!" Dr.Sadeeq yafaɗi haka yana ƙara matseta acikin ƙirjinsa.

Kwantar dakanta tasakeyi ajikinsa cike da ƙaunarsa, haƙiƙa tasamu duk wani abu da takeso, farinciki, soyayya, da kuma zaman lafiya, sosai Doctor ke bata kulawa, bayason ɓacin ranta ko kaɗan, yana ƙaunarta har acikin jininsa, itama kuma tana ƙaunar mijinnata sosai, ayanzu yafiye mata kowa da komai,  yabata farinciki haka kuma yabawa iyayenta, yamantar dasu komai na ɓacin rai da talauci, ya wadatasu da komai na rayuwa, bata da wani  TAURARO sama da shi, shiɗin na musamman ne arayuwarta, koda sau ɗayane bata taɓa yin danasanin kasantuwarsa amatsayin mijinta ba, ko da kowa aduniya zai juya mata baya, tasan banda Mijinta Haskenta Abun Alfaharinta.    Rayuwarta tayi mata daɗi akoda yaushe saidai tace ALHAMDULILLAH..

***
Yana tsaye agaban dressing mirror  yayinda little Zahrah ke tsaye agefensa, tana shan chocolate, Afrah ce tashigo cikin ɗakin hanunta ɗauke da kofin coffee wanda take haɗamasa kullum daren duniya.

Miƙo masa kofin coffee ɗin tayi, ya amsa yana murmushi, aje kofin yayi haɗe dasanya hanu ya jawota jikinsa ya rungumeta, bakinsa ya kai dai dai saitin kunnenta, ahankali yace "Inasonki ƴar lukutar matata!"  

Dariya Afrah tasanya haɗe da cewa "Nima inasonka ɗan lukutin mijina" 

Murmushi kawai yayi haɗe da sanya hanu yashafi kumatunta.

"Nima inasonka Papa na!!"  little Zahrah dake tsaye a gefensu tafaɗi haka da ƙarfi.

"SON SO nake miki farincikina, idan babuke acikin rayuwata, to babu wani haske dazan sake gani, Allah yarayamin ke na aurar dake ga miji na gari!!" yafaɗi haka yana dariya, acikin zuciyarsa kuwa, har yau tsananin danasanin yanda halayansa suka kasance a baya yake, yayi danasani sosai, har gobe kuma akan danasani yake, bazai kuma taɓa daina Istigfari ba har ƙarshen rayuwarsa.

Duk da Little Zahrah bata fahimci me maganganunsa ke nufi ba, amma tasan cewa mace da namiji suna aure, domin wancan satin daya wuce ma sunje auren ƙanwar momynta.

Dagudu taƙaraso ta rungumeshi,  ƙasa ƙasa tace  "Nidai ko zanyi aure bakowa zan auraba sai Friend, aishima yanasona ko Papa?"

Durƙusawa yayi agabanta cike da soyayyarta yace "Yanasonki mana, ai aduniya babu wani wanda zaiƙi me wannan kyakkyawar fuskar, ke ɗin ta musammance My Soul!"

Daɗine yakama Zahrah, sake rungume mahaifinnata tayi, aranta tana ƙara ƙaunar papan nata, domin adunia tasan bayan shi babu wani wanda zaiyi mata irin wannan soyayyar dayakeyi mata a yanzu......
*** *** ***
Duka ahali biyun rayuwarsu ta miƙa komai suna yinshine cikin farinciki da jin daɗi, akowacce rana ta duniya ƙara ƙaunar junansu suke, saidai muce  MASHA ALLAH.

*Alhamdulillah anan nakawo ƙarshen labarin SHU'UMIN NAMIJI ina fatan zakuyi aiki da abun dayake dai dai aciki, inda nayi kuskure kuma Allah Ubangiji yayafemin, nagode sosai da sosai masoyana, haƙiƙa kunbani haɗin kai nakuma ji daɗin haka Allah Yabar Ƙauna,   waƴanda na ɓatawa rai don Allah kuyi haƙuri, balaifina bane, haka labarin yake, haka kuma ƙaddaran  ZAID  da ZAHRAH yake, babu wanda ya isa sauya ƙaddaransa.

*Ku ci gaba da bibiyana Insha ALLAH Zakujini da labarai kala kala wanda ina da tabbacin zasuyi muku daɗi, Ina muku SON ƘAUNA!!!  Insha ALLAH Ina zuwa muku da wani sabon labarin wanda zai ɗare ma Shu'umin Namiji, ina kuma da tabbacin cewa zaku ji daɗinsa sosai.* 


*✔️OTE ME ON WATTPAD*
          @fatymasardauna

            *8/March/2020*


      *Taku Ako da Yaushe*
        fatymasardauna

         

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment